ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 4
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 4: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 4. Yadda Baban Bauchi yake shiga yake fita sai ka rantse da Allah wani abu na aikata, wannan shine…
4,315 words
Yadda Baban Bauchi yake shiga yake fita sai ka rantse da Allah wani abu na aikata, wannan shine burin Ya Hafiz duk ranar da zan zo matuƙar bai mishi ba koda kuwa ya amince tow sai na fuskanci tashin hankali a cikin gidanmu. Ni kuwa kamar wacce ake watsawa ruwan zafi haka nake jin maganar su kamar danyen guba, nasan Iyaye suna kaunar Yaransu akan kansu amma ni nawa Iyayen sun zaɓi abinda za a fada a kansu sama da rayuwata, yadda ya gama fadar ya daka min tsawa akan na roki Ya Hafiz, har a lokacin idanuna wani irin zafi suke min, kaina a sunkuye na ce mishi. "Ya Hafiz ka yafe min." Muryana tana rawa, "Wallahi na yafe miki,matukar ni zan d'aga miki kafa ki shiga aljanna wallahi na d'aga miki ki shiga Allah na yarda da Lubnah Allah ka yarda da Lubnah!" Wannan yar draman da yayi a gaban Babanmu sai ga Baba yana irin farin ciki domin shi dai yaga yadda Ya Hafiz yake kaunata, Ya Hafiz ya ce mishi. "Baban Bauchi ka amsa gaisuwar Princess don Allah!" Cikin murmushi irin na manya ya ce mishi. "Na rasa ganewa Hafiz yadda kake kaunar Lubnah baka hango laifinta. " " Mace ta gari ce, tana da kirki da mutunci. Ba iya soyayya ya bani ita ba, Allah ya yarda da ita ne ya bani ita. " Yadda Ya Hafiz yake faɗan kalaman yabo yasa Baba ya kuma juyowa yayi min nasiha, da nuna min yadda Ya Hafiz yake kaunata kaf duniya babu namijin da zai min irin wannan soyayyar da yake min na rike mijina domin kaf duniya babu me min irin son da yake min.........
*08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu
BIYAR
Tabbas Ya Hafiz yana kaunata, amma kuma me yasa yake min haka? Me yasa sai mun gama kome da shi yake juya min laifin? Ina ga ko yadda ya musu bayani ba haka suka dauka ba, amma zan tambaye shi ko nice ban fahimci yadda suke ganin laifina akan fitowa da nayi ba tare da izininsa ba, domin a sanima da izininsa na fito zuwa gidanmu, a hankali na fito daga dakin Babanmu, a bakin kofar muka hadu da Jalilah yar rikon Yadiko ce, amma yar uwarmu ce sosai, sai dai Jalilah ni da ita bama ga maciji saboda kawai kowa da abinda yake tsammani a tare da shi.
Ni dai ban san me na mata ba, amma tare muka taso, zuwa yanzu dai auren Jalilah uku, tana zawarci sannan yan uwarmu ce na kusa sosai domin Mahaifinta kanin Baba ne, mahaifiyarta kanwar Yadiko, a sanina Jalilah kawar Ya Hafiz ce, kuma kawar Matarsa domin tun aurensu suke tare. Kallo daya tayi min ta dauke kai, nima na dauke kai kamar ban san tana wurin ba. Dakin Yadiko na nufa na ce mata. "Yadiko zamu tafi!" "Tow Allah ya kiyaye hanya, sannan ki daina fitowa ba tare da izinin Mijinki, baki san kin girma ba ne." Ni dai bance mata cin kanki ba, har ta gama magana na wuce dakin Mama na hada kayana. Ina hada kayana sai ga Ya Umar ya shigo da sallama, murmushi nayi na zauna. Sai da ya fara gaida Baban Bauchi da Yadiko, sannan ya shigo ya samu su Hajiyarsu Ya Hafiz ana ta surfa abinci, kallona yayi yana murmushi ya ce min. "Auta shi ne baki karaso makama ba?" Murmushi nayi na ce mishi. "Ina wuni Ya Umar!" "Lafiya lau!" Kafin ya rufe baki Mama ta tab'e baki ta ce mishi. "Ai fitowa tayi ba da izinin Mijinta ba!" Kallona yayi yana murmushi ya ce mata. "Tsakanin da Allah auta ta wuce sai ta nime izinin zata zo gida nan, kada ki manta Hafiz dai a gidan nan ya taso haihuwarshi ce ba ayi ba, sannan na biyu idan Auta ta tawo babu izininsa meye ribarta? Kayyasa Mama Hafiz da Lubnah dukkansu Yaran gidan nan, kuna nazari kafin yanke hukunci gudun kada a tsaya a gefe guda!" Da yake sunan Ya Umar sunan Baba Malam ne wato Kakanmu bata iya ko d'aga mishi murya ta ce mishi. "Mai sunan Baba Malam!" "Mama maganar Allah nake gaya miki kafin Hafiz ya auri Lulu mu ne muka fara auren Yaran wasu, yanzu saboda yadda Habibah ta samu wuri wallahi idan zata fita sau dari bai wuce ta gaya min sau biyu ba, mu Yaran wasu muka musu adalci sai mu namu ne ba zasu samu adalci ba? Mama ita yarinya ce bakiɗaya shekaru tara ake nima da aurenta idan kuka tsannanta mata bata da inda ya wuce nan ku sani shi Hafiz namiji ne, hmm kayya. Lulu kina son wnai abu ne? " Da zumudi na mika mishi takardan da nazo da shi. Budewa yayi sannan ya ce min. " Ok akwai ma a gidan nan kamar jiya aka yanka abokina dan liti zai zo ya saya. Fita yayi ina jin yadda Yadiko take gaya mishi abin da ya faru, itama nan gaya mata gaskiya yayi ya saka Ya Sani ya cire min kajin, duk wannan abin da ake Hajiya kunya ce ta kamata bata iya magana ba, sai sunkuyar da kai itama Mama sanin cewa Ya Umar ya daure ta da jijiyarta yasa bata yi magana ba, a can parlourn Baba naji yadda Ya Hafiz yake faɗa shi da Ya Umar, koda yake Ya Umar ya gaya mishi magana daya ya ce mishi. "Ka gama duk abinda zaka yi, wa'adin Allah gaskiya ce, ni da kai mun san kome! " Ba sai Ya Hafiz ya fusata ba, ya mike tare da sallama yana faɗin. " Na hakura da Lubnah tunda ban muku adalci ba! " Nan Baban Bauchi ya dirkowa Ya Umar fada yake kamar zai cire bakinsa, har da cewa. " Idan kuka kashe mata aurenta ko bayan raina ne ban yafe muku ba. " Murmushi Ya Umar yayi ya ce musu. "Ni ba zan kashe mata aure ba, ai ita mace baka ce mata kaso aurenta ki zo mu zauna wannan wani lamari ne da Allah yake shirya faruwansa! Ka yi hakuri Baba idan na ɓata maka rai!" Ko amsa masa sallama Baba be yi ba ya bar gidan, haka Baba ya zauna da Ya Hafiz yayi ta bashi hakuri, har da kiran Hajiya ya bata hakuri wai ta bawa Ya Hafiz hakuri.
Abin bai yi dad'i ba, domin haka muka baro gidan zuciyata ba dad'i. Kaina a sunkuye a cikin motar. "Ban da rashin mutunci irin na Yaran Salamatu don an rufa muku asiri an yi muku alfarmar auren yarku sai ku saka min d'a a gaba? Wallahi kun yi asarar!" Haka Hajiya take fada,
shi dai bai ce kome ba, zuwawa yanzu ya fara jin wani irin yanayi a tattare da shi, "Hajiya don Allah ki mana shiru!" Yadda yayi magana a karfafe zaka ɗauka ba ita ta haife shi ba, jin yadda ya daka mata tsawa yasa ni na sha jinin jikina na koma gefe da jikin kofar, har muka iso Tambari, na bude motar na fita tare da ɗaukar kayan da nazo da shi, kaya sosai aka hada min Mama da Yadiko wai kada na tashi hankalina. Bayan na shigar da kome na wuce zuwa part dina na saka kome a muhallinsa, sannan na wuce zuwa kitchen na daura ruwan zafin na zuba a flast, kafin na fito a kujeran Parlour na hango shi. "Zo nan!" Ya ce min, na taka a hankali jikina yana rawa domin nasan irin wannan kiran babu alkhairi a cikinsa. Durkusawa nayi a gefen kafarshi ina me sunkuyar da kaina. Shiru ne ya ratsa parlourn kafin ya ce min. "Me kika gayawa Umar?" D'ago kai nayi da sauri ya tsinka min mari, sai da naji wani irin shuuu a kunnena, bakiɗaya kaina ya fara min irin wannan ciwon da yake min tare da juyawa. Rike fuskana nayi da kaina. "Tambayarki nake!" Tsoro da tashin hankali, ya hana ni magana kara rufe fuskana nake ina girgiza kai. "Tambayarki nake?" Ya kara zuba min wani irin gigitaccen mari da yasa ni zama da duwawuna, nace mishi. "Wallahi ban fadi kome ba, ka yarda da ni." Na fada ina fashewa da kuka, haka yasa take ya kyale ni, ya bar parlourn anan na cigaba da kuka har dare ya raba na wuce daki na kwanta, haka nayi kuka har na godewa Allah, kwanciyar da nayi har na fara barci ya shigo ya bani wata magani na amsa na sha, ko minti goma ba ayi ba na fara jin kaina yana wani irin juyawa a hankali na kwanta.
Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai da asuban fari na tashi na shiga wanka, bayan nayi wanka na fito duk yadda naso na tuna mai ya faru na kasa, sallah nafilla nayi na wuce zuwa kitchen, ja daura abinda zan daura sannan na fito zuwa dakin nayi , bayan na idar na koma na fara aikin abin karyawa karfe bakwai saura na nufi bangarensu, na taso Yusrah amma yarinayr nan tayi ta min ihu har da wani abu kamar tana dambe da ni, ihun da take min da kuma yadda nake jin wani abu me karfi a kaina yasa na daka mata tsawa. "Don Allah tsaya na miki wanka!" Wannan abin na mata yarinyar nan ta fasa ihu, sai ga kowa ya shigo ban dakin, ba tare da wani bincike ba ya Hafiz ya rufe ni da duka, kamar zai kashe ni, saboda karfin azabar duka zubewa nayi akan gwiwata hancina yana zuba da jini. "Tashi ki mata wanka!" Ƙasa tashi nayi ina kife a wurin, koda ya d'ago ni, sai komawa nayi na kwanta sharaf kamar an jika tsuma, abinda ya saka hankalinsa ya tashi amma saboda rashin imani ya ce min. "Wallahi idan baki tashi ba, na taso sai na kara taka ki, jaka juya wacce bata san darajar haihuwa ba" "Gara ka gaya mata dai, ban da rashin mutunci ki saka yarinya a gaba da azaba, ke ina danginki gani suke ana cutar da ke!"
Sai dai duk abinda suke yi bai saka na motsa ba, anan suka fahimci fa babu numfashi a jikina, abinda ya firgita su har Tijjani ya shigo yana faɗin. "Yanzu kana ganin daidai ne abin da ka yi? Kana tsammanin yadda Umar yake kallon idanunka zai kyale ka ne idan ya ji abinda ya faru? Kana abu kamar mahaukaci yarinyar nan kana amfani da ita yadda bai dace ba, ba fa Ubanta baya sonta ba ne a'a alfarma ya maka saboda Abbanmu, ka sake aka gano yadda kake azabtar da ita wallahi ka ji na gaya maka, ba ruwan kowa da kai ne ka fara waye ne ya fara. Kuna ganinsa zai kashe musu yar mutane bayan kace jiya ka mare ta, yau kuma ka kara rufe ta da duka. Ji yadda take sume ni dai ina shaye-shaye amma wallahi na fi karfin dukar mace kamar yadda kake yin nan ai abin ya koma jahilci kuma!", daga haka ya fita zai gashi da ruwan gora mai sanyi yana zuwa ya samu fuskata ya zuba min, ajiyar zuciya na sauke ya ce min.." tashi ki koma part dinki, Yarinyar idan baza du shirya yarsu ba, to su barta ko na kira Baban Jama'are yau wallahi na gaji da iskancinka Hafiz na gaji da muguntarka idan kayi wasa sai na gayawa Abbanmu! " Sanin cewa dan shaye-shaye ne bai da mutunci zai aikata. Dakyar na tashi na nufi hanyar fita, tunda na shiga parlourna, rufewa nayi na kwanta a saman kujeran parlourn nayi ta kuka ina jin kamar zuciyata zata buga, na rasa gano laifin da nayiwa Ya Hafiz. Zuwan Kabiru na bude mishi kofa nayi na zuba mishi abinci nace ya je yau ba aiki. "Aunty me ya same ki?" "Ba kome!" Shiru yayi kafin ya ce min. "Aunty ki yi hakuri kin ji, akwai abinda nake son na kawo miki idan kin amince sai na kowa miki!" Gyada mishi kai nayi nace mishi. "Na gode sosai!" Juyawa yayi ya tafi ni kuma na koma daki nayi wanka na kwanta, buga kofar parlourn da aka yi yasa na fito, na buɗe.. "wani irin abu kazan-kaza ne? Uban waye zai bamu abinci muguwa azaluma ke wacce irin dabba ce. Amma kin iya sakawa wancan dan iskar Yaron ke jaka wawuya wacce iyayenta suke niman kai da ita." Ni dai tunda ya fara fada na koma jikin bango na makale ban kara sakewa ba. Har ya gama ya bar parlourn, kitchen din na wuce na hada abin karyawan bakiɗaya na kai musu. Anan Hajiya ma ta rufe ni da zagi cin mutumci da gorin rashin haihuwa, sai na ji ba zan iya kuka a gabansu ba na fito na dawo dakina, ina zama wayata tana kara wacce take saman center table, dauka nayi fada Baban Bauchi ya rufe ni da shi, har da cewa wallahi na sake na kashe Aurena sai dai na nimo wani uban ba shi ba, yana kashe wayar Mama ta kira ni itama ta min tas har da barazanar zata tsine min,tana gamawa. Ya Umar ya kira ni yana tambayata mai ya faru? Murmushi nayi na ce mishi ba kome. Duk yadda yaso yaji me ta faru nace ba kome wallahi.
Haka wunin ranar ban saka kome a bakina ba, washi gari Hajiya suka bar Bauchi amma ta ce zata dawo kwanan don tafiyar ya zame mata dole ne kuma domin danta tayi shi. Sannan tafiyar kusan nice na tura musu kudin mota domin tana zaune ranar Ya Umar ya tura min dubu hamsin ya ce na rike a hannuna, don haka ta cewa danta a kan idanuna. "Yayanta ya bata kudi ban san ko nawa ba ne." "Shine bakar munafuka bata gaya min ba." Fisgar wayar yayi yana faɗin. " Mai mugun hali! " Ya fada bayan ya tura dubu arba'in ya bar min dubu goma shima a take ya turawa Matarshi biyar ya bar min biyar, ya je ya cire musu kudin ya basu dubu sha biyar ya rike ashirin da biyar. Ni dai bance kome ba domin tsoron kada ya kara rufe ni da duka yasa har suka bar gidan ban kara tari ba.
Bayan tafiyarsu da ta tabbatar zasu dawo very soon, haka na cigaba da zama a gidan Ya Hafiz ya min, Matarshi da Yaransa su min. Haka ya sa bakiɗaya na shiga wani irin tashin hankali, idan Yaran suna min ihu wallahi sai naji kamar a cikin kwakwalwar kaina suke ihu hatta jikina wani irin rawa yake lokaci guda sai naji kamar zan mutu, gefe guda kullum sai Ya Hafiz ya bani maganin nan, wanda a cikin sati biyu na fara kaunar maganin domin idan ban sha ba, bana iya barci bana iya rintsawa har gari ya waye.
Haka ya kara min kadaici, kullum ina dakina, shima a cikin duhu babu haske. Sannan bana iya magana idan na ji muryan Ya Hafiz sai na ji kamar wani abu ya cika min raina, haka yasa tsoronshi ya kara cika min rai da gangan jikina. Satin Hajiya uku da tafiya sai gata, can gidan da ya saya a zango suka tafi aka ga gidan the next day, ina kwance a parlourn sai gashi ya shigo. "Malama gobe zamu tashi ban ce ki min gayyar mutane ba!" Ina son na tambaye shi kamar ya gobe zamu tashi? Amma ina d'aga kaina ya bani wani irin tsoro, da sauri na sunkuyar da kaina. Abu daya na iya fada. "Allah ya kai mu!" Daga nan ban kara magana ba, tsoron shi da gudun abinda zai yi yasa nayi shiru. Tunda ya gargade ni da kada na gayawa kowa zamu tashi ban sake nayi ko tari ba, amma a cikin raina bana jin dadi haka na shiga hada shirgina ina tattarawa, da taimakon Kabiru muka hada kome na gidan, ya mika min wani leda ya ce min, ki ajiye wata rana idan kika samu lokaci ki karanta addu'ar da yake ciki ko ki saka a miki rubutunsa ki sha akwai amsoshinki a cikinsu, zan yi kewar Uwar dakina!"
Nima godiya nayi ta mishi na rubuta mishi number na, don ba shii da waya, haka washi gari na shiga makota na sallame su, sai a lokacin suke gaya min ai su tun sati uku da ya wuce suka san zamu tashi, suka mana fatan alkhairi, na musu godiya sannan muka bar unguwar bayan an kwashe min kayana muka bar unguwar da na dauki tsohon shekaru tara ban yi fada da kowa ba yau Yaya ya d'aga ni daga cikin mutanen kirki ban san inda ya kai ni ba, can zango ya kai mu kusa da titin jirgin kasa, anan ya saya yi gidan. Sai dai ko rabin bangarena bai kai ba, dakuna uku ne, amma kuma suna da girma haka na zuba kome nawa a cikin dakin har ma ya kasa domin idan xan yi sallah sai ka rufe kofar kusan ni daya nayi aikin mai da kome na, sai kitchen da yake waje sai na fito tare da ban daki da yake waje, a da can dakinmu yana da nisa da juna amma a yanzu daga dakinsa sai nawa. Haka a ranar dai a dakina Hajiya ta kwana akan gadona da danta ni na kwana a dogon kujera.
Washi gari na tashi na fara aikin abin karyawa, ga wani sanyi da yake ratsa ni haka na gama ina atishawa. Bayan na gama na kai musu kowa dakinsa, sannan na kawowa Hajiya nata, na koma waje na karya sannan na hada ruwan wanka na shiga nayi, ina fitowa naji kamar zazzaɓi zai rufe ni, haka na saka kaya na fito dakin Ya Hafiz, na ce mishi. "Don Allah ka bani magani bani da lafiya ne!" D'ago kai yayi yana kallon yadda nake takure wuri guda. Bai ce kome ba, ya ce min. "Tow!" Ya tashi ya dauko min har da wanda ya ke bani na sha, ya ce min. "Ina son na fara ruin nawa business din Ina son kudi amma narasa inda xan samu ko zaki bani aron kudi ne?" Shiru nayi ina kallonshi kafin na ce mishi.. "Ai!" "Tashi idan kin yi nazarin abinda zaki bani nan kwana uku ina jiranki!" Haka na fito ina mai barin dakinsa na koma dakina na kwanta, kwanciya nayi haka na fara barci sama sama, na ji an zuba min duka a bayana, bude idanu nayi ina kallon Hajiya ce. " Kin tashi ko yaya anya ba shaye-shaye kika fara ba? Waye zai daura mana abincin rana yau har da tuwon dare zaki mana! " Dakyar na mike kaina yana bala'in ciwo, na nufi waje na daura abincin rana, wurin karfe daya na gama nayi sallah na kwanta don ko abincin ban kalla ba, barci yayi gaba da ni wurin karfe hudu na ji an watsa min ruwan sanyi a firgice na tashi Hajiya ce ta saka Yusrah ta watsa min. " Yawwa takwara gara haka, Uban waye zai mana abincin dare! Mau farar kafa kawai tunda Hafiz ya aure ki, tsiya yake binsa. " Haka nayi sallah la'asar sannan na wuce na daura tuwon semovita miyar busashen kubewa, abin da na fara fahimta kayan firjina sun fara narkewa gidan ba wuta, ina cikin wannan nazarin ya Hafiz yanzu da mai aikin wuta, ashe an saka abin invert dinmu bai jona ba ne, haka aka jona mana muka samu wuta, da nazo cin abinci mika min yakin daddawa Hajiya tayi tana faɗin.. "Gashi nan ki na ci da abinci, domin ke na daka na kawo miki . " Amsa nayi nayi ta mata godiya yaushe na samu gatan da har Hajiya zata min kyauta, ai ko zan mutu ba zata ba ni abinta ba sai ma ta amshi nawa, haka na cigaba da abinda nake, kafin na zubo abinci na fara ci ta ce min. " Idan ba zaki ci ba, bani abina. " A hankali na ce mata." Zanci kai! " Na bude ledar na fara cin yajin ina barbadawa a cikin abinci. " Dama sai da na kashe kudi kusan dubu biyar a hada yajin nan, yanzu gashi xan koma bani da sisi dan uwanki kuwa na mishi magana ya ce bai da shi.... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu
SHIDA
Haka kawai Hajiya ba zata min abu don kanta ba sai dai idan tana da buƙatar wani abu daga gare ni, shiru nayi domin yanzu bani da kosisi iya dubu biyu ne a cikin account dina, idan na fada ba yarda zata yi ba. Don haka nayi shiru haka na kyaleta tana ta rabtabo bayaninta ganin bance mata kome ba, sai ta fara masifa ni dai har ta gama bance mata uffan ba, domin nasan kara mata haushi zan yi, haka ta bar dakina zuwa dakin Karimah wacce suke can da Ya Hafiz, suna cin gas meat, shigar Hajiya dakin ta ga sun baje suna ta fama wadaka da abin arziki ga Country Yorghurt a gefensu, zama tayi tana hadiye yawu. "Yanzu Hafiz haka zamu yi da kai, ka zauna kana cin abin arziki ban da ni. " Hade rai yayi yana faɗin. " Hajiya matsalata dake baki da hakuri so nake na gama na kira ki! " Shiru tayi tana kallonshi sannan ya tura mata wani karamin kulli gabanta. Haka ta bude tana tab'e baki alamar ta rena ba haka ta so ba, ta cinye amma maganar gaskiya bai ishe ta ba, amma ba yadda ta iya ta nad'e kwadayinta tayi musu sai da safe. Ina kwance a dogon kujera ta shigo ta kwanta a gadon, bamu jima da fara barci ba invert dinmu ya dauke gashi ba maganin sauro, abin ba dad'i haka muka kwana a kuntacce, domin ban saba da irin wannan rayuwar ba, tun tasowata. Haka muka kwana a can dakinsu Ya Hafiz basu yi irin kwanan da muka yi ba, abin sai ya hadu min goma da ashirin, domin dakin wani irin zafi kamar gidan burodi ya ɗauka, zarewa ne ban yi ba amma har kusan lokacin da nake tashi sallah dare ban iya rintsawa ba, gashi Ya Hafiz bai bani maganin da yake bani ba, abin sai ya min yawa. Bayan sallah asuba na fito na daura musu abin karyawa da ruwan wanka, na shirya Yusrah sannan nayiwa Yasir wanka na basu abinci, nan Yasir yayi ta kuka har sai da Uban ya fito yana faɗin. "Ke dai azzaluma mace, uban me yayi miki!" Nasan ba yinsa ba ne, ina da yakinin zai dame na, zai dainaim. Abinda yake yi ya dawo mu shirya kamar baya. "Ba magana miki ba!" Shiru nayi sai da ya zaburo kamar zai dake ni nace mishi. "Ban san me yake damunsa ba" na fada mishi ina kallon Yaro na yake ta zufa. Karban yaron yayi ya ɗan jijiga shi daidai fitowar Hajiya da Karamcy, amai ya fara yi, kuma ai laifina ne tunda na hango ya koshi amma yaki ya daina cin abincin ni kuma na kasa daina bashi wai kada yayi kuka. Sai da ya amayar da abincin da yaci sannan ya sauke ajiyar zuciya. Cikin jin haushi Karimah ta bangaje ni, na taka aman Yaron na zame nayi zaman yan bori. "Muguwa mai bakar zuciya, ke baki haifa ba. Amma kina son ki kashe min, idan kin yi zuciya ki haifi naki mana. " " Gata mata dai ba zuciyar haifa sai na kashi." Inji Hajiya, ni dai kamar wata sokuwa sai na yi kasake ina kallonsu, ko ya tuna wani abu ne ya fara faɗa, da cewa baya son abinda suke yi. " Luluna tashi da gangan ba zaki cutar da su ba." Ai kuwa na fara gyad'a kai ina kokarin mishi bayani, haka ya dakatar dani da abinda zan faɗa. Haka na tashi na koma daki na sauya kayana, na gyara inda Yasir yayi amai na wanke, da yake gidan akwai rijiya.
Ciwon da kaina yake yasa na gyara kwanciyar da nayi a dogon kujera. " Lulu yunwa nake ji. " Inji Yusrah. "Na kai muku abincinku wurin mamanki! " Wani irin ihu yarinyar ta fasa sai da naji kamar ƙwaƙwalwar kaina zai yo waje, wani irin tartsatsi kawai nake ji a cikin kaina, wanda ya tilasta min na dafe kaina, zufa na karyo min. Sai na rasa me yake damuna ga wani irin sound nake ji yana kara a kaina, ji nayi kamar duniyar tana juya min, a hankali na shiga ambaton Allah tare da komawa jikin kujerar na kwanta ina min zuciyata tana wani irin bugawa mai karfi, shigowa Hajiya da Karimah ganin yadda nake ta haki da zufa sai suka ka ja hannun yarinyar suka fita da ita. Ni kuwa suka bar ni cikin wannan yanayin. Karshe har dare ina kwance a wurin, ya shigo suna ta hidimarsu babu wanda ya gaya mishi ga halin da nake ciki, sai da gama abinda ya mishi kafin ya ce musu. "Yau mugun halin ya motsa taki fitowa!" Babu wacce ta amsa mishi, haka yasa shi mikewa ya leka dakin dubu babu haske, torch din wayarshi ya kunna ya ga halin da nake ciki, "Innalillahi wainnalihir rajoun, Hajiya Karimah me ya same ta?" Ya tambaye su, take suka taso dukkansu suna faɗin. "Tow me zamu sani tunda ita dai bata fitowa cikin mutane." Da sauri ya ciro wayar shi ya kira Abokinsa da yake amsar magani a wurinsa, ƙarshe dai zuwa yayi ya dauko abokin domin tun a can ya mishi bayani, shi kuma ya tawo da kayan aiki. Sai da ya fara gwada hawan jini ya ga yadda ya tashi. "Amma kace matar nan matarka ce?" "Eh kai!" "Gaskiya akwai wani abu!" Haka ya cigaba da aikinsa sai da ya saka min ruwa da allurai, sannan ya rubuta mishi magani a sayo min, a lalace dai sai da aka kashe kusan dubu ashirin da biyar, ai kuwa ran shi ya b'aci domin baya kaunar abinda zai saka ya kashe kudin da ba zasu dawo mishi ba.
Hajiya ta kwana a dakin, amma itama barcinta tayi son ranta.