Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 19

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 19

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 19: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 19. *** Lubnah Yau tunda na dawo nake daki, abinci ma yau dakin aka kawo min, ina ci ina kallon…

4,490 words

*** Lubnah Yau tunda na dawo nake daki, abinci ma yau dakin aka kawo min, ina ci ina kallon handout, ina nazari har kusan karfe tara na dare. Ban fito ba wayar da Ya Ado ya saya min kwanan tayi haske kiranshi na dauka ina faɗin. "Ya Ado?" "Auta ina lafiya dai ban ganki ba ne?" "Bari na fito mu gaisa!" Ka tattara kome na sauko kasa, na samu suna ta hira zama nayi ina kallon Aunty Zakiyah. "SAN yarinyar nan bata tsoron Allah!" Murmushi yayi yana faɗin, "Auta da gaske ne kin shanya Doctor Ahmad?" Idanuna ne suka cika da kwalla, ina kallon kasa ya cigaba da cewa. "Tunda nace kin fara karatu hankalin Mama yake kanki tace tana son ki yi aure Hafiz sai ya rabu da ke?" Ni dai ban ce kome ba, har ya gama maganarshi, na ce mishi. "Zan koma na kwanta." Na mike zan tafi ya ce min.. "Ahmad mutumin kirki ne, ki yi nazari yasan matsalarki kuma zai tsaya miki!" Da gudu na haura sama, ina jin kuka yana zuwa min, ni tsoron maza nake ji bana son abinda zai hana ni dasu, haka yasa na ki kula Ahmad. Kwana nayi ina kuka domin har yau ban manta abinda Ya Hafiz ya min ba. Washi gari tun kafin ya fito na bar gidan, domin bana son Magana ya kuma hada ni da shi, a makaranta na karya shima naci ne gudun kada na wahalar da kaina. Wunin ranar har aka tashi bani da walwala, ina hanyar komawa gida Baby ta kirani. "Yan mata gani a gidanku!" A shake na amsa mata, sannan na ce. "Ina hanya!" Haka na isa gidan a hankali nake takawa, har gidan, motar Doctor Ahmad na hango a harabar gidan, ba don mun yi ido hudu da shi ba da na juya. Haka na daure na shiga na gaishe shi sannan na wuce cikin gidan, na samu Aunty Zakiyah tana gida. Gaishe ta nayi na wuce sama. Baby ta biyo ni. "Yan mata wai meye ya faru ne?" "Babu!" Na fada mata, murmushi tayi ta ce min. "Wancan hot guy din fa? Da me shi ko na ɗauka?" Da sauri na juya ina kallonta. Baby irin mutanen nan masu open mind bata iya boye what she want kome ta gani tana so baya bata wahala ta mallaka. D'aga gira daya tayi tana faɗin. "Ko dai naki ne?" "Yayi miki da gaske?" Na tambaye ta domin ina jin kamar zata raba ni da matsalata ce, idan har ta ce yayi mata tow ba makawa zan samu hanyar rabuwa da shi. "Idan kina son shi zan baku number wayarshi," na fada ina kallon yadda take murmushi, "wallahi yayi min!" "Ok ko bari na fito wanka sai na baki number shi." Na fada ina wucewa toilet, sai da nayi wanka nayi Alwala sannan ka fito na samu tana zaman jirana, abu take zuka na ce mata. "Yaushe zaki daina shan wannan abin ba?" mai da shi jakar mata tayi tana faɗin. "Ina kokarin bari in sha Allah." Ina son gaya mata gaskiya amma kuma san yadda zata dauki maganata ba, kada ya ga kamar don zan hadata da Doctor Ahmad ne, sai na ja bakina nayi shiru na kyale ta har nayi sallah, ina idarwa Adil da Mama suka kawo mana abinci, muka fara ci a hankali, ina lura da yadda bata son abinci, na ce mata. "Ki daina shan drugs, ki fuskanci rayuwa ki ci abinci domin wallahi zai iya haifar miki da wata matsala daga baya ayi ta kuka da juna." Murmushi tayi ta ce min. " In sha Allah zan bari! " Daga haka ta cigaba da tsakuran abincin tana wasa da shi, har muka gama Princess ta shigo ta ce min. " [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 28 "Aunty kizo Mama tana kiranki! " Nasan batun Doctor Ahmad ne, ji nayi gabana yana faduwa, kamar zan yi kuka haka na mike na shiga ban daki na wanke hannuna, sannan na saka mayafi akan riga da zanin jikina, na sauko kasa na same ta tana duba books din Yaran na makaranta. " Lulu kin manta da Doctor Ahmad ne a waje?" Shiru nayi ban bata amsa ba, can dai ta kara magana sannan na d'ago kai ina kallonta kafin na ce mata."to! " So nake na ce mata, ta sallame shi amma na kasa saboda yadda bakina yayi nauyi, hawaye ne ya cika min idanun. Komawa sama nayi na dauki Hijab na saka sannan na sauko kasa, na samu tana waya da Ya Ado, kusan tare muka sauko da Baby ta mata sallama zata tafi, muka hada hanya a waje na samu Doctor Ahmad zaune. Jan plastic chair nayi na zauna ina dan matsawa can nesa da shi, Baby ta tsaya a bayana tana gaishe shi, sannan ta min sallama ta fita a gidan. Har ta bar gidan yana bin ta da idanu. "Ki fita harkan yarinyar nan, bata dace da ke ba." Ni dai ban ce masa kome ba, yadda ya gama surutunsa haka na tashi muka yi sallama. Ban san ya suka kare ba, sai dai kwana biyu da zuwan shi ya kira ni a waya yana tambayata me yasa na bawa Baby numbersa, shiru nayi bani da ta cewa. Ganin naki magana yasa shi katse kiran, washi gari sai gashi ya zo, shiru duk muka yi yana kallon yadda nake wasa da yatsu hannuna na kasa magana tunda na gaishe shi ban kara magana ba. "Kin san yarinyar nan bata kyauta ba? Sannan ta gaya min cewa kece kika bata number ta? Akan me zata na kirana any how? Har matata sai da ta fahimci akwai wani abu a kasa." Sai a lokacin na d'ago kai ina kallonshi. Wato shima dai irin Ya Hafiz ne na shiga gidansa ya gana min azaba da Matarshi, to idan ba mai mata ba, waye zai aure Ni? Ni dai ba samun saurayi xan kara yi ba a karo na biyu, duk tsiya idan ban auri mai mace daya ba zan auri me mata uku na shiga ta huɗu. Wannan abin ya saka min wani irin tsoron shi Ahmad din kansa. Duk mutumin da bai da ikon kasan a gidansa har abada ba mijin aure ba ne. Don haka na tashi na bar shi a wurin haka ya kira Ya Ado ya gaya mishi, lokacin da Ya Ado ya dawo gida ina daki ya shigo dakin, jan stool yayi ya zauna yana kallon yadda nake takure wuri guda. "Lubnah me yasa ba zaki bawa Ahmad dama ba?" Yadda yayi magana yasa na d'ago ina kallonshi, idanuna cike da kwalla har ya gama magana ban ce mishi kome sai kukan da na fara ganin yadda nake kuka da gasken gaske yasa shi zuba min idanu cike da mamaki, har washi gari ban fito ba don bamu da class, ina daki a kwance gashi garin an tashi da ruwan sama, haka yasa nayi luff a dakina suka tafi aiki sannan na fito na karya na wanke kayan na koma na kwanta. Karfe uku na fito saboda hayaniyar Yaran na fito na tsaya suka shiga kafin motar islamiyya ya zo ya dauke su na koma na kwanta. Karfe biyar duk suna gidan ban kara lekowa waje ba, na cigaba da kwanciyata. Wurin karfe goma na dare sai gasu nan su biyu yaran sun kwanta ina kwance, kunan wutar dakin tasa nayi kamar ina barci, zama a bakin gadon Aunty Zakiyah tayi tana kallon yadda na sake jikina. "Ko tayi barci ne?" Inji Aunty Zakiyah, "idonta biyu!" Shima ya ja stool ya zauna yana kallon yadda nake kwance. "Tashi mun zo magana ne akan Ahmad!" Tashi zaune nayi ina kallon gefe guda. Tunda kuka fara kawon farillah da musta'abin halin Ahmad, kasancewar shi mutumin kirki ban san lokacin da na fara kuka me karfi ba, sai suka zuba min idanu. "Me aka miki to?" "Kawai ku mai da ni Bauchi na je can ko kashe ni ne gara su yi! " Shiru Ya Ado yayi yana kallon yadda nake kuka. " Me yasa tow? " " Tsoro suke bani tsoro yake bani, duk wanda zai zo gare ni tsoronshi nake, ku gane ni tsoron maza nake, wallahi cutar da ni zai yi don Allah idan kuna son farin cikina ku kyale ni!" Ganin yadda nake kuka abin dai yayi ta basu mamaki, har suka fara ganin kamar basu so kansu ba, don haka Ya Ado da kanshi ya rarrashe ni, na bar kuka suka hada min abinci na sha tea, sannan suka tafi na kwanta kusan raba dare nayi ina gayawa Allah kukana, tsoro nake ji shima Ahmad din akwai abinda ya gano yasa yake bina, ban san yadda Ya ado ya fahimta da shi ba, amma kuwa na ga ya daina turo min sako ko wani abu sai dai duk ranar juma'a yana turo min da sakon barka da juma'a wato ba zai tab'a give up ba. A bangaren Mama kuwa har zuwa tayi akan matsalar sai dai tana zuwa lagos, ganin yadda ta saka ni a gaba da maganar aure, ban ce mata kome na tafi makatanta na dawo, na same ra bata daina maganar auren nan ba, bata san yadda abin yake ba, ni dai ban san me ya faru ba, sai dai na bude idanuna na ganni a dogon kujeran parlourn, su Ya Ado suna ta min sannu, dakyar na tashi. Rike hannuna Aunty Zakiyah tayi zuwa dakina Yara na kwanta, ta kawo min magani da tea na sha, yana fada min nayi sallah na zo n kwanta tuni barci yayi gaba da Ni, sai karfe daya na dare na farka a lokacin na samu tana kan abin sallah, tashi nayi na shiga ban daki nayi alwala na zo na gabtar da sallah Magariba da Isha, ina idarwa na daura da nafilla. "Lubnah?" "Na'am!" Na kalle ta, yadda take kallona tausayi na take ji, haka yasa na matukar jin tausayin kaina. "Tsoro kike ji ko!" Hawaye ne ya zubo min, ashe ta sani? Ashe tasan ina jin tsoro; bude min hannu tayi na shiga ina wani irin kuka, "Ya isa haka ba zan kara miki maganar aure ba, ba xan kara cewa wani ya miki magana aure ba. Jiya naji kamar na rasa ki kenan, ban san ashe haka abin yake ba. Lubnah ko wani ne yace baya son abu ba zan mishi dole ba, balle ke da na yi miki laifi masu tarin yawa, ina jin idan baki yafe min ba Allah ba zai yafe min ba, " ni dai ina jikinta tare da jin wani dumi me dad'i, haka tayi ta rarrashina tana gaya min nayi hakuri da ƙaddarata haka ta zo min, satinta uku, ta koma Bauchi ta bar mu da kewarta. Haka na cigaba da rayuwata cikin yanci da walwala lokacin da na samu hutu kamar na je Bauchi, amma haka na hakura duk abinda zai hada ni da Hafiz ina kin sa, a zuwan Mama ne muka ji labarin ya kai sadaki da kayan aure a can garin Mamansa. Wai Abba ya sauya mishi gida, ni dai ban ce kala ba har suka gama hiransu. Karshe barci nayi a parlourn ban san lokacin da suka gama hiran aka tashe ni na je na kwanta ba. Bayan tafiyar Mama na sha hutu na koma school. Shekara daya da wasu watanni a lagos wnada yayi daidai da wata na bakwai da fara karatu, haka yasa na kara nutsuwa zuwa yanzu karatun shine mijina da duniyata, course mate dina tun suna kirana silver spoon saboda sun gano nice aka musu kashedi akai, suka yi ta min tsiya da tafiya tayi nisa sai suka watsar da makamansu suka kuma janyo ni muka zaka Family, duk yadda zaka so ka kebe da ni na shata layi ba ruwana da soyayya, tsoron maganar namiji nake, department dinmu har sun gano tsoron mazan da nake ji, wani irin tsoron maza da nake ji duk abinda za ayi ayi na karatu amma bayan nan kana fara wani abu, xan fita harkanka. Duk yadda kowa yaso yasan matsalata da maza ban tab'a magana ba, haka yasa suka kyale ni, na kuma kame kaina na saka a raina ba ruwana da duk wani dan balaja'u. Haka kuwa muka kasance har muka kusan gama karatunmu, a lokacin ina da shekaru biyu cib a jahar lagos. *** KUMO FAMILY MANSION. Kallon Hajiya Khaulatu Daadah tayi cikin wani irin takaici take kallon yarta da son zuciya ya gama rufe masu idanu. "Daddah ki bawa Alhaji hakuri wallahi Khamis ba zai kara ba, kuskuren fahimta aka samu!" Ta fada tana sunkuyar da kai kallonta Daddah tayi cike da mamaki da bakin ciki mara iyaka. "Yake yaronki ce tayi laifi kin zo na saka baki na bawa ita baffanki hakuri Khamis ba zata sake ba." Murmushi tayi irin na manya, sannan ta cigaba da cin mutuncin Hajiya Khaulatu. "Wato ita wancan Yaro Turaki da bata da kowa sai Allah, kika jifeta da shaidar zur, ita kuma Yaronki da take da Uwa da Uba ka zo kare shi saboda shi ne mai gata, ita wancan tana da waye? Bata da kowa sai Allah. Wai na tambaye ka Khaulatu me Yaron nan Aisha da yayunku suka muku da kuka tsane su haka? Ni a sanina basu muku kome ba idan har akwai abinda zaku yi bai wuce tsayawa da Anne Aisha yayi a Kamfanin Alhaji ba, amma kun tsane shi tare da ita yar uwarku." Yadda Daddah take shiga ba nan take fita ba, karshe haka suka yi shiru ta kori Hajiya Khaulatu daga cikin gidan. Wurin karfe uku na yamma Jasminah ta shigo cikin gidan, ta samu Uncle Auta da Hajiya Samirah. " Barka dai datti! " Yay gaida Alhaji ELYakub Kumo, sannan ta juya ga Hajiya Samirah ta ce mata.. "Aunty Barka dai ya kike? Yasu Munawara da Abid?" "Lafiya lau Jasminah, kin leka Hajiya Zeenatu?" Yatsina fuska tayi tana kallon Daddah, "Daddah ya kike ?" " Kaci gidanku! Da kazo ai baka gaishe ni ba sai yanzu zaka ce wai ya nake ba yadda nake ina shure-shure." "Allah ya baki hakuri!" Banza Daddah tayi mata, Alhaji ELYakub ya kalli Jasminah. "Ina jinki!" Gyara zama tayi ta ce mishi. "Gaskiya na gaji, tunda shi Turaki ba zai musu magana ba ya kamata a bani damar nayi magana tunda ina da hakkin akan kasona da yake cikin kamfanin!" Kallonta yayi yana murmushi ya ce mata. "Turaki yayi magana ki ce ya fito da sonkai? Ke kika ce Turaki yana nuna iko dayawa ko za a bada matsayin CEO baki amince a bashi ba, yanzu kuma ki dawo kina blaming ɗinsa shi da ba a kasar yake ba. " Yayi mata magana yana murmushi, bakiɗaya ta ji kamar ta nutse a wurin. " Ita Turaki ta ce ba zata dawo ba, da irin wannan masfar da kuke yi gara kada ta dawo a sakata ta rame. " Daddah ta fada tana hararansu. " Yanzu dai me Jasminah take bukata haka kawai Jasminah bata zuwa akan abinda tasan waye a kai ba?" Shigo da tiren abincin Alhaji ELYakub, tuwon alkama ce miyar kuka wanda yaji kayan kamshi da hadi na musamman. Ajiye tiren abincin Maid suka yi ta yi, har gaban Jasminah. " Ina jin Jasminah? " Alhaji ELYakub ya kara magana, yasan abinda ya kawo ta amma tunda ba zata yi magana ba shima shiru zai yi abinda ya fahimta shine ganin Samirah yasa tayi shiru taki magana, suna zaune a wurin har ya gama cin abincin, Uncle Auta ya shigo suka gaisa shine ma Ya kalli Samirah ya ce mata. " Ya dai na ganki anan? " " Yanzu zan tafi, amma Mujitafa me yasa Matarka da Matar Ubaid basu zo birthday din su Abid ba?" Ta fada tana wani hade rai ita nan an bata mata rai. " Saboda basu fito daga babban zuri'a masu arziki irin naku ba, su zo anayi ta musu kallon banza da basu isa ba! " Ya fada yana kallon Daddah da take gyada kai. " Baffa barka da warhaka, Ubaid ya mika sakon wasu bayanai ga Turaki sauran kuma da a ji da shi, gaskiya Khamis yayi laifi dayawa sai dai yana da kyau a dawo da shi, domin ko babu kome yana lura da shashin tallace-tallace. Amma na gayawa Turaki ya ce duk abinda aka gani shi dai na shi ya saka idanun ne kuma ya yayi bakin kokarinsa sauran na ku ne. " [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 29 "Murmushi Alhaji ELYakub yayi ya nuna Uncle Auta ya ce mishi. " Baka da kunya Mujitafa, wato sauran namu ne bayan kai ma kana da kaso a kamfanin! " Dariya Uncle Auta yayi ya ce mishi. " Ina ana babbakar giwa wa ke ta zomo, shi dai wancan magajin dubbanin nairori ya ji da kome ni a bar ni a dan aika! " Anya kuwa? Na fison ka taya shi riko tunda yaki kula maganar CEO shi baya kasan amma idanunsa yana kan kamfanin." "Cikakken shugaba kenan, baya tare damu amma idanunsa yana kan kome yasan shiga ya san fitar kuɗi!" Jinjina kai Alhaji ELYakub yayi tare da gamsuwa da maganar Uncle Auta, ya ce mishi. "Zenith bank sun kawo kayan wani dan kasuwa nayiwa Ubaid magana!" "Eh ya turo min dazun na kuma turawa Turakin amma bai ce kome ba!" "Alhamdulillahi mu jira mu ji me zai ce. Amma ba zaka mishi magana ya dawo gida ba kenan?" " In sha Allah zai dawo, Baffa hukuncin ya isa haka yau shekara kusan daya da rabi da hukunta Khamis, duk da an biya kudin harajin ya kamata a sassauta mishi, Addah Khaulatu sai sintiri take tsakanin gidana da gidan Ubaid, ta amshi number Turaki yaki daukar kiranta, na tura mishi apologize letter da suka rubuta bai ce kome ba." "Shi kenan Ubaid ya gaya min sannan itama Uwar Yaron tana ta bada hakuri, haka Abbas yana ta bada hakuri sai yadda Turaki ya ce ya cire hannunsa nake son ya hakura da kansa, tunda yace akwai mutanen da suke bayan Khamis shi kaɗai kudin yayi masa yawa, na rasa wnada ya karantar kimiyyar haɗa bama-bamai taya ya san kimiyyar shida da fitar kuɗi har haka? " "Baffa Turaki rabin rayuwarsa yayi ta cikin turawa da larabawa ne, yasan makircin kowa, don haka kada ka yi mamaki don ya ɗan me yake faruwa a kamfanin da kuma yadda yasan yadda za ahada nukiliya da yadda yasan mutane na kaunar kuɗi. " Cikin gamsuwa da bayanin Uncle Auta ya ce mishi. " Tabbas ya gaya min cewa kamar yadda nake son zuriarta ta zauna lafiya, ya ce Datti a cikin gidan akwai wnada zaman lafiya baya cikin tsarinsu, ya ce Datti ba wai ba zan dawo cikinku ba ne, kawai nafi son nesa da kune domin idan ina tare da ku, kullum sai na fito da sabon tsarin zaman lafiya, su ma kullum sai sun fito da tsarin tashin hankali." Inji Alhaji ELYakub ya fada yana dariya. "Baffa sai kace mishi ya cancanci a bashi piece ambassador! " Dariya suka yi sai a lokacin ya juya ga Jasminah ya ce mata. " Daughter ya Case dinku dai? " Komawa Hajiya Samirah tai ta zauna tana mai baza idanunta. " Uncle Auta a bar maganar! " Inji Jasminah tana me mikewa ta gyara zaman abayarta. " Da Abbana yana raye zai saurare ni ba tare da wani ya san me ya kawo ni ba, am so disappointed Datti ka san me ya kawo ni amma ka ki ka bani damar haka, Uncle Auta kasan bani da wata madafa amma ba kome! " Ta juya tare da ɗaukar jakarta tana share kwalla da yake zubo mata ba da wata mafita da ya wuce ta kira shi Turaki kaɗai ne last hope dinta, sai da ta shiga motarta sannan ya kira Numbersa hawaye na zuba mata, bata taɓa kawowa zai saurare ta ba ko zai dauki kiranta. Amma abin mamaki sai gashi ya dauka yana tambayar. " Da fatan lafiya? " Cikin shashekar kuka ta ce mishi." Kasan ciwon da nake ji na kowa ya juya min baya? Kasan yadda nake fama da ciwo na abinda yake damuwana? Kasan yadda nake ruined rayuwar aurena? Ko sau daya ka tab'a jin kukana? Ka tab'a tambayar meke damuna? Brother ka tafi ka bar ni alone baka damu da ni ba, ko don ba ciki daya muka fito ba? I lose Abba, by now I lose everything har career dina, my First child she be mole daga Brother Mijina, nayi magana Mom ta ce na kashe case ɗin, yayi min barazanar ko na saka ku a sake mishi kayansa ko ya sake ni ya kwace min Yarana." Ta cigaba da kuka a hankali, sannan ta hadiye kukan tana faɗin.. "ba kome haka Allah ya nufa, kowa yana son na shi amma ni nawa sun yi abonden dina, na rasa duk wani kwarin gwiwa. But koda gawata aka samu don't blame them just remember that na gaya maka yadda nake shan wahala na gode wannan shine death note dina!" Kashe wayar tayi ta kifa kanta a kan sitiyerin motar, tana jin wani irin kuka yana zuwa mata, wayarta tayi ƙara ta d'ago kai tana kallon kiran, dauka tayi domin ta tab'a yarda zai kara kiranta ba. " Littles Queen, are Kumo Family Queen, akan me ba za a kula ki ba? Ki bani nan da awa biyu ki tafi gidan Ubaid ki zauna kada ki damu Yaranki zasu zo gare ki, Abba baya raye amma ba yana nufin xan bar rayuwarki ta lalace ba ne, kece kawai kika rage min da muka yi sharing blood, taya xan bar ki? I glad kin kira ni for your own, you invited me akan personal life dinki, ki tafi gidan Ubaid ki kwanta kada ki yi drive zan saka Tajudeen ya zo ya kai ki jira yanzu kin ji" sai ra cigaba da kuka ta kasa magana irin kukan farin ciki ka samu wanda ya tsaya maka, yana jin ta bai kashe wayar ba ta ce mishi. "Allah ya jikan Mommy da Abba. Allah ya gabatarwa su Baffa, Brother I miss you, I miss something else!" Murmushi yayi ya ce mata. "Ba gani ba? Remember who you are, kada ki sake barin wani ya cutar dake, idan aka yi magana ki ce kina da Turaki akwai wani marayan zaki da yake gurnani saboda ke!" "Na gode sosai na gode." "Oya share hawayenki bari na kira Tajudeen." Kashe wayar tayi bayan minti goma sai ga Tajudeen, ya gaishe sannan ta fita gaban motar ta koma baya, anan ta zauna har suka isa gidan Ubaid, a lokacin Amirah tana aiki a kitchen, koda ta shiga a parlour ta zauna har Amirah ta fito. "Jasmin!" Murmushi tayi tana sunkuyar da idanunta da suka yi jajjir har daman idanunka yayi ja. "Brother Turaki ya ce na zo nan!" "Ok muje na kai ki daki!" Ta mike Amiraah ta kaita daki, ta zauna a bakin gadon. Kanta a sunkuye. Haka Amirah tayi ta hidima da ita tana cikin masu yiwa Amirah kallon bata kai ba. Amma yau don Allah ya d'aga darajar Amirah gashi nan tana hidima da ita. After 3 hours. Bakiɗaya family kumo kowa ya shiga hankalinsa, idan ka cire Hajiya Zeenatu wacce take bala'i da masifa. "Wato ni Jasminah ni zaki wulakanta? Har zaki yi involved din Turaki cikin wannan lamari? Ni na haife ki ba shi ba, wallahi idan baki zo ba nan da awa daya sai ka tsine miki." Ta fada tana ihu. Ba karamin tashin hankali ta shiga ba, idan har Jasminah ta lalata aurenta tow wannan damar da zata rasa abinda take hari akan Mimih. Wato wani abu da ya faru, shine yana gama wayar da Jasminah, ya kira Uncle Auta da Ubaid ya ce ya basu awa daya kacal su kama Fahad mijin Jasminah a rufe shi kada a bada belinsa, duk wanda yake son karban belinsa a nimo Jasminah ita ce ke da hurimin bada belinsa, sannan aje gidansu a dauko mata Yaranta ko da bala'i. Akwai abinda only money and power kaɗai yake iya aiki, kuma ya nuna musu iyakarsu. Sannan duk wani abin da ya shafi Family Noma family sai da Turaki ya dakatar dasu kuma yayi magana da karfi da kudi yasa aka kama Sudais Kanin mijinta aka rufe shi aka rasa inda aka kai shi, sannan ya kashe wayarshi bayan ta tura mata da sakon. *Kada ki kashe wayarki ki saka a ranki akwai babban challenge da zaki fuskanta kada emotion ya sa ki mika wuyarki, kin ji ko baki ji ba. Ba zan kashe miki aure ba domin nasan kina son Mijinki, nasan kina buƙatarshi and ki holding wannan yanayin yadda zaki kwaci kanki!* Bai gaya mata wanda zasu kalubance ta ba, amma yadda Mamanta ta tsaya sai ta fito daga inda take, amma bata fito ba. Ganin da gaske taki magana kuma taki bayyana kanta. Sai gashi hankalin kowa ya tashi. Shi kanshi Ubaid bai san tana gidansa ba, sai da ya koma domin tunda ta cewa Amirah Brother Turaki ya turo ta bata gaya Mijinta ba, ganin Jasminah a gidan yasa shi duba e-mail dinsa. *Yaran a kai su wurin Hajiya Zeenatu Queen kuma ta zauna a wurinka.* Yana ganin haka, ya fahimci sakon shi. Washi gari ya tafi can KUMO FAMILY MANSION, ya ji yadda ake ciki da maganar Jasminah, haka aka yi ta nimanta. Wunin ranar iyayen Mijin Jasminah suka zo, Alhaji ELYakub Kumo ya ce su je gobe su dawo.

Wasa wasa sai da suka yi zuwa uku a cikin kwanaki biyar, kafin Turaki ya bawa Uncle Auta labarin inda Jasminah take a je a dauko ta, aka kaita gida yanzu su babban damuwarsu a sake Sudais ita kuwa kamar yadda Uncle Auta da Ubaid sun ce ta ce a kai su kotu ta haka ne zai saka su shiga hankalinsu, yadda take kome da maganar da take yasa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo ya Fahimci bakiɗayansu tsarin turaki ne, hatta shima Alhaji ELYakub Kumo abinda yake yi tsarin turaki ne, cizon lips dinsa yayi yana kallonsu domin bai taɓa yarda Turaki zai iya daure shi ba, Alhaji Nasiru Noma babban abokinsa ne kuma abokin cin mushensa, duk wani halin da Jasminah take ciki Alhaji Mudansir ya sani kawai tsabar masifar son kudi ne irin nasu.

Yadda Fahad ya sha azaba ga kayansu da aka rike, domin aka zargin kayan akwai miyagun kwayoyi, burin mijinta shine wani daga cikin manya da suke gefen Turaki su saka hannu yadda idan aka sake mishi kayansa sunansa ba zai baci shi ɗaya ba, sannan koda yayiwa Mahaifinsa magana yayiwa Alhaji Mudansir magana sai ya ce a'a baya son saka hannunsa a cikin irin wadannan dirty stuff din, shine kawai ya tabbatar da su yi ta threating Jasminah yadda dole zata saka Turaki ko Mujitafa su saka mata hannu. Ai kuwa bukata bata biya ba domin gashi nan dai ba a je ko ina ba kome ya b'aci musu tunda sun tab'a me yaya irin Turaki.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull