
Post
Kida a ruwa Book 3 page 3
..... see, what's in it? There are thousands of people who are waiting to be paid. God, I repent of this little bird that I will choose her over money?". "Mtsoww! As for you, I forgot it's a bathtub, you don't distinguish between the right things. Dalla give her the injection and let's go, if I can see her, I can do anything". When they looked at his white face, his eyes were turned upside down because of his lack of sleep. He just got out of the parking lot and called Ammar. He said to him, "I'm out." Looking at Ammar straight, she said, "Are you okay?" Where are you going now that you came in?". He smiled as he said.....
3
..........Waya Mr Specter ya ɗauka yay kiran Jagwa, kai tsaye ya bashi umarnin a yima Nimrah makarin allurar. Sannan su ɗauketa akwai address zai tura musu can zasu kaita. Ya tabbar sanda zasu isa ta ƙarasa warwarewa. Shima zai haɗu da su a can. Sam su Jagwa ba haka suka so ba, dan sun gama sakin jiki yarinyar zata daɗe a wajensu su sha shagalinsu da ita. Dan har ga ALLAH yawunsu ya biya. Amma sun san wanene ogansu Mr Specter, ba mutunci ne da shi ba. Bin umarnin abinda yace dole ne a garesu. Allurar suka haɗa sannan suka nufi ɗakin da take suna faman mita. Tana kwance a ƙasa inda ta silale da tana salla har yanzu, cikin jan tsaki Lio ya janye bargon da take ciki yana faɗin, “Gaskiya Oga ɗan yawa ne, ga nama iya nama ya gasu iya gasuwa har mai na naso amma ya haramta mana. Ni wlhy da za'a bani ladan aiki da ita madadin kuɗin ma nafi buƙata.....” “Amma kai mahaukaci ne Lio”. Jagwa ya katse shi cikin takaici baki a hangame. “To kaga laifina ne? Jiba fa idan idon ka a makance yake”. “Na gani, sai miye a ciki? Akwai fa dubunta sun kama ɗaki suna jira a biya. ALLAH na tuba wannan fiririyar tsuntsuwar ce har zan zaɓeta sama da kuɗi?”. “Mtsoww! Kai fa na manta baho ne, baka banbance abinda ya dace. Dalla yi mata allurar mu wuce, dan wlhy idan ina ganinta komai zan iya aikatawa”. “Hummm”. Cewar Jagwa yana ma Nimrah allura. Daga haka suka cicciɓeta sukai waje da ita zuwa mota kamar yanda oga yace suyi.....
<<<%>>>★<<<%>>>
8:30am Dada ya iso asibitin da Ruƙayya ke kwance. A lokacin awannin Nimrah goma sha biyar a hannun waɗan can mutanen. Simple kaya ne a jikinsa marasa nauyi. Sai slippers masu taushi suma da suka haska farar ƙafarsa. Kamar ko yaushe da facemask a fuskarsa sai siririn farin glass daya ɓoye idanunsa da rashin barci ya sakasu juyewa fiye da yanda suke. Shi da kansa yay driving kansa, dan daga UNIT ZERO kai tsaye nan yayo kawai. Koda ya samu waje yay parking bai fita a motar ba, sai yay kiran layin Ammar. Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga. Yana kammala amsa masa sallamar da yayi kafin ya fara gaishe shi yace masa, “Fito ina waje” daga haka ya yanke kiran. Mammah dake kallon Ammar daya miƙe ta ce, “Lafiya? Ina zaka kuma kai da ka shigo yanzu?”. Ɗan murmushi yayi yana ɗauke idanunsa akan Ruky dake shan tea. “Mammah Dada ne yazo. Bari naje kada yay ta jira”. Kai ta jinjina masa kawai, ya juya ya fita. Ruky dake saurarensu kuwa hawaye ne suka zubo mata. Dan tunda akace Dada yazo hakan na nufin har yanzu babu labarin Ninah ɗinta. Mammah kanta zuciyarta sake raunana tayi. Amma sai ta danne batare komai ba dai ta cigaba da bama Ruky dake share hawaye shayin. A haka Dada da Ammar suka shigo ɗakin. Kallo ɗaya yay ma Mammah yasan cikin tashin hankali take. Slowly ya janye ya maida kan Ruƙayya data zuba masa nata tana hawaye. Sai kawai ya ɗan furzar da iska yana zare eyeglass ɗin idonsa da sauke facemask ɗin ƙasa ya cigaba da takawa inda suke. A kujerar da Ammar ta gyara masa ya zauna, ya gaishe da Mammah cike da girmamawa kamar yanda ya saba. Itama ta amsa masa da kulawa tana mai jin tausayinsa. Dan kallo ɗaya ta masa taga yanda idanunsa suke tasan baiyi barci ba, sai ta sake danne tata damuwar dan sama masa nutsuwa ko yaya. Idanunsa ya maida kan Ruƙayya dake gaishe shi cikin rawar murya. Maimakon amsa mata sai ya kai hannu ya shafa kanta dake sanye da hula. Cikin taushin murya sai dai da dakewarsa ya furta, “Dama idan jarabawa ta samu bawa ba addu'a ya kamata yayi ba?, sannan ya godema UBANGIJI da ni'imomin dayay masa kafin jarabawar?. Baby na fa ƴar soja ce, idan wasu sukaga hawaye na zuba a idanunta anya bazasu mana dariya ba Daughter”. Sosai Murmushi da hawaye suka suɓucema Ruky a lokaci guda. Ta kama hannun Dada tana ƙoƙarin haɗiye kukan. “Dada in sha ALLAHU na daina yin kuka. Amma dan ALLAH ku dawo min da Ninah, idan babu ita a duniyata nima nawa numfashin yazo ƙarshe.” “Kiyi addu'a, in sha ALLAHU nan da wasu awanni zaki ganta. A yanzu haka muna kan aiki tuƙuru, hasali ma mun san inda take amsota kawai ya rage....” “Dada da gaske?”. Ta faɗa cikin washe baki. Murmurshin gefen baki ya mata yana mai lumshe idanunsa da buɗewa alamar tabbatarwa. Ba Ruƙayya kaɗai ba har Mammah da Ammar zancen sa ya musu daɗi. Dan sai da Mmamah ta kauda kai gefe tana ɗauke ƙwallar da suka taru mata a ido, Ammar kuwa ya ɗauki waya ya turama sauran ƴan uwan bayani ta cikin group ɗin su na WhatsApp. Sarai Dada na lure da su su duka har Ammar ɗin. Sai dai baice komai ba. Tea mammah ta haɗa ta bashi. Zai yi magana ta hararesa, murmurshi yayi dole ya amsa. Da zata zuba dankali ne ya lallaɓata yace tea ɗin ya ishesa. Da ƙyar ta yarda. Bai ma wuce sha biyar ba kiran Imran ya shigo masa. Dole ya ajiye yana miƙewa. “Mammah inaga zan barku, su Imran sun kammala shirinsu. Dole kuma zan rigasu wucewa. Ai mana addu'a”. Ko bai fito fili ya faɗi inda zasu je ɗin ba Mammah ta fahimta. Dan haka ta fara jera addu'oi masu nauyi sosai a garesu dama al'umma baki ɗaya. Daga haka ya shafa kan Ruƙayya batare da yace komai ba ya fice Ammar biye da shi. Har mota ya rako shi. Sai da ya shiga har ya mata key sannan Ammar ya matsa ya bashi hanya. Dada akwai nutsuwa, sannan komai nashi zaka sameshi a nutse yake. Sai dai akan aiki baya ƙaunar ƙalula ko wasa, in za'ayi kawai ayi, in baza'ai ba a bari, amma maganar wasa anan ɓangaren ba'ayinsa da shi. Yana da zafin nama irin na jaruman maza...
===============
Kamar yanda suka buƙata an janye sojojin ƙofar yamma tun a daren jiya ƙarfe goma sha ɗaya. Sai dai a maimakon bada Nimrah ko wucewa da abinda suke sonyi wani waje suka kai Nimrah ɗin. Sun kuma nuna mata duk abinda suke son ta sani ta kuma gamsu da su akan zuri'arta. Da farko rashin kunya ta fara zubama su Jagwa dake tare da ita bayan farkowarta, haka ma koda aka kaita gaban wanda sukafi su Jagwa ɗin bata risina ba sai da suka buɗe mata abinda yay matuƙar gigizata. Tabbas tayi shaidar gani da ido, ta kuma shaidar ji da kunne na zahiri. Tayi kuka har hawaye sun daina fita mata. Daga ƙarshe tayi alwashin ɗaukar fansa akan Dada ta hanyar tabbatar masa da DAN HAKKIN DAKA RAINA SHI KE TSOLE MAKA IDO. Dan haka ta ɗauki alwashin zamewa Haysam Abdul-rasheed Shehu Shehu Kobi KIƊA A RUWA. MAI TADA HANKALIN DODO. Idan shi yace ya ƙware a iya FUSKA BIYU zata tabbatar masa da ita kuma RAINON SA ce. Zatai kwanciyar RUWA a gabansa, domin samawa kanta HANYAR wucewa harta ƙofofin gashin jikinsa.....
★★★★
Ƙarfe 12:pm su Imran suka samu saƙon inda zasu amshi Nimrah. Ba kuma a ko'ina bane sai ta inda suka janye sojojinsu. Dan su Oga Jush sunyi alƙawarin a gaban idanun su Imran zasu wuce da kayansu dan su nuna musu MANYAN ƘWARI ne da sukafi ƙarfin kowa. Dan haka suka shirya sosai kuma akan Nimrah da shirin da ita kanta bata sani ba. Koda Imran ya turama Dada saƙon ya jima yana maimaita shi shiru cikin nazari, dan ya tabbatar zasu iya wasa da hankalinsu. Idan kuma sukai irin wannan tunanin zasu iya aikata yanda suka ce. Ya kamata ace duka kada suyi sakaci, musamman ma shi, dan wannan shine zaren da zai kama na fara shinfiɗa aikinsa akan su. Bayan ya gama ƙullawa da kwancewa ya turama Imran saƙo shima. Daga haka ya tashi ya fara shirin cikin uniform ɗin soji domin yin ɓadda kama. Dan shi a yanzu ba jami'in sojoji bane a zahiri. Shi Special Presidential Intelligence & Covert Operations Commander ne a yanzu, amma a wannan gaɓar dole yay ɓadda kama cikin sojojin dan samun abinda yake buƙata. Duk da ya san Imran da Faro zasu iya yin duk abinda zai iya yi in sha ALLAHU.. Kodan ya jima bai saka kanyan ba, ko kuwa dan ya ƙara canjawa da cikar kamalar shekaru ne da nutsuwa. Kayan sun masa ƙyau fiye da shekarun baya ma da yake sakasu da ƙuruciya. Buɗaɗen jikinsa, zuwa shafaffen cikinsa sun zauna fyaram a cikin kayan. Kai da kaga wannan ZAKIN a cikin waɗan nan kayan manyan kasan kasan ba zakin ajiyewa a gidan zoo bane domin kallon yara. Zaki ne na farauta da in ba'a ma saka masa linzami ko takunkumi ba ɓarnar da zai yi sai ya zama abar rubutawa a tarihin da za'a kafe a bangon gidan gwamnatin ƙasa dan ya zama barazana ga BABBA DA JAKA. Bayan ya saka Handkachiff kamar facemask ya saka baƙin eyeglass daya ɓoye idanunsa da ainahinsa gaba ɗaya. Sai da ya tabbatar kayan aikin da duk zai iya buƙata na cikin jikinsa sannan ya fito compound ɗin gidan. Dan yana a UNIT ZERO ne shi kaɗai. Parking space ya nufa kai tsaye cikin takun sa na masu ƙarfin jini da babu wasa a ciki ko wani rangwaɗar shashanci, dan wannan mazan a mazansu suke kai tsaye. Hannu ya kai kan blue tempol da aka rufe wani abu ya yaye shi, sai ga wani gingimemen ƙaton mashin baƙi wulik mai shegen ƙyau da tsari ya bayyana. Da allama madadin tsohon mashin ɗinsa ne ya dawo a sabon salo, sabon zamani. Hularsa dake ajiye samansa ya ɗauka ya saka, kafin ya haye yana karanta addu'a yay masa key. Koda yazo gate remote ya danna ya buɗe da kansa, yana gama ficewa ya maida ya rufe kansa. Shi kuma ya ɗauki hanya..........✍️