Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 5

Post

Kida a ruwa Book 3 page 5

.....she also went towards the servants. She finished her ablution safely and stood up to come out only to be washed away by the smooth water and her voice was heard. Oh Rabbi, they jumped up in confusion, Biebah's son even started praying, she didn't even know she was running. Mammah was giving her hand, and Asma'u was trying to get up. At that time, Bilal was also coming back. All the servants were agitated, Mammah went in first, then Ma'u. They were shocked to see Lailah lying on her stomach on the ground. ALLAH, king Ma'aruff, his body was shaking as if he was going to fall and attack the servants. He scolded Lailah completely and called her name. But there was no sign that she was even breathing. Ammar had already turned and ran to call a doctor and his hair came back. A doctor followed by a woman. Then two nurses carry the bed to send patients. Ruqayya, Asma'u and Biebah cried a lot, and so did Mu'azz. All of Hanoon's emotions are calm and her body is shaking..... "Doctor, how are you?". Ja'afar was in a panic while finding Doctor... data from the room where Lailah was taken. "Follow me to the office close at hand, son, there is no time for the theater. If not, we can lose he

Standalone post1,687 words

5

..........Tun fitar Dada a asibiti hankalin Ruky ya koma kan agogon wayar Mammah da wayar ma gaba ɗaya. Babban burinta kawai taga Dada ya kira yace sun amshi Ninah. Awa ɗaya ta shuɗe shiru. Har ƴan gidan suka zo duka. Shariffa dake jego ce kawai babu. Su Asma'u ma da Khalifa sai gasu. Lolo ya dameta da surutu amma ita hankalinta ba'a nan yake ba. Ba ita kaɗai ba su kansu su Mammah hankalinsu nakan wayoyinsu ne. Babu abinda suka fi ƙishirwa a yanzu kamar kiran Imran ko Dada. Dan tunda suka duba jikinta da tambayarta yaya take ji ta tabbatar musu bata jin komai yanzu suka koma jigum-jigum. A haka lokacin salla yayi. Mazan suka fita sukayi. Biebah da Asma'u ma suka miƙe bayan Mammah ta fara yo alwala. Dan Lailah tace su fara yi zatayi a ƙarshe. Hanoon dai bata da wannan alamar, dan tana gefe tana faman latse-latsen waya. Dama da ƙyar ta biyosu, garama ita, ƴan uwanta Afeef da Dayyan bama su tashi a barci ba har suka baro gidan. Bayan Biebah tayo alwala Asma'u ma ta shiga Lailah ta cicciɓa da ƙyar itama ta nufi bayin. Ta kammala alwalar ta lafiya ta miƙe zata fito kawai santsin ruwa ya kwasheta sai ƙararta suka jiyo. Ya rabbi a rikice suka zabura, dan Biebah ma harta kabbara salla bata san ma ta kwasa a guje ba. Mammah dai ta idar, sai Asma'u dake ƙoƙarin kabbarawa. A kuma lokacin su Bilal ke dawowa suma. Cikin tashin hankali duk sukai bayin, Mammah ta fara shiga sai su Ma'u. Hankalinsu ya tashi da ganin Lailah kife a kan cikinta ƙasa wanwar. ALLAH sarki Ma'aruff shima jikin nasa na rawa kamar zai faɗi ya afka bayin. Shi ya cacumi Lailah gaba ɗaya ya ɗaga yana kiran sunanta. Sai dai babu alamar ma tana numfashi. Ammar da tuni ya juya da gudu kiran likita sai gashi ya dawo. Likita biye da shi mace. Sai Nurses biyu ɗauke da gadon tura marasa lafiya. Kuka sosai Ruƙayya da Asma'u da Biebah keyi, hakama Mu'azz. Duk iskancin Hanoon dai gata ta nutsu itama jiki na rawa.....

“Doctor yaya?”. Ja'afar ya faɗa cikin tashin hankali yana tarar Doctor... data tifo daga ɗakin da aka kai Lailah. “Ku biyoni office kusa hannu dan babu lokaci theater zamuyi mata. Idan ba haka ba za mu iya rasata ita da abinda ke cikinta. Dan tayi mummunar faɗuwa gaskiya.” Ja'afar ɗin ne ya bita. Dan Ma'aruff na zaune ido a rufe alamar jiri yake ji. Bilal na riƙe da hannunsa da Ammar. Su Mammah harda Ruky mara lafiya na tsaitsaye kowa na sharar hawaye. Sukam sun godema UBANGIJI a wannan kwanaki kam. Mintina biyar sai ga Ja'afar ya fito doctor biye da shi. Shi ya nufi inda suke, ita kuma ta nufi wani office. Bata jima ba ta sake fitowa da Doctors guda biyu duk mata. Sai kuma ga wasu Nurse suma biye da su da kayan aiki......

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷

Anan gida kuwa Nabeeha ce da gayyar ƴan rakiyarta suka iso. Dan yau ne take dawowa. Jiya dai suna gyara duk abinda ya dace da safe aka kawo sauran kayanta na sakawa. Shine sai yanzu kuma suke isowa su ƙarfe uku na yamma. Su dai su maigadi ƴan kallo ne kawai. Yanda ba'a tambayesu mutanen gidan ba suma basu ce komai ba. Sai da ma cikin ƴan suyan naman Shariffa da ta nufo sashen Mammah ɗin amsar abu ne ta gansu ta koma tana gayama Shariffa. Shariffa ba yawan magana ne da ita ba, sai kawai tai murmushi da faɗin, “To sannunta da zuwa.” daga haka ta maida hankalinta ga shayar da yaronta. Dan ita hankalinta ma ba'a nan yake ba. Fatanta ƴar uwarta da aka shiga theater da ita ALLAH ya rabata da cikin nan lafiya. Dan lokacin haihuwarta da saura. Suna saka ran sai nan da sati uku ma wannan tsautsayin ya faru. Itama mai kawo zancen duk da Inna take a wajensu su duka ita da Lailah ɗin da taga Shariffa bata tayata suyi ɗin ba yanda take so saita fice tana ƙunƙuni kawai.....

Anan sashen Nabeeha ƙawayenta sun zagayeta anata iya shege. Ita kam daɗi kamar zai kasheta yau dai ta dawo ɗakinta din-din-din. Tun jiya take cike da zumuɗin son ganin Haysam mamanta ta kwaɓeta. Ko bayan tafiyar Momyn su sai da ta saka Ismat yi mata cid amma ta dawo ta tabbatar mata baya gidan. Itama tasan ana wannan taron bazai zauna ba. Sai ta samawa kanta lafiya akan ai yau ma rana ce. Dan haka yau ɗin ma ta matsu su taho da wurin nan. Har akai la'asar ƙawayen nata na nan. Sai da suka gama shaƙiyancinsu da ɗirka mata abubuwa sannan wajen 5 suka tafi. Da Ismat kawai aka barta, dan su Amimah basu biyosu ba. Itama Ismat ɗin Momy bata san ta biyosu ba, so take kuma daga nan ta gudu gidan Abbansu kawai. Ismat ɗin ta tura yau ma gano mata ko yana nan, idan ma baya nan taje wai dan su Mammah su san ta dawo, ai tasan Mammah ɗin zata saka shi zuwa inda take ko bai niyya ba. Sai dai me, Ismat na zuwa ta dawo mata da labari mara daɗi. Cewar shi baima kwana a gidan ba. Su Mammah kuma duk suna asibiti Ruƙayya babu lafiya. Ga kuma Lailah ma ta faɗi an shiga da ita cs har yanzu ba'a fito da ita ba. Maimakon hankalin Nabeeha ya tashi tace suje asibitin sai tayi shiru. Sai ita Ismat ɗin ce ta ce, “Aunty kodai asibitin zamuje muma. Dan na fahimci abin fa babbane, hankalin masu aikin nasu duk a tashe yake wlhy”. “K rabani da wani asibiti Ismat babu inda zanje gaskiya. A gama zuba min wannan uban ƙamshin a jiki da gyara ni na kuma ƙare a asibiti. Ƙamshi nake son D. ya ji ba warin magunguna ba”. “Amma Aunty.....” “Kefa matsalata dake kenan. To ALLAH zan kora ki gida yanzu. Haba ki fahimceni mana. Ke bama ƙya ganin idan nace zan fita daga kawoni akwai ganganci a ciki. Karfa ki manta yanda D. Ya tsani yawo”. “Hummmm”. Ismat ta faɗa kawai. A ranta ko faɗi take (Baki san ya tsani yawon ba sai yanzu. Bayan tunda yabar gidan kema baki zauna ba Aunty. Kina tunanin kuma baza'a sanar masa ba. Ke matsalar ki baƙya son gaskiya da ɗaukar shawara. Kin bar Momy ta tasirantar da ƙiyayyar dangin mijinki kuma ƴan uwanmu ma ta wani fannin a zuciyarki. ALLAH yasa ki gane, dan inba haka ba wannan karon ma zaman nan naki bamai ɗorewa bane. Dan yanzu mutanen gidan nan bana da bane da suke miki kawaici, sun ɗanɗana zama da wasu surukan sun ji daɗi)...

<<••>><•••••><<••>>

“Dada zan MUTU ko? Zan mutu bazan sake ganin Mammah da Ruky ba, bazan sake ganin su Uncle's Ja'afar ba da su Mu'azz”. Dada da hankalinsa gaba ɗaya ke kan aikinsa ya saki murmurshi kaɗan. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Bayan kin shiga labor room sau goma sha biyu, kin haifo magadan SOJA, jikokin Abdul-rasheed Shehu Kobi ko Kiddo?”. Ita sam bata wani fahimcesa ba. Shima kuma yanda yay maganar a basarwarsa yana kuma aikinsa bama zakace shi ya faɗa ɗin ba. Ya sake kallon mintinan da suka rage. 9 kawai. Dai-dai nan Imran dake nufosu ya taka wani abu. Cak ya tsaya yana kallon ƙafarsa. Dan haka Faro dake kallonsa shima ya ce, “Yaya dai?”. Ƙafarsa ya nuna masa sannan yay masa alamar bomb. Sai kuma yay masa nunin yay shiru kada Dada yaji. Ya ilahi wata muguwar bugawa zuciyar Faro tayi, a take jikinsa ya kama rawa. Ya kalla Imran ya kalla su Dada. Ya rasa ma ina zai kama. Suma sauran sojojin hankalinsu ya tashi matuƙa. A take suka fara zagaye wajen da na'urorin bincike bomb. Dan tunda ogansu ya taka hakan na nufin akwai wasu a wajen. Ai ko sai gasu cikin ikon ALLAH kusan bakwai a cikin ƙasa irin wanda Imran ɗin ya taka. Tuni masu ilimin akansa suka fara aikinsu. Sauran jami'an suka ja baya sosai. Sai dai Faro ya kasa yin hakan. Ya kafa ma su Dabo idanunsa kawai da sukayi jazur na tashin hankali...

“Dada ƙara min Dabino”. Nimrah ta faɗa idanunta a rufe dan ta sadaƙar kawai lokaci yayi. Shi kansa uban gayyar hankalinsa ya gama kaiwa ƙarshen tashi. Dan saura minti huɗu ya rage musu. Gashi ya katse waya har biyu basu bane, saima ƙara na ƙidaya lokaci da suka saka bomb ɗin ya fara. Dabinon ya ciro ya saka mata a baki, batare daya bar abinda yake ba. A dai-dai wannan lokacin kuma Faro ne ɗauke da wani ƙaton dutsi yana tafiya a hankali a hankali ta bayan Imran dake tsaye cak a wajen nan har yanzu idanunsa a rufe. Babu abinda yake maimaitawa sai kalmar shahada a zuciyarsa. Dan ya riga ya sadaukar ya kuma sadaƙar yau babu makawa ranar amsa kiran UBANGIJI ce. Babban fatansa Nimrah da Haysam su tsira a idanunsa kafin lokaci ya cika.....

“Dada dan ALLAH ka tafi a wajen nan. Ka tafi ka barni. Ka sanarma Mammah ta yafe min duk rashin jin da muke mata ita da su Uncle Ma'aruff su yafe min. Ruƙayya kace mata ina ƙaunarta, zan mutu da ƙaunarta, in sha ALLAHU zamu haɗu a aljanna....” Ita take furta kalaman shi tsigar jikinsa ke tashi saboda tashin hankali. Saura minti ɗaya ya rage musu. Ya kai hannu zai katse wata waya kawai ta miƙe a zabure tabar wajen a guje. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un NIMRAH!! NIMRAH!!”. Dada ya shiga ƙwala kiran sunanta cikin ƙaraji har jejin na amsawa saboda ƙarfin da muryarsa tayi, da yanda take fita kuma da razani. Amma ina bata sauraresa ba. A kuma dai-dai wannan lokacin Imran ya firgita da yanda Dada ya kira sunan da ƙaraji kawai ya ɗaga ƙafarsa a razane yana zaro idanun sa da suka sauka akan Nimrah dake kwasar gudu. Boooooommmm!!!!!! Kake jin ƙarar fashewar bomb ɗin ta karaɗe illahirin jejin har wani jijjiga yayi. A take wajen ya turniƙe da uban baƙin hayaƙin da wani ma bai iya gane wani. Ga yanda ƙasa tai watsi a cikin hayaƙin ya sake rufe ko'ina.........✍️