Kenza eBookz

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 3

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 3

ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 3: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 3. Ranar Monday kamar ba zan fita ba, haka na shirya na nufi kamfanin don yanzu bana son ma Ya Ado…

4,090 words

Ranar Monday kamar ba zan fita ba, haka na shirya na nufi kamfanin don yanzu bana son ma Ya Ado ya kai ni da kaina nake tafiya, bayan na isa kamfanin na samu yana da baki da hannu Taj ya min alama na shiga na fito, ina fitowa na ga mutumin yana ta wani haɗe rai. Shi na lura duk lokacin da maza a wuri na zo yayi ta wani tsiro da mugun hali kenan. Haka na kai kaya na fito na same shi, da alamu basu gama abinda zasu yi ba ya sallame su. "Eh Taj har sun tafi?" Danne dariyar da take cinsa yayi yana kallon ogansa tare da nuna min shi da idanu, dauke kai nayi na ce mishi. "Har kun gama kenan?" Banza ya bawa ajiyata yayi tafiyarsa, ai kuwa don na kular da shi na biyewa Taj muka yi ta hira har muka isa sama, raka ni office dina Taj yayi muka shi ta hira. "Baka aikin yi ne?" Yadda yayi maganar yana bina da wani irin kallon, wanda matukar baka fahimci Yaren kallon ba zaka ga kamar wata yare ne amma tabbas kallo ce mai ratsa zuciya da hade da gangan jiki. Janye idanuna nayi saboda yadda zuciyata take wani irin pounder kamar zata fito waje, jikina har yana rawa, sake d'ago kai nayi muka yi ido huɗu, tabbas akwai Yaren da baki bata isa fitar da shi, haka zuciya bata iya fesar da shi, dole a barwa idanun aikinta domin kuwa yare ne da iya nan zaka iya fahimtar shi, janye idanuna nayi a karo na biyu, yana tsaye rike da mug, da alamar tea yake sha. Kasa aikin na tsaya nayi shiru ina wasa da yatsuna akan laptop. Sakon da ya shigo na duba shi ya turo sakon, yau kuma azumin magana yake min, ban ɗauki wayar ba na kalle shi, lumshe idanunshi yayi ya bude a karo na biyu, murmushi yayi sannan ya juya yana barin kofar na dauki wayar har hannuna yana rawa na duba me ya turo min. *Idan ba zaki iya aikin ba, zo na nuna miki wani abu* murmushi ne ya subuce min, nayi ta juya wayar. "Ina jiranki" haka ya kara turo min, mikewa nayi na fito. Na same shi a bakin elevator, yadda yake kallona sai na kasa takawa, domin kafafuna sai suka fara rawa kamar wacce ta dauko wani abu, murmushi yayi ya juya min baya a hankali na tawo har zuwa elevator, na shiga cikin na tsaya a can tare da sunkuyar da kai. Wayarshi ya dauko ya fara latse-latse har muka iso kasa kafin ya mika min wayar amsa nayi na ga Mamana, sakawa nayi a kunnena. "Mama" na gaishe ta, sannan muka fito ina wayar da ita, ina bin bayanshi har muka fito. Har muka isa wurin motarshi ashe bude motar yayi na shiga, ya rufe sannan ya koma ya bude bangarenshi muka bar kamfanin tare da barin yan gulma, suna ta leke. Sai hira nake da Mama ina bata labari, duk na shirme ne itama biye min tayi murmushi da yake dauke akan fuskarshi. Haka muka yi ta tafiya ni kaina bana ce ga inda muke ta yawo ba, mun fi awa daya da Mama a waya kafin muka yi sallama, na ajiye mishi wayar a hankali, ina mai cewa. "Kayi hakuri! Na cinye maka kati!" Bai ce min kome ba, sai ma juyowa da yayi zuwa kamfanin, amma sai da ya tsaya a wani eatry ya saya min abinci, sannan muka wuce kamfanin, lokacin da muka shiga kamfanin, Taj ne bude mishi kofar motar ya fito nima ya bude min tare da kwashe kayan abincin, muka shiga cikin kamfanin. "Ke!" D'ago kai nayi kawai matar nan ta watso min ruwa a kofi. Ji nayi ya fisgo ni, ruwan ya zuba a kasa. Kallonshi na tsaya yi baki sake. "Ki kula ba ko da yaushe ake tafiya zuciya sake ba, ki kasance kamar kunama me shiri a koda yaushe, gyada mishi nayi ina jin kamar na zura da gudu, a hankali ya sake hannuna sannan ya kalli Badr da take zare idanu, murmushi yayi ya cewa Taj. "Wuce da ita!" Muna barin wurin sai jin karar mari nayi tass. "Bana ce ba ruwanki da ita ba?" "Hamma ko kashe ni zaka yi wallahi ina sonka ba zan daina sonka ba, kuma idan baka daina fita da ita ba, gaba ruwan battery zan zuba mata." Murmushi yayi ya fisgo hannunta har waje ya ce mata."i don't like you." Fashewa da kuka tayi tana kallonshi. "Hamma don Allah ka rufa min asiri ina sonka!" Murmushi yayi ya cigaba da tafiyarshi yayi ya barta a wurin, yadda kowa yake kallona sai ta muzanta, abinka da wacce saba da kallon idan abu ya same ta ba, ta wuce bangaren office din Babanta da gudu, har tana faduwa, koda ta isa ta zube a kan gwiwarshi tana wani irin shashekar kuka da fitar da numfashi, dakyar da kyar. Haka yasa hankalinsa ya bala'in tashi, haka ya rungume ta, haka yayi ta kiran masinjarshi akan ya dauki mota su tafi asibiti da ita, shi kan gogan ko a cikinsa, haka kuwa ya shiga sabgar shi har zuwa lokacin da aka tashi amma bai san me yake faruwa ba.

Sai da aka tashi yayi juyin duniyar nan ya kawo ni gida, na ce a'a su je kawai, na shiga motar haya zuwa gida, ni bana son a takura min, sai dai wannan kin shiga motar yasa na fara ganin maganar Uncle Auta, domin kuwa yau da ace wani abu ne ya same ni ban san iya adadin abinda zai aikata ba, tunda na isa gida na ga Ya Tahir, cike da mamaki nake kallonshi, "Lafiya dai Ya T?" Murmushi yayi ya ce min. "Na zo na mai dake gidan Hafiz ne?" Murmushi nayi na wuce cikin gidan ina dariya. "Haba dai." Na fada ina nufar cikin gidan, da ya gama abinda yake ya shigo ya samu ina cire safana. "Abba na kawo yana ɓangaren baki!" Da sauri na wuce wurin na same shi yana cin abinci ga Yadiko a gefenshi, a shagwabe na je na zube a jikinta. "Yadiko shine baki gaya min zaki zo ba?" "Auta Abbanku ne ba lafiya amma tun dazun muka zo sai gobe zai ga likitan!" "Abba ya jikinka?" "Da sauki" ya fada yana kallon yadda nake ta narkewa a jikin Yadiko. "Da fatan mun barku lafiya?" "Alhamdulillahi!" Nan muka shiga dan hira sannan na fita sallah Magariba, da gaske akwai wani abu da yake faruwa, wanda ban san yadda aka yi ba, sai dai su biyu nan ina ganin suna kus-kus haka Aunty Zakiyah da Yadiko.

A hankali na fahimci akwai wani babban al'amari da yake faruwa a family amma kamar boye min ake, haka nayi ta zuwa aiki anan ma na ga kamar Mr Turaki yana gudun na ga wasu takardun, karshe cewa yayi. "Ki je na baki hutu!" " Akan me?" "Ki je kawai!" Ya fada da dan fada yadda zan ji ba tafi, haka na dawo gida na samu labarin su Aunty Hindatu zasu zo, hatta Mama zata zo itama za a kawo ta. Kwana biyu da nayi a ciwon Abba ya tashi aka mai da shi asibiti.

Akwai wani abinda idan zumunci ya shiga tsakani dole ayi hakuri. Dole ayi hakuri, zuwa dare Aunty Munah ta iso cike da tashin hankali tana kuka anan ja fahimci wani abu ya faru a Bauchi domin daga cikin kalamanta take cewa. "Duk wnada ya aikata haka Allah ya tarwatsa rayuwarsa." "Wai me ke faruwa ne?" "Ba kome damfarar Abba aka yi;" aunty Zakiyah ta fada min tana me jan hannuna zuwa cikin kitchen haka na cigaba da aikin, sannan na kasa nutsuwa.

A cikin kwanaki uku Yayuna duk sun taru a gidan Ya Ado, sakawa ake ana warwarewa kafin dai aka cimma matsaya dole za a nime yadda za'a yi yanzu haka ranar Laraba Ya Ado da sauran zasu zo Bauchi. Ni dai bana ce ga abinda ya faru ba. Haka na kwashe sati a gida ina son na koma aiki amma ba hali haka yasa na cigaba da kula da abinda yake gabana. Lokacin da Mama tazo itama bata gaya min me yake faruwa ba, nima ganin basu son na sani yasa na share su. Amma zan koma wurin aikina na gaji da zaman gidan nan haka. Ranar juma'a, na isa kamfanin na riga shi zuwa, kusan dai da ji alamar zuwansa. Buga min kofar aka yi na d'ago kai na zata shi ne ashe Khamis ne, gabana na ne ya fadi dama tun zuwana na lura da yadda ake kallona bai wani dame ni ba, indai gulma ce ai kamfanin nan shi za a bawa award na wannan shekarar. Murmushi yayi min nima na mai da shi. Ya ja kujera ya zauna yana murmushi. "Lubnah tambyarki zan yi ki bani amsa." Zuba mishi idanun nayi ina kallonshi. "Ina jinka!" "Yawwa ina son confidence dinki nan!" Ya fada yana dariya kafin ya kalle ni ya ce min. "Misali me wankar gawa ne wata rana aka kawo gawan Ubansa ya zai ji." Kura mishi idanun nayi kafin na ce mishi. " Ya zai ji kuwa kamr yadda kowa yake ji haka zai ji amma idan ya yi hakuri ba wani abu bane tunda wata rana shi zaa wanke. " Na fada murmushi yayi yana shafa kanshi ya ce min." Na ga kamar baki fahimci inda na dosa ba, kowa yayi dariyar motar gawa ubansa zai dauka. " A hankali na kalli takardun da suke gabana, ina jin kamar zuciyata zata buga. Ɗago kai nayi na kalli MD cikin wani irin tashin hankali, murmushi yayi irin wanda ya saba kullum ya ce min. "Na ga kamar family name dinki ko? Kotu tayi gwanjon kadarorrin shine na." Bai rufe baki ba aka turo kofar d'ago kai nayi ina kallonshi na kasa bude baki nayi magana shima ya kasa cewa kome kallona yake irin kallon ki yarda da ni nan. "Yawwa Turaki gaya mata abinda bata sani ba." "Khamis wannan ba lokacin wasa ba ne, kasan yadda lamarin yake a gare ta." A zafaffe ya juya yana kallonshi. " Kana nufin za a cigaba da boye mata kenan? Ok labarin da nake ji gaskiya kenan kuna soyayya a boye.!" A hankali na mike na ce mishi. "Me kake bukata?" "Yes haka nake so naga, yadda kike saka hannu a kan duk wani takardu sannan ki tura office dinsa, haka nake son ki tura mishi." Tass ya ɗauke shi da mari sai da nayi baya. "Ni ka mara akan wata karuwa? Ni ka..." Cin kwalar shi yayi ya janyo shi waje da shi kamar mahaukaci, yaya watsar da shi stair bai tsaya ba haka yayi ta janyo shi har zuwa wajen kamfanin ya ce mishi.." from to day na kore ka a kamfanin ka je ka yi duk abinda zaka yi?" Wani irin shiru nayi na ji kamar kaina zai fashe saboda ciwon da ya fara min, sai na rasa waye zan ji haushi a cikinsu, Iyayena da suka boye min ko shi Turaki da ya boye min, ruwa ya dauko ya ajiye min, a hankali na d'ago kai ina kallonshi. Kamar yadda nake kallonshi haka shima yake kallona, kallon nashi na yanzu kamar niman hanyar da zai bani hakuri yake ko nace yadda zai rarrashe ni, daurewa nake amma tabbas kuka nake son nayi. "Idan zaki yi kuka ki yi yana rage damuwa, ki yi kukanki." D'aga kaina nayi sama sannan na shiga hada kayana, juyawa yayi ya rufe kofar tare da jingina a jikin kofar. Koda na iso yana tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa. "Ki zauna zuwa an jima sai ki tafi gidan!" "Please ka bari na je gida? I don't want to lose my family! Duk saboda ni ne me yasa na zama kamar tsinuwa a gare su?" Na fada ina jin wani abu ya tsaya a kirjina, "zauna!" Ya nuna min kujerar office din kaina a sunkuye, na hada hannuna biyu na kifa kaina, shiru nayi ina jin kamar zuciyata zata fashe. "Please sir ka bar ni na tafi!" Na fada a hankali, "promise me ba zaki yi kuka ba idan muka je" gyada kai nayi, ina hadiye kukan da yake son zuwa min. Wani irin tsinkewa zuciyata tayi jikina ya kama rawa, na koma na zauna ina dafe kirjina. Wayarshi ce tayi ƙara. Ya fita can na gaji na fito wayata na kalla babu wanda ya kira ni. Kokarin kiransu nake amma ya kwace wayar naji ya fisge........... [12/9/2025, 11:35 AM] Maman Walid: 6 Kashewa yayi bakiɗaya yana mai kallon yadda na kura mishi idanu. Juyawa nayi na dauki jakata zan fita ya biyo ni har waje da sassarfa yana faɗin. "Ki nutsu kin ji!" Wani irin b'acin rai ne ya taso min nayi banza da shi, na cigaba da tafiyar har zuwa waje. "Ki shiga na kai ki!" Juyawa nayi na ga yadda ma'aikatan kamfanin suka zuba mana idanu abin kunya ce nayi mishi wani abu da zai zubar da mutuncinsa, sannan shi Babba ne bai cancanci kyautatawa daga gare ni ba, sai nayi kasa da kai na ce mishi. "Kasan halin da iyayena suke ciki?" Lumshe idanunshi yayi ya kuma bude akan lokaci yana mai gyada min kai. "Kasan yadda nake ji?" Gyada min kai yayi, "amma kasan an zalince mu?" Nan ma ya gyad'a min kai, hawaye ne ya zubo min na yi kasa da kaina. "Ko wani hali Abba yake ciki!" Bude min motar yayi sannan ya shiga gefen drive, muka bar kamfanin. A lokacin da muka isa asibitin, Mama da Yadiko sai fada suke tayiwa su Aunty Hindatu da Innah da Aunty Munah. Ji nayi na kasa d'aga kafaffuna na jingina da bango ina kallonsu. Tsayawa yayi a gefena, ganin yadda na zame a hankali ina mai fashewa da kuka mai mugun cin rai, durkusawa yayi shima yana me kallon yadda nake kuka, ya ma rasa me zai min saboda yadda nake kukan jikina har rawa yake. "Ke bana son sakarci, ya isa haka." D'ago kai nayi ina kallon Mama da ta juya gare shi tana mishi fada da fulatancin. "Ka zo ka durkusa a gabanta kana namiji shugaba kuma kana haka waye ya gaya maka cewa ita mace ana bata dukkan abinda take bukata ne? Ita mace bata bukatar a bata abinda ba zai zama nata bakiɗaya ba, ka zama namiji kada ka yarda ka yi rauni akan idanunka. " Mikewa yayi ya barta tayi ta fada kafin ta shiga rarrashina tana gaya min dalilin da yasa aka ki gaya min kenan, a hankali na mike tare da ciro takardun gwanjon gidajen Abba da duk wasu abubuwan da yake da shi, na cigaba da shashekar kuka. " Zan saka hannu na tura mishi office ɗinsa, ranar talata mai zuwa zai tafi Bauchi." Tunda na ciro takardan ya juya ya bar asibitin. Yan'uwana bakiɗaya suka taru. Sai kuma suka fara ganin laifina da shi Mr Turaki. "A'a kul na kara jin wani magana, taya Mahaifinku ya ci bashin banki haka shi zaku fara bincike, ba wai kawai ku ji haushin Yarinya da shi Bilal ba, shi ai kawo mishi banki tayi ya saya ita kuma matsayinta ba sakatariyar shi bata da abinda ya wuce ta saka hannu ai idan bata yi haka ba, taba cika adali ba sau nawa tana saka hannu a na wasu. Auta ki nutsu ki ga abinda ya dace ita Munah da take cewa ki bar aiki idan ya zo ta kanta itama haka zata yi kowa ya godewa Allah da Abban naku yake raye ba wai ku kara shigar da wani tashin hankali kan wanda take ciki ba. " Inji Yadiko, sai kuma jikin kowa yayi sanyi, amma kuma zuwa yanzu da muke zaune babu abinda Abba yake bukata kamar addu'a. Abba bashi da kome banki sun kwace kome matukar gida ya fito da sunansa sun amsa. Abin ya d'aga hankalin kowa. "Yadiko garin Yaya haka ya faru? Nasan Abba shi mutum ne da baya cin bashi kuma baya son bashi, me ya faru da ban sani ba?" Tab'e baki tayi tana me faɗin. "Hafiz!" Tana faɗin haka naji kome ya tsaya min cak. Na kura mata idanu ina jin wani irin kuka yana zuwa min. "Hafiz kuma?" Gyada kai tayi tana faɗin. "Shi kai shine mana waye yake juya kasuwancin Babanku? Duk Yaran nan sai da ya kore su ya ce basu da kwarewa basu iya sana'a ba, kai karewa babu wnada bai ce ya cuce shi ba, tunda Hafiz ya shigo rayuwarshi hatta Yaransa bai yarda da ku ba, ni nayi mamaki me yasa Hafiz yaƙi hakura da ke ashe wannan ta'asar yayi. Allah mun gode maka!" Daga haka tayi shiru sai kuma tayi kwafa. Ni kan tun da ta fadi haka na rasa nutsuwata. Haka nayi ta zama karshe zuwa yamma Ya Ado ya zo ya mai damu gida, a kofar gida na hango motarshi yana tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa. "Auta ga mutumin ki!" Lokacin da motar tayi tsaya na fito tare da fitowa daga cikin gidan na nufe shi, yana ganina ya tako har indA nake. "Ya mai jikin?" "Da sauki sosai!" Na fada mishi, "Na bawa SAN offer ko zai kawo shi Kumo clinic amma yaki." "Alhamdulillahi mun gode!" Na fada ina kallon kasa. "Ki taimaka min da takardun hannunki!" Ya fada kamar yana shakkar abinda zai fito bakina, murmushi nayi mishi tare da cewa.. "A'a adalci ne na tsaya a basu hakkinsu, idan na ce zan bi bayan ahalina ban yi adalci ba sannan suma bankin sun yi adalci da suka yi hakuri har zuwa wannan lokacin. " "Ni zan biya kuɗin ku bani takardun please!" Ya fada kallonshi nayi da kyau kafin na ce mishi." Mun gode! " Na juya zan tafi sai kuma na juyo na ce mishi. " Ina son na kasance a cikin masu tafiya Bauchi da Gombe, please saboda ina son ganin kome!" Na saka a raina matukar na dawo daga haka zan ajiye aikin na hakura ban tab'a fahimtar yadda mutane suke ji ba sai yau da ta fado kaina. Yau na ji yadda mutanen da banki take kwace kayansu, Abba ya rasa hatta gida daya da zai zauna, hadiye kukan nayi ina ji kamar zuciyata zata buga. "Am sorry!" Ya fada a hankali. Juyawa nayi na kalle shi, sannan na shiga cikin gidan.

----- Shiga motar yayi ya bar kofar gidan, burinsa ya hango Khamis, har ya isa KUMO FAMILY MANSION, a kofar gidan iyayenshi ya hango shi, cikin wani irin fushi ya nufe shi, cikin fushi bai gama tsayar da motar ba ya fita kamar wanda aka cilla shi, ya rufe Khamis da mugun duka, shi da ya san me ya aikata dariya yake mishi yana nuna shi da yatsa alamar yayi nasara abinda yake bukata. "Wallahi ko zaka kashe ni, sai na hana soyayyarku tasiri. Kai ba haka ba baka isa ka yi aure ba matuƙar ina raye!" Duka kamar ya samu jaki. Dakyar aka kwace shi ya ce mishi. "Yarinyar nan har abada ka rasata, ai duk abinda kake so matukar zan gani sai na haramta maka ita, ka saka idanun ka gani." Rike hannun Turaki Ubaid yayi yana jan shi har cikin mota bakin ciki ya hana shi magana. "Ka sani ko zaka mutu ita din ta haramta a gare ka" "Sake na kashe dan iskan Yaron nan! " Fisgar motar yayi da ƙarfi kofar gidan Alhaji ELYakub ya nufa, wani irin naushi ya kaiwa glass din motar sai da yayi tsawa, ya fita tare da nufar cikin gidan Alhaji ELYakub, ya zauna shiru sai a lokacin Alhaji Sameerah ya shigo tare da nufar Turaki kamar zata rufe shi da duka, wani irin d'ago kai yayi ya kalleta da jajjayen idanunsa. "Me ya faru?" Ubaid ya gaya mishi abinda ya faru wanda ya gani da idanunsa. A lokacin Khamis ya shigo ya danna fuskarshi da tsumar ƙanƙara. Kallonshi Alhaji ELYakub yayi ya ce mishi. "Khamis me ya faru?" "Kawai don na nunawa sakatariyarsa takardun da suka yi daidai da sunanta na banki sun yi gwanjon kayan Babanta shine ya rufe ni da duka ni me na mishi da zai dake ni?"

A fusace ya sake mikewa Ubaid ya mai da shi, "Please!" Ya fada, yana taping bayansa a hankali alamar yayi hakuri. Cikin fushi Hajiya Sameerah ta ce. "Baffa Marin Khamis yayi a gaban jama'a? Marinsa yayi a gaban kananun ma'aikata, marinsa yayi da akan mace? Baffa haka bai yi mishi ba sai da ya zo ya kara Dukanshi s gaban jama'a, ka yi wani abu domin wallahi abinda Bilal yake ya fara wuce makadi da rawa."

Kallon Bilal Alhaji ELYakub Kumo yayi rabon da ya ganshi haka tun rasuwar Iyayensa, yadda ya zauna ya sunkuyar da kai tare da dunkule hannunsa yayi murmushi ya ce mishi. "Lubnah ce ko?" Bai d'ago kai ba amma ya damke hannunsa sosai, alamar Eh. "Me yasa zaka je gaban Macen da yake so da irin wannan al'amarin?" Murmushi yayi mai sauti sannan ya cigaba da cewa. "Ita din Matar da yake so ce, ba yau nake jin labarin kana kazamin rayuwa da matan kamfanin ba, na tab'a maka magana? Sameerah da kike ihu na tab'a yiwa Khamis magana akan abinda yake aikatawa? Ita yarinyar rabin rayuwarsa ya b'ata yana jiranta, sai ya zuba idanu wani ya lalata mishi damar shi? A kodayaushe kuka tashi magana kuna mantawa cewa Uban Bilal shine ɗana na fari rabin da karin kamfanin dukiyarsa ce gadonsa ce, me ya dace yayi? Ya kare dukiyarsa da ta al'umma. Sai kai Khamis ka manta da cewa kana da aure ne? Kalli matarka da Yaranka biyu amma baka daina tsalle tsalle ba, na maka iyaka da Lubnah ba ruwanka da ita sannan ruwan Bilal ne ya mai da musu kadarorrinsu ruwansa ne ya cigaba da rikewa. Daga yau kada na ƙara ganin wani ya zo da maganar Bilal da Lubnah idan har ya faru dan barranta kaina da shi, idan ba zaku taya shi niman soyayyarta ba, ku kyale shi yayi yakinsa shi ɗaya. Ban haka kowa yayi yadda yake so ba amma shiga rayuwar Bilal kamar cewa ne za ayi yaƙi da ni. Bana son wani ya kara shiga rayuwarsa, Turaki kai kuma ka rage zafin rai ko fushi don Allah. Nasan ya maka ba daidai ba amma yana da kyau ka iya sarrafa fushinka kada ka zama abin dogara mutane suna amfani da fushinka wurin cutar da abinda kake so!" Haka suka yi shiru Hajiya Zeenatu ta ce mishi. " Amma idan da adalci ga mata a cikin gidan, har sai Bilal ya fita ya hango wata can kuma wacce suka fuskanci karayar arziki?" Ganin parlourn babu wanda ya amsa mata, ta cigaba da cewa. " Waye ya sani ko don abin duniyarsa take bi, tunda a wannan age na shi bai zama dole ya samu haihuwa ba, tunda an gama watsar da yaran a kwaroro da lungu da sako." "Amma baki da kunya, amma Sam baki da mutumci a kan idanuna kike fadar haka? Kin manta Uwar Turaki daga titi ta wanko ki, zuwa kamfaninta bayan ta mutu kika auri mijinta, wai matar da take da boyayyen manufa ita ce yau take fadar abinda bata da sani akai." Inji Uncle Auta da ya shigo yana kallon Hajiya Zeenatu, shiru tayi tana kallon shi, zama yayi yana fadar abinda Khamis yake sannan ya ajiye takardan koran da Turaki ya mishi. "Koranshi kuka yi kenan? Haba Mujitafa, amma dai daga Bilal har Khamis Yaranka ne me yasa kake nuna fifiko akan su, idan da Bilal ne yayi haka, shima haka zaka kyale shi ne haka? Ai nasan ba zaka tab'a kin goyan bayanshi ba, ka duba lamarin idan Khamis ya bar aikin a ina zai ci-gaba da aiki?" Shiru parlourn yayi Alhaji Abbas yana rokonsa amma bai ce kome mikewa Bilal yayi ya bar su a parlourn, idan aka ce bai ji zafin abinda aka yi ba, yayi karya kawai ya san idan ba sa'a ba ya rasata kenan. Bakiɗaya yaji tsoron Allah da tsoron rasata. Haka ya shiga motar ya wuce gida. Tare da kiran Taj ya gaya mishi ya saka idanun akan kamfanin zai dauki kwanaki bai zo ba.

Tunda ya shiga gidan ya kwanta bakiɗaya yaji kome ya tsaya mishi, sallah ya samu yayi ya sha tea kawai ya kwanta. Yana nazarin yadda zai da matsala, a yanzu duk yadda zai fito da bukatarsa na aurenta abu daya ne saboda case ɗin ne zai musu rufa-rufa, duk yadda zai yi bai san yadda zai shawo kan danginta ba........ [12/9/2025, 8:05 PM] Maman Walid: 7

Washi gari

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull