Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 22

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 22

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 22: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 22. Bayan fitar sani yace duk wanda ya kara kula Mama da su Lubnah bai yafe ba, Yadiko da take…

4,310 words

Bayan fitar sani yace duk wanda ya kara kula Mama da su Lubnah bai yafe ba, Yadiko da take waje tace mishi. "Wannan dai ita ce ake kira karya domin ba zaka raba su da uwarsu da yan uwansa, kai kar ku sake ku dauki wannan maganar, hakkinku ku kula da Uwarku da Yar kanwarku, kune gatanta." Yadda Yadiko ta nuna musu nasu kada su dauki maganar shi ya kara kwantar musu da hankali, yayi ta fada karshe a daren sai da ya koma asibiti, take Hafiz ya kira Jama'are ya gaya musu cewa ai ga abin da ya faru, sai ga yan Jama'are mota guda, a nan kowa ya nuna Mama bata kyauta ba, jinin halin da Abba yake ciki da kuma ganin yadda yake kwance bai da lafiya, Hafiz ne kanshi ko asibitin yasa aka yi ta zagin Yaranshi da nuna Hafiz ya zama gatanshi tunda gashi ya haife su amma Uwarsu tafi shi moransu, tunda gashi kowa ya juya mishi har Yaran Yadiko, suna tsaka da maganar Yadiko ta iso wayyo ai Mama ita nata karamar yaki ne, Yadiko da ta ji abinda suke fada da ta fara bala'i da cira kamar zata tashi sama............. [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 34 ' Shi yasa Allah ya tsinewa mai tadda fitina, domin kuwa rigima sosai aka yi kamar za a daku, wai duk akan Hafiz da Lubnah. Ai kuwa lamarin har Jama'are, abinda ya dawo kunnen Mama aka yi ta cewa suna son kashe Baban Bauchi ne saboda dukiyarsa, domin su ci gado musamman Mama da yake ita ce Uwar Yara dayawa, wato ita fitina idan tana barci mafi alkhairi a barta ta cigaba da barcinta kada a tashe ta, amma wannan karon sun tashi lukutar masifa, domin Mama har Jama'are ta cimma Goggo Uwani da Talatuwa da suka haddasa rikicin, ta ce sai sun shiga kotu domin wanke mata suna, da suka ce tana son kashe musu dan uwa. Nan fa hankalin kowa ya tashi rigima ake yi tun karfe bakwai na safe har karfe biyar na yamma sallah yake tashin su dakyar da suɗin goshi Mama ta hakura bayan manya daya daga Fada sun shiga lamarin, ta kuma ce a shata mata layi a tsakaninsu, idan wani magana ya fito ba zata yarda ba sai gaban kuliya manta sabo. Jin wannan abinda take shirin yi yasa kowa ya shiga hankalinsa aka fita harkanta da Yaranta. *** A cikin kwanaki biyu ko waje bana lekawa, zai yau da Aunty Nuratu ta zo da kanta. Sai na ji kunya ya kama ni, a hankali na sauko muka shiga mata hidima. Sai da ta ɗan sha ruwa sannan take kallona. "Ina ta jiranki ina lafiya?" Murmushi nayi duk da rashin sabo a tsakaninmu, amma yadda take damuwa da lamarina yasa zuciyata sakewa da ita nace mata. "Ciwon kai da habbo ya hanani fita!" "Kina yawan tunani ko?" Kallon Aunty Zakiyah da ta kawo mata snacks nayi domin ta amsa mata da cewa. "Ai kullum muna magana akan tunanin nan." Kallona tayi can ta ce min. "Duk abinda zai faru ba zai tab'a kai na baya ba, you need to move on. Kin tab'a tsammanin zaki samu freedom haka?" Murmushi tayi tana kallon yadda na rike hannuna da juna. "Ba laifinki ba ne, ƙaddara ce ta zo miki a haka. Sannan idan da kowani mutum yana da iko da ƙaddaransa da dayawa basu yarda ajn haife su a low background ba, amma da yake mu musulmai ne masu bin tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama." Muka karasa salatin tare ta daura da cewa." Me kike tsoro wanda da baki gani ba? Me kike gudu wanda da bai same ki ba, me yasa ba zaki yi accepting din kanki ba? Tsoro yana da kyau amma rashin karban kai shine asalin tsoron da ake gudu, dayawa masu kashe kansu a duniya tsoron karban kansu suke, accepted yourself, love yourself, and move on, idan kika yi haka zai matuƙar wahala wani ya rusa ki, ko yan uwanki zasu kara jin dadin you accepted yourself, zasu iya miki yaki ne idan sun ga kin karbi kanki a yadda kike, a duniya ma zata girmamaki ne idan kin amshi kanki, ko waye zai girmama ki ne idan yaga kin amshi kanki a yadda kike, duniya da mutanen cikinta basu damu da ka mutu ko ka rayu ba, damuwarsu shine taya zaka gaza a maka dariya, amma daga lokacin da kika nunawa Duniya zaki iya survive idan da mutanen cikinta, ko babu ita da mutanen cikinta zaki iya tafiya da kanki, daga lokacin duniya zata dawo bayanki, zata koma tana yayyataki ai ke jaruma ce, a kowani raunin dan adam zaka samu na kusa da shi sun bada gudummawar maganin warka da raunin, amma idan raunin ya gaza warkewa kowa zai watsa a kan rauni, ki kaunaci kanki, duniya sai ta kaunace ki. Ki koyo saka kanki farin ciki duniya sai ta taya ki farin ciki. Ki kashe tsoron da yake ranki sai ki tayi cikin sallama, idan har kika rayu da farin ciki babu wnada ya isa kallonki ya gaya miki magana, shi mutumin da yayi gwagwarmayar domin ya rayu don lafiyarsa zai matuƙar wahala bai samu soyayyar gaskiya ba, kina bukatar ki girma da kanki ba tare da wani ya ce shi ya saka ki girma ba.

Open your heart and make a wish, kina son ki rayu ki ga idan Allah bai raya ki ba, ko da zaki yi addu'a matukar baki yarda da kanki ba, matukar baki saka yakinin ba tow babu inda zaki domin Allah yana amsar Addu'ar wanda ya yarda da shi ya kuma saka yakinin zai taimaka mishi, idan kika ga matan da suke gym din nan, akwai wacce mijinta har sayar da ita yayi ta tafi karuwanci, akwai wacce Mijinta watsa mata ruwan battery yayi bai samu fuskantar ba ya zube a bayanta. Akwai wacce kullum dukarta yake saboda ta haifa mishi yarinya handicap, baki godewa Allah ba da ya miki ni'imar da sauran basu samu ba? Idan da zan bude miki file din kowacce, sai kin ji kamar taki matsalar ba kome ba ne, mu anan ƙabilarmu babban abin tashin hankali namiji ya sake ki, za a nuna miki iyakarki, ina son ki zama mace ta farko Bahaushiya daga arewacin Najeriya da ta san kanta ta kuma yarda da kanta. Idan har kin yarda da kanki, Auntynki Nuratu Kafaya tana kiranki, idan kuma kika sake tsoron nan ya mamamye ki. " Murmushi tayi ta mike tana me daukar jakarta tare da yiwa Aunty Zakiyah magana. " Madam zan tafi! " Fitowa Aunty Zakiyah tayi muka rakata. Cikin wata motar alfarma ta shiga, ta d'aga min hannu, haka naji kamar anya xan iya zama mutum kamar yadda ta ce? Jiki a ma ce na shigo cikin gidan. Ina kallon kasa. "Ya kamata ki kara gaba, sannan ba zaki bikin Sani ba, ke da Bauchi yanzu sai wani Ikon Allah. Ba zaki ko ina ba, ki zauna ki gina kanki na jima da sakawa a raina ba zaki Bauchi ba, ita dai wacce aka koran nan sai ta zama wacce ake kwadayin ganinta, idan Mama kike son gani Allah ba zai hana mu kudin kawo ta nan ta kwana biyu ba, zamu tafi Bauchi ni da Yayanki, ke da Yara zaku zauna anan, a matsayina na wacce makarancin likitanci, idan muka je Bauchi aikin da muka sha wahalar yi dare daya Hafiz da Abba zasu rusa mana, babu inda zaki kin ji aiki domin ba zamu yi gini wani ya rusa mana ba. " Ji nayi kamar an kara yanta ni, murmushi yayi ban ce mata kome ba muka shigo cikin parlourn na tayata kwashe kayan da ta kawowa Bakuwa muka kai kitchen. Nan na wuce dakina na kwanta sai lokacin sallah ka tashi nayi, a cikin addu'ar da nake har da Allah ya bani ikon yarda da kaina.

Sai dai kuma ina gama addu'a naji wasi-wasi a raina, haka na lumshe lekowa har na wani lokaci. Kafin na bude ina kiran sunan Allah. Wasi-wasi ya saka ni a gaba, washi gari na shirya na tafi makaranta, karfe biyu na taso, sai na tsaya a gym din, yan wurin na ganina. " Lulu!" Fuskarsu cike da fara'a suna ta min barka da zuwa. " Tunda kika zo baki kara zuwa da fatan dai lafiya domin dukkanmu nan mun zama daya." Gyada kai nayi ina faɗin. " Ban ji dadi ba ne?" Ai kuwa a rud'e suka yi ta tambayata meke damuna, na ce ciwon kai nan suka yi ta min sannu sannan na shiga wurin Aunty Nuratu Kafaya, na samu tana tattaunawa da wata mata sai kuka matar take. Itama dai katuwa ce. " Ku yi hakuri ba ri na jira a waje! " " A'a gashi ki tafi daya office din ki bawa Wasim zai miki bayani." Gyada kai nayi ina faɗin. " Na gode sosai! "

Na fito na tsaya a bakin kofar ina raba idanuna, yarinyar ta Nasiba na gani zata fita ta ce min. " Aunty kina son abu ne? " Gyada kai nayi mata ina mika mata.." office din Uncle Wasim zaki! Muje na kai ki." Ina bayanta ta kai ni har office dinsa, da sallama muka shiga, shima yana bako, yadda yake magana a nutse zaka fahimci shi din Coach ne da yake ganin mutane daban-daban. "Kanwata shigo!" Ya fada yana murmushi, kafin ya kalli mutumin ya ce mishi. " Yawwa kamar yadda na gaya maka, zaka iya kawo ta mu fara ganin yadda zamu gina lafiyar jikinta. " Mika mishi hannu Mutumin yayi sannan shima ya mika mishi ya mike matsawa nayi mutumin ya fita ya zauna yana nuna min wuri na zauna. Mika mishi takardan Nasiba tayi tana faɗin.. "Uncle ni fita zan yi, naji wai an sake sakamakon Allah yasa ina cikin wadanda zasu diba." "Allahummah Amin Daughter Allah ya bada sa'a." Ya fada yana mata murmushi fita tayi, ya kalle ni. "Shekara biyu kenan tana niman aikin masu kula da fasinjoji na jirginsa, bata tab'a sarewa ba. Bana ma haka har azumi take da sadaka Allah ya bata sa'a. Kin ga kuwa dole mu taya ta da addu'a Allah ya bata sa'a ko?" Ya fada yana kallon takardan hannun.. "Da kibar aka haife ki?" Girgiza kai. "Bana son body language, speak!" "Tow!" "Kin tab'a haihuwa ne?" "A'a;" kallona yayi da kyau, kafin ya ce min.. "kin taɓa birth control ne?" Anan na sunkuyar da kai ina matse hannuna, bude drower yayi ya ciro wani irin ball ya mingiro min, "idan kika shiga irin wannan yanayin us it, kina matsawa yana rage damuwa. Me yasa kika sha birth control?" "Tsohon Mijina ya bani." "Amma yana sonki!" Matsa ball din nayi murmushi yayi sannan ya ce min.. "duk mutumin da yake sonka baya naka abin hana daukar ciki am sorry!!" Shiru yayi ya cigaba da cewa. "Zaki ragu amma sai kin saka a ranki zaki ragu, kina da saurayi ne?" Da sauri na kalle shi. "Oops babu ko?" Ya tambaye ni yana murmushi. "Tow daga yau ki saka a ranki, kina son ki burge saurayinki ne, kin san waye saurayin?" Girgiza kai nayi, murmushi yayi ya ce min. "Kanki, kanki zaki burge ki ji a ranki soyayyar da zaki yiwa jikinki don kanki zaki yi ba don wani ba. Kin san me? Dole ki fada soyayya da kanki haka zai baki damar kula da kanki, sannan ki yi hakuri da kowa ki yi hakuri da kome kada ki sake wani ya ba'ta miki rai, ki ji a ranki kina da kanki da ya tsaya miki all I want to you love yourself, ki yarda da kanki ni kuma zan yi ƙoƙarin baki step by step na kula da kai.

Wannan sune tsarin abincin da zaki fara ci kullum da wanda ya haramta miki,. Idan kina da soyayya da bread da fanta irin naku na Fulani ayi hakuri daga yau an daina shan duk wani abu me zaki, kin ga kibar nan naki idan da za a bincika ba za a rasa uric acid da Diabetes ba, sannan akwai tarin kitse da dole a narka da shi, sai kuma rage cikin abinci mai yawa, idan za a ci a sha ruwa sosai, sai a hada akwai bayani akan nan duba ki gani."

Ga wasu hanyoyi da za su taimaka miki wajen rage kiba da kuma wasu shawarwari a kan abincin da ya kamata ki ci: Hanyoyin Rage Kiba da Inganta Lafiya 1. Kula da Abincin da Kike Ci * Rage Abinci Mai Sukari da Mai: Ki rage cin abinci mai zaki (kamar su alewa, lemo na kwalba, da waina mai sukari) da kuma abinci mai yawan mai (kamar soyayyen abu). * Yawaita Cin 'Ya'yan Itace da Ganyaye: Su na ɗauke da sinadarai (fiber) da ruwa da suke saƙi da ciki, kuma suna da ƙarancin Kalori (calories). * Cin Abinci Mai Wadataccen 'Protein': Irin su kifi, ƙwai, nono marar mai (yogurt), da wake/gyaɗa. Protein yana taimakawa wajen rage yunwa kuma yana ƙarfafa tsoka. * Rage Cin Abinci Mai 'Starch' (Carbohydrates): Abinci irin su shinkafa, taliya, burodi, da fura. Idan za ki ci su, ki ci da 'ya'yan itace ko ganye. 2. Yin Motsa Jiki (Exercise) * Yin Tafiya: Ki fara da tafiya mai tsawo ko da na minti 30 ne a rana. Wannan yana da sauƙi kuma yana da fa'ida sosai. * Gudu Ko Gudun Tsalle: Idan za ki iya, ki dinga yin gudu ko ki yi 'skipping' (tsallen igiya) don ƙona Kalori da yawa. * Yi Motsa Jiki Akai-Akai: Ki maida shi wani ɓangare na rayuwarki, ko da sau uku (3) ne a mako. 3. Shan Ruwa * Yawaita Shan Ruwa: Shan ruwa kafin cin abinci yana taimakawa wajen rage yawan abincin da za ki ci. Ruwa yana da matuƙar muhimmanci ga lafiyar jiki. 4. Kula da Barci * Samun Isasshen Barci: Rashin isasshen barci na iya canza sinadaran jikinki waɗanda ke sarrafa yunwa da koshi, hakan kuma na iya sa ki ci abinci fiye da yadda ya kamata. Ki tabbatar kina samun barci mai kyau na awanni 7 zuwa 8 kowace rana. Abincin da Ya Kamata Ki Dinga Ci Ga wasu misalai na abincin da zai taimaka miki wajen rage kiba: Nau'in Abinci | Abincin Da Ya Dace Dalili Ganyaye | Alayyahu, kubewa, kabewa, latas (Lettuce), kabeji (Cabbage) | Suna cike da sinadarai kuma suna da ƙarancin Kalori. 'Ya'yan Itace Tuffa, lemu, abarba, kankana, ayaba (kaɗan) | Masu zaki na halitta, suna da Fiber. Protein | Kwai (Boiled/Gasashe), Kifi, Nono marar mai (Yogurt), Wake/Gyaɗa, Naman Kaza (Chicken Breast) | Yana saƙi da ciki na dogon lokaci, yana rage sha'awar cin abinci. Abinci Mai Fiber | Hatsi (Oats), Dambu, Gurasa (Whole Grain Bread), Rogo (idan ba mai yawa ba) Yana taimakawa wajen narkewar abinci da sauƙi a ciki. Muhimmin Bayani: "Ki nemi shawarar likita ko kwararre kan abinci (Dietitian) kafin ki fara wani tsari mai tsanani. Za su iya duba lafiyarki su ba ki shawarar da ta dace da ke." [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 35 " In sha Allah!" Haka na mike ya ce min, "Lubnah!" " Na'am! " Na amsa mishi, ki duba time table dinmu, sai ko zabi ranakun da kike so, sai ki nime kayan da zaki na amfani da su." "In sha Allah!" Sannan na fita sai da na leka Aunty Nuratu Kafaya, na mata sallama akan gobe laraba zan fara zuwa ranar Saturday. Haka na koma gida na samu Ya Ado na mike mishi takardan ya ce mu shirya mu fita, haka muka fita dukka gidan muka je wani super market anan Ikeja, sannan ya kai mu wani shagon sayar da kayan kwallon, ya saya min kayan da zan na fita zuwa Exercise da sassafe da kuma wanda zan na sakawa zuwa Gym din, haka ya saya mana har da Yaran da su kansu iyayen muka dawo.

Kamar yadda Ya Ado ya kawo kayan Aunty Zakiyah ta amsa ita ta fara nuna min yadda ko bata nan zan iya dafawa. A ranar dai ban ci abinci dare ba, sai ruwan tea da fruit da sha. Washi gari da safe ya Ado ya cika min water bottle da ruwa ya tashe ni muka fita. Ana sallah asuba muka fita bamu dawo gidan ba sai shiga da arba'in, wanka muka yi na sha nikakken ruwan fruit, sannan na kwanta. Ban tashi ba sai karfe goma, ina fitowa na samu, kunun tsamiya, da faten wake da yaji ganyen alayayu, sai agada, sai da na sha ruwa kafin na karya, ina zaune a parlourn aka yi knocking, Mai aiki ra bude kaya aka kawo, a kwali. Suka shigo da shi Ya Ado yana bayansu. Zuwa yayi nuna inda za a saka sannan ya koma wurin aikinsa. Washi gari ya kama juma'a, shima sai da muka zaga unguwarmu sannan na dawo, kayan da aka kawo machine ne na Exercise, Ya Ado yana dawowa daren jiya ya haɗa ya gwada aiki da shi a daren jiya.

A ranar bayan sun fita nima kusan a kai na wuni, dadare kuwa abincinsu suka ci ni kuma na ci nawa tuwon alkama zalla miyar ayoyo, daga nan kuma na sha fruit na kwanta, ranar asabar karfe goma na tafi Gym, sugar kuwa tuni na yi bye bye da shi, wunin ranar Yorghurt na sha daga kuma sai ya rike min ciki. Karfe biyu na bar gym din zuwa gida yau nayi rayuwa da ban tab'a yi ba, sai nake gani kamar mafarki. Ina typing har na iso Unguwarmu, na karasa gida, a harabar gidan na hango Ya Umar wani murmushi ne ya kwace min na isa gare shi, ya dan rungume yana faɗin.. "Auta manya an zama yan gari. Daga Gym ko?" Gyada kai nayi ya ce min. "Shiga bari na gama waya na shigo." A parlourn na samu Mamana, wani ihu da nayi na isa wurinta da gudu na rungume ta, tana buga bayana. "Sannu Autana, sannu yar jinjirana! Ai tunda suka ce ba zaki zo biki ba nace ban isa ba, zan zo na ganki kada na mutu ban ga autana ba!" "Mama me yasa kike kiran mutuwa? Mama me kika kawo min? Mama ina Yadiko?" "Suna lafiya tana ta shirin bikin Sani!" "Allah sarki!" Na ji dadi sallah ya tashe mu na ja ta sama, tayi ta mita ita bata son sama, ai kuwa tunda ta hauro tace ba isa da ciwon kafa ba, karshe Abinci ma sama aka kawo mata, ni kuwa dad'i kamar na nutse kasa, tun a daren na gayawa Nasiba ta gayawa Mamanta Mamana tazo daga Bauchi. Kwana muka yi da Mama muna hira tana bani labarin abinda ya faru, hakuri nayi ta bata, karshe nayi barci na barta tunda na fara Exercise barci ya daina min wahalar yi. Washi gari Lahadi sai ga Aunty Nuratu Kafaya, ita da Mijinta, Mama ta ji dadi nima na ji dadi gashi an hadu ana ta hiran arzikin, sai la'asar Mijinta ya zo ya dauke ta. Koda na zauna ina cikin ganye Mamaki Mama take ta kasa hakuri ta ce. "Wannan wacce irin rayuwa ce? Yarinyar da rayuwa da ganye ita ba akuya ba ita ba tsutsa ba, Auta dole aka miki ne?" "A'a yana cikin kayan karin lafiya ne, idan ina ce kibar zata ragu ko ta tafi bakiɗaya." "Aiho yanzu na fahimci yadda lamarin yake. Allah ya kara lafiya shi yasa idan na zoma zan ta dafa miki zogale ina shanyawa da rama da yakuwa." Haka Aunty Zakiyah tayi ta mana dariya, satin Mama biyu ta koma Bauchi ta bar ni da kewarta sai waya kawai muke.

Bikin saura wata gudu muka fara jarabawa, na kara mai da hankali sosai sai fa muka sha wuta na tsawon wata guda sannan muka samu hutu, rayuwa tana cike da darasi na musamman Ya Ado da Aunty Zakiyah sun tafi, ni kuma na cigaba da kula da kaina, da taimakon Aunty Nuratu Kafaya, sati daya suka yi wanda aka sha biki da karamin gurmi aka dawo aka bamu labarin wai Yan uwa Ya Hafiz da Yan uwanmu ana ta habaici an tura ni karuwanci suna jiran sakamakon bariki, shine fa Yadiko ta rufe Aunty Nana Asma'u da fada ta ce mata. "Har kina da bakin magana? Karuwanci ai ya kare tunda tana gindinku!"

Rigima sosai a gefe guda Matar Hafiz itama ta kashe auren ne ko yana lilo oho amma dai ana ta rigima tace tunda ta aure shi ita bata gamsuwa, hakuri take da shi. Aka ce Abba kamar yayi hauka yayi ta fada yana rarrashin Hafiz, wannan ya karawa Hafiz wani irin tashin hankali, yayi ta kuka yana rokon Abba ya dawo mishi da Lubnah shi yasa kaf duniya babu Macen da zata iya rufa mishi asiri kamar Lubnah, yadda ya shiga damuwa sosai Abba shima jininsa yayi ta hawa kafin a gama bikin nan sai da ya kwanta a asibiti sau biyu. Abu fa ba dad'i sai gashi har Abba da kanshi wai ya je wurin Mama yana rokon arziki ta dawo da Lubnah, ai kuwa da Abba da Ya Hafiz Mama ta ce sai ta kai su kotu ta ji Uban da suke bukata da Lubnah.

HAFIZ Don shi kanshi bai kawo a ransa Lubnah ba zata zo ba, saboda yadda ya santa da Sani, amma wani ikon Allah bata zo ba ya kuma kudira a ransa da ta zo sai ya san yadda yayi dawo gare shi yadda ba zata kara barin Bauchi ba sai da izninsa amma dai gashi bata zo ba abin ya bashi haushi, ga Nana da ta gudu ta fasa auren. Gashi ya ga hoton Lubnah a wayar Rufa'i da yake zolayar Aunty Zakiyah ta dauke mishi First love dinsa wato Lubnan kasancewar dan Goggo Alti ne, yana jin su yayi kamar baya wurin yana ganin lokacin da ya bashi number Lubnah da kuma hotonta. Bai nuna zallamarsa ba sai da washi gari ana hira ya ce Rufa'i ya bashi aron wayarshi, zai yi abu ne ai kuwa yana amsa ya binciko number Lubnah wanda Rufa'i ya saka mata bazawarata Lubnah, sai hotonta da ya tura kusan kala goma tayi shi da gym outfits, wani baki da ratsin pink yayi azabar kyau ga kanta da ta saka wata hula me kyau gargasar gaban goshinta sun kara fitar da kyanta da ya boya behind kibar ya fara fitowa, wani murmushi tayi, daya kuma ta fitar da harshe waje kamar tana gwalo, wani kuma tana kan abin motsa jiki na gidan daga ita sai riga da wando ta tufke gashin kanta, wani irin gigicewa Hafiz yayi kamar zai zauce. Bai taɓa kawowa a ransa zata dawo kamar da ba. Wannan abin ya d'aga mishi hankali wani hotonta kuwa wani yatsina fuska tayi tana dariya, alamar magana ake mata tayi haka sai kuma ita da yaran, wani kuma a makaranta. Zufa ke karyo masa yana ji ina zai iya ganinta yasan yana ganinta zata fit hayacinta ta nemi dawo mishi, haka ya mai da wayarwa Rufa'i sannan ya koma gidansa yana kallon Yaranshi da suka ci abinci suka koshi, Hajiya tana gidan ita fa Fido. Zuba mishi idanun tayi ta ce mishi. "Duk akan matsiyaciyar yar nan ne?" "A'a Hajiya Lubnah na gani!" Ya cire mata hoton ta gwalalo idanun waje kamar tsohuwar mayya tana faɗin. "Ina ka samo ta don Allah dama yarinyar nan zata dawo kamar da?" Murmushi yayi ya ce mata. "Hajiya ki taimaka min ta dawo gare ni!" "Ba ga zoben nan ba ai shi ne kankat sai kuma shi wancan uban nata kasan yadda zaka yi da shi." Nan suka yi ta tsara yadda zasu dawo da Lubnah. A daren ranar ya tashi hankalin Baban Bauchi da kuka da rokon ya dawo mishi da lubnah itace daidai da rayuwarsa kasancewar akwai sauran yan biki, suka yi ta bashi hakuri da cewa idan Matarshi ce zata dawo gare shi.. Abu kamar wasa sai gashi Baban Bauchi ya tashi hankalinsa sai da ya kwana asibiti, Goggo Alti tayi ta fada. Da Baban Jama'are da Baba Malam suka zo nan suka fara fada ai a dawo da Lubnah. Yadiko da kanta yayi wata ta ce musu. "Tunda tare aka halicce su ai sai ya je ya dawo da ita, sannan aure babu shi a tsakaninsu tunda har sun karbi khulu'i din da ta bayar, haka maganar ya mutu. Ranar daurin aure a shirin da suka yi akan idan aka zo daurin auren Sani sai a hada da na Hafiz da Lubnah, ai kuwa ana gab da daurin auren Babangida da yazo daga Maiduguri ya same shi yake ce mishi. "Daurin auren Sani muka zo yi ya nake jin wai za a sake daura auren Lubnah da Hafiz bayan kace ba kai ba ita? A da can ma baka mata dole ba sai yanzu cikarka Uba na gari shine ka dakatar dasu idan ba haka ba wallahi za a kafa mummunar Tarihi a zuriarka domin zan kashe Hafiz idan aka daura auren nan da shi!" Wannan barazanar da Babangida yayi shi ya dakatar da auren da ake shirin kara daura shi, haushi da takaici ya saka BP dinsa low. Domin yana fama da ita ko ta hau da zaran ranshi ya b'aci zata sauka da gudu, sai dai a ganshi yana fari da idanun da jijjiga.

Hafiz da Baban Jama'are da Baba Malam sun ji haushin wannan lamarin, domin Hafiz saka su yayi a gaba da rokon su saka baki amma al'amarin ya koma haka. Wasa gaske haka aka gama bikin Sani babu wata matsaya domin kuwa babu ita shine daga baya aka je rokon Mama tayi tsalle tace abokin mutuwa take nima akan Lubnah.

A bangaren Hafiz yana son kiranta amma yana tsoron kada ta gayawa Ado ya mishi rashin mutunci haka yasa ya hakuri da kiran yadda kudirinsa xai cika. *** Akwai wani abu da na fahimta, tun da na fara kula da kaina da kuma kula da lafiyata, sai na ga kamar nafi samun kwanciyar hankali. Dadindewa gaba nake kamar ana hankad'a ni.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull