ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 16
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 16: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 16. Kusan fulanin zamanin da akwai zuciya haka yasa yana dawowa ya fara makaranta, shekara daya…
4,377 words
Kusan fulanin zamanin da akwai zuciya haka yasa yana dawowa ya fara makaranta, shekara daya yayi a primary ya tafi secondry School, yana da shekaru ashirin cib ya gama secondry School, a wannan shekarar aka auren mishi yar baffansa Daddah. Zamansu yayi albarka domin kuwa kuwa an haifi Harisu wanda shine Babba,sai Mudansir, Khaulatu, Sameerah, sai Ramatu kafin Uncle Auta wato Mujitafa. Kamar yadda suke su shidan haka kowane a wurin halinsa daban, Alhaji ELYakub ya gina kansa da matsayin da yake ta hanyar sana'ar sayar da shanu daga Gombe zuwa Lagos, kafin wani abu ya faru a gabansa, wani mutum ne ake bi bashin banki, su kuma banki suka zo kwace kadarorin mutumin lokacin duniya tana kwance, a take suka fara kwashe kayan sanin cewa suna tare da bayaraben for while sai ya tambayi kudin da ake bin mutum banki ta fada mishi, cikin ikon Allah sai ya gwada biya, tare da maida wa mutumin kayanshi idan Allah ya hore mishi ya biya shi. Shi dai da farko bai dauki haka a matsayin wani babban al'amari ba.
Bayan an bashi shawarar ya dawo Lagos da zama ai zai fi yana sakawa ana kawo mishi dabbobin daga arewa, ace duk bayan sati biyu yana hanyar Lagos, a lokacin ya haɗa degree dinsa na daya zuwa na biyu, ga shi idan ya ce yana da iyali ƙaryata shi ake domin a lokacin ya cika shekaru talatin a duniya, haka ya nime gida a alaba rago, ya kawo Daddah da Yaranta, dama can ko a Gombe Yaran suna karatu domin Daddah tana haihuwar kunika ne, yaran kusan kansu daya idan ka cire Harisu da ya fi su tsawo, tunda suka dawo Lagos sai rayuwarsu ta kara inganta, idan aka samu jajjirtaccen namiji akan ilimin Yaransa, tow bakiɗaya dauke kome yake yi, haka Alhaji ELYakub ya kasance, ya tsayawa Yaransa musamman harisu da ya kasance mai zuciyar neman na kai, domin shi ya fara bada shawarar Daddah ta fara sayar da fura da nono lokacin bai wuce shekarun sha biyar a duniya ba, da ya gama secondry yana jami'a shi ya fara gayawa Mahaifinsu madadin kudin da yake biyawa mutanen da suka shiga matsala da banki yayi Register da lasin domin ya fara sayan kadarorin mutane, idan ka biya kudinsu ka dauki kayanka, a yanzu an cigaba, shi anan kasar turawa da yake karatu haka suke yi, domin shi a can Rasha ta tafi karatunsa bayanshi babu wnada ya samu wannan damar domin sun dauki irin rayuwar karya da son a san su din wasu ne, Uncle Auta ne kaɗai yayi karatu har zuwa Nijar, da yake shi din na. Musamman ne, Allah ya haɗa jininsa da dan uwansa Harisu, Haris yana da abokai guda biyu, Jibrin Mahaifin Ubaid, sai Abbas, abokai uku nan sun taso cike da kaunar juna da adalci idan ka cire Uncle Auta a cikinsu wnada ya kasance Yaro ne.
Jibrin Mahaifin Ubaid, dan Kanwar Alhaji ELYakub ne, ya dauko shi ya kawo shi gidansa tun suna Yara, shi kuma Abbas dan abokin Alhaji ELYakub ne, mahaifinsa ya rasu Maraya ne, wanda dangin mahaifinsa suka kwashe dukiyarsa suka watsar da shi. Haka Alhaji ELYakub ya haɗa su da nashi.
Lokacin da suka dawo gidan ba karamin wulakanci suke sha da Mudansir ba, domin kiri-kiri yake nuna musu sun zo cin arzikinsu ne, Jibrin yana da zuciya sosai haka yasa ya daina zama a gidan, don yana jami'ar Lagos a can yake karatu yake zaune sai weekend da yake shigowa, Abbas dai yake nanike Mudansir idan Harisu baya nan, domin yana da bala'in kwadayi da son abin duniya.
Lokacin da Harisu ya dawo sai gashi tare da wata yar kasar habasha, amma haifaffiyar kasar rasha, mai suna Annah. Kasancewar Alhaji ELYakub bai hana kowa yadda yake so ba, haka ya amince da abinda dansa yake so, amma da sharadin idan ya gama ya samu lokaci zai aura mishi yar dangi, bai ki ba shima Harisu ya gayawa Annah tana sonshi, haka yasa ta amince, Ubanta mai kudin gaske ne a rasha da Habasha, don kusan da yardan Iyayenta suka tawo gani take idan Harisu ya dawo ba zai tab'a aurenta ba, Annah ba fara bace asalin kalar fatarta na an Ethiopia ne, shi harisu ne ma Faris sosai domin shi ya dauko fatar Daddah don ita farin fatarta har wani jajja yaƙe. Irin tarban da suka yi Annah yasa abin ya bawa yan uwan Harisu haushi, amma Jibirn ya goya mishi baya, satin su biyu suka tafi har can rasha aka basu auren Annah, sai dai tunda aka yi Auren yan uwansa suka tsangwami Annah saboda ita bata sallah, haka yana basu haushi bayan sun manta cewa Addini ya bawa maza musulmai damar auren auren Ahalul kitab. Wani ikon Allah annah tana shigowa sai ciki, wannan cikin ya saka mata kwadayin abubuwa musamman fura da nono, sai tuwon dawa, wanda kusan abincin Alhaji ELYakub ne, haka suka hadu suka yi renon cikin har ta haifi danta, namiji Masha Allah.
Lokacin da sako ya isawa danginta, sun zo domin farin ciki. Ranar suna ta ce ta bar addininta na Kirista ta koma addinin Muslunci, yaro ya ci suna Bilal wanda Jibirin ya ci Turaki domin a lokacin sunan yaron aka kara bunkasa kamfanin KUMO properties nigeria agency, aka kara fadadda shi, a lokacin Jarin Alhaji ELYakub yayi kasa, sai da Annah wacce sunanta ya koma Nana Aishatu, ta tafi har rasha ta nimo kudi, a wurin mahaifinta iya mata uku ya haifa. Annah Aisha ita ce Babba haka yasa da tazo da bukatarta basu hanata ba, ita ce mutum na farko da ta fara saka hannun jari a Kamfanin, kafin Bilal ya cika shekara biyu a duniya Kamfanin KUMO properties nigeria agency yayi wani irin bunƙasa. [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 23
Irin bunƙasa da ba a tab'a kawowa ba, kasancewar ko a can rasha ita take ji da kamfanin mahaifinta, sai Harisu ya ce a bata wani bangare na kasuwanci a kamfanin yadda zata iya jagoranta, duk abinda zai yi sai ya fara da iyayensu sannan ya kawowa abokinsa Jibrin shi yake bashi shawara. Rike kamfanin da Annah A'ishah tayi ya kai kamfanin wata irin matakin nasara, a lokacin ta samu cikinta na biyu, tana kuma jagorantar kamfanin, kafin ta haihu bankin First suka fara kulla Yarjejeniyar kasuwanci, wnada idan aka samu matsala na bashi su zasu fara tuntuba, domin babu kamfanin a kasar nan sai su ne suka fara jagorantar shi. Shekarar Turaki biyu da wata goma aka haifa mishi Yakub wanda suka kiranshi da Baffa, wani irin kaunar Yaran suke kamar su boye su.
Daddah kuwa soyayyar duniya ta daurawa Turaki, sonshi take kusan tun yaye ta rike musu da taki basu. Sai a lokacin Mudansir ya koma makaranta, suma matan da suka fara maganar karatu Alhaji ELYakub ya ce sai dai su yi aikin mazansu. Khaulatu dama suna soyayya da Abbas, Sameerah kuma tana tare da wani dan Kano da yake nan Lagos, ELYakub yaso Jibrin ya auri Ramatu amma yaki domin ya riga Harisu aure, matar ce dai take Gombe, itama tana da Yaro Ubaid wanda kusan wata uku ne tsakaninsu da Bilal Turaki.
Ita Khaulatu tana cikin wani gidan da Alhaji ELYakub ya basu ita da Abbas, haka tayi ta fama itama dai ta koma boko damuwarsu shine matsayin da Aisha da harisu suke kai su samu, sai dai irin wannan matsayin ana samun shi ne ta hanyar da ta halatta, haka suka sakawa ransu kyashi da hassada, wanda yasa suka kasa gaba suka kasa baya. Abin haka yayi ta tafiya har zuwa da ta yaye me sunan Baffa, sai ga wani cikin. Murna a wurin harisu da su Daddah abin ya wuce sanin kowa, haka aka haifi wannan karon namiji, a take yayiwa Yaron huduba da Jibrin suna kiranshi Aydin, bayan wannan Yaron bata kara haihuwa ba, sai bayan shekaru goma, ta haifi Fadime. A lokacin KUMO properties nigeria agency ya kai matakin da sai da aka bude mishi branch a Kano Fatakwal da Abuja. Annah Aisha itace bakiɗaya CEO na kamfanin yayinda Haris yake vice President na kamfanin wanda ya janyo idanun yan uwansa ya tsaya akansu.
Kusan rabin dukiyar kamfanin 65% na Annah da Yaranta ne, 5% na masu saka hannun jari ne, 20% Na ELYakub ne 10% na Harisu. Annah bata yi duhun kai ba duk yaran ta raba musu hannun jarin musamman Bilal Turaki, wanda ta bashi 25% na hannun jarin. Saboda shi yana karatu a King Abdul Aziz International school Riyad tare da Ubaidullah Jibrin Kumo, haka yasa bai wani san damuwa ko tashin hankali ba, yana aji biyar na secondry School, bayan sun kawo mishi ziyara, Allah ya musu rasuwa bakiɗayansu Ita Annah Aisha da Kannensa. Kuma ba a gaya mishi har sai da ya gama karatu suka dawo gida aka gaya mishi a lokacin ya zo ya samu Mahaifinsa da wata mace ba Mommy dinsa ba, kamar yayi hauka don yaji ya tsani. Haka yasa shi yayi fushi ya koma wurin kakaninsa, har izuwa lokacin Ubaidullah bai rabu da shi ba, domin da zai koma Rasha tare suka tafi a can suka cigaba da karatunsu, kaf duniya babu wnada ya fahimci Bilal Turaki sama da Ubaid, yasan halinsa yasan shi sama da sanin da zaka yiwa wani a duniya. A lokacin da Annah Aisha zata rasu a cikin kwanakin ta haɗa kan hannun jarin bakiɗaya ta tattarawa Bilal Turaki, domin tana jin wani strange abu yana bibiyarta, haka yasa ta haɗa kome ta tura Rasha wurin iyayenta da yan uwanta. Bayan haka Haris da ya auri Zeenatu itama tana zuwa ta samu cikin Jasminah a burinta namiji zata kara haifa sai aka yi rashin dace ta haifi Jasminah, wacce suka daurawa jigon 20% na hannun jarin Haris zai bar mata. Shi kuma kamar wanda aka gaya mishi ya raba hannun jarin ya sakawa Ubaidullah 5%. Bilal 5% Hajiya Zeenatu da yarta 10% sai abin ya fisgi hankalinta akan me za a karawa Bilal a kuma bawa Ubaidullah da bai zama kome a cikin KUMO FAMILY GROUP ba. Shi kuwa ya ce ya yanke.
Tsakanin Alhaji Haris da Annah Aisha shekaru shida chib wanda ya tilastawa Bilal Turaki dawowa Nigeria, shi kan Ubaidullah ya jima da dawowa gida domin har yayi aure da zuri'arshi. A lokacin rasuwar Mahaifinsa ne ya zo gobe tun suna Yara sukan zo bikin sallah karamar Sallah da babbar sallah. Haka sai yasa Kumo Family group matan suka saka buri akan magajin KUMO properties nigeria agency, domin ya haɗa degree dinsa na farko yana da shekaru ashirin cib a duniya. Wannan rashin da yayi duk da yana jin zafin mahaifinsa, ya kara pushing dinsa gefe ya saka shi kara zama wani irin mutum me murdaden hali. Da manya da yara na Kumo Family group kowa shakkarsa yake, bayan gefe guda gasa suke da juna.
A lokacin abinda Alhaji ELYakub yayi shine bawa Bilal Turaki kujeran mahaifiyarsa, kasancewar ita ce mafi yawan hannun jari wanda a yanzu Bilal yana da kashi 70% na hannun jarin KUMO properties nigeria agency, sai dai haka kawai ya juya ya koma inda ya fito, ya cigaba da karatunsa. Bai kara dawowa Nijeriya ba sai rasuwar Alhaji Jibirin Kumo,. A lokacin yana da shekaru talatin da wani abu a duniya, akwai ciwon da yaji da yasa shi tattarawa ya koma Germany wurin Ellina, Kanwar Annah Aisha, tana auren wani magajin garin Berlin, anan ya cigaba da aiki da babban Cibiyar nukiliya ta Germany.
Yan mata dayawa sun yi kuka akan Bilal Turaki, amma shi ko a kwalarsa. Bai damu da kowa ba a duniya sai mutane hudu, Alhaji ELYakub, Daddah, Uncle Auta da Ubaid, haka a wurin kakaninsa na Uwa yana sonsu. Turaki mutum ne da baya shiga rayuwar kowa, baya kuma da rawan kai irin na yaran masu kuɗi, duk da gadon da yake da shi Bilal niman kudi yake kamar ba attajirin da aka tara mishi ba, an taɓa hira da shi. Aka tambaye shi me yasa yake niman kudi bayan yana cikin manyan matasan Nigeria masu arziki, budar bakinsa ya a cikin muryansa mai sanyi da dadin amo, ya ce musu. "Wancan dukiyar ba Bilal yayi faffutukar tarawa ba, dukiya ce da mutane uku suka tara idan nayi amfani da shi akan kaina na zama cima zaune idan na nima da kaina zan iya rike kaina da kuma duk wnada zai zauna a gefena." Idan bilal yayi magana mai tsawo haka yana nufin yana son maganar ce.
Kai ko a cikin abokai ne yana iya ware kansa, ya koma gefe yana abinda yaga zai iya. Yana iya daukar nauyin abokansa ayi shagali amma shi zaka hango shi can gefe yana wani aiki abinsa. Idan kana son ganin asalin Introvert tow Bilal ne, domin ko lokacin da ya fara soyayya Ubaid da Alhaji ELYakub suka sani, haka da yarinyar tayi rejected dinsa, sune suka san me ya faru. Da abin ya faru sai da yayi kusan kwanaki uku kafin ya tattara ya bar musu kasansu. A lokacin Alhaji ELYakub yaso ya je har wurin dangin Yarinyar ya nuna musu jikanshi ba talaka ba ne, amma ya ce mishi.. "Ni mace nake so da zata so ni ba tare da tasan who am I, kada ka je ina ji a jikina ita din mahadar rayuwata ce."
Duk da yan matan da suke hauka da fada da dambe akanshi, haka bai taɓa burge shi ko jin a ransa suna kan daidai ko sau daya basa gabanshi.
Hajiya Khaulatu tana da Yara biyu, Khamis da Khamis baya jin magana, niman mata shaye-shaye, fadar area ta dabba. Duk wani iskanci ya kare a gindin Khamis sai yar su ta biyu Badar tare da Alhaji Abbas, wacce take zaman jiran Bilal, don tace sai dai ta mutu bata yi aure ba. Mimi yar wurin Hajiya Zeenatu tsohuwar matar Haris, bayan rasuwarsa aka hada auren da Alhaji Mudansir ELYakub, bayan Jasminah ta haifi Mimi Fatimah, ita bata damu da wani soyayya ba, don ita ce asalin Queen of Kumo Family, ana ji da ita. Zaheeda, yar gidan Hajiya Samirah itama tana son Bilal, don ita har inda yake ta je mishi. Badar kuwa a gidansa da yake Lekki take zaune.
Sai Nasmat wacce take nan lagos a gidan Uncle Auta, shima Uncle Auta da yake da Iyali Yaranshi maza hudu ne, kuma kanana ne, Yakub wanda suke kiranshi da Amir, sai Harisu wanda suke kiranshi da Akhi, sai Jibrin wanda suke kira da Aalim. Kaf duniya daga Ubaid sai Uncle Auta suka san meye Turaki yake so, me yake bukata ja'iri bai da alkibla, akwai wani zuwan da Turaki yayi lokacin Alhaji ELYakub bai da lafiya an dauka mutuwa ma zai yi aka gaya mishi, zuwan da yayi ya tashi wani tashin hankalin da ba taba gani ba, domin ya zo gidan duk babu kowa a gidan domin bai gaya musu yana hanya ba, a lokacin da ya iso gidan domin drop ya dauka har gida, da farko security din basu gane shi ba, domin shigar da yayi sai da ya cire facemask dinsa suka gane shi ne, haka ya shiga gidan akwai wata yar mota da take kai mutane har cikin gidan, ita ya shiga aka kawo shi, zuwan da yayi ya shiga bangaren Daddah anan ya samu Mimi tana yiwa Daddah barna, shi kuwa ya kamata ya zane ta, karshe ya rufe part din Daddah ya tawo asibitin, ana ta murnan ganinsa sai ga kira daga gidan, aka kira Hajiya Zeenatu tana isa gidan ta ga abinda yayiwa Yarta, ai kuwa ta kawo yarinyar, jin haushi da kishin yadda aka wani zagaye shi ta saka hannu a kai tana kuka wai yayiwa Yarta fyade. Wannan abin ya daki Turaki. Kiri-kiri Badar tace mata. "Karya kike Maman Mimi!" Da yake yaran a sangarce suke ba wanda ya kwabe ta.
Case ɗin sai da aka hura shi ya zama babban al'amari, hankalinsu ya kwanta Alhaji ELYakub yana ji yace su bar mishi gidansa, bai lalata na wasu ba, zuriarsa ba zasu lalata nasu ba. A lokacin Turaki yayi fushi ya bar musu kasar, suna son ya dawo ko don yanzu a raba matsayi a kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma yaki dawowa, yaki yin wani motsi su kansu basu san inda yake ba, idan ka cire Uncle Auta da Ubaid, babu wanda zai baka labarin inda Turaki yaƙe.
Ita kuwa Daddah cewa take aljanun sun aure mata jika domin yaki maganar aure, ko irin kiranshi Uncle Auta yayi haka zata gama surutunta baya ce mata cikanki, har mamaki yake yadda bai damu da magana ba, sam shi magana tafi kome bashi wahala. Don da yayi magana gara ya shiga daki ya kwana ya wuni. Shi har mamaki yake idan ya ga mutane na magana, idan da zai yi magana tow abun da zai magana a kai me muhimmanci ne.
*** Lulu. Na samu wata biyu, ina zuwa wurin Mrs Dije Bala, sannan gefe daya ya haɗa min wani tables na abincin da nake ci, domin maganin da haifi yake bani sun yi sanadin da kitse da uric acid ya taru min, haka yasa nake samun wani irin gajiya. A hankali nake bin kome, kullum haka zan tafi wurinta na dawo. Ya Hafiz yaso kashe ni ne, Allah bai nufa ba. A hankali na dan fara samun nutsuwa, ina cika wata uku na gama iddana, a lokacin naji kamar na samu yanci, har da wannan iddar ya saka min traumatic domin gani nake kamar Ya Hafiz zai iya cewa ya dawo da ni, a wurin da nake zuwa akwai Reheb, a nan idan na je naji matsalar wasu ashe ni nawa mai sauki ne, domin gashi wasu yaran masu kuɗi ne wasu matan masu kuɗi amma rayuwarsu ta lalace, akwai wata yarinyar da muka hadu sunanta Baby Mahaifiyarta yar Jos ce, mahaifinta kuma bayarabe amma gata yasa ta lalace, sai gashi ta samu miji shi ya kawo ta wurin Dr Dijah Bala, yarinyar tana da saurin sabo, duk yadda naso na ki biye mata, haka take makale min.
A bangaren Ya Ado abokan aikinsa har mutum uku suna niman izinin aurena, ce musu yayi su yi hakuri har yanzu Lubnah she still small girl... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 24
Wannan kalaman ya saka aka shafa min lafiya, tabbas ina bukatar spaces sosai Ina bukatar nutsuwa wanda zai saka naji nima mutum ce kamar kowa, ina bukatar farin ciki da nutswa amma ta ya? Ta hanyar bani duk wani tazara da zata saka ni farin ciki, a hankali rayuwata ta mike, har watan azumi ya zo farkon watan azumin Ya Ado ya mana albishir da zuwa Umara a can zamu yi sallah, Yadiko Abba ya biya mata da ita da shi, Mama kuma Ya Ado ya hada mu ita xata tashi ta Bauchi, mu kuma ta lagos, wani abu da ya kara d'aga min hankali wannan kibar yana damuwa duk yadda nake son rage shi kamar kara shi nake, haka yasa Doctor Ahmad ya hada ni da wani likita anan lagos a cikin wata azumin kafin mu tafi Umara, lokacin da na ga likitan, ya sake tsara min abinci sannan ya hana ni shan kowani magani da zai saka ni nayi slimming domin na fara shan wasu ganyen shayi, ya hana ni. Kamar da wasa na fara shan kiyayye maganin da yanayin, sai dai kuma ko ana gobe zamu Umara, sai da ciwon ciki ya taso min, haka nayi ta daurewa har muka tafi umara a can kuwa kasa mai tsarkin na fadi na suma haka aka tafi da ni asibiti hankali a tashe, lokacin da aka min test anan aka hango cutar fabroid a cikin mahaifana manya guda biyu sune suka hura min tumbina, suka ce aiki nake bukata, Ya ado yace su bani magani da abinda zasu bani kawai mu koma gida ayi min domin bai zo da shirin aikin ba. Lokacin da ya samu Mama da yadda suka yi da likitan, ta ce mishi. "Wani ba a shirya ba kuma? Kawai mata aikin na hakura guzurin yanzu akwai abinda za a bukata a rayuwar lubnah nace babu shi? Ayi aikin Allah ya bata lafiya kowa rai ya amfana baya ga mai shi ne, ni yanzu bata kaina nake ji ba, ta ita nake ji"
Haka aka yi min aiki a washi gari ranar da aka kai azumi ashirin da uku. An cire tare da kashe waɗanda suka fara zuba karin, sannan aka fito da ni. Yayuna a Bauchi kamar su tawo, don sun tabbatar zasu zo Lagos ganina. Sai nake jin kamar ni daya nafi kowa gata, daren ashirin da uku ake ta saka ran alamun laylatu kadr, yadda ake pretending din yanayin sai bai kasance a wannan daren ba, aka wuce zuwa daren 27, wanda tun wunin ranar Mama da take kula da ni take addu'a nima kuwa Addua nake, karshe Mama kasa hakuri tayi ta saka aka bamu keken mara lafiya muka wuce harami, ranar na ga gundarin kauna a wurin mahaifiyata, mantawa da kanta tayi tana zagaya da ni Ka'aba tana "Allah ga Lubabatuna, Allah ka bata duk abinda ta rasa a baya, Ya Allah ka bata miji na gari. " Sai da naji kamar buga min guduma tayi domin gabana ne ya fadi. Tsoron maza ya kara shiga zuciyata. Haka take addu'a miji na gari har wasu yan Nigeria da Nijar suka yi ta mara dariya, wai tana ta addu'a kamar ita ɗaya ta haifa murmushi take kawai ta ce musu, da kun san irin Izayar da na mata zaku ce ta cancanci haka. Wannan ranar Mama bata mai da ni asibiti na har aka Sha ruwa, ta mai da ni, sannan ta dawo harami yin sallah tahajju.
Asibitin kuwa ana tasowa sai ga Yadiko da su Ya Ado, da Yaran da Aunty Zakiyah, ai kuwa na ji dadi murmushi nake idan suna hira, haka suka yi sahur bayan sun gama suka tafi masallaci, nima a nan nayi sallah bayan sun dawo, Mama ta koma ma sauki ni kuma aka barni Asibitin. Ai kuwa Yadiko suka yi fada da Abba ya ce ta nime abokin tafiyarta ta ce mishi.. "da yake makauniya ka kawo ba." Rigima fa wai akan me tazo duba ni, haka ta fada mana da tazo ni dai umarana ta bana a gadon asibiti nayi shi, ranar ya kasance juma'a, don haka nima an fitar da ni domin ita ce Juma'a ta karshe, ranar Litinin ake saka ran karamar sallah, haka yasa aka fitar da ni. Nayi addu'a Ubangiji ya kawo min nutsuwa da kwanciyar hankali, Ubangiji ya bani kwarin gwiwa, Ubangiji ya cire min tsoron wani abokin halitta a raina, na roki Allah ya mantar da ni rayuwar baya. Ya saka min hakuri da dangana.
Ganina a dakin Ka'aba ya saka min yarda da cewa Ubangiji yana nan yana jina, shi din rayayyen nan ne da baya mutuwa, bai haifa ba, ba haife shi ba. Sai nayi kukan farin ciki ya saukar min wani nutsuwa na musamman. Naji nauyi da zafin da nake ji yana sauka a raina, na ji farin ciki da rabona da naji shi tun ina JIBWIS, a ranar Mama sai da suka yi magana da su Aunty Zakiyah wai sun ga kamar ba ni, haka muka yi ta ibada, har ranar sallah. Wayyo yadda kowa yayi wanka sallah amma ni ba hali saboda dinkina. Haka na saka abaya mai sauki. Sallah da kwana biyar muka dawo gida, haka na cigaba da jinya satin mu daya da zuwa dai ga Aunty Hindatu da Aunty Innah, Aunty Munah da Aunty Raliyah, wato wani abu da na kara fahimta shine yadda suke yiwa Aunty Zakiyah shatara na arziki, ban yi mamaki ba domin basu isa biyanta Alkhairin da take min, bamu isa biyanta biyan ba, Dr Dijah Bala da Baby sun zo min ya jiki, haka Aunty Zakiyah ta cire musu tsaraban da ta musu. Tace musu nice nayi musu sai nayi ta mamaki, wani ikon Allah satinsu Aunty Hindatu daya suka koma.
Wata na biyu goshin layya ina jin duk wanda ya ganni sai ya ji na burge shi, domin jikina ya ragu, a lokacin da Ya Ado yake basu labarin jinyar da nake fama da shi, Aunty Munah sai da tayi ta Bala'i ita sai ta shigar da Hafiz kotu, aka ce a kyale shi tunda na samu sauki yanzu ai da sauki sosai sai a tafi gaba. Haka yasa suka tsayar da shawarar ko zan koma makaranta, nima zaman gidan ya dame ni. Don haka na ce tow, na amince da shawararsu na koma jami'a a karo na biyu. Zanyi MBA wato Master Business Administration and specialization, a tsarin tallace-tallace, Ya Ado. Kullum tambayata yake. "Lulu zaki iya kuwa? Idan kin san har yanzu akwai abinda yake damunki a hakura da shi, kin ga saboda result ɗinki yayi kyau sun baki shekara biyu da wata shida, idan kina ganin akwai matsala a hakura." Yadda Ya Ado ya saka hope a kaina sai naji kamar idan nace mishi ban warke ba ban yi mishi adalci ba. Haka na ce zan iya amma har yau ina tsoron shiga Mutane, ya zanyi tow? Zan tabbata ina zaman gida ne, haka na daure sabon shekara na shiga cikin daliban da aka diba, na kwantar da hankalina, a yanayin acadamy calendar dinmu ba zan wuce shekara daya da wata tara zan gama. Haka yasa na nutswa, daga yanayin shigar da nake yasa an Makarantar suka fahimci na fito daga arewa ce, sannan yanayin fuskata, kuwa face mask nake sakawa saboda har yanzu fuskata kamar an buga donut, haka nayi ta rayuwa da tare da mai da hankali kamar ina yi da wani.
Yadda an ajin mu suke mamakin domin kusan nice karama amma yadda nake mukekiya sai ka dauka na shekara arba'in, a hankali na fara fuskantar body a shame, haka yasa na fara tsargu. Wani lokaci a tsorace nake shiga ajin. Sai ta min dariya ko tsokanata wani lokaci sai naji ana faɗin luxury, ko naji ana faɗin super Mama, haka yasa na fara jin wani irin yanayi ya fara shigata. Ban san me yasa nake jin wani irin damuwa ba, duk yadda naso na kauda kai amma na kasa sai tsoron da nake binnewa ya fara tasowa. Haka muka yi huta First semester din mu,
Haka muka yi hutun sati sati biyu da kwana hudu, zai kama Monday mai kamawa.