ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 26
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 26: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 26. Mikewa nayi na ji kamar cikina ya tsarga. Ya cigaba da gaya min duk maganar da ta fito…
4,494 words
Mikewa nayi na ji kamar cikina ya tsarga. Ya cigaba da gaya min duk maganar da ta fito bakinsa, ji nayi kamar ana kunce min duk wani abu da yake kaina ya ce min, "kina son Iyayenki kuwa? Shi kenan sai ki tuna kamar yadda rayuwarmu take baya yadda kowa yayi shiru akanki yanzu ma bata sauya ba, ki gane mana ina sonki, i a son ganin kukanki na ga kina kuka yana min dad'i sannan idan kika sake wani ya min magana akanki hmmmm abinda zai fi haka muni, don haka ki zuba idanun zuwa na sannan ki gayawa Adamu ya kula min da mahaifina." Wurgi nayi da wayar na koma can kuryar dakin na zauna Kamar marainiya, ko kara wayar tayi sai na zabura, wani irin tsoro ya kama ni. Haka na wuni a dakin har dare ban fita ba, sallah ne kaɗai nayi dakyar, ba sai ga zazzaɓi ya rufe ni ba, kwanciya nayi a dakin har Ya Ado da Aunty Zakiyah suka zo duba ni ban gaya musu ba. Wayata da take can a yashe Aunty Zakiyah ta dauka tana kallon Ya Ado, duba wayar tayi tana faɗin.. "Lafiya wayarki a can!" Da sauri na amshi wayar na kashe, na koma na kwanta. Kusan haka suka gama maganarsu suka fita, kwana biyu wayata a kashe idan Mama ko Aunty Hindatu zata yi magana da ni sai dai a wayar Ya Ado ko Aunty Zakiyah, nan Mama ta sha jinin jikinta, ta cewa Ya Ado ya amshi wayata ya bincika, itama zata taya ni da addu'a, Ya Ado ya amshi wayata ya kuma saka ni a gaba da fada har sai da Aunty Zakiyah ta ce ya kyale ni ya daina min faɗa, kafin na samu ya hakura washi gari sai gashi yazo yana rarrashina, sannan ban san me yayi ba. Sai ya ce min. "Daya layin na turawa su Mama wannan Mtn din ba a iya kiranki ba sai dai idan kece zaki kira, sannan wannan ko Rufa'i ban yarda ki bashi ba, idan Hafiz ya kira ki, ki gaya min ki bude baki ki gaya min." A Bauchi kuwa Mama sai da ta saka aka rufe shagunan da Ya Hafiz yake, duk yadda aka kai da bata hakuri fir taki, shi kuwa kamar zai yi hauka. Da ta gaya mishi zata iya kome akan Lubabatu bai yarda ba, sai da ta saka aka dauke shi a kai aka kai shi office din Yan sanda aka rubuta yarjejeniyar ya fita a harkata tunda abin ya koma yar haka, bata kyale shi ba sai da ta ce ua kyale su Sani su kula da shagon Abba, domin ba ƙaramin mamaki suka sha ba jin yadda kusan tun kafin a kwantar da Abba ba a kuma zuwa sari ba, kayan da yake store ya kare tass, ina kudin? Sai shiru karshe da aka kira shi ya zo, ai kuwa ya gudu aka nemi shi sama da kasa babu shi, babu labarinsa. Abin bai yiwa kowa dad'i ba, sannan kudaden da Abban yake da su ba zasu kai ayi sabon sari ba, haka yasa dole aka fara hada abinda ya sawwaka, aka gayawa Mama tace musu. "Ina ruwana yana da gidaje da filaye ku sayar ai bance ya dauko na shi ya cuce shi ba, balle ace a tare zamu raba zunubi ba." Fir Mama taki ta kuma gayawa Yadiko.
*** Turaki.
Duk yadda yaso kaucewa dawowa haka yayi ta ji zuciyarsa na fisgarshi, duk da yana ƙaryata kanshi da cewa zai dawo ne ba wai don ya ganta ba, asalima don kada a samu matsala zai saka a tura ta tsohon kamfani. Amma kuma da wata bangare na zuciyarshi ya tuna mishi cewa akwai Khamis akan mata ko taure ya sallama mishi, sai ya ji ranshi ya ɓaci, yanzu idan yayi wani abu za iya d'agota, duk da file dinta ya shigo ta email address kamfanin ne, ba ta hannun Uncle Auta ba, duk yadda yaso ya kaucewa haka amma zuciyarsa ƙara tunzura shi take, sai dai duk yadda ta tunzura shi idan ya tuna tana da aure sai jikinshi ya kara sanyi, wani hanzari ba gudu ba, idan kuma mijinta ya mara hanyar samun aikin fa? "Tsuk!" Ya sake wata guntuwar tsaki yana kallon waje, ta parlourn.. "Bilyl" kallon Granny yayi tasha rigan sanyi. Murmushi yana kad'a kafarshi. "Bilyl ko baka da lafiya ne?" Kallonta yayi irin kallon mamakin nan, zama tayi tana kara bude mishi kalmar rashin lafiya da take nufi. "Ina nufin ko baka da karfin maza ne!" Bai cika dariya haka ba, sai dai idan ya ga abu ya wuce lissfinsa, a hankali ya sake wata dariya yana kallon tv a hankali, ya ce mata. "Granny me ya kawo wannan zancen?" Yana shafa kai, kallon kanshi yayi a nutse yana kuma lissafin bayaninta wato haka ake kallonshi a mara lafiya. Murmushi yayi ya zuba mata idanun kafin ya juya ga wajen da yake kallo. "Naga bayan labubu baka sake kula wata mace ba!" Shafa sajensa yayi yana jinjina kai. "Granny yau fa alhamis ina azumin Alhamis da Litinin, yana kare mutum daga sharrin zina da wasu abubuwan, ni lafiya ta lau, kawai matan ne basu gabana." "Tow ko kai gay ne?" Zare idanu yayi ya kuma tuntsirewa da dariya yana kallonta, tsakaninta da Allah take magana ta cigaba da cewa. "Saboda haka nayi maka booking ganin likita da zai taimaka maka yadda zaka fara jin sha'awar mace." Mikewa yayi yana faɗin. "A'a ni lafiyata lau, ba sai kin hada ni da aiki ba!" Ai kuwa tsohuwar nan tayi ta masifa tana binsa ya zo su tafi asibiti amma yaki karshe shiryawa yayi ya bar gidan ma, duk da sanyin da ake yi kuwa.
Yana isa coffee shop dinsa sai ga kiran Ubaid. Dauka yayi suka fara magana akan kayan da Uba bank suka kawo musu talla, ya ce mishi "Ubaid ku biya da kudin hannunku man." Ya fada yana kallon wasu masoya da suka shigo shagon.. "Sau nawa zan gaya maka babu kudin nan da kake magana wallahi wannan watan sai da aka tab'a kudinka sannan aka biya albashi, ka fahimci abinda nake nufi, muna ta sayan kaya amma ba halin mu wayar domin ko mun zo sayarwa za a samu babu wasu abubuwan, ka ga a wulakance ake sayarwa sannan kafin su bada kudin ya xama aiki!" Cike da mamaki yake jin wannan labarin. "Ubaid me yasa baka tab'a gaya min ba?" Ya fada ranshi a b'ace, yana kin zafi sosai. "Duk lokacin da na maka magana zaka ga kamar ina son lallai ka dawo ne, wanda ni bs nufina kenan!" Shiru yayi yana jin kamar ya dirka ta wayar, ba a tab'a rena mishi hankali irin na yau. Duk yadda Ubaid yake mishi bayani ya fahimta yaki cewa uffan har ya gama maganar shi ta kyale shi karshe ya lashe wayar. Haka ya fara shirin tattara duk wani abu na shi mai muhimmanci, bayan ya gama ya zubawa wayar idanu yana jin wani irin ciwo, tow me yasa suddenly ya sauya ra'ayinsa? Ba zai maganar Lubnah ba ne ta rinjayi sauran? Idan har haka ne tow ya ji kunya, babba ma kuwa. Karshe sai ya watsar da Maganar komawa Nigeria da gaggawa, ya tattara ya watsar kamar ma bai da niyya ne ko ya fasa ma bakiɗaya, haka kwanaki suka wuce, babu labarin shirin tafiya Alhaji ELYakub Kumo da yaji shiru ai kuwa ya kira shi nan ma ya fara inda-inda karshe shima dattijon ya sha zuciya ya ce ya kyale shi yayi yadda yake so, tantance ma'aikata babu bashi nan da wasu kwanaki. Abin ya bashi mamaki yadda kakan na shi yayi fushi, kuma ya hana kowa kula shi, ai saboda ya ga an damu da shine, don haka sai abin ya dame shi, duk yadda yaso ya dauke kai sai ya kasa duk waɗanda suke kiranshi yake kin dauka ko yake saka musu busy yau babu ko daya da ya sake kiranshi, duk da baya tare da su amma yana jin dadi da farin cikin kiran da suke mishi haka yana nufin basu manta da shi ba, sannan abu na gaba shima Alhaji ELYakub yayi haka ne don ya nuna mishi ko dashi a rayuwarsu ko baya cikin rayuwarsu zasu rayu ba shi bane yake basu abinda suke bukata. Kuma ya gane karatun domin da kanshi yayi ta kiransu amma babu wnada ya dauka sai ma busy da suke saka mishi, tuni sai hankalinsa yayi wani irin tashi, shi kamar kwai yake bai saba da horo ba, bai ma san horo a rayuwarsa ba, haka yasa shi cikin kasa da sati daya ya tashi hankalinsa domin a lissafinsa Alhajin ne bai da lafiya suka boye mishi, nan kuwa bulala suke mishi ta hanyar da shima yake yiwa wasu.
Ranar juma'a jirgin maxi airline ya sauka a International airport na lagos wato Murtala Muhammad International airport, da misalin karfe tara na dare, kai tsaye ya dauki drop domin shi bai gaya musu dai zo ba, wannan muguwar dabi'ar nashi ya saba da ita baya fadar yana hanya kuma baya fadar zai bar garin idan har kasan ranar da yazo kawai ya rike domin ba zaka tab'a sanin ranar tafiyarsa, wurin sha daya na dare suka isa gidansa da yake Lekki, ya biya mai motar da ya dauka drop, sannan ya isa bakin gate din yayi magana da mai kula da gidan, a hankali ya fito ya haska masa torch da sauri ya kashe yana faɗin.. "Ka gafarce ni Sir;" ya bashi hanya ya shiga, haka ya shiga ya nufi cikin gidan shi kuma ya daukar mishi kayansa. Har cikin gidan ya shiga gidan nan kamar yadda kullum ake kula da shi. "Kada ka gaya musu nazo!" "Ok sir;" ya wuce upstairs ya wuce dakinsa, sai da ya karkade sannan ya gyara da kyau kafin ya samu wuri ya kwanta ya huta, sannan ya shiga ban daki yayi wanka da alola. Kafin ya fito ya gabatar da sallah Magariba da Isha, hada socket yayi na kettle ya dafa ruwan zafi ya shan coffee, ba tare da ya kara niman wani abu ba, ya bi lafiyar gado. Sai lokacin yaji wani irin nutsuwa da kewa irin na abokin tarayya,idan da yana da mata da ya dawo nan kawai zata tarbe shi Yaranshi suna ta murna, Papa ya dawo amma yau ba ko sauro da yasan da zuwansa abin ya dame shi ainun a yanzu ko da Lubnah ko babu ita ya shirya zama da mace koda baya sonta, amma ban da wadancan yaran family dinsu shi bai da ra'ayin auren family...... (Ku min hakuri bana jin dadi ne) [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 43 Akidarsa kenan, ra'ayinsa kenan bai da wani ra'ayi na auren zumunci.Sun kasa boye yunwarsu da zallamarsu, shi kuma ɗan ra'ayine duk yadda kake tsammanin zaka burge shi baya taɓa ganin haka a wata tsiya. Washi gari ya fita Masallaci, yayi Sallah kuma ya dawo da wuri, can dakin Gym dinsa ya shiga yayi ta motsa jiki har karfe takwas saura, sannan ya wuce kitchen dinsa, shi fa Allah ya gani yana adawa da duk wani abinda zai saka ya ji yunwa, kallon maka makan deep freezer da suke kitchen din yayi, ya bude ya ga ba kome asalima a kashe suke, shiru yayi kafin ya fito parlour ya zauna tare da cire wayarshi a charge domin yana dawowa sallah asuba ya saka anan,nan ya cire a Flight mode da ya saka, ai kuwa sai ga kiran Granny. "Bilyl ka iso lafiya?" "Eh granny wani abu ne?" "Dama na amso maka magani ne likita ya ce yana da kyau da karfi kamar doki!" " Granny ba na gaya miki lafiya ta lau ba?" Cikin rarrashi da tattali ta ce mishi. "Ai haka ne dayawa haka suke cewa lafiyarsu lau, amma idan aka bincika basu da lafiya." Takaici kamar ya fasa ihu a hankali ya ce mata. "Kada ki sake a kawo min maganin nan domin zubar da shi zan yi na gaya miki." Shiru tayi kafin ta ce mishi.. "Shi kenan, da fatan ka karya ko?" "Granny ni fa ba yaro bane!" "Haka ne kan amma ai tunda baka yi aure ba har yau yaro nake kallonka." Sanin zata saka shi magana da zai haifar mishi da ciwon kai, ya ce mata. "Granny bari na sauke noodle yana kan wuta zai fara kamawa!" Ya kashe wayar yana kallon screen din, murmushi yayi yana faɗin. "Granny kece matsalata!" Sannan ya wuce kan sofa ya zauna, yana mai janyo laptop ya fara aiki a hankali. Resume kan file dinta yayi yana kallo a hankali ya isa kan maritial, ya ga babu wani information haka ya wuce ya ga first class ta fito, dauke kai yayi yana zukar iskar bakinsa sannan ya cigaba da duba wasu bayanin, abin mamaki shine taba nimam 29 yrs ta hada degree da master a wannan yan shekarunta, tribe ya duba ya ga an saka hausa/fulani, hararan file din yayi a ranshi yana faɗin. *Hausa Hausa Fulani Fulani, no wani hausa fulani idan na renin hankali ba* a can ya duba ko tana da Yara, aka saka babu, tabe baki yayi yana ainawa a ransa da cewa.*Waye ya sani ko ta tara dozen na yara!* Ya fada fuskarshi tana wani irin ja, irin na kishin nan, bakin ciki ne ya saka shi kashe laptop din ma bakiɗaya, waye ya sani ko Yaranta har da budurwa, tsaki yayi a fili. "Mtseew!" Kamar wani tsaka, can kuma yayi kwafa irin wanda takaici ya kusan kurmushe shi. Dakyar ya kai zuciya nesa ya cigaba da aikinsa, kusan ita ce mutum na sittin da yayi select dinta, sauran kuma ya ture su domin tun daga can yake daukar waɗanda suka dace.
Yana gamawa ya turawa Uncle Auta cewa ya gama s tura mishi wanda suka diba, ba dadewa kuwa ya turo mishi mutane talatin a bangarenshi, haka yayiwa Ubaid magana ko minti goma ba ayi ba ya turo mishi mutane sha tara, da ta dauka bakiɗaya mutane dari da yan kai, daga nan ya tura musu yadda zasu raba mutane ranar interviews din. Sannan da kuma yadda zasu duba su. Sannan ya ce musu a tura musu sakon yau yadda zasu shirya akan lokaci. Haka ya tura musu yadda ya tsara, kowane su zai dauki ya 27 har da Jasminah. A ranar suka gama tsara kome. Yadda yake basu hit yasa Uncle Auta ya kira shi yana cewa. "Kai don ubanka yaushe ka shigo?" "Ni kuma?" Ya rena mishi hankali, sanin cewa bai gaya musu zai shigo ba, sai kuma ya saka a ransa cewa. "Kawai ina zargin kamar ka shigo ne." Murmushi yayi ya ce mishi. "Na zata ka shigo ne!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ka cika zargi!" Daga haka ya shashatar da zancen, suka cigaba da abinda ya tara su. Domin daga karshe conference call suka yi. Kusan wunin ranar aikin da suka yi kenan, tunda aka kawo mishi abinci mai gadinsa ya amsa ya kawo mishi, ya ci ya bar sauran. Can ya kara odar na dare. Kusan sallah yake d'aga shi a wurin bayan ya gama ya wuce ya tafi unguwa. Bai dauki mota ba, sai dai taxi d ya dauka haya, ya tafi kamfanin lokacin an tashi ya shiga dakyar suka bari ya shiga shima sai da ya bada cin hanci, bai nuna musu waye shi ba ya shiga yana kallon yadda ma'aikatan yake, daga nan ya wuce tsohon side, daga can ya hango office din MD Khamis ya bude asalima kamar akwai wani a cikinsa, haka yasa shi isa har kofar office din abinda ake zargi ya gani da idanunsa, daya daga cikin ma'aikatan ce take kuka, da rokon ya barta da mutuncinta sannan ya duba tana da ciki dakyar suka samu cikin kada wani abu ya same cikin rayuwarsu zata shiga garari, amma Khamis ya shafawa idanunsa toka ya daka mata tsawa, tura office din yayi yana faɗin. "Taso ki tafi!" Ta cire hular kanshi na face cap din da ya saka ya riƙe. Kunya ne ya kama shi, "thank you sir!" Murmushi yayi ya ce mata. "Ki dauki maternity leave mana idan cikin yayi kwari sai ki dawo, yana da kyau hakan!" Cikin wani irin girmama ta ce mishi. "Zan dauka sir!" Bata san waye shi ba, amma a yadda ya bata umarni, kuma Oga Khamis bai magana ba, haka ya tabbatar mata da shi wani ne, juyawa yayi ya rakata har bakin gate din, sannan ya nufi new side dinsu, ya gama kallon wurin da kyau, kafin ya wuce ya fita. Koda ya isa gidan da abinci ya isa, ya haura parlourn sama ya baje.
Next day ya kar shiryawa ya tafi ma'aikatan, ya samu suka bar shi ya shiga yasan Khamis ba zai tab'a bada labarin ya dawo ba ko don a tambaye shi yaushe? A ina ya ganshi? Haka ya gama zaga kamfanin har ya hadu da masu sata a kamfanin, haka ya dawo gidan ya rubuta, kome zuwa uku yayiwa kamfanin. Khamis kuwa tattarawa yayi ya gudu Abuja, don yasan idan har suka sake ido hudu da shaidani Turaki tow sai dai ya bar kamfanin. Shi yasa ya gudu kafin su sake haduwa.
*** Yau kwanaki hudu kenan da aka ce mu je interviews, Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata har da su Aunty Hindatu, aka yi ta murna a Bauchi Mama kan har da sadaka tayi, domin gani take kamar na amshi kaddarata ne, amma har yau na kasa nutsuwa zuciyata tana wani irin tsalle a duk lokacin da na tuna da Ya Hafiz yana nan sai na ji bakiɗaya kome ya rikice min, Ya Ado ya haɗa ni da Dr Dijah Bala, ta min yan tambayoyi na bata amsa, ta ce mishi yayi hakuri abin yana barin mutum ne a hankali, amma da zaran wani abu da ya shafi past dina ya dawo tow zai cigaba da hunt ɗina, Haka Aunty Nuratu Kafaya ta gaya masa, kusan sati aka saka a zuwa interview din, haka yasa Ya Ado ne ya kai ni kasuwa muka sayi kayan da zanyi amfani da shi, kuma yana da yakinin Allah zai bani sa'a, ranar ashirin da watan June aka saka zamu. Yau sha bakwai ina kwance da yamma a parlour kasance Asabar ne, Rufa'i ya shigo da sallama, tashi nayi na zauna ina kallonshi yayi dariya yana faɗin.. "Manya Lubnah ki amince na kawo dubu goma a daura mana aure, ni bani da matsala xan amince ki ta juya ni kamar masa." Murmushi nayi na ce mishi. "Kai dan Yaro da kai ne zan amince na aure amma ka mugun rena min hankali." "Samun kyakkyawar saurayi irina sai an cika form, Gara na miki talla kafin mata su kwace miki ni." Haushi ya kama ni na kalle shi na yi kwafa, Aunty Zakiyah ta fito tana mana dariya sai zoyalat suke karshe na biye musu aka wuce wurin, haka ya zauna har Ya ado ya dawo ya amshi abinda ya zo amsa ya koma, ranar Lahadi kuwa jin wani irin tsoro ya kama ni nake, ban taba zuwa irin wuri haka ba, nayi su goge karamin fashion hijab din da zan daura akan kayan, sai takalmana da na kara goge shi, sannan na koma na zauna ina ta azkar, domin zuciyata ta gama razana, lokacin da na ga kamfanin da Ya ado ya nuna min, da kuma aikinsu, sannan ya gaya min wani abu.." kada ki rena kanki, idan kika yi haka ma'aikata zasu yi bullied dinki, please ki tsaya akanki kada ki bada fuskar da za a wulakanta mana ke, ki yarda da kanki."
Daga haka na ji a raina zan yi kome don na wanke Ya ado, ruwan sama aka fara kamar da bakin ƙwarya, bayan na ci abinci na kwanta sannan na kara nazarin takardun da zan tafi da su, kafin na hada kome a wani jaka. Washi gari tun asuba Ya Ado ya buga min kofar dakin ya bani wayarshi. Addu'a mama take min kamar ta aro kafa ta biyo wayar, tayi min Addu'ar nasara da sa'a tare da dace, haka na amsa da Amin, bayan mun gama wayar na shiga wanka na hada da Alwala, sannan na yi sallah na shirya tsaf, karfe bakwai saura muka bar gidan tare da Ya Ado da Aunty Zakiyah, ita ta sauka a can asibiti ni kuma Ya Ado ya kawo ni inda ma'aikatan take.
Ikorodu Local Government.
Anan kamfanin yake, kafin mu wuce ya ce min.. "idan kika fito daga kamfanin idan kin samu abin hawa zasu kawo ki can inda mutane suka tsaya sunan wurin Garaj kenan, daga nan zaki samu mota zuwa gida kin ji ko?" Gyada mishi kai nayi ya dunkule hannunshi yace Goodluck! Murmushi nayi ya kawo ni har kofar kamfanin ya ajiye ni, ya fito zuwa bayan motar ya mika min lema da rigar ruwa nace mishi. " Ya Ado wannan ma ya isa." Ciro dubu goma yayi ya ce min. " Ki rike wannan! " Murmushi nayi na ce mishi. " Allah ya kara budi. " Har ya juya zai tafi ya dawo ya ɗan janyo ni jikinshi.." ki kula kada ki bari a rena min ke kin ji ko? " Gyada kai nayi, yayi murmushi sannan ya wuce ya shiga motarshi sai da ya tafi na shiga kamfanin, ana ta taruwa, ina shiga na ga matasa ire-irena, ina zuwa wurin na musu sallama babu wanda ya amsa min, kame kaina nayi na koma gefe, domin daga dukkan alamu duk masu zuwa interview ne, har wurin karfe takwas motocin alfarma suka fara shigowa kamfani, gabana ne ya fadi sosai, haka wasu fararen mutane suka fito, ni dai ban tab'a ganin irinsu ba, haka suke fitowa tare da tafiya cikin kamfanin kamar zasu tashi sama, kowa ka gani sanye yake da coat irin na aikin nan black kusan shigar mu ce da su, wurin karfe goma saura wata mota ta shigo kamfanin wanda yayi daidai da fara kiran sunayen mutane, Yara ne guda biyu suka fito, daya tana cin abu a cikin kwali, tana ta zaga wurin. Kiran wasu mutanen aka yi a lokacin na lura bamu wuce ashirin da wani abu ba, haka muka cigaba da zama, har karfe sha biyu ba rana sai ga wata mota ta shigo, a lokacin Yaran nan sun zo kusa da ni suna wasa, masu kula da Yaran suna ta tare tare da su, ban san ya aka yi ba sai ganin daya daga cikin yara biyun ta tsaya........ [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 44
Cak idanunta kawai yake motsawa, a daidai lokacin da aka kira sunana kenan, yadda yarinyar ta tsaya zaka zata ko wasa take tana kallon mutane amma ni nasan ba haka ba ne, saboda ya tab'a faruwa da Yasir ya saka abu a bakinsa sai da na rungume shi ta baya na matse mishi cikinsa abin ya fado da amai. Da gudu nayi watsi da takarduna, na nufi yarinyar da kowa ya kama gabanshi tana niman faduwa, na rungume ta ta baya na shiga matse cikinta tare da buga bayan da kaina sau biyu nayi mata na ukun sai ga amai da kwallon abin ya fado, zubewa muka yi dukkan mu, domin ta suma ne, da sauri na kara gyara mata kwanciya a jikina masu kula da su, suka shiga ihu, "ban ruwa!" Ka fada musu, mika min suka yi na kunsa a bakina na watsa mata sau uku sai gashi ta fara ajiyar zuciya. Nima ajiyar zuciyar nake saukewa, na tashi duk kayana yayi kura, ashe labarin abinda ya faru har an isar ciki, tallafo yarinyar nayi na zauna da ita a kujeran da na tashi. "Sannu daga yau kada ki kara cin abu a tsaye, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce yana daga kyauwun dan uwanku ya ci abu cikin nutsuwa, haka zai kiyayye daga sharrin shaidan da sauran abokan halitta, idan zaki ci abu ki daina zuwa gaban jama'a kin ji, ki samu can gefe guda ki ci, mutane ba kowa bane normal wani yana da evil eyes, evil tongue, da bad mouth. Kada ki sake tsaya a gaban mutane kin ji." Gyada min kai tayi na mike tare da kallon masu kula da su. "Iyayen Yaran nan sun yarda da ku, suka baku amanarsu, sannan sun amince da nagartakun suka bar Yaransu a wurinku, ku kula da aikinku kowacce addini da kabila ta yarda da gaskiya da rikon amana, please ku taya su kula da Yaransu. Allah ya bamu sa'a." Lokacin da na juya na ga bakiɗaya mutanen da suka fito sun koma ciki abinsu, ajiyar zuciya na sauke na tattara takarduna, sannan na nufi ciki don sai yanzu na tuna da an kira ni fa, ina shiga cikin hall din naga wasu daga cikin staff din sai kallona suke irin kallon wulakancin nan, kofofi uku ne, kuma dukkansu an rubuta interview, wurin matan na isa na ce musu. " Don Allah a wacce kofa aka kira sunana? " Ina ga wannan ba wani abu ba ne da na fada da zafi, amma daya daga cikin matar ta ce min. " Kin ajiye mu ne mu ji ko an kira sunanki?" Kalaman Ya ado ya dawo min na kada na bari a wulakanta ni, kuma kada na wulakanta kowa, murmushi nayi nace mata. " Sorry! " Daga nan na wuce na zauna har wurin karfe biyu bakiɗaya suka fito mazan suka tafi sallah wasu daga cikin wadanda suka zo interviews din suma sun fito, haka nima na fita nayi sallah, ashe sun rigani dawowa, ina zuwa kuma suka fito wai ashe an yi ta kiran sunana, bana nan. Sai nayi kamar na kunyata Ya Ado ne, haka na tattara kayana wani mutum ya ce min. "Mrs Jama'are!" Wani irin kwallar farin ciki ne ya cika min idanu, na juya ya ce min.." ana kiranki! " Gyada kai nayi na bi bayansa, wani hadadden office ne, muka bi stair aka kai ni, kusan tattaunawa ake suke suna faɗin " a cikin mutane dari da wani abu bakiɗaya mutane sha bakwai ne suka tsallake!" "Sha takwas dai Uncle Auta, sha takwai kamar ya?" Shigowar da nayi yasa suka zuba min idanu, murmushi Macen cikinsu tayi duk da bata kai su shekaru ba, amma da alamar suna ji da ita ga Yaranta s gefe, d'aga min hannu daya wacce na taimaka yayi na mata murmushi. "Mom ita ce ta ceto rayuwata!" Mikewa uwar tayi ta mika min hannu. "Na gode da abinda kika yi, yau kamfani tana alfahari da ke da kuma irin wannan ceto ran da kika yi, min gode." Gyada kai nayi ban iya amsawa ba. "Me yasa kika yi missing interview din?" Wani can na gefenta ya tambaye ni, cikin girmamawa na ce mishi. "Na farko na tsaya ceton Rayuwarta ne, saboda yar adam ce kuma hakki ne a kaina na tsaya na taimaka mata, na biyu idan da na tafi na barta wani abu ya same ta har abada ba zan yafewa kaina ba, koda ace ban samu aikin nan ba, ba laifi amma nayi sa'ar ceton Rayuwarta. "