
Post
Kida a ruwa Book 3 page 50
..... and the bridge is giving Nimrah a hot look. To their astonishment, Nimrah instead of going to the house to greet them, she just took herself and slipped into her own bed after mixing with the luxury sheets and went to sleep, as if she didn't know about their existence and was even trying to call Feedo back. Nabeeha, who was hearing Nimrah's hatred, said loudly, "But this naughty girl, don't you have any shame and morals? Are you even looking at this nonsense?". To their astonishment, Nimrah burst out laughing and said, "Kawalli has a night call?". From there, Feedoh said, "Shegiya Ninah, until we were shown and entered from inside..." That Nimrah is giving a new laugh. Nabeeha grabbed her phone and threw it on the bed. Nimrah swallowed her laughter and looked at her, as if she was going to speak, but she just shook her head. Frustration gripped Nabeeha again. She just wants Nimrah to do what she wants her father to do right now. The First Lady herself was shocked by Nimrah's behavior. Then she picked up her phone again with a sly smile and her mind was relaxed. Hajja Mangu, a friend of the First Lady, said, "Nabeeha, you have a job ahead of you. This urinal is like this, daug
50
.........Shigowar saƙon Ruky wayar Nimrah ya sata sakin siririyar dariya tana miƙewa da wayar a hannu. Reply tai mata da (ALLAH yasa abin arziƙi ne? Jira ni). Tana gama turawa ta miƙe hankali kwance batare data ma tuna a ina take ba. Sai dai shigowar kira a wayar tata ya sakata tsayawa kuma. Feedo ce dan haka tai ƴar dariya tana ƙoƙarin ɗagawar da tai dai-dai da shigowar Nabeeha, First Lady da ƴar kazaginta biye da ita. Daga sashenta suke, dan tun magrib suna gidan wai sun zo yi mata nasiha, sai dai babu komai a nasihar sai zuga da ɗorata akan keken ɓera. Yanzu ma ta rako su ne zasu tafi First Lady ɗin tace ta rakasu sashen amarya. Sam Nabeeha bata so zuwan ba, amma sai bata musa ba ta nufi sashen Nimrah ɗin suka bi bayanta. Yanda suka shigo bedroom ɗin kai tsaye babu sallama ya saka Nimrah dakatawa daga ƙoƙarin ɗaga kiran Feedo. Kallonsu take kamar yanda suke kallon ta, sai dai tuni annurin fuskarta ya gushe, ta kuma ƙiyin magana. “K baki iya gaisuwa bane?”. First Lady ta faɗa cike da gadara tana watsama Nimrah kallo mai zafi. A mamakinsu yanzu ɗin ma Nimrah maimakon ta tanka kota gaishe sun sai ma ta ɗauke kanta kawai tare da zamewa a makeken gadon nata daya gama haɗuwa da shimfiɗu na alfarma ta kwanta, tamkar bata san da wanzuwar su ba tana ma ƙoƙarin kira Feedo back. Nabeeha dake jin wata irin tsanar Nimrah cikin tsawa ta ce, “Amma ƴar iskar yarinyar nan baki da kunya da tarbiyya? Mune kike ma kallon banzar nan?”. A mamakinsu baki Nimrah ta taɓe yanzu ma tana wani sakin dariyar da faɗin, “Ƙawalli ya da kiran dare?”. Daga can Feedoh ta ce, “Shegiya Ninah, har an fara nuna mana an shiga daga ciki...” “To ya ranki?”. Cewar Nimrah tana sake wata sabuwar dariyar. Wayar Nabeeha ta fisge tai jifa da ita saman gadon. Nimrah ta haɗiye dariyar fukarta tana kallonta, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta girgiza kai kawai. Takaici ya sake kama Nabeeha. Dan so take kawai Nimrah tayi abinda zata ci ubanta yanzun nan. Su kansu su First Lady iskancin Nimrah ɗin ya kaisu wuya. Dan kuwa ta sake ɗakko wayarta tana wani murmushin iskanci hankalinta kwance. Kasa haƙuri Hajja Mangu aminiyar First Lady tai, ta ce, “A lallai Nabeeha akwai aiki gabanki. Wannan fitsara haka yarinyar ƴar fitt amma ido kamar an soya gyaɗa marau-marau. Yo ALLAH na tuba banda namiji da jaraba ina abin yake nan balle romonsa”. Karo na farko Nimrah taji bazata iya haƙuri ba, ta ɗago ido ta kalla Hajja Mangu ɗin, cikin basarwar magana kamar ba ita ta faɗa ba ta furta, “Hajjaju baki san ko'a cikin nama jariran ƴan shila sunfi zaƙi ba?, ki tambaya kiji, duk mai cin ƴan shila har ƙashi baya iya bari”. Kallon juna First Lady da Hajja Mangu sukai, kallo irin na mamaki, yayi da Nabeeha ta zabura da shirin nufarta, sai dai a taku biyu ta tsaya cak sakamakon buɗe ƙofar bedroom ɗin da akayi. A tare ƙamshin turaren Dada ya daki hanci nan su, dai-dai kuma yana bayyana a cikin idanun su. Babu shiri Nabeeha ta koma ta tsaya idanunta na sauka a kansa. Jitai gaba ɗaya ta daburce, lips ɗinta suka kama rawa-rawar motsi alamar son yin magana. Dada dake kallon fuskar tata kansa tsaye zuwa lips ɗinta dake rawa ya kauda idanun nasa ya maida kan Nimrah data kwaɓe fuska zatai kuka tsabar sharri saboda ganinsa. A mamakin su First Lady sai gani sukai kawai Nimrah ta fara kukan kuwa. Sai kuma ta sakko a gadon ta nufo inda Dada yake. Koda tazo gabansa ƙarfin kukan nata ta ƙara har tana ɗan bubbuga ƙafafu a ƙasa. Idanunsa ya ɗan lumshe a slowly. Koda ya buɗe kuma sai ya wani sake zuba su a kanta cike da nuna gajiyar dake tare da shi a bayyane. Hannu ya miƙa mata, babu musu kuwa ta matsa kusa da shi tana ƙara jan shashshekar dake tada masa gashin jiki. Baiyi magana ba, amma ya zubama Nabeeha idanunsa cike da tuhumar da har su First Lady sai da suka daburce. Sai dai cikin dauriya First Lady ta furta, “Amma dai wannan yarinya anyi sheɗaniya. Mangu kina ganin ikon ALLAH?”. Kasa magana Hajja Mangu tayi dan mamaki. Yayinda Nimrah ta ƙara jan shashsheka da faɗin “Dadaaah!”. Yanzu ma baiyi magana ba, amma yanayinsa na nuni da ya bata dukan hankalinsa. Bata damu ba ta cigaba da faɗin, “Sai zaginka suke, wai kai mayen mata ne, mi zakayi dani abu ba abu ba. Ni kuma nace musu ai ko a cikin nama ƴan shila sunfi daɗi, shiyyasa ake cinyewa har ƙashin su ko?”. Ta ƙare maganar da wara masa idanunta. Ji Dadah yay tamkar ya kwashe da dariya, amma ya dake da ƙyar yana mai jinjina wautar yarinyar nan. Ji wasu manyan magana a bakinta fa. Anya kuwa tama san ma'anar abinda ta faɗa?. Shi gaba ɗaya ma ya rasa amsar da zai bata, tunda dai bai ɗanɗana wannan ƴar shilar ba balle ya yanke hukunci mizai ce. A zahiri kam sai wani kafeta da yay da idanunsa da suka shanye ciki sosai. Ƙasa Nimrah tayi da kanta dan bazata iya jurar sabon salon kallon nasa ba, sai dai ta tura baki gaba ta yanda har abin yaso bashi dariya yanzu ma, amma baiyi ba. Hannunta dake riƙe da nashin ya ɗan matsa, hakan ya sata ɗagowa ta sake kallonsa. Da ido yay mata alamar mi ye kuma?. A shagwaɓe ta ce, “Dada ka rama min ni dai”. Murmushi yayi a karo na farko. Hakan ya sakata jin wani kalar daɗi, harta juya taima su Nabeeha gwalo. Sai kuma ta juyo tana sake kallonsa. “Shike nan Dadah barsu ma na yafe ai na basu amsa. Dadah naje wajen Ruky?”. “A'a”. “Dada wajen Ruky fa. Abu zata nuna min ne”. Anan ma kansa kawai ya ɗan girgiza, a ransa yana faɗin (Kije dai bata labarin abinda akayi) a fili kam sai ya ƙara damƙe hannunta dake cikin nasan har yanzu ya fara tafiya inda gadon yake. Da sauri su First Lady da sukai sumar tsaye na mamakin rainin hankalin na wannan mutumin da yarinyar da suka nuna tamkar bama su san da su ba a ɗakin suka shiga matsawa gefe dan basu hanya. Dan yanda Dadan ya taho kai tsaye sai ka rantse zai bi takansu ne, irin baya ma ganin kowa a ɗakin sai Nimrah ɗin kamar yanda ya nuna tun farko. A nutsensa ya kai zaune bakin gadon ya jingina da fuskarsa, hakan yasa shi yin zaman ƙafa ɗaya a ƙasa ɗayar ya tanƙwasheta a kan gadon, sannan bayansa ya jingina da fuskar gadon. Itama Nimrah dake cika baki da iska ya zaunar da ita a kusa da shi. Yanda ta ɗan kauda kai gefe tana faman ƙwaɓe fuska na irin nayi fushi ɗin nan, ya sashi ɗora tattausan tafin hannun nasa a saman fuskarta, juyo da ita yay suna fuskantar juna, tare da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata. Idanun ta rufe ruff. Karo na biyu ya saki wani ƙayataccen murmushi tare da jan hancinta. Dai-dai yana furta, “Small Tiger! fushi baya mata ƙyau sam”. Kafaɗa Nimrah ta maƙe tana matso hawayen ƙarya. Sai kawai ya jawota gaba ɗayanta zuwa jikinsa ya sakata a ciki. Kallon juna First Lady da aminiyarta Hakka Mangu sukayi. Yayinda jikin Nabeeha ke rawa tana binsu da kallo. Da sauri First Lady ta riƙo hannunta, zatai magana ta shiga girgiza mata kai alamar kar tace komai. Sai kawai ta saki musu kuka dan zuciyarta tazo maƙoshi saboda kishi da zugar data sha wajen mutane daban-daban a yau ɗin. Hajja Mangu ta gyara tsayuwa zatai magana sai dai kafin tayin Nabeeha ta zabura jikinta har yana rawar ɓacin rai ta fice a ɗakin. Da sauri suma duk suka bita dan dama hanyar fitar suke nema kafin Dadan ya aikata abinda zasuyi nadama kamar yanda suke ganin take-taken sa.
Dada da Nimrah duk suna jinsu. Musamman Dada da daƙyar ya iya danne zuciyarsa daman. Dan kuwa saboda su ya shigo ɗakin. Bayan sallamar su Bilal ya fito daga sashen Mammah datai masa tata nasihar shima. Yana shigowa sashen su Nabeeha ke shigewa ɓangaren Nimrah. Har yayi kamar zai share yayi nashi sashen ya fasa. Dan yasan idan Nabeeha Nabeeha ce, itama fa Nimrah ɗin Nimrah ce. Baya kuma fatan wani abu saɓanin abinda yake shirya ma zuciyarsa a kansu tun a ranar farko, dan haka ya nufo sashen Nimrah ɗin kai tsaye, shine ya iske wannan cakwakiyar da aka gama zubawa aka kwashe yanzu..........✍️