ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 14
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 14: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 14. Gyara zama Ya Ado yayi ya ce mishi.. "Za a fitar da ita ne wani wajen?" Girgiza kai Doctor…
4,374 words
Gyara zama Ya Ado yayi ya ce mishi.. "Za a fitar da ita ne wani wajen?" Girgiza kai Doctor Ahmad yayi ya cigaba da cewa. "Kanwarka tana dama da cutar Deja'vu" shiru Ya Ado yayi kaman mai son tuno wani abu kafin ya kalli Doctor Ahmad ya ce mishi. "Kai naso sanin wannan kalmar amma na rasa inda na santa!"
"A bayyane yake wannan kalmar ba wata babba bace amma tana da matukar hatsari ga lafiyar dan Adam, bari na maka misali akwai wani lokaci zaka ga kamar ka tab'a ganin wani abu ko wani wuri amma baka tab'a zuwa wurin ba, wani lokaci kuma mutum zaka gani baka tab'a ganinsa ba amma zaka ji a ƙwaƙwalwarka ka tab'a ganinsa!" Inji Doctor Ahmad, gyada kai Ya Ado yayi yana faɗin. "Anyi haka! Kuma sai yanzu na fahimci sunan. To meye alakarshi da Lubnah! Tana gane gane ne?" Gyada zama Doctor Ahmad yayi domin yana son yayiwa Adamu UU Jama'are. Ya ce mishi. "Wannan yanayi da yake bayyana ganin abin da bai taɓa faruwa ba amma mutum ya ɗauka ya faru ko yana faruwa da shi ana kiransa da Déjà vu (furucin Faransanci ne da ke nufin "An riga an gani"). Déjà vu wani abu ne da ke faruwa a cikin ƙwaƙwalwa, kuma kusan kashi 97% na mutane sun taɓa fuskantar shi a rayuwarsu. Masana kimiyyar ƙwaƙwalwa da jijiyoyin jiki (Neurology) suna da ra'ayoyi daban-daban game da abin da ke haifar da shi, amma ga manyan dalilai: 1. Ƙwaƙwalwar Ƙwaƙwalwa (Memory Glitch/Misfire) Ana ganin Déjà vu na faruwa ne lokacin da wani ɓangare na kwakwalwa ke yin aiki ba daidai ba na ɗan lokaci: * Rikicin Ma'aji da Sanin Sani: Ƙwaƙwalwa tana da wurare biyu daban-daban: wanda ke adana abubuwan da suka faru (ƙwaƙwalwar ajiya) da wanda ke ba mu jin cewa muna da masaniya da wani abu (sanin sani/familiarity). A lokacin déjà vu, wataƙila ɓangaren da ke ba da jin cewa an saba da abu (sense of familiarity) ya kunna, ba tare da ɓangaren ƙwaƙwalwar ajiya ya kunna don tuna ainihin lokacin da abu ya faru a baya ba. Wannan yana haifar da jin cewa an gani/an saba da abu, amma mutum ya kasa gano lokacin da wurin da abin ya faru. * Shiga Cikin Ƙwaƙwalwar Ajiya Mai Tsayi (Short-circuiting): Wasu suna ganin cewa sabon bayani da ya shigo cikin kwakwalwa na iya ɗaukar wata gajeriyar hanya zuwa wurin ajiye ƙwaƙwalwa mai tsayi, maimakon bin tsari na al'ada. Wannan yana sa sabon abin da ke faruwa ya zama kamar tsohon abin da aka daɗe da adanawa. 2. Tsallake Karɓar Bayanai (Split Perception) Wani ra'ayi kuma shi ne cewa déjà vu na iya faruwa lokacin da mutum ya karɓi bayani daga muhalli sau biyu a jere, amma a wata hanya daban-daban: * Kallon Farko na Rashin Kulawa: A karon farko da ka ga wani abu ko ka shiga wani wuri, wataƙila ba ka mai da hankali sosai ba, ko kuma ka gani ne a cikin rabi-rabi (misali, daga gefen ido ko lokacin da ka shagala). * Kallon Biyu Cikin Kulawa: Lokacin da ka sake kallon abu ɗaya, ƙwaƙwalwarka ta danganta shi da ɗan bayanin da ta ɗauka a farkon kallon da ba ka kula sosai ba. Wannan yana haifar da jin cewa an riga an gani, saboda a gaskiya an gani, amma ba ka tuna shi a sarari ba. 3. Jinkirin Bayanai (Delayed Processing) Wata ka'ida ta ce bayanai na iya shiga cikin kwakwalwa ta hanyoyi biyu daban-daban, kuma idan ɗayan hanyar ya isa ya ɗan makara kaɗan fiye da ɗayan, ƙwaƙwalwar za ta fassara abin da ya isa da farko a matsayin "yanzu," sannan kuma abin da ya makara a matsayin "tsohon abin da aka riga aka gani." 4. Dalilai Masu Alaƙa da Jiki Déjà vu kuma na iya zama mai alaƙa da yanayin jiki, kamar: * Gajiya ko Rashin Barci: Rashin hutawa ko damuwa na iya shafar yadda ƙwaƙwalwa ke aiwatar da sabbin bayanai da ƙwaƙwalwar ajiya. * Epilepsy (Ciwan Jijiyoyi): A wasu lokuta, musamman idan déjà vu na faruwa akai-akai, yana iya zama alama ta ƙananan canje-canje na lantarki a cikin wani ɓangare na kwakwalwa da ake kira temporal lobe, wanda yake da alaƙa da ciwon farfaɗiya (epilepsy). Amma ga yawancin mutane masu lafiya, ba alamar wata babbar matsala ba ce. A taƙaice, Déjà vu shine kuskuren jin sanin sani (false sense of familiarity) da ƙwaƙwalwa ke yi a lokacin da wani abu sabo ke faruwa." Shiru Ya Ado yayi kafin ya ce mishi. "Haka yana da alaƙa da ciwon damuwa kenan?" Ajiyar zuciya Doctor Ahmad yayi yana me mikewa daga kujeran da yake kallon Ya Ado ya ce mishi. "
E, akwai yiwuwar a sami alaƙa tsakanin Déjà vu da ciwon damuwa (anxiety), amma ba a kowane hali ba. Ga bayanin yadda alakar ke kasancewa: 1. Déjà Vu Na Yau da Kullum da Damuwa (Normal Déjà Vu) Ga mutane da yawa, fuskantar Déjà vu lokaci zuwa lokaci (misali, sau ɗaya ko sau biyu a shekara) ba alama ce ta damuwa ko wata babbar matsalar ƙwaƙwalwa ba ce. * A lokacin da yake faruwa: Déjà vu na iya faruwa a lokacin da mutum yake cikin damuwa (stress) ko gajiya (fatigue/rashin barci). Waɗannan yanayi na iya shafar yadda ƙwaƙwalwa ke aiwatar da bayanan da suke shigowa, wanda hakan zai iya haifar da wannan gajeren kuskuren ƙwaƙwalwar ajiya (memory glitch). 2. Déjà Vu Mai Alaƙa da Ciwon Damuwa (Anxiety Disorder) Mutanen da ke fama da ciwon damuwa mai tsanani (Generalized Anxiety Disorder - GAD) ko ciwon firgita (Panic Disorder) na iya samun déjà vu akai-akai ko kuma su ɗauke shi a matsayin wata alama mai ban tsoro. * Ƙara Mai da Hankali: Mutumin da ke da damuwa yakan mai da hankali sosai ga abubuwan da ke faruwa a cikin jikinsa. Idan Déjà vu ya faru, wanda yake da damuwa zai iya fassara shi a matsayin wata barazana ko alama ta hauka, maimakon kuskuren ƙwaƙwalwa na al'ada. Wannan yawan tunani da fassarar da ba daidai ba na ƙara tsananta damuwa. * Depersonalization/Derealization: Ciwon damuwa mai tsanani na iya haifar da wasu yanayi masu alaƙa kamar: * Depersonalization (Jin Cewa Ba Kai bane): Jin cewa ba ka cikin jikinka ko duniyar ba gaskiya ba ce. * Derealization (Jin Cewa Duniya ba Gaskiya ba ce): Jin cewa abubuwan da ke kewaye da kai ba gaskiya ba ne. * Waɗannan yanayi na iya kara kama da Déjà vu ko kuma a fassara su a matsayin wani abu na daban, wanda hakan zai ƙara wa mutum damuwa. 3. Idan Ya Zama Akai-Akai Ko Mai Tsanani Ya kamata a nemi shawarar likita idan Déjà vu ya zama: * Aka-akai: Yana faruwa sau da yawa a cikin wata guda ko mako. * Mai Tsanani: Yana faruwa tare da alamun ban mamaki kamar zazzabi, jin jiri, ko rashin sanin inda mutum yake. * A irin waɗannan lokutan, déjà vu na iya zama aura (alamar farko) ta wani ƙaramin ciwon jijiyoyin jiki (kamar temporal lobe epilepsy), wanda kuma ya bambanta da damuwa. A taƙaice, damuwa na iya haifar da gajiya da rashin barci waɗanda ke ƙara yiwuwar Déjà vu ya faru. Amma musamman, damuwa na iya sa mutum ya firgita da fassarar Déjà vu a matsayin wata babbar matsala, wanda hakan ke ƙara masa damuwa."
Cikin son sanin wani hali Lubnah take ciki ya ce mishi. " Ahmad wani hali Lubnah take ciki?" " Adam kanwarka tana fama da Depersonalization, tana jin kamar ba ita ba ce, tsaya kana waje me ka ga take yi da nake tambayarta? " Shiru yayi kafin ya ce mishi. " Na ga tana karce farcen ta." " Good tana ganin ita kamar ba ita ba ce, bata jin zafi ko ciwo idan ta jiwa kanta ciwo, bata yarda da kanta ba kamar yadda take kallon kowa, sannan abinda ya faru da ita yana hunting dinta har shi Ex dinta tana jin kamar yana nan kusa da ita shi yasa take samun attack na Deja'vu akai akai, idan aka cigaba da haka zai haukata ƙwaƙwalwarta domin bata yarda da cewa duk abinda yake faruwa da ita kamar gizo bane gani take kamar a zahiri yake faruwa da ita. Idan har aka tsallake wannan matakin bata dawo hayacinta ba, abu na gaba da zata fara shine Derealization, shi kuma mutum bai yarda da kome a duniya ba, kowa ma ya gani zai cutar da shi ne. "
Dafe kanshi yayi yana faɗin. " Innalillahi wainnalihir rajoun, Innalillahi wainnalihir rajoun, Ya Allah na tuba ka sassautawa baiwarka. Ahmad gaya min me ake bukata?"
Gyara zama yayi yana faɗin. " Baya ga maganin da zan daurata a kai, zata fara ganin Doctor Dijah Bala, wata Therapist ce, a nan Lagos take, zata na bata shawara da yadda zata dawo tunaninta." " Zai dauki wata nawa kafin ta dawo daidai?" " Tabdijam tow idan har aka samu kulawar da ya dace zata iya dawowa a kasa da wata shida, kai idan ba a samu yadda ake so ba, zata iya kaiwa shekara ko fi da haka ya danganta da inda take, a rage hayaniya da tashin hankali. Soyayya take bukata a yanzu duk abinda zata gani ya sakata nishadi, sai abu na gaba shine mu saka Allah a cikin lamarin ta, Addu'a karatun Alqur'ani, azkar. Sauraren tafsirin malamai daban daban both hausa and English, zuwa wuraren shakatawa da dan tafiye-tafiye idan da hali SAN nasan kana da hali ma, a kaita ko Umara ne, taimaka da sakata farin ciki yadda zata ji itama mutum ce........... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN CHIB
Ajiyar zuciya Ya Ado ya sauke deep inside dinsa ya kalli Doctor Ahmad for while kafin ya lashe busashen lips dinsa. Ya ma rasa me zai ce, sannan daga ina zai fara? Daga shi har Zakiyah basu zaman gida. A yadda ya fahimci bayanin Doctor Ahmad Lulu tana bukatar wani a kusa da ita kada ya cutar da kanta. "Condition dinta baya bukatar zaman asibiti, idan tana tare da wani a gefenta, zata fi samun sauki da sakewa kuma ko bata magana wasu abubuwan zasu sauya sosai." Gyada kai Ya Ado yake yana jin kamar ya isa Bauchi ya rataye Hafiz a hankali ya ce mishi. " Me ya haifar da haka? " Ya tambaye shi kamar zai yi kuka.
" Domestic violence and abuse anxiety, yake haifar da haka, daga yadda namiji ya mai da mace kamar abin huce haushinsa tow daga nan irin wannan abin yake faruwa. Ka ga bata gaya min cewa yana dukarta ba amma daga yadda take ganinsa zai tawo yasa na fahimci girma da yadda ta fuskanci rayuwa a hannunsa. Wai ma waye shi ne haka ya lalata mata rayuwa haka? Kasan ba sai namiji ya kwanta da mace ko yayi mata fyade bane lalacewar rayuwa namiji ya mai da mace kamar dan uwansa namiji wurin duka da cin mutumci yana haifar da irin wannan abin.
Sannan idan har mace zata iya kawo batu gabanka a matsayinka na nata, tana buƙatar a shiga lamarinta ne wai me ya same ta ne!?" Ajiyar zuciya Ya Ado ya sauke ya ce mishi. " Ahmad kasan me? Iyaye da mu ne, muka aikata haka domin kuwa Yarinyar nan tasha zuwa ki har kirana aka yi ana gaya min nazo na raba auren kanwata tana shan wahala." A hankali ya Ado ya warware mishi duk abinda ya faru. " Kune kuka kashe yar uwarku, sannan iyaye suka goya muku baya, a gaskiya ba zan boye maka ba kun zalunci yarinyar nan." Yadda take magana zaka fahimci har cikin ransa haka ne, sannan ya ce mishi. " Ka je ka ɗauke ta, sannan da kace kun nima mata aiki waye ya gaya maka yanzu aiki ne matsalarta? A yanzu ita kanta bata san waye ita ba, kuyi kokarin ganin kun dawo da ita hayacinta. "
Mika mishi hannu yayi suka sake musabaha, sannan ya saka kai zai fita ya ce mishi." Zan bawa Zakiyah sako ta kawo maka! " " Na gode! " Daga haka ya bar ofishin Ahmad din, shima dama ba wai yazo aikin ba ne, jin Adamu zai zo yasa shi zuwa. Ba zai tab'a biyan Ya Ado abinda ya mishi ba. Kowani mutum yana da yadda kake jinsa a rayuwarka. A lokacin da aka sako shi a gaba sakamakon mutuwar wani mara lafiya aka jingina mishi laifin wanda ya kai da har ana ƙoƙarin kwace mishi lasin dinsa, Ya Ado ne yayi ta Shari'a har barazana zai da aka mishi amma ya tsaya sai da yayi nasara, sannan ya dawo aikin a lokacin ya kara tafiya karo ilimi tun lokacin yake son ganin ya kyautata Ya Ado domin biyan shi abinda ya mishi, s yanzu haka zumunci suke da family dinsa da na Ya Ado.
Ina zaune Ya Ado ya zo ta rike hannuna muka tafi har wurin Aunty Zakiyah, ya ajiye ni ya tafi sayo min magani, yana dawowa muka wuce gida, bai kai ni gida ba sai da ya wuce da ni wurin saloon. "Zakiyah ma zata zo anjima ki zauna anan kin ji!" Babban wurin saloon ne da span. Zare hijab dina nayi, na lullube kirjina na cigaba da zama daya daga cikin masu aikin tazo ta tsafe min kitsona tana murmushi ta ce min. "Ke Fulani ne?" A yadda tayi maganar kamar ta saba ganin gashi mai yawo balle ni nawa gashi ja ne kuma akwai cika da tsawo, gidansu Abba muka yo domin mazanmu ma sun fi mu yawan gashi, amma ana yawan cewa ni nafi su gashi. Zamana da Ya Hafiz yasa gashin ya koma baya. Haka ta wanke min tare da tsame min. Muna zaune sai ga wasu yan mata sun shigo, gaskiya sun yi kyau kamar wasu hurul ain, saboda kyau da gayu ga wasu maid da suke dauke musu da jaka suna bin bayansu, tare da wasu security service karti majiya karfi, daga yadda suke tafiya tare da wasu yan mata uku kamar kawayen juna ne. Wurin zama suka wuce alamar can ne VIP, yadda masu aikin suka yi ta shiga da fita. Me da hankali nayi kan madubin gabana, matar ta ce min. "Madam ayi miki kitso ne?" Idan aka bar gashin ma addabata zai yi domin wani lokaci ji nake kamar na yanke shi na huta. Shafa gashin tayi da ya sauka har gadon bayana.
A hankali ta fara busar da gashin, sannan tana gamawa ta dauko abin kitso. Ina zaune wani delivery Man ya shigo ya ce mana. "Mrs Jama'are nake nima?" Kallonshi nayi nace mishi. "Nice!" "Mika min wata jakar leda da kwali da tarkace ya ce min. "Daga Daily Meals! " Mika min takarda da biro yayi yace nayi sign, haka nayi na mika mishi, ya fita. "Mijinki ko?" Girgiza kai nayi ina kallon parkage din, Ya Ado ne. Haka matar ta cigaba da min kitso har wani lokaci gashi ta kwashi kitson yan dai-dai. Fitowa wata daga cikin yan matan nan, tana zuwa ta ce mata. "Biolah fix kuke yi da wig?" Da sauri ta juya tana faɗin. "No ma is just natural hair." Takowa tayi s hankali, tana mai kai hannu zata tab'a gashin nayi maza na mike ina zare idanu. "Sorry Ma wai zata ga gashin ne?" Mai da hijab dina nayi ina kallonsu. "Shi kenan zauna ba sai ta tab'a ba" tsoro yasa naki zama, tsaki budurwa tayi ta fita can sai gata wani gaye, da sauri nayi kasa da kaina. Kamar da wasa sai ga shagon ta can wurin VIP ya cika da Manya Yara, tana gama min kitso, Aunty Zakiyah tana shigowa. "Baby girl! Kin ci abincinki kuwa?" Nuna mata nayi, ta zauna aka fara tsefe mata kitsonta, aka wanke mata nata sannan aka mata parking a lokacin da yan matan nan suka fito, ni dai kaina a sunkuye suka fita sai budurwan nan ta tsaya tana faɗin. "Ke uwar tsoro gashinki yayi min kyau, idan na kara haduwa da ke sai na taɓa." Yan matansu suka kwashe da dariya, irin sun ga abin dariya ni dai ina bayan Aunty Zakiyah. Yadda na rike rigar ta yasa ta yi ta tab'a hannu.
"Badar yarinyar bata burge ki bane, natural hair fa, gashi ja kamar wata baturiya." Kallon Zuhra tai ta ce mata. "Who care? Duk wata mace so nake ta dawo bayana, bana son ta dawo gabana amma ke da yake kin iya kwashe kwashe ke duk wata mace mai kyau burge ki take ko bata da kyau matukar tana da gashi da yake ke kwakwaido ce." Murmushi tayi ya ce mata mata. " Yes ni kwakwaido ce, amma waye zai damu da haka? Abu daya na sani ina cikin madagar KUMO FAMILY GROUP, ko a so ni ko kada a so ni Am Queen! " Shiga motarsu kowacce tayiwa motar wuta suka bar harabar wurin saloon ɗin.
Riko hannuna Aunty Zakiyah tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta ce min. "Yaran masu kuɗi ne basu da hankali. Muje" haka na biyo ya har wurin motar, ina ji a raina sun yi dace sun samu abinda suke so. Sun samu irin gatar da na rasa, idan da nima na samu gata haka da ba makawa da ina cikin manya matan alfarma. Sai dai yadda na hango fuskarsu ya nuna basu cikin farin ciki, basu jin dadin tasu rayuwar ko don ni bana jin dadin tawa rayuwar nake hango kowa ma haka? Har muka iso gida zuciyata bata bani damar kome ba, bayan mun yi sallah naci abinci na sha magani na koma na kwanta. Ban farka ba sai karfe biyar nayi sallah na cigaba da zaman dakin, shigowa Aunty Zakiyah tayi tana faɗin. "Oya zo nan zamu fita ne, ki shirya muna jiranki." "Tow!" Na amsa mata, sannan tana fita na shirya cikin doguwar riga abaya na saka hula na yane kaina. Sannan na sauko kasa. "Waw you look beautiful Aunty Lulu!" Yaran suka fada, sai na kasa yarda da haka na fara jin wani irin yanayi kamar sun muzanta ni. "Baby girl kinyi kyau ko Doctor, she looks good" jin yadda Ya Ado shima ya kara fada sai na ji wani iri, riko hannuna Adil yayi ya ce min. "Daga yau ni mun zama abokai ko Dady!" "No da ni zata yi aboki!" Inji Princess, Wai ni yau ake fada a kaina, sai naji hawaye na zuba min abin yayi touched heart dina, a hankali Ya Ado ya ce musu. "Ba zata yi abota da ku ba, she is my favorite sister, oya ku je wurin Maamah ita take bukatarku!" Ya fada yana riko hannuna muka fita suna faɗin. "No Dady, a'a kawai ka bamu ita, kaima sai kace Hajiyar Bauchi ta kawo maka wata Barbie din, but Aunty Lulu she look like Barbie!" Irin wannan maganar da suke sai yasa na fara jin like I miss something important a rayuwata, akwai wanda ya tab'a gaya min you look like Barbie princess, musamman idan kika saka uniform din nan!" Hawaye ne ya shiga zuba min a idanuna. Dama zan samu wanda zai gaya min yadda nake ni da shekaru goma da wani abu na fuskanci muzantawa da gwatsalewa, har ake gaya min bani da kyau. Fita muka yi har wani unguwa wai Yaba, a nan muka je ashe ogan Ya ado ne yake birthday. For the first time a rayuwata da na shiga irin wannan taron.
Muna wurin taron, aka yi ta gabatarwa har Ya ado ya mika mishi abinda ya kawo, kasancewar mutumin yana ji da Ya Ado sai gabatar da shi yake a wurin manya clients dinsa, yana gaya musu yadda yake aiki, su kuma sai amsar compliment card din Ya Ado suke, sannan ya gabatar da mu a matsayin Family dinsa, tare da nuna musu nice auta a family dinsa. Hannuna yana rike da na Adil. Don tunda muka zo Aunty Zakiyah ta kira shi ta mishi magana, ya zauna a gefena kamar me jin barci kanshi a arm dina, yayi shiru haka sai ya saka min jin nutsuwa. Duk abinda ake yana ji kuma yana sane amma haka da yayi ya haifar min da nutsuwa idan aka yi wani magana da yarvanci na tambaye shi yana bani amsa haka ya sani kara fahimtar yadda yake jin harshen, ina kallon kome har lokacin da Aunty Zakiyah tazo ta d'aga mu, muka je aka gaida mutanen. Har lokacin hannunshi yana cikin nawa. Wasu bakin alfarma aka yi a wurin na Ya Ado da ogansa sun tafi tarbo bakin wani dattijo ne kamar dan arewa, yana tafiya da sand. Yadda Ya Ado da ogansa tare da wasu team na aikinsu, suka rufawa dattijon na fahimci babban mutum ne mai daraja. Sannan suna ganin girmansa sosai firm ɗinsu.
Da yake mun yi sallah magariba muka fito taron, sai duk naji na damu ina son nayi sallah isha amma har lokacin kamar yanzu ake taron, muna tsaye manyan yan kasuwa, yan siyasa na garin Lagos. "Kin gansu nan, dayawansu suna tare da office ɗinsu Dady ne, idan har Shari'a za ayi ta kasada da rayuwa da dukiya. Office dinsu Dady ake yinta. Amma shi ba kowacce Shari'a yake amsa ba, kuma suma sun san da haka yana kiyayye hakkin Allah." Inji Aunty Zakiyah, gyada kai nayi ina kallonshi. Jan shi Mutumin nan da ya shigo yana taɓa bayansa tare da mishi magana da bamu fahimta ba, sai ganin Ya Ado muka yi yana ta Godiya tare da mikawa mutumin hannu. Haka manya mutane suke ta gaisawa da Ya Ado da yake Ogansa ya gabatar da shi, sannan a nan y fara magana kamar haka.
"A yau sha biyar ga watan Mayun, nake shaida muku na ajiye aikina wato nayi ritaya, yau ina da shekaru saba'in cib, duk tun shekarun baya naso na ajiye aiki amma team din da suke sponsor na office dinmu suka ce basu ji ba basu gani ba. Yau amma yau na hakura da aiki inda zan gabatar da Abdulwahab Adekunle Adebayo matsayin shugaban team dinmu. " A hankali yayi ta kiran sunayen mutane dayawa yana gabatar da matsayinsu. Ya ce a wurin. " Nasan wasu zasu ce Why Adam U.U Jama'are? Sai dai ko wacce kusurwa tana bukatar jekariya, mu kungiyar da abokan huldanmu sun bukaci jekariya, shi din nan dai gashi koda aka fitar d sunansa da kanshi ya zo ya ce nayi hakuri na cire. Na barshi da abinda yake yi, idan na fahimci Adam UU Jama'are, yana da buri shi yasa bai amshi ragamar shugabancin ƙungiyar SAN ba, koda yake shi din d'a ne a gare ni, nagartashi da amanarshi abin alfahari ne, don haka a yau nake gaya mishi kuma nake sanar da al'umma cewa daga yau duk wani Shari'a da zamu yi ko zaa kawo firm dinmu Adam UU shi zai jagoranci shi. " Take wurin ya kara daukar tafi. Kafin yayi gode da sauran al'ummar da suka samu halartar Birthday din, sai na ji na gaji haka nayi ta lumshe idanuna. Har wurin karfe goma aka tashi muka bar gidan, koda muka iso gida wanka nayi tare da sallah, na sha magani sannan na kwanta a hankali barci yayi gaba da ni.
*** Mama yadda ta kafe babu wanda ya isa dawo da auren Hafiz da Lubnah, haka yasa ta tattara ta bar gidan Baban Bauchi, wanda haka yayiwa Hajiyarsu Hafiz dad'i. Sannan ta kuma saka aranta duk Inda Lubnah tana zata dawo wurin Hafiz domin ganin yadda halinsa yayi mugun tashin nan bayan an rufe shin nan, ta tambaye shi akan me yasa ya damu da Lubnah bai boye mata ba, ya gaya mata gaskiya abinda ya faru, da kuma dalilin da yasa yake son ganin ya kara dawo da Lubnah, taji tsoro ta kuma kadu, sannan ta saka duk wani abinda take da shi a kasuwa domin a bine kome, sai dai a yanzu kan an binne kome, kome kuma ya rufu kamar yadda suke fata yanzu Lubnah ita ce harinsu, shi yasa yake ta bibiyar Baban Bauchi ya gaya mishi inda take koda a wajen kasar nan ne sai ya nimo ta, Lubnah tashi ce shi ɗaya daga shi kuwa babu wanda ya isa zama da ita koda kuwa zai mutu ne Lubnah bata isa tarayya da wani da namiji ba. Wannan shine alkawarinsa.
Yau karfe daya na dare ya shigo gidansa, da wata Yarinya a gefensa, yar lukuta da ita ya bude mata kofar dakin Lubnah wanda yake nan har da kayan ba a dauka ba, karshe ma dakinsa ya mayar da shi. Yana ganin yarinyar ta shiga, ya wuce dakin Karimcy tana barci, daga gani barcin ta wahala ce domin daga ita har Yaran babu wnada yaci wani abu a cikinsa. Tashinta yayi ta bude idanun tana kallonshi. Ta gaji sosai domin zuciyarta ba zata iya daukar ukubar da ya fara gana mata ba ta ce mishi.. "Ka dawo ka bani hakuri ne?" Murmushi yayi ya ce mata. "Ko daya nazo ne na gaya miki gaskiya ko ki fita ki fara girki kamar sauran matan ko kuma bakin ciki da yunwa ma sun ishe ki" shiru tayi sannan ta ce mishi. "Ba zan yi ko daya ba, kai ne ma zan kafa maka sharadi. Idan kana son kanka da arziki ka ajiye abinda kake aikatawa da wanda kake shirin aikatawa. Kasan nasan abinda yake faruwa, har abinda Hajiya take aikatawa domin rufa maka asiri. Ni kasan ban da sirri ko kashe ni ka yi ina da hujjar da na bada shi ba nan kusa ba har gaba da Bauchi na saka a ajiye min daga ranar da suka ji labarin mutuwata su bayyanawa duniya tasan waye kai. " Yadda yayi magana da confidence yasa shi razana, bafa kowa bane Lubnah ta ce mishi. " Ni ba Lubnah ba ce da zan rufa maka asiri ba, bayan ni ba koshi nayi da kai ba. Ruwanka ne ka ja tsumar rayuwarka, sannan ina son kudi a cikin account dina, ko kuma na kira waya nace a saka labarin nan zuwa ga Yayun lubnah su ji yadda ka kashe Mahaifinsu da ita Lubnah. "
Yana murnan ya kashe maciji, ashe bai saure kai ba. Domin Karimah ita ce kan macijin da bai sare kanshi ba. Duk sai ya ji kamar zai zauce domin Karimah tafi shi iskanci. Eh ai ko a shekaru Karimah ba sa'arshl ba ce. Domin tun can ta girme shi a bariki suka hadu da ita tana yawo bariki, suka haɗu.