Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 29

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 29

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 29: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 29. Muna haurawa na samu har an gama aikin, abin ya bani mamaki yaushe na zo har an gama. Office…

3,761 words

Muna haurawa na samu har an gama aikin, abin ya bani mamaki yaushe na zo har an gama. Office dinsa muka shiga Taj ya ce min. "An yi miki office dinki na wajen nan, nan zaki zauna ke daya babu yawo babu fita ko ina, akwai toilet a can gaba kaɗan. Duk abinda zaki yi kama daga sallah zuwa wani abu ba sai kin fita ba, abinci xan na kawo miki." Yadda yake bayanin saura kiris na kware. Wannan wacce irin takura ne? Muryanshi ce ta dawo ni daga duniyar tunanin. "Zaki cigaba da aiki daga nan ban da sauka kasa." Ban san yadda aka yi maganar ta kwace a bakina ba, sai da na rike bakina. "Amma wannan bauta ce ba aiki..." Yadda suka zuba min idanu, nayi maza na rufe bakina, da sauri na fita. Sai yayi kamar bai ji ba, shima Taj din kamar bai ji ba aka bar maganar. Wunin ranar baki muka yi daya office dinsa zuwa kasa, ni da shi mun sauka ya fi sau goma, kafin na dawo nayi sallah naci abinci, ina gamawa Taj ya kawo min laptop kiran kamfanin Dellu ya ajiye min, ya kara min da table tap, sai takardu da printing machine. "Ranki shi dade daga ko ina zaki amshi sakon kuma zaki yi printing dinsa ki tura, bari na nuna miki." Haka ya shiga nuna min ina tambayar shi yana bani amsa kamar an ce in d'ago kai, masufaffen mutumin nan ne a tsaye a bakin kofar, da sauri na sunkuyar da kaina.. "wannan anya kanshi daya?" Na tambayi kaina ko da mq d'ago baya nan, sai sake wani irin net yayi a jikin kofar.. ajiyar zuciya na sauke. "Idan aka tashi zaki tafi da kayanki ba zaki bar ko daya ba." Gyada kai nayi, yana gamawa ya bar ni, kamar mayya wata yar wayar da aka saka a wurin yayi kara dauka nayi nace.. "Hello!" "Akwai baki yallabai yasan da zuwansu ne?" "Ok rike wayar!" Na ce sannan na tashi na isa bakin kofar na buga ya ce ma shiga, ina shiga na ce mishi. "Sir kasan da zuwan baki ne?" Bai amsa min ba, wannan mutumin dan girman kai ne, tsayuwa na cigaba da yi, can ya ce min. "Ki duba tap dinki!" Da sauri na fita na duba, daukar wayar nayi na ce mata. " A kai su dakin tattaunawa gashi nan zuwa!" Na koma na gaya mishi suna jiranshi, kamar ya mangare Ni, haka na biyo bayanshi da laptop dinsa. A meet room din har da wannan Khamis din, nan aka yi meeting din ina zaune a next na Masifaffen. Ana gama meeting din Khamis ya zo ya zauna yana mai juya kujerar da nake kai yana faɗin. "Idan kina da wata matsala ina wancan tsohon side din ki zo!" Yadda Masifaffen ya mike haka nima na mike, tare da bin bayansa. Sai ji nayi mutumin nan ya kai min mari a mazaunai na, yana faɗin. "You too hot baby!" Wani irin abu naji ya zo min wuya kamar yadda Masifaffen ya tsaya cak haka na juya tare da kifa mishi mari, sai da ya zauna.. "Koda nazo aiki ni ha kazama ba ce." "Muje!" Haka ya ce ,tare da matsa min na fita ya juya ga Khamis. " Kayi hauka ne? Ko an gaya maka kowacce mace kazama ce! " Daga haka ya bar shi nan da ciwon baki.

Tun kafin mu tashi taj ya gaya min oga zai yi tafiya Abuja, tare da shi ni gobe ba sai na zo ba, tafiyar zata dauki kwanaki uku zuwa hudu ranar Laraba zan zo wurin aikin kenan, wayyo dad'i kamar na zuba ruwa na sha. Haka muka tashi na hada kome nawa, har lokacin Masifaffen yana office, hala jira yake na je na tattara mishi kayansa Kamar yadda na fada a raina haka ne fa, shiga nayi na hada mishi kayansa yana zaune, ina gamawa Taj yana shigowa na mika mishi. Ni dai da muka fito motar ma'aikata na shiga, ya kawo ni Garej, sannan na wuce gida.

*** Wannan marin da Lubnah tayiwa Khamis, ya janyo rigima da meeting. Da aka zauna ya ce ba zai zo ba tafiya ne gaban shi, ai kuwa abin ya bakanta ran Alhaji Abbas da Alhaji Mudansir, lokacin da Uncle yake music bayanin rashin mutunci da Khamis yayi karyawa suka yi tare da cewa. "Khamis me zai yi da low background irinta, idan lalata yan mata yake ba ga yan matan da suka fita haduwa a gari ba...." Yadda suke jaraba da masifa kamar an yanki namar fuskarshi. Haka suka kai ƙara wurin Alhaji ELYakub ya zuba musu idanu ya ce a jira Turaki ya dawo sai ayi magana. Tunda abu ne na bangaren biyu zuwa uku sai aji uku waye mai gaskiya. Abin ai ba na fada bane, nan ma suka yi ta mita. Wani abu da suka kasa ganewa akan Turaki Alhaji ELYakub bai da hakuri kuma baya karban maganar kowa haka yasa suka yi ta jin haushi da mitar an ki amsar Maganarsu kome ya faru Turaki ne mai Gaskiya, ba su ba..... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 49

*Anya kuna fahimtar tafiyar nan kuwa?*

Rigima taki ci ta ki cinya, domin kuwa Hajiya Sameerah ta saka a ranta sai an kori yarinyar da ta kwatsamawa danta mari, haka shima Kawun Khamis sun mai da al'amarin babban al'amari, wannan abin da suka ta yi yasa Alhaji ELYakub ya kira Turaki lallai yana son ganinshi, duk da yasan baya gari amma ya mishi alƙawarin yana dawowa zai shigo.

*** Ranakun da nayi a gida, sai nake jin kaina kamar wata mai yanci. Nasan duk tsiya ranar Alhamis zan koma sai nake ji kamar kada na koma na ji dadin gida, a kwanakin da nake gida ne naji Ya Ado yana cewa zai mai da Abba gida an sallame shi. Sai da suka yi kwanaki a gidan Ya Ado, domin yace ba zai mai da shi gida ba, sai ya nutsu. Kullum muna tare ina zuwa na gaishe shi domin a daya gefen gidan ya ajiye su, na zauna ina karanta mishi karatun Alqur'ani, ranar da zan koma aiki na je dakin na zauna ina faɗin. "Yau naji zaku tafi ni kuma zan koma aiki, Allah ya kai ku lafiya, a gaida mutanen gidan." Har na gama maganar da nake bai amsa min ba, duk dama baya wani kula ni. Haka na fito ina jin wani irin nauyi a raina, a harabar gidan na sami Baban Jama'are da Baba Malam, sai Ya Hafiz da Rufa'i. Sama sama na gaida iyayena maza na wuce wurin Motar Ya Ado na shiga ko Rufa'i yanzu na daina bashi fuska domin na fahimci shi yake bawa Ya Hafiz wani bayani a kaina. Ina tsaye a wurin ina wasa da wayata. "Luluna!" Banza nayi kamar ban ji shi ba fitowar Ya Ado ya ke ce min. "Auta muje na sauke ko na dawo domin yau akwai inda xan je zan kuma ajiye su Abba a airport shi da Yadiko da Rufa'i, su Baba kuma xasu bi motar kasuwa. " " Tow ba kome!" Na shiga gaban motar na zauna." Ado kun raba ni da Matata! " Ya fada yana kallon yadda na dauke kai. " Luluna ki dawo gare ni!" " Wanda muka yi a baya ma Allah ya yafe min!" Daga haka muka bar gidan, a hanya Ya Ado ya sake murmushi. " Bakinki ya fara magana!" Shiru nayi ban ce kome ba. Ya ajiye ni inda zan samu motar Garej, ina fita kuwa na samu motar minti talatin da biyar muka isa na biya tare da sauka na cigaba da tafiya a kafa. Horn da naji a bayana, juyawa nayi na ga motar Jasminah ne, ta tsaya tare da sauke glass din ta ce min. "Shigo!" "A'a na kusan isa fada mata ina murmushi. " Shigo dai mu karasa!" Ta fada tana buɗe min kofar ta ciki, shiga nayi a hankali ina murmushi. " Na gode!" Na daura jakata a cinyata. "Kawai don oganki baya nan sai ki lafe a gida?" Murmushi nayi nace mata." Ai shi yace na zauna!" Jingina kai tayi kar muka isa cikin kamfanin a tare muka shiga na isa inda zanyi sign na wuce, " Sai yau kika gadamar zuwa?" Juyawa nayi na kalleta sannan na ce mata. "Oga ne ya ce na zauna a gida tunda baya gari." Sai suka shiga kallon juna irin mamakin nan waye aka tab'a bashi wannan damar haka sai ni? "Karya ne Oga ba zai tab'a baki wannan damar ba." "Stella me ya kawo wannan maganar?" Jasminah ta tambaye ta, "Ma gani nayi zata yiwa oga karya!" "Ta miki kama makaryaciya ce?" "No Ma!" Ta fada, daga haka ta ce min. "Ki tafi office dinki!" "Tow!" Na ce na wuce abuna, ban kara tsayawa ba, ganin da gaske zan wuce sai wata take cewa. "Me kika fi sauran mala'ikatan!" Ban kula su ba, na wuce zan hau elevator, "ya daina aiki!" Wucewa stair nayi na fara haurawa a hankali, dama ai haurawan ba sabon abu ba ne.

Ina isa office din na samu tarin aiki, na bude table tap din, na fara aiki kamar yadda na gani, na shigar da bayanai, na tura mishi office ɗinsa, na turawa Taj da Jasminah, sai karfe biyu na samu kaina.

*** Yana zaune duk yan uwan babanshi sun taru ana son dalilin kwatsamawa Khamis mari da Lubnah tayi, yadda yake shan fruit hankalinsa kwance, sai da ya sha ya koshi, ya mike yana faɗin. "Daddah ke da Dattijo ban san dalilin kiran da kuka min ba, gashi nazo babu wani bayani sai tambayar da ni dai nasan da yarinyar bata mare shi ba, sai na karya mishi hannun da ya tab'a da shi, tsalle tsallensa ya tsaya inda yake da iko idan ya shigo wurina ya tab'a min ma'aikta!" Mikewa yayi bayan ya gama daure takalminsa, ya dauki jacket dinsa ya saka yana mai kallon Uncle Auta ya ce mishi. "Wallahi sai na kwashe mishi kayan aiki!" Daga haka ya fita abinsa bayan ya saka Black prada a idanunsa ya nufi waje.. har ya fita sai ya dawo ya ce musu. "Yaran da kuka turo min na mai da su Office din Uncle Mudansir ina ga zasu dacewa da can!" Daga haka ya yi tafiyarshi idan kana niman hayaki fidda na koko to Bilal ya kai wannan matakin wai sun zo gaban Alhaji ELYakub amma bai hana yayi yadda yake so, kuma ba yadda suka iya.

Don ya zame musu kadangare bakin tulu a karka, a kar tulu. A barka ka b'ata ruwa. " Baffa kana ganin abinda yayi ko?" Mikewa Uncle Auta yayi yana faɗin. " Me ya aikata? Ni ban ga wani abin da yayi ba. Ku jawa Khamis kunne ya san limit ɗinsa." Daga haka ya juya ya fita, " ka godewa Allah da ita yarinyar tana wurin, shi din yasan darajar jini da ace bata wurin daga abinda ka yi ta fita tow wallahi inda zaka yi fitsari na sai an daura maka leda! Kayi kazamtarka a idan aka baka dama banda inda yake karewa domin mutuncin kansa. " Inji Ubaid, sannan ya fita daga cikin gidan. Waɗannan mutane biyu sun yi kaurin suna wurin kare Turaki.

* Karfe uku da wani abu suka shigo, bata nan bai wani damu ba. Haka ya wuce Taj yana bin bayansa koda ya shiga office ya samu ta ajiye mishi printing din da ya da ce duk wani abinda ya dace tayi. Cire jacket din yayi taj yana me amsa ya rataye mishi ya ce mishi." Oga na ga ta gama aikin saura kaɗan ne?" Tsayawa yayi yana kallon aikin da tayi. " Daga ina aka turo wannan abin? " Ya d'aga wani bunch na white paper, wanda har da pin ɗinsu tayi. Dauka Taj yayi ya fara dubawa. " Oh My God! Daga office din Badr ya fito ba sakon nan ba ne?" " Kira ta" ya fada a hasale, fita yayi da sauri yana zuwa ya samu har lokacin bata dawo ba. Shi kuwa sai cira yake ya ɗan zauna a gaban table ɗinsa tare da harde hannu a kirjinsa yana kallon kofar. Yana jin wayarshi yana ringing amma bai dauka ba, asalima dauke kai yayi yana kallon kofar.

Taj kuwa haka yayi ta bi yana nimanta, bai same ta ba sai da ya fito waje ya hangota rike da ledar abinci da kuma daya ledar kamar abu ta sayo mr muhimmanci, a hankali take takawa.

Murmushi nayi lokacin da na ga taj yana jirana, amsar ledar yayi tare da cewa. "Me kika aikata haka? Na bar miki kome amma kika yi shirme haka, yau Allah kaɗai zai kwace ki, domin Oga yana can yana jin rigima a ransa. Hadiye yawu nayi na ce mishi."Me ya faru?" "Muje!" Hannu ya kai zai dauki daya ledar nayi baya da shi. "Wannan dai!" Na fada ina murmushi, amma ni daya nasan yadda nake ji, a hankali nake tafiya saboda zuwan al'adata bazata, kuma nasan yau da gobe zan shiga wani irin tasku ne. "Don Allah ki yi tafiya da jikinki." Kamar ance na d'ago kai, yana tsaye yana kallona, da sauri na sunkuyar da kaina ina tsoronshi sosai. Lokacin da na shiga, cikin building na kamfanin sauran abokan aikin sai dariya suke min, ni ban kula su ba. Haka na wuce na shiga elevator. Lokacin da na shiga jingina bayana nayi da jikin elevator, bakiɗaya naji kamar xan yi amai. Haka muka fita har zuwa kofar office dina, daga shi har ni Dan tsorace muke shi yana tashi ya shiga da ledar hannunsa, nima kuma haka na shiga da na hannuna tare da dunkule shi, kasancewar pad ne a ciki. Ajiye ledar yayi ya dauko min takardun ya ce min. "Mene ne wannan?" Ba tare da kome ba nace mishi. "Sakon da ka bar min na yi printing dinsa shine nayi na turo mishi." "Ba shi bane ina wanda na baki?" "Kamar Ya? Ban gane ba!" Na fada a hankali, ina cizon bakina. "Na bar miki akan table ɗinki fa!" "Ni iya shi na gani wallahi azim ban ga kome ba sai su!" "Tow ina kika je?" Ogan ya jefa min tambayar, kaina a sunkuye nace mishi.. "abinci na je sayowa!" Na fada ina rike ledar hannuna da kyau. "Babu a kamfanin ne?" "Bana son na kamfanin ne!" Sai a lokacin ya zuba min idanu. Kaina a sunkuye, "ko karfe nawa zata kai i don't care daga kai har ita ku hada min aikina ina jiran ku!" Daga ya shuri takalminsa ya bar mu a office din. Haka muka fito na kalli Taj nace mishi.. "kayi hakuri!" "Ba kome dauka aka yi domin na Ajiye miki." Shi kuwa yana fita ganinsa ya fito babu jacket dinsa yasa yan mata dayawa binsa da idanu, ga wani tafiyar da yake ya zuba hannu a cikin aljuhun wandonsa, can tsohon office din ya nufa, yana shiga ya hadu da Badr. Zuba mata sirrintaccen idanunsa yayi cikin wani irin tsinannen kallo me cike da tsana da b'acin ran ya ke bin ta da shi, juyawa tayi ba musu ba tare da ya ce mata bani abinda kika dauka ba, ta wuce ya tsaya a wurin ma'aikata sai gaishe shi suke yana amsawa, Alhaji Abbas da yaji labarin yana wurin ya fito da sauri. "Yallabai shigo mana!" "I'm ok da nan!" Can sai gata nan dauke da takardun, nuna mata hanya yayi ba musu ta wuce ya cigaba da tafiya yana latsa wayarshi. Har office dinsa, kamar yadda ta shiga ta dauka haka ta dawo da shi cike da kunya. ,harde hannunsa yayi a kirjinsa. "Ke ina wasa da ke?" "Am sorry sir! Ba zan kara ba ayi hakuri." Ta shiga bashi labarin. "Na dakatar dake har na tsawon sati biyu!" "Don Allah Hamma kayi hakuri!" "Get out of my sign!" Da sauri ta fito, ni kuwa bawan Allah nan haka ya kira Taj ya kara jibga min kaya, haka har karshe shida ina wurin ga ciwon ciki, shima don bakin mugunta yana office din yaki fita, fitowa yayi lokacin ina amsa wayar Ya Ado. "Ya ina hanya ne hau aikin ya min yawa ne, kayi hakuri gani nan zuwa." Na kashe wayar ina mai binsa da harara "mugu kawai!" Na fada ina jin marana yana ciwo. Taj ne ya shigo yana faɗin. "Muje a sauke ki a gida!" A hankali na tashi na nufi wurin da Abayana yake na saka, zuwa yanzu na san na bata jikina, shi yasa na saka pad din a inda na zauna, lokacin da da muka sauko ina ta Addu'a Allah yasa na zauna a baya, cikin ikon Allah kuwa bayan na zauna kafin na shiga haka na bude sabon pad na saka a inda xan zauna, kamar nayi kuka, bawan Allah nan mugu ne ko saka abin ban yi a jikina ba. Haka na shiga na zauna, ina jin kamar nayi kuka. Har muka isa gida, na dan haska wayata na dauki pad din da jakata na, musu godiya sannan na shiga cikin gidan da sauri, ban tsaya ba ban dakin yara na wuce na wanke jikina na tura Ummu ta dauko min pant da wasu kayan na gyara jikina, ina sauke ajiyar zuciya. Laptop dina gida na dauko nayi login din na kamfanin ba fara aiki. ...... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 50 Da yake ke yana gaba ne shi da Taj har suka isa Taj ya dauki jakarshi ya shiga da shi cikin shi kuma ya wuce masallaci. Taj na isowa ya bi shi suka tafi. Koda aka yi sallah isha taj ya wuce gida shi kuma ya nufi inda motar yake zai duba abu, yana budewa ya kunna wutar motar ya saka hannu ya dauki file din da yake bayan motar, idanunsa ne ya kai kan jinin da yake manne a jikin kujeran. Mamaki ne ya kama shi. A hankali yayi lissafi yau ya zo mata, shi yasa take kome sanyi-sanyi. Kiran Taj yayi ya ce mishi. "Kace yarinyar nan ta zauna sai Monday!" Ya kashe wayar, sannan ya koma cikin gidan ya dauko kayan wankin ya zo ya wanke sit din ya jingina da motar yana nazarin har yau bata daina fama da ciwon cikin ba ne? Shiru yayi yana nazarin lamarinta, duk da yana jin zafinta amma a duk lokacin da ya kalleta sai ya ga kamar tana boye wani abu fuskarta, idanunta yana fadar abinda fuskanta yake faɗa daban. Wayarshi ce tayi ƙara ya saka a kunne. "Oga ban samu numbeta ba, domin bani da shi." "Ok"

Haka ya wuce gidan Ubaid ganin Nihla suka yi ta wasa da Yarinyar amma zuciyarshi tana wani irin yanayi. Bude wayar yayi ya kara bincike ko ya dauki number wayarta yasan gobe zata zo da mood din. Amma bai samu ba abinci ya ci ya nufi gidan Uncle Auta, nan ma fura ya sha yana dawowa gidan ya wuce Gym ya motsa jikinsa. Rabin daren yayi shi akan aiki ne amma bakiɗaya Lubnah ce a ransa.

---- Kusan har gari yayi tsit ina aiki, tashi nayi na dauko faten da wanke na sha. Sannan na zo na kwanta saboda hajijiyar da nake ji, haka nayi barci a wahale ban farka ba sai karfe shida na safe. Na shiga nayi wanka na wanke jikina duk na b'ata zanin gadon haka na hada na wanke da kayan jiya, sannan na shafa mai da body spray. Na saka kaya irinta hausawa saboda yau juma'a ce, pad dina guda goma na zuba a jakar, domin kada a kara samun matsala.

Doguwar riga ce ta atamfa, sai hijab da na saka yadi biyu da rabi da na saka, na fito Ya Ado ya ce min. "Allah yasa kada a koro ki, kin makara." Murmushi nayi na shiga muka fita, a inda ya saba ajiye ni ya ajiye ni, na dauki jakata na wuce na jira motar kamr kullum muka wuce, ina isa na biya tare da fita na nufi hanyar kamfanin, a hankali nake tafiya kaina a sunkuye. Har na kusan kamfanin na ji muryan Khamis, gabana ne ya fadi. Na kalle shi dauke kai nayi na cigaba da tafiya, karar horn da aka yi fa karfi yasa ni juyawa. Yau shine da kanshi ba Taj ba. Daina bina Khamis yayi, ya tsaya matsawa nayi a gefen hanyar yayi kan Khamis da motar ya matsa yana ihu da dariya kamar mahaukaci. Da yazo kusa da ni,sai ya rage gudun motar yadda nake tafiya a hankali, bar na shiga kamfanin haka yake bin bayana, ajiyar zuciya na sauke ashe bashi daya ba ne a motar shi kan ma yana baya, daya mutumin nan ne. Fita yayi a motar ya nufi hanyar waje. Mai tuka motar ya ce mishi. "Kaga ka daina zubawa rauni gishiri." Zuciya ce take cinsa, bai saurare shi ba haka ya fita can ihun Khamis muka ji, bakiɗaya muka fito wajen. Aka yi juyin duniyar nan ya sake Khamis amma fir yaki, sai da nace mishi. "Don Allah ka kyale shi mana!" Ture shi yayi ya juya tare da damkar hannuna. Har office dinsa ya kai ni, tare da cewa. "Daga yau ki tsaya a inda ake sauke ki na gaya miki!" Ya daka min tsawa, shiru nayi tare da rufe idanuna, haka ya fita ya bar ni kamar mayya a office ɗinsa, shigowa mutumin da suka tawo tare yayi ya zuba min harara ya daka min tsawa. "Wacece ke? Me yasa saboda ke yake abinda bai taɓa yi ba!?" Kuka ne ya zo min dai-dai lokacin da ya shigo office, "Tambayar ki nake ba kuka nace ki min ba!" Ya daka min tsawa, "Malam ya isheka haka, ya ishe ka nace!" Ya fada a masifance. "Bai isa ba Turaki nima zaka dake ni ne kamar yadda ka dake shi, wace ce ita da kake fada akanta?" Ture mutumin yayi har waje. "Kada na kara ganinka a inda nake!" Daga haka ya rufe kofar. Ai kuwa nima ya juya ya fara min fada tare da cewa na zo ina juya jikina har maza na kai min yadda yake fadar kamar ya rufe ni da duka, sannan ya koro ni waje tare da kiran Taj ya zo ya kawo min aikin, nasha kuka kamar an yi min mutuwa sannan na cigaba da aikin kamar jaka, na jiya ban gama ba, yau aka kara kawo min wani aikin, jikina har ciwo yake abinci kuwa taj ya kawo min faten wake da soyayyar agada, naci sai ruwan tea, wurin karfe biyu ya fito cikin fararen kaya, da hular da ya karya, sau daya na kalle shi na cigaba da abinda nake yi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull