ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 7
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 7: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 7. Washi gari naki fitowa na daura abin karyawa haka ya gama barazanarshi ya fita, yana fita nima…
3,818 words
Washi gari naki fitowa na daura abin karyawa haka ya gama barazanarshi ya fita, yana fita nima na dauki hanya na nufi gidan. Ashe ina fita Karimah ta kira shi ta gaya masa gani nan na fita. Idan nace ban daku ba nayi karya, haka yasa na kwaso jiki na kawo ƙara, sai dai ban kai ga isa gidan ba Ya Hafiz ya kira Baba ya gaya mishi karya da gaskiya, ina isa gida Mama da Yadiko suka fatattake ni, akan na koma, don ba zan kashe musu aure ba, Baba yace musu duk wacce na zauna a wurinta a bakin aurenta, wannan ya bawa Ya Hafiz lasisin mai da ni jakarshi da zaran nayi laifi zai rufe ni da duka, wanda ya cusa min tsoro da tashin hankali, wannan dukar da zalinci yasa ni jin dole na rayu ko don na rabu da Ya Hafiz, na gaji.
Kaf yayuna aka rasa wanda zai tsaya min, Maman Na'ilah kaɗai ta bani shawarar na fara niman zabin Allah, idan da alkhairi a zamanmu Allah ya shiga lamarin idan babu shawara daya ne, na kai shi kotu a raba auren domin idan aka cigaba da irin wannan zaman karshe daya zai iya rasa rayuwarsa. Haka na dukufa da azumi da addu'a sallah dare da sadaka. Sai da na shafe wata hudu cib har zuwa lokacin ba wai ina da nutsuwa bane, sai dai na ji n koma baya na saurari karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i, duk da zuciyata bata yarda da abinda nake nufi ba, amma ni a kaina na gaji, ni a karan kaina ina son na rabu da shi, ina son na bashi iska ko zai gane yadda nake ji, duk wannan lokacin Ya Hafiz bai tab'a nuna yayi nadamar abinda yake aikatawa ba, kai hatta Yaransa suka yi kuka da ni zai min dukar da dai na tsani kaina. Duk wannan abin da yake faruwa kowa yana jin takaici amma ba yadda suka iya tunda ni ban ga hanyar fita ba, bani da wata madogara, sannan ba ni da wata makama, haka yasa na zubawa sarautar Allah idanu.
A cikin wannan ukubar na samu Maman Na'ilah da Na'ima na ce mata.. "Don Allah ina son kudin nan zan samu, idan ba xan samu ba ki barshi kawai!" "In sha Allah zaki samu yanzu ma kuwa!" Mikewa tayi ta shiga can cikin dakinta, ta janyo abu a kasan gadonta, ta ce min. "Lubnah shigo mana!" Mikawa nayi na shiga cikin dakin, ta ciro wata akwatin katako, ta fita tare da dauko wuka ta fasa kan akwatin katako, sai da ta fasa saman sannan ta saka hannu ta bude shi da kyau, kafin ta kalle ni tana faɗin. "Gashi nan ki zazzage shi!" Ƙasa kai hannuna nayi ita da kanta ta zazzage shi tas a gabana. Tow me zanyi da kudin nan?............... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu
GOMA
Wannan shine abinda na tambayi kaina me zanyi da kuɗin? A hankali na ji zuciyata bata amince min da abinda nake shirin ba nace mata. "Maman Na'ilah ki bar kudin tunda na ga yadda suke!" Na juya zan fita ta riko hannuna. "Me yasa kuma Lubnah?" Murmushi yake na mata. "Tow me zanyi da shi?" Yadda nayi maganar sai ita kanta abin ya dame ta, ta zata ko ina zarginta ne ta ce min. "Wallahi summa tallahi babu kwandala naki da na." "Har abada bana zarginki kuma ba zan tab'a zarginki ba, kawai bani da abinda zan yi da shi ne." Daga haka na bar gidan.
Na dawo na samu Karimah da Yaranta da wata kawarta suna ta hira, yadda nayi sallama basu amsa ba haka nima ban ce musu uffan ba na wuce dakina, tunda na shiga na zauna bakiɗaya naji duniyar tayi min kunci, ko na rabu da Ya Hafiz Iyayena ba zasu tab'a karbana ba. Sai naji bakiɗaya duniyar ta juya min baya, bakiɗaya duniyar kamar ni daya ce mata amfani a cikinsu, haka nayi ta jin kamar zan mutu. Ina zaune a dakin naji sallamarshi, ban d'aga kai ba ya shigo yana faɗin. "Wani wacce irin iskanci ne da ba zaki yi abinci a gidan ba?" A da ina ina ya Hafiz zai sauya amma by now sai nake ganin kamar har abada ba zai sauya ba. "Bakya ji ina miki magana ne?" "Me kace?" Na faɗa ina kallonshi. Fita yayi daga dakin ina jin shi yana ta b'ab'atu, kiran sallah azhar yasa na fita nayi alwala na dawo dakin nayi sallah, can sai gashi da kaya niki-niki a leda har da kayan abinci ya saka a kofar dakina ya fita yayi ya shigo da abincin tunda na ga haka na fahimci wata ya shirya min, don haka ina zaune ya kawo min takeaway, kamar ba zan amsa ba na amsa na ajiye na ce mishi. "Nagode" na cigaba da addu'ar da nake, can bayan ya fita na shafa,. Sannan na ja ledar abinci ne mai kyau, dauka nayi na fara ci a lokacin ya fara shigo da kayan abincin, yana zubawa a bayan kofana. Ni dai ban ce mishi cikanka ba balle har ya dauka ko na damu da shi ne, zama yayi yana min murmushin mugunta, ban bi ta kanshi ba ya mike ya fita, haka na gama na fita da ledar da robar na kai waje, sannan na dawo dakina bayan na wanke bakina. Tunda na shigo naji kamar jikina yana sakewa a daddafe nayi sallah Asr, a wurin dai na cigaba da zama ko kwanciya nayi Allah shine masanin.
Ashe kwanakina hudu me kyau a gadon asibiti, sai ranar na hudun na farka. Naga hannuna daure da abin karin ruwa, kamshin abin wanke asibiti ya tabbatar min da asibitin nake, a hankali na yi yunkurin mikewa zaune domin ina jin kamar maganar mutane sama sama, na ji kamar an mai da ni baya, bude idanu nayi a buge amma ban san waye a kaina ba can can naji ana cewa. "Koma ki kwanta!" Haka na kara komawa na kwanta tare da lumshe idanuna, ban kara budewa ba sai washi gari da misalin karfe biyu na rana naji Muryan Ya Ado, a hankali na kara mike jikina duk ciwo yake min. "Sannu Lubnah!" Inji Umma Kanwar Mama wacce take aure a azare, lumshe idanuna nayi na kara budewa akanta, ta mike da sauri ta shiga ƙoƙarin taimaka min na zauna ina sauke wani irin numfashi kamar mai cutar asthma. Kallona Ya Ado yayi a hankali ya ce min. "Ina ke miki ciwo?" Girgiza kai nayi alamar babu. "Sannu ko." Ya ce min haka ta rike hannuna muka tafi ban daki ta haɗa min ruwan wanka nayi da ruwa me zafi, sannan na hada da alwala na fito na zauna a bakin gadon fita Ya Ado yayi ya bamu damar sauya kayana. Bayan na sauya na gabatar da salolin da suke kaina, ina idarwa Umma ta zuba min tea me zafi a daidai shigowar Ya Ado da Ya Umar, sai Albashir da Ya Tahir, Ya Sani, ba Ya Ubaidullahi da Ya Mustapha, suna shigowa Aunty Hindatu da Aunty Innah suka shigo, zama suka yi akan kafet, ina cin abinci a hankali. Hiransu suke na abin da ya shafe su bayan na gama na shiga ban daki na wanke hannuna da bakina. "Barista ina ga mu bar maganar nan sai anyi la'asar ko kada mu fara mu katse saura minti goma a shiga sallah! " Inji Ya Tahir, "Ok Malam muje ko!" Kallonsu nayi suma kallona suke yi. " Kina son wani abu ne Auta? " Inji Ya Sani, " A'a bana son kome!" Nayi shiru suma basu fita ba Ya Umar ya ce min.." kina son tambayar wani abu ne?" Yadda yayi min maganar a tausashe yasa na ce mishi. " Me ya faru na ganni a nan?" " Baki da lafiya ne!" Kallonsu nayi kafin na ce musu. " Na fara hauka ko? " Idanuna ya cika da kwalla, fita suka yi na hango tausayi a idanunsu, a for the first time da na hango yarda da aminci a tattare da su, bayan fitarsu Aunty Hindatu ta mike tare da alwala tazo tayi sallah, Umma ma haka, nima a zaune nayi sallah saboda yadda nake jin jiri. Tunda na idar da sallah nayi shiru, maganar gaskiya ko addu'a a yanzu na rasa ta me zanyi, ta rokon Allah ya saka ya Hafiz ya sake ni ne ko ta nimawa kaina mafita ne, shigowar Yan mazan ne yasa ni kallonsu, tare da Yadiko wacce take tsakiyarsu, shigowa suka yi Umma ta ce mata. "Ina Yaya Salamatu? Yau kwanaki biyar yarinyar nan tana asibiti bata leko ba? Wallahi zan kira Inna na gaya mata tunda ita bata tsoron Allah a haka zata kashe Yarta." Sai a lokacin na kalle su naga yadda Yadiko take zabga min harara. "Yaushe kika fara shaye-shaye Lubnah meye amfanin wannan abin kunyar da kika aikata?" "Yadiko a dai bi kome a hankali kada azo ana danasani!" Inji Ya Tahir wanda ya kasance dan Yadikon ne na fari. Juyawa tayi a fusace ta fara faɗa. Wani irin kara kaina ya fara na dafe kan ina ƙoƙarin jin kamar ana buga min abu a cikin kwakwalwata. Rike ni Aunty Innah tayi tana faɗin. "Duba min alluran da yake cikin farin kwalba da sauri!" Ba musu Aunty Hindatu ta mika mata, ta ce mata.. "fasa min!" Haka ta bude bakin, sannan ta mika mata, ita kuma ta rike ni domin wani irin jijjiga na fara kamar ana fifigar jijiyar kaina, shiru Yadiko tayi ganin yadda nake jijjiga ga jinin da yake zuba ta hancina, abin ya razanata, dama haka lamarin ya ke. Alluran aka min sannan suka yi tare tare aka daura ni gadon tare da daure min hannuna, barci me nauyi ya dauke ni.
Hindatu. "Kai wallahi karya ne Lulu bata san amfanin kwayar da ta sha ba, da ta sani ba zata shiga wannan yanayin ba, imma an jima ana bata tana sha." Cikin fada Yadiko ta rufe Hindatu. Tahir ya ce mata." Yadiko lokaci yayi da ya dace ku san waye yake auren Lubnah kun ga haka muke yiwa Yaran wasu? Me yasa sai ita? Me yasa a duk lokacin da tazo da bukatar a saurare ta ba a bata damar ta fadi abinda yake ranta? Yadiko lokaci yayi da zaku cire kanku, ku kyale mu da Mijinku ya isa haka ya isa haka. Idan da Munah ko Raliya ne a cikin wannan yanayin hakan zaki hana mu magana? Duk lokacin da aka yi abu Lubnah ce mai laifi me yasa ko sau daya kun tab'a tambayarta meke faruwa? " " Amma ka ga yadda muka samu kayan maye da abin hana daukar ciki? " Murmushi yayi ya ce mata. " Waye bai san Hafiz ba? An gaya miki bakiɗayanmu basu san halinsa ba ne? A cikinmu ya tashi fa, a lokacin da Uwarsa ta watsar da shi Abba ya janyo shi jiki saboda nakasar Baban Jama'are, Yadiko ni nan Hafiz ban gaya miki ba ne, Hafiz shine yayi sanadin da na bar shagon Abba, shi yayi dalilin da kowa cikin mu ya bar shagon Abba muka dauki abinda ya mana. Yadiko lokaci ya kure da zamu kyale wannan lamarin." Yadda suka tsaya akan maganar yasa Yadiko tayi shiru ai al'amarin matukar ba kai ya fadawa ba, tow tabbas ba zaka fahimci yadda abin yake ba.
Sai da lokacin Sallah yayi suka tafi masallaci, su Aunty Hindatu suka yi sallah har da Yadikon bayan sun idar, suka ci abinci suka ajiyewa yan mazan, lokacin da suka iso an kawo na gidan Ya Umar da Ya Tahir haka suka hadu suka ci, sai karfe tara suka bar asibitin suka kai Yadiko gida.
Hafiz Bakiɗaya hankalinsa yayi azabar tashi, domin ya hango kwabarsa zata yi ruwa, yasan matuƙar ya rabu da Lulu tow ba makawa duk abinda yake zai fito fili haka yasa shi kiran Baba Malam suka gaisa ya ce mishi.. "Alhaji ka ga sun dauke min matata, bayan ina sonta don Allah ka saka baki su bani matata wallahi ina sonta zan turo maka da kuɗin mai a saka a mota a kawo ka kaji alhajina." "Shi kenan in sha Allah zan tawo gobe!" Godiya yayi ta mishi yana kara gode mishi. A hankali ya ajiye wayar yana kallon Karimah da take zaune a gabanshi ta hade rai. "Baby Karimcy kada ki damu ai!" "Ya isa haka!" Ta fada tana kokarin mikewa ya janyo ta suka fada wata duniya na daban.
*** Kiran sallah farko akan kunne na aka yi shi, na tashi nayi raka'atu fijir, ina cikin sallah Aunty Innah ta shigo, murmushi tayi ta shafa kaina ta wuce ban daki tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah nafila, a hankali ta ajiye min wata waya a gefena. "Ki duba akwai Alqur'ani a ciki zaki iya saurarenshi, ga airbon ki hada da shi kada maganar wani ya kara saka ki cikin tashin hankali har ki razana, domin condition dinki yana da matuƙar hatsari kin ji." Gyada mata kai nayi, har ta haɗa min abin karyawa da magani na sha sannan ta koma wurin aikinta. Sai karfe bakwai ta shigo lokacin ta gama zata koma gida. "Zan koma na huta an jima zan dawo bakiɗaya kin ji kina son wani abu ne?" "Duk abinda kika kawo min zanci " murmushi tayi ta shafa kaina tana me rungume ni a jikinta. Tana bubuga bayana. "Ki yi hakuri kin ji kome zai wuce wata rana zaki ga kamar mafarki ne kin ji ko?" Murmushi nayi mata nace mata.."Nagode!" Haka ta mana sallama ta tafi, wurin karfe takwas sai ga Mama da Abba, tsoron ganinsu yasa na rikice ina mai niman hanyar da zan gudu ban daki, amma ba hali shigowar Ya Ado da yaga yadda jikina yake kerma ya zo inda make ya zauna tare da kwantar da kaina a kafad'arshi. "Shiiiiii!" Yake furtawa a hankali, yana matse hannuna rintsa idanuna nayi hawaye na zuba min, a hankali a kafad'arshi. "Tow Yar gata, yar kwai ko nace yar gwal!" "Hajiya Shehu idan kana son tayi aman ƙwaƙwalwarta sai ka gyara wuri ka zauna domin ina ga haka ya dace da ku kai da Yaya Salamatu;" jin haka yasa shi kallon Umma ya ce mata. "Aminatu amma kin san abinda tayi bai dace ba?" "Ai rashin dacewar yasa zance maka kai ka tab'a tambayarta me yake faruwa a rayuwar aurenta? Yanzu yar gurin kishiyata da muka aurar bariya a lokacin ƙaƙa ina cewa saboda ita na fari ce uwar ta watsar da batunda mijin nan yayi ta cutarta ba a sani ba karshe sai da ya dauko mata lalura yarinyar nan ta rasu a wurin haihuwa bayan ciwo ya cinye ta ita da abin cikin ina lokacin da yar take kawo karar koranta muke? Sauyin Lubnah yayi yawa. Shirunta cuta ce ga rayuwarta ko ku shiga lamarin ko kuma muna nan daku zaayi kukan mutuwarta. Da yake Allah ya bata wani mugun jiki ne da baya bayyana tashin hankali da wata ce ta kare tas sai kashi da hakora rakwacan! " Kasancewar Umma Aminatu abokiyar wasarshi ce ita kanta Mama Abokiyar wasan Abba ne domin su Ya'yan mace, shi kuma ɗan namiji. Haka yasa ta hana shi magana kuma akwai mutuntawa a tsakaninsu domin Mijinta da ya rasu aminin Abba ne, cikin nuna damuwa ta ce mishi. "Nasan da Madaki yana raye da shi zai dauki lamarin Lubnah da muhimmanci, gaskiya abin ba dad'i duk da har yau bata ce mana uffan ba, shiru idan yayi shiru mace idan ta tashi mutuwa aman jini take yi saboda lokacin da ya dace tayi magana an rufe mata bakinta." Ambaton Madaki yasa Abba ya juya yana faɗin." Kai anan zaka lalace ba zaka koma aikinka ba!" "Zan koma ina son na ga yadda al'amarin zai kasance ne!" Juyawa Abba yayi ya zuba masa idanu kafin ya harare shi. "Kada ka sake ka lalata mata aure domin ba zan dauki haka a matsayin kuskure ba." Shi dai bai ce kome ba har ya janye ni a jikinsa ya rako Abba da yake Mama zata zauna da ni.
Har ya dawo ya samu ina karyawa, ban yi magana ba, amsar nashi abun karyawa yayi yana waya da Aunty Zakiya har da mika min na gaishe ta daga haka nayi shiru na cigaba da karyawa. Mama ta fara magana a hankali. "Shi rayuwar aure dan hakuri ne." "Ai kuwa idan irin na Lubnah ne kabari ne wurin zamanta kawai domin daga alamu kun fifita zumuncin uban yaron akan Yarku!" Jin haka Mama ta rufe Umma da Fada itama Umma ta hau sama suka rikito ashe itama yar bala'i ce, daukar airbon din nayi na saka a kunne na, na fara ƙoƙarin kunna karatun Alkur'ani, sannan ba kure karar, yadda ba zan tab'a jin muryansu ba. Haka ce ta faru kuwa, sai abin ya zo min da sauki har suka gama hayaniyarsu ban san me ya faru ba don Ya Ado yana gefena har barci ya dauke ni. Gyara min kwanciya yayi, bai kashe karatun ba ya cigaba da yi.
Karfe daya na rana na farko a lokacin wai Mama ta tafi da na tambayi Umma Aminatu sai tabe baki tayi wai tana faɗin.. "taga ni da lauya munki bin bayan shegen Yaron nan shine ta yi zuciya Allah yasa ta daka da kafa har Dutsen tanshi idan tana da zuciya." Wanka nayi nazo na gabatar da sallah, ina addu'a Ya Hafiz da Baba Malam suna shigowa, wani irin bugawa kirjina yayi wanda ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba. Gaishe Baba Malam Umma Aminatu tayi tana kallon Hafiz da yake kallona cikin jin dadi. "Kaso daga gidanka a wuce da ita dungulbi ko?" Take ya gyara fuskarshi yana kallon Baba Malam.. "yanzu ba wannan ba yaushe da a sallame ta ne ta koma dakinta. Na kashe wannan maganar domin na samu Usmanun na gaya mishi na kashe zancen nan har abada a bashi matarsa Allah ya taya shi riko! " Kaina a kasa har aka turo kofar yana kara jaddadawa an kashe maganar, Ya Umar ya ce mishi. " Magana dai bata mutu ba, sai yq gaya mana inda ya kai mata da duk abinda ta mallaka. " " Umaru ina magana kana magana da nuna min abinda na isa da shi!"
Gyara tsayuwa Ya Hafiz yayi yana kallona, kafin ya ce musu. " Gata nan ku tambaye ta yadda tayi da dukiyarta? Har shaidu ina da shi, yarinyar nan Alhaji nayi hakuri da ita yarinyar da ta bada jinginar gidanta kawai don a bata kwaya ta sha, meye ne ban mata ba? Kayan sawanta ta haɗa ta sayar kome nata ta sayar wallahi na rantse da wanda rayuwata take hannunsa yarinyar nan ba karamin bashi ta cillani ba, Alhaji kasan yadda nake kaunar Lubnah amma ni yanzu idan yan uwanta suka ce ba zata zauna da ni ba, zan iya hakura da ita ba gaji! " Yadda na kafe ya Hafiz da idanun yasa ji wani abu me daci ya cika min wuyana. Ban san yadda aka yi duk soyayyar da nake yiwa Ya Hazif ya dawo kiyayya ba, shin dama ba soyayya ba ce to idan ba soyayya ba ce mece ce nayi mishi? A sanina dai na kaunace shi, nayi mishi biyayya na wulakanta kaina na boye kaɗan daga cikin miyagun halayenshi, kura mishi idanu nayi ban iya magana ba, haka akayi ta rikici ni dai har lokacin ban ce kome ba, kuma bana son na ce kome, haka suka tafi ashe bayan barin asibitin babban rigima aka yi da Baba Malam wanda ya tilasta Abba cewa daga asibiti idan aka sallame ni a wuce da ni gidan Mijina. Ba zan mutu ba sai naga karshen Ya Hafiz haka yasa koda na warke aka sallame ni ban cewa kome daga abinda yake faruwa ba, haka suka yi ta bina akan na musamman abinda ya fada karya ne nace musu A'a ai gaskiya ya faɗa, wannan abin da nayi ya fusata yan uwana, haka suka mai da ni dakina, tunda na fahimci an gyara min dakin an saka min sabin kayan dakin, sai na tsaya a kaina da zuciyata dole na kwaci kaina a hannun Ya Hafiz, amma ta ya? Shine ta hanyar shigar da shi kotu amma kuma idan na kai zancen kotu ya familyna zasu dauki al'amarin, sai na kara jin na shiga wani irin damuwa mai danne zuciya. Hankalina yayi azabar tashi.
Bani da hanyar da zan iya yakince Ya Hafiz a rayuwata sai na ji bani da wani kwarin gwiwa, tunda na dawo kuwa iskanci da cin zarafi sai da yafi na baya, gori kuwa ina shan shi, tun ina dauke kai har ta kai da idan na rama sai ya dake ni, haka yasa na kara shiga wani irin kuncin rayuwa, domin kuwa Ya Hafiz ya saka Abba haramtawa kowa zuwa inda nake, haka yasa babu wnada ya san halin da nake ciki, sau biyu ina faduwa a ban daki. Haka zan farka na ganni dauke da karin ruwa. Faduwar da nayi na biyu ranar Maman Boy ta shigo ta ga na fadi suka kama ni suka kai ni daki, suka yi ta min fifita dama ya dake ni kenan ya fita shine na fadi, itama Karimah ta fita abinta. "Har ga Allah lokaci yayi da zaki samawa kanki Yanci idan kika kai shi kotu kudin wanke muni zaki biya!" Shiru nayi ina nazarin maganar, bayan fitarsu. Ina kwance na kira Ya Ado. "Ya Ado!" Amsa min yayi kafin ya ce min.. "na'am Auta!" "Ya Ado idan nace zan rabu da Ya Hafiz Abba zai hana ni wurin zama!" "Are You ready!"
*Wannan littafin na kudi ne* *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu
SHA ƊAYA.
Kamar yana gabana na gyad'a kai ina jan hancina. "Lubabatu kin shirya rabuwa da Hafiz ko baki shirya ba?" Sai na ji tambayar ya zo min a wani irin rude, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rasa meke min dad'i shin mai yayi zafi da zan kashe auren. " Abba zai kore ni!" Ina jin yadda ya sauke numfashi ya ce min. " You're not ready!" Ya kashe wayar. Haka na cigaba da kuka na rasa yadda zan saka kaina, haka na wuni suku-suku har dare yayi ban daura abinci ba, ko da Ya Hafiz ya dawo ganin babu alamar na daura aninci sai bai ce kome ba, ya fita ya sayo abinci ni kuma ko kallo bai ishe ni ba, ina da sauran kayan tea shi na sha na kwanta. Tun daga lokacin wani irin kunci da kasala ya shige ni, a daddafe nake ibada da alamarun gidan wanda ya dauki idanun ya zuba min, ina kiyaye lafiyata domin duk bayan sati biyu ina zuwa ganin likita wanda su Mama ba su sani ba, haka muka ci gaba da zama, ba ana haka Azizat matar Ya Tahir ta haihu, kiri kiri ya hana ni, zuwa.