ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 24
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 24: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 24. Da dare muna parlourn Ya Ado ya ce min. " Ke bani e-mail ɗinki don na lura yadda kika tsani…
4,097 words
Da dare muna parlourn Ya Ado ya ce min. " Ke bani e-mail ɗinki don na lura yadda kika tsani aikin nan ko an turo miki ba zaki fada ba!" Lubabatushehuusmanjamare'a@gmail.com daga haka na cigaba da shan fruit dina. "Shima password din sai na roke ki?" Nifa aikin kamfanin nan sam bai min ba," ni wallahi aikin nan haushi yake bani! Lulu@19" na fada ina hura hanci, " don Allah dube ta yadda take hura hanci kamar wata sauro ke yanzu baki ji dad'i kin samu aiki a Lagos ba, kin zama big girl!" Kalaman Abba ne ya dawo min........ [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 38 " Idan karuwanci ne dubunki sun yi babu riba." Hadiye yawun bakina nayi da yayi min kauri yanzu haka Abba zai zo ba halin na je na ganshi ko na ji muryansa sai na ji lokaci guda tsoronsu ya kama ni daga shi har Ya Hafiz, wani irin masifaffen tsoronsu ya kama ni. "Lubnah!" Kallonsu nayi na mike a hankali zan wuce sama Ya Ado ya ce min. "Kina tsoro ko?" Tsayawa nayi ina mai da kwallar da ya cika min idanu ciki na ce mishi. "A'a kawai im wondering yadda zamu zan ga Abba ne!" "Kada ki damu zaki ganshi." Da sauri na koma sama, ranar dai saboda na saka tsoro da damuwa sai da nayi mafarkin, wai gashi nan Ya Hafiz zai tura shi a rami, amma na kasa zuwa cetonshi, karshe ina ji ina gani ya fada. Da wannan mummunar mafarkin na farka around 3am, ban daki na shiga nayi alwala na zo na gabatar da sallah Nafilla, ina zaune a wurin har aka kira sallah farko nayi raka'atu fijir, ina idarwa na cigaba da addu'a domin wannan lokacin yana da muhimmanci, karfe biyar da wani abu aka yi sallah asuba nima nayi, da na idar sai na ji na kasa fita motsa jiki, haka na kwanta saboda barcin da ya cika min idanu. Ban farka ba sai karfe daya na rana, ashe tun karfe goma su Mama suka iso, ganin kayanta nayi a kusa da ni ga kamshin turarenta na Touch me, da sauri na shiga ban daki nayi wanka na saka wata riga irin bubu din nan na sauko kasa, ba kowa a gidan, wayata na koma na dauko na shiga kitchen na hada abincin da zanci wanda ganye yafi yawa na zauna na fara ci a hankali, ina shan tea, a hankali ina kallon tv. Wayata na kunna, sannan na cigaba da kallon tv ina jin kamar wani abu yana damuna. Can na duba wayar na kira Mama. "Mama shi ne ko ki tashe ni?!" Murmushi tayi tana faɗin, "tow sannu ban tashe ki ba jinjiirata na ga kina barci ne kamar mage." Murmushi nayi na ce mata. "Kun iso lafiya ya Abba da jikin?" Bana gabanta amma yadda ta amsa min kamar irin she does care ta ce min. "Gashi can ana ta fama da shi." "Kamar ya?" "Tow ai yaki ya tsaya a duba shi dai fama ake yana tirjewa!" Idanuna ne suka cika da kwalla. "Allah sarki Abbana Ubangiji ya bashi lafiya." "Ke kashe wayar kada ki fara min kuka!" Haka na kashe wayar ina jin wani iri a raina, karfe shida na yamma ta dawo gidan ita da Ya Ado don Aunty ta dawo da wuri tayi abinci ta kai, naso na bita ta ce min. Na zauna saboda Yara. Tana kaiwa bata jima ba sai gata nan.
Tow dai gasu Mama ma sun dawo, Kallonsu nayi na tafi na rungume ta. "Mama ya Abba da jikin?" "Da sauki matsa min na je nayi isha,." Ta fada tana wucewa haka na bi bayanta ina faɗin. "Mama zasu min dariya!" "Yo ba sai na musu rashin mutunci ba!" Haka dai ta amsa min anan ta shiga ban daki tayi Alwala da wanka sannan ta fito ya sauya kaya na kawo mata abinci, tana idar da sallah ta fara cin abincin, ni kan gasashen kaza Ya Ado ya kawo mana, na fara ci ina kallonta. Tashi nayi tafi kitchen na hada Yorghurt fruit na dawo dakin ina sha. "Yanzu haka rayuwarki zata koma ba abinci mai taimakawa sai irin wannan?" "Mama kibar da ba aso zan yi!" Gyada kai tayi tana kallon yadda na ci kaɗan na namar sauran kuwa na barshi sai Yorghurt din na shanye, muka cigaba da hira.. "Lubnah!" Kallonta nayi don yadda ta kira sunan yasa na fahimci maganar ba na wasa ba ne. "Kin san yadda kome yake tafiya ko?" Gyada kai nayi ta cigaba da cewa. "Yanzu na ji Adamu yana cewa zai nima miki aiki babu wani ne da yake nimanki?" Wani irin tsoro ne ya lullube ni har nake ji kamar an lullube ni da danyen nama. " Ko har yanzu tsoron yana nan!" Bakina yana rawa na rufe shi, domin sai naji kamar xan yi amai ne, a hankali jikina ya ɗauki wani irin rawa. Ai kuwa da sauri na shiga ban daki sai da nayi aman abincin da na ci, na dawo na kishingida bata kara min magana ba, ta yi shiru da zancen ranar a wurinta na kwana. Washi gari Yaran gidan da gulma wai. " Aunty Lulu yau ta kwana a wuri Mamanta." Sosa kai nayi na ce musu. "Oh dai Mamana ce!" Haka na raka su har inda school ɗinsu yake, daga can kuma zasu wuce islamiyya don an sauya musu na yamma nan, idan suka dawo zamu yi karatun dare da su, har da home work.
Bayan na karya su Mama suna ta shirin tafiya Asibiti, Mama take gaya min ai tun asuban fari Ya Ado ya kaiwa Tahir abinci, ya dawo ya tafi aiki. Ina can ina baza kafasiti a wurin Uwata. Karfe goma Aunty Nuratu ta zo muka tafi asibitin da ita, daga waje na tsaya ina kallonshi da yake ta barci.. hawaye ne ya zubo min haka na koma na zauna ina kallon ina share hawayen da yake zubo min, fitowa suka yi a lokacin Ya Tahir ya iso yana min tsiya. "Who is this fine lady? Daga wata kasar take anya ba daga Somalia ba ce!" "Ya Tahir zaka fara ko?" "No na ga wata hadaddiyar baby doll ce, mai kalar Somalias." Murmushi nayi ya kai maganin sannan ya fito nan aka yi ta gaisawa da raha. "Kafaya kin ga yarinyar nan ko a hanya na hadu da ita dai dai na juya nace kamar na santa!" "Allah ya ganar da kai Attahiru." "Mama da dai kin ce Dahiru zai fi gane yana tsokanata!" "Mama don Allah kada ki biye mata!"? Haka muka yi ta hira, wurin karfe biyu sai gashi ya je ya sayo abinci, ni nawa kusan rabi ganye sai fried rice da grilled fish, sai soda drink. Ya ajiye min yana faɗin. "Nasan ba zaki hada kifi da madara ba, shi yasa na amso miki soda!" Da yake an kebe dakin mutum daya ne, kuma maganar gaskiya a can amenity muke akwai parlourn da family zasu zauna, kuma abin dad'i babu al'umma sosai a wurin haka yasa na sake naci abincin, wanda a lokacin ya lura da yadda nake cin ganye ya ce min. "Ganye yafi kara lafiya kenan?" "Eh shi shinkafar akwai starch a cikinsa, shi kuma yana bin jini ne!" Matsa lemon tsami nayi akan abincin da kuma kan kifin, "shi kuma na meye?" "Yana narka da kitse da maiko!" "Sodar fa?" "Ita tana hana ciki cika ya kumbura, ruwan da na fara sha shi zai hana ni cin abincin kamar yadda baa so!" Jinjina kai yake sai a lokacin Mama ta ce min. " Tow idan kika auri talaka fa?" Murmushi nayi nace mata, "Alayawu, kafi Egu, tafasa, bawon kabeji. Lemo da gwaiba ba arasa su a gidan talaka, rama da yakuwa duk suna da amfani zanci ai babu inda Allah baya kai mutum." "Yanzu bakya cin kome fa!" " Eh duk wani abu me starch bana sonshi, saboda akwai wata ƙwaya da nayi tasha bude tsoka take sai mutum ya bude kamar an hura shi, har da shi a karin kibar jikina." " Allah ya kyauta!" " Amin Ya Allah! " Daga haka muka cigaba da hira kar yamma sallah yake tashinmu, wurin karfe biyar sai ga Ya Ado da fruit da abincin dare, nan aka sake bude hira anan na ji sun ce ashe Rufa'i da su Aunty Hindatu da Aunty Innah zasu zo. Shi Ya Tahir zai koma, sai Ya Sani yazo. Idan Allah yana sonka da arziki sai ba ka ikon yiwa Yaranka hidima a kananun shekarunsu da zarar sun girma su biya wannan abin da ka yi musu. Wannan abinda ake kashewa babu kwandalar kowa Ya Ado ne yake a cikin aljuhunsa abu daya yace ba zai dauki nauyin kawo kowa ba. Su kuma da yake sun saka ransu zasu so suka ce ya huta, muna isowa gida na ga sakon River State ya iso doya ce manya manya. Kamar yadda nake zaton akwai wani abu da yake faruwa yadda na ga Ya ado da Ya Tahir tattaunawa, ban sani ba amma ko Mama basu bari ta sani ba. Da muka dawo ina kwance a dogon kujerar parlourn ina kallon wani yoroba film da yake zuwana nima na zama jikar oduduwa, ina son film dinsu musamman irin na kauye na zamanin baya, yana nuna yadda suke kare martabarsu da kimar kabilarsu. "Lulu!" Tashi nayi ina amsawa, "kin san wannan kwayar?" Kallonsa nayi kafin nace mishi. "A ina ka samu?" Gabana yana faduwa, "Kin san shi kenan?" "Eh!" Na fada idanuna yana kawo ruwa, ba dai shima Abba ya fada irin matsalar da nake ciki ba ne. "A ina kika san shi?" "A wurin Ya Hafiz!" Daga haka ya maida aljuhunsa, ni kuwa na fashe da kuka, bai gaya min kome ba. Amma na ji a raina akwai wani abu. "Ya Ado mai ke faruwa? Ka gaya min don Allah!" "Ba kome kawai bincike muke!" Duk yadda naso yayi magana yaki, "ki yi shiru kada Mama ta san me yake faruwa zan tafi Bauchi ranar Monday, idan na dawo dan miki bayani!" Haka ya Ado ya bar ni a dame.
Kamar yadda ya ce kuwa haka ce ta faru, ranar Monday ya wuce Bauchi. Sai dai zuwan shi Bauchi bai haifar da ɗa mai ido ba, domin anyi wani irin tashin hankali ne akan maganin Baban Jama'are ya ce shi ya kaiwa Abba yayinda yan uwanmu bakiɗaya aka zargi Ya Hafiz amma kiri-kiri mutumin nan ya wanke danshi, sannan suka ce ko da basu da arzikin Jirgin sama zasu zo su ga dan uwansa. Karshe haka Goggo Alti ta kashe case ɗin, amma don goyan bayan sun goyi bayan Hafiz har da cewa ai kafin suyi yunkurin kai Abba lagos waye yake kula da shi, Baba Malam tsohon munafuki har da cewa a gaya min na dawo dakina na daina yawon gantali da karuwanci. "In sha Allah Ubangiji ya ƙare Lubnah wannan fatar sai dai ka ganshi a cikin wasu jikokin da kafi so!" Inji Yadiko, kai anyi gurmi Goggo Alti ce kawai bata yi magana ba, tace ita bata ga laifin Yaran Baban Bauchi ba, da gaskiyarsu, haka suka bar zancen washi gari shi da su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka bar Bauchi har da Rufa'i aka tawo jos daga Jos suka hadu da Aunty Raliyah suka biyo jirgi, sai tsiya suke ta yiwa Rufa'i wai Allah ya kira shi lagos, amma yana da rabon zuwa lagos. Da yake shima akwai baki tuni ya kare kanshi.
*** Hafiz Ya razana yadda aka fahimci shi yake bawa Baban Bauchi magani tow meye dalilinsa? Amma haka suka bar zancen shi babban damuwarsa ya ga Lubnah in sha Allah duk ranar da ya ganta ko tana so ko bata so sai ya kwanta da ita, domin a yanzu da yake nan babu wata mace da take tare da shi, ko ya dauko maganar aure za a lalata mishi, ga Baban Jama'are da ya dawo Bauchi shima ya dawo shagon ɗan uwansa, hmm wani abu da Yaran Baban Bauchi basu sani ba shine ana ta murkushe kudin shago domin kuwa na karamin barna Hafiz yake yi ba. Wanda haka da Baban Bauchi ya d'ago ne yayi sanadin da Hafiz ya fara dirka mishi magani. (Wash hannuna 🤸🏼♀️😂🤣) [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 39
Ganin yadda lokaci guda asirinsa ya nime tonuwa ne Baban Jama'are ya saka shi a gaba da tambayar me ya faru, sanin cewa Babanshi yana tare da shi amma sai ya kasa faɗa mishi gaskiya ya ce musu. "Kawai don sun tsane ni ne, amma me nayi musu da zasu ji haushi bayan ni nake kula musu da mahaifinsu da suka yi watsa da shi, meye ban shi ba. Me kuma bana mishi kawai ban san me na musu suka tsane ni ba ne." Wannan magana sai yayi tasiri a ran Uban Hafiz ya cigaba da cewa. "Idan sun tsane ni saboda Lubnah har yau Lubnah matata ce tunda ba ni na sake ta, kuma ban amince da sakin ga har yanzu ina son Matata." Yadda yake maganar a dame yasa Uban shima ya shiga damuwa, ya tafi dakin da Baba Malam yake ya gaya mishi, nan dai suka kara kulla wata munafuncin zasu zo lagos su ga halin da Abban yake ciki su gaya mishi abinda Yaransa suke zargin Hafiz da shi.
Wannan kuwa ya yiwa Hafiz dad'i, wanda ya kai har cikin ransa yaso ya biyo su. Amma suka hana shi, da yake sun san al'amarin na kudi ne, basu fara zuwa da batun kudin jirgi ba, can bypass suka nufa anan suka biya kudin mota dubu sha bakwai daga Bauchi to lagos, sannan suka dawo idan bar aka samu fasinjoji zasu tafi, a Hajiya da ta ji labarin abinda ya faru bata yi kasa a gwiwa ta kira Malaminta ta gaya masa. Abin da ya gaya ya, ba karamin dadi ya mata ba, ta kuma ta ji a ranta idan har Lubnah zata dawo rayuwar d'anta bata ki tayi kome a kai ba, wannan abin ya saka ta kara tura kuɗi. Sai dai shima ai ya boye mata gaskiya ya barta da duhun zuciya. Bayan haka ita kanta tasan yaudarar kanta take amma da yake ta sauka akan hanyar da ya dace kyaleta kawai ta dace ayi ta ji a jikinta.
**** Lokacin da su Aunty Hindatu suka iso sai da suka fara biyawa asibiti kayansu aka kawo, ina kan injin motsa jiki nayi zufa shakaf kunnena ina sauraren karatun Alqur'ani, suka turo kofar. Zuba min idanun suka yi kasancewar na basu baya. A hankali Aunty Innah ta lallabo sai da ta zo kusa da ni na ji an tab'a ni, da sauri na juya ina ganinta ba fasa ihu, tare da rungume ta. Da sauri na koma wurin Aunty Munah da Aunty Raliyah, sai Aunty Hindatu da ita kan har da daukata. "Auta kece haka kika koma fine lady haka ashe da gaske Tahir yake da yace mana, wallahi kuka ga auta sai kin rantse ba ita ba ce, yarinyar nan ta kara kyau dole idan Hafiz ta ganta ya kusan mutuwa." Murmushi nayi ina kallonsu na shiga kitchen na dauko musu ruwa da kayan abinci. "Kun yi sallah ne?" "Omo ku ji yadda take magana kamar ba lulunmu ba!" Inji Aunty Munah, "kai Aunty Munah Hausar ma dabance da taku;" "kwarai da gaske baki ji yadda kike maganar a ganyance!" "Ni din nake yanga." "Wallahi Innah har da wani kalar shagwaba irin na Ajebo." Dariya suka bani na haura sama da gudu na sauya kayana, "Jama'a ku ga yadda take gudu kamar dama can ta saba da zuba gudu!" Inji Aunty Raliyah, murmushi Aunty Hindatu take tana mai share kwalla da yake shirin sauka mata. "Kamar ba yarinyar nan ba ce ta kusan haukacewa, yau ku ga yadda ta koma?" Hawaye ya zubo mata, duk sai suka koma tuno abinda ya faru.
Ni dai watsa rywa nayi na sauya kaya sannan na fito kafin nan sai da na kara auna tsawona, na ga dai na sauka ajiyar zuciya na sauke na sauko sanye da riga da zani na atamfa, ina zuwa na zauna a gefensu har mun fara hira na mike na hado fruit salad, na zo na zauna ina sha ina kallonsu, murmushi nake. "Yan mata babu bazawari ne?" Kwarewa nayi na fara tari Aunty Hindatu ta make Innah da tayi maganar. "Ke dai baki da girma sai na jikinki yaushe ta samu lafiyar da za'a fara maganar aure?" Inji Aunty Munah, "kyale ta mana Lulu take your time, duk abinda ya zo maka mai kyau ko mara kyau daga Allah ne, kada ki yi rushing a hankali Mijinki zai zo miki." Ji nayi fruit din ya hau min kai, na ajiye shi ina kallon tv. "Ya Abba da jikin?" "Da sauki tunda gashi nan yana gane kowa ." Murmushi nayi na ce musu. "Allah ya bashi lafiya yasa zakkar jiki ne." "Amin Ya Allah!" "Ya batun aikinki yaushe zaki fara?" Tura baki nayi nace mata. "Dukkanku aikin gwamnati kuke ya ado ya nima min aikin kamfanin ni wallahi tsoron aikin kamfani nake kada sai ka sake jiki a kore ka!" Murmushi Aunty Raliyah tayi tana kallon yadda nake magana. "Auta kin ga yadda kika yi kyau da maganar nan, asalin kin fito yan mata babu wnada zai yarda kin tab'a aure, like how you look beautiful and charming, auta gaya min me ye sirrin!" Rufe fuskana nayi ina dariya, " bude na ga beautiful lady din da take gabana, wallahi kamar na sace ki Yar nan! " "Innah dube ta fa, yadda kika san irin yan 23 uku nan koda yake yanzu wasu daga cikin sa'oinki suke aure dubi yadda ta samu natsuwa da kwanciyar hankali." Yanzu maganar Wasim da Aunty Nuratu Kafaya ya dawo min daga lokacin da kike tsaya da kafarki a lokacin kowa zai soki." Murmushi nayi haka suka ci abinci, sannan suka shiga ciki suka yi wanka da hutawa la'asar tana yi muka shirya bakiɗaya zuwa Asibitin, tunda Rufa'i ya ganni ya rike baki. " Adamu yarinyar nan sakata kuka yi a injin amma? Ke Lubnah gaya min wanke ki aka yi a injin ko?" Dama can na san halins sai haka bai wani dame ni ba, haka muka yi ta hira na leka Abba yana barci. " Shi barci kullum yake yi ne?" Murmushi tayi tana faɗin. " Eh yana farkawa har ya ci abinci ma, tow jininsa da yake yawan sauka ake son a iya sarrafa shi." "Allah ya bashi lafiya!" Kuka sai na fara kuka idan har wani abu ya sami Abba bai saka min albarka a rayuwata ba, ba zan yi kyakyawar karshe ba. Kukan da nake yi ne ya dami Mama ta ja hannuna muka fita. Kusan yadda abin ya tashi hankalina. "Tow meye na kuka?" "Mama idan Abba bai yafe min ba, rayuwata zata lalace domin ina jin a raina ni ce sanadin wannan ciwon nashi." Kura min idanun tayi tana jin wani irin abu a ranta. "Wani ya zarge ki da cewa ke ce sillar ciwonsa ne?" Cikin shashekar kuka na bude baki xan yi magana tura min kwakwa tayi a bakina. "Ya isa haka, ba ke ce sanadin ciwonsa ba haka kuma ba zaki tab'a zama sanadin wani ba, ina da yakinin cewa Ubangiji ya amsa min addu'ata akanki, don haka ki daina kuka akan abinda baki da ikon sawa ko hanawa, kada ki manta Mamanki tana tare da ke a kodayaushe, kofata a bude take." Haka tauna kwakwan da nake ya hana ni kuka, Mama tana sona sama da baya Mama tana kokarin bada har Rayuwarta domin ni.. "shekaranjiya nayi mafarkin wani kyakkyawan bafulatani ya dauke min ke." Ta fada tana murmushi, kallonta nayi sai kuma na tura baki nace mata."Mama dauke ni fa!" "Eh amma na gaya mishi idan ya saka ki kuka ba xan yarda ba, idan ya saka ki damuwa ba xan yarda ba, idan ya sake wani abu ya same ki ba zan yarda ba, domin na hango shi cikin kuraye da macizai ne, sai dai ina ji a jikina shi jarumi ne domin shi ɗaya rike da sanda ya rike hannunki har wani kyakkyawar gida, kin ga kenan idan ba jarumi ba, babu wanda zai iya ratsa waɗannan halittun ya wuce lafiya lau. Da haka nake jin a jikina Ubangiji ya amshi addu'ata ya kuma ajiye ta zuwa lokacin da zai biya min ita." Yake nayi mata domin naga Mama ita fa tayi nisa a kaina,Aqur'an bata jin kira. A hankali ta riko hannuna ta zaunar da ni a kujeran da yake gaban wata office. "Kin san yadda nake son ki yi farin ciki kuwa? Kaf duniya babu wanda ya kai ni son ki yi farin ciki, sai dai abu daya zan gaya miki daga yau kada ki kara zama wani ya wulakanta ki, kada ki kuma cutar da kanki saboda zaa ce kina yawon aure kada ki damu ban kuma ce ki rena duk wanda zai zo rayuwarki da sunan aure ba, amma kuma kada ki rena kanki." Kwantar da kaina anyi a kafadar Mama ina jin wani irin nutsuwa na shiga ita uwa duniya ce ga Yaranta, baya ga ita kanta tana bukatar kowa a tare da ita. Uwa ita take manta da kanta tayiwa danta addu'a. Mama she is amazing mother of me, ta gwammace ta rayu da ni akan aurenta. Mika min goran ruwa tayi wanda ta ciro a jakarta tana faɗin. "Gashi sha na san kina shan ruwa dama da kome!" Amsa nayi na sha domin bakin a bude yaƙe.. "Mama kina ganin na karbi aikin da Ya Ado ya nima min ni nafi son aikin gwamnati ne!" Zungure min goshi tayi tana faɗin. "Waye yasan gobe ban da Allah idan kika yi hakuri kafin ki dauki lokaci sai Allah ya sauya miki da abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a duk wata rayuwa tana bukatar addu'a, ita Addu'a mukulin dukkan wata Alkhairi ne da toshe duk wata sharri." "Mamana, in sha Allah."
"Wai Mama nan kuka zo kuka zauna kun manta da da wasu a cikin." Inji Aunty Raliyah, ta ce mata. "Raliyah bana son gulma taya zaki biyo Uwa da Autartar!" "Allah ya baku hakuri ya kuma bamu hakuri ." Dariya na saka muka wuce cikin asibitin mika cigaba da hira, har na manta abinda ya faru. Kusan mutane da suke zuwa ganin Abba abokan aikin ya Ado ne, kwanakin su Aunty Hindatu biyar suka juya zuwa gida, nayi kewarsu sosai. Itama Mama tana cika sati biyu ta koma Bauchi aka kawo Yadiko, zuwan Mama ban tab'a shiga wurin Abba ba, amma yadiko tana zuwa ta saka ni a gaba har inda yake zaune suna magana da Rufa'i, yana ganina ya dauke kai, haka na koma bayan Yadiko na tsaya ta ce min.. "fito ke ai shi ya samar dake idan ya isa sai ya gayawa Allah baya kaunarki sai na san inda zan ajiye lamarin,." Abinda na lura Abba ya ɗan yi sanyi. Haka dai tayi ta surutu koda na gaishe bai amsa ba, ban kara ba. Ina zaune har Ya Ado ya zo yana zuwa na bishi muka bar asibitin. Ashe bayan fitata yake cewa Yadiko. "Yaushe Yarinyar nan tayi kyan gani haka?" "Lokacin da kaso kashe ta Allah bai nufa ba, lokacin da ka ji gara ta mutu da ta cigaba da amsa sunarka. Lokacin da ka ji a ranka baka kaunar ganinta har kake mata fatar karuwa. Allah Alhaji ka ji tsoron Allah ka ji tsoron wanda ya mika lamarinsa ga Allah dubi Yarinyar nan yadda ta koma kamar yar tsanar zinari." Jin haka yasa yayi shiru, da Yadiko take gayawa Ya Ado ya sha mamaki, da ya sauko kamar bashi ba, yana kuma iya gaya mishi yadda yake ji, babban matsalar da yake fama da shi shine rashin barci wanda shi yake haifar mishi da ciwon kai mai tsanani karshe jininsa yayi kasa. Haka yasa aka kara rike shi, basu san me yake damunsa ba, amma idan har akwai wani abu da yake damunsa bai wuce yadda Lubnah taki komawa gidan mijinta ba.
--- A Lagos din kuwa Baban Jama'are ne fa Baba Malam suke ta yawo a garin Lagos basu dan inda Ya Ado sun kashe kudin hannunsa, gashi an sace wayar Baban Jama'are, wanda da ita yake kiran Hafiz Baba Malam kuwa yaki bada wayarshi domin kanshi kamar zai juye da suka shigo lagos sun zata kamar Bauchi ne da bata da girma haka. Haka yasa suka yi ta yawo daga nan zuwa can daga can zuwa nan duk sun galabaita kusan sati biyu, haka yasa suka fara bara, suna samun abinci da zasu ci.