Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 33

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 33

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 33: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 33. Ya nima da lafiyarsa da karfinsa amma yau an wayi gari kome ya kare shi. A haka shima Baba…

3,845 words

Ya nima da lafiyarsa da karfinsa amma yau an wayi gari kome ya kare shi. A haka shima Baba Malam ya kwanta rashin lafiya, sosai fa ya kwanta jinya. Duk da wannan yanayin da yake ciki sai da ya kai ya kawo yana fama da jinya amma yana sakawa a kira Abba ya tuna mishi lallai ko bayan ransa ne a tabbatar na koma gidan Hafiz, shi Abba ba lafiyar ce da shi ba, amma a haka ya tafi jama'are ya samu tashin hankalin da ya wuce tunanina domin Hafiz ya zo ya gaya musu karya da gaskiya, lokacin da suka dawo daga lagos, bai magana ba kuma Ya ado bai fadawa iyaye mazan abinda ya faru ba, Yadiko ce ta sani, ai kuwa rako su Baba Malam gida domin inda Baban Jama'are zai makale an rufe gidan da yake shirin rikewa Ya Umar ya ce an saka a kasuwa saboda zasu saka kaya a shago, wannan ya kara bawa Hafiz daman zuduma sharri son ransa. Wannan abin yayi bala'in d'agawa Abba hankali wanda ya haifar da saukar jininsa har ya nemi faduwa, don ma Allah ya so da Sani suka tafi.. haka suka yi ta kula da shi, wato cewa Hafiz yayi shi duk abinda zasu mishi zai karba amma su sani ba zai tab'a gudun Lubnah da take karuwanci a Lagos ba, haka yasa har Rufa'i sai da ya bada shaidar Lubnah karuwanci take har da hotonta suka nuna wanda take motsa jiki a cikin gidan. Wannan abin yayiwa kowa zafi Mama da bata da hakuri har Jama'are ta isa aka yi uwa ubanka, wannan abin ya tsaya mata a rai, tayi kuka har ta godewa Allah, Hafiz ya ki rabuwa da Lubnah duk inda ya zauna sai ya zage ya ce shi zai rufa mata asiri, koda ciwo zata kwaso zai zauna da ita a haka, wannan abin ya saka aka manta da itin cutar da yayiwa Lubnah aka fara ganin ƙoƙarinsa da yadda ya ganta kuma zai zauna da ita, sharri kuwa ai dan aike ne. Haka Abba ya dawo Bauchi da ciwo hade da bakin ciki, Yadiko ta ce mishi. "Alhaji ai baka ci ta kuka ba, Maman Lubnah ce da kuka domin ita aka cuta kuma Allah sai ya saka mata, wannan zalinci har ina kuma kaima Hafiz bai barka ba." Wannan abin ya taru ya mishi yawa, ga bakin ciki ga takaicin Hafiz. *** Lagos Kwana uku a tsakanin wanda yayi daidai da Monday na koma aiki, yadda naga ana kallona yasa na dan tsargu. Ashe gulma aka yi me zafi. Wanda Sarah ce ta iya bani labarin wai ai Airah ta ce mata a daki daya muka sauka sannan mun ta yawon dare da sheke ayarmu. Kallonta nayi tare da dariya na ce mata. "Duk abinda aka fada a kaina da wanda na sani da wanda ban sani ba na yafe, idan kin gadama ki yarda idan baki gadama ba ki watsar. Ni ban zo kamfanin nan don shirme ba, su da suka ga zasu iya Bismillah."

Haka lamarin ya cigaba da tafiya, ba dad'i ga gidan Jaridu da suka sako shi a gaba da kafe hotonshi a magazine ana cewa yana sheke ayarsa da sakatariyarsa, kanwar wani babban lauya a nan lagos, har kamfanin ake zuwa leken asiri wannan yasa na ajiye aikin na tafi hutu don ma Allah yasa saura sati biyu a fara azumi. Kanshi ya dauki wuta haka yayi ta min masifa akan me zan dauki hutu bayan ba ni daya ba ce a cikin wannan tashin hankalin har dashi, kashe wayar nayi na tattara na bar lagos da goyan bayan Ya Ado na tafi rives wurin Aunty Munah hutu, a can na yi sati biyu, Ya ado da fari ya zata ko ina sonshi ne nake wannan abin ni kuwa ba wannan tunanin kawai na gaji da matsalar kamfaninsa ne, wata na biyu kenan a kamfanin amma kamar don ni aka bude kamfanin satin biyu cib Ya Ado yazo da kanshi wai na koma gida Mama tazo. Haka muka iso gidan cike da farin ciki, na ga Mama na ji dadi sosai. Kusan kwana muka yi a tare muna hira, washi muna karyawa ya jifo min tambayar da tasa na kusan kwarewa. "Ance kina aiki da wani namiji wanda ake ganinku tare waye shi?" "Mama oga na ne na wurin aiki." "Sonki yake yi ne?" "Amma aiki ya haɗa mu fa, babu wani maganar so ni yanzu babu aure a gabana." Shiru tayi kafin ta ce min. "Babu aure a gabanki taya aka yi har wannan hotunan suka Bayyana a idanun duniya." Ta watsa min hoton, wani irin razana nayi tare da rufe bakina. Zan yi magana ta dakatar da ni. "Bana son jin kome a bakinki. Ki ajiye aikin ki hada kayanki mu koma Bauchi.."

** "Na gaya maka bata bukatarka, wannan gayen da ka daka a kanta wanan ranar shine Mijinta, har yau yana nan bai rabu da ita ba, idan akwai abinda kake yi da ita tow ka daina ita din matar aure ce." Inji Ubaid. Cike da mamaki yake kallon Ubaid cikin sanyin murya ya ce mishi. " Zargina kake? " Gaskiya na gaya maka, ka rabu da ita." [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 57 Murmushi Turaki yayi mishi tare da mikewa, ya nufe shi ture shi yayi har suka fito waje. "Idan na kara ganinka, a rayuwata ko a rayuwar lubnah, sai na kashe ka!" Ya tura shi waje. "Akan mace zaka rabu da ni? Akan mace zaka lalata alakarmu?" "Dama can Alakar ta lalace, ai dama can alakar babu ita, dama can babu wata kauna ko soyayya da yake tsakaninmu, stop pretending like kana tare da ni bayan na san kai da sauran yan gidan so kuke su kashe ni da goyan bayanka, idan ma Lubnah tana da aure zan cigaba da tafiya ba zan tsaya ba, idan bata da aure zan tsaya na ga me take bukata a rayuwata. Ba kai ba Mujitafa idan ya ce zai nunawa Lubnah yatsa sai na karya shi balle kai karan kade miya, fita kada na kara ganin munafikar fuskarka." Cike da mamaki Ubaid yake kallon Turaki da ya kore shi. "Korana kayi fa? Korana kayi Turaki?" Murmushin takaici ya sake mishi tare da cewa, "abinda yafi haka ma zan maka fita!" Ya daka mishi tsawa. Girgiza kai yayi ya fita, duk fuskar da aka bibiya shine bai kyautata Alakarshi da turaki ba, ya san yayi kuskure amma duk lokacin da yayi da wani katobarar kara nisanta kanshi da Turaki yake ya rasa me yasa yake jin haushin Yarinyar.

*** Tsare Mama nayi da idanu, na rasa abinda zan fada. Amma sai na ji akan kaina Mama bata yi kuskure ba, ta yiwu wani abu aka kintsa mata, duk yadda aka yi da wani abu. "Mama Bauchi kuma?" Yadda nayi maganar sanyin murya sai ta kuma sauko da kanta ta ce min. "Eh Bauchi zamu koma, mu je ki zauna har Allah ya kawo miki mijin aure." "Alhamdulillahi Ubangiji ya amince!" Na fada mata, domin kuwa babu amfanin zan yi musu da Mama domin duk abinda zata yi tana yi ne domin ni. Can ina tura abincin ta cewa Ya Ado. "Jiya Yaron Rufa'i ya kawo min hoton abinda yake faruwa , Adamu ka min adalci!" Girgixa kai yayi cikin ladabi ya ce mata. "Ni ba zan ce ni adali ba ne, amma nasan ke Adalar uwa ce wacce take tsaye domin Yaranta akan me zan musanta abinda kike da hujja a kai, nayi kuskure babba na sakaci da tarbiyyar da kika bani, amma ki yi hakuri haka ba zai kara faruwa ba." Akwai wata duniya da Allah da kanshi ya ginawa Uwa domin Yayanta, wannan duniyar iya uwa da Ƴaƴanta suke ninkaya a cikinsa. Murmushi tayi ta ce mishi." Ban ga gazawarka, amma Lubnah ba zata koma aikin nan ba, idan har shi shugabanta mutumin kirki ne, da kanshi zai zo nimanta, idan kuwa mutumin banza ne ba zai tab'a zuwa ba sai dai ta je mishi. Nan da sati ba zata aikin ba." A hankali na saukr ajiyar zuciya, mother like no other. Duk wannan abinda take don mutuncina da kimata take.

Haka na kwashe kayan abincin na kai kitchen suka yi ta hira, haka suka tafi aiki suka barmu, nima ina gamawa na ce ta shirya muje gidan Aunty Nuratu Kafaya, haka kuwa muka tafi a can muka wuni sai yamma likis muka dawo a gajiye, har ga Allah mutane sun mana mummunar fahimta, amma yadda na fahimci Mama bata Zafaffa ba, amma kuma ta zuba idanun tana kallonmu ni da Ya ado, maganar gaskiya Ya Ado shi ya ma manta da batun, a daren ta amshi wayata ta kashe, ban wani damu ba na bar mata dama Ya ado ya gaya min na dauke kaina akan kome. Ranar da Mama ta cika kwanaki biyar da zuwa, bayan sallah isha ina sama ina gyara kayana, Princess ta shigo tana faɗin. "Aunty ki zo inji Kakar Bauchi." "Ok!" "Ok ina zuwa." Na fada ina tattara kayan, can na fito sanye da riga da wando palazzo sai rigar iya gwiwata kaina sanye da hula, tun kafin na isa parlourn mayyen kamshin turarensa mai mugun kama wuri ya min maraba, da hanzari na sauko ina son gani da gaske ne shi din ne. Da gudu Yaran kanwarsa suka rungume ni. "Mom ita ce mana kin daina zuwa aiki, waye ya miki laifi?" Jan kumatunsu nayi na ce musu. "Break na ɗauka." "Yaushe zaki dawo?" "Mama ta ce zan tafi Bauchi!" Na fada ina satar kallonshi, ya fada kamar bai da lafiya. "Eh zata koma Bauchi da zama!" "Kakar Bauchi, ki barta kin ji Mom tace tana da kirki, kuma nima ai ta min kirki." Murmushi Mama tayi tana faɗin. "Tow kishiya amma ba zan bari ki aure min Alhaji ba, domin nima ina da gashi yala-yala irin naki." Dariya Ilham yayi tana faɗin. "Kaka ai naki yayi fari, ba irin na Aunty Lulu ba ne, ita nata fa ranar donut na ga tayi da shi ko Mom bata donut. Uncle kace kai ma Mom ɗinka tafi Aunty Lulu gashi, amma tana kama da Mom ɗinka." "Da gaske Bro haka ka fada musu." Bai ce kome ba, ni ce ma nayi maza na toshe bakinta, na mata rad'a a kunne. "Bakyau fadar sirrin da kuka yi da wani ko?" Na fada ina kallon Mama da take kallona. "Aunty Jasmin ya kwana biyu?" "Alhamdulillahi, kin ajiye aiki ko? Brother ma jiya aka sallame shi bai da lafiya!" Da sauri na d'ago ina kallonshi, ya tara Kaduna, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa na ce mata. "Allah ya bashi lafiya!" "Amin Ya Allah, yaushe zaki koma aikinki?" Gyara zama Mama tayi sannan ta ce mata. "Ta gama aiki da ku ai, zata koma Bauchi ta cigaba da aikin a can anan ana bibiyar rayuwarta. Sannan su waɗanda hotunan ban san ma'anarsu ba, na ji ance kai ne mai gidanta." Shiru yayi yana kallon hotunan daya na wurin abinci ne, na biyu na Eko hotel ne, na uku dawowarmu daga Japan. Tasowa yayi ya durkusa a gaban ta. Cikin sanyin murya ya dauki hotunan ya ce mata. "Kasancewarta sakatarinya, ina bukatarta a kusa da ni. Wannan wani kasuwanci muka yi shine sanadin da ta bi ni hotel, wannan gidan abinci ne bata ma ci ba sai tawowa tayi da shi, na uku tafiya ce na kasuwanci. Na rantse miki da wannan rayuwa da mutuwa take hannunsa, sai da tace min ba zata ba, har wata ta ce zata nace a'a. Mama! " Ya kira sunanta a hankali, cikin rarrashi da niman afwa ya ce mata. " Ko bayan ranki, Yarki ba zata zubar da mutuncinta ba, ba zata wulakanta tarbiyyar da kika mata ba. Mama da ace Yarki zata yi wani abu da tayi. " Kallona yayi kafin ya sunkuyar da kai kasa, ya cigaba da cewa." Allah ya sani ita din Mutuniyar kirki ce, kamila ce, Saliha , mijinta ya dace da mace ta gari. Yaranta zasu yi Alfahari da ita a matsayin Uwa ta gari. Don Allah ki barta anan wallahi ni da kaina zan tayaku kare mutuncinta, kamar yadda xan kare uwar Yaran nan da su Yaran Lubnah ma zan kare mutuncinta." Ceo yana da hikima,. A yadda yake iya kasuwanci da mu'amala da mutane haka duk wanda ya zauna da shi sai ya fahimci haka. Kaina a sunkuye ina wasa da yatsuna ina jin tsigar jikina yana mikewa, ina ƙara jin wani abu yana tab'a ruhina da zuciyata, d'ago kai nayi ban san yadda aka yi na ji yana bani tausayi ba, a yau na ga yadda damuwa take cike da idanunsa, zuciyata tayi rauni ainun. Kasa jure yadda yake rokon Mama nayi, na riko hannun Yaran muka wuce sama, kafin nayi nisa na tsinci wasu kalmomi da suka fito daga bakinsa. "Ni maraya ne, amma ina da gata. Na fuskanci cin amana tun ina yaro har zuwa yau da nake gabanki, duk cikin mutanen da suke zagaye da ni daga Kanin Mahaifina, sai Jasminah kanwata sune basu tab'a cutar da ni ba, sai Yar autarki. Ita ce bana gabanta. Tun fil azal haka." Shiru yayi juyowa nayi ina kallon yadda ya sunkuyar da kai kasa. "Bana zo nan akan ta koma aiki bane, na zo ne na bata hakuri akan abinda aka fada a kanta. Idan ma ina son lalata ai ba zan yi da ita ba domin ta fito daga gidan da yake da babban zaure, ita din fata ce da yakini." Murmushi yayi sannan ya ci-gaba da cewa. "Zata iya rubuta takardan barin aikin na gode da bani aronta." Yadda Mama ta fahince shi kaf duniya babu wanda ya mishi irin wannan fahimtar. Amma tayi murmushi kafin ta ce mishi." Zan barta na wani lokaci, na ga kamar kana da bukatar haka, amma ka ji tsoron Allah kada ka kara daukarta zuwa wata duniya, yanxu an daina kiwon dabba mutane ake kiwo, idan har na ga wani abu ba haka ba raina zai b'aci. Duk da ban san sunanka ba, amma kayi wani abu da na kasa fahimta, Auta ta kasa zama ta ga kana rokona. " D'ago kai yayi yana kallon Mama jinjina kai tayi. Ta ce mishi." Ban san wacce alaka ce a tdakaninku ba, amma kuma naga ta kasa zama ta wuce sama da Yara, da kace kai Maraya ne ta tsaya cak, nasan wace ce ita. " Murmushi tayi ta cigaba da cewa." Allah ya dafa mana! " Tayi shiru, tana kallon Ya Ado, gyada mishi kai tayi tana kallon Turaki da yake gabanta, tabbas idan har abinda Ado ya fada mata gaskiya ne, Yaron ya cancanci zama da Lubnah. "Amma ya batun iyali!" Shafa kai yayi yana murmushi, kafi ya ce. "Na so wata yar Bauchi tace bata sona na mata kama da gardawa tun daga lokacin Daddah take karbo maganin aljanu sun aure ni." Ai kuwa parlourn aka yi ta dariya, Mama ta ce mishi. "Kuma yanzu baka da wacce tace tana sonka ai kai ba dai budurwa ko?" Shafa kai yayi ya ce.. "Mama na baki wuka da Nama ki nimo min wacce zata iya da tsufa." Rike baki tayi tana faɗin, "ai kuwa zan iya cewa babu wata Y'a a gabana da na baka ita!" Sosa kai yayi yana faɗin. "Ikon Allah, babu ko kanwar Lubnah ce." "Gaskiya bani da ita, Allah ya baka ta gari." Ta yanke hiran, duk yadda ya so Mama ta yi mishi barin zance akan Lubnah amma fir taki, don shi har yau kallon matar aure yake mata, sai yayi shiru wurin karfe goma suka bar gidan, duk sun fita ina bakin kofar, ina kallonshi. D'ago kai yayi ya kalle ni na dauke kaina, ina jin Jasminah tana cewa. "Mama gobe ta zo aiki don Allah." "Ubangiji ya kai mu gobe lafiya!"

