Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 2

Post

Kida a ruwa Book 3 page 2

..... outside, he started drinking the coffee while focusing his attention on the place with one hand in his pocket. "The line on the phone was completely taken down. Then all information on it was deleted, preventing it from working forever." All of their faces changed from listening to Dabo speak. But to their surprise, Dada is also recovering. The son slowly walked back to where they were, and sat where he left, placing one foot on the other. As if he didn't say anything for a minute, he was drinking his coffee. Seeing the way they are staring at him now, he smiled again, and he said, "This is not the work of the ignorant. If my calculations are correct, they have taken her to divert our attention to her so that they can do what they want. Imran, Pharaoh, withdraw your soldiers from the gate that they told to give me my wife." Imran rolled his eyes because of the word (My wife) and laughed, and so did Faro. Dabo seems to be shocked only in terms of work, even though they know Nimrah since she was in her prime, but they don't know about marriage, and they don't understand their boss's statement now. Imran impatiently said, "Your calculation is correct. But making this decision is

Standalone post1,663 words

2

........Yanda duk suka zuba masa idanu zai tabbatar maka da ƙagararsu na son jin yace wani abu. Shima ya fahimci zalamar tasu, dan haka kai tsaye ya furta, “Imran bama Dabo yay tracking number ɗin nan?”. Cikin bin umarni ya amsa da. “Okay”. Babu ɓata lokaci Dabo ya fidda laptop ɗinsa a jakarta, dan da abinsa yazo. Faro ya miƙa masa wayar. Karo na farko Dada ya miƙe yana kai-kawo a falon hannayensa duk goye a bayansa. Jikin window ya ƙarasa ya tsaya. Yanda ya zubama compound ɗin gidan idanu ya saka Yusuf miƙewa shima ya nufi inda yake hango coffee maker. Sai da ya duba duk coffee powder ɗin dake wajen sannan ya haɗa wanda yasan boss na sha a da, duk da bai sani ba ko ya canja a yanzu. Amma dai ya haɗa ya jira har coffee maker ɗin ta gama matso masa shi sannan ya ɗauka. Koda ya miƙa masa cike da girmamawa sai Dada ya murmusa. A hankali ya furta, “You’re the best”. Yusuf yay murmushi shima har haƙoransa na bayyana. Cikin ƙara sirinar da kai ya ce, “Yace thanks you Boss”. Daga haka yabar wajen, shi kuma ya fara shan coffee ɗin yana maida hankalinsa ga wajen dai hannunsa ɗaya a aljihu.

“An sauke layin akan waya gaba ɗaya fa. Sannan an goge duk wani information a kansa, tare da hanashi aiki na har abada.” Gaba ɗaya fuskokinsu ya canja daga sauraren Dabo mai maganar. Amma shi Dada a mamakinsu murmurshi ma yake yi. Dan a hankali ya tako ya dawo inda suke, ya zauna a inda ya tashi yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Kamar bazai ce komai ba tsahon minti guda yana ta shan coffee ɗinsa. Ganin yanda a yanzu ma suka zuba masa idanun ya sashi sake murmusawa, sannan ya furta, “Wannan ba aikin jahilai bane. Idan lissafi na yayi dai-dai sun ɗauke ta ne dan karkata hankalinmu a kanta kawai su sami yin abinda suke so, Imran, Faro ku janye sojojin ku na ƙofar da sukace su sakar min matata”. Imran ya zaro idanu saboda kalmar (Matata) ɗin yana gimtse dariya, hakama Faro. Su Dabo kam sun girgiza ne kawai ta ɓangaren aiki duk da sun san Nimrah tun tana ficiciyarta, sai dai batun aure basu san da shi ba, ba kuma su fahimci furucin boss ɗin nasu ba a yanzu. Cikin kasa haƙuri Imran ya ce, “Lissafin ka dai-dai ne. Amma yanke wannan hukuncin duka akwai ruɗani.” Caraf Faro ya karɓe da, “Tabbas akwai ruɗani Imran, dan kuwa hakan na nufin zasu aikata abinda suka shirya a wannan yankin, sannan ba lallai idan sun sami biyan buƙata su saketa ba, ko kuma su cutar da ita kafin su saketa. Mutanen nan fa sun wuce duk yanda muke zato da tsammani Boss, ni nafi gane kawai mu farmake su, mu amso ta wlhy”. Dada da kamar baima jin abinda suke faɗa ya wani lumshe idanunsa ya sake buɗewa. Sai kuma ya taɓe baki kaɗan. Hankalinsa kwance ya furta, “Daga lokacin da lissafi ya zama RUƊANI ko mabiyan addini kan kasance a rikice ne. Dan zasu gagara gane waya kamata su bautamawa? Sai dai abu ɗaya tak da zasu nutsu da shi, mafitar mai sauƙi ce. Bayan ANNABIN ƙarshe UBANGIJI bai sake turo wani MANZO ba, kenan duk wanda zai faɗa maka wanene UBANGIJINKA zai koyar dakai bin ALLAH ne da koyarwar MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMAD (S.A.W). UBANGIJI ya halicci abubuwa guda biyu dake bama duniya hasken da har idanun mu ke banbance wanne muke ciki. Hasken RANA, dA hasken FARIN WATA. RANA duhun hadari, ko shigowar dare, ko shigowar hazo na sanyi ne kawai ke iya risinar da ita a garemu, amma hakan baya hana muga hasken DUNIYA. FARIN WATA, canjawar farkon wata zuwa tsakiya da ƙarshe ke canja mana ganin cikakken kaifin haskensa, sai kaga a ƴan awannin nan daya rissina dole muke amfani da fitilu. Shin hakan na nufin mun makanta ne? ko wannan hasken shine dama sandar jagorar idanun mu bisa hukuncin mai hukuntawa?”. Imran ya ɗan furzar da iska yana mai sakin murmushi. Dan shi ya fahimci komai, saboda yasan Zak-Shadow sanin da ko alfahari yayi da duk duniya babu wanda yay masa irin wannan sanin dole a yarda. Faro dai ba komai ya samu warwara a kansa ba. Amma da yake shima ALLAH ya bashi kaifin basira na tunani, sannan ya yarda da Dada yarda ta haƙiƙa sai ya jinjina kai kawai. Dabo, Yusuf dama masu koyi ne daga ƙyawawan hali irin na boss ɗin su. Sannan masu biyayya ne akan ayyukansa musu ƙyau dan sunyi imanin in sha ALLAHU bazai taɓa karkatar da su zuwa mummunar hanyar bijirema UBANGIJI ba. Shima dai gogan bai sake cewa komai ba. Dan daga haka ma ya miƙe abinsa ya nufi ɗakin nan na sirri ya barsu a falon suna cigaba da tattaunawa. Saboda yanzu dai aiki ya rage garesu.....

<••••><•••><•••><••••>

A gidan Mammah cikin tashin hankalin Ruƙayya suke bayan wanda suke ciki. Dan ta rikice musu ga jikinta ya ɗauki mugun zazzaɓi sai amai take. An kira doctor ya dubata ya tabbatar musu damuwa ce sannan gudun zuciyarta ya canja sosai. Dole ya buƙaci su wuce da ita asibiti. Hakan dole akayi, Ammar ya ɗauketa gaba ɗaya zuwa mota. Yaya Bilal yaja. Ma'aruff da Ja'afar da Mammah suna wata motar. Dan tace bazata iya zama a gidan ba. Suna isa aka fara bata taimakon gaggawa.. Abinda ya sake tada hankalinsu har bayan awanni biyu allurar da sukai mata ta barci taƙi ɗaukar jikinta. Kuma babu abinda sukafi buƙata tayi irin barcin a yanzu. Sunan Ninah kawai take kira. Da ƙyar, da addu'oin da Mammah keta faman tofa mata aka samu nasarar barcin ya ɗauketa. A lokacin kusan 2:30 na dare. Su Ja'afar sun gagara barin asibitin. Dan cikin ikon ALLAH ma a kusan lokacin sai ga kiran Dada ya shigo wayar Bilal. Ya kira ne dan son jin yaya Mammah ta kwanta dai ko? Sai kuma ya ji akasin lissafi. Yay ɗan jimm na sakanni, kafin ya furta. “Wane asibiti ne?”. Sunan asibitin Bilal ya sanar masa. Dada bai ce komai ba ya yanke wayar. Fitowa yay daga ɗakin sirrin daya shiga. Su Imran dake ta faman aiki duk suka ɗago suna kallonsa. “Faro cikin jami'an daka haɗa ɓangaren masu farin kaya mutum goma suje kk hospital ka tura musu number ɗin su Ma'aruff”. “Wani abu ne ya faru?”. Cewar Imran yana tsaresa da idanu. A taƙaice ya ce, “Ruƙayya ce ba lafiya”. Daga haka ya sake juyawa ya koma. Imran ma aikinsa ya cigaba da yi, sai Faro ne daya ɗauka waya ya fara ƙoƙarin neman ɗaya daga cikin jam'an sirri daya haɗa batare da kowa yasan ɗan uwansa ba.....

★)))((((★))))(((★

“What!”. Ya faɗa cikin ƙaraji da mamaki yana miƙewa tsaye kamar wanda kunama ta halba a uwawu. Suma sauran duk kallonsa sukayi a razane, kowa na neman ƙarin bayani. Mr Specter ya kalla Oga Jush lips na rawa ya furta, “Wai kasan sun saki hanyar kuwa Oga!”. Gaba ɗaya meeting room ɗin babu wanda bai nuna razana ba maimakon murna da farin ciki. Black Spider ya ce, “Kai ina akwai matsala. Zak-Shadow ba mahaukaci bane ba fa?.” “Tabbas ba mahaukaci bane, dan gadararsa ma bazata bari yayi abinda muke so ba cikin awannin goma kacal.” Viper ya faɗa shima cikin tabbatarwa. Scythe ya ce, “To mi hakan ke nufi?”. Babu mai wannan amsar, dan haka duk suka zubama Oga Jush da baice komai ba idanu. Sai dai bashi da alamar zai ce ɗin tsahon mintuna uku. Sai da ya gama zuƙe sigarinsa tas kafin. “Ba mahaukaci bane, sannan ba TSORO yaji ba. Amma dole yay hakan bisa dalilai biyu. Na farko Imran, shine zai tirsasashi dan yarinyar ta dawo, sannan zartarwa da gidan soja a hannun Imran kawai take yanzu tunda shi bai koma aiki ba. Na biyu yana SONTA. Hakan ya nuna a randa ya je station kan case ɗinsu na makaranta...” yaja iska yana ƙoƙarin kunna sabuwar sigari. Dan gaka Iron Fang ya samu damar faɗin, “Amma Oga baka ganin zai yi hakan da wani abu a ƙasa?”. Baki Oga Jush ya taɓe. “Wannan tunanin naka nakan hanya, dan yana aiki da WAYO fiye da Ƙwaƙwalwa. Amma kar wannan ya dame ka. Ayi mata allurar da zata karya halin da take ciki. A daren nan a kaita inda next plan ɗinmu yake. A ɗorata kan komai cikin awannin da suka rage. Dan hannun karɓa, hannun bayarwa za'ai, kuma a cikin mintunan ƙarshe biyar kacal”. “What! Oga yanzu nan sakar masa yarinyar nan zamuyi?”. “Muma yin hakan dole ne a garemu. Dan munfi buƙatarta a wajensa fiye da a wajenmu a yanzu. Sannan tana da muhimmanci fiye da komai a garemu a yanzu. Ku ɗauka mune GANGAR JIKI, ita kuma ITACE NUMFASHI. Mi kuke tunani idan da ɗaya babu ɗaya?”. Tabbas wannan maganar ta Oga ta masifar girgiza su. Dan yanzu sun fahimci girman yarinyar ya wuce ƙaramin tunaninsu a wannan tafiyar. Kuma sai da ita sannan zasu cimma nasarar da suke buƙata. Ashe ba ƙarya bane da akace da yawan yaƙe-yaƙen waɗan nan ƙarnukan suna fara ne ta sanadiyyar MATA. Ga kuwa zahiri suna gani a yau ɗinsu. To bara suga yaya za'a kwashe wannan wasan. SU-NE ko SHI-NE.. Cikin sauke numfashi mai nauyi Viper ya furta, “Tabbas oga mun fahimce ka. Sannan mun gamsu da wannan shirin. Musamman idan mukai dubi da She is a very clever girl. Dan ni ban taɓa ganin mace data bani mamaki ba irinta, idan har a wannan ƙarancin shekarun nata tana a haka ya kake gani nan da wasu 5-years masu zuwa kuma?....” “A gaskiyar ka Viper, yarinyar KADARA ce mai daraja. Kuma ya kamata ubanta ya ci wannan baiwar tata yanda ya kamata Oga. Lokaci yayi da ƙungiya zata ƙara duba ma Mole ko kuwa ƴan uwa?”. Yanda ya ƙare maganar da kallonsu su duka. Kai tsaye suka nuna amincewa. Dan girman kai irin na Mr Specter kaga ya yaba wani lallai ko waye ya ciri tuta............✍️