Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 25

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 25

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 25: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 25. *** *Russia* Moscow Zaune yake gaban laptop hannunsa daya yana tallafe da fuskarshi. Idanunsa…

4,156 words

*** *Russia* Moscow Zaune yake gaban laptop hannunsa daya yana tallafe da fuskarshi. Idanunsa yana kan files da aka turo musu yana bin sunayen kowani mutum a hankali idanunsa ya sauka akan Lubabatu Usman Umar Jama'are, jikinshi ne yayi wani iri-iri amsawa yummmmmmm......... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 40 A nutse yake kallon dan hoton passport da yake jikin CV din, a hankali yake bin information dinta, wani irin abu ne ya ji ya tsaya mishi a rai, lokacin da yaga wurin marital status, sai ya tsinci kanshi da kashe laptop din, yana mai jin wani abu a ransa, amma a fusakarshi bai nuna yadda abin ya dake shi ba, wata zuciya ce ta ce mishi. "Ba ita ba ce wata ce daban!" Wani bangare na zuciyar ta sake ce mishi. "Ina ga ita ce ba wata ba ce." Zare medical glass din idanunsa yayi ya ɗan saka yatsu biyu a tsakanin idanunsa yana dan taɓa tare da musu massage, mikewa yayi tare da mika sai da kasusuwanshi suka amsa sannan ya kalli hadadden dakinsa, da yake can yamma da cikin gidan, bude kofar yayi yaji yanayin gidan ya sauya daga sanyin da ya koro shi dazun, yana da wani irin lalura da baya son sanyi sam, dumin da gidan ya dauka ya bashi damar fitowa, sanye yake da trouser brown na kamfanin Adidas, sai rigar shirt din jikinsa na kamfanin polo, kafarshi kuwa sanye yake da safa baki, a duniya abu daya yake gudu sanyi. Infact yana da allergy da sanyi idan ya cika yawa yana iya samun attack na mura mai tsanani, shi yasa a tsarin rayuwarsa tunda ya fahimci baya son sanyi ya haramtawa kanshi shan kankara ko wani abu me sanyi tun yana Yaro har zuwa yau da ya girma. Yadda gidan ya dauki dumi yasan mutane biyu ne zasu kula da yanayin domin har yau kallon Baby boy suke mishi. A hankali yake takawa duk da kasancewar shi lafiyayye mai kuzari amma idan lokacin sanyi yazo haka komawa yake kamar kazar da ruwa ta mishi duka, a hankali ya dauko daga stair din da ya sada shi da parlourn, da aka wura wuta a irin gidajen turawa. "Bilyl!" Wata dattijuwar baturiya ta kira shi, "Na'am Granny!" "Ka fito?" Murmushi yayi mata sannan ya isa gaban dinner table ya dauki kofi ya zuba ruwa ya dauka ya sha. "Na zata ka ayi barci ne?" Wuce ta yayi ya zauna a daya daga cikin kujerun parlourn da alfarma. Juyawa fararen idanunsa yayi a kanta, ba zaka ce ya kai shekaru arba'in da wani abu ba, asalima yanzu yake jin kanshi. Dai irin yanayinsa na rashin son magana da hayaniya yasa tayi shiru. Yadda ya kalleta nan tasan ya gaji da magana ne. "Kai dai baka da halin wannan idan shi mace zata gani ta soka tow ba zaka tab'a aure ba sai dai ka mutu a tuzuru." Wata karamar murmushi yayi wanda ya fitar da asalin yanayinsa na shi ba Bature ba shi ba kuma bafulatani ba, ya mai da kansa ya daura a jikin kujeran. Turo kofar da yake cikin parlourn aka yi ya juya wata mata ce ba zata huce irin sittin da wani abu ba, amma saboda yadda jikinta ya samu kulawa zaka ɗauka irin yar talatin din nan ne. Sai ka nutsu zaka fahimci ai da wuce shekarunta. "Turaki!" Ita ɗaya ce take iya kiran sunan shi kai tsaye kamar yadda yan Nigeria suke kiran sunan. Shiru yayi bai amsa mata ba sai zuba mata idanu da yayi yana kallonta. "Am sorry, amma ai na gaya maka ba yadda xan yi da Mandy!" Tabe baki yayi yana cigaba da kallon tv yadda ake shirin bikin Christmas ya kalli kakar da kyau, itama kallon Yarta take tana mata magana da idanu. "Amma kinsan ba zaki iya rike ta ba me yasa kika dawo da ita Herlim." "Amma Mama kin san dai ba zan barwa William Yata ba ko? Mutumin da bai da aiki sai safara da damfara!" " "Ya isa haka Please!" Ya fada yana dafe kanshi, ya fito waje ya sha iska na so yake a kara mishi wanda ya gani a laptop ba, turo kofar gidan aka yi wata matashiyar budurwa da ba zata wuce ashirin da uku ba, ta shigo tana marisa. Tashi yayi ya wuce kitchen daura tukunya yayi akan gas tare da zuba traditional Herb, ya juya ya kalli yarinyar tana ta marisa da surutu irin na wanda ya sha ya bugu. Shigowa wani matashi da kayanta yana zuwa ya gaishe su sannan ya ajiye ya gaida Turaki ya ajiye key. "Mandy me yasa bakya jin magana ne?" "Mom taya zanji maganarshi bayan ya ce baya sona, cewa yayi baya sona zuciyarshi ya bawa wata can da bata san darajarshi ba, Mom ina son Bil!" Ta kama shakuwa, rikota Uwar tayi zuwa dakinta ko kafin su isa ban daki ta kwara amai a dakin zuwa ban dakin ban da kirnin giya ba abinda yake tashi. Tana maganar uwar ya shiga wanke mata, sannan ta zube a gadon barci ya dauke ta, a lokacin ya gama dafa kayan ya zuba a kofi sannan ya mikawa kakar ya ce mata. "Granny!" Yadda ya kira sunanta a kausashe kafin ya fadi abinda yake ranshi ta ce mishi. "Ka kusan komawa gida ko?" Yadda tayi magana sai ya kashe mishi jiki. Amma kuma yasan Datti yayi hakuri da rashinsa, Daddah tayi hakuri da rashinsa idan ya cigaba da zama baya jin yayiwa mutane biyun nan adalci. "Zasu so ka kamar ni kuwa? Ina sonka idan na kalle ka iyayenka nake tunawa da su." Wato drama a cikin tsohuwar nan Allah kaɗai ya san yawansa, tasan abinda zai iya hana shi komawa shine ta fara kirkiro drama domin ita har yau bata yarda mutuwar Mahaifiyarshi ta Allah ce ta faru da ita tafi yarda da cewa kashe ta aka yi, kuma babban abin zarginta Hajiya Zeenatu.. A hankali ta fara girgiza kai ta sake kofin ruwan da yake hannunta ya fashe tare da watsuwa a jikinta. " A'a Bilyl kashe zasu yi, ka zauna anan. " Karar fashewar abin yasa Herlim ta fito tana kallonsu. " Meye kuma? " Da sauri ta zo ta rike hannunta. " Herlim ki ji wai zai tafi Nigeria, bayan kashe shi zasu yi." Murmushi tayi ta ce mata.." Mama shima fa akwai wnada suke buƙatarshi! " "Ai dole ki fadi haka tunda bakya kaunar fadar da yake yiwa Mandy." " A'a Mama kada mu yi haka dake Turaki yana da tashi rayuwar kin turke shi wuri guda, akan me? Gaskiya ya kamata ya tafi idan ya samu sarari ya zo ya ganmu!" Ai kuwa nan ta fashe da kuka ta wuce dakinta ta fara kiran number Sarah wacce take Germany tunda ya zauna a can." Hello Sarah kin ji wai zasu tura Bilyl Nigeria yadda suka kashe Anna haka zasu kashe min shi." Murmushi tayi ta ce mata. "Mama aiki da ya bari ya zo nan da zama ki barshi ya tafi Please Mama shima can suna buƙatarshi Bulal ba yaro ba ne, da za a ce lallai sai ya zauna Bulal yana bukatar iyalin yana bukatar rayuwa akan me zaki rike shi? Wannan son Kai ne!" Da yake tana son Yaranta Kuma tana jin maganarsu sai ta ce mata." Shi kenan amma sai after bikin Christmas zai tafi!" "Tow duk yadda kika ce amma ki sani shi fa CEO ne guda fa." Ta fada mata haka, sai kuma tayi shiru ta fara rarrashin mahaifiyar tasu. A can parlourn kuwa kallonshi Herlim tayi tana girgiza kai ta ce mishi. " Ce mata kayi zaka tafi?" Shiru yayi kafin ya ce mata. " Eh! " Ya cika da cin apple din da yake kan table din. "Kai baka iya lallabata ba ne sai ka na gaya mata magana gatsu?" Kallonta yayi kafin yaa dauke kai idan ya ce zai yi magana maybe itama ya cabb'a mata mara daɗi, kwanciya yayi abinsa bai kara ce mata cikanki ba, ita tayi ta masifa kafin ta ce mishi. "Nasan kana son ka kome amma maganar gaskiya Mama tana tsoron kada wani abu ya same ka ne kamar Annah!" "Sannan ka ga kai ko auren baka yi ba?" "Wannan ba reason ba ne!" Ya furta a hankali, yana cigaba da lumshe idanunshi. Shi fa bai ga dalilin da zai saka a cigaba da rike shi domin hatta kayansa yana dakin Granny amma ace bai da yancin motsi mai ƙarfi, idan yana son ya fita sai ta tsare shi da tambayoyi kamar wata jami'ar tsaro. Yana daukar haka ne a matsayin soyayyar da take yiwa Mahaifiyarshi shine duk kome ya dawo kanshi. Tabe baki yayi yana jin kamar ya tattara ya bar kasar, amma yadda yaji tana kuka dazun sai yaji kome ya fita kanshi. "Ok ki ce mata na fasa!" Ajiyar zuciya Herlim ta sauke ta wuce dakin mahaifiyarsu ta sameta tana shafa hoton mahaifiyar Turaki da sauran kannensa da suka rasu, zama a gefenta Herlim tayi ya ce mata. "Mama yace ya fasa tafiya!" "Zai tafi na ji haka a jikina zai tafi lokacin tafiyarshi ce tayi idan ba haka ba wata rana zai tafi ban sani ba!" "Amma dai shi yace ya fasa tafiya." "Shekarun baya da ya tafi kin sani ne? A yanzu ma da yace ya fasa zai tafi adalcin da zan mishi kenan ya tafi suma dangin mahaifinsa suna buƙatarshi. Idan nace yayi ta zama da ni yaushe zai tafi? Idan nace ya zauna nayi mishi adalci ne? Hmmm baki san wani abu ba, a ranshi yaji zai tafi gara na barshi ya tafi ba mamaki wata ƙaddaran ce ya kira shi, amma bana jin zan iya samun nutsuwa idan baya nan, amma haka zan sakawa raina hakuri da dangana, shi namiji ne yana bukatar rayuwa." Yadda take magana a sanyayye zai tabbatar maka da ita kanta tana son yaki da kanta ne, turawa suna da mugun son Yara, don har sun fi Larabawa kaunar Yara, ita har yau ganin shi take kamar dan karamin Yaron nan, ganin dan karamin yaro tana tuna lokacin da ya rasa Mahaifiyarshi, yadda ya zauna silent na tsawon kwanaki uku baya ko magana da kowa, lokacin da yaji labarin tunda baya kasar a lokacin, ta girdɗslmama shirunsa, take kuma girmama duk lokacin da zai yi magana to a wurinsa mai muhimmanci ne. Domin a lokacin da ya ji labarin mutuwar fushi yayi yaki zuwa ga babansa, duk da Baban yana zuwa amma shi ya yanke kafarshi da kasar, koda ya rasu lokacin ya gama karatunsa na farko, cewa yayi ai dama yasan main target ɗinsu kenan, domin da suka kashe Mamarshi sun san ba zasu samu kome ba, tun tun daga lokacin Granny ta rike a ranta kashe mata ya da suruki aka yi kuma idan har lissafinta daidai ne Turaki shine next target ɗinsu, Granny babu church din da bata je ba domin rokon abin bautarta ya amintar da soul din jikanta ya nisanta shi da duk wata masifa da fitina, sai gashi ya kara dawowa da wutar son da ya rasa, anan yan mata yadda suke mutuwar sonshi amma shi sam basa gabanshi, shekarun baya ita wannan kwailar dai ita ce yake mata kallon apple of him eyes, baya jin zai kuma kaunar wata mace bayan ita, Granny ta sani idan tana son su yi dogon hira tana ce mishi Labubu shi kenan, zata iya catch attention dinsa da duk wani abu da take so tana kiran Labubu, akwai ranar da ta ce mishi me yasa yake son under age, ai karya hakki ne da cutarwa, ya ce mata. "Granny me yasa Yaranku suke bin maza duk wanda yace yana sonsu zasu bashi kansu, me yasa?" Sai ta yi shiru. "Da zinar wuri gara auren wuri! Gara a mata auren da wannan shekarun ta kara samun tarbiyyar Mijinta sama da ta samu tarbiyyar mazan waje." "Kai dai akan Labubu baka ji baka gani!" Murmushi yayi ya ce mata. "Luna ita din wata yanki ce ta rayuwata amma wani ya tafi da ita!" ........... Wash [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 41 ............. Washi gari. Kusan rayuwar Turaki a gida yake yinta, domin tunda ya bar aiki da babban Cibiyar nukiliya ta Germany, ya koma zaman gida ba wai bai da abin yi ba ne, asalima abinda ya tara na wancan aikin bai yin kome da ita, amma yana da wata shago da yake sayar da coffee tun kafin ya dawo rasha da zama, domin a love story din Iyayensa a coffee shop suka hadu haka yasa ya tashi da son bude shagon, idan har zaka ganshi a shagon to kuwa abu me muhimmanci yake kawo shi shagon, sannan shagon yana dauke da baki bakaken fata, wanda ya dauke su aiki, shagon coffee din yana rage mishi abubuwa dayawa, musamman idan ya tuna da yadda ya rasa abinda yake so kawai saboda yanayinsa, a gefen shagon akwai gym da ake yi duk na shi ne. A halin yanzu yana da shaguna manya sosai a cikin Moscow, sai dai idan ka kalle shi zaka iya hango murmushi a kan fuskarsa amma a cikin ransa ba murmushi ba ne, kawai yanayinsa ne haka, duk da kasancewa shi haf Nigeria, yana da wata dabi'a duk inda dan Nigeria yake ya kuma samu wata matsala kafin ka ga wani a wurin turaki ya riga kowa zuwa wurin, ya dibi dalibai maza da mata both Muslim da Christian, domin kuwa abinda ya yarda da shi duk wanda ya zo nan daga gidansu yake ba daga ko ina ba, ya yarda Duk wani dan Nigeria danginsa ne. Sai dai wani lokaci da aka yi wani case na damfara da fashi wani Imyamuri a lokacin ya cire inyamurai a cikin mutanen da yake tallafa wa domin gayen yaso cilla shi cikin matsala, amma bincike irin na kasar suka samu bai da alaka da Yaron. Rayuwarshi babu girman kai, sai dai akwai abinda yayi imani da shi, tsoron mutum duk yadda yake da mutane yana tsoron sharrinsu, sannan idan ka ganshi da matasa tow labarin cigaba ne. A yanzu haka a mutanen da ya diba a nan rasha yan Nigeria ne da zasu yi aiki da shi kuma ya gaya musu gaskiya da albashin da zai basu, dayawa sun yarda domin ita kanta kasar babu wani ma'aikatan gwamnati da basu kuka da ita, gara su yi aiki da kamfaninsa. Rayuwarshi a matsayinsa na wanda ya taso cikin maraici ya saka abubuwa a ransa, ya kuma hakura da abubuwa dayawa don idan ya ce kudi ne ko karfi zai nuna soyayyar da yake kulafuci ba zai samu ba. Shi yasa ya yarda da abinda zuciyarshi take gaya mishi duk abinda ya nima Allah yana bashi sai dai ita da ya nima tace bata buƙatarshi me ya kawo ta kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY? Wannan shine tambayar da suke ta birkita mishi lissafi tun da ya ga sunanta kuma ya kasa yin wani abin arziki, idan kana son mutum kome na rayuwarshi sakawa kake a duniyarka, me yasa ya kasa daina sonta? Me yasa ya kasa ganin laifinta? Saboda ta fito fili ta gaya masa abinda yake ranta da abinda ya ta yanke a ranta. Gaskiyarta da kwarin gwiwarta a lokacin ya hango, ba zai ce ko ta tab'a kallonshi a tsanake amma kuma yaji a ransa tunda ta iya siffanta shi da almajirai ta kalle shi koda kuwa sau daya ne, a hankali ya bude idanunsa da suka yi wani luhu-luhu, ya kafa akan agogon parlourn, karfe uku saura na dare tashi yayi ya nufi dakinsa, koda ya shiga sallah Nafilla yayi sannan ya zauna ya cigaba da addu'a yayi addu'ar idan har Alkhairi ne ya kawo ta kamfanin Allah ya tabbatar idan kuma wani abu ne ya kawo ta Allah ya sa ta bar kamfanin da kafarta ba tare da wani abu ya cutar da ita ba, har kusan asuba, sai da yayi Sallah asuba sannan ya kwanta. Barci ne me nauyi ya dauke shi, amma duk da haka cikin barcin mafarkinta ne wanda tun na wancan fuskar yarinta. Yadda ya ganta ya sa shi farkawa dole ya shiga ban daki yayi wanka, ya kuma fito ya haɗa coffee da kanshi, yau kan ma an tashi da niki-nikin sanyi domin ta ko ina ƙanƙara ne ke sauka. Bai da yawan cin abinci kasancewar nasu na turawa amma a Nigeria yana son abincin Daddah. Dakin ya shiga ya ji gunjin wayarshi tana niman taimako a dauke ta, jan kujeran da yake aiki yayi ya zauna har wayar ta yanke a karo na biyu, yana kallonta ta kara yankewa a karo na uku ne ya ɗauka. "Hmm!" "Amma kana Ina nayi ta kira baka dauka ba?" Kurban tea din yayi ya ce mishi. "Ina kallon wayar!" Shiru Uncle Auta yayi kafin ya danna mishi Ash'aria, murmushi yayi kafin ya ce mishi. "Me kake yi da cv din har yau baka turo an ga wadanda suka yi qualified ba?"

Shiru yayi kamar bai da ta cewa har Uncle Auta ya kara fusata. "Dan iska mai zubin yan daudu ina magana kana min yanga." "Da kaina zan musu interviews!" "Da gaske? Zaka zo kenan?" "Ina tunanin haka." "Baffa ya sani ne?" Shiru yayi yana kallon coffee din ya ce mishi. "No zasu ta jirana, i don't like su ta jirana." Murmushi Uncle Auta yayi yana faɗin. "Akwai abinda zai dawo da kai ne?" Shiru yayi yana zoben azurfan hannunsa ya sake wata karamar murmushi ya ce mishi. "Uncle akwai abinda kake gudun na gani ne idan na zo?" "Kai tafi can uban me zan boye maka!" Anan ya shiga bashi labarin yadda suka yi fa Granny, sannan ya sake murmushi yana kallon dakin yana son dakin, ya ajiye dakin nan a matsayin dakin da zai fara honeymoon idan har Allah ya bashi damar yin aure. Can ya ce . "Uncle Auta, a mutanen da ka diba aiki har da, manta kawai." Shiru Uncle Auta yayi kafin ya ce mishi. " Kana nufin akwai wani abu ne?" Daha kasar zuciyarshi ya furta wata kalma da ya kusan saka shi jin kunya. "Uncle idan na dawo na hadu da ita fa?" Sai kuma ya ce . " Ba haka nake nufi ba!" " Har yanzu baka hakura da Lubabatu ne? Anya ba aljana ba ce kuwa ka hadu da ita?" Tsaki yayi ya share zancen ya ce mishi." Batun ghost worker's?" "Ba shi nake magana na Turaki magana nake akan har yanzu!" Kashe wayar yayi, sake kiranshi Uncle Auta yayi yaki ɗauka, y kira yafi sau goma amma bai dauka ba, bayan wani lokaci Datti ya kira dauka yayi ya saka a kunnensa. "Mujitafa ya ce zaka zo haka ne?" Shiru yayi ya fara kame-kame, "wato" "ban sanka da magana biyu ba, kuma ya ce kai zaka yiwa sabin ma'aikata interviews tabbas muna bukatar kazo don Allah, kazo don Allah muna buƙatarka!" Wani irin shiru yayi yana sauke numfashi.

***

Daga Bauchi aka yi ta kiran Ya Ado, da cewa ai su Baban Jama'are da Baba Malam sun zo lagos, amma ba a kuma jin labarinsu ba, wannan abin bai yiwa kowa dad'i ba. A wurina cewa nayi Allah yasa su fada hannun yan yankan kai, domin idan sun zo babu alkhairi a zuwan nasu, haka akayi ya bin office din Yan sanda ana niman, dama kuma akwai wata hukumar da gwamnatin lagos ta ware na musamman idan aka kama mabarata ana tara su sannan a saka su a babbar mota ya kawo su arewa, Goggo Alti ce ta d'agawa Rufa'i da Ya ado hankali akan Babansu mara mutuncin tsoho, ni ko a jikina. Haka ayi ta nimansu har inda ake tara mabarata a can aka same su sun sha uban azaba ba uwar azaba ba. Haka aka kai Baba Malam asibiti shima saboda muran da ta kama shi, Baban Jama'are kan da sauki sai kin yar kunyar da take damunsa ya kasa sake jiki da kowa, gidan wani abokin Ya Ado can ya kai su da yake akwai BQ, anan suka zauna don kwanan Baba Malam daya aka sallame shi. Haka suka daurawa kowa dawainiyya da jigila, idan suka zo asibiti dakyar suke komawa masaukina. Yadiko kuwa ta wanke Baban Jama'are da cewa.. "Ba fa dole aka ce sai kun zo ba, fisabiilillahi kun zo kuna daurawa mutane dawainiyya, yaji da na iyalinsa ko yaji da na mahaifinsa, wannan ba yi bane" Tunda tayi magana sai suka dauke kafa da zuwa asibiti irin sun yi zuciyar nan. Ranar wata juma'a muka tawo gaida Abba, da sauki ma dai ya amsa min sama-sama, sai dai wani abu da ya dake ni zuwan Doctor Ahmad da kayan dubayya, yadda yake ta kallona da jana da hira, amma naki sakewa da shi, duk abinda yake faruwa a kan idanun Abba, da yake mun zo bayan an sauko juma'a shima Ahmad ya shigo, wurin karfe hudu sai gasu Baban Jama'are, ko basu gane ni bane, da suka shigo suka gaida Baba da jiki nida su Adil muka gaishe su, sai sake Baba Malam yayi yana faɗin." Wannan ba luba ba ce?" " Ita ce Baba wani abu ne?" " Ita ce dai da gaske?" Ganin yadda suke ta mamakin ganina sai Yadiko ta ce min. " Zo ki kai wannan abin waje ki zubar ki ta addu'a ido guba ne." Haka na fita jiki a mace. Rufa'i da Ya Ado suka shigo lokacin na fita kenan muka hadu a hanya. " Ya ka mai damu gida!" "Ok! " Yana shiga ya ga su Baban Jama'are, nan ya sha jinin jikinsa. Haka na zubar tare da dawowa dakin. " Akan me zata koma? Ita tace muku zata ko?" Inji Yadiko,Gabana ne ya fadi lokacin da na shiga ina jin maganar da take a hasale. "Yadiko ai Abba ya sallama min Lubnah kaf duniya babu me iko da ita sama da ni, idan shi Hafiz din jahili ne ai ni ba jahili ba ne, aure fa babu shi ko ina zasu sai su je, ke muje gida ga wannan idan ya muku zaku iya tafiya idan kun ga bai muku ba, ku cigaba da xama amma ba gidan Abokina ba domin ina jin kunyar shi."

Fashewa da kuka Baba Malam yayi yana fadawa Abba ai yana gani amma ya kasa magana. "Yadiko ki taya yarki da addu'a nan fa sati biyu zasu tafi jarabawa, zata fara aiki." addu'a sosai tayi sannan muka bar Asibitin, ashe basu tafi ba kuma Rufa'i yayi musu bayani da inda zasu je su hau motar Yola amma suka ki, karshe a masallacin asibitin suka kwana. Duk yadda suka so ganina don su kunna min wuta Allah ya taimakawa Ya Ado ya hanani kara zuwa asibitin wannan abin ya dame su, suka yi ta kunnawa Abba magana da tashin hankalin da sai da jininsa ya sauka har ya fara alamar zai suma, aka kore su. Wannan abin ba wai iya su kaɗai ya shafa ba domin Baba Malam ya kira mutanen Jama'are ya gaya musu.

---- Kusan tun da muka rabu da Ya Hafiz ban kara jin shi ba, ina zaune yau Lahadi, aka kira ni dauka nayi, na saka a kunnena.. "Kina nufin don kin zo lagos kin kin sabe wannan tsutsar jikin naki, zai saka na manta da cewa ke Matata ce? Ki ji da kyau ke Matata ce ni Hafiz Umar Jama'are ban sake ki ba, ki gama haukarki ina nan ina jiranki. " Ji nayi kai na ya sara, na kasa amsa mishi wani tsawa ya daka min sai da naji kamar guduma ya buga ya kara buga min tsada idanuna jajur ga wani tsoron da ya cika min rai na ce mishi. "Meye nayi maka ne?" Aikuwa ya shiga zagina da cin mutuncina da zarafina yana gaya min matuƙar ban je na ga Baban Jama'are ba sai ya bani mamaki ya kara da cewa.. "Zan miki abinda kaf duniya babu wanda zai yarda ni nayi miki, nafi ki sanin Lagos idan ban saka an dauko min ke nayi yadda nake so da ke ba shege nake..... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 42 *Traumatic yana da alaka da abinda ya samu mutum na tsawon lokaci ko kuma na tun daga Yarantar mutum ba wai ina son nunawa mutane cewa Lubnah bata da yadda zata yi ba ne, akan Hafiz Lubnah bata da karfin da zata iya karban kanta ba wai ta gaza ba ne, ko yaro ne aka fuskaci domestic violence haka zai taso a kangare na taɓa jin wani karatun malamin addinin Muslunci da Yaron ya turawa malamin cewa saboda abinda Babansu yake yiwa Uwarsa yake jin kamar ya kashe shi. Na ga a wani blog na Garkuwar Arewa da wata yarinyar ta turo cewa saboda wannan domestic violence ta kasa bawa duk wani d'a namiji, ba ita aka yiwa ba mahaifiyarta Ubanta yake cutarwa amma tana ganin idan ta hadu da namiji irin Ubanta ne! I don't mean to push Lubnah amma akwai irin masu halin da take ciki! Please be patient with the story Nagode sosai*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull