
Post
Kida a ruwa Book 3 page 1
.....dy Imran moved the sign of incoming call. But he looked and saw that the caller didn't speak, he just went to the door, put in the password, and the device at the door finished listing their names and the door opened. Pharaoh appeared, followed by Yusuf and Dabo. At one glance, Imran's face understood what was going on, the doorman had just finished opening and turned his back. Tamar Dabo and Yusuf will let out a cry of joy to see Dada, but the situation is not the way they wanted it to be. However, they had to salute him three times with a style of respect for the soldier and the most beloved master in the heart, and then they began to line up their greetings. He smirked a little, opening his eyes as the madman turned to the horror. They did not even Imran and Faro until they heard the fall of the front. Because of this situation, it is a very difficult situation. Hanu extended his hand to Dabo as a sign to come to him, he still felt the love of the three children in his heart, including Ojo, he looked at them as younger brothers like Ja'afar. They also know this, that's why they love him so much, even in the blood of their bodies. Yusuf's hand started to be held, even though
*_BOOK 3_* _Chapter 1_
__________________
*_Assalamu alaikum._*
_Fatan alkairi a gareku baki ɗaya tare da Barka da salla. UBANGIJI ya karɓi ibadunmu. Ya Rabbi yasa muna cikin bayin da aka ƴanta a wannan wata mai alfarma da rahama. Ya Rabbi ka gafartama iyayenmu ka karɓi ibadunmu da addu'oin mu. UBANGIJI kai mana maganin abubuwan dake tunkaro mu. Alkairin ALLAH ya kai gareku baki ɗaya a duk inda kuke a faɗin duniya 😘😘😘❤️🙏_.
..........“Mtsoww!! Nifa gaba ɗaya nama rikice. A duk bayanan dana tattara babu wani suspect ɗaya daya ɗauki hankalina anan Haysam. Saboda Suspect ɗin mu basuyi dai-dai da maganar waccan jakin ba. Ɓangare na biyu kowa daya shigo gidan a yau zai iya zama suspect”. Daddy Imran ne mai wannan magana yana faman kaiwa da komowa akan ƙafafunsa. Dan gaba ɗaya ransa a matuƙar ɓace yake. Dada na zaune cikin kujera idanunsa a lumshe, dan tunda suka shigo UNIT ZERO ya zauna kawai ya lumshe idanun, zaka rantse barci yake, amma manya sun tafi dogon nazari ne. Dai-dai nan wayar Daddy Imran tai motsi alamar shigowar kira. Koda ya duba yaga mai kiran baiyi magana ba kawai ya nufi ƙofa, password ya saka, sai da na'urar jikin ƙofar ta gama jero sunayensu sannan ƙofar ta buɗe. Faro ya bayyana, sai Yusuf da Dabo. A kallo ɗaya da sukama fuskar Imran ɗin suka fahimci abin babbane, dan ƙofar na kammala buɗewa ya juya abinsa, koda suka gama shigowa sai ta maida kanta ta kulle. Tamar Dabo da Yusuf zasu saki kukan farin cikin ganin Dada, gashi yanayin yazo musu ba'a yanda suka so ba. Amma duk da haka sai da suka ƙame da salute ɗinsa har sau uku da wani kalar salo irin na girmamawar soja da ubangida mafi soyuwa a zuciya, sannan suka fara jera gaisuwa. Ya ɗan murmusa kaɗan, yana mai buɗe idanunsa da sukai mahaukacin juyewa abin tsoro. Ba su ba hatta Imran da Faro sai da suka ji faɗuwar gaba. Saboda irin wannan yanayin nashi yanayi ne mai tsauri matuƙa. Hannu ya miƙa ma su Dabo alamar suzo gareshi, dan har cikin ransa yake jin ƙaunar yaran su ukun nan, harda Ojo, yana musu kallon ƙanne kamar su Ja'afar. Suma sun san haka, shiyyasa suke matuƙar ƙaunarsa har cikin jinin jikinsu. Hannun Yusuf ya fara riƙewa, shi ko yana durƙurshe a yanayin kneeling yama kasa kallonsa. Dada daya ɗan murmusa yana kallon fuskar Yusuf ɗin ya ƙara matsa hannunsa, dole Yusuf ɗin ya ɗago. Sai kawai Dadan ya ɗage masa gira ɗaya tare da ɗan ɗaga masa kai. Yusuf yayi murmurshi, dan babu yaren da basa ganewa na Zak-Shadow. Ya musu wani kalar horo ne na musamman a gidan soja. “I really miss you Sir”. Yusuf ya faɗa hawaye na faɗo masa. Dada ya girgiza kai yana ɗan ƙara matsa hannun nasa sannan ya shafa kansa. Hannun Dabo ya kamo shima, shima dai yana a yanda Yusuf ɗin yake ne. Koda ya kalla Dadan shima sai ya fashe da kuka yana faɗin, “Sir kai na daban ne, ALLAH ya ƙara baka kariya. Munyi kewar ka, munyi kuka har muna tunanin hawayen zasu iya ƙarewa.” Sai kawai Dada dake murmurshi ya kalla Faro da Imran. “Kun ƙara koya musu shagwaɓa ko?”. Daga Faro har Imran murmushi sukayi na ƙarfin hali. Kafin Faro ya amsa da, “Ai rainon ka ne, abinda ka fara muka ƙarasa.” “Haka ne?”. Dada ya faɗa a taƙaice. Imran da Faro sukai ƙaramar dariya. Shima sai ya shafa kan Dabo kamar yanda yay ma Yusuf yana faɗin, “ALLAH ya cigaba sanya albarka a rayuwarku. Ku tashi ku zauna”. A tare suka amsa da amin har su Imran. Kafin subi umarninsa su tashi su zauna ɗin babu ko gardama. Daga haka falon yay shiru. Kusan na minti guda, kafin Faro ya katse shirun da tambaya. “Yanzu da wane mataki aka fara?”. Daddy Imran dake rubutu a laptop ya ɗago yana kallon sa. Sai kuma ya maida kansa ga laptop ɗin. “Muna da Suspect na zahiri guda uku. Sai dai basu da cikakken inganci, saboda kiran wayar da akayi”. “Okay wanne da wanne ne?”. Laptop ɗin ya miƙa masa. “Sun sami saɓani da yaron tsohon shugaban ƙasa a School satin daya wuce. Dan har hukumar ƴan sandan farin kaya mun je. Daga ƙarshe mukace akai maganar kotu. Na biyu akwai wani yaro wai Adeel a sanda ta fito sun haɗu da shi da abokinsa, sai dai ta wuce su kuma sukazo gaban gate suka tsaya wai suna neman Ammar. Sai dai basu jima ba suka bar wajen, barin nasu kuma babu jimawa abin ya faru. An duba gidan da suke kuma basa nan har muka baro anguwar yanzu. Yanzu haka muna kan bincike a kansa dan zuwa ƙasar yayi. Na uku....” sai yay shiru. Dan kuwa wannan kamar lamari ne na cikin gida. Dan kuwa Hajiya Hasiba ce da Nabeeha kasancewar Aunty Ummi ta musu bayanin komai daya faru. Sannan duk wannan abin da ake ashe Nabeeha bata gidan, bayan sun kammala gyara babu wanda yasan ita da ƙannenta sun tafi sai da Aunty Ummi tai musu ƙarin bayani Imran ya nufi sashen da kansa yaga basa nan. Da aka tambayi maigadi sai yace su tun bayan la'asar babu jimawa suka fita, kusan ma lokaci guda ne da fitar Nimrah a gidan. Wannan shine dalilin saka su a Suspect.. Faro da shima ya karanta a rubuce baice komai ba. Sai ya ƙarasa duba batun mai kira, kafin ya kalla Imran. “Anyi recording call ɗin ne?”.. Wayar kawai Imran ya miƙa masa. Ya kunna duk suka saurara. Kamar an tunatar da Dada wani abu, ya buɗe ido da sauri. Nuni yay ma Faro ya bashi wayar. Ya ko miƙa masa. Sau uku ya sake sauraren recording ɗin kafin ya saki wani murmushi yana jinjina kansa. Suko da duk suka zuba masa ido cikin kasa haƙuri Imran ya ce, “Yaya?”. Maimakon amsa masa sai ya ce, “Bani takarda da pen”. Da sauri Yusuf ya ɗauka ya miƙa masa. Ya fara rubutu zirrrr zirrrr. Dukansu ido kawai suka zuba masa, kusan mintina biyar kafin ya kammala.....
>>>>>>★<<<<<<
“Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.” Addu'ar data fara ambatawa kenan kafin ahankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi, sai dai dishi-dishi take gani da su. Yatsine black beauty face ɗinta mai cikar zati dake zane da kwalliya raɗam da bata goge ba har yanzu tayi, ta sake matse idannunta samnan ta buɗe a karo na biyu. Har yanzu jinsu take da nauyi sosai, sai dai sun washe tana iya gani komai yanzu. Ɗaki ne mai ƙyau kuma akan gado take. Sai da ta gama ƙare masa kallo kafin abinda ya faru da ita ya fara dawo mata dalla-dalla. Kai tsaye ta furta kalmar... “Kidnapping? Why?”. Sai kuma ta dafe kanta daya sara mata tana sake ambaton “Kadarullahi Wama Sha'a Fa'ala” ta sake ambaton “Allahummak finihim bima shi'ita”. Tafi mintina biyar tana ambaton addu'oi daban-daban kafin ta sake bin ɗakin da kallo. Ta tsaida idannunta akan agogon dake manne a bango. Ƙarfe biyu da wasu mintina na dare. Taja numfashi ta fesar, ba kanta take tausayi ba a yanzu, halin da su Mammah ke ciki musamman Ruky data san tafi kowa rashin ƙarfin zuciya. Wani gefe na zuciyarta kuwa jera mata tambayoyi yake akan su wanene da wannan aikin? Miyasa? Saboda mi?”. Maimakon cigaba da neman waɗan nan amsoshin batun salla ne ya faɗo mata a tsakiyar tunanin. Magrib da isha'i. Ai da sauri ta miƙe, dan duk rashin jinsu daga ita har Ruƙayya basu san wasa da salla ba. Wannan horo ne da Mammah ta musu, yabi jininsu kuma yabi numfashin su. Saboda nauyin da jikinta yayi sai da ta koma ta sake zama, dan jiri take ji, bayan minti guda ta sake miƙewa tana addu'a a ranta ALLAH yasa bayi ne ƙofar da hankalinta ke kai... Nimrah wata irin yarinya ce da kai tsaye da wuya kaga abu ya ruɗata koya rikitata irin a zahirin nan kaga mutum ya birkice. Duk yanda abu yakai da girma ALLAH ya azurtata da ƙarfin zuciyar sakama kanta ƙarfin gwiwar ƙarfafa kai. Takan ce ba haukana zai sa nasan kaza kona ma kaina maganin kaza ba, wanda ya halicceni yafi kowa gani na da sanin halin da nake ciki. Jarabawa ƙawa ce ta numfashi. Duk tsananin da rayuwa zata shiga abu biyu ne zai tabbata. Kodai a rasa NUMFASHIN ko kuma a fuskanci RAƊAƊIN JARABAWAR numfashin na cikin gangar jikin... Da lalube ta isa ƙofar, dan jiri ke ɗibarta sosai, ta sauke numfashi mai ƙarfi ganin toilet ne kuwa. A ciki ma da bin bangon tayi komai sannan ta fito, sai dai ba hijjab babu abin salla. Ta ƙara bin ɗakin da kallo, akwai wadrobe, dan haka ita ta nufa ta hau buɗewa. Babu komai a ciki sai bargo. Itafa yin sallar nan ne kwanciyar hankalinta, in ba haka ba bazata cigaba da iya gane komai ba, dan haka ta finciki bargon kawai, yana runjayarta saboda nauyi da rashin ƙarfin nata jikin a hakan ta rufa shi ta tayar da salla akan carpet ɗin gaban gadon. Ta fara gabatar da magriba, sannan isha'i. Da ƙyar tai shafa'i, tana cikin yin wutri a sujida ta sake ɓingirewa barci. Dan abinda suka fesa mata mai ƙarfi ne sosai......
%%%%%%%%
“Tab ɗi, amma yarinyar nan bala'i ce Jagwa. Wai kasan tun ɗazun ina nan na lalace ina kallonta ta tv.” Wanda ke shigowa falon da ledoji a hannu ya ajiye yana ƙarasowa inda mai maganar yake. Shima dai idanunsa a television ɗin falo dake aiki da cctv camaras da aka zagaye ko ina na gidan. Ɓangaren ɗakin da Nimrah take da wancan ya ƙara zooming shima yake kallo. “Bara na dawo maka da shi baya ka gani”. Na ɗazun dai ya sake magana yana ɗaukar remote. Shima kansa wata ashariya ya ɗuro yana kaiwa zaune. Ya cigaba da faɗin, “Bala'i, wannan spry ɗin dake ɗaukar 2days mutum bai san inda yake ba ita ta farka a awanni goma! Har tai salla?”. “Wlhy, nima abun ya bugani”. “Kai Lio sai na kira oga na faɗa mas kuwa. Dan na rantse wannan abar ƴar baiwa ce ko Aljana ma zance”. “A ina bayanka wlhy, rattaɓa mas kira. Nima shaida ne tana da almatsotsai” Da alama ogan nasu ma ya shiga mamaki, dan sai maimaita abin yake, daga ƙarshe yace su tura masa footage ɗin tashin nata. “An gama oga”. Cewar Jagwa yana wani kaɗa kai da jiki. Kai daka gansa kaga cikakken ɗan hau. Gashi wani garƙeƙen ƙato. Suna gama tura masa suka baje abincin da yaje ya sayo musu suka hau ci. Dan yunwa suke ji bata wasa ba..........✍️