ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 23
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 23: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 23. Kwanaki suna tafiya satika suna gudu, watanin na zuwa daya bayan daya a hankali na gama…
4,080 words
Kwanaki suna tafiya satika suna gudu, watanin na zuwa daya bayan daya a hankali na gama master dina da gagarumin nasara, ga shi dai na sauka sosai, idan ka kalle ni sai ka kara kallona, sai ka yi ta mamaki kamar ba ni ba a cikin wata shida da wani abu sai gani ina kyauta da kayana. Har Bauchi aka kawo aka kai Jama'are aka rabawa yan uwan Mama da Jikokin Goggo Alti, ai kuwa Goggo Uwani da Talatuwa suka yi ta fada wai ba asan da su ba, shi yasa aka rabawa waɗanda ake so, Mama da bata iya kyale su ta ce musu ai da na basu kayan sai ta biyo ta kwace yadda basu da mutunci karya su ci arzikin Lubnah....... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 36 Zuwa yanzu ina son kaina, na fahimci duk wnada zai soka bayan kaso kanka ne ka kuma girmama kanka. Duk wanda ba zai soka ba babu amfanin zama da shi, amma firstly ka so kanka ka kaunaci kanka yau na ji kaf duniya babu wanda ya dace na so sama da kaina, amma har yau ina jin a raina ya Hafiz shine ajalina yadda nake bala'in tsoronshi har yau ban cire wannan tsoron na a raina. Ina tsoronshi daga kasar zuciyata. Wani irin tsoron shi nake tare da sauran maza bakiɗaya. Idan akwai abinda zai hada ni da maza tow na hakura da shi, haka yasa hatta waɗanda muke wurin Gym din suma suka kame kansu babu wanda ya tab'a shige min, duk da na sauka amma haka bai hana na cigaba da motsa jikin ba, wani abinda ya fara daukar hankalin mutanen wurin shine ni dai kiba na ke son ragewa amma wani abun mamaki sai ya kasance daga samata na ragu sosai, zuwa kasata sai ya bada shape irin yadda zaka ga wasu suna bukatar domin cinyata zuwa mazaunai na, sai suka fita fess, wanda ya haifar da cikina zuwa kirjina ya wani irin fita kamar dai yadda ke kira coca cola, haka shape din ya fita, a lokacin da na fara yiwa Aunty Nuratu Kafaya magana abinda ta ce min kuwa ya saka ni shiru. "Ai dama haka halittarki take yanzu kuwa zaki dawo asalin yadda kike, tumbin da ake gani yanzu ba gashi yana ta sauka ba, a hankali kafin nan da shekara daya duk zaki dawo yar cass yanayinki zai fito kamar na yan boko yan yayi." Kawai sai ban kara damuwa ba, a lokacin aunty Zakiya har da min tsiya wai na koma kamar wata yar Nigeria Film, ni dai ban kulata ba.
*** KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY.
Yau Litinin kusan wata shida da mutuwar Auren Jasminah, mahaifiyarta ta sakota a gaba haka yasa tayi give up bakiɗaya take kuma jin rayuwarta bata da amfani, sai dai a yadda Uncle Auta da Ubaid suke tsaye a kanta yasa ta ke samun nutsuwa. Yau aka turo mata da shaidar an dauke ta aiki a kamfanin duk da ba aikin da tayi ba kenan amma kai tsaye Turaki ya ga dacewar ta fara aikin haka zai rage mata damuwa da halin da take ciki, sannan zata nutsu sosai ta kula da Yaranta.
Karfe takwas yayi mata a cikin kamfanin, kiran wayar aka yi ta dauka tana faɗin. "Na gode sosai, gani a office din." "Na baki awa 48 ki fitar min da abinda nake bukata daga cikin yanayin ma'aikata zuwa sauran abinda ake bukata." "In sha Allah!" Ta fada, tana kallon office din, tana mai girgiza kanta. Abinda ta fara dubawa ma'aikata nawa ne a cikin kamfanin? Don haka ta fara fita ta isa office din MD Khamis Abbas Kumo, buga kofar tayi amma baa bude ba. Masinjasa yace mata. "Hajiya bai isa ba an jima kaɗan zai iso;" "tow! Ina ne office din shugaban ma'aikata?" "Office din Mrs Thomas kenan muje!" Ba musu ya rakata, ta samu ta zo tana ta aiki ta haɗa nan ta haɗa can, mika mata hannu tayi suka gaisa nan ta gaya mata me ake ciki a kamfanin.
Murmushi tayi ta ce mata. "'kamar yadda kika gani ma'aikata dayawa basu shigowa sai lokacin da yayi musu, haka basu tashi sai a lokacin da ya dace, sannan idan wata yayi aka samu jinkirin albashi su ta korafi! Muje ki gani!" Haka suka cigaba da tafiya kamar yadda dai ake fama da kowacce irin ma'aikatan da kamfanonin, haka inda ake ajiye kayan ma ya lalace, ga ba ma'aikatar da ya dace. "Sannan Madam ana sata anan kayan da ake sacewa dole ya baki mamaki!" Ita dai Jasminah tana rubutawa, tana kara mata tambayoyi har suka isa cikin store din da ya lalace. "Ko last year an karbi kudin gyaran nan sama da miliyan talatin amma ba a gaya ba, ita kanta kamfanin tana bukatar gyara da asalin ma'aikata masu son aiki ba irin wadanda aka lalata su da rashin son aiki ba. Oga Ubaid yana kokari amma da zai yi wani motsi take za a fara mishi gorin yafi yan gidan kamfanin zakewa, yana son yayi aikin amma da zaran ya fara aiki za a fara magana kai ko dakatar da mutum yayi MD zai dawo da shi ko vice chairman, kamfanin nan ana abubuwa dayawa amma baka da ikon magana, akwai abinda nake son ki sani mu kanmu ma'aikata mata we are not safe daga baragurbi irin MD Khamis Abbas Kumo." Shiru tayi tana me kawo ta wurin ajiyar kayayyakin da ake kwaso kayan gwanjon ta ce mata. " Kin ga wannan motar da sauran sun lalace idan har xa'a yi amfani da shi sai mun dauki haya, madadin a gyara mana wannan, sannan zuwa yanzu akwai bankunan da suke bin kamfanin nan sauran cikon kuɗinsu. Na gayawa Ubaid ya ce ba ruwansa domin ko na bankin UBA da yayi magana karshe sai da aka samu matsala akace yana da hannu a ciki aka so shi frame dinsa da laifin cin hanci abinda na sani idan har CEO ne a kamfanin nan dole a kawo gyara da sauyi don Allah muna bukatar ma'aikata da waɗanda zasu tsara mana yadda kamfanin zai yi gaba ba kullum a baya ba, kaf Nigeria ita ce ɗaya idan har aka samu na biyu tow tasirin kamfanin zai yi kasa ki duba maganata da idanun basira. " Haka suka gama zagaye kamfanin sannan suka dawo bakin kofar kamfanin suka zauna suna kallon mutane da suke ta zuwa har suka gama bata ce musu cikanku ba, ta mike ta na me nufar cikin kamfanin, office dinta ta shiga ta fara aiki ba kama hannun yaro, karfe daya Ubaid ya shigo, kallonsa tayi tana faɗin. "Sai na fadawa CEO mukaddashinsa sai karfe daya yake shigowa kamfanin." "Ai kuwa da kin kyauta dama ya haɗa ni da aiki ne nake son na rabu da shi na ji da aikina ko da aikinsa?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Zauna Hamma Ubaid!" Zama yayi ta fara tattara bayanin da ta haɗa na yau ta ce mishi. "Yau na leka kamfanin bakiɗaya na ga abinda bai dace ace na gani ba, karfi da yaji ana son kashe kamfanin nan meke faruwa ne?" Ta mika mishi bayanan da ta hada. Murmushi yayi yana faɗin. "Wannan ai tsohon lamari ne, amma idan kina son ganin yadda rayuwar kamfanin yake ki fara da office din Vice chairman, zuwa office din babban sakatare zuwa na MD kafin ki zo na sauran ma'aikatan, ki yi bincike duk abinda baki gane ba ki tuntube ni." " In sha Allah! " Ta ce mishi sannan ya fita, itama sallah tayi a office din sannan ta ji tana son cin abinci, mikewa tayi a hankali, a saninta lokacin da Babanta yake kamfanin abinci da ake ci kyauta ce don jin daɗin ma'aikata, fitowa tayi a lokacin ta ga shigar wata mace office din MD, office din Mrs Thomas ta isa ta ce mata. " Mrs Thomas ya batun abinci har yanzu ana yi kuwa? Don yunwa nake ji. " Girgiza kai matar tayi ta ce mata. " Tunda aka yi gobara a dakin girkin aka rufe bada abinci ga ma'aikatan kamfanin nan." Shiru tayi tana me jinjina kai, sannan ta juyo tare da nufar office din MD, tana isa kafin Masinjan ya mata magana tuni ta tura kanta. Abin da ta gani yasa tayi baya da sauri. Bata yi magana ba ta juya ta bar wurin. Turawa Turaki sako tayi bayan ta zauna a kujeranta. *Ni dai gaskiya ka cilla ni a uku kamfanin nan sai kai ne kaɗai zaka daura shi akan hanya a yanzu kan kome ya lalace don Allah ka dawo.* Bai cika reply messages ba amma yau da ta tura mishi sai ga sakonshi ya dawo mata. _Ki yi duk abinda na zaka ki sannan duk abinda kika ga ya dace ki yi idan na ga abin yayi zan kara tuntubarki_ Tura baki tayi tana hararan wayar, haka ana tashi ta wuce gida. Koda ta isa gida wasu files ta amsa a wurin Ubaid tayi ta bincike, sannan ta cigaba da tura mishi bayanin halin da ake ciki tare da gaya mishi ana bukatar sabin ma'aikata amma yanzu a fara gyara kamfanin, haka ya turo musu kudi ya ce kada a tab'a na kamfanin domin yana da lissafi akan kudin kamfanin. A tsakanin sati biyu aka fara aikin tare da kwashe tsofaffin kayan akayi ta sayar da su ga yan bola jari, wani abin haushi duk an yi sata wasu ma karafunan kamfanin sarrafa mota na kasar Japan aka sayarwa don asarar tayi yawa, haka sai ya bawa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo mamaki tare da Abbas Kumo domin dare daya suka ga ana ta aiki kamfanin ma an sabunta shi, hankalinsu a tashe suka sakata a gaba da tambayar me yake faruwa, karshe har gaban Alhaji ELYakub Kumo aka kaita, ya ce musu. "Aikin da kuka gaza yi ne take yi kuma Umarni aka bata daga CEO idan zaku iya sai ku dakatar da ita." Jin haka yasa suka sha jinin jikinsu. Nan matan suka fara tambayar dawowa zai yi?
Kwatsam Badr ta koma gidansa na Lekki da zama, amma bata kwana a gidan gidan Uncle Auta take kwana, ita dai Jasminah bata ce mata kome ba, a can office din kuwa an gyara wurin girki da hall din cin abincin, sannan an hada duk wani abu me muhimmanci kama daga kayan abinci, zuwa sauransu. Tana aikinta tana tura mishi hotuna da bidiyo na abinda take, asalin karatun da Jasminah tayi zanen gidaje wato ita mazanina ce, ya jefota ne domin ta taya shi ganin kamfanin kuma cikin ikon Allah da yake ta san darajar ilminta sai gashi ta kara faɗin kamfanin har ta fara bada shawarar a bude sabon kamfanin wannan wurin sai ya zama wurin ajiye kayayyakin kamfanin da za ayi gwanjonsu, ya tambaye ta a cikin wata nawa zata iya aikin? Murmushi tayi ta ce mishi. Matukar akwai kudi a kasa ita bata ganin aikin zai haura wata uku. Jin haka ya gayawa su Mujitafa da Ubaid, tare da Alhaji suka ce sun bata goyan, aka kuwa zuba mata kudi, da mijin Uwarta Baffanta da Mijin Goggonta tare da cousin dinta, da sauran ma'aikata sai gani suka yi an fara aiki babu kama hannun Yaro, haka suka sha bakin ciki, suka kara kai ƙararta Alhaji ELYakub Kumo ya kore su, ita kanta aiki take kamar wata injin, Uwarta kuwa jin labarin kudin da aka zuba mata ta fara lallabata akan ta kwashe Abinda zata iya ta yi aikin ko oho, blocking Mamarta tayi bata da lokacinta, yanzu da take jin batun kudi shine zata dawo da ita jikinta. Daga masu aikin zuwa kan ita kanta mazaniyar basu zaune basu tsaye duk yadda aka so a mata barazana abin ya ci tura har bibiyarta aka fara yi ta gayawa dan uwanta, tow abinka da miskili bai ce mata kome ba, sai dai yana can sai gashi ya saka an kama waɗanda suke binta aka hada su da yan sanda, karshe shi kuma yasa aka karbo su ya saka aka musu kashedi, su kuma take mata baya.
Idan akwai kudi da karfin iko uban kowa ma zaka taka, ya nuna musu shi fa yana iya kome da kudinsa yana sarrafa kudinsa yayi yadda yake so, don haka duk abinda zasu zasu gana ba nasara. A wannan yanayin wata ranar lahadi Mrs Thomas ta fito church kuwa da motarta Allah yasa ita ɗaya ce, aka mata kiran gaggawa daga kamfanin a hanyar zuwa suka saka mota ta buge motar Matar nan, kai abin yayiwa Alhaji ELYakub ciwo yayi fada yayi fada. Kuma yayiwa duk wanda ya mata wannan abin Allah ya isa kuma ko waye asirinta ya tonu sai yayi shara'a da shi, Mrs Thomas tayi aiki da kamfanin tun zamanin Iyayen Turaki ita ba kamar sauran ma'aikata ba ne, kamar yar uwa suka dauke ta.. kasancewar tayi dogon suma wanda ake kira coma....... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 37 Tashin hankalin da aka shiga a family ba na wasa ba, shi yasa hatta abinda za a kashe KUMO FAMILY suka dauki nauyin abin. Wannan abin da ya faru bai saka Jasminah fasa abinda take ba ai an san suna tare da Mrs Thomas, Kuma anyi haka ne domin durkusar da aikin, kamar yadda Turaki ya gayawa Uncle Auta, kullum Jami'an tsaro suke kaita tare da saka idanu akanta, na biyu kuma aka biyar lafiyar abin hawanta, haka yasa kowa yake tsaye a kanta, babban abinda yasa aka yi haka domin gani ake ai idan da ita Jasmin ce da aikin ya dawo hannunsu, sannan kuma zasu yi yadda suke so amma aba a san waye yayi wannan aikin ba. Kamar yadda ta ce wata biyu a cikin wata biyu wanda yayi daidai da saukar daminar bana, wannan wata biyu da aka diba an samu ban iska idan a damina ne aikin ba zai yi ba, amma ganin yadda aka sha isa ba ruwa yasa ta yi aikin cikin nutsuwa, ba dai ga aiki ya fito fess, Alhaji Mudansir ya ce shi ba zai koma sabon building ba, ai kuwa ya samu sako ta email address dinsa da cewa ai dama building din ba na shi bane na CEO. Abin ya bashi mamaki haka ya kara kai ƙara Alhaji ELYakub Kumo yayi mishi fata-fata, amma wani abu da ya tsaya musu a rai yadda kowa ya sha jininsa. Bayan an gama aikin aka fara ƙoƙarin diban saba'in ma'aikata, a wannan lokacin manya mutane sun so lallai a debi yaransu, a wannan bangaren Uncle Auta shi yake da hakkin sabin ma'aikata. Wannan karon masu degree aka nima ba wasu kasa da diploma, haka yasa tsofin ma'aikata da aka same su da laifin rashin gaskiya aka sallame mu, musamman maza matan dama duk ba musulmai ne, a cikin wadanda aka kuma dakatar har da Badr Abbas Kumo, domin bata zuwa aiki kawai albashin take ciki, nan Uwarta tayi tsalle ta dirke bata yarda ba. Alhaji ELYakub kuwa yace ta gode da ba koranta aka yi ba, waɗanda basu da dogon laifi an bar su a tsoron ma'aikatan, wannan abin ya bawa kowa haushi wato sune yan iska zasu zauna a tsohon wuri aikuwa suka ce ba zasu yi aikin da shi ba, shi kuwa ya rubuta musu cewa duk wanda ya bar tsohon ma'aikatan ya bari kenan share dinsa za a rike bakiɗaya Saboda an same su da laifi dama. Jin zasu yi biyu babu yasa suka hakura. Hauka suke da zasu asara. An raba abubuwan sanarwar daukar ma'aikata ta ko ina babu kama hannun Yaro. *** Lubnah Gym kaɗai nake zuwa, bana zuwa ko ina sai zaman ya fara gundura na. Ina zaune a parlourn ni da Ummu da Princess ina daura lalle a yatsuna, shekaranjiya ya Ado ya dawo daga Bauchi akan jikin Abba, ya je dole ya ganshi kusan cutar saukar jini da tagayyara da mutum, haka yasa shi ya je har yana ganin ko za akawo shi nan lagos ne, sun dai ajiye maganar idan jikin yaki dole lagos za a kawo shi. Shine Mama da aka yi ta rokon arziki ta dawo dakinta, ki tayi sai da na saka baki na rarrashe ta, ta amince ta dawo. Duk da haka ana d'ago maganata zata takawa kowa burki ita fa mama na lura ta zama yar kunar bakin wake yanzu abu kaɗan zata tashi boom.
Da zai dawo ta haɗa mishi tsara har da madarar kuka da yake na gaya mata ina ciwon mara kwanaki, shine ta ce idan aka samu me zuwa zata bani madaran kuka. Kullum da safe ina shan cokali daya na hada ruwan dumi, ba lallai sai da na dumin ba, saboda yana wanke mara da maganin sanyi. Sai lalle da nake so saboda yatsuna, sai magarya, nomi ridi mai gishiri da yaji da mai, gyada mai gishiri, aya da suga na yara ne, ni dai kayan cina har da garin karago, haka dai aka turo min da acca da kome na irin namu masu gyaran jiki.
Aunty Zakiyah da safe madarar kukan ta haɗa min da fruit ta min shaka da shi, sai yar yau da tayi da kunun gy'ada wanda ta zuba alkama a ciki, sai da na sha shaka kafin na taɓa abincin, a cikin kayan Aunty Zakiyah na ga har da wani hadin daka da Mama ta turo mata, tunda na gana kunshe dariya na, ta zungure min goshi. "Munafunci kawai surukata ta aiko mun da kayan gyaran aure ne, bana son saka idanu?" Ban san me ya jefo tambayar kan harshe na ba nace mata. "Idan nima na samu nutsuwa irin taki haka Uwar mijina zata min hidima?" Juyawa tayi tana kallona cike da mamaki ta ce min. "Kina da saurayin ne?" Girgixa mata kai nayi da sauri ina rike bakina. "Da gaske kina da interest akan aure?" Ajiyar zuciya na sauke na ce mata. "A'a ni fa kawai yazo bakina ne, bawai don ina da ra'ayin yin auren ba ne, sannan wa nake da shi?" "Doctor Ahmad!" Kallonta nayi nace mata, "don Allah mu bar maganar nan Allah ya gani bana son shi, kuma ban tab'a daukar shi a matsayin wanda zan zauna da shi ba, asalima yaya na dauke shi, don Allah kada wani ya ji ya dauka ko na ajiyewa wani ne!" "Lubnah zo ki bani document dinki ga wani opportunity ya samu Allah yasa a dace!" Fitowa nayi na samu Ya Ado ya nutsu akan computer dinsa, ya d'ago kai yana faɗin. "Oya dauko min takardunki zan rubuta miku VC letter ana niman ma'aikata har da masu irin matakin karatunki." Haurawa sama nayi da gudu na gaji da zaman gida kusan for good 3 yrs, a yanzu fa ina ina gudu ni kaina sai naga ina burge kaina, ba da kamar wata bukka ba, amma a yanzu jikina a tsantsame. Wargaza wardrobe dina nayi na kwaso takardun na sauko da gudu na kawo mishi, sannan na tsaya a bayanshi ina ganin yadda ake cike vc din. "Wacce ma'aikata ce a ma'aikatan sufurin kudi ne?" (Wato ministry of financial) " Kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ne!" Wani yatsina fuska nayi ina faɗin. " Wannan ba zai wani abun arziki ba idan ba zaman shan shayi ba! Amma ai kudi yana aikin gwamnati!" " Ki cigaba da jiran aikin gwamnati idan a kasan nan ne kafin ki samu aiki da takardarki, babbar Yarki ta gama jami'a har da yara uku gare ta. Sai dai ko idan kina son koyarwa?" " Haba Ya Ado, aikin gwamnati bai da wuya kai da kake lauya fa! " Na fada ina tura baki. " Ai suma organization ce ta bude firm ɗinsu, ba gwamnati ba sannan baki ga su ma da kansu suna shara'a da gwamnatin ba, kudin da suke samu ana bayansu daga kudin da clients dinsu suke biya ne idan za ayi Shari'a, so su ba gwamnati ba ne, su masu zaman kansu ne!" Inji Aunty Zakiyah, ta kare Mijinta. "Ikon Allah, a gidan nan ne zaka yi magana da mata miji ya shigar mata kayi da miji matar ta shigar mishi. Ke ba aikin gwamnati kike ba?" Na tambaye ta ina tura baki. " Nima da farko wata kungiya ce ta dauke ni aikin wucin gadi daga baya kuma sai asibitin suka ga ana bukatar gurbina. Idan kuma zaki yi aikin goge goge da share share ai duk aikin gwamnati ne sai ki zo mu baki!" Tura baki nayi Princess ta kwashe da dariya wai. " Aunty Lulu idan kika yi haka sai ki yi kama da Moana, ki ga yadda kika yi da face ɗinki, ko Ummu?" Kallon iyayen nayi da suke ta min dariya, "Allah dai na gayawa Mama abinda kuke min!" Wayar Ya Ado ne yayi kara ya dauka yana magana a hankali, " ok bari na shirya booking Allah ya kawo ku lafiya!" " Lafiya Ya Ado!?? " " SAN lafiya? " " Daddy lafiya?" Duk lokaci guda muka mishi tambayar. Katse kiran yayi ya ce mana." Jikin Abba yaki za a kawo shi nan ne." Ya fada yana kallon laptop din, ai kuwa hankalina ya tashi take na nime walwalar da nake na rasa. " Shi da waye zasu zo?" Aunty Zakiyah ta jefa mishi tambayar. Tana kallona. "Shi da Tahir da Mama ta yadiko zata zauna, matar Sani bata da lafiya tayi bari." Ajiyar zuciya na sauke murmushi tayi ta ce min. "Zai tab'a samun damar zuwa inda kike ba har abada!" Hawaye ne ya cika min idanun. Na zauna jikina a mace, "je ki motsa jikinki, yar lukuta." Ba musu na wuce don tasan kuka zan yi, haka ya Ado ya ajiye aikin da yake ya koma nima musu jirgin Jos to lagos, bayan nan ya saka Aunty Zakiyah ta nima musu likita anan kuwa cikin ikon Allah wani abokin aikinta Dr Abraham Abati, shi ta samu ta gaya mishi ya ce mata ba damuwa Allah ka kawo su lafiya. Bayan sun gama waya sai ga kiran Aunty Hindatu ta ke ce mata.. "Maman Abbana, zamu zo muma amma sai zuwa weekend ki gayawa Mijinki na kira yana busy." "Wayyo Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, don Allah a zo mana da doya." " Amma matar nan baki da kirki a jirgi zamu zo fa! " " Ku saka a mota ya rigaku zuwa." "Ai kuwa kin kawo shawara me kyau bari na gayawa Raliyah a saka ta jos." Ai kuwa kamar yadda ta fada a group aunty Munah ta ce musu. " Ku tura mata dankalin turawa tunda mun fi kusa zan saka a mota idan zan zo!" Haka suka tsayar da magana, dakin da yake gefena na kara gyara musu, da inda Mama zata zauna a kasa don tace Allah ya kashe ta ba zata kara yarda da yaudareta ta zauna a sama ba, A lokacin muka mai da hankali a gyaran gidan, washi gari Ya Ado da safe yake gaya min cewa. "Na tura takardanki!" "Na gode!" "Naga kin fison aikin gwamnati ko?" "Eh mana ga fansho da garatuti, wannan fa idan haukarsu ta motsa zasu kore ka aiki!" "Daga nan sai mu ce miki korariya!" Inji Aunty Zakiyah"Ai duk abinda kike min sai na gayawa Mama ita ɗaya ta damu da lamirina!" " Gaskiya kan yar lukuta autar mu, SAN baka lura da wani abu ba, su fa yan auta kiba ce da su." Tura baki nayi nace mata. " Maganarki ba zai yi aiki akan wannan kyakkyawar matashiyar ba!" Na fada ina barin parlourn, ai sun san ba kibar sai dai idan suna son takura min sai su ce min yar lukuta. Shiga daki nayi na kalli kaina a madubi, wanda yake tsaye zalla. Ka juya ina kallon bayana, sannan na kalli gabana, ni dai kamar ba mace ba babu ya'yan gwaiba da za a gani ya ja hankalin kowa, wai tsaya me yasa nake tunanin jan hankalin wani ne? Na ga yan tsakanin nan sai batun wani ko aure, rintsa idanuna nayi sharrin makiya ko? Zasu sako ni a gaba, na kalli kaina a madubi na ce. " Ke Lubnah ki nutsu, idan baki manta ba kin sha wuta a hannun Hafiz!!" Daga haka na cigaba da shirmena a madubi, wayata ce tayi ƙara na ɗauka. " Ashe za a kawo Alhaji ba lafiya?" " Sorry Aunty Nuratu, mantawa nayi ban gaya miki ba, za a kawo shi gobe in sha Allah." " Allah ya kai mu, Allah ya bashi lafiya." " Amin Ya Allah!" Ta lashe wayar kuma fa naje Gym din ni na ma manta da wani kawo Abba sai da na dawo aka tashi zancen, kasancewar yau Laraba.