Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 4

Post

Kida a ruwa Book 3 page 4

.....yes, the answer is only one life, the life of a woman, the woman is a 16-year-old girl. This is very annoying, even though they are officers who protect the community, they should not let a single person have their time wasted there. Since they don't know what plans these people have against them. It is possible that they have planned a coup or a brutal murder for them after they have achieved their goal. "Mtsoww!!" He pulled back and looked at the clock. Gulma wants to be close to him, but I don't have the opportunity to look at them. He has to be patient like everyone else. So 4pm is over. The worshipers even presented. At 4:23pm, a call came to Imran's line. Together with Imran and Dada, one of Imran's children looked at the phone so that no one recognized him. Then they made eye contact. Dadan's eyes blinked at him and he raised the sign, and then he straightened up and went back to the way the children were. However, whatever Imran listens to on the phone, he also hears it. "In thirty-seven minutes, our goods will arrive. They will pass and we will give her to you. If you say that you will make an effort, you will have the same result on her. And.....

Standalone post1,623 words

4

........“Mtsowww!!”. Wani soja yaja tsaki yana kallon agogon hannunsa. Tun 12:30 suke a wajen nan, gashi har 3pm babu alamar abinda suke zaman jira ɗin zai samu. Gashi ko zaman cin abinci a nutse oga ya hana su. Salla kawai ake basu damar yi, wanda ma basayi su basu da ko minti na hutawa. A kaikaice ya ɗan wurgama Imran harara, yana ganin zai juyo ya tsume ya gyara tsaiwarsa. Oho shi Imran ɗin ma bai san yanayi ba, umarni ne dai ya bayar matsayinsa na oga kuma dole-dole abi. A daji suke iya daji, dan ko dabbobin jeji akace za'a samu masu haɗari a wajen baza'ai musu ba. Dajin mahaɗa ce ta ƙasashe guda uku, daga nan zaka iya shiga kowacce ƙasa cikin sauƙi. Hakan yasa akowane iyaka akwai jami'an soji da aka ajiye na kowacce ƙasa da sauran jami'ai. Sai dai kowa da yanda yake gudanar da aikin sa da kuma iyakarsa. A tasu iyakar babu soja ko ɗaya bayan su ɗin nan da aka kawo awanni uku da suka gabata, gaba ɗayansu su ashirin ne kuma har oganni su guda uku. Abin takaicin kuma wai an kawosu ne kawai dan amsar rai guda ɗaya, ran ma na mace, macen ma yarinya ƙarama ƴar 16years. Wannan wane kalar abin haushi ne, duk da su jami'ai ne masu bada kariya ga al'umma ai bai kamata ace dan rai ɗaya an lalatar da lokacinsu a wajen ba, lalatarwar kuma da suma zasu iya rasa nasu ran. Tunda basu san wane shiri mutanen nan ke da shi ba a kansu. Zata iya yiwuwa sun shirya musu wani tuggu ko kisan mummuƙe bayan sun samu cikar burinsu. “Mtsoww!!” ya sake jan tsakin dai yana kallon agogo. Gulma yake son suyi dana kusa da shi, amma ba dama oga na kallonsu. Dole ya haƙura kamar kowa shima ya dake. A haka 4pm ta cika. Masu salla har sun gabatar. 4:23pm dai-dai kira ya shigo layin Imran. A tare Imran da Dada daya saje cikin yaran Imran ta yanda babu wanda ya gane shi ne suka kalla wayar. Sai kuma suka haɗa ido. Idanu Dadan ya lumshe masa alamar ya ɗaga, sai kuma ya gyara tsaiwa cikin basarwa ya koma kamar yanda yaran keta kai kawo. Sai dai duk abinda Imran ke saurare a cikin wayar shima yana ji, dan sun raba bluetooth ɗin ne kowa da ɗaya a kunnensa. “Nan da mintuna talatin da bakwai kayanmu zasu iso. Zasu wuce zamu baku ita. Idan kukace zakuyi wani yunƙuri zakuga sakamakon hakanne a kanta. Daga yanzu ka fara ƙirga lokaci, sannan ga saƙo ka faɗama oganka, YA KULA DA KANSA. Idan ya shagala a kula da wannan ƘASAR, shine zai zama ƘASAR dan a maimakon kejin prison wannan karon CIKIN KABARI zai shiga”. Ƙittt. Wayar ta yanke kafin Imran ya iya cewa komai. Kamar yanda Imran ya ji komai, shi ma Dada ya ji komai. Sai dai wannan ba shine lissafin sa ba a yanzu. Ta inda Nimrah kawai zata bayyana yake kallo.

4:40pm dai-dai baƙar mota mai duhun glass ta iso wajen, sai dai nesa da su kaɗan. Sannan ta ɗayan ɓangaren ba ɓangaren da suke ba. Gaba ɗaya hankalinsu akan motar yake, sai dai tunda ta tsaya babu wanda ya fita a ciki sai da ƙurar da suka tayar ta gama kwanciya kusan mintuna uku. 4:45 aka buɗe murfin motar, jibga-jibgan garada guda biyu majiya ƙarfi suka fito cikin shigar rufe jiki gaba ɗaya dan babu abinda ake gani nasu. Ɗaya ya buɗe baya Nimrah ta fito. Kayan dake jikinta ne dai na jiya, sai dai yanzu an rufe mata baki, hakama idanunta da baƙin ƙyalle. Ƙafarata babu takalmi. Sannan an ɗaure mata hannayenta da aka maida baya. Sun lulluɓa mata towel alamar akwai abinda suka rufe a jikinta. Dan Imran har ya motsa saukar idanunsa akan towel ɗin da suka rufa mata ɗin ne ya saka shi tsayawa cak. Shi fa jam'in soja ne, daya kwashe shekaru yana aiki tun ƙuruciya. Ta ya zai gagara gane kowanne makirci koda daga nesa ne. Inda Dada yake ya kalla, sai ya ga shima Dada ya kallo shi. Da ido Imran ya masa magana, Dada ya mayar masa murtani alamar ya gane komai. Sake maida dubansu sukai kan Nimrah, a kuma dai-dai lokacin mutanen dake tare da ita suka yaye towel ɗin jikin nata. Bayyanar rigar bomb ta saka yaran sojojin zabura baya a firgice, shi kansa Imran da Dada sai da zukatansu suka buga duk da dama abinda sukai hasashen gani kenan. Daga can Faro dake ɓoye da wasu jami'ai ya ce, “Ya rabbi, amma mutanen nan ƴan iska ne”. Daga Dada har Imran sun ji shi, saboda yana magana ne ta hanyar sadarwa dake a kunnensu. Cikin danne kai murya ƙasa-ƙasa Dada ya furta, “Kar wanda ya tada hankalinsa. Ku basu damarsu”. Badan hankalin nasu ya kwanta ba suka amsa masa. Dan gaba ɗaya Imran ya jiƙe da zufa. Shi kansa Dadan goshinsa a jiƙe yake, kawai dan fuskarsa a rufe take shiyyasa ba'a gani. Yanda mutanen basuyi magana ba haka suma babu wanda yay magana har suka cire ƙyallen dake rufe da idanun Nimrah. Nimrah da sai yanzu ta fahimci halin da take ciki ƙirjinta yay wani masifar bugawa. Ta kalla bomb ɗin dake jikinta, ta kalla mutanen guda biyu da bata sansu ba. Dan daga inda aka baro da ita ta shiga motar nan bata sake sanin halin da take ciki ba. Waɗan nan mutanen sai yanzu ta gansu, sannan wannan ɗaurin goron duk a motar nan akai mata shi tabbas. Hango Daddy Imran daya zubo mata idanun sa da ke rikice ya saka nata idanun tara hawaye. Ba kukan tsoro bane, kukan tausayin da jin kewar barin Ruƙayya da su Mammah ne, ta tabbatar bomb a jikin mutum dai mutuwa ce, ita kuma mutuwa guda ɗaya ce tak. Bayanin mutanen can ya shiga dawo mata a rai dalla-dalla tamkar yanzu ne suke yi mata shi, ta sake kallon bomb ɗin zuciyarta na kawo mata hoton Dada. Sai kawai tayi murmushi mai ciwo, dan ta gama gaskata abinda suke son ta yardan tun ma kafin aje da nisa..... Isowar wasu jerarrun motoci guda goma ciff ya katse tunanin Nimrah. Lokacin 4:50pm. Yanda suka shigo a guje ya saka ƙura tashi sosai, sai da takai sojojin nan sun rufe hancinansu, duk da dama fuskokinsu sun shafa baƙin abu domin ɓoye ainahin su kamar yanda dokar soja take. Kamar yanda Imran yay umarni babu wani soja daya motsa a inda yake balle yin wani yunƙuri, sai da suka wuce lokacin 5pm na cika ciff sannan waɗanda ke tsare da Nimrah sukai wuff suka shige moto. Nuni ɗaya ya yo musu da remote ɗin bomb ɗin jikin Nimrah dake hannunsa, hakan yasa anan ma babu wanda yay wani yunƙuri har sai da motar ta ɓace ma ganinsu. Dada dake jinsa a matuƙar fusace ya matse hannunsa da masifar ƙarfi har sai da ƙasusuwan sukai ƙara. Haka ma sauran sojojin babu wanda ransa ba'a ɓace ba. Waɗan da ke ɓoye duk sun fito, sai masu cire bomb da suka zagaye Nimrah. Cikin tashin hankali ɗaya a cikinsu ya kallo inda su Imran suke. “Sir akwai matsala fa. Sunyi masifar rikita wayoyin ta yanda yanke wata kai tsaye zai iya sakawa a haɗa da wata. Gashi 30minutes ne kawai...” Iska mai nauyi Dada ya furzar daga bakinsa, dan sai yanzu ya dawo hayyacinsa daga ɓacin rai mutanen nan. Komai baice da kowa ba ya nufi inda Nimrah take shima. Sosai hankalin Imran ya tashi, duk da yasan Dada ya ƙware matuƙa wajen iya warware bomb, to amma wannan idan an ɗana shi ne dan tarko fa, duk da yasan ko cikin yaransu dake wajen bayan Faro da Yusuf babu wanda yasan Zak-Shadow ɗin ne. Kusan a tare suka yinƙuro domin yi masa magana shi da Faro. Amma sai ya dakatar da su ta hanyar ɗaga masa hannu. Yana zuwa ya bama wanda ke wajen umarnin tafiya. Dama hankalinsu a tare yake, duk da kuwa aikinsu ne amma magana fa ake ta bomb, bomb ɗin ma da remote ɗinsa ke hannun wasu. Idanu ya zubama Nimrah da gaba ɗaya ta gama jiƙewa da zufar tashin hankali. Ga idanunta a rufe lips ɗinta dake a bushe na ɗan rawa kaɗan-kaɗan. Samun kansa yay da yin murmushi ƙarfin hali daga cikin handkachiff ɗin daya rufe fuska. Kafin a hankali ya janye shi zuwa ƙasa bayan ya kai duƙe a gabanta dan tana zaune ne. “Kiddo. Open your eyes”. Da wani kalar sauri Nimrah ta buɗe idanun nata. Duk da kuwa yayi maganar ne da murya mai taushe domin danne fushi da tashin hankalin da yake ciki. Ya tabbatar mutanen nan basu da hankali, kaɗan daga aikinsu su tada bomb ɗin jikin nata.... “Da....d...dah!”. Ta faɗa lips ɗin nata na rawa sosai fiye da da. Murmurshi mai nauyi ya sakar mata. Murmurshin da zata iya rantsuwar bata taɓa ganin irinsa akan fuskarsa ba. Sai kawai hawaye suka shiga silalo mata. Ta sake buɗe baki zata yi magana ya girgiza mata kansa. Tare da ciro dabino a aljihunsa ya sashi a bakinsa ya raba biyu ya cire rabin ya nufi bakinta da shi... “Haah”. Ya faɗa a hankali. Ai bama tasan ta buɗe lips ɗin nata ba a hankali ya saka mata. Sai kuma ya shafa lips ɗin nata da yatsa yana sakar mata wani murmushin. Ita dai kallonsa take kamar sakara, tama kasa tauna dabinon. Yanda ma ta shagala a kallonsa kamar wadda ta suma sai da ya fara share mata hawayen da suka gagara tsayawa sannan ta kawo nannauyan numfashi alamar dawowa hayyacinta.. Baiyi magana ba, bai kuma daina murmurshin ba, ya dai maida hankalinsa akan wayoyin bomb ɗin cike da nazari, bayan ya kalla lokacin daya rage musu 18-minutes.........✍️