ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 32
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 32: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 32. Ranar wuni nayi cikin farin ciki, washi gari da safe ina motsa jiki a parlourn aka buga gidan…
4,125 words
Ranar wuni nayi cikin farin ciki, washi gari da safe ina motsa jiki a parlourn aka buga gidan da kaina na fita na duba, Jasminah ce. "Laa aunty kece!" "Eh gani nan sauri nake, don Allah ki taimaka mana Oganki yau kwanansa kusan hudu baya nan baya zuwa office ko zaki tab'a mana shi a waya!" Sosa kai nayi ina yake nace mata. "Aunty bani da number shi?" Zare idanu tayi nima abin sai nayi ya min wani iri, shiga motarta tayi ta rubuta min number ta bani tana faɗin. "Don Allah ki taimaka mana!" "In sha Allah!" Sannan ta juya abinta, ni kuma na shiga cikin gidan ina tunanin yadda xan kira shi. Tow me ya faru da ya bar gida? Mutum sai kace mai aljanu. Parlourn na shiga na zauna ina tunanin, kafin na haura sama. Wayata na dauka nayi shiru ina ta tunanin yadda xan kira shi, a hankali na saka number nayi shahadar kuda na kira Number, har ya gama ya tsinke bai dauka ba, haka na kira bai dauka ba, sai da nayi kira na uku sai gashi ya ɗauka. Muryanshi very calm kamar bai san me yake faruwa ba. Na ce mishi. "Dama na ga sakon kudi ne jiya!" Sai nayi shiru can na cigaba da cewa. "Dama ina son nayi submit takardan barin aikina ne." Na kashe wayar, ina kashewa kuwa ya biyo kiran. "Me aka miki zaki bar aikin?" Kashe wayar nayi bakiɗaya, na sauke ajiyar zuciya ina kallon wayar da nayi switch up dinsa, ina zaune a wurin Adil ya shigo da gudu yana haki. "Aunty Lulu ki zo kin yi bako!"zare idanun nayi na ce mishi. "Baba gaya min waye?" "Wannan wanda Abba ya ce oganki ne!" "Shi kenan!" Na fada a raina, kafin na saka jalbab na sauko kasa, ina jin wani abu yana yawo a kaina. Wucewa kitchen nayi na dauko kunun aya da sauran breakfast din da aka yi na dumama masa ce fa sauce din kodar saniya, na kawo mishi a hankali na jera mishi. Sannan na ce mishi "ka kaci!" Ba musu ya saka sannu ya fara cin masar da yake miyar da dan yaji tari ya fara na bude mishi kunun aya na zuba mishi ya sha, sannan ya kalle ni, kafin ya ajiye ya cigaba da cin masar, har zuwa lokacin bai ce min uffan ba, nima kuma ban ce mishi ba kaina a sunkuye, nayi mamakin da yaci abincin sosai, ya ce min ya koshi, na tattara kayan na kai kitchen, na dawo na zauna a can gefe. Shiru muka yi kafin ya ce min. "Gobe ki dawo aiki!" "Tow Allah ya kai mu!" "Amin Ya Allah!" Daga haka ya mike zai fita ya ce min. "Yaranki nawa? Mijinki yana ina?" Bai tsaya jiran amsata ba yayi gaba abinsa, wannan dan renin hankalin, shi kuma haka yake rayuwa kamar me aljanu.
Bayan tafiyarshi Ya Ado ya fara zolayata, "wato Lubna baki da mutunci, don kina son ganinsa shine kika kira shi." "Ni wallahi ba kiran shi nayi ba!" Na fada ina tura baki, dariya yayi suka yi ta tsokanata. Washi gari. Na same shi a office din ne. Ga sabbin ma'aikata, da gaske koran wadancan yayi. Gaisawa muka yi da wata ina ga irin kabilun arewan ko yar Kaduna ko yar Jos, sai dai ban gama tantance ta ba ta ce min. "Sunana Sarah daga Gombe ƙaramar hukumar kaltungo." Murmushi nayi nace mata. "Lubabatu daga Bauchi, karamar hukumar Jama'are." "Allah sarki akwai yar uwata Ayrah tana sama wurin CEO!" Gyada kai nayi nace mata. "Da kyau bari na isa office din!" Na wuce sama, kofar dama a rufe take, sai da na ajiye kaina na kunna table tap, na shiga office. Matar da na hango tafi Sarah a shekaru, cikin girmamawa na gaishe ta sama sama ta amsa sannan na gaishe ya amsa yana aiki na fara zayyano mishi abinda yake da su a a yau, ban gama ba sai ga Tajudeen........ [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 55 Murmushi nayi na juya ina kallonshi, a hankali na ce mishi. "Nayi kewarka!" Murmushi ya sakar min ya wuce gaban Masifatu ya ajiye document ɗin da ya kawo, sai lokacin na mai da hankali kanshi ashe ya shaka, wani irin kallon rashin mutunci yake min, yayi shiru rubutu yake a laptop ya rufe ta da karfi tare da mikewa ya fita ya bar ni nan tsaye, anya mutumin nan bai da aljanu? Fitowa nayi na same shi yana magana da Taj, wucewa nayi dan zauna ya ce min. "Kin gama report din ne?" Kallonshi nayi cikin mamaki yanzu fa ya fito a office din, ban gama ba sannan ya zo yana tambayar na gama nima share shi nayi kamar ban ji ba, mamaki ya kama shi. Na kuwa hade rai domin ga irin kallon da matar take min na kusa da shi. "Ina jiranki a mota!" Ya saka kai ya fita sai da na gama abinda zan na taso na nufi kasa, don ma na bashi haushi stair zan bi ba zan bi elevator ba, kuma a hankali nake sauka ya jima bai kore ni ba. Sai da na shafe minti goma kafin na iso, na hango Taj yana ta leke ta ina xan fito. "Gani ta nan!" Na fada ina nufar hanyar waje, ina zuwa na same shi ya cika kamar balloon, sai kallon agogon hannunsa yake, hango matar nan da nayi sai na koma gaba na zauna kuma ai dama gaba nake zama, muka dauki hanyar inda zamu. "Sir maganar zuwa Japan din yana nan ne?" Shiru yayi yana kallon table tap din da Taj ya mika mishi. "Kamfanin Rivers sun tara kayan sosai, dole sai an je da su Japan." Shiru yayi sannan ya ce mishi. "Na Kano ma haka, Abuja babu kayan gaskiya." "Ka shirya tafiyar har da sakatariya." Jin an ambace ni yasa na juya na kalli Taj," tafiya ina? Har da ni kuma?" " Eh ai aikinki har da tafiye-tafiye!" Yana sane ya fadi haka ya ji ko ya zata fuskanci Mijinta. Hadiye yawu yayi yana kin zuciyarshi kamar aka lugude a kai, wani irin yanayi yake ji a kanshi, yana tsoron kada ta ce tana da miji. "Amma gaskiya ba zai yiwu ba, domin ko ka tambayi iznin zuwa ba zaa a bar ni ba, ka duba ni mace ce kuma Bahaushiya idan nace zan yi tafiya wata ƙasa da wani namijin ai abin ba zai making sense ba, ina ga a cire sunana a bar ni anan, abinda ya shafi gida Nigeria. " "Idan don Mijinki ne, ki bada passport ɗinsa sai a tafi da shi, but i need you! " Daga haka ya fita a motar domin har mun iso bankin UBA, gaba yayi na fito airah ta ja min tsaki, kallona Taj yayi yana faɗin. "Kina sa'ar Oga, tunda har da mijinki zaku tafi." "Ni fa ba zan bishi ba." Haka na cigaba da tafiya, ya juya yana kallon yadda nake bawa Taj amsa, tsaki yayi yarinya karamar da ya sani a wancan shekarun bata da wannan kula kowa, amma wannan da aurenta ma, sakewa take da kowa shi yaushe zai zama dan iska irin Mijinta, idan da shi ne Mijinta, zai ga yadda zata kula kowa domin a banza zai ta sare kan mutane ne, tsaki yayi ya cigaba da tafiya. Har inda aka yi zaman muka isa sannan muka fita inda aka ajiye kayan, na shiga ina rubuta abubuwan da Taj yake gaya min, har muka gama na juya kenan kawai muka ci karo da shi, kamar xan fadi ya riko hannuna, ya tsayar da ni. Ya harare ni cikin masifa ya ce min. "Idan Mijinki baya kishinki, ke ba zaki iya kishin kanki ba ne? Kin zauna sai wangale hakora kike da wani? Ki sani ba zaki janyo min masifa a kamfanina ba, idan aurenki aurenki idan kuma kule-kule ne sai ki bar min aikin na gaya miki, kuma xan gayawa SAN yasan abinda kike aikatawa." Irin kallon da nake mishi na tausayi ne, domin bakiɗaya masifarshi ta rufe mishi idanun kawai fada yake kamar zai dake ni, wani abu da yake bani mamaki shi fa idan yana masifar ma baka tab'a jin tashin muryan sai dai ayi ta maganar cikin wuya da baki, irin kada a ji yana fada, tattara kayan nayi na rab'a gefenshi na wuce, kafin na isa wurin motar na shiga Taj na min magana na ki kula shi, shima da yazo ya zauna a motar muka bar bankin muna hanya amma naki kula Taj, ganin haka yasa shi cewa Taj. "Ka kai mu Chinese dish." "Ok sir!" Bayan mun dauki hanya naji muryan Airah. "Turaki ni ban ga wani aikin da sakatariyarka take ba, maganar tafiya kuwa sai na yi replace dinta." Duk muna jinta, ni sai na fi kowa murna cikin farin ciki na ce mata.. "Alhamdulillahi Ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, kai Masha Allah." Ganin yadda na nuna farin cikina tare da musu addu'a, ya cika da mamaki yana ta taɓa table tap amma zuciyarshi kamar ta dirko daga kirjinsa, har sai da ya kai hannu ya danne kirjin, ko da muka iso shagon ita da Taj ya tura shagon. Tunda na ji ya ce ita da ita da Taj su je su fita su amso na fahimci zai hau masifa ne, dauko airpies na saka s kunnena na kunna wayata. "Cire!" Ya fada a fusace, na cire daga kunnen na juya ina kallon titi raina yana b'aci, "tafiya da ke xan yi idan kin so ki ajiye aiki yau!" Daga haka ya cigaba da aikinsa. Haka suka dawo muka bar shagon, koda muka iso office mika min abincin Taj yayi na ce mishi. "Ina azumi!" "Yau wacce rana kenan?" Banza nayi mishi ban kara kula shi ba. Har aka tashi na wuce gida, ina isowa gida abin mamaki na same shi har ya rigani zuwa gidan, na samu suna magana da Ya Ado. Wuce su nayi na tafi cikin gidan. Ban san tafiyarshi ba, sai ganin Ya Ado nayi ya zauna yana kallona. "Kuna da tafiya ne a kamfaninku?" "Eh amma ni nace ba zan samu zuwa ba, saboda." "Zaki je, abu daya nake so dake ki kama kanki, sannan ki rike mutuncinki. Kada ki manta Allah yana ganinki, kada ganin bamu nan yasa ki fada wani irin yanayi, ki sani Allah yana kallonki." Idanuna ne suka cika da kwalla, haka yayi ta min nasiha duk da ni na nuna bana son zuwa amma ya ado ya ce na je, haka na cigaba da jin wannan abin haushin, ranar juma'a ba wani zama muka yi ba, aka tashi yau kan shi da kasan yazo kamfanin don haka da aka tashi, na fito zan je Garej ya tsaya tare da cewa. "Shigo!" Kamar ba zan shiga ba, sai kuma na shiga na ja belt na daura, muka cigaba da tafiya. Wannan dan renin hankalin ba abinda ya ce min, har muka isa gida na cire belt din xan fita ya ce min. "Are you angry?" Share nayi na bar shi a wajen ai tun da naje ya ga yadda fuskata take masifar haɗe, haka yasa shi fahimtar raina a b'ace yake, wai kuma don renin hankali yana tambayata wai ina jin haushi ne?
Ranar asabar, ina tsaka da barci domin duk jikina a gajiye nake tun daren jiya Aunty Zakiyah ta ce zata shiga asibiti. Wurin karfe goma, mai aikin ta ce nazo ina da baki, saukowa nayi shine da su Ilham. Cike da mamaki yaran suka taso da gudu na sauko nima na rungume su. "Aunty Lulu!" "Na'am yau kunne!" Zama nayi nace mishi. "Ina kwana?" Hankalinsa yana kan wayarshi sai latsawa yake, kamar bai ji ni ba, sai da na sake gaishe shi ya amsa, kitchen na nufa na shiga aikin gaggawa domin Yaran gidanmu sun tafi Islamiyya. Babu wani abin karyawa don dumamen tuwo suka ci, doya na fere na turara musu, tare da miyar sauce din kwai, sai kunun tsamiya da na dama musu na shiga fito da shi, na hada bakiɗaya a gabansu, yaran na zuba musu. Sannan na koma na matse fruit nayi musu juice da shi na fito na zuba musu. Abin ya bani mamaki yadda yake cikin abincin kamar bashi ba. Komawa sama nayi, wanka da brush nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa, na karya dan daurin dan kwali, Ban san me ya ke fisgana ba, amma na samu kaina da shafe jikina da humra mai kamshi, sannan ka fito na samu ya gama yana fama da wayarshi ne, lokacin da na iso parlourn kura min idanu yayi, sai da na kama shi yana kallona ya wayance kamar bai yi kome ba, na wuce kitchen na zauna a can na karya sannan na fito yaran suka gama cin nasu na tattara na kai kitchen. Sai Santi suke. "Aunty Lulu zaki raka mu, muje birthday party na yar class dinmu, kuma ance anan son two parent su zo ne, kin san Mom ba zata amince ba, shine muka zo da Uncle ko zaki bi mu. Please!" Yadda suka yi maganar kamar nayi kuka, domin na fahimci ba wai zuwan kansu ba ne ba mamaki shi ya shirya musu haka. "Bari ka kira Mijina na gaya mishi!" Na tsinci kaina da fadar haka, bai d'ago ya kalle ni ba har na haura sama na gama abinda zan yi ja fito sanye da wata laffaya akan kayan jikina. Na fito a hankali nake takawa, yadda na iso yaran suka yi ta murna, haka muka fita satar kallona yake sau biyu ina kama shi, amma sai wani haɗe rai yake..
A wurin Birthday din hidima sosai aka yi, mu kanmu iyayen yaran sai da suka saka mana wani gasa. Kusan a tare muka ci gasar, karon farko da naji wata irin soyayyar Yara ya kama ni, domin saboda Yaran nan sai da nayi kawaye Iyayen Yara, dayawa a wurin dauka suka yi ni Matarshi, ce kasancewar an san shi sai ya zamana idanun mutane akanmu, a kyautar da ya bada har da dollar guda ashirin, sai gift da yaran suka bada. A waje haka mutumin nan yana da mutunci, rashin mutuncinsa a office suke. Haka muka gama bikin muka dawo suka ajiye ni a gida, fitowa yayi daga motar yana dan matsa hannunsa, ni duk a tunani na crwa zai yi na gode. "Idan kika shiga ki yi wanka domin turarenki." Kambu, banza nayi da shi na wuce humran nawa ne zan yi wanka akan shi wanda idan ba kazo kusa da Ni.... Rufe bakina nayi wata irin kunya ta kama ni, kenan turaren ya. Da gudu na shige parlourn tare da haurawa sama, yayi gaskiya Innalillahi wainnalihir rajoun, wanka nayi tare da tsarkake jikina. Duk kunya ya kama ni, haka nayi ta juyi har lokacin cin abinci yayi, ina cin abincin kawai sai naji gabana yana faduwa, sakamakon tuno maganarshi, gaskiya tafiya Japan ba zai yiwu ba, don ma azumi ya kusa. Haka nayi ta cakalar abincin har Ya ado yace min.." idan ba zaki ci ba ai ba a miki dole ba! " Mikewa nayi na dawo parlourn da Yorghurt ina sha a hankali, ni fa yanzu na lura wannan aikin ya kara ramar da ni, domin yan dukiyar fulanina basu zama a cikin yar bra da nake sakawa.
Haka nayi ta juya maganar, nan har barci ya dauke ni, Washi gari lahadi, sakon da na gani ya turo min ya ce min. *Daren yau zamu tafi please kada ki hada kayanki d wannan perfume din yana da karfi bana sonshi* kambu mutumin nan ya rena min hankali, buga kofar da Ya ado yayi na ce mishi. "Na'am!" "Dazu oganki yake gaya min tafiyarku karfe shida na yamma!" "Tow!" Haka na shiga hada kayana bakiɗaya dogayen ruguna ne, humran nan barinsa nayi na dauki body spray sai roll on na hammata, saukowa kasa nayi na samu Aunty Zakiyah na ce mata. "Wai Aunty Zakiyah humran nan meye amfaninsa ne?" Dariya tayi tana faɗin. "Kin saka ne?" "Eh kai yana da dad'i." "Sannu ko, tow na masu miji ne ranar ina ta son hanaki ɗauka, amma saboda Maman Amal ta cinye ki da baki kika ɗauka." Kasa kasa ta ce min. "Na masu maza ne. Idan kika saka namiji haukacewa zai yi akanki...." Da gudu na haura sama ban yarda na ji karshen bayaninta ba, na je na dauka na boye idan aka samu Mama ko Aunty Hindatu suka zo zan basu su su raba fa Aunty Innah. Allah sarki shi yasa duk ya shiga damuwa.
Har dare ina kwance kawai nazarin yadda zan ganshi ne, karfe biyar da rabi Ya ado ya saka muka fito, na saka kayana a cikin motar dukkan yan gidan suka rako ni.
Yana cikin mota shi da Ubaid da Uncle Auta, kallonshi Uncle Auta yayi ya ce mishi. "Bilal zaka tafi da Yar mutane kuma kace matar aure ce, please and please ka taya ta kare kimar aurenta, don Allah kada ka sake wani abu ya tab'a kimar aurenta Please." "Wai wace ce ita da ya damu kansa da ita ne?............ [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 56 Shiru Uncle Auta yayi, suka fito domin raka Turaki har cikin airport ɗin, ganin yadda take rungume Yayanta yasa shi jin wani irin abu. Ɗauke kai yayi har suka gama alamar rarrashinta yake ita kuwa sai wani kukan shagwaba take, haushi ya kama shi kamar ya ce ya fasa kowa ya kama gabansa. Anan dai suka daure har suka gaisa da Uncle Auta da Ya Ado, Ubaid ma sama sama suka gaisa da juna. Wurin bakwai da wani abu jirginsu ya tashi.
Kallon Uncle Auta Ubaid yayi yana faɗin. "Kana ta ja min tai wacece ita?" "Lubnarsa yarinyar da ya so ya Bauchi. A yanzu Allah ya haɗa su a wuri guda amma ita kamar bata san shi ne wanda ya sota a Bauchi ba." "A'a renin hankali dai ni dama tun ganinta na ji bana sonta, haushi take bani kawai bata dace da shi ba shine yake haukarshi akanta, gaskiya ba zan tab'a barin ta kara saka mu, rasa shi ba domin babu alkhairi a tarayyarsu."
"Ba ruwanka da ita idan har kaso son alakarku tayi tsawo kada ka shiga tsakaninsa da ita ka ga yadda yake jin kishin nan tas zai iya yanke hukunci rabuwa da kai, a yanzu haka bai san bata da aure ba. baffa ya nuna mishi tana da aure kada ya ce zai yi wani abu na daban. Don Allah kada ka yi wani abu da zai lalata alakarku!" Jin shi Ubaid yake amma yasan tabbas tazo sake yaudarar dan uwansa ne kafin tayi haka tabbas ya shiga tsakaninsu har abada."
Zance wannan ce karo na farko da nayo tafiya da wani ba muharramina ba, duk sai na takura. Wani abinda na fahimta inda muka zauna VIP ne. Tunda muka shiga wurina daban wurinsa daban, amma sau biyu ina kama shi dumu dumu yana kallona, na dauke kai ban kara kallon inda yake ba, har muka isa dubai da rana. Mun bar can dare ya shiga mun shiga dubai da rana, anan muka yi sallah asuba da na duhur, kafin muka dawo airport ɗin ya zo min da abinci, na amsa ina kallon kasa. Har muka shiga jirgi ban ci abincin ba.
Haka yasa bakiɗaya yayi ta duba ni ko naci abincin, ni kuwa naki cin abincin. Haka muka isa kasar Japan da dare anan mukumukun sanyi, abin bai kara bani mamaki ba sai da na ga garin na kara godewa Allah da ya hankad'o ni nazo na ga sabon duniya, mun sauka a Tokyo anan aka yi taron na tsawon kwanaki uku, daga ni har shi bamu haduwa da juna sai zamu tafi taron, idan muka dawo kowa ya shige dakinsa, zai matuƙar wahala ka ga mutum ya leko, a cikin sati daya zuwa kwana goma sau biyu muka zauna a wuri guda. Sai ana jibi zamu dawo ya buga min kofa, ba bude kallona yayi daga sama zuwa kasa ya ce min. "Ins jiranki!" Komawa cikin nayi na gyara jikina, sannan na fito sanye da doguwar riga sai katon coat na sanyi da na daura, sannan muka fita yawo. A ranar yawo kan munyi shi, sannan ya ja ni zuwa wurin part na abokansa, a lokacin da suka hadu aka yi ta hira, amma hankalinsa rabi yana kaina, ban san me aka mika min a kwalba ba, dawowa kusa da ni yayi a hankali ya sa hannu a ture ruwan, kallonshi nayi domin ruwan har wani hayaki yake, kallonshi abokan suka yi ya kalli wata daga cikin abokansa mata ya ce mata. "Tinah kaita ta wanke jikinta." Muna tashi suka fara mishi magana. "Me yasa zaka zubar da liquor din da muka ba ta?" Murmushi yayi ya mike tare da ɗaukar jakarta. "Ita muslmace kamar ni, kamar yadda Allah ya haramta haka nima hakkina ne na kare mutuncinta, sannan kuma ai baku gaya min zaku bata wani abu ta sha ba, da ta sha kuwa sai ka hadiye kwalbar!" Iya nan naji ya mika min jakar muka bar wurin. A hankali muke tafiya daga ni har shi jikinmu a mace yake, na rasa me zance me shi, shima kuma bai min magana ba har muka isa masaukinmu. Sai da na bude kofar na shiga ya wuce abinsa. Washi gari da sassafe ya tashe ni muka je sayayya. Muna gamawa aka wuce da shi airport kafin gobe sun gama kome, da la'asar na dan fito daga hotel din ina tsaye a waje na hango Airah da shi suna magana, yaushe ta zo? Abin ya bani mamaki ganin na hango su yasa ta karaso. Cikin yanga da jan hankali ta ce min. "Duk iya kwanakin da kika yi da shi bai isa ba sai kin biyo shi?" Ban fahimci me take nufi ba, don haka kallo daya na mata na dauke kai. Na cigaba da kallon garin sai da ta hauro inda nake zata tab'a ni na rike hannunta. "Kul kada na ji kada na gani, ni ba sa'ar yinli ba ne don haka ba zaki saka hannunki a jikina ba." Na ture hannunta, "karuwa me bin namijin da bai damu da ita ba." Wannan maganar ya min ciwo, murmushi nayi nace mata. "Ke ya kamata na kira haka tunda zuwan da kika ce kina so ya nuna baya yin zuwanki sai ni. Yana da kyau na kira ki da Uwar karuwai ni wancan abin ko a kafa aka daura kin shi bana yinsa." Na wuce abina, ita ta damu da namiji har take faɗa akanshi, amma ni da na sha wuta a hannun da namiji har wani abin burgewa ce da su da zan damu kaina. Mtseew, na ja tsaki. Ashe ina barin wurin kai ƙarata tayi wurinsa, ban san ya suka kare ba. Da asuba muka hadu da ita a nan airport. Ni ban shiga harkanta ba, kuma ban wani damu da ita ba. Ban san me ya gaya mata ba amma tabbas naga ta shiga hankalinta, amma tana harara ta idan muka hada ido ba mistake.
Mun iso Nigeria kai tsaye, da misalin karfe sha biyu saura na dare, kallona yayi ya ce min. "Ko zaki kwana a gidan Uncle Auta idan gari." Ban barshi ya kai aya ba nace mishi. "A'a bamu yi haka da kai ba, kawai kai ni gida!" Na fada ina kallon gefe tsaki tayi haka muka kira Uncle Auta ya zo, ya dauke ni, ni da ita muna baya. Shi da Uncle Auta suna gaba, har kofar gidan Ya ado aka ajiye ni sai da ya buga gidan Ya gaisa da Ya Ado, sannan ya ce mishi. "Ga amanar da ka bani!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Na gode sosai da wannan abin da ka yi na yarda kai me amana ne!" Ya ji dadi, ni kan dakin kasa na wuce ka kwanta, tunda nayi sallah asuba na koma na kwanta sai sha biyu na tashi da mugun mura na kwaso sanyin can, ai muryata ta dishe, mura sosai da zazzaɓi na kwanta.
Ban sani ba ko Ya Ado ne ya gaya mishi, bayan isha sai gashi da kayan dubayya, ya zo duba ni. Kaya niki-niki sai da abin ya dasawa Aunty Zakiyah ayar tambaya. Ganin haka yasa bayan tafiyar naki magana duk yadda taso nayi magana naki, sai ta zuba min idanu.
*** Bauchi
Jikin Abba da sauki sai dai ya daina zuwa kasuwa, koda yake kasuwar ma yanzu suna ce domin shagonsa ya mutu murus na atamfofi, sauran da yake ba a hannun Hafiz suke ba yasa kome yake tafiya normal, wani abu da Abba yayi shine raba hannunsa da yayi, shine kawai Allah bai bada ikon karya shi ba, amma shagon sai da aka rufe domin babu kome a cikin shagon kamar wacce aka yi mata yasa.