Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 34

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 34

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 34: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 34. Ranar wata juma'a, ina zaune ciwon ciki ya dame ni. Bakiɗaya na kasa sakewa dan abu kaɗan…

4,176 words

Ranar wata juma'a, ina zaune ciwon ciki ya dame ni. Bakiɗaya na kasa sakewa dan abu kaɗan haushi yake ba ni. Fitowa yayi ya ga na kifa kaina da table din, fita yayi can bayan minti goma sai ga Jasminah. Office dinta muka je, ta haɗa ruwan dumi a gora, saboda na gaya mata gaskiya abinda yake damuna, ina kwance ta kawo min tare da cewa. "Dan saka akan maranki zaki ji sauki!" Haka nayi ta sakawa ina murzawa har barci yayi gaba da ni, hayaniyar Ubaid na ji yasa na bude idanuna a tsaye yake a kaina.. "zaki yi danasanin show up da kika yi a wannan lokacin, idan har ba da wata manufa kike bibiyar Turaki ba ki ajiye aikin ki kama gabanki." Murmushi nayi na ce mishi. "Ban san me kake nufi ba, ban san me yasa kake bibiyata da fitina ba, ka yi tunani idan kanwarka ce fa.?" "Kanwata Allah ya mata tsari da irin rayuwarki, bari na gaya miki kowa yasan kina juya mishi tunani ne, lokacin da ya so ki, ai cewa kika yi ba zaki auri mai zubin Gardawa ba, yau kin san waye shi shine bari ki kashe aurenki!" Ji nayi zuciyata tayi wani irin bugawa kamar nayi kuka. "Ban fahimci me kake nufi ba?" Na tambaye shi a rud'e. "Ubaid me kake aikatawa ne haka?" "Bari na gaya mata Jasminah ta sani ba ita ɗaya ba ce kowa ma yasan yadda take juya mishi tunani, Malamin da ya dauke ku Physic daga 1-2 kika ce kin samu wanda ya fi shi kudi shine wannan, mayyar kudi, kudin wancan mijin naki ya kare ne?" Tass na wanke shi da mari wanda yayi daidai da shigowarsa, shima ya d'aga hannunshi, amma ya rike hannun yana faɗin. "Me ka zo yi a kamfanina? Ba nace kada na kara ganinka ba?" Ya janyo shi waje. Murmushi yayi ya ce mishi. "Wallahi tunda ta mare ni sai ka ɓattar da ita." "Idan ka fasa ka rena wanda ya halicce ka, tab'ata daidai yake da. Nihla!" Wani naushi ya kaiwa Bilal shi kuwa ya kauce fada ya rutsa a tsakaninsu, kamar Yara dambe. Zama nayi dirshan nayi na zubawa kasa idanu, sai a lokacin abubuwan da suke ya faruwa ya dawo kaina, jin ihun Jasminah ya sani fitowa kamar wacce ruwa ya yiwa duka, na kai hannu a hankali dafa kafad'arshi na ce mishi. "Ka bar fadar nan don Allah!" Sake Ubaid yayi shi kuwa ya kai mishi naushi, ai kuwa akan fuskarshi ya same shi, sai da glass dinsa ya fadi, zai rama na shiga tsakaninsu tare da tallafo fuskarshi.. "kalle ni ya isa haka, ni ce matsalarka? Ka yi hakuri zan bar aikin ka ji ka yi hakuri kada ka kara fada a kaina don Allah!" Na mika mishi glass dinsa ina kallon yadda yake jin kamar zai tashi sama. "Muje ka saka maka magani!" Jasminah ta ja hannunsa har office ni kuma na hada kayana, na bar office din ina fitowa na ga yadda ake kallona. Sai naji wani irin abu ya tsaya min a rai,na iso gida na samu Mama sai lokacin na fashe da mata da kuka, na zauna a gabanta ina kuka kamar raina zai fita, rike hannuna tayi tana faɗin. "Me ya faru?" "Mama dama shine Malamin da ya tab'a cewa yana sona a Bauchi? Mama me yasa ya boye min? Mama me yasa yake faɗa da kowa a kaina? Mama me yasa na kasa tuna shi sai yanzu?" Murmushi tayi ta ce min. "Yana sonki ne shi yasa yake faɗa akanki, yana sonki ne yasa ya zame miki izuwa yana sonki ne yasa yake bayyanawa duniya akanki zai tari aradu da fadin kai, yana sonki ne yasa yake faɗa da kowa yake yaki da kowa saboda kada ya rasa ki, a yanzu da bai san kina da aure ko baki da aure ba, ya iya kare kimarki ki yi lissafin idan aka ce yasan baki auren kowa akanki. Tow ba makawa sai yadda karfinsa ya ƙare, shi wannan da gaske yake sonki ba cutar dake zai yi ba. " " Yan uwansa basu sona!" Na fada ina kuka," akan me zasu su so ki?" "Mama ya fi karfina, Mama danginsa wasu irin dangine, na masifa Mama ba zan iya bude mishi zuciyata ba, Mama ban tab'a sonshi ba tun farko a yau ma ina kara fada kamar farko bana sonshi." Murmushi Mama tayi ta ce min. "Nasan ai zuciyarki a rufe take shi yasa kika ki yarda ko kalli kowani mutum da sunan soyayya, amma ba zan boye miki ba, kina son Bilal Koda baki fada ba." Kuka na saka mata ina ta rantsuwa wallahi bana sonshi.

Weekend a gida nayi shi, ranar lahadi sai gashi da Yaran kanwarsa a lokacin na tambaye su basu Islamiyya ne,. Suka ce eh basu zuwa. Turawa Uwarsu sako nayi na kama hannunsu na kai su makarantar su Adil na musu registration na Islamiyya, aka basu uniform suka zauna, ko da na dawo na samu yana bada hakuri ne, murmushi kawai Mama take ta ce mishi. "Ai ni ba ruwana kai da abokiyar aikinka, ni ba ruwana ku yi duk yadda zaku yi amma ka sani Lubnah tana bukatar hutu saboda tayi fama da mentally healthy ill, shi yasa bana son damuwa ya dame ta domin ta kai har matakin GENERALIZED ANXIETY DISORDER, idan har zamanku babu alkhairi kowa ya kama gabansa." Kasa magana yayi zuciyarsa tayi sanyi ya ce mata. "Taya ta hadu da wannan laluran?" Murmushi Mama tayi ta ce mishi. "Rayuwa ya haɗa ta da wannan laluran idan da ranka ai ka sha kallo." Idanunsa yayi mugun ja, haka yayi ta wasa da kafet din parlourn.

Mama ta fahimci yana son ya tambaye ta, Abubuwa dayawa amma kuma yadda yake da zurfin cikin. Tana mamaki ma da yake dogon hira da ita domin irinsu basu cika hira har da kowa ba. A hankali ya ce mata. "Allah ya kyauta, xan tafi an jima zan zo daukar Yaran ." "Allah ya kai." Abinda na fahimta ya zama ɗan gida kowa ji da shi yake da yamma bayan isha da yaso ya samu yaran sun ci abinci sai da ya ci tuwon alkama miyar kuka, sannan ya dauki yaran zuwa gida bayan na biyo shi waje na ce mishi. "Ka yi hakuri da abinda nayi naga rayuwar mata ne, shine na ce bari na biya musu kudin Islamiyya, amma don Allah ku yi hakuri." Murmushi yayi ya ce min. "Kin kyauta ai!" Daga haka ya shiga motar ya bar gidan.

Mama take gaya min mutane irinsu, suna son mace amma aikace suke nuna mata so, basu damu da su gaya mata ba domin ya zama old fashioned a wurinsu. Kuma dabi'ar masu irin halinsu ne, suna da zurfin ciki domin kamar basu yarda da kowa ba, sannan basu cika yarda su yi hira da kowa ba sai wanda ya fahimci halinsu, idan baka fahimce su ba zaka yi ta ganin suna wani abu kamar basu ba, ta ce haka suke kuma dai da tayi magana na fahimci yadda yake masifa kamar nayi mishi laifi musamman idan aka yi baki maza ina musu bayani yayi ta wani fushi da fisga karshe korani yake waje ya ce musu zan bada abinda suke so ba,ya kira Taj, idan da taj muke hira yayi ta fushi ranar daga ni har Taj kamar zai rataye mu, don masifa. Ni kuma tausayi yake bani domin idan haka ita ce soyayya gaskiya am not ready, zuciyata a rufe take.

Washi gari kuwa da safe suka zo da Taj, Ashe Ya Ado yasan da zuwansa. Don fushi nayi naki zuwa aikin haka kawai zasu daura min hawan jini, a gidan suka karya tunda na fahimci yazo fir naki fitowa ba ayi, kuma ai kakanshi ya ce kada na gaya mishi haka ya share zamanshi har yayiwa Mama kyautar kuɗi, wanda ya damu da kuɗinsa shi ya ji wurin. Ni bayan gabana balle ya ce don kuɗinsa nake, ni magana da Ubaid ya gaya min ma ya ishe ni.

** KUMO FAMILY

Fada Alhaji ELYakub Kumo yake kamar ya mari Uncle Auta, ya ce mishi."kasan tana tare da Yaron nan ne saboda kai, amma ka gaya mishi wacece Yarinyar bayan ba kaunarshi yake da gaske ba, ina sane da cewa Turaki yana bin ra'ayinka ne yake kula Yaron nan, kada ka kara bawa wani labarin rayuwar Turaki.

Da shi da aka hada baki aka kore shi a shekarar karshen shi a secondry School, kasan sharrin da ya so a kulla mishi? Kasan yadda ya lalata mishi rayuwa? Ban da Allah yana tare da shi da rayuwarsa tafi haka lalacewar don Allah kada ka kara gaya mishi kome akan Bilal wanda ya mishi a baya ma, ya isa yanzu meye ribar shiga rayuwarsa?" Yadda yake shiga ba nan yake fita ba, fada kamar zai mari Uncle Auta. Yayi fada sosai domin kuwa yana jin zafin abinda Ubaid yayiwa Turaki a lokacin.

Abu guda biyu da suka lalata alakar Turaki da Ubaid na wani abu ne, duk da kowani mutane yana da hali me kyau ko mara kyau, idan har Turaki yayi kuskure tow ya dace ya samu mutumin da zai tsaya a tare shi, tow har ana niman haka tow Ubaid ya kai wannan matsayin, sai dai tun suna Yara Ubaid baya kaunar Turaki yayi sabon aboki ko kuma ya taimakawa wani, yayi ta fushi da kuncin rai kenan. Duk yadda za'a gaya maka matukar ba faruwa yayi da kai ba, ba zaka gane ba. Ubaid ya bawa Bilal wahala akan wannan lamarin domin Ubaid yana ganin Turaki da sabon aboki yayi ta fushi kenan har sai ya raba shi da abokin, sai da Ubaid ya kai ko me turaki zai yi to bai iya ba shi ɗaya ya iya........(Sometimes silent pain yana kashe mutane dayawa, lokaci yayi da zaka fadi ra'ayinka lokaci yayi da zaka rusa wancan bond din da kake gani kamar sasari ne let move together) [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 59 Abinda ya fara faruwa shine kama yara da aka yi suna lalacewa a cikin Makarantar, wnada a lokacin iyayensu suka raye maza sun zo akan case ɗin, wanda yayi sanadiyar da Turaki ya bar makarantar domin Ubaid ya bada shaidar yana lalacewa irin ta mazan da aka tsinewa, kasancewar akwai kyakkyawar alaka tsakanin kakaninshi na Rasha da kasar Saudiya musamman ta harkan kasuwanci suka kashe zancen ya koma Rasha wurin kakarshi sai da ya dauki wata goma ya koma Saudiya yayi jarabawar barin makaranta. Daga nan ya koma can yayi jami'arsa a lokacin Ubaid azo suka yi karatun tare, duk da wannan abinda yayi mishi yayi hakuri sai ya kasance duk wani abin asha kiri-kiri Ubaid yake danganta shi da Turaki, amma bai taɓa kawowa a ransa yana haka ne don ya cutar da shi ba,

A hankali yayi ta amfani da wannan damar yana raba Turaki da duk wanda ya zo gare shi, ana haka iyayensu suka rasu mazan sai da Hajiya Amina mahaifiyar Ubaid zata koma gida Alhaji ELYakub ya amshi rikon Ubaid yace idan ya tafi Turaki zai shiga kadaici, a wannan lokacin kowa ya amshi haka amma kuma a ransu basu son Ubaid din da Turaki domin kowa so yake ya rabu Turaki ya cutar da shi, amma an rasa yadda za ayi, ba a san me ya faru ba. Amma lokacin amma wani satar da aka yi a cikin gidan ElYakub kumo wanda ya girgiza ilahirin family ana cikin binciken baa tambaye shi ba, kawai ya ce ai Turaki ne yayi satan wani abin takaici aka nime kudin ba a samu a wurin Turaki, a lokacin fushin da Turaki yayi dakyar aka shawo kanshi yake kula shi, babban rigimarsu shine akan Mimih wanda aka ce zai aikata, a lokacin ya ce zai aikata ya ci-gaba daga maza ya koma kan mata, tun daga wannan lokacin Turaki ya watsar da shi, amma yana kyautatawa Iyalinsa da duk wani dangin mahaifinsa da na Mahaifiyarshi. Amma ya yanke duk wani abu da yake tsakaninsu, ko rike office din Turaki da yayi ai Alhaji ELYakub ya bashi domin kusan shima bai da mutunci akan gaskiya zai iya aikata kome.

Yadda alakarsu ya lalace musamman yadda yake zargin Turaki yafi kome bashi haushi. *** "Ke bana son rashin hankali, ya zaa yi ace mutum ya zo baki sauko kun gaisa ba." Tura baki nayi nace mata. "Wurinki dai ya zo!" "Amma kanki daya kuwa!" Mirgina mata kaina nayi nace mata. "Kin ga shi ɗaya ne babu kari!" Make ni tayi, haka ta fita, na tura baki ina ruwana da shi. Ba dai ga shi bayan isha ba, muna parlour muna kallon super story, da yake Alhamis ne, zare idanun nayi kaina yana cinyar Mama tana zaune a kasa nima na kwantar da kaina akan cinyarta. Lumshe idanuna nayi kamar me barci, ai kuwa cikin ikon Allah barci yayi gaba da ni, nan suka shiga hira har tara tayi, na musu sallama ya tafi yana fita daga parlourn Mama ta zuba min mari a kafada. "Tashi ja'ira yau kin kunyata ni!" Sosa wurin nake ina tura baki. "Allah ya shirya ki!" Tashi nayi na wuce sama, washi gari ba naki zuwa aiki ba, sai ga Taj da aika tulin aiki kamar nayi hauka Mama kuma taki bani goyan baya, haka nayi ta aiki kamar jaka kwana biyu nayi ina aiki. Dole ranar Monday na koma aiki domin aikin kamar zai hallaka ni. Tun da na dawo sai na ga yayi sanyi ba masifar nan, nima kuma wannan karon sai na kama kaina. Bakiɗaya satin Mama biyu ta bar Lagos, bamu gaya mishi ba. Haka aka fara azumi, azumi na da kwana biyu muka wuce Umara, ashe ta Bauchi Mama itama ta zo haka muka yi ta ibada tayi min addu'a kamar zata kara haifa na, wani jallabiya me tsadar gaske Mama ta saya mishi da agogon azurfa da zube, ta saya mishi da wani turare wanda kuɗinsa zai kai Naira dubu dari biyu, hidimar da tayi mishi kamar wani danta haushi suka bani har da kukana bata saya min ba, haka ta haɗa min a kayana, wai na kawo mishi haka nayi ta mita ina kuka, sallah saura kwana tara muka dawo, cike da farin ciki muka iso, kwana uku na dawo aiki yadda zaku san bana gabanshi, kallo ɗaya yayi min yayi ta wani cin magani. Tsarabar Sarah da Taj, Sai na Jasminah da Yaranta. Shi kuwa ko dabino ban bashi ba. Uncle Auta kuwa da ya min barka da dawowa na bashi kyautar wani zoben azurfa da turare. Wayyo Allah, ina wutar da za a saka ni. Fushi sosai yayi, ya daina min magana sai dai Taj ya min Magana. Ina sane nayi mishi wannan wulakancin. Sallah saura kwana biyar aka bamu hutu kowa yayi Sallah, wannan shine karon farko da zan zo Bauchi sallah.

Sakonsa na wurina da Mama ta bani yaki zuwa gidanmu, ranar na kira Taj ya zo ya amsa na gaya mishi inji Mama ta turo mishi. Bayan an sha ruwa Mama ta kira ni, "ke ce kika bashi number na ya kira sai godiya yake min, wato ke dai ba zaki bar halinki ba, sai yanzu kika bashi sakon?" "Mama daga shan ruwa zaki fara min faɗa." Murmushi tayi tana faɗin. "Allah ya shirya ki!" Nan muka sha hira, ban san Ya aka yi yasan zamu je Bauchi sallah ba, koda yake ba mamaki Mama ta gaya mishi. Haka yazo da katon jaka wai na kaiwa Mama kayan sallah da na azumi da bai mata. Kallon kayan nayi na nad'e hannun a kirjina. Lashe baki nayi nace mishi. "Kayi hakuri ba zan tafi da kayan nan ba!" Na fada ina me juyawa zan bar wurin ya ce." Ai ba ke na bawa ba, wa Mama na ce a kai min idan ma baki ba ai shi san zai kai min!" Takaici ya sa na juya ina kallonshi amma kwarjininsa da cikar halittarsa ya sa ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina cizon bakina. "Dauka ba naki ba ne!" Y fada yana shiga motarshi ya bar gidan nan wannan dan renin hankali ne wallahi, dauka nayi na tura mishi da sakon. *Don Allah wannan ya zama last da zaka kara kawo mata kaya because we are not money Morga, min iya da rufin asirinmu*

Daga haka na wurga da wayar ina hararan kayan kamar na rufe shi da duka. Haka na wuni da takaici, washi gari muka nufi airport domin da wuri muke son shiga Bauchi, tunda Ya Umar yana hanyar Jos. Abin ya matukar min dad'i sai dai me muna isa airport ɗin na hango shi. Suka gaisa da Ya Ado a raina na ce *wannan kamar maye* wai ma ya aka yi wancan lokacin na iya biyewa shashancina na kula wannan mutumin, haushin kaina na ji sosai fa. Da gayya na saka airpies a kunne na, har zuwa lokacin da muka tashi tafiya. Ashe shima Gombe zai wuce, tab'e baki nayi har muka bar lagos idanuna a rufe. Karfe daya na rana muka sauka a Jos, muna isowa sallah muka yi a masallacin da yake gefen airport ɗin, muka yi sallah Aunty Raliyah ta kawo mana kayan lambu da fruit, daga nan muka yi sallama. Bamu tsaya ko ina ba sai a nabardo muka sayi fura da nono, sannan muka wuce Bauchi. Karfe hudu saura muka isa dutsen tanshi, na yi kewar Bauchi sai na zama kamar Bakuwa haka muka isa gidan, da yake cike da yan karban sadaka. Mun samu tarba a wurin Yan uwana da suka zo shan ruwa tunda aka ce zan zo na ga gata sai da nayi kuka don farin ciki. Abba ma ba yabo ba fallasa haka muka gaisa. Ranar sai sha daya Yayuna suka bar gidan na kwana a bayan Mamana, cike da so da kauna nayi kewarta. Lokacin da na tashi sahur na ga sakonshi. _Da fatan kun isa lafiya ya Mamana da Abba tare da Yadiko? Nima na isa lafiya._ share text din naso yi sai na ji ban kyauta ba, kawai sai na tura mishi..*Alhamdulillahi kai ma ya naka tafiyar? Da fatan ka isa lafiya,* can kamar minti ɗaya zuwa biyu sai ga sakonshi. _Masha Allah, baki ce min akan Mamana ba?_ wani iyayi da shishigi tura mishi nayi da ce. *Oops tana lafiya* daga haka na share wayar na cigaba da abinda nake, bayan na idar da sahur nayi Nafilla, sannan na zauna aka yi sallah asuba, kafin na kwanta ban tashi ba sai karfe daya, muka yi wanka ashe Aunty Zakiyah ta wuce gidanta da yake Ibrahim bako tare da kannenta maza biyu da mata uku, kiranta nayi a waya nace mata. "Shine baki tashe n?" "Ikon Allah Auta ta zo wurin Mamanta taya xan tashe ta, jinjira tana jin dumin Mama!" " Aunty Zakiyah gaya min magana mike fa a fakaice fa! " Dariya tayi tana faɗin. "Allah Yayanki ya ce a bar ki wurin Abba shi yasa ban tashe ki ba, kuma suna bukatar wani a kusa da su. " Haka na jita, muka rabu na fito n taya su Mama aiki Abba yana tsakar gidan yana jin yadda Mama take waya da Turaki tana ta saka mishi albarka, ta ji dadin wannan sakon da ya aiko mata, bayan ta gama ta kalli Abba ta ce mishi." Mai gidanta na wurin aikin ta ne ya turo min sako!" Ina jin ta tana gaya mishi har da wani shadda ya turo bashi yace baya son kayan da sai da aka sabawa Allah sannan aka kawo ni. "Eh fa haka ne, bayan saɓon Allah ya wuce na annobar da aka kawo muku a cikin zuri'a, in sha Allah taraba da yasin zamu cigaba saboda harshenku!" Inji Yadiko, Mama kan murmushi tayi tana faɗin."Ai shi kenan! Zan turawa Yayana ya samu a mishi dinkin layya." Bayan isha ta dauki turmin yadiko ya bata tare da sauran kyaututtukan da ya hada har da madara da milo, duk ta turawa Yadiko, kaya ne me tsada. Washi gari ana gobe sallah aka nimo mana mai lalle ni da Yaran Jiddah da Ummu da aunty Zakiyah aka zo aka mana sallah da yake baki suna zuwa daga Jamaare su ne suka yi aikin kome mu kan ana mana lallen hannu da kafa ni kan ja aka min me kyau da ɗaukar idanu, a daren muka wuce gidan Aunty Hindatu aka mana saloon a can wurin karfe biyu na dare muka dawo. Washi gari tun asuba muka tashi, muka tashi saboda Masallacin Malam Idris zamu bi. Da wuri muka fita domin bakwai yake sallah idininsa, muna idarwa muka iso gida ta saman dutse, muna shigowa gidan aka sake shewa aka rungume juna, nan aka bude chapter yaushe gamo.

Kusan kowa yayi kewata, Aunty Munah tana azare sun zo itama zasu karaso Bauchi, haka muka yi ta farin ciki. Har dare ana tare sai hoto ake, sai lokacin Mama ta kawo musu tsarabar da Turaki ya turo ni da shi, ta cirewa Yaranta kowa turmi turmi, dakin Yadiko ma ta cire musu, bayan tafiyarsu na shiga wurin Abba da aka ce yana kirana, kaina a sunkuye yayi shiru. Kafin ya ce min. "Shi abokin shaidancinki, aurenki zai yi?" Rike zuciyata nayi amma tabbas yadda Abba yake danganta Turaki da wasu irin kalmai yana saka ni jin wani irin yanayi, mutumin da ko hannuna bai taba rikewa ba, me yasa Abba yake yin haka ne? Haka ya gama fadarshi iya hakuri nake bashi ina kara nutsuwar da kai na, har zuwa ya gama abinda yake sannan ya ce na je, lokacin da na koma daki Mama tayi tayi tasan me yake faruwa ban gaya mata ba. -Washi gari. Tun safe na ga Mama da Yadiko suna ta aiki kamar zasu yi wani abincin sallah bayan daga gidan Yayuna ake kawowa sallah da kwana biyu ake wunin gidanmu, haka yasa nayi ta mamaki. Amma ban tambaya ba don yadda suke aikin cikin nishadi, na fahimci akwai wani abu.

Wurin karfe tara muna gama shirin tafiya kallon hawa da yake a g.r.a muke kallon, Ya Sani dasu Aunty Inna muna dauki wata sienna muka fita bayan Ya Ado ya turo kudi aka zuba a cikin motar. Muka fita sai kudin da Ya Umar ya bamu, haka muka tafi da kular ruwa da kayan ciye-ciye, haka muka kutsa da kyar zuwa old GRA Bauchi daidai alhayat nan muka samu wuri har an fara wucewa. Sanye nake da wata lace mint green wanda aka min dinki Bubu sai daurin da na kafa a kaina mayafina fari ne da takalmi da jakana, sai madubin da na saka. Ruma Mai shadda muka hadu da ita ina tsaye da lema. "Lubnah Shehu Umar?" Dariya muka saka, na isa inda take ina mai amsar Yaronta alamar sabon haihuwa ce. "Mai shadda kece haka? Kin zama Mama!" "Ke nan ce min zama wata yar 18yrs ba sai ni yar renin wayo!" Wata yar budurwa Yarta na gani tana mai gaishe ni, ta hado kan kannenta. "Ruma beautiful familynki kenan?" Murmushi tayi tana faɗin. " Kema ai naki suna hanya in sha Allah, ki ,zuba idanun suna nan tafe fa wallahi uku uku zaki ya dirke mata duk bayan shekara daya." Murmushi nayi amma nasan ni ai narasa wanan damar har abada. Haka muka sha hira kafin ta wuce. Sai bayan tafiyarta na nutsu sosai. Ina son Yara, ina son Yara amma ni bani da rabon Yaran domin na gama da mahaifana. Taya xan samu haihuwa ko nayi aure? Ina ga Madadin na sakawa kaina damuwar auren gara na hakura na rike aikina, domin babu namiji da zai aure ne ba tare da ya karu da ni ba. Tab'a ni Aunty Innah tayi na kalle ta. "Na ga tun kawarki ta tafi kike tunani, shi fa aure da haihuwa na Allah ne idan kika yi hakuri Allah zai baki wanda baki zata ba. Ki kasance mai yarda da ƙaddara da kuma hakuri da juriya, wallahi ba kowa Allah yake jarabta ba, sai mai imani a jarabce ka ma Allah yana sonka ne ga mutane dayawa suna saɓon Allah kuma suna raye me yafi wannan muni, ki saka a ranki kome ya baki rabonki ne idan bai yi niyya ba Alhamdulillahi ba akanki aka fara haka ba. Ki godewa Allah kina muslma mai imani da ƙaddara. Alhamdulillahi da Allah ya raba ki da wancan Tsinannen da ko Abba bai bari ba, ke Alhamdulillahi kin auna arziki domin da kina nan tare da shi da kin mutu ba wanda ya san yadda kike cin azaba gashi daga rabuwarku har yau bai kara ajiye mace ba, itama Yarinyar da auro a Gyembu a kotu suka rabu, hmmm yanxu haka a Jama'aren an hana shi aure, domin kuwa cewa suke tunda ya iya rabuwa da ke babu Macen da zai samu ya rike tsakani da Allah. " Abin sai ya zo min bazata wato idan baka da hakkin mutum sai Allah ya fito da kome sarari, a yadda nake jin labarin kamar a mafarki wai Ya Hafiz ne yake ikirarin sai samu wacce zata zauna da shi hm....... [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 60

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull