Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 17

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 17

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 17: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 17. *** Yau ya kasance Lahad, ana gobe zamu koma makaranta. Ina ta ɗan hada kayan makaranta na…

4,270 words

*** Yau ya kasance Lahad, ana gobe zamu koma makaranta. Ina ta ɗan hada kayan makaranta na nutsu naji wayata tai kara, dauka nayi a hankali. Na saka a kunnena. "Ruɓaɓiyar tsutsa mara haihuwa!" Ji nayi gabana yayi mugun bugawa a ina Ya Hafiz ya samu numberta yadda yayi ta gaza min magana har sai da naji kaina ya fara sarawa, hawaye ya fara zuba min kamar zan mutu kuma ya rantse min idan na sake na kashe wayata abinda zai min sai na rasa inda zan cusa kaina. Haka ya gama cin mutuncina sannan ya gaya min ko mutuwa nayi a gidansa za a min sutura, kafin ya kashe wayar, wurgi nayi da wayar yadda ya tsorata ni na ji wani irin tsoro ya kama ni. Dakyar nayi barci cike da tsoro wanda ya haifar min da mugun mafarki da rashin hankali.

Daidai buguwar agogon bangon dakin wanda ya ja burki da wani "ki...ki" cikin barci nake amma sai da naji gabana yayi mugun faduwa, bude idanu nayi ina kallon hasken waje tare da bishiyar da take kad'awa, hadari ne ya gangamo amma sai naji kome ya tsaya min, barcin ma na nime shi na rasa, Innalillahi wainnalihir rajoun, yau ya xan yi ni da ya dace na farko tun 4am. Da sauri na sauka a gadon na shiga ban daki nayi wanka da brush, sannan na haɗa da alwala, na fito ina jin kamar zuciyata zata fado, saboda tashin hankalin. Ina shafa mai na saka kayana, sannan na gabatar da sallah asuba, lokacin ruwa ake tsugawa kamar da bakin ƙwarya. Ji nayi kome na kaina ya sake kuncewa wai ma yau ba Monday ba ne koda yake abinda ya faru jiya ne ya d'aga min hankali Ya Hafiz me yake nufi da Ni ne,? na dauki jakata na rataya zuciyata tana wani irin bugawa,, sannan na fito parlourn na samu Ya Ado wanda shima cikin shirinsa na zuwa aiki. "Ina kwana Ya Ado?" "Lafiya lau Lulu kin tashi lafiya!" Gyada kai nayi na nufi kitchen inda Aunty Zakiyah take aiki na ce mata. "Good Morning Aunty Doctor!" "Morning My love, kin tashi lafiya" "Alhamdulillahi!" Ta mika min abincina. Tsayawa nayi ina kallon abincin, ina son na yi mata magana amma kuma ban san yadda zance ba. "My lovely ya dai?" "Wai dama abincin!" "Idan ba zaki koshi ba kawo a kara meye amfanin niman da muke?" Sai naji hawaye yana shirin zubo min, na kalleta a hankali na ce mata. "Na gode!" "Kada ki yi min godiya kuma ki dauke hawayenki domin Barista sai ya kusan cinye nama na danye!" Murmushi nayi da ya kara fitar da kumatuna waje."na gode!" "Sai ki yi!" Ta fada tana barin kitchen din, kasa fitowa nayi na zauna a saman kujera tamu ta hausa yar tsugunne, na shiga tura abincin. A hankali nake turawa bakiɗaya sai naji taste din abincin ya fita min a kai. A yayinda ƙwaƙwalwata da zuciyata suka hasaso min wani lokaci can irin wannan zaman nayi ina cikin abincin. Hawaye ne ya shiga zubo min ban san me yasa a duk lokacin da zan tuna wani bangare na rayuwata nake jin ciwo da zafi ba, kuka ne ya kwace min,.na ajiye abincin ina mai toshe bakina, na nufi pampo ina shan ruwa. Kalaman da aka fada a can baya yau jin shi nake kamar yanzu ake fada min. *Rubabbiyayyar tsutsa mara amfani, ke ba haihuwa ba sai kayan tsoka kamar tsutsa. Aikin kenan ga baki ga ci darling kama take da irin tsutsan da suke cikin kashi!* Amai ne ya zo min sakamakon kwarewa da nayi da ruwa, nayi ta tari wanda yayi sanadin shigowarsu dakin. "Lubnah lafiya?" Kasancewar idanuna yayi jajjur sai kukan da nayi ya tafi a kan kwarewa nayi. "Sannu kin kware ko? Kin ma ci abincin kuwa?" Gyada kai nayi nace mata. "Na ci!" "Tow muje parlourn ina ga haka zamu tafi fa!" "Abban Naylah bata ci abincin ba wallahi! Bari na mata park dinsa a cikin lunching box ta tafi da shi." Kallona yayi yaga ina sunkuyar da kai tare da kare fuskana, kaina a kasa ina sunsukuyarwa. Hannunsa ya kai zai tab'a ni, nayi maza na kare kaina daga shi har Aunty Zakiyah suka zuba min idanu. "Ba dukanki zai yi ba!" Ya fada tana kallona, shi da yake namiji ya kasa jurewa fita yayi yana zaga parlourn. Hannunta itama ta kai na koma jikin bangon kitchen din na makale. "Ba dukanki zamu yi, Lubnah me yasa kike dawo da abinda ya wuce?" Wurga-wurga idanuna na fara kamar wacce nayi karya ko sata na ce mata. "Ba haka ba ne,.na zata zai dake ni ne don ban ci abincin ba." "Lubnah wani yana threating dinki a makarants ne?" "A'a Aunty don Allah kada ki yi da karfi ya dauka ko wani abu ake min." Na fada ina kallonta tare da rike hannunta alamar roko! "Na ji amma me yasa?" "Ba kome!" Sai ta yi ta kallona da dukkanin zuciyarta take tausayi na. "Kina da kyau!" Ta fada shafa kumatuna nayi da suka kasance kamar donout ya sha bugu. Sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa, don nasan hala itama zolayata take. "Ina jiranku fa!" Ina ga bai rufe baki ba na rigata fitowa waje, kallona yayi ya ce min. "Idan kin gama muje. Gyada kai nayi tare da ɗaukar jakata, na amshi lunching box din na fito ya bude min mota na shiga. Ina kallon kayan wasan Yaran da ruwa yake sauka akansu. Haka muka bar Estate din, ya kunna karatun Alqur'ani a muryan Sheikh Afif, muna tafiya yana bin karatun. Nima a hankali nake bi, suratul lukman.... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 25 "Akwai wani abu ne?" Ya Ado ya tambaye ni, girgiza kai nayi ina danne damuwar da take fuskata. Tuki yake har ya iso makarantarmu, sannan ya juya bayan motar ya dauko lema guda biyu ya mika min daya shi kuma ya dauki daya muka fito tare, har cikin makarantar ya raka ni wurin department dinmu, daga nan ya wuce office din HOD, ban san me ya faru ba, sai dai bayan tafiyarshi, HOD dinmu ya shigo yayi magana sosai sannan ya kara da cewa. "Cin mutunci ko cin zarafi abu ne da ba a yarda da shi, idan kana ganin zaka yi tow kayi a wajen makarantar nan, daya daga cikin manyan lauyoyin jahar nan yayi dokaciya akan kanwarsa, idan ka sake ko kika sake wani abu ya faru na cin zarafi ku sani abin yana da doka a kundin tsarin mulkin kasar nan, kuma za a hukuntaka daidai da laifinka ko a yanke maka hukuncin zaman gidan kaso!" Jin hakan na sha jinin jikina, tabbas Ya ado ne, wannan dokaciyar sai ta sama min yanci duk da naki yarda na saba da kowa domin gani nake zasu cutar da ni, s gefe guda barazanarshi ya kara d'aga min hankali, ko barci nake ya kira ni ban isa d'agawa ba, Ya Hafiz ya hana ni sakat, saboda tsananin tashin hankali sai na fara jin kamar anya na cancanci farin ciki? Domin ya Hafiz bai da burin ganin nayi rayuwa cikin sallama.

Wata rana mun fito sallah wurin alola ya kira ni, yadda na dauka na kasa magana dama kuma ba maganar nake ba, haka na ajiye wayar a wurin sanadin da aka sace wayar, koda na tafi masallaci nayi sallah na dawo na duba ban ga wayar ba, a hankali na koma aji, koda na koma gida da kaina, Ya Ado ya kira Aunty Zakiyah ta gaya mishi gani nan wayata ce ta fadi ne, da zai dawo sai ya zo min da sabon. Akan washi gari zai kai ni a yi min welcome back, kai tsaye na ce mishi. "A'a bana so, ka barshi kawai idan aka tashi zan dawo da kaina." Na faɗa mishi. "Tow idan ana son magana da ke fa?" Shiru nayi ban kara magana ba, haka ya kyale ni tunda raina baya son wayar, kuma Alhamdulillahi kin wayar ya kawo min kwanciyar hankali.

Don nasan Hafiz yana can yana niman wayata. Bai samu ba, ***

Yau asabar babu aiki, Hakazalika kowa yana hutun karshen mako. Hajiya Daddah tana dakinta tana tattara Alqur'ani dinta mai falle falle. Badr ta shigo dakin. Zama tayi tana kallon Daddah da tunda ta shigo bata d'ago kai ta kalle ta ba, shiru Badr tayi tana mamakin kakarsu a saninsu Yaran mace ake so da kauna, musamman yadda Mamanta take kula da Daddah, duk ana yin haka ne don a samu kyakkyawar alaka mai karfi, amma Daddah ko kallo basu ishe ta ba, a hankali ta ce mata. "Ina kwana Daddah!" Yadda kasan da dutse take magana Daddah bata d'ago kai ta mata magana, haka kuma bata amsa mata ba. Hannu ta kai tsabar reni irin nata zata tab'a jakar Alqur'anin Daddah ta daka mata tsawa. "Kul na ka taba min kayana, bana son reni da rashin kunya irin naka ni ba abokin wasanka ba ne." A hankali ta janye hannunta. "Amma Daddah tun dazun nazo." "Assalamualaikum." Mimih ta rangad'a sallama da muryanta mai sanyi, "Amin waalaikumunsalam." "Daddah ina kwana?" "Lafiya lau, takwara ka tashi lafiya?" "Lafiya lau Daddah, cika Badr tayi tana kallon yadda Daddah take amsawa Mimi. " Daddah jiya na turawa Hamma Turaki sakonki." Bata wani damu ba, don tasan waye Turaki tunda kusan saboda ita ya ki zuwa kasar ya yi fushi sosai. ,yadda bata amsa mata ba ta cigaba da cewa. "Ya bude yace yana kewarki! " Anan ne ta ce mata, "Takwara shi karya bai da kyau, ka daina karya Turaki bata amsa wayar kowa daga Ubaid da Auta bayan nan sai kiran Alhaji. " Tayi haka ne don yadda Badr take ta cika tana batsewa, gyaran murya Alhaji ELYakub yayi yana rike da sandar shi ya ce mata. " Fadime ga turaki akan waya!" Ba tare da ta ji nauyi ba, ta mike da sauri ta isa zuwa gare shi, ta amshi wayar tana faɗin. " Alhamdulillahi Turaki kina lafiya? " Daga can ya ce mata. " Hmm! " " Turaki yaushe zaki dawo gida, ko dai na mutu zaki dawo?" Kome ya gaya mata ta sake murmushi tana faɗin. " Tow Allah ya baki hakuri, tunda bakya son dawowa ki cigaba da zamanki har Allah ya baki damar dawowa." Kusan ita ce take mishi hiran domin bata yi shiru ba sai magana take tana bashi labari, yadda zaka fahimci how she miss him, wani irin kewarshi take daga karshe da aka gama wayar sai da ta fashe da kuka, fita tayi ta kai mishi wayar Badr ta watsawa Mimih harara ta ce mata. "Munafuka waye ya gaya miki bamu san cewa baya kiran kowa kuma ba ya daukar kiran kowa na gidan nan sai mutane uku, ki bar wawantar da kanki. Mun san kome da kike wannan iyayin kin manta idan da kunya ai babu aure a tsakaninku?" Murmushi tayi Mimih tayi na wani lokaci kafin ta ce mata. "Eh kin san ni kawai ana iya kallona ne, amma wani abu ai a bude yaƙe muna raye cikin haske amma a inuwarmu akwai duhu me matukar hatsari." Daga haka ta wuce ta barta ita ɗaya a dakin Daddah, ranta yayi masifar b'aci, haka ta gama cika ta batse.

Itama barin dakin Daddah tayi tana jin wani daci daci a ranta, a haka suna son juna amma a zahirin gaskiya tsanar juna suke akan Turaki. Tana fita dama da motarta ta zo, shiga tayi ta fisge ta da gudu. Tana ji kamar zata tashi sama, haka ta wuce gidansu tana isa ko parking Mai kyau bata yi ba, ta bar motar a bude ta shiga cikin gidan da gudu, Hajiya Khaulatu da Alhaji Abbas suna lissafi ta shigo a guje. "QueenB ya dai?" Da gudu ta haura sama, tana kuka. Hankalin uwar ya tashi ta bita sama, ta samu tana ta razga kuka. "Me aka miki?" "Daddah ce ta ki kula ni, amma Mimih tana zuwa ta kulata." "Ba na hana ki zuwa gidan Daddah ba?" "But Mom taya xan yi ina son Hamma Turaki." "Bana ce ki bar kome a hannuna ba." Nan ta zauna tayi ta mata fada da cewa ta nisanta kanta da Daddah ita zata mata fight samun Turaki, amma ita bata isa ba. Haka ta gama Uban yana bakin kofar yana kallonsu cikin murmushi ya ce musu.. "indai turaki ne zan yi wani abu guda daya da zai saka kowa ya amince." "Ko?" "Eh kai, ranar Litinin zamu yi azumi kamar yadda Baffa yake yi. Ba zan manta Harisu ya ce idan yana raye zamu hada auratayya a tsakanin Yaranmu. Kuma akan idanun Baffa aka yi Allah ya jikan Harisu. " Ya fada yana kallon yarshi, domin yanzu ya fahimci duk abinda zai faru, Yayanshi suna sama da kome, shi yasa yake ta kokuwar bawa Khamis MD na kamfanin domin a karba a hannun Jasminah tunda ba wani abu take tsinanawa a kamfanin. Haka suka gama kitsa mata kome.

------- Bakiɗaya wancan satin nayi shi a zirga-zirga, amma yau da muke weekend. Ya Ado ya hana ni barci. Wai sai mu shirya mu tafi beach. A kasale na fito na isa parlourn ina sanye da riga da skirt English wear, duk da na ragu sosai amma yanayin fuskata idan ka kalla zaka ɗauka fulawa ce ta ji yis. Haka muka fito bakiɗaya muka shiga motar, ina baya da su Adil. Sai hira suke min ina amsawa, koda muka isa bakin ruwan yaran wasa suke Adil ya hau doki, mai sunan Mama tana wasa da ruwa idan ya zo da gudu ta dawo wurinmu idan ya tafi ta bishi da gudu, sai dariya muke mata, Allah sarki Princes tsoro ya hanata zuwa inda muke sai tsoro take tana cewa ruwa zai dauke ta, wani irin nishadi da nutsuwa ya shige ni. Wayar Aunty Zakiyah Mama ta kira na ɗauka, da yake wayar tana kusa da ni. "Mama bata kusa ne!" Da yake ta saka Mamanmu, mamanta kuwa ta saka Maman Dass. "Ina wayarki nake kira kullum baya shiga?" "Hmm ya fadi ne, kuma nace bana son wani." "Me yasa tow?" "Ya zan yi Mama Ya Hafiz ya samu numbeta sai d'aga min hankali yake Mama kamar zan mutu idan ban dauki wayarsa ba, idan na dauka kuma na ji gara na mutu na huta, shi yasa da wayar ya faɗi naji na samu sukuni." "Wato Yaron nan don kutumar ubansa bai kyale ki ba? Waye ya bashi number ki? " " Ina zan sani Mama!" Haka muka gama wayar sannan na mikawa Aunty Zakiyah da take jin mu sai kwafa take, tana amsa suka daura tsinewa Ya Hafiz, sai naji wani irin yadda suka tsane shi. Wurin karfe biyar muka bar Beach zuwa gida, daga nan muka baje domin abinci ma oda Ya ado yayi mana. Daren ranar bayan yara sun yi barci Ya Ado ya tsare ni da fada kamar zai dake, bayan ya gama ya kira Baban Jama'are, ya ce ya shiga tsakanina da Ya Hafiz ya daina shiga harkokina, sai dai maganar da Baban Jama'are ya fada ya saka Ya Ado harzuka, wai ai shi aure rai ne da shi idan akwai yiwuwar kara zama sai Allah ya nufa. Wannan abin ya daki ya Ado, tun daga lokacin na ji na shiga tashin hankali mara misaltuwa domin ji nake kamar zan mutu, kusan sai da na samu tsaiko s karatuna, ai kuwa Ya Ado ya zo Bauchi na tsawon kwanaki uku, zan iya cewa koda ya dawo bai ce mana kome ba, amma na ga kwanciyar hankali a tare da shi. Ya Hafiz bai san waye yake rigima da shi ba, bai kuma fahimci yadda ake rigima ba, sai dai wannan karon daga shi har yan gidansu sai da suka yi danasanin shiga harkata a gaban jama'a Hajiyarsu take cewa. "Idan har kai dan sunnah ne ba shege ba, na maka iyaka da Lubabatu idan kuwa na ji ko a mafarki ka sake shiga Rayuwarta sai na maka baki ka lalace." Shima Abba ya ce ya zare ni cikin Yaranshi kada na tab'a kiran shi a matsayin Mahaifi, idan kuwa na sake na zo kan gawarshi sai Allah ya tsayar da shi yayi mana hisabi. Babu wnada ya gaya min sai Aunty Innah. Mama kuwa ta yi tsalle ta ce ai dama sai da ya mutu a haka amma har Abada an rabu kenan.

A bangaren Ya Hafiz, abinda yake damunsa gani yake duk abinda yake da samun da yake yayi baya, duk da yadda yake gina Karimah da kanshi amma fa baya ganin haske, duk yadda yaso yayi gaba abun ya ci tura. Haka Hajiya Asiya ta dauke shi zuwa wurin Malaminta, ya zana ya goge, ya kuma buga kasa sannan ya ce mishi. "Yarinyar nan itace daukakarka, ita ce arzikinka, ita ce kome naka. Amma ba zata tab'a dawowa gare ka ba matukar Yayunta da Mahaifiyarsu suna tare da ita. Ka raba su ko ta halin k'ak'a, amma bari na gaya maka daga ita har danginta babu kofar da wani aljani ko sihiri yayi aiki akansu, gara Ubansu zaka iya juya shi don yana tare da kai amma Yarinyar da kafin ta bar Bauchi ne zamu iya mata wani aikin amma yanzu da take can wata duniya ko anyi ba zai same ta ba domin ba ƙaramin kasada ba ce kowa yana tsaye a kanta har matar ubanta, kai babu yan ubanci ko kishi da zai wargaza iyayen balle Ya'yan. "Hajiya Asiya ta ce mishi. " Malam babu wani hanya da zamu zaunar da ita har abada? " Sake zane yayi ya jinjina kai ya kara ya jinjina kai, yana karawa ya buga kasa ya ce musu. " Kai ina rayuwarta da ƙaddaranta yana can sai dai ya san yadda zai yi ya koma can amma akwai duhun da kai ka kirkiro da kanka kuma zai hadiye ka da shi Ubanta, abu daya xan baka shine ka kusanci inda take duk lokacin da kuka hadu ta yi amfani da wannan turaren, ta haka zaka kara rabata da nutsuwarta. Amma kada ka sake wani ya shiga tsakaninku.......... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 26 "Ga wannan zoben ka saka a hannunka, akwai lokacin da zakai ka gare ta. A ranar ka hadu da ita kada ka sake wani ya shiga cikin lamarin ka daidaici lokaci domin sa'arka zata fara idan har bukatar ya biya zoben zata haske idan kuma ka bari tayi baki bukatar ta lalace. Idan kuka hadu ba zata tab'a bijire maka ba, duk abinda kake so da ita zata maka, koda kuwa cewa kayi ya kashe kanta ko wani nata ne kuwa. " Jinjina kai yayi yana kallon Malam irin kallon rashin yarda nan, Malamin ya janyo wata kwanon sha ya ce mishi. " Nasan baka yarda ba. Amma bude wannan abin zaka yarda da ni, ba yau nake maka aiki ba hatta rashin fadar da ta kasa yi mune muke danne bakinta, mun yi haka ne don ka dangwali arziki son ranka. " Hannunsa yana rawa ya bude kwanon, sai ga Lulu zaune akan abin sallah. Ya cigaba da cewa. "Ka rufe!" Ba musu ya rufe, ya kuma ce mishi. "Bude!" Mama ce take zuba abinci a takeaway ana fita da shi sadaka. "Kai din banza kasan har rago aka yanka domin kawai ka nisanci yarta, ita fa a tsaye take ko ta mutu ko tayi rai ita Yarta kawai take son tayi farin ciki." "Malam yanzu me ake so?" Kallonshi Malamin yayi yana shafa gemunsa cikin son abin duniya ya ce mishi. "Mahaifyarka ta san abinda take biya, ni bana yanke kudi amma ana bani kudi me nauyi ne, sannan babban abinda yake lalata min aikina wasi-wasi."

Jin haka yasa Hafiz nutsuwa domin yana jin haka a ransa, haka suka bada kusan dubu hamsin, sannan suka fito daga gidan Hajiya Asiyah tana gaya mishi yadda zai yi, haka dai suka bar unguwar suka wuce gida, bai kwana ba ya dawo Bauchi, bai shigo ba sai karfe tara na dare, kin isa gidansa yayi ya wuce bayan gari a can ya kwana yana sheke ayarsa, washi gari ya isa gida yana muzurai, sai dai ganin wani bako a gidan ya bashi mamaki, sai yayi kamar bai damu ba, bayan ya huta bakon ya tafi sai ga Karimah, ta tsaya mishi a tsaye. "Waye wancan mutumin?" "Ai dan uwana ne?" "Kamar ya dan uwanki ne?" Ganin zai bata mata lokaci ta juya ta bar dakin, shi kuwa zuciya ta kwashe shi ya bita dakin ya ga gadon a wargaje. Yaransa ma gasu nan suna ta barci har lokacin basu farka ba, ga bra dinta da pant dinta a kasa, ba kawai sai Malam Hafiz ya rufe ta da mugun duka ba, kamar dai kashe ta. Dakyar ta kwace ta fita kamar mahaukaciya haka ta bar gidan, ya kama Yaran ya musu wanka. Ya kira Hajiya ya gaya mata, ta ce maza ya sake ta. Ya shirya ya tafi gembu ya aure yar dan uwanta, ya ce mata tayi hakuri zai kira Baban ya gaya mishi yadda suka yi, ai kuwa haka aka yi ya kira shi ya gaya masa, karya da gaskiya Baban Bauchi ya tausaya masa tare da cewa yayi hakuri kada ya sake ta,ya zo maza.

Haka ya tattara yaran ya wuce dutsen tanshi, ya samu Yadiko da mai aikinsu suna ta aiki, yadda ya shigo gidan hankali a tashe ga yaran a hargitse, yadda ya zauna gaban Baban Bauchi yana rusa kuka yaran na taya tashi, duk sai Baban Bauchi yaji wani abu na damunshi don haka ya ce mishi. "Ka nimo auren ko yar waye, in sha Allah zan tsaya maka ita kuma babu amfanin zama da mace irinta, abin tausayi Allah ya jarabce ka da rashin mata na gari." Haka yayi ta rarrashinsa tare da cewa ya bar Yaran a gidan Yadiko ta kula da su, ai daga waje ta ce mishi. "Gara tun wuri ku nima musu wurin zama amma ni ba zan yi renon yarana da jikokina na kara da na shi, dama ace Yaran Lubnah ce zan karba." Kiri-kiri ta ce ba zata amsa ba. Haka ya batawa Abba rai ya kira Munah don ya lura sun fi jin maganar Yaransu akan maganarshi. Haka yasa shi gayawa Munah, kiri-kiri ta gaya mishi ai suna tare da uwarsu abin sai ya fusata Abba. Dakyar Yadiko ta rike Yaran zuwa washi gari ya wuce da su Jamaare, daga can ya wuce Gembu. Kwanaki biyar yayi ya dawo, sannan ya gayawa Abba, aka saka karshen wata za a tafi gembu a nima masa auren.

*** Lubnah

Duk ranar Lahadi ina da dabi'ar wanki da guga, duk da cewa kuwa ana mana wankin ne. Haka na hada kayana na goge su gugar ma kaiwa ake. Monday ya kama Yau da wuri na fita domin muna da test, ina shiga makarantar. Ban san waye shi ba ni dai naga yana ta bina a mota har na shiga department dinmu, wurin karfe daya muka fito. Masallaci muka wuce nayi alwala na gabatar da sallah, sannan na tafi cafeteria, na sayi ruwa na wuce hanyar Library. "Excuse me?" Aka fada ta gefena, juyawa nayi na kalle shi, gabana yana faduwa. "Sannu ko!" Ya kara ce min. Ni dai ban amsa mishi ba, da za a lura da ni ba karamin rawa jikina yake ba, kallona yayi a tsanake ganin yadda nake raba idanu yasa shi ce min. "Sunana Rafiq" kafin ya cigaba da magana na ga wasu yan iskan abokai masu kama da yan kwaya, da wani irin sauri na bar wurin na bar wurin suka ta min dariya. Ya Ado ya zo daukana na nufi motarshi, sai ga gaye nan, ya tare ni ai kuwa Ya Ado ya fito yana ganinsa ya ce mishi. Barista Yar uwarka ce." Kallonsa ya Ado yayi da kyau. Ya ce min." Shiga mota ina zuwa!" Haka na wuce motar na zauna ya ce mishi. "Ita ce autarmu, don't mess wrong person, kada ka kuma shiga rayuwarta, kasan har yanzu akwai sauran case dinmu, idan karatu ka zaba tow idan kuma zamu koma kotu ne mai sauki ne. Domin na kare ta babu abinda ba zan aikata ba na gaya maka." Daga haka ya dawo motar muka bar makarantar. " Tun yaushe ya fara damunki?" " Yau!" Na bashi amsar a sanyayye, " baya jin magana iyayensa na kokari amma yana janyo musu magana, ina fatan bai miki wani abu ba." " Ni tsoro ya bani;" na fada ina kallon gefen hanya.

Murmushi yayi ya ce min. " Ba abinda zai miki, na gargade shi." " Allah yasa ya ji!" " Yana son gobensa zai matuƙar wahala bai kiyaye ba, yasan idan na kure mishi gudu sai ya rasa inda zai boya. Da haka muka isa gidan, ya bawa Aunty Zakiyah labarin abinda ya faru tayi ta dariya tana faɗin.."idan ubansa ya ji sai ya kusan mutuwa yadda yazo akan case ɗin kudirat ai kasan basu ji da dad'i a hannunka ba, gaskiya SAN kana vocalno." Wuce ta yayi yana faɗin. "Ke kuwa kina aman kankara!" Jin zasu sake layi na wuce sama da sauri Princess tana bani labarin Auntynsu me eyelashes, ko baka da niyyar dariya lamarin Auntynsu nan sai ka dara, yadda Princess take takaicin Eyelashes din nan.

**** KUMO FAMILY Mansion . A harabar gidan da aka kawata shi da kayan bud'e baki, aka hadu duk da layya ta kusa amma a duk sati Alhaji ELYakub yana da dabi'ar azumi da mazan gidan, idan aka sha ruwa aka yi sallah za a zo kofar harabar Alhaji ELYakub a sha ruwa kafin lokacin isha yayi a kara zama tattauna akan abinda ya shafi family din na alkhairi da sharri, cigaba da koma baya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull