Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 6

Post

Kida a ruwa Book 3 page 6

..... don't smile. Then she raised her hand and touched his face. He grabbed her hand, brought it closer to his lips and kissed it. Before going down, he said, "GOD bless you Maratussaliha. GOD bless you." She just nodded to him with her eyes closed and her eyes were heavy. When they arrived, Mammah started trying to withdraw her hand that was still on his face. He did not see his eyes on her, so he held him again. Then Ja'afar surrounded him full of passion. He raised his head to meet Mammah and Khadijah. He ran to the ground and grabbed Lailah's hand. They and Bilal laughed. Ammar spoke softly in Bilal's ear. "How are you Billa? God bless you. I have been taken away." Bilal gave him a hot kiss on his stomach. He said "Unch!". They all turned to look at him. Ruky let out an unintended laugh. Turning around where she was, he was handing her a hand. She quickly attached the body of Gwaggon Alawiyya. Mammah who was waiting for him said, "Now who is in the hospital bed, are you going to kill Ammar?". "Mamma, laugh at me." "Well, this shout and jump you made should not be laughed at, you should say who the scorpion shot.....

Standalone post1,510 words

6

.........Fitowar doctors ya sanya gaba ɗayansu zabura, Gwaggo Khadijah da Mammah ne kawai basu tashi ba. Doctor ta saki murmushi mai faɗi ganin duk sun zubo mata idanun cike da ƙaguwa. “Alhamdullahi congratulations. Mun samu nasarar ciro Baby girl cikin ƙoshin lafiya”. Wasu irin nauyayan ajiyar zuciya suka shiga saukewa a tare. Yayinda Ma'aruff ya kai duƙe yay sujidar shukur. Dai-dai nan Nurse ɗin dake ɗauke da jaririyar ta fito daga bayan doctor. Hannu biyu Ammar dake kusa da ita ya saka ya amshi Babyn, fuskarsa washe da murmushi ya nufi Mammah. Amma saboda kawaici irin nata sai ta nuna masa Gwaggo Khadijah. Ƙaramar dariya yayi cikin jin kunyar abinda yay ɗin shima ya miƙama Gwaggo Khadijah ɗin... Suna cikin farin cikin kallon Baby aka fito da Lailah da za'a miƙa ɗakin hutu. Ma'aruff ya kai duƙe gaban gadon yana mai kama hannunta. Itama kallonsa take dan idanunta biyu har akayi aka kammala Alhmdllh. Yanda shima ya zuba mata idanunsa da suka rine saboda tashin hankali ya sata sakar masa murmushi. Sai kuma ta ɗaga hannunta takai fuskarsa ta shafa. Hannun nata ya kamo, ya matso da shi a hankali kan lips ɗinsa ya sumbata. Kafin ƙasa-ƙasa ya furta, “ALLAH yay miki albarka Mar'atussaliha. ALLAH ya baki lafiya”. Kai ta jinjina masa kawai cikin lumshe idanunta da sukai mata nauyi. Isowar su Mammah wajen yasa ta fara ƙoƙarin janye hannunta da har yanzu yake akan fuskarsa. Shi ko idanunsa akanta suke bai gansu ba, sai ya sake damƙeshi. Sai da Ja'afar ya zungure shi cike da shaƙiyanci. Ya ɗago da nufin harararsa sukai ido huɗu da Mammah da Gwaggo Khadijah. Ai da gudu yay ƙasa da kansa yana sakarma Lailah hannu. Su Bilal suka gimtse dariya. Ƙasa-ƙasa Ammar yay magana a kunnen Bilal. “Yaya Billa muma dai ALLAH ya aurar damu. Dan gaskiya an tafi da ni”. Mintsini mai zafi Bilal ya sakar masa ya gefen ciki. Ya ce “Unch!”. Duk juyowa sukai suna kallonsa. Ruky ta saki dariya batare da tayi niyya ba. Juyawa yay inda take yana kai mata rankwashi. Da sauri ta maƙale jikin Gwaggon Alawiyya. Mammah dake harararsa ta ce, “Yanzu wadda ke gadon asibiti zaka daka Ammar?”. “Mammah dariya fa tamin”. “To wannan ihun da tsallen daka buga ba dole tai dariya ba, sai kace wanda kunama ta harba”. Caraf Ruky ta ce, “Mammah mintsini ya sha wajen Uncle Billa, wai aure yake so dan ALLAH a gaggauta a masa kada ya.....” Da bala'in sauri Ammar ya waro idanu waje jin harda sharri ta ƙara masa. Bilal ya kwashe da dariya. Dan gaba ɗaya yanda Ammar ɗin ya daburce har yana damƙo Ruky ya rufe mata baki dole abin ya ta baka dariya. Su kansu su Ja'afar daƙyar suka danne. Ruky nata mutsu-mutsun san ƙwacewa yaƙi sakinta sai da Mammah tace, “Malam sakar min yarinya kada ka cire mata haƙori. Badai aure ba, bari Muhammad yazo za'a maka”. Bashi da zaɓin daya wuce sakin Ruky yabar wajen saboda kunya, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige. A ransa kam ayyanawa yake sai yayi maganin bakin Ruky. Murmushi kawai su Ma'aruff sukai suna girgiza kawuna. Sai Mu'azz dake ma Ruky gwalo tana harrarsa da gyara hular kanta da Uncle Ammar ya zame tana maƙale da Mammah. An shigar da Lailah dan haka suma suka koma ɗakin jiyyar Ruƙayya aka fara kiran ƴan uwa da abokan arziƙi kuma. Duk da hankalinsu a rarrabe yake akan al'amarin Nimrah, amma an fita daga wata matsalar Alhamdullah. Dan kasancewar jaririyar a hannunsu har yanzu har hirar da yanzu tana nan data hana kowa ɗauka akayi. Atake damuwarsu ta sake dawowa sabuwa. Kowa ya shiga jero addu'oin gareta. Mammah da batace komai ba kuwa layin Dada ta fara ƙoƙarin kira. Sai dai gashi tana ringing amma ba'a ɗaga ba. Bata damu ba dan tasan tunda har ta yanke bai ɗaga ɗin ba yana kan aiki ne........

×××××××××××××××

Vibration ɗin wayarsa dake jikinsa ne ya farko da shi daga ƙaramar sumar da yayi sakamakon azababbiyar bugun zuciyar data riski ƙirjinsa a lokacin da ƙarar fashewar bomb ɗin ta nema tarwatsa dodon kunnensa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya zubama sauran baƙin hayaƙin dake yawo a samaniyar inda suken. Sai kuma tarin sauran sojoji daya karaɗe wajen da ƙananun hayaniya... “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Imran...” Kalma ta farko data sakashi tashi a razane. Bai damu da ƙasar data wanke jikinsa ba. Ya kai dubansa inda ake kiran Imran ɗin. Ganin Faro ya ɗago shi fuskarsa wanke da jini ya saka duniyarsa sake girgizawa. Baima san ya miƙe kan ƙafafunsa ya nufi inda suke ba. A lokacin su ma su Yusuf suka iso da gudu ɗauke da ɗan gadon bada taimakon gaggawa. Dada ji yake kamar kansa zai tarwatse. Dan yana isowa daga can wani soja cikin ƙaraji ya furta, “Bomb ɗin nan ya tashi da yarinyar nan f....” Ai baima ƙarasa ba duhu ya mamaye idanun Dada. Kawai yaci tuntuɓe da Faro zai zube sai da aka riƙoshi. Dole Faro ya sakar musu Imran ya miƙe yana kama Dada. Zaunar da shi yayi, tare da amsar gorar ruwan da wani soja ya kawo ya ɓalle murfin ya saka masa a baki. Hannu yasa zai ture Faro yay saurin dakatar da shi... “Dan ALLAH kasha ko kaɗan”. Kurɓa ɗaya yayi ya kauda kansa. Faro zai sake magana wani soja ya katse hakan ta hanyar ƙwala kira, “Sirs!!!!!”. Ai a tare suka zabura. Sojoji sukai wajen da gudu. Dole Faro ya miƙe shima. Sai kawai Dada ya miƙe cikin ƙoƙarin danne firgicinsa shima ya nufesu. Yayinda motar data ɗauki Imran tabar wajen dan nufar asibiti da shi... “Bata mutu ba!”. Furucin daya nema sakashi amayo zuciyarsa ta baki. Tuni ya fasa sojojin ya shiga. Caraf ta riƙe sojan dake ƙoƙarin kai hannu kan Nimrah dake kwance ƙasa ta buleta har ba'a ganinta da ƙyau. Sojan zai yi magana Faro ya ce, “Leave...” Dole yaja jikinsa baya. Dada yakai duƙe wajen yana saka hannayesa ya zarota gaba ɗayanta, bai damu da ƙasar dake jikinta ba ya sakata a nashi jikin kawai ya rungume yana sauke wani irin bahagon wahallen jerarrun ajiyar zuciya. Ganin haka Faro yama sojojin umarnin barin wajen domin bincika ya akai haka. Dan bomb ɗin daya tashi dai na jikinta ne. Wanda Imran ya taka yayi nasarar danna masa dutsi a dai-dai lokacin da na jikin nata ke fashewa, shi kuma Imran ya ɗaga ƙafarsa saboda razanin tunanin wanda ya taka ne, shine sukai tsalle gefe kan Imran ya daki dutsin....

“Tabbas yarinyar nan nada wayo, dan sai dai idan cire rigar nan tai tayi jifa da ita Sir”. Sosai Faro ke jin gamsuwa da abinda sojan ke faɗa. Haka ma sauran sojojin dan sun gama dube-duben su da aune-aune. Kuma gaba ɗaya alama ta nuna musu a sama Bomb ɗin ya tashi musamman yanda yay nesa da inda suke. Sannan itama aka cillata gefe ƙasa ta rufeta. Dada dake ƙoƙarin sake zubama Nimrah ruwa a fuska da Yusuf ke zuba masa a hannu duk yana saurarensu. Sai dai hankalinsa ba'a kansu yake ba. Zubawa ta uku babu alamar zata farfaɗo. Ga masu son bata taimakon gaggawa yaƙi basu dama. Ya zuba mata na huɗu yana ɗan bubbuga kumatunta wani ya yunƙuro zai yi maganar kodai a wuce da ita asibiti kawai saita wani irin banƙare, da sauri ya riƙota da ƙyau ya matse a jikinsa. Wata razananniyar ƙara ta saki mai firgitarwa tana fisga zata fita a jikin nashi gaba ɗaya. Da yake ƙarfin ba ɗaya ba dannawa ɗaya ya maida ita. Dole hankalin su Faro ya dawo wajen gaba ɗaya, cikin sauri aka kawo mota wajen, dan dole a wuce da ita asibiti da gaggawa....

©©©©©©©©©©©

“Done Oga. Komai yazo hannu”. Wani murmushin ƙasaita Oga Jush ya saki yana kallon Viper. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar yazo gareshi. Matsawa yay suka rungume juna. “Proud of you darling”. Oga Jush ya faɗa yana bubbuga bayan Viper. Matuƙar farin ciki Viper ya ƙara jinsa a ciki. Ya rissina cike da girmamawa shima ya ce, “Proud of you too Sir”. Oga Jush yay murmushi mai faɗi yana jinjina masa kai da lumshe idanu. Kafin ya gyara zama da faɗin, “Yarinyar fa?”. “Gaskiya tana da wayo, ta kuɓuta. Amma kaɗan ya rage a samu matsala”. “Hakan na nufin zatai mana abinda muke buƙata sosai ai”. “Tabbas zata iya, sai dai Oga data mutu fa?”. “Dama ɗayan biyu ne tsarin ai, kota mutu a wannan gaɓar ubanta ya ƙarasa aikin, shi kuma mu gigita duniyarsa da rashinta. Kota tsira tayi mana aikin. Kaga tunda ta tsira ƴar sa'a ce kenan.” “Gaskiya ƴar sa'a ce kam Sir. Abinda ma zai saka ka farin ciki shine, duk abinda muka nuna mata tayi na'am da shi, damma bata san waye ke aureta nata ba”. “Wannan ai shine babban makamin mu a kanta, shiyyasa nace kada ku faɗa mata waye mijin, taje ta bincika da kanta. Yaya batun yaran?”. “Duk sun bamu haɗin kai. Sannan da yawansu ta tuna fuskokinsu”. “Good. Sai mu je Batch B. A sanar da kowa akwai meeting gobe da safe.” “Okay Sir”...........✍️