Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 18

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 18

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 18: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 18. Da sallama wani dogon matashi, hannunsa rike da wata yar yarinya kyakywa, ga gefe guda…

2,095 words

Da sallama wani dogon matashi, hannunsa rike da wata yar yarinya kyakywa, ga gefe guda Matarshi tana dauke da wata baby, da sallama suka zauna domin aka haduwa maza da mata ne, cikin girmamawa ya ce. "Alhaji Baffa Barka da shan ruwa ya ibada." "Alhamdulillahi Khamis ya aikin da can Kano?" "Lafiya lau."Ya fada yana shafa kai Alhaji ELYakub ya kalli matar da take dan takure tana gaida iyayensu, duk da itama kusan har cousin din Abbas ce, Baban Khamis din, amma rayuwar aurenta ba sauki. " Annah! " Juyawa tayi tana murmushi ta ce mishi. " Baffa ya jikin girma? " Murmushi yayi ya ce mata. " Alhamdulillahi ya can Kanon da fatan babu matsala ko? " " Eh ba matsalar kome!" " Masha Allah! " Ya furta haka suka sha ruwa ana kiran sallah isha mazan suka tafi masallaci matan suka kafa dandalin hira, har mazan suka dawo aka cigaba da hiran. Bayan hira yayi tsawo sai lokacin Uncle Auta da Ubaid suka iso da iyalansu. Su kan basu cikin estate din don sun ce ba zasu zauna ba sai ranar da Turaki ya dawo ta ce zai zauna a estate din zasu dawo idan ya ki kuwa dama unguwarsu daya Lekki gidansu ma na kusa da juna. Kuma irin hauka da hayaniyar da ake a KFM basu cikinsa basu sani ba sai sun zo ne a basu labari. Nan hira ya kara dinkewa bayan an yi gaishe gaishe, daga Ubaid da Auta babu wnada ya zo da iyalinsa domin sun fahimci yadda ake rena musu mata. Gyada zama Alhaji Abbas yayi karkace kai cikin iya makirci ya ce. "Baffa idan baka manta ba, akwai alƙawarin da Marigayi ya kulla a tsakaninmu." Gyara zaman glass dinsa Alhaji ELYakub yayi yana saurarensa. Ya cigaba da cewa., "marigayi ya ce idan har ni ko Jibirin dayanmu ya haifi y'a mace yana kamawa Turaki!" Murmushi Alhaji ELYakub yayi yana kallon Abbas, ya ce mishi. "Tabbas anyi baka wani zuwanmu Gombe ko? Sai dai a lokacin ba cewa yayi dole ayi auren ba idan Turaki yana ra'ayin yaran sai a kulla zumunci idan bai ra'ayi ai baa yi namiji auren dole."

" Mujitafa amma ai ya dace Turaki ya ajiye iyalin haka indai ba maganar da ake ta yaɗawa na cewa yana homo ba! " Inji Hajiya Khaulatu, lumshe idanu Alhaji ELYakub yayi da karfi, ya jima kafin ya bude kanshi a sunkuye.. cikin dattako ya ce musu. " Ba zan yiwa Bilal Turaki dole ba, idan ma ya ga dama ya rayu babu mace ba sabon abu bane, domin akwai bayin Allah da suka koma ga Allah babu abinda ya dame su da mace. " Haka suka yi shiru ya kalli Hajiya Khaulatu ya ce mata. " Kika ce ana zarginshi ko?" "A'a baffa!" Dakatar da ita yayi ya nuna mata hanya ta bar wurin ya kuma rantse ya baya bukatarta a wurin shan ruwansa. Karshe haka aka tashi abin bai yi dad'i ba, a hanya Uncle Auta da Ubaid suka kira shi, sai da aka yi kira biyar a na shida ya dauka. "What?" Wani Uban Ash'aria Ubaid ya watsa mishi, amma ba kula shi ba, sai da Ubaid yayi mishi mugun zagi da cin mutumci kafin ya ce mishi. "Ubana da yake gefenka yana godiya!" Bakin ciki yasa, Ubaid sake tsaki ya ce mishi. "Dan kutumar uba, shege dan daudu. Kuma auren dole za a maka idan baka zo naija ba." Nan ma din bai bashi amsa ba sai da yaji Ubaid ya sauke ajiyar zuciya ya ce mishi. "Ka gama?" Wani uban ashar ya danna mishi, Uncle Auta ya ce mishi. "Ubaid ya isa haka, Son ka dawo haka?!" "Tow Uncle!" Ya amsa mishi yana sauke numfashi, "shege waye ya sani ko iskanci kake da wannan ajiyar zuciyar!" Uncle Ubaid da dama can ya saba da wannan halin nasu. "Ya isa Son kyale shi haka yaushe zaka dawo Boy!?" Sai da yayi shiru kamar ba zai magana ba ya ce mishi. " In sha Allah soon! " Cikin takaici Ubaid ya ce mishi. " Soon da baturen da ya kirkiro sun ci kaniyarsu!" Katse wayar yayi dan ya gaji da hayaniyar Ubaid ya ishe shi...... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 27 "Wai kai kan yaushe zaku girma ne?" Cikin takaici Ubaid ya kauda kanshi yana huci, har suka iso unguwarsu, sai da ya ga tsaya Uncle Auta ya shiga gidansa sannan ya juya zuwa gidanshi da yake kusa da na Turaki, kallon yadda aka kunna haske gidan yake shi bai tab'a kwana ya wuni ba tare da yasan me yake faruwa a rayuwar gidan ba, don haka yana shiga cikin gidanshi, ya nufi cikin gidan. Matarshi da take ta zaman jiran shi. Mikewa tayi tana faɗin.. "Daddyn Nihla barka da dawowa?" "Yawwa Fahimah." Ya fada yana nufar dakinsa, haka ta bishi kamar ta sani ta ce mishi. "Key zaka ɗauka?" Bai juya ba ya gyad'a mata kai. "Dazun an kawo sako yana store." Juyawa yayi yana kallonta. "An kawo sako kika ce?" "Eh" ta fada tana matsa mishi a hanya, ta taka a hankali har dakin da aka ajiye sakon, daga rubutun da yake jikin ledar kwalin zuwa girman kwallin yasa shi juyawa ya fita, gidan ya shiga ya samu ko ina fesa. Gwanin ban sha'awa. Ciro wayarshi yayi ya saka a kunne. Yana kira da shi. Rejected din kiran aka yi, sannan ya turo mishi. "Sorry Man im busy!" Me Turaki yake haka da yake da muhimmanci sama da shi? Idanunsa ne cika cika da kwalla. *Ba kome nake bukata ba sai lokacinka nake bukata Please ka saurare ni dan uwanka* kusan minti talatin yana jiran sakon, amma babu alamar haka.

Sai da ya gama zamanshi har ya mike zai fita sako ya shigo mishi. *Captain Ubaidullahi am sorry, bani da lokaci ne! Zan kira ka gobe sai ka sakawa princess naji muryanta.* Rintsa idanunshi yayi yana tuno wani babban al'amari da ya shiga tsakaninsu lokacin da ya dace ya yarda da shi amma ya juya mishi baya, ya bada shaidar da bata dace ba akanshi, yasan ya rusa yarda da take tsakaninsu, amma ba yana nufin haka ya raba su bane asalima yayi haka ne don Turakin ba wai don kanshi ba. Amma tun daga lokacin ya lura da Turaki yana gudunsa. Wannan yafi kowa yi mishi ciwo a ce Amininka yana gudunka.

Haka ya nufi gida zuciyarsa ba dad'i, ya wuce dakinsa ya kwanta ko kayan jikinsa bai iya cirewa ba, haka ya kwanta ringigine yana kallon sama, yana ji kamar kome ya dawo da baya ya goge kuskuren da ya aikata. Amma ina kome ya tafi fiye da yadda ba zato, anyi amfani da amintarsu an lalata alakarsu. A hankali ya kwana rabi barci rabi nazarin tsakaninsu, kuma yasan threating dinsa aka yi har yayi magana idan ba haka ba, tow da ba zai tab'a bude bakinsa ba.

Karfe shida na safe ya wuce dakin motsa jiki, ya jima yana motsa jikinsa sannan ya dawo yayi wanka ya shirya ya samu Amirah tana abin karyawa tana juyawa ta kawo mishi parlourn ɗan rungume ta yayi yana sumbatar goshinta. "Morning beauty" "Morning my star!" "Ina Nihla?" "Tana barci haka ya cigaba da karyawa wayarsa ce tayi ƙara yana dubawa ya ga Introvert. " Assalamualaikum! " " Amin waalaikumunsalam! Barka da safiya." Daga can ya ce mishi. " Yawwa ina princess? Ina Mamana? Ina abar kauna?" Tashi yayi yana hadiye abin bakinsa ya ce mishi." Tana dakinsu bari na duba ta. Haurawa sama yayi da gudu ya same ta tana juyi, shafa kanta yayi ya ce mata. "Honey tashi da Appa!" Ya saka mata wayar a kunne, nan ya shiga mata waka ta fara dariya alamar tana nemansa a zahiri, yadda take raba idanu tana wangale yan hakoranta kwaya hudu zai tabbatar maka tayiwa Introvert din mugun sani, irin sanin da ko shi Ubaid da yake Mahaifinta bata mishi wannan sanin ba, yadda take dariya har da tashi ta zauna, zaka girmama shakuwar da yake tsakaninsu.

Sun jima sai da Uban ya cire wayar ya ce mishi.. "Malam zan tafi aiki? Ka kira Amirah ta bata wayar." Ya fada yana gyara daukar ta. Ya fito da ita yana faɗin.. "Amirah zo ki amshi yarinyar nan ta cika pamper dinta da kashi sai tsami yake." Ya dauki abinda zai ɗauka suka cigaba da wayar shi tunda ya raba wayar da yarinyar tuni ya ja bakinsa ya tsuke, bayan ko minti biyar ba a yi da raba shi da yarinyar ba, sai shine yake ta zuba a kofar gate ya hango Uncle Auta yana jiranshi, zuwa yayi ya dauke shi. Sannan ya kai shi inda yake aikinsa sannan ya ajiye shi kafin shi ya wuce KUMO properties nigeria agency. Yana shiga yayi parking, office din da yake na shi ya isa ya fara abinda ya kawo shi domin bayan nan yana da kasuwancin da suke yi tare da Mr Turaki. Shigowa aka yi tare da banko kofar, bai d'ago kai ba don yasan cikin marasa kunyar Jikokin Alhaji ELYakub Kumo ne. "Kai matsayici taya Turaki da baya kasar nan ya san me ke tafiya a kamfanin nan? Sannan maganar haraji!" "Khamis Mudansir ELYakub Kumo Please zaka iya fita daga office dina?" "Lallai ne ka samu wuri, daga kai har Mrs Thomas zaku yi bayani!" Y cigaba da ihu da fada da jidali, kamar zai daki Ubaid, shigowa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo yayi ya kifa mishi mari sai da ya zauna a kujerar da yake kallon na Ubaid, wannan abin bai saka Ubaid d'aga kai ya san suna wurin ba, "Dad!" Sake kifa mishi mari yayi yana faɗin.." Ka yi hauka ne? " Ya fada cikin zafin rai. Shigowa Alhaji ELYakub yayi yana kallon Ubaid da yake aikinsa kamar babu mutane a dakin ya ce. " Da fatan dai lafiya ko?" Murmushi yayi ya ce mishi." Alhamdulillahi Alhaji barka da safiya. " " Barka dai ya me ake tattarawa ne? " " Alhaji takardun tax din nan ne nake haɗawa, domin CEO ya ce a shigar da kome kafin karshen shekarar nan, "da kyau!" Inji Alhaji ELYakub, yana murmushi, "Mudansir ya ake ciki batun bayanin kenan?" "Ni da Abbas mun sakar musu da kuɗinsu na 2019-2020." Alhaji Mudansir ya fada yana kallon Ubaid yana son ta hango yadda zai dauki maganar, murmushi Ubaid din yayi ya ce mishi. "Sir kudi ya fita ranar biyar ga watan Mayun 2019 daga office dinka, amma bai shiga asusun ofishin haraji na jaha ba, 2020 May 10 ya fita amma bai shiga ba, ga shaidar da office din haraji suka turo haka yana nufin suna bin na tsawon shekaru biyu kafin aka daina tura musu yau muka 2023. Sannan na turawa Lauyar da Alhaji ya haɗa ni da shi, wannan tsakaninsu da ofishin haraji na jaha ce, na gama nawa a matsayina mai shiga da fice na kamfani, sai case na biyu, Bankin First ta turo kayanta har na Naira miliyan dari biyu amma ba a tura mata ba, shima ba ni na binciko ba CEO ya binciko kuma ya turo min da sakon. Gasu nan nayi printing ɗinsu." Ya hada tare da mika Mrs Thomas da take gefen ta bawa Khamis, wanda ya jike da gumi. Yadda suke wasa da dukiyar kamfanin kamar basu Allah a ransu, shi kuma CEO baya kamfanin amma kuma twinkle eyes dinsa suna spark a kamfanin fiye da wanda yake kwana gefen kamfanin.

Karba takardun Alhaji Mudansir yayi jikinsa yana rawa, bai taɓa tunanin kari da ragi da yake yi a office ɗinsa zai iya fita a takarda tar haka ba, dole ya dauki mataki akan kowani dan iska ya rasa wannan rashin wayon Khamis gashi nan dai kamar me wayo amma bakiɗaya daga Turaki har Ubaid suna iya kifar da shi, duk yadda yaso Abbas ya dauke idanunsa akan Khamis din amma a bayan fage sai sun nuna son zuciyarsu.

Cizon lips dinsa Alhaji Mudansir yake har Alhaji ELYakub ya fita daga office din Ubaid, kanshi kamar zai bindiga, ya juya ya kalli Ubaid. "Ka kula da kanka!" "Ka kula da Mimih domin ba san me gobe zai haifar ba, kasancewar ita ɗaya ce maka." Hadiye yawun bakinsa yayi yana kallon Ubaid , ko kiftawa bai yi ba, mamaki yadda ya iya mishi barazana da yarsa. A hankali ya fita daga office din, ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin sauki da nutsuwa a ransa. Daga nan ya tattara takardun ya kira Number Lauyar da Alhaji ELYakub ya haɗa su, ya gaya mishi inda zai kai mishi, koda ya kai mishi sama sama suka gaida juna sannan kowa ya kama gabansa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull