Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 12

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 12

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 12: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 12. Wani irin faduwa gabana yayi wnada ya saka ni ji kamar na juya da gudu, me ya kawo Ya Hafiz…

2,682 words

Wani irin faduwa gabana yayi wnada ya saka ni ji kamar na juya da gudu, me ya kawo Ya Hafiz inda nake aiki? Me ya kawo shi? Abinda zuciyata take ta tambayata kenan jikina yana rawa a hankali. "Shigo mana Malama Lubnah!" Ya fada yana murmushi, wani irin kuka ne yaso min, na shigo ina gaida headmistress, "Auta kin tashi lafiya!" Kasa nayi da kaina ina faɗin. "Alhamdulillahi Aunty Barakah." "Masha Allah, ga sabin dalibai ne aka kawo miki sai kuma Malam Hafiz yace yana son yasan Malamar domin dai fada mata yadda zata kula da Yaran " "tow!" Na fada muryana yana rawa. "Yawwa Madam na gode, ga Yaran Aliyu Hafiz Aliyu Jama'are, Asiyah Hafiz Aliyu Jama'are ." "A'a tsaya ba sai kai ne Ex dinta!" Inji Headmistress, murmushi yayi irin wanda ya saba yaudarar mutane da shi, ya ce mata. "Madam ba wani Ex raba mu Dole suka yi amma nasan Luluna tana sona!" "Aunty Barakah zan tafi Class idan ya gama ya kaai yaran!" Na aro jarumta nayi waje kafin ta samu damar sake wani Magana, ina tafiya amma bani da nutsuwa duk wnada ta ganni musamman yadda nake kallon office din Aunty Barakah zaka fahimci a tsorace nake, haka na isa ajin yaran suka gaishe ni na amsa tare da zama ina sauke numfashi, daya daga cikin Yaran da suke me suna Munir ya kawo min ruwa da gudu, ya mika min. Murmushi nayi na nuna mishi nawa, murmushi yayi na ce mishi. "Je ka zauna na gode!" Komawa yayi ya zauna na fara kiran sunansu, ina cikin kiran Ya Hafiz ya iso class din, tare da Yaransa ni dai ban d'ago kai na kalle shi ba, haka na cigaba da aikina ina kiran sunan Yaran. Yadda yazo ya min rumfa a kaina ya janyo min wani irin tashin hankali da tsoro uwa Uba jikina wani irin rawa yake. "Luluna, nayi kewarki ina bukatarki sosai ina jin kewar kome naki, ina jin kewar can ƙasarki me jekewa jabga!" Wani irin mikewa nayi jikina yana wani irin rawa. Na fara ja da baya, yana takowa har sai da ya kure ni a bangon. " Ki dawo ko kuma na saka miki abinda zai saka ki dawo dole!" Yadda yayi magana yasa ni durkusawa a wurin tare da toshe kunnena. A tsorace hawaye na zuba min ashe ina murna na rabu da shi ashe zai dawo innalillahi wainnalihir rajoun, Ya Allah me nayi da zafi haka, fita yayi ya bar Yaran suna ta min dariya, ni dai ban kula ba bayan fitarsu na ji kaina yana amsawa da dariyarsu, daurewa nayi na fara koyarwa a lokacin Yaron nan ya fara kuka, wato Yasir, kuka irin me d'aga hankali sai ji nayi kaina kamar zai fita shi dai a kai shi Yusrah. Ranar Yaron nan da ya saka ni a gaba da kuka, sai da naji kamar zan yi hauka. Haka ya Hafiz yake zuwa yayi ta min rashin mutunci, idan ta kama kamar dai rufe ni da duka a gaban jama'a, da yake gaya musu ya mayar da ni, yan uwana suka zuga ni, a hankali sai damuwar da na rabu da ita ya fara dawowa, na kasa fadawa kowa domin ya tabbatar min duk ranar da aka kira shi aka mishi magana wallahi zai dauke ni a nime ni a rasa wannan yasa Ya Hafiz ya sake dawowa Rayuwata, kamar zan yi hauka rashin mutunci sai wanda ya karu.

A hankali na fara kin zuwa aikin sai dai na kwanta idan kuma zan fita zan tafi wurin Aunty Hindatu ko aunty Innah, idan suka tambaye ni me yasa ban tafi aiki na sai naki basu amsar tambayoyinsu. Ranar dai Headmistress ta kira Aunty Innah tace kusan sati biyu ban zo makaranta ba, Aunty Innah tayi ta fada ta kira Ya Ado ta gaya mishi, kai tsaye ya ce mata. "Lubnah ba zata ki zuwa makarantar ba, akwai wani abu da yake faruwa. Ta je zan tura Sani ya bi bayanta ya kuma yi min bincike idan da wani abu ya gaya min."

Haka ta kira ni ta ce na shirya na tafi, kuka ne ya zo min tsoro da fargaba ya cika ni, domin kullum sai kira ni da barazanar sai ya dauke ni ko ya kashe ni kowa ya rasa, tunda naki na zo makarantar. Haka yasa na shirya ina kuka na tafi, ina isa wurin parking na fita daga motar sai gashi, yadda ya juyar da ni yayi ta kifa min mari, Malamai maza suka zo ya daka musu tsawa tare da kwatar key motar ya bude zai saka ni, Ya Sani ya rufe shi da duka, wani irin dambe suka kama yi, na shiga motar na rufe kaina ina kerma. Dole Headmistress ta kira Aunty Innah tare da gaya mata abinda yake faruwa, ita kuma ta kira Ya Umar daga muda lawan suka nufo makaranta lokacin an samu an raba fadar da kyar, Ya Sani yana faɗin. "Kai uban waye ya tsaya maka a Bauchi shege bagidaje, ka kuma taba Lubabatu sai na karya maka hannu."

"Wallahi idan ina raye Lubnah ba zata tab'a samun peace of mind ba, matuƙar ina numfashi, sai dai ta ga wasu mazan da idanu, amma wallahi babu namijin da ya isa samunta, gara ta kare rayuwarta a matsayin karuwa!" Zuwan Ya Umar da Yan sanda yasa aka kama ya Hafiz ni kuwa Aunty Hindatu tana zuwa a hankali na saka kafa na fito, wani duhu ne ya lullube min ganina, a wurin na zube sumammiya.

Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai bayan wani lokaci, na farka na ga Yadiko tana zaune suna hira. "Yar iska munafuka ta koma wurin Uwarta ban isa ba, ni ina nan ina tausayin Jalilah ashe ita ta gaya masa har inda Lubnah take, kai hatta number Lubnah munafuka ita ta bashi, nayi mamakin ashe duk abinda yayi ta faruwa tana sane da ita Hafiz yake hada baki a cutar da ita me Lubnah tayi mata? Ai Sani ya so zane ta, na ce ya kyale ta ta ji Allah zai mata sakayya mene ne a cikin duniyar wanda Lubnah bata gani ba, Allah yasa haka ne mafi alkhairi, zaman Bauchi ya kare itama Lubnan ta bar Bauchi hala wani arzikin ne yake nimanta!" Inji Yadiko tana fada kallon yadda na tashi a hankali, ina kuma zan tafi? Na gaji na gaji da rayuwar da nake ji nake kamar rayuwata tafi buƙatar mutuwa da wannan rayuwar, na rasa yadda zan yi da kome baya min dadi, sai da nayi alwala na fito na gabatar da sallah azhar da asar, ina idarwa Yadiko ta tura min abinci, kallon abincin nake ina kallonshi kamar naga sabon abu, haka nayi ta kallon abincin. "Ci abinci Auta!" Haka na dauki cokalin na dibi jollop din macaroni na kai bakina, ina ci hawaye na zuba min. "Ba zan hana ki kuka ba, domin lokacin da kika so fahimce ki mun kasa fahimtar ki, yanzu kuwa da muka fahimce ki ba zamu hana ki kuka ba." Haka yasa na dan ture abincin na cigaba da kukana, shigowar Ya Tahir yana waya. " Yawwa gata ta farka bari na bata. " Mika min wayar yayi, na dauka ina shashekar kuka. " Lulu" " bana son sunan nan" na fada a sanyayye. " Lily fa! " Sauke kukan nayi a hankali na ce mishi" Ya Ado!" " Na saka Innah su hada miki kayanki, in sha Allah zan miki booking flight nan da yan kwanaki, am sorry bana nan amma nasan Attahiru da Umar da Sani sun yi duk abinda zan yi, Lily i promise you in sha Allah daga lokacin da kika dawo wurina ba zaa ki sake samun wani threat daga wani ko ayi bullied dinki ba zan tab'a bari ba. Zan zame miki Abba zan zame miki Mama zan zame miki kowa naki, ba zaki kara kuka ba. " Sai ga hawaye wannan nabin wannan, sharewa nake. " Ba zai kuma sanin inda kike ba, kai ko takowa ba zai kara ba, in sha Allah ba zaki kara kuka ba. Lily na gaya miki in sha Allah. " Kukan da nake yi ne ya sa ya kashe wayar. " Ya Tahir ni daya ce mace da Ya Hafiz ba zai kyale ba? Me nayi haka da wannan sharrin yake bibiyarta rayuwata?" Murmushi Yadiko tayi tana faɗin. " Baki yi kome ba, sai kara samun kusanci da Ubangiji, ai ba kowa Allah yake jarabta ba dai me imani da tawwakali, Allah yana son bayinsa masu hakuri da takawwa, Allah yana son bayinsa masu yarda da imani da shi, idan kika amshi ragamar ƙaddararki Allah zai miki musaya da abinda yafi alkhairi. Allah zai baki miji na.. " "A'a Yadiko bar kiran wani mijin tsoro nake ji, tsoro nake ji zan iya mutuwa idan naji wannan kalmar! " Na fada ina cusa kaina cikin cinyoyina. Jikina rawa yake kamar an kunna min lantarki, iya Ya Hafiz da nasan halinsa ma ban sha ta dadi ba balle wani da ban san shi ba. Na rantse da Allah gara a gaya min ranar mutuwata da sunan da namiji, gara na ga mutuwata. Namiji ya shayar dani mamaki namiji ya kashe min duk wani jin dadin rayuwa, mace babu da babu bari ai da ciwo Yaya suna cikin abinda Allah ya bada na jin dadin rayuwar duniya. Amma ni Ya Hafiz ya kashe min wannan jin daɗin, waye zai zauna da ni bana haihuwa waye zai yarda ya zauna da ni da cutar hauka, bayan ya Hafiz ya cusa min damuwa a raina. Ni a kan kaina na tsani kaina ba zan ina tsayawa kaina ba, taya xan amshi kaina.

Wannan kukan da nake ya dami Ya Tahir don haka ya fita. *** A can office din Yan sanda Baban Bauchi da kanshi ya je yayi belin Hafiz, fuskarshi babu walwala ya ce mishi. "Shin baka yarda da abinda na ce maka ba ne? Ba na ce ka kyale ta na wani lokaci zan duba lamarinka ba ne? Me yasa abinda ba ka yi yanzu ka fara? Na gaya maka ko Lubnah zata mutu a gidanka zata mutu wato ban isa nace kayi abu ba kenan? " Ƙasa yayi da kai yana faɗin. " Ba haka bane, Allah ya gani ina son Lubnah, Kuma ban mata haka da wata manufa ba, Sani ne kawai ya kama ni da dambe, wallahi ba zan iya cutar da ita ba. Bayan ina son raunin baya ya warke don Allah ka yi hakuri ba zan kara magana ba sai ranar da ka min magana in sha Allah. " Har zuwa yau Abba bai ga gundarin laifin da Hafiz yayi asalima gani yake kamar sharri ne da an fi karfinka, sannan kunyar dan uwansa da amshi case ɗin a hannunsa, sannan baya son dan uwansa ya hango gazawarsa akan Yaransa wato shi ya iya tankwara Hafiz amma shi kuma nashi Yaransa sun fi karfinsa, haka yasa ya zuba musu idanun su gama abinda zasu karshe dare daya Lubnah ta koma dakinta ko tana so ko bata so, shi ba zaa zubar mishi da zumunci a karon iska ba da darajarshi da kimarsa Yara da Matarshi suna juya shi, ba zai dauka ba. Ace kamar shi sai yadda aka yi da shi. "Muje ka ajiye ni a gida." Haka kuwa ya wuce gaba zuwa inda motar Abba yake, don da zai zo ya kira Sani akan yazo ya tuka shi, sai gashi ya ce mishi ai baya gari yana can hanyar Jos dan banza yana nan bai je ko ina ba yana asibiti.

Haka yasa ya tuko kanshi zuwa office din Yan sanda, ya je yayi belinsa, haka ya tuko Abba zuwa gida, a lokacin ya samu Umar ya kawo yadiko yana mai dauke da basket din Abinci, a hankali Mama ta fito tana kallon Abba ganinsu tare da . Hafiz yasa ta wuce bata kalli inda yake ba, sama sama Umar ya gaida Abba din ya budewa Mama mota. "Ina zaki Salamatu!" "Asibiti wurin Lubnah!" "Da izinin waye?" "Ai bana jiranka akan Lubnah, ka zabi abinda kake so, nima na zabi abinda nake so ai ba kuskure ba ne? Muje Umar." Tana shiga motar Umar ya shiga tashi motar suka bar gidan.

Bayan fitarsu Hafiz ya shiga tashin hankali, kamar yayi kuka yake kallon kasa. "Abba kayi hakuri amma ba zan iya rayuwa babu babu Lubnah ba, gara na mutu da na rasata!" "In sha Allah ba zaka rasata ba." Ya fada yana kara tausayin Hafiz domin har ga Allah tausayin Hafiz din. Dakyar ya shigar da shi cikin gidan. Bai iya cin abincin da aka bashi ba, kanshi a sunkuye kamar zai yi kuka ya rasa yadda aka yi har yayi shirme haka. * Ajiyar zuciya na sauke lokacin da nake kallon Mama yadda ta zuba min abinci tare da ita, ina murmushi nayi tana bani ina murmushi. " Mama nifa ina kishin yarinyar nan!" Inji Sani, ya fada yana hararata. " Mama ka kalli yadda yake wani hura hanci!" Murmushi tayi tana faɗin." Sani na, kyaleta tayi maka shigar sauri."

A hankali yake murmushi ya dauki spoon ya fara bani abincin shima Mama tana bashi, shigowa Aunty Innah tayi tana faɗin. " Ikon Allah yau naga abinda ya ture turatu uwar Turanci a ramin tururuwa, ok nima bari na shiga." Ta dauki spoon ta fara ci, a hankali tana mai diba itama ta bani, Ya Sani ya bata. Turo kofar da Aunty Hindatu tayi tana faɗin. "Cin amana a jinin gidan Baba Malam Umaru yake oya ku matsa min." Haka yasa ta zauna ta fara ci itama kafin ta kai loma sai da ta fara bani, Aunty Innah ta bata.

Bayan mun gama Aunty Innah ta ce mana."an sallame ki yar nan!" "Na gode sosai." Haka muka shiga tattara kayanmu dama ba wani kaya ba, gidan Ya Tahir na koma,

A can gidan kuwa sai ga Hajiya Asiyah tazo Ita da su Aunty Nana Asma'u. Kwanansu daya suka roki Abba ya basu damar ganina ya ce su sami Yadiko, haka ya gayawa Mama. Mama kuwa ta ce musu. "Kunzo ku kara sa min ita ne?" "A'a zamu bata hakuri tayi hakuri Hafiz ya gane!" "Ya bita makaranta ya rufe da duka ko?" "Amma ai Alhaji yace zata koma!" Inji Hajiya tana murmushi. "Murmushi Mama itama tayi ta ce mata. " Ba mamaki idan na fitar da gawata Lubabatu zata koma gidan Hafiz kamar yadda ya ce ta haramtawa wa wani da namiji in sha Allah ya haramta mishi. Idan kina ganin karya ne ki same shi ki ce ni Salamatu Galadima nace Lubabatuna ta haramtawa Hafiz ya ce bata haramta ba." Yadda take d'aga murya shi kanshi Baban Bauchi yana ji amma ba yadda ya iya ta kara da cewa. " Ni ba haifi lubnah kuma naga wanda ya isa mata dole! Wallahi tun daga karamin kotu har babban kotu sai an jimu da shi, ku fita kafin na haukace muku lokacin da kuke musguna mata kun manta tana da uwa ko? Kun zata kowa haka yake, ke baki ji kunya ba ita da take juya zaki biyo ai Lubabatuna ta gama da danku sai dai wani ba shi ba." Ba sai ga gagarumin rigima kai karshe suka dauki ai Hafiz bai sake ni ba, magana har kotu, abinda ya kara lalata lamarin.

Kamar yadda Ya Ado ya ce, ranar da yasa Yayuna maza da mata suka raka Jos tare da rakiyar Mama, haka nayi ta kuka da xan shiga jirgin. Na k'amk'ame Mama ina kuka.suna tsaye har jirginmu ya tashi, daga nan suka wuce gidan Aunty Raliya, taji haushi tayi ta mita suna sallah la'asar suka baro Jos. Nan suka sami bugun Bala'i da masifa na Baba Malam ya ce shi ya bada umarnin a mai da auren Lubnah Mama kuwa ta ce babu mahalukin da isa wannan aikin rigimar da ta kaure har Abba ya ce mata.. "Sai ki zaba aurenki ko Na Lubnah domin ba gaji da lalata min zumunta da kuke da sunan kuna bayan Lubnan?.........

Alhamdulillahi bakiɗaya anan na kawo karshen Free pages. *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 18

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull