Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 13

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 13

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 13: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 13. Lagos Mun bar Jos karfe biyu da rabi, karfe hudu cib muka sauka. Garin yayi wani irin yanayi…

4,485 words

Lagos Mun bar Jos karfe biyu da rabi, karfe hudu cib muka sauka. Garin yayi wani irin yanayi na alamar da ayi ruwan sama. Tun daga Murtala Muhammad International airport na shaki kyakyawar iskar da babu hadi a cikinta. A hankali nake takawa ina jin kamar an sauya ni rayuwata ƙaddarata. A yadda na fahimci mutanen garin kowa akan kafarshi yake, yadda suke kujiba-kujiba. D'ago kai nayi ina niman Ya Ado, daga can nesa na hango shi a wurin Arrived, da dan sassarfa na isa babban wurin taruwan baki tare da masu barin kasar da komawa jahohinsu. "Lubnah" ya d'aga min hannu, murmushi nayi wanda kana gani kasan yake ne. Hannu ya mika min na isa gare shi ya ɗan rungume ni, irin side hug din, sannan muka jira kayana ya iso, ya tambaye ni ba gaya mishi sannan ya dauko min. Ya riko hannuna yana faɗin. "Welcome to lagos!" Yake nayi har muka shiga mota, ina zaune kamar wata bakuwa, duk na kasa sake jiki da shi. Haka muka bar airport din minti goma sha biyar ya kai mu estate din da Ya Ado yake zaune. Royal Garden Estate, close alausa Mitv, alausa Ikeja. A kofar wani gida me kyau muka yi parking, ya kalle ni a hankali ya ce min.. "welcome to home!" Murmushi nayi na bude kofar na fito ina kallon yadda tsarin kowani gida yake ba kamar mu nan arewa ba, karya ka yi parking a kofar gidanka, aka bi motar har cikin gidan ma aka dauke. Sai naji na samu nutswa musamman da garin yake hade rai, alamar zasu sha ruwa don gari ne na ruwa. "Sweet haka muje ko?" Gyada kai nayi na bi bayansa da yar karamar hand bag dina, har muka shiga cikin gidan. Aunty Zakiya ta zo ta rungume ni hannunta dauke da ludayin miya. "Baby sai yanzu ka dawo, Auta barka da zuwa welcome to home!" Murmushi nayi ina kallonta. "Muje na nuna miki dakinki a sama!" Kallon stair din nayi na kalle su a hankali na ce musu. "Na gode!" "Never mind!" Muka haura saman, dakin farko aka bude min. Juyawa nayi na kalle su a hankali na furta da cewa. "Tsarki ya tabbata ga Allah gwanin da babu irinsa!" Ba don kome ba sai don yadda aka tsara min dakin sai nake gani kamar ban cancanci zama a dakin ba. "Shigo dakinki ne, bamu gama gyara dakin ba amma ki yi maneji kafin a gama!" Gyada kai nayi ina faɗin. "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi." Ban daki ta bude tana faɗin. " Look at the toilet yayi miki? " Gyada kai nayi ina kallon ban dakin. " Shi kenan bari na karasa abinci, sai ki yi wanka da sallah muna jiranki. " Gyada kai nayi, na zauna bayan fitarta na cire kayan da zan saka na shiga nayi wanka da Alwala na fito, nayi ta kallon inda zan fahimci gabas ne, turo kofar Ya Ado yayi yana faɗin." Jikina ya bani kina niman alkibla!" Karamin murmushi nayi ya nuna min gaban gadon." Shimfida abin sallah nayi na gabatar da sallah asar sannan na zauna a wurin ina addu'a. Bayan na idar ne na sauya kaya riga da zani na daura, sannan na cigaba da zama a wurin na tsunduma cikin tunani, wanda ni kaina ban san me nake tunawa ba, ni dai na b'ata shiru. Turo kofar dakin aka yi ta zuba min idanu. Juyawa tayi ta sauko kasa, ta ce mishi. "SAN kazo don Allah!" "Wani abu ne?" Ya tambaye ta yana mikewa da sauri, "just come!" Ta fada tana haurawa. Haka suka nufo dakin ya shiga ya ja stool ya zauna a gabana har lokacin ban san sun shigo ba. Itama zuwa tayi ta zauna a gefena. "Lubnah!" Ya kira sunana, ban amsa ba, ya kara kiran sunana a karo na biyu, shima shiru dafa ni yayi, na wani irin zabura tare da fasa ihu. Rungume ni Aunty Zakiya tayi tana faɗin. "Sorry Baby girl we're here!" Ta fada tana shafa bayana, kuka na fashe da shi, tayi ta shafa bayana tana faɗin. "Ya isa haka, muna nan babu me cutar da ke!" "Tsoro nake ji, ina jin tsoro! Don Allah ku boye ni!" Har lokacin shafa bayana take tana faɗin. "Wanda zai cutar ke, you in safe place. Daga ni har SAN ba zaku bari wani ya tab'a ki ba!" Mikewa Ya Ado yayi ya ce mata. "Doctor ina son ki mana booking ganin neurologist please!" "In sha Allah, SAN!" Haka tayi ta bubuga bayana, har nayi shiru karshe dai barci ne yayi gaba da ni, ta kwantar da ni. Sai da ta gyara min kwanciya lokacin Yaran gidan sun dawo daga makaranta, har sun fara ihu ta ja su zuwa daki ta zaunar dasu. "Aunty Lubnah tazo, and please bata son ihu ko hayaniya, yana iya dakata faint ko tayi loser control, please ku zama good children, kunji ban da fada Ummu Salma, Adil kai ne Babba kada ka yarda su saka ka magana. Prince kada ki yi ihu ko kukan banza kin ji! " " Mommy me ya same ta? " " Bata da lafiya ne idan kuka yi sallah ku saka ta cikin addu'arku ko?!" Gyada mata kai suka yi, suka fito bayan sun sauya kaya. Yaransu uku ne Adil sunansa Usman sunan Abba, sai Ummu Salma me sunan Mama. Sai Princess me sunan Maman Aunty Zakiya wato Hauwa'u. Aunty Zakiya da Ya Ado sun hadu a BUK ne, kusan shekarar shi biyu da fara karatu ta shiga a lokacin ta samu medicine ne, wani abun da nake son a sani Aunty Zakiya Bajara ce daga Dass, iyayenta yan boko ne, sosai sannan tana da yayu maza da mata, a lokacin da suka hadu har magana tayi nisa Abba yaki auren, Baban Jama'are ne ya tsaya aka yi kome, domin a lokacin shi Abba Aunty Nana Asma'u yaso Ya Ado ya aura, amma yaki aka yi ta rigima, Baban Jama'are ne ya kashe maganar bayan ya gaya mishi ai Nana Asma'u tana da wanda take so da wannan aka kashe rigimar, itama Aunty Zakiya kamar tasan an yi wannan rikicin, ita da danginta da aka fara zancen auren sun tsaya sosai kuma sun yi abinda ya dace duk wasu iyayen zasu yi akan Yarsu. Sun nuna mata fada da gaya mata gaskiya. Ta rike su a matsayin nata, tayi kuma hakuri da kome. Haka kuwa aka yi ta zo gidan a matsayin wacce bamu amshe ta ba, saboda Abba ya nuna bata mishi ba. Amma wani ikon Allah ba a shekara ba sai gashi da kanmu muke sonta. Tana da wani irin kyawawan halayen da sai ka ji kana matuƙar kaunarta, a lokacin da aka yi aurensu Ya Ado saro kaya yake yana turowa shagon Abba, a lokacin duk yan makarantasu gani suke kamar ya cika zakewa akan niman kudi, idan aka ce musu dan Bauchi ne. Sai su ce dama yan Bauchi suna kasuwanci haka, domin da kanshi yake shiga kwari yayi sayayya ya cika manyan motoci a turo Bauchi, dayawa idan aka ce musu dan Bauchi ne sai su ce a'a ba dai yan Bauchi ba, domin basu damu da kasuwanci haka ba. A lokacin Ya Tahir yana da shagon provision haka dai shiga singa ya mishi sayayya ya turo mishi. Koda ya gama karatunsa, sai da suka tura shi school of law Lagos, ya shekara daya. Bayan ya dawo ya tafi service na wata tara, sannan ya dawo BUK a lokacin itama tana gab da gama karatu, a shekarar aka haifi Adil, wanda yadiko da kanta ta zo Kano ta zauna da ita, da har Iyayenta suna damuwa da maganar tazo wanka gida, sai suka ji labarin Yadiko tana nan, abin da yasa Abba ya sauko ya bar Yadiko tazo, don jin Haihuwar da namiji aka yi kuma Ya Ado ya gaya mishi sunansa yayi masa huduba da shi, itama kuma ta tabbatar da haka. Tare da mishi Alkunya da adil. Sai take ta tara mishi nauyi da kunyarta, musamman yadda yake share ta, idan ta zo gaishe shi yayi kamar bai ji ba, wannan soyayyar da ya wayi gari da shi akan Jikansa na farko ya matuƙar amfani iyayen, domin a Bauchi ma har walima aka yi na sunan Usman Adil Adam Usman. Yadiko bata bar Kano ba sai da suka yi kwanaki Hamsin haka Abba ya ce tayi, sannan da zata dawo Ya Ado da ita Aunty Zakiya suka mata shatara na arziki kasancewar tana da jarabawa, yasa bata zo ba sai da Yaron ya cika wata biyu da rabi, sannan suka zo ganin gida. Tunda suka iso dutsen tanshi, Abba ya dauki Yaron ya lullube a wurinsa sai nono da wanka kawai ke sakawa ya bada yaron ko idan zai tafi central. Wannan kaunar yasa ita uwar Yaron bata wani saka yaron a ranta ba, haka da ta tafi gida da Yaron Abba kullum sai saka Mama ta kira ta, a saka mishi muryan Yaron, dan wata biyu iyayenta da dangin sun fi kowa farin ciki, da tayi kwanaki zata koma suka hada mata kaya har da na su Mama da Abba aka hada mishi zuma da zabi aka kawo musu anan fa ta kara daraja da kima. Adil na shekara daya a duniya ta fara service inda aka tura ta Niger minna, ai kuwa ta kai Adil wurinsu Mama ta tafi service dinta inda zata yi sati uku ta dawo Kano ta karasa domin mijinta yana ta shige da fice akan haka. Yaro kan da ya saba da ganin Abba don haka kawai zai bushi iska ya zo kano ganin Adil kada ku manta yana da wasu jikokin na Yara mata amma shi wannan gani yake kamar na shine bakiɗaya, yaron ma ya saba da shi. Ai kuwa shekarar da aka kawo shi Abba ya tafi da shi Umara, saboda gata da soyayya. Iyayen Yaron hakura suka yi suka barwa Abba Yaron. Har suka gama karatunsu. Kwatsam Ya ado ya samu aiki a Abuja yana can ita tana aiki a Bauchi, Allah ya kara mishi wani nasibi a lokacin tana goyon Ummu Salmah, a shekarar suka koma Lagos domin wani Shari'a yayi kuma yayi nasara, sai gashi cikin ikon Allah suna ta gaba a Lagos itama tayi master dinta, wnada ya kara d'aga darajarsu. Abba ya basu dansu domin zai fi dacewa su daura shi yadda suke so. Shekararsu daya a lagos ta haifi Princess, yanzu shekarar su biyar kenan. Bayan sun ci abinci, suka yi sallah Magariba, sai a lokacin Ya Ado ya zo ta tashe ni. Bayan na farka na bude idanuna addu'a nayi sannan na tashi na shiga ban daki, nayi alwala nazo na gabatar da sallah Magariba, ina idarwa Aunty Zakiya ta shigo tana waya. "Gata nan Hindatu kada ki fasa min dodon kunnena." Ta fada tana murmushi. Mika min wayar tayi tana faɗin. "Gashi idan kin gama muna jiranki a kasa zamu ci abinci." Karban wayar nayi ina kallon kasa. " Auta kin isa lafiya? Na kira dazun wai kina barci. " Inji Aunty Hindatu, " Eh ban jima da farkawa ba!" Na fada a sanyayye. " Ya kika ga garin? Yayi miki ko? " Ko bai min ba dole na amsa da dai na cigaba da zama a Bauchi Ya Hafiz yana min barazanar zai sace ni. " Yayi min! " Na furta a hankali, ina wasa da bakin hijab din jikina. " Auta ki saki jikinki kin ji ko." " Ehmm! " Nace mata bayan nan shiru nayi, , Ya Ado yace zaki fara ganin likita ko?" Shima sai da nayi shiru kafin nace mata. " Amma ai lafiyata lau." "Eh lafiyarki lau kai, amma ana son ki ga likita da kyau." Shiru nayi ina jin yadda take ta bayani da ta fahimci ba zan iya cewa kome ba, sai ta kyale ni. " Auta ki tafi ki ci abinci!" " Tow sai da safe."nace mata ina me kashe ki wayar, na nufi hanyar waje, suna ta hira sama-sama cikin nishadi da jin dadi, haka ma sauko na gaishe da Ya Ado da Aunty Zakiya, yaran suka gaishe ni yadda na amsa musu yasa suka fara kallon iyayen, har yanzu akwai rashin sabo a tare da ni, izuwa yanzu ban san yadda zan gyara kaina na fahimci mutanen da suke gefena ba, tsoro nake ji kada a kwana biyu su juya min baya. A hankali na zauna Aunty Zakiya ta saka min abinci, ta ce min. " A kara miki ne! " Kallon abincin da ta zuba min nake ina tunanin. "Auta lafiya? Tana magana baki ce kome ba." "Abincin zata rage yayi yawa!" Na fada muryana yana rawa. "A'a bai su yawa ba, kici kawai idan zaki kara sai a kara miki ba." Kalaman Ya Hafiz ne suka shiga yawo a kaina. _Jaka sai aikin ci ba haihuwa! Dama a jaka ya dace ki zo ba a mace ba, jakar ma mara haihuwa_ da sauri na tura mata nace mata. "Don Allah ki rage!" Haka ta rage rabin abincin, shima ban iya ci a gabansu ba, juya abincin nake ina kallon yadda suke ci, tashi Ya Ado yayi ya dauki plat din ya riko hannuna muka bar parlourn dakina ya mai da ni, sannan ya ajiye min abincin a gabana. "Zauna ki ci!" Ba musu na fara ci ina kallon kofar da ya fita, kafin ya kawo min ruwa na cinye abincin kuma ban koshi ba, ajiye min ruwan yayi ya je ya karo abincin ya zo ya ajiye min. "Bana son kina zama alone ne amma na fahimci kafin ki saba da mutane zaki dauki lokaci." Shiru nayi haka ya juya ya fita na zauna naci abincin sosai. Daga nan na dawo hayacina na tashi na wanke hannuna, na tattara kayan na sauko da shi kasa. Yaran suna parlourn babu wanda ya kula ni, ni tun kan su Yusrah tsoron yara nake, haka gidan Ya Tahir Yaransa basu hayaniya idan ina gidan. Shiga kitchen nayi na ajiye kayan abincin. "Hi" gabana ne ya fadi, na juya a hankali Princess ce, mika min hannu tayi ta ce min. "Zamu iya zama abokai?" Yadda take kallona yasa na dan durkusa na ce mata. "To!" Na mika mata hannu, kamar yadda ta mika min, sannan na sake hannunta na wuce hanyar sama. Tunda na koma sallah isha nayi, na kwanta tunawa nayi na dauko magani na sha, sannan na kwanta a hankali. Tunani mai zurfi nake a sannu sannu barci yayi gaba da ni, daga nan ban kara sanin me nake ciki. Ya Ado "Dr kina nufin ba zan samu ganin shi ba kenan?" Kallonshi tayi ta ce mishi. "SAN baya gari ne, da yana nan da na gaya maka. " Shiru yayi yana kallon laptop dinsa, "ina son na ga ta fara ganin likita duk da tana da maganin da take sha amma yana da kyau ta kara ganin wani likitan, zuciya tayi rauni akan Lulu, duk halin da take ciki mune muka jefata a cikinsa." " Ubangiji ya bata lafiya. Ya bamu ikon kula da ita. " " Amin Ya Allah! " Ya fada yana cigaba da aikin da yake, tana gajiya ta kwanta ta barshi a wurin. Ya Ado kasungurmin lauya ne, wanda idan har ka kawo case wurinsa. Tow fa matukar kaina ne da gaskiya magana ya ƙare, bai cika amsar case ɗin da aka yi zalinci ba, haka yasa ya kara zama wani gwaska. Wurin karfe biyu na dare, ya kashe laptop din. Sannan ya shiga ban daki yayi uzurinsa ya fito, sannan ya ji kai bari ya leka Yaran da kuma Lubnah. Haka ya leka dakin yara ya kara musu addu'a sannan ya wuce dakin Lubnah ya same tana shasheka tare da zabura, kamar zata farka sai motsi take, juyawa yayi ta fita ya jira Matarshi wacce tayi nisa a cikin barci haka suka shigo dakin tana hamma. Zama tayi a gefen gadon tana shafa fuskar Lubnah. "Ya Isa haka you safe Lubnah." Yadda take shafa kanta tare da magana a hankali, har ta bude idanu wanda suka yi ja saboda yadda take mafarki ganin Ya Ado a tsaye yasa ta razana tare da fashe da wani irin kuka. K'amk'ame Aunty Zakiya nayi tare da boye fuskana jikinta, jikina yana rawa. Abin ne da ciwo irin wannan sai anyi da gaske kafin mutum ya manta da shi. Matsowa yayi na kara k'amk'ame ta. "Ka tafi zan zauna da ita har ta koma!" Fita yayi jikinshi a sanyayye, yana jin wani irin yanayi yana saukar mishi. Ina jikin Aunty Zakiya har wani lokaci. " Ya isa haka, tashi ki yi alwala sai ki yi sallah kin ji." Haka na mike na shiga ban daki nayi alwala sannan na fito na samu ta shimfida min abin sallah.

Wannan sai da ta ga na fara sallah, sannan ta bar dakin bayan na idar ta shigo ta same ni a wurin da nayi sallah na kwanta ina barci, janyo bargo tayi ta lullube ni, ban san me yasa tayi haka ba.. ko kuma tana tunanin idan na farka ba zan iya komawa ba ne, haka yasa na cigaba da barci a wurin.

Duk yadda naso na cire Ya Hafiz na kasa, domin ko yaya na kwanta sai nayi mafarkin Ya Hafiz da irin azabar da yake shirin min, haka yasa na kasa yarda da kaina balle kowa. Sannan zuciyata tana raya min Hafiz sai zo gare ni.

Washi gari da sassafe na farka na fara yin Sallah, wanka na yi sannan na duba jakata na dauki magani na sha, turo kofar aka yi na kalli me shigowa. "Lubnah!" Ya Ado ya kira sunana, "Na'am!" Na amsa mishi, shigowa yayi da mug a hannunsa ya janyo stool ya zauna, yana me mika min kofin. Amsa nayi ina kallonshi. " Na gode!" Na furta a hankali, zuba maganin nayi a bakina na sha a ruwan tea din. Sannan na rike kofin ina kallon kofin. "Naso muje ganin likita yau!" Kafe shi nayi da idanu, kafin na cigaba da kurban tea din ya cigaba da cewa. "Amma likitan baya nan, gashi zamu tafi aiki zaki iya zama a cikin gidan nan ke daya ko?" Gyada kai nayi ina ajiye kofin a gefe guda....... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: SHA TARA

"Me yasa sai na ga likitan to?" Na tambaye shi a hankali, ina dan karce farcen hannuna, ban damu da zafin da nake ji ba. Ni kaina ban san lokacin da na zama haka ba. "Saboda ki samu nutswa da kwanciyar hankali zaki ga likitan ƙwaƙwalwa." "Na haukace ne?" Kalaman Ya Hafiz ne suka dawo min. *Ki dawo gare ni, ni daya ne ba zan cigaba da miki kallon abar tausayi kuma mahaukaciya ba! Amma duk wanda zai zauna dake kallon mahaukaciya zai na miki* da sauri na kalli Ya Ado, "kana min kallon mahaukaciya ce?" "A'a ko daya bana miki kallon haka."

Kin yarda nayi na fashe da kuka, Ya Hafiz yayi gaskiya tun a Bauchi nake kallon yadda kowa yake min kallon tausayi ko kallon wance rayuwarta ya ƙare, haka nayi ta kuka tabbas ina jin ciwo amma ban san yadda zan fitar da zafin ba. Dakyar ya rarrashe ni sannan ya fita, kasancewar maganin akwai na barci tunda na kwanta har suka fita ban sani ba, sai farkawa nayi na ga yar karama not a gefen tiren abincin.. *Idan kin farka ki karya sai ki sauko akwai me aiki tana zuwa mana aiki sunanta Yemi tana nan Please ki karya kin ji* SAN Adamu U.U Jama'are. A hankali na wanke bakina na zo na karya lokacin karfe daya saura, sannan nayi wanka na sauya kaya na fito parlourn kasa, mai aikin ce tana ta aiki a kitchen din. Lekata nayi ma ga tana faman kwashe abinci a cikin kular. "Good Afternoon Ma!" Ta gaishe ni, gyada kai nayi ina amsa mata a hankali. Barin kofar nayi na dawo parlourn na zauna a kujeran, lekowa tayi ta ga ina zaune amma na kurawa tv parlourn idanun kuma ba a kunna ba, tana fitowa ta kunna. Sannan ta koma wurin karfe biyu ta fito tana fadin.. "Zan koma sai an jima!" Gyada mata kai nayi, ta fita na koma na kwanta sai lokacin na nufi zan kwanta na manta ana kashe tv don haka na saka kai zan fita daga tv aka ce. "Kin zata zaki iya gudu ne?" Da harshen turanci. Domin film din da turanci ake yi amma sai tunanin da nake na Ya Hafiz ya juye min irin muryansa. "Nace kin zata zaki iya guduwa ne? Kin dauka idan kika gudu ba zan iya samo ki bane? " Yadda na tsaya jikina yana rawa na kasa juyawa gani nake kamar yana bayana. Hawaye ne ya shiga zubo min a hankali na ji motsin takunshi har har gabana.Wani irin rikicewa nayi tare da zubewa a kasa ina jin kamar zuciyata zata fita. Kukan da nake naji ya makale sakamakon ce min da yayi. "Shiiiiii!" Hadiye yawun bakina nayi tare da rintsa idanuna, ina me saka hannu bibbiyu na kare fuskata. "Ya isa haka, bar kuka na gaya miki duk inda kika shiga zan binciko ai, ya isa bar kukan nan ko sai na mare ki ne?" Ya fada da karfi, ja da baya bayi ya mike tare da zare belt din jikin wandonsa, ya d'aga belt din zai zuga min na fasa wata irin kara me firgitawa, wanda yayi daidai da shigowar Ya Ado yayi mantawa ne ya dawo gidan. Ganin halin da nake ciki yasa shi isowa gare ni, duk na firgita na fita hayancina sai ihu nake, yayi maza ya rungume ni. "Ya Isa Lubnah ya isa haka. Gani nan Yaya Adamu ne, ya isa bar tsoron haka gani nan a tare da ke. " Kara rungume shi nayi tare da kifa kaina a gefen kafad'arshi, ina faɗin." Ya nimo ni, wallahi na ganshi." Wayarshi ya cire daga aljuhun rigarshi ya shiga kira da shi. " Doctor ba wani likita ne?" Daga can ta ce mishi. " Yanzu nake son kiranka ya dawo!" " Ok gamu nan zuwa! " Ya kashe wayar. Jan hannuna yayi zuwa sama ya dauko min hijab dina tare da maganin da nake sha, sannan ya riko hannuna ya kai ni cikin mota, kafin ya kara komawa cikin gidan ya dauko file din da ya manta, sannan ya rufe gidan ya nufo motar muka bar cikin estate din.

Sai da ya fara zuwa office ɗinsu, ya bada file din sannan ya dawo ya wuce da ni asibitin, lumshe idanuna nayi har muka isa asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos, a wurin parking muka samu Aunty Zakiya tana jiranmu, riko hannuna tayi muka cigaba da tafiya, har cikin asibitin can bangaren likitan ƙwaƙwalwa, muna shiga likitan ya ce mana. "SAN da kanka?" Yana kallon yadda na koma bayan Aunty Zakiya ina mai boye fuskana. "Ku zauna, Doctor ke kuma wuce bangarenku!" Murmushi tayi tana faɗin. "Shi kenan Doctor!"

Fita tayi tana faɗin. "Dady idan kun fito ka kira ni." "Ok Maamah." "Why not ki dauke shi kawai!" Yana maganar idanunsa yana kaina. "Zakiyah ta gaya min sakonka tun jiya, dalilin da yasa na katse abinda nake yi kenan na dawo." Murmushi yayi, yana kallona. "Auta ko?" "Eh ita!" Ya Ado ya bashi amsa, cigaba yayi da aiki da computer dinsa. "Lubabatu Usman Umar Jama'are ko?" Nan nayi mamakin yadda aka yi yasan sunana. "26 yrs!" Daga nan ya zuba min idanu. "Wannan kibar taki tun da kina da ita ce?" Kallon Ya Ado nayi, rike hannuna yayi. "Daga baya tayi kibar!" "Tow Adam ai naga duk Yaran gidanku babu me kiba sam!" Ya fada yana cigaba da aikinsa. "Eh dukkanmu bamu da kiba, itama daga baya tayi shi." Haka ya cigaba da aikinsa. "Yanzu me yake damunta!" "Dawowa nayi na same ta tana kuka da ihu, tare da boye kanta kamar wani zai dake ta." D'aga mishi hannu yayi ya ce mishi. "Malam fita ka gama naka aikin kalle mu daga jikin window." "Amma Ahmad!" "Tow zo ka duba ta mara mutunci a ko ina sai ka nuna min halinka na lauyoyi! " Ya fada yana mikewa, kujeran da Ya ado ya mike ya zauna tare da fuskantata. Fita ya Ado yayi ya zuba mana idanu ta window glass din,

Daukar wayarsa yayi ya turawa Ya Ado.. *Ka kalleta da kyau, sannan ka saka idanu akanta akwai abinda nake son ka fahimta please* sannan ya ajiye wayar, yana kallona duk da ban san me yayi da wayar ba, amma jikina yana bani wani abu yayi. " Lubnah! " Ya kira sunana, har lokacin ina karce farcen hannuna. " Ya razana ki?" Shiru nayi ina karce farcen, sake tambayar yayi, ban bashi amsar ba. " Baki jin zafin farcen ne baki ga jini yake yi ba? " Ya tambaye ni. " Gaya min meke damunki?" Muryana tana rawa na bude baki zan yi magana sai nayi shiru. "Kina son Ado ya sake asarar da yayi yau ya cigaba da faruwa saboda ke ne?" Kallon window nayi ina kallon Ya Ado, "asara kuma?" Na tambaye shi. "Wata Shari'a yake yayi mantuwa karshe ya ajiye shari'ar saboda halin da kike ciki! Don haka idan baki son haka ya kara faruwa gaya min meke damunki?" "Shi ne yake zuwa yace ba zai tab'a rabuwa da ni ba." Na fada ina jin kuka na zuwa min. "Waye kenan?" Ya tambaye ni, "Ya Hafiz!" Na fada ina karce farcen da yayi jini, " yana ina? " Ya tambaye ni, " Bauchi!" Nace mishi," Idan ni na yarda, waye zai yarda kina ganin Ya Hafiz?" Kallonshi nayi kafin na sunkuyar da kai. " Sau nawa kike ganin shi?" "Jiya da yamma sai da dare sai kuma dazun." " Yana razana ki ne?" Hawaye ne ya zubo min ya ce. " Ba zai tab'a rabuwa da ni ba! " Shiru yayi yana kallon yadda nake share kwalla. " Me yasa baki yarda kin yi nisa da ba zai iya zuwa gare ki ba. " Hawaye ne ya zubo min nace mishi. " Zai zo!" " Ciwonki yana jini!" Ya dauki tissue ya bani na nad'e hannun, sannan ya mike ya nufi wata drower ya ciro wata yar box ya tawo gabana yana me saka handglove. Ya dauki abinda treatment ya fara wanke min hannu. " Babu zafi ne?" Ya tambaye ni, "Bana jin zafin ne! " Kura min idanu yayi. " Baki zafin spirit din ba?" Girgiza mishi kai nayi, sai da ya gama sannan ya mike tare da ɗaukar wayar landline, ya kira wata a cikin wayar. "Ok ina jiranki! " Can sai ga wasu nurse biyu sun zo. "Ki saka mata drip" da wasu allurai, sannan ya kalli window yayiwa Ya Ado alama da ya shigo, koda ya shiga zama yayi yana faɗin. "Doctor Ahmad lafiya kuwa?" Komawa yayi ya zauna a kujeran da kyau yana juyawa kujeran. "Kanwarka bata da lafiya, duk da tana shan magani amma da gaske bata da lafiya da zata fahimci me ake so da ita."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull