ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 31
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 31: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 31. Daga nan Gym na wuce nayi motsa jiki na na gayawa Aunty Nuratu Kafaya halin da nake ciki. "Ki…
4,194 words
Daga nan Gym na wuce nayi motsa jiki na na gayawa Aunty Nuratu Kafaya halin da nake ciki. "Ki yi hakuri na tsawon wata uku idan baki ga canji ba sai a bar aikin a nime wani ko!" Anan na karasa wuni lokacin tashi na wuce gida, washi gari da wuri na isa office din, sai dai ban samu shiga ba. Saboda wani tsarin da wannan Masifaffen yake ta kawowa, a yanzu ko kazo sai an baka wani kati idan zaka shiga ka nuna, ban san an raba ba da yake da wuri na tafi.
Ina wurin a zaune wata bwn karama ta shigo harabar kamfanin, wani kyakkyawan matashi irin larabawan nan, amma yadda ya fito da fara'arshi, yana gaida kowa yasa na fahimci irin ruwa biyu nan ne, ina zaune ya zo ya zauna a gefena. "Hey Yan mata?!" Ya d'aga min hannu, kallonshi nayi na ce mishi "barka!" Mika min hannu yayi yana faɗin "Tarik Mustapha Takai, babana yana cikin masu hannun jarin Meeting din aka yi jiya, ina shigowa na ga kin yi min! Nice to meet you?!" Ya mika min hannu yana murmushi, kallon hannun nayi kafin na bude baki zan yi magana sai ga motar Masifaffen nan ya shigo, mikewa nayi na tsaya. Shima ya mike yana murmushi. Da dan saurinsa ya isa wurin motar Yana fitowa suka rungume juna, irin sun san juna nan. "Uncle B!" Ya kira sunansa a hankali, daidai na isa wurin na amshi jakarshi shi kuma ya amshi nawa, yana faɗin. "Uncle B taya zaka bawa Miss World jaka kawo na rike miki." Ya kwace min jaka, wani kallon da Masifaffen mutumin nan yake min ya kashe min jiki, haka yasa na ki bashi jakar na amsa har da nashi, koda muka je ya mika min katin na shiga, shima haka. Tunda muka shiga Tarik Mustapha Takai yake wasu abubuwan sai dai ba halin magana, ni kuwa yadda ya like min, sai na ga kamar Masifaffen nan yana wani haɗe rai.
Bayan na gama mishi duk abinda zan yi, na sako kasa na amshi ruwa ashe Tarik ya biyo ni, ai kuwa muka je har wurin abinci da shi, a yadda na tambaye shi shekarunsa ashirin da biyar ne, murmushi nayi nace mishi. "Kai kani na ne, na baka shekaru huɗu don haka ka girmama ni!" Daga ni har shi haka muka yi ta zolayar juna, madadin mu bi elevator, sai ya ce mu bi Stair, haka muka ta bi har muka isa office din, wato bawan Allah nan da ya ce mishi. "Shiga cikin office ina zuwa." Yana shiga ya rufe ni da fada kamar zai dake ni, nayi shiru ban kara cewa uffan ba, don tunda na ce yayi hakuri ya kara hawa yasa na yi kasa da kaina. Bayan ya gama ya shiga, tsabar haushi lokacin tashi bai yi ba na tashi abina, na bar office din.
Wasa gaske sai shakuwa ta shiga tsakanina da Tarik, irin mugun shakuwar nan Yaro ne da bai san kome ba sai wauta da shirme, idan ya zo office kuwa ba damuwa ba ne ya fita ya kashe min kudi, ina zaune da karfe daya na rana aka kira ni a waya da yake ranar asabar ne, na dauka ina faɗin. "Waye?" "Baki yi saving number na ba?" "Sorry na manta ne, Tarik ya kake? Lulu yau ina jin wani irin gajiya ne kuma ina kewarki!" Murmushi nayi na ce mishi." Ayya ai zuwa gobe jibi mun koma aiki!" " Ni dai ki gaya min gidanki na zo!" " Kallon Ya Ado da yake aikinsa na ce mishi. "Ok!" Na mishi kwatance, na mike da sauri na nufi kitchen na fara hada abincin da Aunty Zakiyah ta gama na diba mishi na hada fruit salad, sannan na duba samosa na fara soya mishi, sannan na hada abinda xan hada can sai ga kiranshi. Da sauri na dauki wayar na saka a kunne. "Gani nan!" "Ok gani nan fitowa da Yara!" Haka na fita leke can na ganshi da wata mota ni sai yau na fara ganinta. Horn yayi min na sake murmushi, na d'aga mishi hannu. Yana zuwa yayi parking tare da fitowa da wasu jakukunan, murmushi yayi min ya ce min. "Sorry na tsaya sayan abu ne, ban karaso ba." Girgiza mishi kai nayi muka shiga har cikin gidan, ya ajiye kayan yana gaida Ya Ado. "Tarik Mustapha Takai." Murmushi Ya ado ya mishi ya ce mishi. "SAN Adamu Usman Jama'are." Ya mika mishi hannu. [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 53 Cike da mamaki nake kallon yadda yake son sabawa da kowa, ba tare da b'ata lokaci ba Ya ado ya mika mishi hannu suka zauna ana ta hira, ya kirA Yaran ya mika musu jakunan da ya kawo. " Bata gaya min da Yara a gidan ba, ita na sayawa chocolate!" Irin mutane nan ne masu budaddiyar zuciya, duk abinda suka gani suna so basu boyewa, haka suka yi ta hira yana gaya musu alakarshi da CEO, da gaske kawunsa ne, domin kanwar Uwarsa ta haifi Uwar Yaron, su biyu ta haifa kafin suka rabu ta dauki Yaranta, Namiji da Mace, amma tana Germany da zama shima a can yaron yake jin Kawunsa ya dawo Lagos shine ya biyo shi. Mustapha Takai babban dan kasuwa ne a arewacin Najeriya, irin shegen aure-auren mazan Hausawa ya aurota, ta haifa mishi Yara biyu ganin yadda yake rititata kishiyoyinta suka hanata zama da barazanar zasu kashe ta, shine aka raba auren ba wai don tana kinsa ba ne a'a kawai basu da yadda suka iya ne, da bakinsa yake bada labarin. Haka na kawo mishi abinci da ruwa tare da sobo. Yaci sosai har da santi. Ranar dai a gidan ya wuni da dare bayan isha ya tafi.
Ya Ado ya kalle ni a nutse, ganin ina tattara inda suka ci abincin dare, ya ce min. "Auta Yaron nan yana sonki." Gabana ne ya fadi ya kalle shi, kafin na ce mishi. "Ya Ado yaro ne fa, kuma na girme shi bar irin wannan zancen dan masu kuɗi ne fa." "Eh na sani amma ki dakatar da shi, tunda ba sonshi kike ba." Murmushi nayi na ce mishi. "Kada ka damu!" Haka na ji shi, da na shiga na kwanta ya shiga kirana a waya yana min shiririta. Har lokacin barci yayi na kashe wayar na kwanta. Da safe sai goma na tashi nayi wanka tare da sallah walaha, domin da safe nan na ga jinin ya dauke min, yadda na fito na samu abin karyawa na gama na koma dakin na kunna wayata. Kirana yayi muka shiga waya duk da a takure nake. Amma haka nayi ta kai zuciya nesa. Domin Yaro ne sosai idan yayi wani abu sai dai ka bi shi da fatan shirya. Ranar Monday da muka hadu da shi, ya makale min, haka muka yi ta kaiwa da komowa, Har Kawunsa ya gaji ya ce mishi. "Aiki ka zo ko bin mace kamar bindi." Ban san yadda suka kare ba amma bakiɗaya ban kara ganinsa ba, ni kuwa na sha masifa tare da min fada na daina biyewa shashancin Tarik na kama kaina kowa yana kallona, haka na cigaba da aikina. A lokacin Kanwar Jasminah wato Mimih ta shiga zuwa office dinmu wurin Tarik din, da aka ware mishi office a hawa na biyu amma haka zai tare a wurina. Yau ina aiki sai gashi nan, kallo daya nayi mishi na cigaba da aikina, yana tsaye jikin table. Ya shagwabe min fuska. "Don Allah ki min printing din wannan ki tura min ko ki kawo min." Dama uban Yan masifa baya nan, na ce mishi. "Don Allah ka tafi zan kawo maka!" "Ba inda zan tafi, sai dai ki zo muje yunwa nake ji!" Kallonshi nake bakina a sake kafin nace mishi. "Zaka ja min a kore ni kenan?" "Bari na kira shi." Kiran shi yayi mishi magana da harshen Germany, ban san yadda aka yi ba, ya ce min. "Taso mu tafi na gaya mishi." "Kayi hakuri ba zan bika ba." Na fada na cigaba da aikina, ai kuwa ya ja kujera ya zauna ya zuba tagumi yana kallona, har kawunsa ya shigo tare da yan uwansa, yadda ya hade rai ya watsa min kallon banza, na rasa yadda zan yi d Tarik haka ya dame ni amma shi Masifaffen duniya gani yake ni nake kiran Tarik. "Zan dakata da Yaron nan, domin ya hana yarinyar nan aikinta." Ya fada yana cire tie din wuyarshi sai ga Tarik ɗin ya shigo office din, " Uncle B please ka ce Lulu ta raka ni ina jin yunwa ne!" Yadda yayi rikon sai da yaji kamar ya mutu, domin ya tsani wani da namiji yana like mata kamar wani kaska. "Ba inda zata bika, kai baka ganta bata cika shiga abinda bai dame ta ba." " Ok tunda kai ka ki bari na kira San na gaya mishi." Ya fada yana dauko wayarshi ya kira Ya Ado ya koro mishi jawabi. Ya Ado zuciyarshi daya ya ce shi kenan zai mata magana. Ai kuwa ya juya yayiwa kawunsa bye bye, ya bar office ɗin. Shiru CEO yayi bai san lokacin da ya mike ba, a zafaffe ya nufi waje yana fitowa ya samu suna ta musu, cewa yayi. "Ku zo muje!" Y fada kai tsaye haka na hada kayana, na saka a locker na bi bayansu, haka muka je wajen cin abinci na Chinese dish, nan muka je ya kai mu har can VIP aka yi oda, aka jera mana, ni dai ban wani saba cin abinci a gaban jama'a ba, haka Tarik ya yi ta zuba min abinci domin ya ado ya gaya mishi ina kula da abinda Zanci, sai yake zaba min abinda zanci da kuma wanda ba zai yiwu na ci ba, abun sai ya bawa CEO mamaki yana kallon yadda yake cire duk wani abin da ba zan ci ba, har ya kira waiter ɗinsu ya ce ga irin drinks din da zan sha, sai gashi kuwa an kawo ina kallonshi cike da mamaki. "Ci wannan tsokar kifi ne, zai fi kici irinsu shrimp da danginsu kaza da sauran danginsu ba naki ba ne. Ci iya mune Uncle ya sayi wurin baki daya." Tashi kuwa Uncle dinsa yayi ya dauki abincin ya kai wani table din ya ajiye min ya kara zuwa ya dauki juice din da ruwan ya ce min. "Je can ki ci!" Tashi nayi na je wajen na basu baya, tashi Tarik yayi ya rike hannunsa. "Kasan bana wasa a kalmaina!" Yadda yayi magana yasa ya zauna, ya cigaba da latsa wayarshi ya cigaba da cewa. "Yarinyar nan matar aure ce. A Muslunce kuwa haramun ne bibiyar matar aure. Ina baka shawarar ka koma Berlin ka ji aiki!" Gyada kai yayi yadda yayi mishi magana a nutse yasa Yaron ya fahimta. Haka muka gama cin abincin, sannan muka bar shagon, kamfani muka wuce. Haka na cigaba da aiki. Tunda muka fito naga jikinsa yayi sanyi. Har muka tashi, na dawo ban ga kiranshi ba na tab'a shi ya ce min jikinshi ne baya jin dad'i, haka muka yi magana sama sama, da dare kuwa aikin gabana na rage, sannan na cigaba da sabgogina. Ni dai ban san me ya faru ba washi gari na iso na sami Dan uwan CEO, yana ganina ya hade rai. "Wacece ke?" "Ni kuma?" Daka min tsawa, nayi baya domin a gaban jama'a yake min fada da masifar da na ga kamar gadonta suka yi domin kows a cikinsu Masifaffe ne, "sir mai nayi kuma?" "Ki tafi an dakatar dake!" "Me nayi to?" "Idan baki min shiru ba sai na mare ki!"dariya nayi na ce mishi. "Maybe baka san wacece ni ba, idan ka mare ni zan rama no matter how, zan mara kuma da kake min ihu so what idan ka ce na bar kamfanin ni ban fito gidan da ake jin yinwa ba, ba ina aikin nan don cika cikina da yake jin yunwa ba ne, ba zai yiwu kowa ya zo ya ce zai taka ni ba. Kudi ko daukaka muna da shi a gidanmu I'm not beggar da zaka na min ihu,kudin kamfaninku ba zai saka ni nayi arziki ko talauci ba, so ba kai ka ɗauke ni aiki ba, amma nasan kana cikin waɗanda suka dauke ni aiki." Na juya na cire ID din da yake makale a wuyata, na juya zan fita bayan na ajiye a kan table din Mrs stalle. Idanuna suka fada cikin na shi, dauke kai nayi, a yau na ga wani abu da ban tab'a gani ba, tsoro da tashin hankali. Haka na gyara zaman jakata na wuce zan bar cikin kamfanin. "Ban karbi ajiye aikin ba! Kuma ki same ni a office ina jiranki!"
Sannan ya wuce ba tare da ya cewa Ubaid uffan ba, yadda ya wuce haka abun ta bashi mamaki ya ce mishi. " N dakatar da ita ka dawo da ita?" " Ka rubuto min korafi a takarda sai na san me zan yi." Daga ya wuce shi, nima da na kame a wurin kamar an dasa ni, haka sai naji kamar ban cancanci zama a cikin kamfanin ba, haka na juya na bi bayanshi yana tsaye a bakin kofar elevator, ina zuwa na amshi jakarshi. Bai ce min kome ba, haka yasa na sunkuyar da kai. Har muka isa office dinmu daga nan ya shiga cikin na kai jakar na fitar da menu, sannan na gama na fito na zo na zauna kenan sai ga Jasminah da Badr kallonta nayi na ga kamar na santa.." Lubnah me ya faru? " Nan na gaya mata gaskiya abinda ya faru, shiru tayi kafin ta shiga cikin office din Dan uwanta. Ban san me suka yi ba na ga ta fito daga cikin office din ta tsaya a kaina ta ce min." Ki yi hakuri kin ji matsalar akwai munafikai ne! " Tana barin wurina, Badr ta kalle ni. " Ke mayya ce? " Ta tambaye ni, kallonta nayi nima na ce Mata. " Inda kika ci anan naci nawa" cikin fusata ya d'ago hannu zata mare ni, ai kuwa na rike hannunta, tare da murda shi, domin ba girma ta tayi ba, na murde hannun da karfi sai da yayi ƙara ƙarfi, nace mata. "Kalle ni da kyau ni ba sa'arki ba ce, kika kara zuwa inda nake sai nayi maganinki!" Na ture hannunta sannan na cigaba da aikina, kiran wayar yayi na mike na shiga lokacin har ta bar office din. Ina shiga na tsaya a gabanshi, tare da sunkuyar da kaina, ya zuba min idanu ban san tunanin me yake yi ba. _Yarinyar da ya sani a shekarun baya irin yaran nan ne masu hankali kuzari da surutu tare da Rawan kai da fitina! Yarinyar da kowa na cikin JIBWIS ya santa saboda ƙoƙarinta da kuma rawan kanta! Yarinyar da ta juyawa duniyarsa baya tare da cewa tana da wanda take so yau ita ce a gabanshi a matsayin sakatariyar kai da kai! He can believe ita ce, bai yarda ita din ce ba, sai dai sunanta da ya zame mishi daidai da ayar da ya haddace ya kuma bata matsuguni na musamman a cikin ƙwaƙwalwarshi. Me yake shirin faruwa? Me yake dawo da kome baya? Me ya kawo ta nan? A yau tana gabanshi ne sannan a gobe bai san wani matsayi zai ajiye ta ba, amma ya kasance yana jin motsinta ina Mijinta? Me yasa take tare da bro dinta! Shin ko Mijinta ne baya kasar? Me yasa yake jin wani babban al'amari a haduwarsu, shi dai yasan bai yi kome ba amma me yasa kowa yake jin ba dadi shi ba wani ririta yayi ba bare a ce ya ware ta!_ Saboda wani abu can ba, ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta a karo na biyu, kafin ya ce mata. "Ki duba na tura miki sako bana son kuskure " "Ok Sir!"
Haka na fita na bar shi ba shiga aiki ina printing, hayaniya da ake yi yana kusanto inda muke yasa ni d'ago kai, wani farin bafulatani ni ne ya shigo da yayansa. Cikin girmamawa na gaishe shi tare da sauran Yaranshi, dakatar da sauran Yaranshi yayi ya ce min. "Ina son ganinki." Tashi nayi na bi bayanshi har stair su kuma suka shiga office ɗinsa. "Lubabatu Usman Umar Jama'are ko?" Da mamaki na kalle shi, murmushi yayi ya ce min. "Kina da aure ne?" Da sauri na d'ago kai na kalle shi kafin na ce mishi. "A'a;" murmushi yayi sannan ya ce min. "Oganki ya sani ne?" Girgiza mishi kai nayi. "Ina son ki min alƙawarin ɗaya." "Tow ina jinka, Allah ya bani ikon ɗauka." Na fada muryana yana rawa. "Don Allah kada ki tab'a gaya masa, ki bari shi ya bincika haka da kanshi kin ji ko..... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 54 D'ago kai nayi zan tambaye shi me yasa zan yi shiru? Tow meye alakata da shi? Sai nayi shiru kafin na ce mishi "tow!" Murmushi yayi yana faɗin. "Na gode sai abu daya da nake son niman alfarmanki akai" a raina na ce kuma dai, murmushi yayi ya ce min. "Don Allah kiyi hakuri da shi." Gyada kai nayi, bayan ya gama min magana ya wuce office din jikanshi, murmushi yayi ya zauna akan daya daya cikin kujerun office din, sauka nayi can kitchen na amso ruwa da drinks na fito zan wuce na ji wata tana faɗin. "Wasu ina ganin ba iya golden digger ba ne, har da can ɗinsu na zinari ne." Ban kula ba sai nayi kamar ban ji ba, haka na wuce na haura abina ban kula tasu ba.
Ina shiga office din na ga ya daura kafa akan center table din da zan daura ruwan, kallonshi nayi na ga ya dauke kai, kuma bai dauke kafar ba, a raina nace. *Jarababbe haka dai zaka kare* a fuskata sai na saka a dan gabansu. "Kece Lubnah kawar Tarik?" Murmushi nayi na kalli mutumin da yayi magana, duk da baki ne amma na hango yadda suke kama da Tarik. "Gashi ya ce na baki!" Ya mika min wata paper Bag, sai da na kalli CEO da yake tari, kamar ya kware dole na dauki goran ruwa na bude mishi, yana sha ya ce min. " Ki dauki key mota ki ce Ade ya kai ki Chinese dish ku amso musu abinci. " Nufar wurin nayi na dauka, sakon da ban amsa ba kenan, na bar office din kamar yadda ya ce haka muka amso abincin sai dai abin haushi muna zuwa suna fita, koda muka iso da abinci, wani kallon banza yayi min ya fara faɗa a gaban jama'a. " Wannan rashin kuzarin da kike yi a aiki ta fara isata, akan me baki zasu tafi basu ci abinci ba, wannan ai wulakanci ne. Sai ki je ku raba da mutane." "Haba Turaki kayi hakuri mana, ai nan da inda ka aiketa tafiyar minti ashirin ne, sannan sai da suka tafi ka kira, Yarinyata na var miki sakon abokinki! " Gyada kai nayi ina godiya, a wani gaggauce suna barin harabar zuwa cikin main building na kamfanin, ina cikin kokarin zama sai gashi. Kallona yayi nima na kalle shi a sace sai na ga ya wuce office dinsa, kiri-kiri ya hana ni sakon, har muka tashi ban san me ya kai ni ga magana ba, ina riga shi fita amma yau na tsaya, yana fitowa na ce mishi. "Nace ba, sakon nan ya ce ya bari a office dinka?" Wani irin shiru yayi kafin ya ce min. " Na zubar a dustbin." Daga haka yayi tafiyarshi, haushi ya kama ni kamar na koma office dinsa na dauki kayana, ai zai ga rashin mutunci. Haka na fito na bar office din nima.
A gida sai masifa nake ina faɗin, "Fisabiilillahi an bada sako bawan Allah nan ya kama ya zubar sai kace a kanshi aka saka ni dai wallahi ba zan iya yafewa ba." " Tow me yasa ba zaki iya gaya mishi a can ba sai a nan!" " Ni wallahi kamar dodo yake min ina son na samu dare daya na gurza mishi rashin mutunci." Dariya Aunty Zakiyah tayi tana faɗin. " Allah yasa ki iya!" Abin ba dad'i fa, haka suka yi ta manna min hauka nayi shiru na kyale su.
Washi gari Ina isa na ga Paper Bag a kan table dina, asalima ya riga ni zuwa, dauka nayi na ga flora gown ce mai mayafi, sai turare masu kyau da tsada da kuma chocolate kwali biyu mara sugar da fat, abaya guda biyu. Bayan flora gown din, ban tab'a ba har zuwa lokacin break na mike zan sauka kasa naci abinci sai ga Mrs stalle ta kawo min jakan abinci, ta min tana min wani irin kallon kurulla, ban kula ta ba na amsa ina zauna a kasa naci. Jakar nan dai anan, ina gama cin abincin na tafi nayi alola na zo na gabatar da sallah, ina idar na ji motsinsa, mikewa nayi naga yana kallon jakar yadda ya kalla nima haka na kalla na cigaba da abinda nake, wucewa yayi abinsa, bayan tafiyarshi sai ga Yan matan family dinsu sun zo tare da Mrs stalle da wasu matan office din, suka zo. Daukar jakar daya da na ji ance mata Batul tayi tare da juye shi a kasa, ashe har da wani box na sakar karamin box kamar Pandora, suka yi ta d'aga kayan ita ogarsu ta ce musu. "Ku fito min da shegiya na gaji da ganinta tare da shi." Suna dayawa amma kuma dole na koyo tsayawa kaina, finciko ware din laptop dina nayi dama da kauri. Suna zagayowa na rufe su da bulala karfin hali nake, ganin ina shud'a musu yasa suka fara baya har nayi nasarar kure sannan na juya da gudu na nufi elevator, na danna jin muryansu yasa ni juyawa da baya, daidai kofar ta buɗe. Muka yi wani irin karo da shi, na fada mishi bakiɗaya. Yadda na rikice ban san tare yake da wasu ba, ni dai burina na ceci kaina. Hannunsa nayi a bayana, daidai gadon bayana, dukkan hannu bibbiyu ya rufe ni da shi, kaina a kife a kirjinsa, da xan kwace amma jin kamshin turarensa yasa na nutsu, na kifa kaina a kirjinsa." Ya isa haka!" Ya fada tare da janye ni a jikinsa, ya zuba musu idanu, yana kallon abinda suka yi da kayan da ya kashe kudi akansu. Murmushi yayi ya kalli Ubaid ya ce mishi. "Ban san sunansu dukkan ba, zaka iya koransu a aiki su kuma waɗannan jin da su daya bayan ɗaya." Sannan ya rako ni har wurin aikina, sai da ya ga na zauna ya tsuguna da kanshi ya kwashe kayan da aka zubar ya zuba a jakan, ya dauki sakar ya zuba mishi idanun. Kafin ya mai da cikin boxs din. "Turaki!" Kallon wnada ya kira shi yayi. "Ka yi hakuri!" "Wallahi sai sun bar kamfanin nan ka ji na rantse!" Kasa magana nayi na kalle shi, "sir su bar aikin saboda ni?" Na fada bakina yana rawa, a fusace ya juya tare da cewa. "Kema na dakatar da ke. Tunda dambe kika zo yi a kamfanin." Kafin ya rufe baki na hada kayana, na bar office. A ranshi kuwa haka yake son ganin mace, ba kamar sauran kamar mayyu sai hakuri suke bashi ba. Ina barin wurin shima ya wuce office ɗinsa, Ni kan ba zan iya wannan halinsa ba, misalin uku da rabi na isa gida na huta ban gaya musu me ya faru ba.
Ina samun kaina na kashe wayata su je can da kamfaninsu me shegen matsalar tsiya. Daga nan na rufe babinsa in sha Allah ranar Monday zan rubuta takardan barin aiki.
** Yana tashi don masifa bai wuce gida ba, ya nufi gidan Hajiya Samirah kumo yayiwa yarta duka, sannan ya dawo ya samu Badr itama yayi mata dukar har da ji mata ciwo a hannu, Mimi ma bai kyaleta ba, domin kamar wanda ya sha kwaya haka yake jinsa. Duk yadda Alhaji ELYakub ya so boye b'acin ransa sai da ya yi magana tare da nuna mishi kuskuren da yake aikatawa ai ba a haka, dama already Ubaid ya jima da nuna adawarshi a fili, Uncle Auta ne ya goyi bayansa har ya ce bai ga laifin abinda yayi ba ai ya musu warning me ya kai su wutinsa? Jin haka yasa shi shima yayi zuciya ya bar gidan, kai hatta kamfanin fushi yayi ya daina zuwa aikin.
--- Yau kwana uku kenan da aka dakatar da ni, na rasa yadda zan gayawa Ya Ado, ina Gym na zurfaffa tunanina sai jin wayata tayi ƙara, dauka nayi na ga alart har na dubu dari uku da hamsin an saka salary, daga KPAN, mamaki nayi albashina na farko kiran Mama nayi na gaya mata ta ce na kira Ya ado na gaya mishi, nace idan na koma gida zan gaya mishi, haka kuwa aka yi ina komawa gida na nunawa Ya Ado shi kuma ya karbi kudin ya turawa Mama dukka, ya tura min dubu hamsin ya ce min. "Wannan ni na baki, wancan kuma a bar mata tayi yadda take so da shi." Murmushi nayi ina faɗin. "Allah ya kara budi."