Bayan tafiyarsu na riga su wucewa dakin Mama na kwanta da tazo dakin sai da tayi sallah shafa'i da wutir, bayan ya idar ne ta cigaba da addu'a. Har na fara barci ta ce min. "Kina son Mai gidanki ne?" Da wani sauri na tashi zaune ina zare idanu. Kirjina yana bugawa da karfi. Murmushi tayi ta ce min. "Eh kina son shi Lubnah." "A'a wallahi Mama, ni ba wannan a tsakaninmu idan ma ya gaya miki wallahi karya ce." Hannu ta kai bakina ta rufe. "Bai gaya min haka ba, amma ni naga haka a tattare da ke, ni Uwa ce kuma dole na fahimci haka amma tunda kin ce bakya sonshi ai shi kenan amma ki sani kafin Azumin baɗi ina son ganin mijin aurenki don Allah na baki wannan lokacin ne domin ki samu wanda ya dace da ke, amma ni idan har zaki dauki shawarata wannan mutumin yana buƙatarki sosai. Yana sonki yana kuma girmamaki!" Murmushi tayi. Sannan ta kwanta kamar nayi kuka haka na ji maganarta taya zata ce yana sona bayan kuwa ba wani mutumci muke ba, haka na kwanta sai na kada barci nayi ta juyi. Tun ranar da Mama ta ce tana son ganin Turaki, Ya ado ya zauna ya mata bayani da rokon da Alhaji ELYakub ya roko da kada ya nuna mishi Lubnah bata da aure yin haka zai haifar da daukar kome fa zafi, a haka ya dauka tana da auren in sha Allah akwai jarabawar da yake akan Bilal din yayi nasara da kanshi zai nima mishi auren Lubnah, sai dai a yanzu baya son ya san cewa bata da aure ne. Tun ranar da ya ga CV dinta yake ta fada mishi ta dawo aiki, amma kasancewar shi mai takatsantsa a rayuwarshi yasa yaki nuna ita ce daga Alhaji ELYakub sai kawunsa suka san ita ce, shi yasa da girmamawa suke kara bibiyar lamarin. Duk sun san bata da aure shi ɗaya suka bari a baya. Murmushi Mama tayi ba mamaki Addu'arta ne Allah ya amsa ya bata mijin maraniya, mijinta ita ɗaya mijin da kafin a ce wata ta samu irinsa zata wahala, murmushi Mama tayi tare da sujada Allah ya bashi ikon cinye jarabawar da Alhaji ELYakub ya ke mishi. Sai ga Mama ta kasa barci juyi kadan ta kalli Autarta tausayi da soyayya take ji akanta, kamar ta mai da ta ciki, tasan rokon da yake mata ba rokon ta koma aiki ba, ja'iri miskilin banza. *** A bangaren Turaki kwana yayi yana juyi, karshe sai da ya tafi sallah dare, a jingine da gadon yayi barci. Yana me jin kamar gari ya waye ya ganshi a office duk baya jin dadi amma haka bai haka shi jin wannan karsashin ba, washi gari da safe da wuri ya tashi likitan yazo ya mishi allura da bashi magani ya sha ya shirya sai da ya ga Yaran Jasminah sun tafi makaranta sannan ya tattara ya wuce office, shi da Taj. Idanunsa a lumshe yana jin Taj yayi horn, ajiyar zuciya ya sauke domin yasan ita ce kawai Taj zai yiwa Horn haka, tsayawa yayi.

Duk da saurin da nake domin garin nan bai rabuwa da ruwan sama. Don hadari ne a narke a sama Taj yayi min horn, na san shi da ogansa ne sai na ɗan matsa gefe har ya tsaya. Sauke glass yayi ya ce min. "Shigo mana!" Shiga nayi ina faɗin. "Amma kun yi sauri ko?" Gyada kai yayi yana faɗin., "short cut na bi." "Ayya!" Muka cigaba da tafiya, "Baki san Oga bai da lafiya ba ne?" Juyawa nayi na kalle shi tare da cewa. "Ya jiki?" Banza yayi min wannan mutumin anya aljanu basu kanshi. Haka muka isa kamfanin zan dauki jakarshi ya dauke abinsa, sake baki nayi ina kallon ya cigaba da tafiya a hankali ba bi shi da idanun, sai nake ganin kamar na san wani da yake irin wannan tafiya da jimawa, juya kaina nayi tare da son tuno a ina nasan me irin wannan tafiyar? Ganin zan bawa kaina wahala amma kuma ina fara tafiya, naji gabana yana wani irin bugawa d'ago kai nayi ina kallonshi ya juyo yana kallona. Nima shi nake kallo, akwai wani alaka da ya tab'a faruwa a tsakaninmu da shi ne? A ina na tab'a ganinshi, zuciyata tana wani irin bugawa, idanunshi cikin nawa. Sunkuyar da kai nayi tare da rike jakata da kyau. Jikina yana rawa, wani irin kuka nake son nayi wanda ban san dalilin ba, kuka ne wanda nake ji kamar nayi kewar wani ko wata a rayuwata da jima, nayi kewar wanda ban sani ba waye shi hawaye suka shiga zubo min da gudu......... *DIJAH BORNO, Zully da Naj, ayi hakuri sai yanzu ku yi maneji yau na ci uwar sabada da aiki ne.* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 58 Zuba min idanu yayi ganin har zuwa lokacin ina tsaye. "Taj ka shigo da ita ta daina wannan shirmen!" Ya fada yana me nufar cikin kamfanin, zuwan Taj ya tsaya a gefena." Me ya faru kuma?" Da sauri na goge hawayen da yake ta zuba na ce mlshi. " Ba kome" muka shiga cikin kamfanin, a tunanina yadda ya je har gidan mu yayi bikona. Zai zama me yawan min uzuri, sai dai wannan me shafar aljanun ba haka yake ba, an jima zai birkice an jima zai dawo kamar bashi ba, tun da na fahimci yana da matsalar ƙwaƙwalwa, wanda yake birkita mishi lissafi. Sai na mishi uzuri domin irin wannan halinsa ba iya ni kaɗai ba kowa ma tsoronsa yake, a cikin wata biyu da nayi ya kori mutane a cikinsu kuwa har da shugabar gudanarwa na kamfanin sai ya fara bani tsoro. Shugaban gudanarwa, kwashe wasu abubuwan yayi fa akan lallai sai na zo office dinsa nayi wasu cike-cike. Gudun matsala na tafi nayi, sai da na je na ga mutumin bai da kirki sam, domin na fara aikin kenan ya taso ya fara ƙoƙarin yi min iskanci, kamar wanda aka jefo shi ya daki kofar sai da ta buɗe. Ganin yadda razana domin nima na dauki wani bokitin zuba datti, ina ƙoƙarin kare kaina, sai gashi nan ya zo. Ajiyar zuciya na sauke me nauyi, tare da sake bokitin a kasa. "Na kore ka!" Ya fada yana me juyawa na rufa mishi ba, sai da muka isa office ɗinsa ya zuba min idanu. Ya rasa me yasa kome yake zuwa a haka, na farko ba shigar banza take ba, na biyu bata cika shiga harkan kowa ba abinda yake gabanta ya ishe ta, amma ya rasa me yasa kome yake zuwa kamar an tsara shine. "Da ba gaya min ba haka zaki zauna ya wulakanta ki?" Kaina a kasa, na ce mishi. "Allah ya fishi." "Abinda nake son na fahimta kenan, je ki." Haka na juya na fita, haka muka cigaba da aikin da dad'i ba dad'i ga Airah da ta saka ni gaba duk abinda zan yi ban iya ba, kai da ta ishe ni ce mata nayi. "Ki fita harkata tunda bana shiga rayuwarki, ban ga dalilin da zaki shiga rayuwata ba." Iya wannan na gaya mata na cigaba da abinda yake gabana, wani abin da yake ƙara bani mamaki, duk yadda za a kai mishi magana baya bi ta kai.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull