ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 27
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 27: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 27. " Bayan nan an kara kiranki bakya nan ina kika je? " Ya kara cilla mun tambayar. " Ibada na…
4,443 words
" Bayan nan an kara kiranki bakya nan ina kika je? " Ya kara cilla mun tambayar. " Ibada na tafi, koda na dawo na samu an tashi, duk abinda ake nima a duniyar nan, anan zamu barshi, can ne dolenmu don na rasa wannan damar ba wani abu bane, babbar damar da zan rasa shine rasa sallah nan."
" Kina magana da kawazuci, me yasa kika ajiye son kika dauki kawazuci?" Yar dariya nayi, yadda suka kalle ni sai na rufe bakina, kaina a kasa kafin na ce mishi. " Duk wata mace a duniyar nan idan har ta isa mace uwa ce, ko ta haifa ko kada ta haife ita din uwa ce, idan har da rayuwa ta bamu abinda muke so, zan ji ciwon idan aka ce Y'ata ce a cikin wannan yanayin, akwai abinda dukiya baya iya siyansa a cikinsu kuwa har da Yara, kawazuci ba iya mutane ke raye akanshi ba hatta dabbobi suna da ita. "
Jinjina kai yayi ya kara da cewa. " Yanzu idan kamfanin nan tana cikin wani irin yanayi kuma lokancin sallah yayi zaki iya tsallakewa ki yi sallah!" Kallon kasa nayi nace mishi. "Ba mamaki wanda ya tsaya har kamfanin ya iso wannan matakin bata raye, yau ya tara amma baya nan balle ya ga yadda yake tafiya, an tambayi wani daha cikin magabata me tafi yin addu'a a kai game da Lokaci, ya ce Allah ya bashi aron numfashi ya kara ganin wata lokacin da zai ibada, kamfani bata kai ibadana muhimmanci ba, zan bawa kamfani lokacina amma banda ta ibada ta." Daga haka suka yi shiru basu kara magana ba, Nima kuma ban ce uffan ba, ina tsaye a wurin karar shigar sakon da aka musu na d'ago kai ina kallonsu, daya babban cikinsu ya ce min. "Mrs Jama'are, idan aka baki damar aiki da kamfanin nan me kike ganin zaki yi har ya kai ga nasara." Jan iskar bakina nayi na ce mishi. " Na karancin hadahadar kasuwanci a degree na farko, na kara yin master a tallace-tallace, idan har akwai abinda xan yi shine zan tsara yadda kamfanin nan zata fito idanun duniya. Zan mai da hankalina wurin daidaita kamfanin izuwa ga sauran takwarorinta na duniya, sannan zan bawa aikina muhimmanci sama da kome da kowa na kamfanin. "
" Mrs Jama'are idan kamfanin ta dauko karyewa, nasan kin san aikin kamfanin me kike ganin zaki mata kada ta karye?" Lashe bakina, na sauke ajiyar zuciya kafin na ce." A matsayina na karamar ma'aikaciya kuma wacce take da ilmin tsara tallace tallace, shine zan fara duba yadda zan janyo hankalin masu zuba hannun jari, daga gida zuwa kasashen ketare, aanan kuma zan yi ƙoƙarin rufe duk wata kofa da zata janyo min karyewa a cikin kuwa shine zan zubar da ma'aikata, ba zan debi sabbin ma'aikata ba, tsofin zan kara basu horo sannan na kara inganta ilimin su yadda zasu fuskanci yanayin da ake ciki, za a rage wasu abubuwan da ake yiwa ma'aikata idan kamfani ta farfaɗo sai a kara musu, wannan tsarin economic ne ta kowacce kamfani da kuma manyan ma'aikatun duniya." " Kina nufin a watsar da tsarin diban ma'aikata kenan? Idan haka ne kuwa har dake a cikin haka ya miki?" Gabana ne ya fadi shi kenan nayiwa kaina, sai nayi murmushi na ce mishi." Haka ma ba laifi bane, kowacce kamfani tana kokarin ceto rayuwarta ne. Idan har aka duba masalahar kamfanin babu amfanin diban ma'aikata, idan kuma kamfanin tana da buƙatar haka ai ba laifi bane. " " Mrs Jama'are ko dai zaki gare muradinki ne? " Inji matar, murmushi nayi mata nace mata. " Ko daya ni ina da nawa ra'ayin ba wai aikin kamfani nake da buri ba, amma a tambayar da aka min dole na bada amsa." Cidar d garin ya fara alamar za ayi ruwa yasa na kalli agogon hannuna. "Shi kenan zaki iya tafiya!" "Na gode!" Na fita ai nasan ba wani batun daukar aiki, ya xan yi da Ya Ado?
Ruwan da aka fara yasa da na sauko kasa ba tsaya ina kallon waje kamar yadda kowa ya tsaya, matan nan sai gulma suke.
Bayan fitar ta ya juyo kujeran, yana ta rubuce-rubuce. "Bro yarinyar tayi tana da kwarin gwiwa!" Inji Jasminah, "Kuma da alamu zata yi abinda ya dace, shi dai bai ce kome ba, " can dai Uncle Auta ya ce mishi. " Sunan yarinyar kamar yaso na taɓa jin sa a wani wuri?" " Usman Umar Jama'are, Baristan nan!" Inji Ubaid, " wow dole ta samu confidence, irin wannan ake bukata asalin kwarin gwiwa na gani a cikin kalmanta!" Shi dai shiru yayi can Uncle Auta ya ce mishi. " Ni kuwa yarinyar ta min, tana da nutswa da hankali!" " Oo Uncle Auta fell in love daga kallo daya." Buga table din yayi ya ce musu." Bata min ba ta cika surutu, mai surutu baya abinda ya dace!" Daga haka ya bar office din yana mai riko hannun Yaran.." Uncle BT amma tana da kirki, me yasa ba zaka dauke ta ba. Ina sonta." " Princess idan aka kawo ta kamfani ba zata yi aikin da ya dace ba zata yi ta hira da mutane ne." " Uncle BT yana da kirki Please!" Dan durkusawa yayi yana kallon yarinyar da take murza idanunta. " Uncle tana da kirki she is a good person!" Taya zai gaya mata bata da kirki, bayan ta ceto rayuwarta. " Princess kada ki damu da irinsu." Idanunta ne suka cika da kwalla, har suka zubo mata ta ce mishi."please!" " Ok ok bar kukan haka kin ji! " Gyada kai tayi tana murmushi, haka suka fito sai lokacin ya hango tana fita daga kamfanin a hankali tana tafiya ruwa na zuba kaɗan kaɗan, bodyguard dinsa ne suka fito da lema suka saka mishi bayan ya dauki Yarinyar, suka bude motar ya sakata, ya daura mata belt sannan ya shiga suka tashi motar, a hankali suka bar kamfanin a bakin gate suka tsaya sakamakon wata motar da ta danno kai.
A hankali nake tafiya har na samu wani abin hawa na gaya mishi inda zai ajiye ni, ya ce na shiga, sai dai cikin ikon Allah motar taki tashi dole na sauka na cigaba da tafiya nayi tafiya sosai, kafin na nufi garej, kamar ance na d'ago kaina daga lemar na hango ya Hafiz ban san lokacin da na sake lemar na fara ja da baya ba, murmushi ya sake yana kallona, daidai sake wata irin ruwa mai karfin gaske shaaa, karafuna ne suka dauka rawa, na ji kamar cikina ya hautsine, wani irin abu na ji ya tsaya min a wuyana. Na fara ja da baya, yana bina ina ja da baya yana bina, ga titin ba motar da suke wucewa, hawaye ne ya fara zubo min. Karar horn na ji na kalli wurin, na hango motar kamfanin ce, wani irin kuka ne ya kwace min ganin yadda suka wuce. "Ba fa mai taimakonki, kaf duniya babu sai ni, ni kaɗai ne last hope dinki!" Yadda yake tawowa ban san me ya tare ni ba, haka na zube yayi kaina zai damke ni, na kare kaina tare da fasa wata irin kara tare da kiran sunan Allah, na rufe idanuna hannuna biyu na saka ina mai kare kaina, wani irin kara naji wanda ban san yadda akayi na bude idanuna ba, sai ganin............. (Alhamdulillahi na gode sosai🥺🚶 wannan wurin nasan sai an ji kamar a cije ni kuma duk wnada ya zagi hafiz shi da kanshi) [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 45 Kamar yadda aka ce mata suna suka tara, haka ma Maza sun kashi gida daban daban, domin ni dai ban tab'a ganin irin wannan mutumin ba, hannun da ya Hafiz ya kai zai damko ni ita aka murder a baya sai da tayi wata irin ƙara, kafin ni da shi mu farfaɗo, bawan Allah nan ya kara sake mishi naushi. Sai na kasa fahimtar tsoron waye zan ji a tsakaninsu Hafiz ne ko wannan mutumin da sauri na kara kifa kaina kasa ina wani irin kuka, ji nayi an lullube ni da abu, an d'aga ni. Muryan mace na ji tana faɗin.. "Sannu muje mota, ai ke ma'aikaciyarmu ce, Sir ba zai bari wani abu ya same ma'aikancinsa ba." Haka ta saka ni a motar sannan ta koma ta dauko min lemana da tarkace na, a hankali na kalli inda Ya Hafiz yake kwance, mutumin ya murde hannunsa. Sai zabga mishi naushi yake irin na b'acin ran nan, barin wurin muka yi, na kifa kaina a kan cinyata, idanuna rufe. "Wacece unguwa kike?" A hankali na gaya musu ma cigaba da kuka.
--- A can kuwa Garej Mr Turaki bai yi niyyar shiga al'amarin ba, tunawa da yadda aka yiwa Mrs Thomas yasa shi kiran security na kamfanin kafin ya fita da sauri duk da kiyayyarshi da sanyi kuwa, amma ta gane ta ne da lemarta. Sannan Ilham ta kara ce mishi, ga wacce ta taimake ta. Haka yasa shi tsayar da motar, umarni ya bawa Tajudeen akan ya kira sauran security din domin ya tuna abinda ya faru da wancan matar haka yasa shi sauka ya samu Hafiz. Ba zai ce ya yake ji ba, domin abu ne me sauki da mutum zai bada labarin yadda ya ji shi, wani babban al'amari ne da Allah kaɗai yasan yadda abin yaƙe.
Yadda ya dage da dukkan zuciyarshi yake kai mishi duka zaka rantse da Allah irin yasan Mafarin lamarin ne, amma ina shi zuciyarshi abinda ya bashi ita din mace ce me rauni kuma tana bukatar taimakon shi, fisge shi Ubaid yayi yana faɗin. "T meye haka? Me yayi maka? Haba da girmanka?" Huci yake yana nunawa security Hafiz. "Ku tabbatar kun hada shi da yan sanda." Sannan ya juya ya bar wurin ranshi yana soya, ko ruwan da ake yi bai dame shi ba, tunda Ya shiga motar yake jin wani irin zafi. Har suka isa Mansion na Kumo bai magana ba, yana zaune shiru towel Jasminah ta lullube shi da shi tana faɗin. "Sanyi zai kama ka!" Komawa gefensa Alhaji ELYakub yayi ya zauna yana press din hannunsa a hankali, alamar yana calming dinsa da ya huce wani irin zuciya ce me cike da kishi, dafe kanshi yayi ga hannunsa da ya ji ciwo yayi ja saboda naushin fuskar Hafiz kawai," Me ya faru da ita?" Daddah ta tambaye su hankalinta a tashe, " Fada yayi da wani!" Uncle Auta ya fada yana kallonshi. " Fada!!!" Duk suka hada baki, domin abin da mamaki Daddah ta ce. "Wai yaushe ma taso ne?" "Muma ganinsa muka yi dazun!" Ubaid ya bata amsa, cike da mamaki Alhaji ELYakub yake kallonshi. " Kuna nufin bai gaya muku zai shigo ba?" Alhaji ELYakub ya tambaye su cike da mamaki, shigowa Alhaji Abbas kumo yayi yana faɗin.." Amma wannan wacce irin abin kunya ne Bilal ya aikata? Duk an dauki videon ana yaɗawa a duniya. Baffa ya kamata ka yi wani abu, taya zai shirya interviews without our knewing, ba laifi sai ya je ya kama fada da yan iska idan wani abu ya same shi fa? Ya yake tunanin al'amarin zai kasance ga masu saka hannun jari." Mikewa yayi bai karasa jin mai yake faɗa ba yayi waje abinsa, " Turaki! " Ina tuni ya bar cikin gidan abinsa. Shi dansa ne zai saka shi gaba yana mishi ihu, ko dansa da yake abinda yaso baya mishi ihu, " Bilal listn to me!" Kwace rikon da Ubaid yayi mishi yayi yana kallonshi. " Ni Yaro ne?" Ya tambayi Ubaid, girgiza mishi kai yayi yana faɗin." Muje na sauke ka a gida." Haka ya shiga motar yana shiga ya fara jera atishawa, yana yi yana karawa. Har suka iso gida, kusan sanyi ya gama kama shi. Wanda ya haɗa har da zazzaɓi me karfi, tare da mura. Karshe sai da Uncle Auta ya haɗa da kiran likitan family din ya mishi allura. Alhaji ELYakub ya zo shima hankalin Familynshi ya tashi sosai saboda sun san yana da irin wannan ciwon wannan wani abu daya da suke son kara amfani da shi, ba kome bane sai maganar fadar da aka yi. Hajiya Khaulatu da tazo ta ganshi, ba ta bar gidan ba sai da ta san yadda ta samu Alhaji ELYakub ta ce mishi. "Tunda babu wanda zai zauna da shi Badr ta zauna da shi mana, zai so ya bukaci wani abu idan ya farka." Uncle Auta yasan manufar yar uwarsa, amma idan yayi magana, zata ce yana hana su samun kusanci da Turaki, haka yasa shi zuba mata idanu, Mahaifinsu kuwa ya amince, haka ta fita tare da kiran Badr tazo gidan tayi jinyar Turaki.
Shi kan tunda aka saka mishi ruwa da allurai ya cigaba da barci.
*** Har gida suka kawo ni, kuma har lokacin ban daina kuka ba, domin na razana ba wai Hafiz ba, ganin yadda mutumin nan yake dukar Hafiz sai ya bani tsoro matar ta ce min. "Mun iso nan ne ko?" A hankali na fito ta rako ni har kofar gidan sai da ta ga shigana sannan suka bar kofar gidan. Tunda na ga motar Ya Ado, kukan da nake ya karu, ban san yadda aka yi ba sai naji kamar an cire min duk wani tsoron Ya Hafiz dake ji, naji a raina idan na kara ganinsa sai dai wani ba shi ba. Haka na shiga parlourn na tsaya daga bakin kofar, zuba min idanu suka yi ganin yadda nake kuka. Tasowa Aunty Zakiyah tayi ta nufo ni. "Hafiz ko?" Cikin shashekar kuka na ce mata. "Eh!" Haka ta wuce da ni dakin kasa ta haɗa min ruwa nayi wanka , ina fitowa ta bani magani na sha da tea me zafi na kwanta, karfe shida saura na tashi. Nayi sallah la'asar da ta kwace min, da sallah Magariba, ina zaune a wurin Ya Ado ya shigo. "Ya interview din?" Kallonshi nayi idanuna cike da kwalla. "Kayi hakuri nayi missing dinsa, ban samu yi ba." Zama yayi s stool yana kallona. "Hafiz ya bi ki can ko?" Hawaye ne suka zo min, na cigaba da wasa da yatsuna. "Shi kenan, wannan karon ya hadu da dai-dai da shi, ya kira ni dazu nace bana gari. Yaji yadda ake ji, and Abu daya xan gaya Hafiz ba Mala'ikan mutuwa ba ne, ya isa haka tsoron da kike ji, kin san yadda nake jin ciwon halin da kike ciki kuwa? Ni ban ce ki yi fada ba amma at least ki tsayawa kanki taya kullum mutum daya zai na koro ki, taya kullum muna murnan kin samu lafiya ashe mu kike kashewa da ranmu, don Allah idan ba zaki iya daina tsoronshi ba, ki koma Bauchi daga nan zan kula da duk wani abinda kike bukata na gaji, na gaji Lubabatu ke daya ce aka tab'a jarabta da ba zaki yakince shi a ranki ba, haba don Allah kullum wani dan iska ya kore ki, ko ya gaya miki wani abu yanzu so kike na kira Mama na gaya mata hankalinta ya tashi d'an jininta da bai hau ba ya haura, akanki tana fada da kowa yanzu idan ta ji Hafiz yazo nan me kike son ta dauke ni, look kowa Ni mutum yana da zuciya a kirjinsa ne, amma ƙalilan suke fada da zuciyarsu, idan kin ga zaki iya kwatar kinki shi kenan idan ba zaki iya ki koma Bauchi na gaji, haba don Allah akan ki aka fara ne? Balle ki ce babu wata victim sai ke, fisabiilillahi kina driving dina crazy, na rasa gane waye yake bani wahala a cikinku Hafiz ne ko ke? Nq gaji idan kika rasa wannan aikin in sha Allah karshe watan da zamu shiga zaki koma gida na gaya miki, ko je can ki ta fama ba zan iya miki ba, tunda baki iya kome na sai kuka kina nan kamar wawuya, Hafiz din banza ko ihu ba zaki yi ki tara mishi jama'a ba." " SAN ya isa haka don Allah ta ji ai!" " Ba zaki gane yadda nake ji bane." "Na amma itama tana fama mentally ill ne ai, idan har aka ce za'ayi fadar pushing dinta gaba zamu yi madadin mu dawo da ita baya, please ka yi hakuri yara kowa ya gudu daki jin kana fada Please. " Wannan maganar da tayi yasa shi fita a dakin, na hada kaina da gwiwa na cigaba da kuma har ta gaji ta bar dakin, na san gaskiya ta gaya ya fada amma kuma yadda yake ta fada da cewa ya gaji sai na ga kamar ban cancanci haka daga gare shi ba, kuma bakiɗaya ya daura min laifi fisabiilillahi don ba shi bane ya sha wuta a hannun Ya Hafiz, sai na kasa yarda da zuciyata nice da laifi ba shi ba, haka na kwana da abin a raina da safe ko fitowa ban yi ba, suna sane suka share ni. Ai kuwa zuwa la'asar sai ga kiran Aunty Hindatu fada take inda take shiga ba nan take fita ba, sai da na rena kaina maganar da ta fada min yasa ni shiga hankalina. "Idan kina son ki karasa mata aure sai ki dawo a cigaba da ganinki ana yab'a mata magana, ko wancan satin sai da aka gaya mata magana dakyar muka dawo gida jininta ya hau, kullum da ke take kwana ke ba zaki iya kwatar kanki ba sai mun taya ki? Fisabiilillahi muna da tamu rayuwar." wannan Maganar ya dake ni, sun gaji da ni, haka na ji a raina sun gaji da ni. *** Da karfe biyar na asuba ya farka, a hankali ya tashi ya cire robar karin ruwan ya sauke kafarshi, kasa tare da saka slipper ɗinsa, zuwa ban daki, yayi wanka da alwala sannan ya fito ya zauna a bakin gadon har yanzu alluran nan basu sake shi ba, daddafe ya yi sallah sannan ya fito ya sauka kasa kitchen ya nufa ya haɗa coffee, sannan ya dawo parlourn ya zauna sai da ya sha, sannan ya koma ya kwanta a kujeran, wani barci ne ya dauke shi.
Karfe sha daya na safe yaji maganar mutane a can kasa-kasa. Bude idanun yayi ya zuba musu idanu Ubaid da Jasminah tare da Uncle Auta, sai Badr da suke ta mishi sannu. Tashi yayi Ubaid ya dauko kular abincin, kallon Badr ya ce musu. "Who is she?" Yadda yayi maganar kamar me koyar magana, yasa suka zuba mata idanu har lokacin idanunsa yana kanta.. "Badr ce yar gidan Hajiya Khaulatu!" "Uban waye ya bata iznin shigo min gida?" Shiru suka yi suna kallonshi. "Before na bude idanuna ta bar gidan nan ko nayi kwallo da ita!" Ai ba ita ba hatta Jasminah da sauri ta mike tare da jan hannunta suka fitar da ita kayanta ma aka shiga duka dauko. Sannan suka sallame ta abin tausayi gashi ana ruwan sama. Juyawa yayi ya kafe Uncle Auta da idanu. Yadda yake mishi wani irin kallon tuhuma. "Ka ga bar min irin wannan kallon ba ni nace ta zauna ba, wallahi Uwarta ce kuma." Dauke kai yayi yana kallon yadda Ubaid yake motsu-motsu. "Ban kira sunanka ba!" Ya cigaba da shan kunun da aka zuba mishi. "Gayen nan dan uwan Barista Jama'are ne!" Banza yayi bai kuma kula su ba. "Please ka bada umarni a sake shi." Kallonsu yayi ya kama tari yana dafe kirjinsa, kafin ya cigaba da cin abincin. "Son kayi hakuri mana!" Cigaba da karyawa yake kamar ba da shi ake ba, iskancin ya motsa kawai bai da niyyar ya amsa musu, kallon Jasminah yayi ya ce mata. "Ki nimo min professional chef." [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 46 "In sha Allah zan nima maka mace ko namiji!" Kallon wayarshi da yake ringing yayi ya ce mata. "Male!" Ya fada dan zafaffe, a yadda yake din nan kamar ya rufe mutane da duka. Kusan haushinsu yake ji, definitely ba sune suke bashi haushi ba, kishin da yake cin ransa musamman da Ubaid yake gaya mishi ai Baristan nan ya zo akan case ɗin, kamar ya rufe su da duka, amma fuskarshi babu al'amar yana cikin fushi ko b'acin rai. "Son!" "Yau baka da aiki ne a office!" Ya tari numfashin Uncle Auta, domin kada ya kara ce mishi kome kiran wayar Uncle Auta Hajiya Khaulatu tayi tana ta fada akan me zasu koro mata Yarinyar ba tare da sun kira a zo a dauke ta ba. Lumshe idanunshi yayi ya kwanta da kyau yana jin yadda take bala'i har da cewa a saka a handfree da yake shima dan yau ne irinta murmushi yayi yana rayawa a ransa idan har da zai ina bude baki ya mata rashin mutunci ga abinda zai gaya mata amma ya koyi wani abu yana jin dadi idan ya saka mutane suna ihu a kanshi. Tow uban me zata min, idan na kara ganinta a inda nake sai na karya, wannan shi ne abinda zuciyarshi ya gaya masa, amma sai ya share ya kuma cigaba da kallonshi domin baya son ya karawa kanshi wani zafin kai.
Ubaid da Uncle Auta suna ganin jaraba, mikewa Uncle Auta yayi zai fita ya ce mishi. "Ka taimakawa kanka ka yi aure wannan rayuwar taka bata da amfani." Shiru yayi bai kula Uncle Auta ba har ya fita da yake bai da mutunci sai ce mishi yayi.. "Ka nima min auren Nihla!" Ba Uncle Auta ba, hatta Uban Nihla sai da ya kusan faduwa daga kujerar da yake zaune. Saboda kaduwa, kuma kamar ba shi yayi maganar ba, wato idan Allah ya haɗa ka da dan iska yana fa kyau ka ɗan yadda zaka zauna da shi. "Amma ka zare ne?" Banza ya musu ya bawa iska ajiyarsu. Mikewa Ubaid yayi har ya isa bakin kofar fita zai kuma ya ce mishi. "Baka ce kome akan Yarinyar nan ba a tura mata sakon ɗaukar aiki ne?" Bawan Allah nan haka yayi shiru ya kyale su, har abin ya fusata Uncle Auta zai magana. Ubaid ya riko hannunsa. " Shi kenan muje ba sai an tura ba." Kasan ranshi yana son yayi magana amma kuma yana gudun abinda za a dauke shi, haka yasa shi ya share shi har suka fita. Kwanciya yayi a dogon kujeran parlourn, yana nazarin yadda kome yake tafiya, a hankali ya janyo wayarshi zai tura sako sai ya fasa. Abu daya yake damunsa shin ta isa gida lafiya? Wani hali take ciki? Ko itama ta samu matsala na mura ne? Tsaki yayi da ya tuna matar aure ce, bai san me yasa zuciyarsa take janshi ba, cikin hade rai ya wani cigaba da kwanciyar shi, Granny ya kira suka sha hira wanda ita ce ke jan shi da hiran, daga karshe suka yi sallama.
Kwanakin da ya biyo baya ya murmure, amma yaki zuwa family house dinsu. Domin ba zai iya daukar renin hankali ba, ranar Monday ya shirya zuwa office. Anan ya ga sabin ma'aikatan da suka ɗauka. Duk inda ya wuce gaishe shi ake, har ya shiga elevator da zai kai shi hawa ukku na kamfanin, anan office ɗinsa yake, yana isa ya nufi office ɗinsa, zare necktie dinsa yayi ya wurga a can gefe, sannan ya cigaba da aikin da yake yi, sai dai zuciyarsa tana wani irin akilo a duk lokacin da ya tuna cewa basu tura mata sako ba, kusan aikin suku-suku suka yi shi, kafin can ya dauki shawarar da wata bangaren na zuciyarshi ta bashi ya shiga email din Ubaid ya tura mishi sakon a dauke ta aiki. Sanin cewa idan har Ubaid ta ga sakon zai biyo bayanshi, sai ya cigaba da kallon wayar time to time yana jiran kiran Ubaid amma har kusan awa daya babu reply, sai wurin karfe biyu na rana Ubaid ya kira shi, wani tsaki ya ja yana ganin kiran yasan abinda zai gaya mishi bai wuce an tura mata ba, sai me? Haka ya cigaba da aiki can, ya sauka ya nufi masallaci a can suka hadu da Ubaid ya zuba mishi idanu yadda ya wani hade giransa zaka rantse da Allah ai tab'a dariya ba, haka ya idar da ibadar ya nufi waje. Shima Ubaid a gurguje yayi addu'ar ya fito. "Na ga sakonka, ai ni tuntuni na tura mata sakon." Yadda ya zuba mishi idanu, kamar zai cinye shi Ubaid ya ce mishi "ina nufin na gaya mata an dauke ta aiki ne, sai dai nayi mamaki da bata zo ba yau Monday." Duk da yaji dadin da basu jira shi ba, amma gudun kada a rena shi ya ce mishi." Na tambaye ka ne?" Ya fada yana wani hade rai, shima Ubaid tabe baki yayi. Haka suka jera har office ɗinsa, muka zauna suna kusan Ubaid ke bashi labarin yadda ake ciki a kamfanin shi kuma yana nadewa, yayi shiru har Uncle Auta ya shigo ya samu wuri ya zauna, suka fara tattaunawa wanda shi baza musu kunne yake yana jin me suke fada sai can da aka gama maganar ya ce, musu. "Ku shirya meeting gobe!" Daga nan ya wuce kan table dinsa, kafin ya cigaba da aikinsa. Karshe da ya ga tunaninta zai dame shi sai ya tattarata ya watsar ya cigaba da abinda yake yi har kusan uku da rabi lokacin aka kawo musu abinci suka ci sosai, shi kan drinks ya tab'a yana faɗin. "Zance naci towon laushi wurin Dadda!" Daga haka ya cigaba da aiki. Karfe hudu ake tashi, haka yasa yana fita ya hangi inda ya ganta ranar, abin mamaki yake bashi. Tow me nashi a cikin.
*** Tabbas an turo min sakon an dauke ni a aikin kusan kwanaki uku da suka wuce amma kuma ban san me yasa bana son zuwa wurin aikin domin idan na tuna da abinda ya faru sai naga kamar Ya Hafiz zai dawo, ban kuma jin labarin yadda aka kare ba. Har ranar da sati ya zagayo wai ni fushi nake naki kula kowa. Ina daki Ya Ado ya kira Ya Umar yana gaya mishi, an dauke ni aiki amma gashi nan zan fara mishi rashin mutunci, wannan abin ya min ciwo sai da na kasa hakuri yadda Ya Umar yayi ta dura asharia, haka yasa nima na kira Mama nayi ta kuka, itama fada ta min da nasiha tare ta rarrashina. Washi gari ranar talata kamar yadda ta umarce ni na shirya na tafi aikin. Ba musu na shirya tsaf na nufi wurin aikin, da wurwuri kusan kowa ya same ni ina jiransu, haka ya kawo ni Garej na tsaya jiran motar da zai shiga da ki ikorodu. Wurin minti goma sai ga motar tazo na shiga a hankali na zauna tare da jiran su tambayi kudinsu. Aikuwa bamu jima da tafiya suka tambaye kudin na bawa kwandusta.