Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 6

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 6

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 6: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 6. Bayan sallah da sati uku. Weekend Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake…

4,591 words

Bayan sallah da sati uku. Weekend Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake ya jima da na sauke amma da yake yana da wuyar sha'anin, sai na ta saka idanun akanshi saboda Yaran nan da zarar na sauke tukunyar fresh milk sun ta kara kaina akai kenan, har sai na hada na basu. Hankalina yana kan zobo wanda nake ta saurin haɗawa. Sai naji an tab'a murfin tukunyar, da sauri na juya Yusrah ce rike da kofi ta bude tukunyar fresh milk din zata har ta saka kofin ta dibo da yake na juya mata baya, a matuƙar razane na kalle ta ina faɗin. "Gaskiya Yusrah bakya jin magana maza rufe min ki mai da kafin na zo wurin." "Ba zan mai da ba." Ta fada tana kallon cikin kwayar idanuna, abin da ya bani haushi da takaici yanzu ta kone Iyayenta su ce na konata. Mikewa da zan yi kuwa ta kwasa da gudu ai kuwa sai gashi ta taka ledar Bevimix ta zame bakiɗaya fresh milk din ya kware a gefen kirjinta, abinka da zafi sai kuwa ta fasa ihu wanda yayi daidai shigowar Mahaifinta da fitowar Uwarta a dakin, wani irin bugawa zuciyata tayi na tsaya cak kafin na karasa da sauri nace mata. "Kin ga abinda nake gaya miki ko?" Na yi maza na shiga daki na dauko kamun da aka niko min zan yi kunu na sha na watsa mata a kirjinta bayan na cire mata rigar, bakiɗaya iyayen babu wanda ya ce min ci kaina. Haka na zaunar da ita na cire mata rigar ba wani tashi wurin ba, amma yadda take kuka da ihu yasa Uban ya karaso ya bangaje ni sai da na fadi, sannan ya dauki yar ya fita da ita, wasa wasa basu dawo ba har dare habaici da cin mutumci babu wanda Karimah bata min ba, ni dai bance mata uffan ba, wajen karfe biyar Mama ta kira ni. "Kin kyauta Lubnah wacce irin kishi ne haka yake damunki?" Bata ba ni damar magana ba. "Saboda kishi zaki kyale yarinya kamar Yusra ta kona kanta?"

Ni dai ƙasa magana nayi har sai da Mama ta ce min. "Saboda mugun nufinki Allah ya hana ki haihuwa domin da ya baki da Yaranki zasu dauki mugun halinki!" Komawa daki nayi na zauna shiru. Haka Baban Bauchi ya kira ni ya ce sai ya ga wanda ya isa min, wasa wasa sai ga al'amarin ya girma yadda ban zata ba, yusrah kwantar da ita aka yi a gadon asibiti. Sannan wacce take gudun Mama ce. A wannan lokacin na ji duniyar ta min zafi, kaf duniya mutum daya ce ta fahimce ni Aunty Hindatu, dole na bawa Aunty Hindatu special respect a duniyata, ita kaɗai sai Ya Ado suka fahimci abin domin abin ya faru da kwana biyu Baban Bauchi ya zo har gida ya saka aka kwashe kayan sana'ar aka fita da su. A wannan lokacin Ya Hafiz ya zata ni yayiwa mugunta. Ya zata ni ya rusa tabbas ya Hafiz ya rusa ni, sai da na kusan zarewa domin babu wnada ya saurare ni, kowa ya juya min baya sai Aunty Hindatu da ita ɗaya ce take rarrashina, kwana Yusrah biyar a gadon asibiti Hajiya da Baban Jama'are suka iso a ranar Karimah ta dauki matakin da Baban Bauchi ya goya mata baya.

Ina zaune wurin karfe biyu na rana aka yi sallama a gidan, fitowa nayi ina amsa sallamar. Yan sanda ne mata biyu suka shigo. "Sannunku da zuwa!" Yadda nayi magana a matuƙar tsorace. "Kece Lubabatu Usman Umar Jama'are?" Jikina ne ya dauki rawa. "Eh nice!" "Ok ko zaki zo muje office din Yan sanda!" Ji nayi kamar ina yawo a saman iska. "Akan me zan bi ku Office dinku bayan ban yi kome ba?" "Eh tow idan muka je zaki ji abinda ya faru!" "Tow bari na kira mijina;" na shiga kiran Ya Hafiz amma bai dauka ba, haka nayi ta kiran Yan uwana har Baban Bauchi na kira Babu wanda ya dauka, sake magana suka yi na fito ko su shigo dakin. Haka na fito a sanyayye da hijab har kasa. Ina kara kiran Aunty Hindatu. Daidai na shiga bayan motar. Dauka tayi tana faɗin "Auta yi hakuri bana kusa ne!" "Aunty Yan sanda sun zo zasu tafi da ni!" "Akan me?" "Ban sani ba Aunty! Don Allah ki zo!" "Shi kenan gani nan zuwa!" Haka ya kashe wayar muka Office din Yan sanda da yake dutsen tanshi, anan na samu Karimah ashe shirinta kenan ita da Uwanta da iyayenta, muka shiga suka amshi wayata da kome suka tura ni cell suka ki min magana, ina zaune wata yar sanda ta shigo ta d'aga hannu tayi ta kifa min mari, yan uwan Karimah suna faɗin. " Saboda kishi ne ita Allah bai bata haihuwa, koda yake ta kashe mahaifarta da maganin hana daukar ciki shine bari ta kashe yar kishiyarta, Allah ya sa yarinyar ta auna arziki!" An tozarta ni, an ci mutuncina haka na kasa ko kuka sai sunkuyar da kai da nayi idanuna bana gani. Muryan Ya Hafiz da naji yana ta fada a waje. " Akan me zaki shigo da hukuma cikin maganar? Ko an gaya miki ban san yadda zan yi ba ne? Gaskiya kin bata min rai yanzu da wani idanun xan kalli iyayenmu?" Yadda Ya Hafiz yayi ruwa yayi makarbiya yasa ni shiga rud'ani amma ai ya ga kirana. Fada sosai yayiwa Karimah, Aunty Hindatu da Ya Umar da Ya Albashir suka karbi belina, haka na fito kamar wacce ruwa ya mata duka, fuskana ya dan kumbura saboda marin da yar sanda tayi min. A hankali nake takawa har wurin motar Ya Hafiz da ya nuna shi xan bi na je nayi wanka. Haka muka bar office din zuwa gida, a hanya yake cewa. " Kin san ina sonki, sannan abinda ya faru nasan bakida laifi Yusrah ta gaya min, amma kuma ita mahaifiyarta ba zata ji dadi ba idan na nuna baki da laifi don haka ki amshi laifinki ta haka ne kawai zaki wanke kanki kowa zai gane cewa bada wata manufa kika yi ba!" " Ya Hafiz me yasa?" Na tambaye shi, " Me yasa ka zabi kuntatta min? Me nayi maka da yake damunka har haka? A sanina ban maka wani abu ba? A sanina ban cutar da kai ba, ina saka ran wata rana zamu koma kamar baya kamar farko-farkon aurenmu, Ya Hafiz duk irin shirun da nayi na cancanci haka daga gare ka?" Shiru yayi da alamar maganar ya ratsa shi kenan. " Ka saka kowa ya tsane ni, ka saka kowa yana jin haushina, idan abu ya faru ba zaka gaya musu gaskiya ba sai ka bar maganar a daura min laifi me yasa sai ni? Ya Hafiz rabon da ka nemi ni a shimfidar aurenmu shekara kusan guda dawowarmu zango na gaji wallahi na gaji ka sawwake min nima na gaji!" Na fada ina kuka domin sai yanzu nake jin kamar bakina ya buɗe. " Ko na sake ki ai baki da wanda zai aure ki? Lubnah ki kalli kanki da kyau har abada babu namijin da zai tab'a jin sha'awarki, Lubnah na ajiye ki ne domin kowa yasan ina ƙoƙari da mugun halinki, ke har kina da bakin da zaki gaya min magana? Bayan na rufa miki asiri ne, jaka me kama da alade kalle babu abinda wani zai gani na burgewa a tare da ke kazama wawuya, kuma daga hau sai na hana ki farin ciki." Haka muka isa yana zagina da cin mutuncina har nayi wanka kai karewar masifa kofar ban dakin ya shigo yana cin zarafina. Haka na gama na shirya muka tafi cikin gidan inda Yusrah take da iyayenmu, anan ya min barazanar matukar nayi magana sai ya sake Baban Bauchi wato Babanmu ya tsine min shi kuma ya sake ni domin ba zai zauna da tsinanniya ba.

Lokacin da muka isa gidan Baban Jama'are yana nan haka Hajiya ma, sai Iyayena da yan uwana. Tunda na zauna aka bude taron da Addu'a. Aka rufe ni da fada babu wnada ya ji yadda kome ya faru haka na sunkuyar da kaina ina jin Baban Bauchi yana faɗin. " Munafuka ban da kishi da munafunci me kika ajiye ace har degree gare ki ya zama na banza. Sai bakar kishi tow da abinda kike takama da shi na kwashe dama yana gaya min tunda kika fara sana'a kika sauya bakya jin maganarshi, kin yi sabi iyaye masu daura miki mugun abu akanki wallahi kin ji kunya." " Amma Baba ya kamata a ji me ya faru? " Inji Aunty Hindatu, da take wani irin cirra, juyawa yayi a fusace ya zabga mata harara, ya rufe ta da fada da cewa ai ita take zuga ni, haushi ya sa ta bar parlourn ma don bakin ciki haka Baba Malam ya amshi fadar yayi ya ce min. "Yanzu kin kyauta abin da kika aikata? Da Asiya kike kishi ko da Uwar Asiyah? Yanzu ban da mun fi karfin yarinyar nan ina sai dai kotu ta shiga lamarin nan?" "Malam wallahi ban san cewa haka dai faru ba,.Malam na rantse da Allah ban yi haka domin kona yusrah ba yayi hakuri ba da gayya ba ne!" Zuba min idanu Malam yayi yana faɗin.."Allah ya kyauta amma ina amfanin kishi irin naki? Akan ki aka fara kishiya ne?" Cikin shashekar kuka na ce mishi. "Wallahi ban san zata shiga ban dakin ba, ka yarda da ni!" "Kai yanzu Hafiz me ka gani?" Juyawa yayi ya kalli Baban Bauchi wato mahaifina ya ce mishi. "Duk abinda Baban Bauchi ya ce ai shi kenan!" "A'a Hafizillah kada ka cutar da kanka, na ga ƙoƙarin zaman da ka yi da Lubnah idan ba zaka iya da mugun halinta ba sakota na gaji da kullum ana abu daya a cikin shekaru goma kullum Lubna tana saka ni magana." "A'a Usman, Lubna ko bata auri Hafiz ba, akwai alakar jini balle kuma alaka ce da ta haɗa da ta zuci, ai ta ce ba da gayya ta konata ba kuma yadda ake ta ririta al'amarin da na ga ciwon ai ba wani babban al'amari ba ne, lamarin mata ne kawai da ririta lamarin da bai kai ya kawo ba, yi shiru Y'ata share hawayenki. Kul na kara jin wani yayi magana da cewa za a kai batun nan ga hukuma kunar da bai wani tashi ba, ga yadda yayi baki kasan ai ba zai tashi ba, sannan kai Hafiz ka tuna akwai ranar da zamu tsaya a gaban Ubangiji, ka ji tsoron Allah kada son zuciya ya kai ka ya baro ka, kawai jikina yana bani haka kawai Lubna ba zata aikata kome ba." Kunya ce da bori tasa shi, kame-kame amma a cikin ranshi bai so haka ba yasan Baban Bauchi da za a bar shi sai ya mari Lubnah shi yanzu yadda zai bakanta mata rai yafi bukata akan wannan abin. Duk da an ce yau da gobe bai bar kome ba, Iyayena da dangi babu wanda ya hango mutuwar tsaye da nake yi saboda Ya Hafiz, Babu wanda ya yarda da cewa ina cutuwa, a'a kowa gani yake kamar ba cuta ba ce ni ce nake cutarsa saboda shi mutumin kirki ne, bayan shi ya shiga rigar mutanen kirki ne. Yayi ado da kwalliya a cikinsa, sannan babu wanda zai kalle shi ya ce mutumin banza ne. Amma bakin maciji ne sanye da tufafi yan adam, haka muka bar gidan, bayan an mana nasiha. Ni dai nasan cewa zuciyata ta gama mutuwa bani da wata amfani. A hankali gidan ya zame mini kamar hell fire, bani da kwanciyar hankali bani da sukuni, idan abin ya dame ni sai na rufe kaina a daki na ki fitowa, a hankali abubuwan suka ta tsanani domin kuwa na daina sayar da kome na daina yin kome, shi kanshi Ya Hafiz da ya fahimci bani da wani amfani sai ya cigaba da azabtar dani da abubuwan da zai saka na ji har na tsani zaman gidan, damuwa ya kara tsananta min domin ba wani abu ba ne su min gorin haihuwa.

Bayan wata biyu kusan watan Mauludi, Ya Ado ya dawo, ni ya fara kira a lokacin babbar wayar hannuna na sayar domin Ya Hafiz ya zo ya saka ni a gaba yana son kudi haka na hada da wayar da sarkata ta gwal na bashi, kunsan me a duk lokacin da zai same ni yana bukatar wani abu tow ba irin yaudarar da baya min, haka zai zo da soyayya ya cutar da zuciyata, har yau ina da yakinin zai shiryu ya daina abun da yake min don na fara tunanin kamar shiga tsakaninmu aka yi.

Cikin murmushi na ce mishi. "Barka da dawowa yasu Aunty Zakiya? Kun iso lafiya?" "Alhamdulillahi Auta nace ke zan fara kira ki san na dawo!" "Masha Allah sannu da hanya madalla!" Yadda muke wayar naki sake jiki da shi, ya sa shi kashe wayar da zai kira wani lokaci, tunda Ya Ado ya dawo Nigeria kullum zai kira ni, zamu gaisa daga nan zan yi shiru. Haka zai ta ja na da hira, har ya gaji ya kyale ni.

A hankali abin sai ya zame min jiki, sannan ban kara yarda mun yi tashin hankali da wani abu cikin gidan ba, wani abu daya da na fahimta idan na kashe auren ma bani da wani amfani, haka yasa babu amfanin na gayawa kowa halin da nake ciki, sannan kwasar bakin ciki a wurin Ya Hafiz da danginsa kamar shafa ce ta alola. Haka yan uwansa zasu zo musamman Aunty Nana, haka zata yi ta min kome da gadara da iko iko, idan nayi magana zata ce gidan dan uwanta ne.

Haka zan zuba musu idanu, kome zai wuce amma idan ban mutu ba zan sha kallo. Idan ka kalle ni bani da matsala sam, amma deep in side ina cikin wani irin mugun yanayi ne. Sai dai ba wanda ya san da haka sai wanda Allah ya jarabta da irin halin da nake ciki.

*

Yau Dan wake nayi shima dai nice nayi cefanen, musamman duk ranar da ya tashi rashin mutunci ni ce zan yi kome har na gidan, ya daina kawo abinci domin kuwa Karimah ta ce mishi ai idan aka kawo kayan abinci sayarwa nake sai dai idan ya tashi ya auno mudu idan ya gadama idan bai gadama ba zai ce na ranta mishi, yasan bani da kosisi. Haka zan ta kame kame har na hada abincin aci.

Har lokacin Maman Na'ilah bata bani fuskar da zan tambaye ta kudin ba, abu daya take gaya min. "Duk ranar da zaki yi aikin alkhairi wa rayuwarki in sha Allah zan baki kudinki amma idan har wa Mijinki ne wallahi kwandala ba zan baki ba, karshe ma zance sharri kika min!". Murmushi nayi da yake tasan ba zan yi magana ba, shi yasa nima na barta.

"Ke Yusrah kawo min kular Babanki na saka mishi abincinsa tun dazu sai magana nake kin ki kula ni!" Cikin rashin kunya ta ce min. " Eh din ba zan dauko ba ko dauko da kanki mana! Tunda bake kika haife ni ba. " Haushi yasa na zo na dauka na kuwa zungure kanta, ai kuwa ta fasa ihu. " Sai ki yi mara kunya kawai! " Na je na dauka ina mai komawa kitchen na zuba musu abincin. "Ina kika san zafin d'a ke kin san yadda wahalar daukar ciki da reno yake ne? Ina zaki sani bayan an lalata mahaifa da alluran family planner, kawai don ta ce ba zata ba sai ki saka min ita a gaba da fada idan fitsari banza ce kaza tayi mana!" Ka sake nayi ina kallon Karima tana gaya min magana akan nayiwa Yusrah fada taki dauko min kular da xan sakawa Ubanta abinci. Shigowa yayi yana faɗin. "Ya dai kaza uwa Yaya mai ya faru Agwagwata uwar albarka?" "Waye ban da juyar matarka da ita bata san haifa ba sai dai kashi a masai." Kumshe bakinsa yayi yana dariya mai sauti. "Yau kuma waye na samu da suna juya au lulu love ce!" Ya fada yana kallon yadda jikina yake rawa. "Ita mana ita dai da bata san ciwon kanta ba, wacce dad'i miji ya kaita aka ta zuba mata alluran hana ciki!" Cikin isgilanci ya ce mata. ."tow waye zai yarda ni ne bana son haihuwa da ita? Bayan nasan ba sonta nake ba kin san idan iyaye suka ga kana kula yarinya sai su dauka wani abu ne a tsakaninku, musamman idan Iyayen yarinyar suka gano cewa yarsu bata jin maganarsu sai naka!" "Ya Hafiz da bakinka kake fadar haka? Kada ka manta da mahaifina da naka Uwa daya Uba daya!" "And so what? Dube ki kitse ya taru a jikinki ke kanki ba zaki iya gudun minti goma ba, dube ki don Allah har kunya nake na ce ke matata ce, domin dariya zaa ayi min, balle kuma." Dariya yayi ta min yana fadar cewa.."wallahi matse matsinki wari suke balle kuma can kasar idan kika kwanta kamar an zuba kashi a bola!" Sai naji jikina yayi sanyi duk abinda zai gaya min naji ciwo ya san ni. "Ka sake ta mana Habibi wannan mai kama da dorinar ruwan tsoro take bani!" Dariya yayi sosai ya ce mata. "Karimcy ba zan iya sake ta ba, kai ko da na sake ta waye zai aure ta? Kada ki manta yadda take tafiya da kyar da kyar waye zai aure ta? Abin dariya nama na jan kare." A hankali na bar abin da nake na wuce daki, na zauna na fashe da wani irin kuka. Ina jin kamar zuciyata zata buga wallahi naji zafi amma ya zanyi, ina son ya Hafiz sosai ba wani abu bane fadar da yayi, shigowa dakin yayi ina zaune ya ce min. "Uban waye zai miki aikin da kika fara? Kin ga Lubnah bana son iskanci da renin wayo, wallahi zan tattaka ki, zaki fita ko sai na zane ki, ga ki katuwa amma kanki babu ƙwaƙwalwa!" Ba yau ya saba duka na ba, sannan ba yau ce zai daina ba. Tsoron dukan da yake fadar zai yi yasa na mike ina faɗin. "Kayi hakuri!" A duk lokacin da yazo ya fara wannan masifar ya tsani yayi magana nayi shiru, idan ban bashi hakuri ba marina zai ta yi. Har sai na bashi hakuri.... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*

Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu

TARA

Haka na fito na karasa aikin, ina kuka na gaji na gaji da abinda yake min, a hankali na gama na koma daki. Yanayin ba dad'i, ko nace ni ce bana jin dad'insa. Ana haka bikin yar gidan Aunty Hindatu da aka saka ana d'agawa ya taso saboda mijin ba a kasar yake ba, haka yasa aka saka bikin karshen wata June, tun daga kan kayan da zamu saka da kome Yayuna suka min, har lokacin Mama da Yadiko babu wanda yake shiga harkata tow ba ma damuwa suka yi da ni ba, idan bani na kira ba tow da babu wanda zai kira ni a cikinsu.

Bikin Maamah yar Aunty Hindatu da za ayi ya saka na dan samu yanci, domin Ya Ado ya kira Ya Hafiz ya gaya masa batun bikin da niman alfarman nazo ayi kome da ni, yadda yasan halin Ya Ado bai da sauki yasa bai yi musu ba, shima Ya Ado zai zo da Yaransa.

* Yau da wuri Umar ya bar muda lawan kasancewar mashin suke sayarwa shi a bangarenshi amma yana aiki da ma'aikatan shige da ficen jahar Bauchi. Yana kokarin hawa motar shi wani magidanci ya ce mishi. "Malam Umar ko?" "Eh nine lafiya?" "Hmm dama ina son na tambaye ka ne? Ya kuke da matar Alhaji Hafiz ne?" "Eh kanwata ce!" "Tow gaskiya ku sayi likkafanin da zaku lullubeta idan ta mutu, ni shawara da zan baka kenan idan kun so ku tsaya mata idan kun so ku barta ta cigaba da mutuwar tsaye!" Daga haka mutumin ya tsare abin hawa ya bar wurin.

Da wannan tunanin ya iso gida, ya sami Maman Aunty matarshi ya bata labari. "Ba tuntuni ake gaya muku ba, sau nawa ina baki a gidan nan bayan mun gaisa zasu ce don Allah idan ina da yadda zan yi na kaiwa Lubnah ɗauki." Haka suka ta tattaunawa da fadar ko da zasu wani abu su Mama ba zasu bari ba, shi yasa kowa yake shakkar shiga rigimar. Haka suka yi ta tattaunawa a tsakanin al'amarin. * Haka bikin ya karaso aka fara hidimar biki babu ji babu gani, kullum xan je kuma Ya Sani shi yake kawo ni har gida, domin Ya Hafiz ya hana ni kwana. Ranar daurin aure ina ta shirin fita da yake ita ranar ta gama wuninta, tunda asuba nake aikin gidana har na gama da wuri Ya Hafiz ya tambayi Karimah ta ce ba zata ba, haka yasa na gama shirina da wuri, wurin karfe tara na fito ba sai ga Karima ba. " Zan je bikin fa! " " Tow don Allah ki hanzarta! " Na fada ina kallon agogon hannuna. Tunda Karimah ta shiga daki ta manta da ni sai da na kara mata magana wasa wasa bamu bar gidan ba dai karfe biyu da wani abu. Kamar nayi kuka da gayya tayi haka sai dariyar mugunta take min, Ni dai ban kula ta ba. Har muka isa gidan da ya cika da mutane. Muna shiga cikin gidan Aunty Hindatu ta watsa min harara tana faɗin. "Wai ke me yasa baki kome da jikinki? Kullum zaki zo sai kin makara." Zan amsa caran Karima ta ce musu.."jiki duk tarin kitse taya zata yi sauri? Ai kun san Habibi yana kokari ko?" Wani hade rai Aunty Innah tayi tana kallonta cikin haɗe giran sama da kasa ta ce mata.."An kasa dake ne?" Da sauri na cewa Aunty Innah.."Inna uwa maba da mama bata yi karya ba, jikin nan damuna yake ni kaina da ina da hanyar rage shi da na rage, gaskiya ta fada!" Duk da na gama aikin gidan da wuri ita ta makarar da mu. A hankali na wuce bayan na fadi haka na barta nan kunya da yadda sauran yan uwana da yan uwan Ya Hafiz suka mata ca, Mama tana jin su bata amsa ba amma kuma zuwa yanzu ta fara jin kamar akwai abinda suke ƙoƙarin aikatawa. Dakin Aunty Hindatu nayi na zauna can kuryan gadonta. Shigowa Aunty Nana tayi ta ce min. "Ke kullum aka yi magana sai ki nuna babu kome, Alhamdulillahi tunda ba kome amma ki sani Ubangiji yana madakata!" Ta fada min tana wani dauke kai Aunty Nana Yayar Ya Hafiz ce, kuma na hannun damanta uwa uba Karima kanwar Mijinta ne, murmushi nayi na de mata. "Kiyi hakuri wallahi ni ce na makarar damu kamar yadda ta faɗa!" Na fada mata kamar xan yi kuka. Tsaki tayi ta bar dakin Yaya Asabe da take alolan a ban daki ta fito tana faɗin.." Lubabatu ba zaki daina cutar da kanki ba?" Washe mata hakori nayi ina faɗin " ba kome fa" "da kome mana, na akanki aka fara aure ne Lubabatu meke faruwa a gidanki" dariya na fara mata, dariya irin wanda kana gani kasan ba lafiya ba, na ce mata.."ba kome wallahi!" Shiru tayi tana kallon yadda na koma na yi shiru. Ina murmushi. Ina zaune Aunty Hindatu ta kawo min kayan anko dinmu da su, na saka na fito ɗas da ni. Kowacce ta saka sarkan gwal dinta ni dai bani da shi sai wata fashion da na saka Aunty Munah ta ce min. "Lulu ina gwal ɗinki?" Da yake iya mune a dakin. Zare idanun nayi ina kallonsu. "Ina gwal ɗinki?" Aunty Innah ta kara jefa min tambayar bakina yana rawa nace musu. "Na sayar da shi?!" Wani katon salati suka saka tare da zaro idanu. "Karya kike munafuka gaya min gaskiya ko naci ubanki ina kika kai sarkokin gwal ɗinki!" Shiru nayi naki magana, shigowar Yadiko dakin ta ji suna sake tambaya ta ina na kai sarkan gwala-gwalai na. "Na sayar nace!" "Me kika yi da shi Lubabatuna." "Inji Goggo alti Yayarsu Baba mace ce mai fahimta da sanin ya kamata, tana da zurfin ilimin addini sosai. Ta ce gaya min. "Gaya min ina kika kai sarkokin gwal ɗinki!" Jikina ne ya dauki rawa. Nace musu. "Goggo na sayar!" Wani irin mari Mama ta kifa min sai da na ga haske, na rintsa idanuna bakina yana rawa nace mata. "Na sayar da su!" Shiru dakin ya ɗauka haka aka bar zancen amma ran Mama ya b'aci. "Kome kin sayar gidanki, kin sayar kome kin sayar shi yasa kudin Umaranki na shekara biyu na ce kada a baki don baki da hankali!" Ni dai ban ce musu kome ba. Bayan mun gama muka fito waje, muka bar Goggo Alti da Goggo Uwani sai Yadiko da Mama.. "Salamatu ina jan hankalinki da ki tashi akan Yarki, wallahi yarinyar nan tana bukatar wani a tare da ita, ni dai bana zargi amma yarinyar ko baki kika mata iya ka kenan." Haka muka sha hidimar bikin sannan aka shiga hadadar kai Amarya dama ban saka kaina ba, haka na shirya muka tattaro muka dawo gida ashe akwai buhun bala'in da yake jirana. Tunda muka shiga gidan Ya Hafiz yake Bala'i da fada zagi da cin mutuncina har sai da nayi kuka. "Ke gaki mai yan uwa har zasu tsare ta da magana suna gaya mata abinda ransu yaso, don na rufa miki asiri na zauna dake haka na kuma zauna da wannan fuskar naki mai kama da ta giwar zasu zagar min Mata wallahi sai na sake ki,.na rantse da Allah idan na sake ki ba zaki tab'a samun wanda zai aure ki ba wallahi billahi azmin, wannan tarin jikin naki mugu da shi kamar kashi." "Kayi hakuri!" "Hakurin Uban me kike ba ni? Bayan kaf duniya babu mummuna irinki, ga baki ga muni ga munin hali da na halitta, ina kallonki gani nake kamar zan mutu don takaici!" Kaina a sunkuye ya gama zagina na ce kuma ce mishi. "Kayi hakuri na gode sosai, Allah ya baka hakuri." "Don na rufa miki asiri ina zauna dake zaki ci mutumcin matata!" "Kayi hakuri ba zan kara ba!" "Kina nan tibi-tibi sai kace aladiya!" "Na gode sosai!" "In ba don ina kunya Mama da Baban Bauchi ba wallahi da na sake ki, domin ya gaya min duk ranar da na sake ki sai dai ki nime wani uban ba dai shi ba.". "Kayi hakuri ba zan kara ba." Na fito ina murmushi, abubuwa dayawa sun boya a bayan murmushi na, kuka da ihu sun boya a bayan fuskana, amma haka na share na manta da kamar ba ayi ba. A tunani na zancen ya kare, sai dai a wurin Karamcy bai kare ba, domin kuwa bori ta saka mishi a kan sai ya min duka shine zata huce. Ya rasa yadda zai yi da ita kuma yasan matuƙar ta fara fushin nan zai zame mishi tashin hankali, don haka ya fito ya tsaya bakin kofar dakina yana faɗin. "Ke Jaka fito ki bata hakuri!" Wani hakuri kuma? Kawai daurewa nayi na fito waje ya ce min muje ki durkusa ki bata hakuri.. "Ni dai gaskiya ba zan durkusa ba domin hakuri kan xan mata amma ban da durkusawa." Dama kamar jira yake kawai ya rufe ni da duka. Duka sosai sai da makota Baban Na'ilah da Na'ima tare da basu Boy suka shigo gidan dakyar ai kwace ni a hannunsa. Tunda na shiga dakina na rufe na kwana ina kuka.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull