Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 15

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 15

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 15: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 15. Washi gari kuwa da Karimah ta fito ta ga yarinyar da Hafiz ya kwana da ita bata ce mata kome…

4,348 words

Washi gari kuwa da Karimah ta fito ta ga yarinyar da Hafiz ya kwana da ita bata ce mata kome ba, ta shiga kitchen ta dauko itace ta shiga dakin Lubnah Hafiz yana barci ta rufe Yar mutane da duka. Dakyar ya kwace ta, tana haki ta ce mishi.. "Ni ba Lubnah ba ce, wallahi baka isa kawo min wata mace cikin gidana ba. Idan kuwa kayi haka ka saka a ranka nice ajalinta." Shi fa ya zata kowacce mace kamar Lubnah take, sai gashi lokaci guda Karimah ta goge mishi zero. Sannan ta masa barazanar sai ta kai ƙarar shi wurin Baban Bauchi, tunda shi ya zama ɗan akuya zata tona mishi asirin da yake rufawa tunda tasan sirrinsa. Wannan abin yasa shi kara shiga hankalinsa, ya koma mata biyayya bai kara shigo mata da mace gidan ba, domin kuwa ta rike mishi wuya, kuma bata girki kudin dai tana samu son ranta. Kuma shima tana cin ubansa dai-dai gwargwado. Duk ya fita hayacinsa bai da hankalin da zai fahimci barnan da yake shi dai burinsa asirinsa ya rufu, a irin wannan yanayin ne aka Baban Jama'are ya fadi jininsa yayi mugun hawa, haka suka dauko shi daga Jamaare aka kawo shi Bauchi, Teaching hospital Bauchi, wannan abin ya sake gigita Hafiz yayi ta ji kamar yayi hauka. Domin hawan jini da diebetis suka buga shi da kasa.......... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA ƊAYA

Duk da wannan abinda ya faru, daga Mama har Yadiko sun kyale Baban Bauchi yayi yadda yake so, suka bar mishi gidan shi kuwa ya dauki dokin zuciya ya daura a kansa tare da wani irin girman kai da son kai, suma Yaran maza da mata suka zuba mishi idanu yayi yadda yake so ba dai Hafiz ne suka bar mishi.

Sai da Baban Jama'are yayi kwanaki kafin ya dawo hayacinsa, ya kalli Hafiz cikin tsananin bakin ciki. "Hafiz maka baki ba, ba zan ce zaka gani ba. Amma matuƙar Lubabatu bata zalince ba, kai da nutsuwa har abada idan kuwa ita ce ta zalince ka Allah ba zai barta ba, kai Hafiz bana jin yarinyar nan zata iya abinda ya raba ku. " Juyar da kai yayi domin maganar Allah yana jin zafi da ciwo, yana ji kamar ya cire zuciyarsa idan ya tuna yadda Yaransa suka mai da Lubnah idan ya tuna yadda suke mata wulakanci har akan idanunsa sai yayi kamar laifin nasa ne, donin bakidaya yayi kuskuren da har abada ba zai gyaru ba, kusan da iyayen Lubnah suka juya mata baya, kasa yin kome yayi amma shi dansa yana yadda ya so. Akwai wani abu da yake faruwa a wannan duniyar daga lokacin da kace na wani bai isa dariya ba, har abada naka ba zai tab'a maka daidai ba, a lokacin da yake ji yake gani ana azabtar da Lubnah shi a lokacin yayi kamar bai gani ba sai ya rufe bakinsa da kunnensa yayi kamar bai ji ba bai gani ba. Share kwalla da ya zubo mishi yayi.

Sai dai tun daga ranar bai kara yiwa Hafiz magana ba. yadiko taxo ta ga jikinsa, bayan ta koma gida ta gayawa Mama ta waya, ai kuwa ranar talata bayan laasar Mama ta zo da matar Ya Umar, suka samu Abba wato Baban Bauchi. Yadda yake wani jiji da kai yasa Mama itama ta nuna mishi daga fada take. Ta wani dauke kai suka gaisa da Baban Jama'are, ya yi kasa da murya ya ce mata. "Don Allah Hajiya Salamatu, ki koma dakinki haka yanzu ku ba yara bane." Murmushi tayi tana me faɗin. "Idan na gaya maka gaskiya zaka yarda?" Ya jinjina kai ta ce mishi. "Zabi ya bani har abada ba zan dawo gare shi ba kamar yadda Lubnah ta haramtawa Hafiz, idan kuwa ka ga ta dawo ga Hafiz tow mutuwa nayi kasa ya rufe min idanu kenan. Kai ko gawar Lubnah da ta koma gida Hafiz gara wuta ya cinye ta." Ta fada tana murmushin bakin ciki domin ita ɗaya tasan yadda take jin ciwon halin da Lubnah take ciki, mikewa tayi tana faɗin. "Muje kin ji Allah ya kyauta,." Haka ta fita Abba ya ja tsaki yana faɗin "Sai me idan ba ta dawo ba ita Yadiko idan bata koma ba wallahi sai dai aurenta ya mutu don ya gaji ai ba da ita yake rigima ba, ita kuwa da yake tafi shi kwaya tace a gaya mishi ita bata tsoron saki ai idan har ya iya Hajiya Salamatu haka babu wacce ba zai yiwa haka ba, ba zata koma ba Hajiya Asiya su mishi replace abinda suka gaza mishi. Sosai aka yi ta rigima yaran kuwa sun koma gefe dama kowa ya gaji da abinda yake yi, ganin haka yasa Manya gaba cikin family uku suka taru aka dawo da Yadiko domin ya kafe Mama ba zata dawo ba, idan kuma zata dawo sai dai ta dawo da Lubnah kafin shi, ita kuwa Mama ta ce bai ji ka ba tukun, ai yanzu ba da bane Lubnah kuwa tayi musu nisa. Wannan abin ya bala'in bata mishi rai. Shi yasa shima ya kafe ba zata dawo ba. Ita kuwa ta ce tafi nono fari. Faruwan wannan al'amarin ya kara sakawa Baban Jama'are damuwa sosai domin yana ganin ai duk abin nan ya faru ne ta silar danshi. Sannan masu ganin laifin Lubnah yanzu sun dawo bayanta, domin abin da ya faru ya nuna sun so kansu duk abin nan gashi ita ta rasa iyayenta amma shi da yake shafaffe da mai ne gashi nan yana zaune tare da kowa na shi, sai yaji tsoron Allah ya shige shi dansa yayi sanadin auren da aka ɗauki shekaru, sannan a lokacin da ya rasa madafa su wadannan mutanen sune suka tsaya mishi. "Innalillahi wainnalihir rajoun!" Ya nanata kalmar nan tafi sau dubu ya tsani kanshi da zuciyarsa.

Lokacin da ya dawo Jama'are, sai kunya da kuma yadda mutane suke ganin laifin Hafiz ya kara susuta shi ya dinga blaming kansa wannan abin sai ya kara hurt din zuciyarsa, har sati biyu ya cika Babangida ya mai da shi ganin likita. A lokacin da suka hadu da Hafiz ya ce mishi. "Ban san me kayiwa Lubnah ba, amma ka sani ba zaka tab'a farin ciki da jin dadin rayuwa ba, sai kun sake zama duk da kowa yana son yaji matsayata akan Lubnah abu daya zan gaya maka a duk lokacin da ka ji inda take kafin wani ya rugaka samunta ka kara niman soyayyarta a karo na biyu, ka dawo da ita rayuwarka idan ta amince idan bata amince ba, tabbas ka tafka mummunar asara a rayuwarka, ka dube ka kai kanka baka da nutsuwa ka cutar da ita ka cutar da iyayenta. Ina ji kamar na mutu da bakin cikinka! " Ya fada yana jin kuka na zuwa mishi. Haka ya ga likita sannan Hafiz ya kawo shi kasuwar Central. Yadda Baban Bauchi ya ga dan uwansa ba karamin dadi ya ji ba, haka ya dauke shi suka yi ta zaga manya shagunansu, yana karawa bawa dan uwansa hakuri akan batun lubnah wanda yake niman wata guda da faruwa. Ya kuma yiwa ɗan uwansa alƙawarin. " Matukar ni na haife ta kuma ina raye Hafiz shine mijin Uwata, ba zan tab'a sauka akan kalamai na ba. " " Ya Shehu, ka sani matuƙar Lubnah ta gama Idda tana da damar zabawa kanta abinda take so, sannan ita kanta zuwa yanzu tana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali. Hafiz ya mata laifi. " " Ai dan uwanta ne idan bata rufa mishi asiri ba waje zata rufawa? Iskanci ne da rashin mutunci ni kuma ina daidai da ita duk inda taje zata dawo ko shekara dubu ne!"

Wannan ya kara nuna son Kai da son zuciya irin na dan Adam, bakiɗaya suka saka a ransu idan har ta dawo su ke da iko da ita. Anyi hiran nan a gaban Ya Sani shi kuwa ya kira Ya Umar ya gaya mishi, ai kuwa maganar ta fada kunnen Mama, kwafa tayi ta ce Allah ya basu Sa'a tana jiransu.

*** IKEJA LAGOS GRA ELYAKUB MUHAMMAD KUMO St. Aka rubuta da karamin allo, wanda aka yi zanen da wata golden paint, babban gare da zai sadaka da cikin gidan irin kafceccen nan ne, mai nauyin gaske nan ne, a hankali hancin wata kyakyawar mota kiran kamfanin Roll Royce , ta cigaba da tafiya izuwa kantamemmen gidan da yake cikin unguwar wanda yake tsakiyar unguwar mai zubin fadar sarki. A hankali yake wuce gidajen da suke yiwa wannan kyakkyawan gida kawayan, har ya isa zuwa kofar da zata sada shi da wannan kyakyawar fadar. Ya jima a cikin motar yana shiru kafin ya tattaro duk wani abinda zai ɗauka sannan ya fito daga motar, ya nufi hanyar da zata sada dashi da asalin kofar da zata kai shi main Street na gidan, kofa ce mai security service, yana zuwa wani kare ya fara mishi haushi tare da kad'a mishi bindi a hankali ya isa gaban karen da ya tawo da gudu yana kawaye mutumin murmushi yayi ya ce mishi. "Max ya kake?" Ya shafa wuyar karen wanda kana gani zaka fahimci karen Ya sanshi irin sosai din nan. Mikawa daya daga cikin security din key yayi ya ce mishi. "Akwai abincinsa a boot!" Daga haka ya isa bakin kofar computer din tayi screening dinsa tare da scanner. A hankali ta ce mishi. "Barka da zuwa Captain Ubaidullah Jibirl Kumo, na'ura ta tantance ka." "Na gode Husnah ina sonki da zan kara aure ke zan aura." Ya fada yana murmushi yana jin ta ce mishi. "Bani da kawazuci sannan ni na'uran AI ce." "Ai na sani shi yasa nake kara kaunarki." "Na gode Ubaidullahi. " Daga haka tayi shiru ya wuce idan da sabo ko su, security din wajen sun san draman AI Husnah fa Oga Ubaid

A hankali ya ke tafiya har zuwa cikin gidan, kyakywan Yara yan mata suka tawo da gudu. " Uncle Ubaid, oyoyo!" Rungume su yayi sannan ya mike tare da ciro chocolate a aljahunsa ya mika musu yana faɗin. "Oya cigaba da wasa." Ya wuce su, bai kai entery na gidan ba, sai ga Maid sun fito cikin girmamawa suka bude kofar suna mishi. "Barka da zuwa Sir!" Jinjina kai yayi ya cire takalmi a wurin suka rufa mishi baya masu gyara zaman takalmin suka gyara shi kuma yana shiga inter door na gidan ya samu wasu takalma an zuba mishi maid din tana mishi sannu da zuwa. Kamshin turaren wuta zamani na FAMAS SCENT OF LEGEND GIDAN TURAREN WUTA ya daki hancinsa, wani irin kamshi ne mai hade da sanyin Ac ya bada wani irin perfect kanshi me shegen dad'i, daga shiga cikin gidan zaka fahimci how yanayin kamshin yake ratsa zuciya da gangan jiki, wata maid ya samu ta ce mishi. "Barka da zuwa sir muje ta wannan hanyar." Duk da ba yau ya fara zuwa gidan nan ba, sannan kusan rayuwarsa bakiɗaya yayi ne domin gidan nan, amma duk lokacin da abu me muhimmanci ya kawo shi, jagora ake mishi. Har zuwa babban main entrance parlourn na gidan, da sallama ya shiga wani kyakkyawan bafulatani dattijon da ya sha gwagwarmaya ya gyara zaman glass din sa ya zuba mishi idanun cikin wani irin murmushi yana me amsa sallamarsa a nutse. "Ubaid!" Ka rasa yayi gaba wani karamin abin wanke hannu ya ajiye file din sannan ya wanke hannunsa, tare da shafa hand sanitizer, sannan ya dauki file din ya isa gaban dattijon ya ce mishi. "Barka da hutawa Alhaji!" Gyara zaman glass din yayi ya ce mishi.. "Barka dai Captain! Yau kai ɗaya ne ina Amaryan lalle?" Gyara zama yayi yana faɗin.. "tana lafiya, Alhaji Hajiya Dadda tana nan kuwa?!" "Tana nan zata fito ai idan ita ce." "Allah yasa mu gama bata fito ba." Ya fada yana murmushi, abin motsa baki aka fara kawo mishi, ana jera mishi a gabansa, har suka gama Alhaji ELYakub Kumo ya ce mishi. "Fura zaka zuba min." Mikewa yayi ya zuba masa sannan ya mika mishi shi kuma ya dauki hadaddiyar fruit da ya sha madara, ya fara sha yana sauraren Alhaji ELYakub Kumo.

"Yau ma sakon ya baka ka kawo min?" Ya tambaye shi yana murmushi, irin murmushi irin na manya. Cikin wani deep sorrow voice ya ce mishi. "Ko don ba ni ba haife shi bane? Amma ai ni na haifi Mahaifinsa." Sai yayi murmushin takaici irin wanda kana ganin abinda kake so amma kana ji kana gani yafi karfin ka. "Ubaid ina da ikon hana ƙaddara ikonta ne?" Girgiza kai Ubaid yayi yana tausayin dattijon. "Kayi hakuri Alhaji!" Murmushi yayi a karo na uku wanda kamar ita din anyi ta ne domin fuskarshi kuma tana kawata mishi fuskarsa da wannan kyakkyawan murmushi. "Amma kasan ban yi mishi kome ba ko? Ban cutar da Turaki ba, duk abinda zanyi domin ya zama karaya a gare shi nake yi. Amma kasan na tsufa ko? Me yasa Turaki yake gudana? Da farko na dauka don rasa mahaifiyarsa ne yake gudun Ubansa, sai mutuwar Ubansa yasa na hango kiyayyar da Turaki yake min, bani da wani abu da zan rike Turaki. " Tari ya fara a hankali yana me ajiye furan ya dauki ruwan da Ubaid ya mika mishi. Kurba yayi yana me ajiyewa. " Kowacce rayuwa tana da fuskar da ƙaddara take bude mata, Turaki shine kaddarata, ban rena iyawarsa ba amma ya dawo gabana im dead in side, ya dawo yazo ga tsohon nan da baya jin kome sai kamshin mutuwa! " Shafa kai Ubaid yayi yana tuno abinda ya faru anan parlourn, numfashi ya sauke a hankali, yaji muryan Hajiya Dadda tana faɗin. " Ba zan ci ba, shima maganin ba zan sha ba. Wuce ki baka wuri tun ban haifi Ubanta ba nake jinya har na haifi Ubanta haka yasa na mutu ne? Ta je can ta cigaba da zama ai dama nasan bayinta ba ne, domin ko jiya wani malami ta gaya min bakin asiri aka mata, sai kuma macen aljan da suke tare wanda har sun yi aure har da zuri'a. Shi yasa bata son zaman cikin mutane." Ta isa wurin dattijon ta zauna cikin ladabi da biyayya irinta matan da suka ga koya suka ga yau, gashi har gobe ana saka musu ran zasu gani cikin harshen fulatanci ta ce mishi. " Jam na?" Kallonta yayi na wani lokaci kafin ya ce mata. "Lafiya lau Hajja!" Gyara zama tayi cikin ladabi ta ce mishi. "Ina son na gaya miki, ko zaki yiwa Auta magana ta kira malamin nan zata turo abin nan da ake tura kudi ta ciki!" Murmushi yayi ya ce mata." Hajja kina tsammanin Turaki zai dawo ne?" Cikin tsantsan biyayya ta ce mishi. " Nasan bayin kanta bane zata dawo, waye nake da shi bayan Harisu? Turaki ita ce nake kallon a matsayin Harisu, ki yi hakuri ki bada umarni ta tura mata kudin. " Wato dariyar da Ubaid yake kamar cikinsa zai kulle, ya tab'a zuwa gidan nan bai fita bai dara ba ai kuwa? Babu ranar domin ita kanta Hajja comedian ce. Alhaji ELYakub kuwa so yake ta daina yarda da wannan maganar domin wanke ta ake yi. " Alhaji baki ce kome ba?" Murmushi yayi yana kallonta. Hango yar karamar kanwarsa da suka hada Iyaye maza wacce aka ce ya je ya ganta ko tayi mishi, yar kwailar nan da suka je ganinta, tayi ta zuba gudu da boya ance saurayi ya zo wurinta. "Alhaji baki ce kome ba?" Ta kara fada Hajja a wurinta mace namiji ne, namiji kuma mace, ta juya musu lamarinsu mai sauki ne kusan dabi'ar Fulani da Barebari da nufawa, haka harshensu take taking over na jinsin matukar bada yaransu zasu yi maganar ba.

Akwai wani abu da Hajja da Alhaji ELYakub suka kasa boye shi, kaunar Jikansu da yake bala'in wahalar da su. Domin kaf duniya babu wnada yake juya kakaninsa, kamarshi sauran jikokin basu samu wannan damar ba yo Alhaji ELYakub bai yarda da wasan jika da kaka ba, domin yana da zurfin ilimin addini da na boko, gogaggen dan kasuwa ne, top-notch wanda aka sani a nan kudu da arewa. Mutum ne da yake faɗa aji, domin ya bunkasa fiye da kima, hatta Yarbawan lagos suna matukar ganin girmansa, kamar yadda suke ganin girman dan gote. Idan za ayi lissafin attajirai da suka boye kansu ELYakub Kumo yana cikin manya na farko.

Domin yana da hadin gwiwa da bankunar kasar nan, irinsu First bank, UBA, Union Bank, Zenith bank, ya kawo wannan hadin gwiwar? Duk da bankunan ne suka bukaci alaƙa da shi ba shi ya bukaci alaƙa da su ba, akwai lokacin da idan mutum ya isa wani limit baya bukatar ya tura kansa sai anyi da shi, lokaci yake zuwa ayi da kai. Haka ce ta faru. "Alhaji baki ce kome ba?" "Shi kenan zan gaya mishi shi kenan?" Gyada kai tayi ta gyara zama ta fara bashi labarin da Malamin ya gaya mata akan Turaki wanda kusan tishi ce ai ya saba jin wannan labarin ba sabo ba ne a wurinsa. Karshe ma ga yadda hiran ta kasance. "Ita Turaki ta hadu da aljani suka auri juna har suka hayayyafa yaran suna zuwa cikin gidan nan har wurinki, yanzu da ayi kiranye kenan?" Shiru yayi yana kallon yadda ta damu kuma ya ce mata. "Gaya min me Malamin ya ce miki." Gyara zama tayi ta ce mishi. "Kin san bana bin makamai amma wannan karon nace bari na hada malami guda biyu, tow ita ɗaya ta Gombe ta ce min babu abinda ya faru, ƙaddaranta ce har yanzu bata zo gare ta ba. Amma ni ban yarda da ita ba, don bata ce za'ayi aikin kome ba, ta dai ce kome da yake faruwa haka Allah yaso, idan aka yi hakuri ita Turaki zata dawo da kanta, tow na dai bada abin sadaka ya ce ita bata karban Kudi dayawa shi yasa na fahimci karya take yi, tow ita ɗaya ta kome tace akwai mata aljani suna tare har suna da Yara da shi, ita Turaki ya auri matar aljani ne, shi yasa shi matar aljani ya dauke shi daga wurin mu, idan har muna so ya dawo sai an biya kudin kamar dubu dari hudu da saniya baka wuluk sai a sayi farin kaza, dan taure baki, kaza buja-buja. Jan dawa, bakin dawa, kaura, da fura kwarya goma." "Hajja karya yake shi yake son cin kudinki." Inji Alhaji ELYakub, shiru tayi tana kallonshi idanunta ne suka shiga cika da kwalla. "Alhaji ki fahimci yadda nake ji!" Riko hannunta yayi ya saka nata a cikin hannunsa ya dunkule hannun a hankali yana bugawa yace mata. "Fadime, ki yarda da maganar wancan malamin farkon shi mutumin kirki ne, shi kuma wannan dan damfara ne, Fadime ina son ki yarda kaf duniya ba mai yi sai Allah. Ni nasan Turaki zai dawo lokaci ne kawai bai yi ba, idan kika ce zaki dawo da shi da karfi zai koma. Kin tuna yadda ya dawo wasu shekaru kafin lamarin ya lalace haka. In sha Allah Turakinki zai dawo gare ki." Mikewa Ubaid yayi ya basu wuri can wajen gidan ya fita ya damu daya daga cikin kujerun alfarma ya zauna ya zaro wayarshi. Sai da ya cire shi a key ya tsaya yana kallon hotonsu na kuruciya, suna dariya ya danne bayan Turakin. Murmushi yayi sannan ya cigaba da. Lalubar wayar har ya zo kan number shi wanda ya rubuta Introvert. Wayar har ta gama ringing ba a dauka ba, sai can aka turo mishi sako da number. *Ya suke?*........... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA BIYU

Daga wannan babu wani sakon, har leka bayan wayar Ubaid yayi ko zai ga sauran sun makale, amma ina iya su kenan kalma biyu, harufa hudu? Wato shi dai ba zai tab'a sauya ba. Cikin fushi shima ya tura masa da Ash'ar. Tunda ya tura ya kai minti goma a wurin ba reply ai yasan ko sama da kasa zasu hadu ba zai dawo mishi da sakon ba, idan yayi sa'a gobe ma da zai kara tura mishi abu daya ne zai sake turo mishi. Sake kiran layin yayi ya danna mishi busy. Takaici ya saka shi wucewa gidan ya samu Hajja da Alhaji ELYakub sun koma hiransu, mika mishi File din yayi ya ce mishi. "Wannan sune sakon da ya bani, sannan da farko ban fahimci yadda sakon yake ba, sai dazun nan na fahimci sakon." A hankali ya fara warware mishi bayanin da Turaki ya turo mishi, shiru yayi yana mamakin yadda, kome yake tafiya ba tare da saninsu ba. Sannan wani abin da ya bashi tsoro yadda aka karkata da kuɗi ta wani hanyar da bai dace ba. "An samu masu hannu a cikin lamarin?" Bude baki Ubaid yayi zai magana aka turo kofar, Alhaji Mudansir ELYakub Kumo ya shigo cikin wata danyen Wagabari dark blue, yayi ya wani irin daukar fatarshi. Sai wani shaki yake kamar dare kwana sha huɗu, duk wanda ya ganshi yaga wanda arziki ya zauna mishi, cikin isa da kasaita ya samu wuri ya zauna cikin girmamawa ya gaida iyayensa. A hankali ya mai da hankalinsa wurin Mahaifinsu da ya ga ya tattara nutsuwarsa ga Ubaidullahi. "Yanzu ka mai da mishi sakon kace yayi duk abinda yake ganin ya dace, sauran kuma zan dauki mataki in sha Allah ba zan bar kome ya tafi a haka ba." Wani irin harara Alhaji Mudansir ELYakub ya watsawa Ubaidullahi ya cigaba da sauraren maganarsu da ba fahimtar inda suka nufa yake ba, tunda kusan a dunkule suke maganar. Mikewa yayi don ya fahimci a al'amarin duniyar nan matukar maganar Turaki ne tow dattijon Mahaifinsu baya sauraren kowa kuma baya fahimtar kome idan har da a furta sunan Turaki a gabanshi ko a gefensa. "Baffa zan leka kamfani." Kallonshi Hajiya Dadda tayi ta ce mishi. "Saurin me kike yi da ba zaki zauna ta gama magana ba? Ban san me yake ciwon ranki idan kika zo ki ka ga ana magana akan Turaki sai ki tsirfo da wani hali." Daga haka bata kara magana ba, ta dauke kamata kamar ba ita tayi maganar ba, kunya ce ta sa shi komawa ya zauna. Burinsa ya fita waje ya jira Ubaid yaji wani abu suke shiryawa. Bai gama wannan nazarin ba sai ga Alhaji Mujitafa, wanda suke kiranshi Auta. Cikin girmamawa ya gaida Iyayen nasu sannan ya kalli Ubaida ya ce mishi. "Second love, kai ne da sassafen nan?" Gyada kai yayi yana murmushi ya ce mishi. "Uncle Auta barka dai." "Barka second love, ina wancan Introvert din ya shiga ne? Na kira bai dauka ba." Kunshe dariya Ubaid yayi yana kallon Uncle Auta da yake ƙara duba wayarshi. "Duba ai ba zai gaza turo maka sako ba!" Dubawa yayi yaga sakon. "Sorry im busy!" Tsaki yayi ya ce musu. "Baffa na gaji da halin Turaki." Make shi Hajiya Dadda tayi cikin wannan rikitaccen hausar nan nata me juya mace namiji , namiji mace ta ce mishi. "Kin ci gidanku, mara kunya in gaji da halinta, wani hali ne da ita banda halin kwarai, ita yaron nan Turaki mutumin kirki ce, kowa yasan tana da kirki amma bakin halin zeenatu da yayiwa Turaki sharri, ina da tana nan da nata iyalin, wai yaron dan uwanku kenan kuka juya mata baya ke Auta da nake gani a mutumin kirki amma kike cewa kin gaji da halinta. " Matsawa can yayi yana jin zafin yatsun hannunta. " Daddah kece kika bawa Turaki dama yayi yadda yake so, Fisabiilillahi me ya nima ya rasa. " " Abubuwa dayawa. " Inji Alhaji ELYakub Kumo ya fada ya ce mishi. " At teenage ya rasa Uwa da Kannensa, sai Jasminah itama don ba yadda ta iya da shi ne, tunda su biyu suka rage, tunda ta zama yar amshin shatar zeenatu, koda yake uwarta ce ba yadda ta iya amma a gefe guda ina ganin laifinka ne, Mudansir. " " Baffa ni kuma?" Ya nuna kanshi da muryanshi a shake, " Eh kai;" shigowa wasu matan alfarma suka yi tare da wani shima babba a cikin gidan. " Daddy! " Ta kira sunansa. Kallonta yayi yana mai mika mata hannu ta zauna a kusa da shi, tana kallon Alhaji ELYakub Kumo ta ce mishi. "Baffa ina kwana?" " Lafiya lau Fadima." "Barka da safiya Kawu?" " Barka dai Munir!" Shigowar wata hamshiyar mace parlourn cikin wani uban ado kamar zata biki da daya daga cikin yan matan nan da suka je salon, nunawa yarinayr wurin zama daya yarinyar tayi. " Badar ga wuri! " Wani yatsina fuska tayi, tana kallon gefen da mahaifiyarta ta zauna. Itama nan ta zauna.

Kallon zuri'arshi yayi babu bare a cikinsu dukkansu ahalin Kumo ne, kuma masu hannun jari a kamfanin KUMO properties nigeria agency, kamfani ce fa take sayan duk wani kadara da gwamnati zata yi gwanjonsa, kamfani ne da banku suke binta, ba iya nan ba akwai wasu iyalan nan, domin kuwa lissafin a bayyane take.

Su waye KUMO properties nigeria agency?

Alhaji ELYakub Kumo, dan asalin Gombe ne da ya fito daga garin kumo, ba fulatani ne da ya gaji arziki daga iyaye da kakanni domin su ke da sarautar Sarkin Fulani Kumo anan lagos sarautar ce da ita ta Sarkin Fulanin lagos., dogaye ne masu matsakaicin jiki yayinda matan cikinsu suka kasance sirara iyayen suka kasance yan chubbys.

Alhaji ELYakub yana mata daya Hajiya Fadime, wacce suke kiranta da Daddah. Ita ta haifi Yara shida maza uku mata uku. Marigayi Alhaji Haris shi ya fara bada shawarar kafa kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma har yanzu sana'arsu ta gado sayar da shanu da madara basu fada ba domin bude wani kamfani aka yi na sayar da madarar shanu da namar shanu. Kasancewar Alhaji ELYakub da girmansa ya fada harkan boko, domin lokacin da ya auri Dadda bai gama secondry School ba, tun yana Yaro dan shekaru goma sha uku yake kad'a shanu daga Gombe to lagos, a cikin gwangwaro. Haka yasa wani bayarabe ya bashi shawara ya fara karatu domin Allah ya mishi baiwar iya sarrafa kudi, gashi tun yana wannan shekarun turanci ya zauna akan harshensa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull