ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 30
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 30: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 30. Shigowar wasu yan mata na family ɗinsu, ya sani mikewa nace musu. "Sannunku da zuwa, da mai…
4,486 words
Shigowar wasu yan mata na family ɗinsu, ya sani mikewa nace musu. "Sannunku da zuwa, da mai za a taimaka muku?" "Mun zo miki kashedi ne ki fita harkan hamma Turaki!" Kallonsu nake kafin na ce musu." Ayi hakuri ba zan kara shiga harkansa ba!" " Aiki kika zo nan, ba shige mishi ba!" Yadda suka yi ta min maganar banza ni dai ban ce musu kome ba, sai can na ce musu. " Mr Turaki ya saka cctv idan kuka matsa dayawa zai dauki mataki! " Na nuna musu, wurin da camera din yake, sai suka fara baya Baya. Bar suka fita, bayan ya dawo na tattara takardun na kai mishi, ya duba sannan ya watsa min a fuska ya ce min. " Ki gyara basu yi min yadda nake so ba!" " Tow" na kwashe, haka na dawo na zauna karfin hali nake amma ni daya nasan yadda nake ji da ciwon ciki amma mutumin nan ya kara dawo min da aiki ba. Hawaye ne ya zubo min, haka na kara zama na fara sabon aiki karshe ya fita abinsa, shigowa Taj yazo ya amshi aikin yana taya ni, ni kuma na zauna ina hutawa, muka yi ta hira da Taj har ya gama min aikin ya ce min. "Aikin na da wahala amma a madadin sai kin sake type kawai copy and paste zaki yi." " Kamar ya? " Na tambaye shi, ina sani. Mikewa nayi kafin ya bani amsa na wuce ban dakin da aka nuna min, na gyara jikina. Ina dawowa na samu baya nan, sai Masifaffen nan ne a tsaye, " aiki kika zo ko yawo?" Kasa magana nayi ina kasa domin kwarjini ne da shi, baka iya tsayawa ka kare mishi kallo. Kamar nayi kuka haka na wuce bakina yana rawa nace mishi." Toilet! Banza ya bawa ajiyata yayi gaba abinsa, takaici ne ya kama na cigaba aiki har karfe biyar da rabi, na mike zan hada kayan fitowa yayi fuskarshi a haɗe yayi tare da kafe ni da idanu, diriricewa nayi na fara niman inda zan tsaya kawai sai na koma na zauna, ba magana ba zagi amma wannan idanunsa masu kama da na dodanni, sun iya hukunta mutum. Haka na cigaba da aiki har karfe shida ya wuce. Ina wajen, ban san lokacin da hawaye ya fara zuba min ba. Haka na cigaba da aikin ina kuka. " Lubnah! " Naji muryan Jasminah, d'ago kai nayi ina kallonta na fashe da kuka. " Taso muje!" Haka na taso ina kuka, " ina zaki kaita?" " Bro lokacin tashi ya wuce fa, idan aikin ya mata yawa." " Koma ki cigaba da aikinki" haka na koma na zauna tare da cigaba da aiki ina shashekar kuka, ya juya ya banko mana kofar. Ya cigaba da aikinsa, ina ta kallon wayata ko Ya Ado zai kira ni, amma bai kira itama Jasminah Yaranta suna ta kiranta, haka ta mike tana gaya musu. "Gani nan zuwa!" Kallona tayi ta ce min. "Hankalin Yaran ya tashi." Cikin dauriya nace mata. "Ba kome!" Na fada tana barin wurin na kurawa kofar office ɗinsa idanun ina jin wani irin haushinsa, haka na dauke kai na cigaba da aikin har na kammala na koma ban daki na gyara jikina koda na fito babu kowa kusa fitilar wurin a kashe office dinsa ma hasken a kashe, da sauri na tafi wurin zamana na kunna wayata, ina d'ago kai muka yi ido hudu da shi, wani irin kara na sake tare da wurgi da wayata. Zube a kasa tare da rike kirjina da amsa min da wani irin ciwo. Ina haki kunna wutar parlourn yayi ya tsaya tare da hade rai. Kuka na saka ina zaune akan gwiwata. "Ina da abin yi." Wato yana jirana, da sauri na mike na hada kayan da na zo da shi. Na bi bayanshi da sauri domin ya kashe wutar parlourn, garin binsa haka na yi karo da bayansa cak ya tsaya nima nayi, tare da ja da baya. Ina jan hancina na ce mishi. "Sorry sir sorry Sir." Cigaba yayi da tafiya nima na bi bayansa. Har muka shiga elevator, tsayawa nayi can bayanshi ina sunkuyar da kaina har muka fito kasa. Sai da muka fita aka rufe office din bakiɗaya. Wurin motarshi muka nufa baya shiga, ni kuma na shiga gaba. "Har kun taso?" "Eh!" Na cewa Taj da ya tambaye ni, "kamar kin yi kuka?" "A'a ban yi ba!" Na fada, zai kara magana Masifaffen nan yayi gyaran murya, haka muka cigaba da tafiyar har muka iso gida, fitowa Taj yayi ya bude boot din motar ya ciro min wasu paper Bag har guda uku, ya ce min. "Inji Oga gobe Saturday akwai meeting din da za a yi a Eko hotel da fatan zaki shirya da wuri." "Har Saturday ma akwai aiki ne?" "Eh amma ba wai na office ba. Wasu mutane ne zasu sayi kayan kamfanin yana da kyau ki shirya da wuri!" "Gaskiya!" "Tow ni yau xan tafi Abuja akan meeting, idan ya ji kina musu tura ki kano zai yi!" Jin haka yasa na ce mishi. "Tow shi kenan!" Mishi godiya tare da shiga cikin gidan, Ya Ado na samu yaran sun kwanta, Aunty Zakiyah tana kitchen, gabansa na je na zauna. "Yaya na gaji aikin nan ba irin nawa ba ne!" Na fara mishi kuka. "Mutumin nan bai da imani, kome nayi fada yake min, ba halin nayi mistake yayi ta faɗa kamar ni daya ce na fara kuskure." Murmushi yayi ya ce min. "Haka kowa yake farawa, sannan ai ya kira ya gaya min yau da gobe kuna da ganawa da wasu yan kasuwan kasashen ketare, shi yasa ba zaki dawo da wuri ba." Sake baki nayi ina kallon Ya Ado wato Masifaffen nan ya san kan duniya ya kira Ya Ado ya kare kanshi, kada ace na jima har da fada mishi aikin da muke da shi gobe. " Ni dai ba zan je ba!" Na fada ina kuka. "Tow shi kenan!" Ya fada yana kallon kayan da ba shigo da shi, kusan kayan ci ne sai pad. Da sauri na maida shi cikin na wuce dakina na can sama na wanka na shiga nayi sannan na fito na gyara jikina, na fito na ci abinci sannan na dawo na rage sauran aikin na kwanta. Wayyo Allah dad'i nayi barci har karfe tara na safe, don cikin dare da na sauya pad na koma na kwanta ban kara bude ido ba. Sai da na ji ana buga min gadon na bude idanuna." Kin yi baki suna parlour." " Baki kuma? Su waye?" Na tambaye ta bata kula ni ba tayi tafiyarta, hulata na dauka na saka akan riga da wando na barcin da yake jikina. Ban daki na shiga na yi brush na wanke fuskana sannan na fito,. Na sauko kasa ina faɗin. " Kuma dai weekend din ma ina murna na rabu da jarabar wancan Masifaffen mutumin me kama da yan damben turawa....... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 51 "Fisabiilillahi ko a gidan gwamnati Asabar da Lahadi hutu ake. Ni yanzu ko Gym na daina zuwa tunda na fara wannan aikin me shegen wahala waye ya sani ko sai na gama aikin ma karshe a ce za a kore, Aunty Mutumin nan ya cika barga, haka ya min shekaranjiya wai zai kore ni, ko jiya oho. Kin ga yadda ke tafiya kamar wani robot" Na sauko har parlourn, ina kwaikwayar tafiyarsa, kawai kamar ance ns duba kujeran da yake kallon tv, da sauri nayi baya ina faɗin. " Innalillahi! " Nayi baya ina toshe bakina, kafin na juya da wani Muslimin gudu aikuwa na ji abu ya kwashe ni sama, na hantsila tare da dokuwa da kasa, takalmina kafa daya yayi tsalle sai a fuskarsa, Allah ban san lokacin da na ce. "Na mutu!" Na tashi na haura sama da gudu, ina fadin shi kenan. Abin ya zo wani iri amma kuma Ya Ado sai da yayi dariya yana faɗin. "Silly girl, don Allah ka yi hakuri bamu san zata fito tana mocking dinka ba don Allah ka yi hakuri!" Murmushin yake yayi yana faɗin.. "Muna jiranta." Ya saka kai ya fita, bai san dalilin da yake son ya ganta a kusa da shi ba. Bai sai me yasa yake jin haushinta ba, amma a duk lokacin da ya ganta yana jin kamar ita din da ya sani can ita ce a gabanshi. Sai dai ita wannan ta sauya dayawa. Fitowa yayi waje, wato asalin yadda aka yi ya shiga cikin gidan, ya zo ya tsaya tare da tunanin wanda zai tura cikin gidan sai ga Ya Ado ya dawo daga Gym da yake weekend yana zuwa, kawai sai ya ganshi a kofar gidan, har zai wuce sai ya dawo ya mika mishi hannu suka gaisa ya ce mishi. "Kana son ganin Lubnah ko?" "Eh" kawai sabo da a fakaice kallon Ya Ado yake yason ya ga ko mijinta ne amma wani abun mamaki sai ya ga suna kama da Lubnah, sai ya kauda kai har ya ado ya ce mishi zai duba ko ta shirya, yana zuwa ya samu tana barci shi ne ya fita tare da shigo da shi cikin gidan. Shine ta mishi rashin mutunci. Lashe bakinshi yayi yana godewa Allah da iya shi kaɗai yazo bai dauko wani ba, balle ya sha kunya.
Tunda na shiga nake jin kamar zuciyata zata kwace a kirjina, "wayyo Allah na!" Na fada a hankali, kamar xan yi kuka. Buga kofar aka yi daga waje Ya ado ya ce min. "Ki fito yana jiranki, kuma zaki sani ba dai bakinki bai da lizami ba" bude kofar nayi da karfi ina faɗin. "Ya ado kun san shine ya zo, ba ku gaya min ba." "Je ki shirya yana jiranki ai ba zai nuna miki ya ji me kika ce."
Kamar nayi kuka haka na haura nayi wanka na shirya tsaf, sannan na dauko abaya na saka tare da daura hula kafin na saka gyale na nad'e kaina. Haka na shirya ina fitowa Aunty Zakiyah tana mika min wata yar jaka tana faɗin." Baki karya ba, gashi nan ki karya a can." Kamar nayi kuka haka na fito kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki. Har waje na fito yana mota, ina zuwa na gwada bude bayan mota amma a rufe gaban na zaga na bude na zauna. Kasa kallonshi nayi domin sai yanzu nake jin abin a raina, har ya tashi motar ban iya ce mishi cikanka ba. Ni kaina kamar na nutse kasa, haka ya cigaba da tuki cikin kwarewa. Wani unguwa muka isa wanda yake bakin ruwa. Yayi horn a bakin kofar gidan. Aka bude kallonshi nayi naga fuskarshi a haɗe kamar yaga hadiri. Haka ya shiga cikin gidan, aka zo aka bude kofar inda yake aka yi tare da inda nake. Haka ya fito, "kafin ki samu abin zagina ki hado kome yana baya!" Kamar ba fasa ihu haka na ji, a hankali na dauki kayan na bi shi da su. Wani kwali ne mai kyau sai wani jaka paper Bag, muka shiga cikin gidan. A hankali nake bin bayanshi, har muka wuce ta wani lambu kafin muka isa babban fili manyan mutane, kamar na juya saboda yadda ake kallona tare da da shi. Yatsawa yayi kamar zan yi tuntube ya ce min. "Ki nutsu! Bani kayan!" Mika mishi nayi muka jera tare har zuwa cikin wurin da ake a taron, suna ganinsa bakiɗaya suka mike suna ta tafawa ana faɗin gashi nan ya zo. A hankali yake kutsawa wurin manya mutanen da suke can gaban, ni kuma na tsaya daga dan baya baya. Juyawa yayi ya hango ni ina tsaye a gaban wasu table. Kallona yayi irin kallon meye haka? Kawai sai na taka wurin da yake na isa, mika min hannu wani mutum yayi amma ban bashi hannun ba, yadda ya bi mutumin da wata lalatacciyar kallo yasa ya koma nan aka gabatar da abinda ya haɗa su, sannan suka fara jawabi, tare da tsaya akan abinda ya tara su. Ina jinsu kusan akan taron karawa juna ilimi akan kasuwanci ne, sai wasu fiyale da aka saya, har aka gama maganar ina tsaye, kusan awa daya muka yi kafin aka tashi muka fito, sai hoto ake da shi, a yadda yake hade rai da nuna baya son na shiga hoton na koma can, Masifaffe kawai, na fada a raina. Muna gamawa da wurin muka wuce Eko hotel, kafin mu bar wannan guest house din ya mika min table tap din, wayarshi ya shiga kira, bayan ya kira aka dauka "Sir kana tare da ita ne?" "Hmm!" "Lubnah dama kin san jiya na gaya miki zaku Meeting tow ki duba abubuwan da zaku tattauna a wurin meeting din, yana cikin table tap din na shirya kome!" "Ok na gode!" Bai jira me zai ce ba, ya kashe wayar. Haka na cigaba da duba tap din wani abu da na fahimta shine yadda yake tuka motar a hankali kamar ba zai isa inda zamu ba, yana tuka motar yana kallon agogon hannunsa. Ganin na ɗauki biro da takarda a cikin jakata na fara rubuta abin da ya dace ina gamawa na ajiye mishi tap dinsa, ai kuwa da azabar gudu ya ja motar muka bar titin, lokacin da muka isa saura minti biyar a fara taron, yana tafiya ina bin bayanshi har inda za'a yi taron, tunda muka shiga ya samu wuri ya zauna aka fara dogon turanci nan, aka fara gabatar da kai, nima na kalle shi ya dauke kai, sannan na gabatar da kaina. Sannan na fadi abinda ya kawo. Bayan na gama na zauna. Cikin abinda bai wuce minti talatin ba, aka fara gabatar da abinda ya kawo an sayar da kayan shi akan kuɗi me yawan gaske wasu yaci riba wasu ya fadi sosai, kuma dama kasuwa ta gaji haka, amma ribar tafi asarar yawa, yana gamawa. Muka fito , wani dan kasar China ne ya ce mishi. "Mr Turaki ko zaka zo mu ci abincin rana ne?" Sai lokacin na tuna fa na zo da abinci, "Mr Ma na gode." "Haba ko ita ba zata ci ba!" Kallona yayi ya ga yadda nake kauda kai. "Itama!" "A'a Mr Turaki barta muje ta ci!" Haka muka wuce aka kai mu wani wurin cikin abinci irin VIP nan! Wurin ya hadu kamar me iya haduwa zama nayi, aka kawo abincin hatta yadda abincin yake tururi sai da ya sa naji cikina yana wani irin ƙara irin ina jin yunwa. Kallonshi nayi na kai hannuna cikin, bai wani damu da ya kalle ni, abincin ya fara ci ina kallon abincin, "Dig!" Ya ce min, haka nayi ta juya abincin ina hadiye yawu, tashi yayi tare da barin wurin, da sauri na fara cin abincin, ina ci ina kallon ta inda ya bi kada ya dawo ya samu ina ci, na kai loma kenan na hango, haka na ajiye cokalin. Na bar abinci me shegen dad'i. Da yazo ya ga yadda na ci ba sosai ba, haka ya ce min. "Zan tafi fa!" Mikewa nayi kamar na juye abincina, sau biyu yana kamani ina kallon abincin har ga Allah ban koshi ba, haka yayi gaba abinsa, sai da muka shiga mota sai ga masu aikin wurin sun kawo min leda me dauke da Chinese dish, kallonshi nayi naga shi ba ma tani yake ba, a hankali na risina ina faɗin. "Na gode!" Daga nan bai tsaya da ni ko ina ba sai Lekki. A kofar wani hadadden gida ya tsaya, fitowa yayi yana mai nufar cikin gidan nima na bishi, muna shiga Yaran nan suka lullube shi da murna, suna ganina suka fara ihu. Haka na shiga na same su, ya fita ya shigo da ledojin nan, daga nan ya juya yayi tafiyarshi. Cikin gidan muka shiga ina tambayar su. "Ina Mamanku?" "Ta tafi Kumo Family Mansion" abinci na juye mana muka ci ina kallon yadda suke ta wasa da abincin, na ce a raina Yaran attajirai fa haka suke basu damu da abinci ba kamar irinmu yan medieun class, kazar guda ce muka ci rabi me aikin ta dauki sauran ta saka a frij, muka cigaba da hira har bayan la'asar da malaminsu ya zo, sai lokacin Mamar ta shigo tare da shi, tana kuka idanunta yayi jajjur ganin yadda bakiɗayansu suke kallona yaushe nazo. "Ke me ya kawo ki?" Kafin na bashi amsa ya shigo yana waya , da hannu ya min alama da na fito mu tafi. Haka na fita muka wuce gida, kular abincin da nazo da shi na dauka sai nayi wayam, babu kome a ciki, s hankali na ajiye ina satar kallonshi, wani hade rai yayi irin baya son wasa, lokacin da muka isa gidan na fita tare da ɗaukar kular na rufe mishi kofar, na shiga cikin gidan. Ina shiga cikin gidan na zube a parlourn ina nishi, na gaji sosai. Duk da ban yi wani aiki ba amma kuma zama wuri ɗaya ya dame ni. Da wuri na kwanta bayan mun sha waya da Mama, kai na ji dadi.
---- Wato wani irin rigima ake a family house ɗinsu, akan Jasminah sun matsa lallai sai ta koma dakinta , ko kuma ta bawa Fahad Yaransa. Ita kuma ta ce sai dai ta mutu da ta bashi Yaranta, akan idanunta ma aka yiwa yarta fyade. Wannan abin ya tab'a Turaki, don haka ya ce a shigar da maganar kotu domin ta bata damar rike Yaranta, uwarta kuwa ta ce idan ta haifeta kuwa ta kai Fahad kotu, sai ta mata baki shine, abinda ya d'aga mata hankali, wani irin kuka take wanda yake damun dan uwanta. Yana ajiye Lubnah ya wuce gidan Noma family, ana cewa gashi nan ya zo a lissafinsu ya zo basu hakuri su kyale ta, sai dai lissafinsu bai zo yadda ya dace ba, domin yana shiga gidan da shi da Barista Abdul Hakim, wanda ya samu yana jiranshi a kofar gidan a tare suka shiga cikin nan, yan gidan na ganinsa suka fara dariya, zama yayi ya ce. "ina son ganin Alhaji Noma." Fitowa Dattijon yayi yana wani buɗewa kamar kifi ya samu wurin zuba kwai, yana kallon Turaki gabanshi ya fadi amma kuma sai ya dake har ya shigo cikin parlourn ya zauna. "Na ji ka kafa dokar ko Yaran Jasminah ko dakin Mijinta." Tashi turaki yayi yana kallon parlourn bakiɗaya ya ce mishi. "Ni kuwa sai naga kamar wannan gidan da duk abinda Noma yake da shi, aro Alhaji Haris Kumo ya bashi domin akwai sa hannun a wurin nan...... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 52 Ya mikawa Barista abdulhakim hannu, sai ga takardu. Da aka saka abu kusan shekaru ya kalli Baristan ya ce mishi. "Amma kasan takardun nan sun yi kura? Dai dai kuma kome tar kamar yanzu aka saka hannun!" Ya fada tare da kardakade takardan, yana mai daura takardan a kan table, ya kuma d'ago kai ya kalli Alhaji Noma. "Na baka awa ashirin da hudu ina bukatar kudin nan, ko kuma kilu ta ja bau, idan" daga haka ya mike zai fita Alhaji Noma ya ce mishi. "Me kake bukata?" Shafa sajensa yayi yana kallon kanshi a madubi. "Duk wata matsalar da yake kunno kai a kashe ta ta hanyar da aka bi, ko kuma ni na kashe ta, ta irin wannan hanyar?!" Ya fada yana d'aga kafad'arshi. Yadda ya juya yana faɗin. " Ina da thousands of this copys" sannan ya juya ya kalli mutumin da akalla zai yi sa'ar Babansa ya saka yatsu biyu ya saka a saman idanunsa alamar ina kallonka, daga nan ya wuce yana mai barin gidan shi da Barista abdulhakim, " Amma baka niman zaman lafiya, yanzu kana ganin haka zai yi aiki?" "Sosai kai, zuba idanu ka ga ikon Allah." Daga haka suka rabu.
Kamar yadda ya shiga tsakaninsu, haka lamarin ya mutu kamar daukewar wuta. Ai idan kana da kudi babu abinda ba zai yiwu ba, sai ikon Allah. Da wannan Jasminah ta samu zaman lafiya, Fahad ya kirata ya ce ya janye ta rike Yaranta idan yaran suka samu lokaci su zo hutu, ta amince aka kashe maganar bakiɗaya kamar bai tab'a faruwa na, dama ai zancen kenan.
*** Kallon Ya Ado da yake waya da Ya Umar yake tambayarshi. "Na shiga maganar ne domin na kara nisanta ta da shi, sannan yadda suka yi juya hankalin Abba yasa na shiga lamarin amma idanun kamfanin yana kanshi a duk inda yake saboda sun ce suna da case nasu a kasa tow sai CEO din ya kama shi yana ƙoƙarin cutar da ita ba wani abu ba ne, shi a nashi lissafin ya razanata ne ta amince da shi, amma akwai wani abu da na fahimtar da nayi mishi, kamar akwai sanayya da juna!"
Kallon Ya Ado nayi da kyau kafin na kara mai da hankalina, kafin ya gama wayar anan na fahimci wato da wancan Masifaffen rufe shi yayi, da yadda aka fito da shi, sai na ji kamar ni aka ceto daga farmakin Ya Hafiz. Tunda na ji haka sai na ji mutumin ya ɗan yi abin arziki, kuma sai ban damu da na ji wani abu daga gare shi ba, washi gari ya kama Monday, sai da na jira Ya Ado ya sauke ni,da wuri na isa na fara aikin da na ga an jibga min, sai da na harari kofar ya kai sau goma, ina tura baki gaba. Tun karfe takwas nake abu daya har wurin karfe goma da ya shigo, na tashi na bi shi na karanto mishi menu na yau bakiɗaya. "Yau bana son ganin kowa!" "Ok sir!" Na fito na cigaba da aikina wurin karfe sha biyu saura wasu mata shigo da sauri na fito na gaishe tare da cewa. "Yau ya ce ba zai gana da kowa ba, yana da aik...." Saukar wani gigitaccen mari na ji a gefen fuskana, wanda yayi daidai da fitowarshi zai fita. Ban san wacece ita ba amma yadda ta mare ni, ya saka ni jin wani abu. "Me tayi miki?" Ya tambaye ta, "Ubanta ne ya gina kamfanin da zata dakatar da ni!" "Ba Ubanta ba ne, amma Ubana da Uwata suka tsayar da kamfanin haka,. Kin yi dacen na fito da sai ta rama domin na gaya duk shegen da ya taɓa ta ta rama!" " Ni ce shegiya?" Gefenta ya bi ya wuce, ta kama ihu da fada akan ya kashe mata auren yarta, ni dama tunda na ganta nasan ba arziki ya kawo ta ba, don haka ban wani damu ba. Ganin yadda Jasminah ta zo tana kallonta cikin fushi da b'acin rai. " Na rantse da Allah, idan baki rabu da shi ba sai nayi ruined rayuwarshi." Duk yadda ta kai da dakewa, sai da ta ce mata." Ba zaki iya ba, tun yana Yaro kike kokarin haka me yasa baki yi nasara ba, rayuwarki xa kika cika shi da karya da yaudarawa babu abinda kika sani. Anya ke uwa ce? Shi bai tare miki kome ba, ko ba kome zan ji kamar Abba yana raye!" Rike ta nayi ina girgiza mata kai, ina faɗin. " Kada ki. Aikata haka, Uwa ce ba a wasa da lamarinsu. " Kwace hannuna tayi tana faɗin." Kyale ni na gayawa wannan matar Abinda take aikatawa, da fari ta ci Amanar Mss Annah A'ishah kasancewarta sakatarinyarta, tsiyar ka dauko mutum daga poor background ka ja shi jikinka kenan, wannan masifar da bakin ciki na talauci da haushin masu arziki... " Tass aka dauke ta da mari, wanda ya nuna mata yatsa, tsabar ya bani tsoro haka na koma gefe na na tsaya ina zare idanu. "Ki girmama ta, koma me take miki." "But she hate me! Bata kaunar farin cikina, idan na kara haduwa da ita sai na kashe ta, wallahi i will kill you;" daga haka ta bar wurin ni dai sai na zama yar kallo. "Duk yadda ka shiga rayuwar wani kai ma sai an shiga naka, bar ganin Allah ya baka aron numfashi ka zata ya kyale ka ne, ni bana bukatar fansa iyayena. Amma ki sani akwai wani Yaro a garin Kano mai suna Khalid yana nan zuwa." Daga haka ya wuce ya barta a tsaye a matuƙar razane, domin bata kawo Jasminah zata yi magana ba, har zai shiga cikin office dinsa ya ce mata. "Daga yau kada ki kara shigo min office har ki Mari sakatariyata!" Sannan ya shiga cikin, sai da suka bar office din ya kira ni ta wayar landline, na amsa tare da shiga office din, d'ago kai yayi na wani lokaci kafin ya ce min.. "Mijinki yana dukarki ne?" Maganar tazo min a bazata sai nace mishi. "Me ye?" Wani haɗe rai yayi yana min wani kallon bana son renin wayo. Tura baki nayi ina dauke kai. "Ni kin iya min rashin kunya amma su da suke marinki, baki iya ramawa ba!, daga yau duk wanda ya kara miki kallon banza ki rama idan kika kara sakewa wani ya mari wannan fuskar naki sai na kore ki! Kin ji ko?" " Hmm!" Nace ina tura bakina gaba. Bai kara min takaina ba ya nuna min hanyar waje, bakin da yayi aka kira ni daga kasa aka gaya min. Na je na tarbe su, sannan na dawo na kai su dakin Meeting na koma zan shiga elevator, ina shiga Khamis yana shiga, wani irin tsoro ne ya cika min rai, na koma gefe na tsaya."ki bani abinda kike bawa Oganki mana." Ni dai ban tanka mishi ba, addu'a kawai nake yi domin wallahi na gama razana, jin yana takowa, na rintsa idanuna da karfi. Jin kofar ta bude nayi saurin xan fita ya dawo da ni, wanda haka yayi daidai da isowarshi bakin kofar. Lashe baki Khamis yayi ina kokarin kwace kaina. "Sake ta!" Amma yaki, kafin ya kara wata magana na gantsara mishi cizo, da sauri ya sake ni yana faɗin. "Na gode da cizon kauna!" Ya fada yana kallonshi, ban san me zai aikata ba, haka yasa ya nufi kofar a fusace shi kuwa Khamis ya rufe kofar da sauri yayi kasa. Da gudu yayi stair na ce mishi. "Ba fa shi bane me muhimmanci, kana da baki masu muhimmanci. Idan ka cigaba da biye mishi kullum sai ya yi abinda zai bakanta maka rai, zuwa yanzu na fahimci duniyar da kowa yake, tunda na fito daga duniyar da ba kowa yake fahimtata ba, don Allah ka kyale shi ka fuskanci abinda yake gabanka, ni ba abinda nayi kawai kwatar kaina nayi! " Kallona ya shiga yi yana son yayi magana na ce mishi." Irinsu haka suke idan aka cigaba da kula su kamar an basu damar yin abinda a so ne, don Allah kayi hakuri ban san dalilinka na jin ba dad'i ba, amma duk da haka nasan don kare mutuncina ne." Daga haka yayi gaba na bi bayansa har inda aka yi taron, ban san mene ne shirinsa ba, amma tunda aka gama taron y sallame ni, na bar office din.