Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 3

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 3

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 3: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 3. A hankali na shigo parlourn ba kome a tare da ni, suka zuba min idanu. " Ya Hafiz ko zaka zo! "…

4,368 words

A hankali na shigo parlourn ba kome a tare da ni, suka zuba min idanu. " Ya Hafiz ko zaka zo! " Shiru yayi kafin ya mike yana dafe kirjinsa da yake nuna min alamar yana mishi ciwo. " Don Allah riki ni, jiri nake ji." Haka na matsa jikinshi, muka fito har zuwa parlourna, ya zauna a dogon kujera ya kishingida yana lumshe idanunshi. Dakin na wuce na dauko kwatin yan kunayena,. Na ajiye mishi sannan na koma gefe na zauna. "Ban san me ya faru ba, amma ga shi ka. Biya abinda ake binka." Kallona yayi kafin ya dauke kai yana dafe kirjinsa. "Lubnah bar dukiyarki kada yan uwanki su ji, su kara himmar raba mu, ki barshi kawai Allah yana nan." "Kudin ne ba zai iya ba?" Hawaye ne ya zubo mishi ya ce min. "Wato wani ƙaddara ne ya fada min, a shagon Baban Bauchi. Gashi saura kwana uku na hada kudin." "Baban Bauchi bai sani ba ne?" Dafe kanshi yayi da hannu bibbiyu yana nishi. Ban san lokacin da na kara rudewa ba, na riko hannunshi tare da janyo shi jikina ina tab'a shi. "Ya Hafiz ko mu tafi asibiti ne? Innalillahi wainnalihir rajoun! Ya Hafiz lafiya?" Yadda ya mike min kamar gawa yasa na kara kidimewa, garin juyawa na ci tuntube da center table din parlona, ban damu da zafin ba amma har cikin raina na ji ciwon sai dai halin da Ya Hafiz yake ciki yasa na manta da ciwon da naci, sai na kasa gane kukan da xan yi na ciwon ne ko kuma na halin da ya Hafiz yake ciki ne? Bakiɗaya na shiga tashin hankali, ban san adadin soyayyar da nake yiwa ya Hafiz ba, haka yasa na kara birkice na rungume shi, ina kuka sosai, domin zuciyata ta karye ainun. Bana son naga abinda zai d'aga mishi hankali, a daren muka kai shi asibitin ni'ima aka bashi kulawar da ta dace har da karin ruwa, Tijjani muka bari a can asibitin muka dawo gida, Hajiya sai kuka take, tana shashekar duk sai naji na damu da kai, dakyar muka dawo tambari inda Unguwar yake, na tura kan motata zuwa cikin gidan, dama motar da yake hawa tawa ce, tunda ya sayar da tashi kwanakin baya ya dauki tawa yana amfani da shi.

Koda muka fito Hajiyarsu ta ce min. "Lubabatu dama nace ko." kallonta nayi ina son naji me zata ce, sai ta ce min. "Dama kada ki gayawa Iyayenki halin da ake ciki domin idan kika gaya musu abin ba zai yi dadi ba, idan babanku na Jama'are yayi cewa ga abinda ya faru. Ki zama mace mai rufawa Mijinta asiri haka zai saka Allah ya rufa miki ta yadda baki zata ba." Gyada kai nayi ina faɗin.. "in sha Allah Hajiyarmu!" Na fita daga motar na nufi cikin gidan, na rufe bangarena parlourn na zauna nayi ta tunani kafin na shiga na kwanta, karfe biyu da arba'in da biyar na farka sallah dare, ina yi ina gayawa Allah kuka ta da matsalata, nayi tawassali da sunayen Allah tsarkaka, Allah ba zai tab'a wulakantamu ba.

Ina zaune har aka yi sallah asuba, sannan na yi raka'atu fijir, ina idarwa na daura da sallah asuba, sannan na fita na fere doya na daura a wuta, sannan na daura ruwan tea, a hankali nake bin kome ina lissafin yadda xan shawo kan matsalar ya Hafiz, wurin karfe bakwai sai ga Tijjani yazo daukar mota zai je dauko shi, "kenan ba sai an saka muku abincin ba zaku dawo ?" "Eh!" Ya ce ya fita, kafin bakwai da rabi, na hada abincin Yusrah na kai mata, na tashe ta na mata wanka, sannan na shiryata tana ihu, sai ga Hajiya ta fito. " Wai me kike mata ne? " " Wanka na mata Hajiya zan shiryata ne! " " Wanka ko mugunta? Ke fa muguwa ce ba mamaki ruwan da zafi kika yi ta kona mara mutunci, ke baki haihu ba amma salon muguntarki yafi karfinki wallahi ki ji tsoron Allah! " Kwalla ne ya cika min idanu, na gama shiryata na kawo mata abin karyawanta, tana sha tana kukan rashin mutunci. " Ni tea din ya min zafi, yana kona min baki kaka yana kona min baki! " " Ai dama nasan muguwa zata kashe ki ne! " Hajiya ta fada tana daukar tea din ta kurba, sai zare idanun tayi tana faɗin. " Takwara ai ba wani zafi, yadda yayi sanyin nan ma kulle miki ciki zai yi! " Kamar nayi kuka haka na bata doya ta furza min a fuska. " Ni kin cika yaji! " Wani irin bakin ciki naji ya cika min rai, na ce mata.. "ayya Yusra me yasa kike min haka ne? Ki ci don Allah!" Kamar nayi kuka nayi maganar, sai tura baki tayi tana faɗin. "Ba zanci ba." "Ai ba dole ba ne sai ta ci a barta haka don Allah!" Haka na hakura na barta, na kuma wuce na barsu na kawowa su Hajiya nasu don ta fara min ihun ita yunwa take ji taliyar jiya bai rike ta ba.

Haka na kawo abin karyawan, tana ci tana faɗin. "Kin iya girki amma salon mugunta irin naki sai kin azabtar da mutane!" Kaina a sunkuye na barta na riko hannun Yusra na kai ta makaranta, har lokacin ban ga Karima ba, sai da na kaita makarantar na juyo zan dawo gida, na hango su Ya Hafiz, na zata zasu tsaya su dauke ni ne, a'a sai suka yi tafiyarsu. Haka ba karasa gidan a gajiya na shiga na hada mishi abin karyawa yana zaune a parlourna, sai da yayi wanka ya dawo ya zauna yana karyawa hajiyarsa ta shigo ita da Tijjani da Yasir da har lokacin bai yi wanka ba. "Lulu waye zai yiwa Yasir wanka ne ?" Ya Hafiz ya tambaye ni, "ni ce!" Na fada ina daukar yaron da ya fara tsalla ihu, haka yayi ta ihu har kaina ta fara wani irin juyawa, gashi ya cika kashi a pamper dinsa, haka na wanke na mishi wanka na fito na shirya shi, garin shirya Yaron nan na kara fama tuntube na, wani irin kuka ne ya so kwace min, haka na daure na kai shi waje na koma daki na shiga ban daki na fashe da kuka, don sai yanzu na lura da farcen kafana ya fashe, baka hawaye yake zuba min ina jin kamar na mutu da bakin ciki, haka na gasa kafar na fito nayi wanka, na shirya cikin material.

Bayan na saka kwalli da man baki na fito, na samu sauran abin karyawan nawa da yake kitchen Hajiya da Karima sun dauka sun cinye, kitchen din na koma na dafa indomie da kwai, na zauna a kitchen din naci, sannan na fito na samu suna ta magana. Shi kuma yana zaune yana jin su, can aka buga gidan na zata Almajirin da yake min aiki ne, na koma daki tare da dauko Hijab na saka sannan na fita na bude gidan, wasu magidanta ne guda biyu, suka shigo gidan. "Alhaji Hafiz yana nan?" "Eh yana cikin bari na mishi magana,!" Na fada tare da nufar cikin gidan, "tow mun gode" haka suka jira na koma parlourn na ce mishi. "Ya Hafiz kana da baki a waje" "sun iso kenan?" Ya fada yana yatsina fuska. "Yaya kasan likita ya ce kada ka saka damuwa a ranka domin zuciyarka tana dab da bugawa!" Lumshe idanunshi yayi ya bude a kaina yana min alama da idanu wato naji dai. Sunkuyar da kai nayi ya fita, shi da Tijjani, Hajiya ta zauna tana ta zuba kwadayi tana bawa Karima labarin yadda ta sha wahala akan Ya Hafiz ni dai na wuce kitchen na wanke kayan da nayi amfani da shi, sai gashi ya shigo kitchen din, "Ina takardun gidan nan?" "Yana dakina!" "Ko zaki bani aron gidan na sayar idan na biya bashin da ake bina zan!" Rufe mishi bakinsa nayi da hannuna, ya sumbaci hannun yana cire bakinshi a hannun ya tako har jikin dogon deeper freeze na, ya haɗa ni da jikin freeze din ya shiga sumbatar goshina da manyan kumataina. Abu daya nake bukata a gare shi, shine soyayya amma na rasa ni dai a bangarena bai rasa soyayyar da nake mishi ba, haka ya gigita ni, daidai shigowar Karima kitchen din ta kawo kayan da suka ci abinci da shi, ganin halin da muke ciki yasa ta jan tsaki tayi waje, sake ni yayi ya ce min. "Maza dauko min na manta mun bar mutane a waje!" Haka na wuce dakin na dauko takardun bakiɗaya, na mika mishi kamar wacce aka katse min tunanina da lissafina haka ya amsa ya fita, ban kara ganinsa ba, sai karfe daya da ya dauko Yusra, suka shigo na zuba mata abinci tana ci sai ga Hajiya ta shigo dama tuwo nayi miyar shuwaka, na kawo mata abincinta, ta fara ci tana mita. "Kin san yadda na tsani shuwaka shine kika yi miyar fisabiilillahi gudawa zanyi!" "Ki yi hakuri Hajiya ban sani ba ne!" Na fada ina bata hakuri, na kara kallonshi na ce mishi. "Yaya Mama bata ji dadi ba, ina son na je na gaishe ta!" "Daga nan ki gaya musu ya sayar miki da gidanki ko?" Inji Hajiya, girgiza kai nayi na ce mata. "Haba Hajiya wannan fa duk bata taso ba." Hayayyako min tayi kamar zata rufe ni da duka, "Hajiya ai ta gaya miki Mama bata da lafiya ne, ki kyale ta an jima ta je. Luluna ki shirya ki tafi kin ji idan na gama zan zo daukarki!" "Shi kenan na gode!" *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*

Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu

HUƊU

Wani irin dad'i ne ya lullube ni, na gyad'a mishi. Ina me da hawayen da suka fara cika min idanu, murmushi yayi ya ce min. "Tashi ki je ki fara mata abinda zaki kai mata!" Mikewa nayi ina ta godiya. Domin ya min abinda ban zata ba, haka na wuce dakina, na sauya kayan na fito ina zuwa na samu basu nan shi da Hajiyarsu, kitchen na wuce.

Hafiz "Hajiya me yasa baki da hakuri ne? Kina irin wannan ba sai ta fara jin wani abu a ranta ba? Hajiya gaskiya ki daina min haka, kin ga yadda Allah ya taimaka asirina ya rufu akan wannan lamarin." " Amma Hafiz kasan dole dai mu kula domin tunda yan uwanta suka fara zargin wani abu dole mu kara mikewa. " Murmushi yayi ya ce mata. " Hajiya ni ba kamar ki ba, a wurin Lubnah bana buƙatar boka ko Malam, idan na tsaya ga kaina ina alfahari da haka, don Allah kada ki saka mata magana a bakinta." Shiru Hajiya tayi tana faɗin. " Tow shi kenan amma ka kula domin kuwa Malamin nan ya ce a cigaba da kulawa." " Na gaya miki ni ban yi wani aiki da abinda ya fada ba, ni kaina Aljanu ma tsorona suke." Daga haka ya bar gidan, duk sai Hajiya ta shiga damuwa, ta dauki wayarta ta kira Malaminta, ta gaya masa abin da yake faruwa. Shiru tayi kafin can ta ce mishi. " Toh bari na turo maka da kuɗin!"

* Ina ta aiki gyara kayan miya sai gaKabiru almajirina, mikewa nayi ina faɗin. "Ka iso? Ko zaka fara da shara sai kazo ka sayo min kaza." Durkusawa yayi yana faɗin. " Ina kwana Aunty? Eh na iso shi kenan!" " Shi kenan kayi sharar ina jiranka!" Na cigaba da aikina ya shiga share filin gidan bakiɗaya, ni kuma na cigaba da aikina. " Kai Uban waye ya baka izinin shigowa?" Dariya Karimah tayi tana faɗin. " Hajiya ai almajirinta ne. " " Eh samun wuri!" Yana cikin sharar sai ga Ya Hafiz tare da Tijjani, suka shigo ganin Hajiya a filin gidan suka tsaya. " Hajiya lafiya? " " Ina lafiya ashe gidanka har yayi arahar da kowani kare da doki zasu shigo? " Kallon Kabiru yayi ya hade rai. " Idan bai shigo ya taya ta da aiki ba me kike so nayi? Ita wannan me ta iya? Kin ga Hajiya ban kira ki, ki zo ku rusa min gida kamar yadda kika rusa gidan Nuru ba, ba ruwanki na gaya miki!" Shiru tayi tana da wani sunkuyar da kai.

Ina gama hada abinda nake ya shigo. " Luluna sannu ko zaki zo ina son magana da ke?" " Tow "na fada wanke hannuna, a bakin kofar parlourn na ji muryan Kabiru na fito na same shi mika mishi atm dina nayi na ce mishi. " Kaji guda uku, zaka sayo sai kifi kilo biyu da rabi ka ga bani da lokaci ka dawo da sauri don Allah!" " Tow Aunty!" Ya saka kai ya fita, na bi bayan Ya Hafiz zuwa dakina. Ina shiga na same shi a tube, yasan ina da aiki me ya kawo irin wannan lamarin yanzu? Kamar nayi kuka na ce mishi.."Ya Hafiz ko!" "Hakkina nake so!" Yadda yayi min magana take ya koma Ya Hafiz din da na sani, kwabe kayan nayi na haura gadon, .kamar yadda na sani ko minti goma ba ayi ba ya fara nishi daga nan ya sauka ya saka kayansa ya fita, ni kuma na wuce ban daki nayi wanka na sauya kaya, ina fitowa na sami Hajiya da Karima a parlourn, sai wani irin kallo suke bina da shi. "Akuya tana haihuwa domin ana kwasar Yaranta zuwa kasuwa, ke kuma sai dai ki tsotse min Yaro, bakya gaba ba kya ba." Shiru nayi na wuce kitchen na wanke shinkafa na zuba karasa da pea da green beans da karas ,na daura akan wuta na juye ruwan zafi a kai. Na daidaita wutar ina jin kamar na hadiye zuciyata. Ina cikin aikin Kabiru ya yi sallama na fito na amshi kayan na wuce ciki suna parlourn suna cigaba da zagina. Abin karyawar da na hada mishi na kawo mishi, sannan na ce mishi.."ko xaka dawo an jima ban gama ba rana ba!" "Ba kome Aunty na gode!" Yayi sallama ya tafi ni kuma na cigaba da aikina wurin karfe biyu saura na zuba abincin yan gidan, sannan na shiga wanka na sauya shigata cikin wata lace peach colour na fito ina gyara daurin dan kwallina, kitchen din na shiga turus nayi cike da mamaki. Hajiya ce ta bude kular abincin da miyar da xan kaiwa Mama, ban ce mata cikanki ba na ce wuce inda na daura farfesun kifin na sauko a hankali, na dauko wata kula na juye shi a hankali, kamar wacce kwai ya fashewa haka ta saka kai ta fita. Bayan fitar ta na d'ago tare da isa wurin kular na kara gyarawa sannan na dauko sauran da na rage na karyawa na kara sannan na gama kome na saka a basket na fito, daidai isowar Kabiru na koma kitchen na dauko mishi nashi sai godiya yake ta min, bayan na sallame shi na dawo na shiga dakina, na tattara duk wani abina me daraja na boye shi, domin nasan ba a abin mamaki ba ne gobe na gani a jikin Aunty Nana ko Haulatu, haka yasa na rufe dakin da kome nawa, sannan na saka key ɗin a jakata na fito na bar gidan, don shi kan Ya Hafiz tun dazu ya sake fita da wasu mutane.

*Dutsen tashi*

Daidai gidan Marigayi Malam Idris anan gidanmu yake, kafin ka isa gidan Malam Idris, anan aka sauke ni da basket guda uku, kafin na samu napep a unguwarmu sai da na fito bakin titin tambari housing estate, na sha zama don ma Maman Ummi da zata fita ta rage min hanya zuwa bakin hanyar unguwarmu, na tsaya kafin na samu abin hawa, haka muka iso gidan.

Yaran unguwarmu yan matasan suka taso da sauri suna faɗin. "Lubnah barka da zuwa!" Murmushi nayi suka dauki kayan ina amsa musu. "Yawwa Amir kai ia girma haka? Lallai girman dan mutum, Jamal ka ne haka ka zama kato!" "Kai Aunty Lubnah ba wani katon da na zama, ga Waheed naj baki ga girmanshi ba sai ni! " Suka fada murmushi nayi muka isa kofar gidanmu me dauke da shagunan provision. " Lubancy ke ce daga sama haka? " Murmushi nayi na ce. " Eh Malam Anas ni ce! " Na wuce Yaran suna bina da kayan har cikin gidan, yadda muryata ya karad'e cikin gidan sai da kowa ya fito har da Aunty Innah dama tazo ne? Wani murmushi suka min na karasa har da Aunty Munah. " Aunty Munah yaushe a gari?" " Korata kike kenan? Ke dai mugun halinki na kin mutane yana nan har yau baki sauya ba." Murmushi nayi na koma inda Yadiko take alola na durkusa har kasa na gaishe ta. "Da fatan da izininshi kika fito? " Gyada kai nayi ina kallon kasa. " Tow sai ki gama ki koma da wuri don unguwarki da nisa!" " Haba Yadiko daga zuwa kamar mai ɗaukar wuta sai a fara mata maganar ta gama ta koma! " Inji Aunty Munah, daga can dakin aka ce mata. " Ai baki ga kome ba, sannan yadiko ta mata da kauna tsaya ki ga yadda Mama zata mata. " Inji Ya Sani da yake dakin yana cin abinci. Ya fito dauke da plat din abinci, " dube ta kamar Bakuwa" ya fada yana mita. " Aunty xamu tafi sai mun kara shigowa. " " Ku tsaya mana! " Na fada ina buɗe jakata na dauko dubu daya na mika musu. " Ban san zan ganku ba, ban saya muku tsara ba;" " a'a yayi yawa mun gode ko Waheed! " "Maza karba kafin na saka ki wanke gidan! " Inji Ya Sani, karba suka yi tare da fita da gudu suna godiya. " Mama tana ciki? " " Eh! " A hankali na ja kafa na nufi parlournta zuciyata tana wani irin tsalle. A hankali na shiga parlourn tana addu'a, ga Aunty Hindatu da take ta fama da laptop dinta. "Yar renin hankali tun yaushe na gaya miki bata da lafiya!" Zama nayi a gefenta, tare da daura kaina a kafadarta. "Am soweer." Na fada ina wasa da yatsuna. Shafa addu'ar muka yi abinda ya fito a bakin Mama yafi kome dukana.. "Me ya kawo ki? Da izinin waye kika tawo? Bayan ko yau sai da Mijinki ya gaya mana baya gari idan ya dawo zaku zo tare." Wani irin abu ne ya tsaya min a rai, yaushe Ya Hafiz yayi tafiya, amma sai na yi shiru ban ce mata kome ba. Ta kara da cewa. "Ya gaya mana Tijani zai kawo Hajiya Asiya an jima Asibiti kuma ya kamata ace kina gidan." Yadda Mama take shiga ba nan take fita ba, sai naji zuciyata tana wani irin ciwo kamar kaikayi. Ni dai kamar yadda aka saba kaina a sunkuye, wayar Mama ne yayi kara ta dauka tana faɗin. "Na'am Alhaji gata nan tazo!" Ta mika min wayar. Yadda ya balbale ni da fada yasa nayi shiru kamar yana gabana ya cigaba da cewa. "Kin san Abokiyar zamanki bata gari, sannan ta bar miki Yarinyarta taya zaki kai yarinyar makota? Ke wacce irin mahaukaciya ce? Don Allah bai baki haihuwa ba sai ki na wulakanta mishi Yarshi? Wai ma da izinin waye kike fito? Ga Hajiya Asiya can da Tijjani sun je gidan ba kowa, ke a rayuwarki idan baki saka mu magana ba, bakya jin dadi ne?" baba yana yin nashi a waya, ta yadda yake shiga ba nan yake fita ba, haka Mama tana yin tana kamar ta rufe ni da duka. Nasan cewa duk lokacin da zan zo matuƙar ba shi zai kawo ni ba, tow na rantse da Allah kamar yar riko haka nake komawa amma idan ya kawo ni kowa yayi ta ririta ni. Aunty Hindatu na ta kasa jure fadar Mama ta ce mata. " Mama dai, ya kamata ku fahimci Lulu ba zata fito don kanta ba, sannan taya zata fito a ce! " "Gafara can, an gaya miki bamu san yadda kike hure mata kunne ba ne? Ko an ce miki bamu san yaddA kika mata wayo kina rabata da kuɗinta, me yaron nan ya rage ta da shi? Ko an gaya miki ban san me nake yi ba ne? Wallahi Hindatu idan baki daina shiga rayuwar Lubnah da gidan aurenta ba na rantse da Allah sai na miki Allah ya isa, kuma ki zauna yanzu su Hajiya Asiya zasu tawo ku koma gida Wallahi, ina zaman lafiya da Mijina ba zaku kashe min aure ba ke da Yan uwanki! " Cikin fushi Aunty Hindatu ta shiga hada kayanta Ya Sani daga waje da Aunty Munah, suka shiga kananun magana, yadda Ya Sani yake mita yasa Yadiko ta dirko musu kamar zata rufe shi da duka, har tana faɗin. "Idan wani ya kara shiga rayuwar auren Lubabatu sai na mishi Allah ya isa, tunda burinku shine ku kashe mana aure, idan da kuna da hankali tausarta zaku yi ba ku tsaya kai da fata bata yin kuskure, tun kafin ta iso muka san cewa gaban kanta tayi, haba me yasa Lubabatu take haka ne? Yaron nan yana girmama ki amma ke kin dage sai kin zubar da mutuncinki."

Kiri-kiri suka hade kai suka min tas Aunty Munah da haushi ya mata itama barin musu gidan tayi ta nufi gidan Ya Umar da yake makama jahun, Ya Sani ma haka ya bar gidan babu shiri, ni daya kamar mayya haka suka yi ta fada bayan sun gama, kuma suka sauko tare da min nasiha, har Yadiko ta shigo da abincin da na kawo suka ci da Mama, ni dai kaina yana kasa har lokacin ban d'ago kai ba, sannan ban ce musu cikanku ba. Kai mai karatu wannan sai ya zame maka sabo amma a wurina ba sabon abu bane, da na san haka zai faru da Hajiya tace na fasa zuwa da na fasa. Kiran Sallah la'asar ya saka na mike zuwa ban dakin Mama nayi alola na fito na gabatar da sallah la'asar. Bayan na idar ina zaune sai ga Hajiya da Yusrah, tana zuwa da gudu ta fada jikina tana faɗin. "Lulu shine kika tafi kika bar ni." "Yusrah babu Mama sai Lulu ba uwaki ba ce?" D'ago kai yarinyar tayi ta ce mata. "Allah ya kiyaye ta zama Uwata, ko Hajiya " wani diriricewa Hajiya tayi Tijjani ya daka mata tsawa, yana faɗin. "Kun ga yarinya mara tarbiyya, Lubnah haka kike tarbiyyar Yarki!" Ni dai bance musu kome ba, ina jin suka gaisa da su Mama da Yadiko, sannan aka zubo musu abinci suka ci sosai.. har a lokacin mamaki bai daina kamani ba yadda suka tawo da tsaraba niki -niki, suka bawa su Mama da Yadiko, yadda Hajiya take wani tarerayata, abin sai yafi kome bani tsoro tabbas Hajiya idan suka saka mu jariri zasu cije shi ya mutu har lahira.

Duk uban abincin da na saka musu amma anan da aka kawo musu abinci sai da suka ci kamar ba mutane ba, har zuwa lokacin idanun Hajiya yana kan kular abincin, sai da Yadiko ta zuba mata hankalinta ya kwanta tana ci tana murmushin, a hankali na tashi na koma dakin Mama na kwanta, wayata ta ce tayi ƙara na ɗauka tare da kallon screen din wayar, shine dauka nayi a sanyayye ya ce min. "Da fatan kin sami kowa lafiya!" Murmushi nayi nace mishi. "Suna lafiya!" Sai yayi shiru. "Luluna ki yi hakuri wallahi nayi haka." "Wani abu ne ya faru kake bani hakuri?" Shiru yayi yana jina kafin ya ce min. "Sai kin zo gida zan miki bayani!" "Wani bayani babu abinda ya faru, don Allah ka daina damuwa akan haka." Daga haka na kashe wayar, na kwanta duk da haka sai da ya kira ni ina gani naki dauka har na kwanta kaina azabar ciwo yake, da yake mun san cewa barcin yamma babu kyau amma saboda yadda kaina yake ciwo yasa na kwanta. Karfe shida da wani abu ba ji kiran sallah, sai lokacin na lura da yadda aka lullube ni da mayafi. A hankali ba bude idanuna da suka min nauyi, na dafe goshina ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu. Zama nayi ina dafe da kan har Mama ta shigo dakin. "Baki da lafiya ne?" D'ago kai nayi ina murmushi na ce mata. "Lafiya lau!" Na mike da kyar na nufi ban daki na yi alola na fito, na gabatar da sallah, itama sallah na samu tana yi ina idarwa na zauna a wurin shiru sai da ta shafa addu'a sannan ta ce min. "Me yasa kika fito ba da izninsa ba?" "Ba kome!" Shiru tayi tana kallon yadda nayi shiru. "Kina son Abbanku ya sake ni ne?" Girgiza kai nayi, sannan ta cigaba da min nasiha tare da fada domin babu wani abu me kama da rarrashi a cikin kalma ta don gaya min take zan kashe mata aure ne, tunda nasan cewa akan Hafiz Baban Bauchi bai da hakuri, ni dai ban ce mata cikanki ba har ta gama maganarta sannan ta fita, bayan isha na isa parlourn Abba na gaishe shi, ashe Ya Hafiz ya iso sai lissafi yake tare da gaya mishi abubu yan da ya faru a tafiyar da wasu dalilai da yasa aka samu matsala. Yadda Baban Bauchi ya yarda da Ya Hafiz kaf Yayuna maza da mata babu wanda ya yarda shi haka, durkusawa nayi na gaida Baba yaƙi amsa min, sai da Ya Hafiz ya ce mishi. "Baba tana gaishe ka!" "Ba zan amsa mata ba, akan me zan amsa mata bayan ta fito ba da izininka ba, tasan irin masifar da take shirin kawo min idan da yau mutuwa nayi da Allah zai saka Mala'iku su d'aga ni su ce ga abinda Yarka take yi!" Nan dai Ya Hafiz yayi ta rarrashinsa da kalmai masu dad'i, sannan ya kara da cewa. "Matukar kina son na kaunace ki Lubabatu ki bi Mijinki sau da kafa, don baki san irin asarar da kika janyo mishi ba ne ke da Hindatu itama zan kira Mijinta na ja mishi kunne tunda ku Yahudawa baku san yadda zaku bi aurenku sau da kafa ba. Kuma zan kira Addu'a da Umar da Tahir na ja musu kunne kada wani ya kara tura miki kosisi tunda ba zaman aure zaki yi ba."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull