
Post
Kida a ruwa Book 3 page 49
.....silence in the body of his younger brother. From Bilal to Ammar, the eyes were closed as if they were about to cry. Barema and Mammah answered with her own. Her son and all of them joined together and he was the father himself. In the end, she closed with a prayer and dismissed them as the night began to fall. They all straightened up, except for him, like Dada, he didn't move. They left him in Mammah's room. It's interesting how they accompanied Jaafar in their time, history repeats itself today. Together, the four of them started to accompany Bilal to his department. They found Asma'u lying in the living room and she cried until she thanked the Lord for taking her to sleep in the long chair, after stopping the medicine that Lailah had brought her. Bilal was going to wake her up and Ma'aruff stopped him, and then unfortunately she woke up on her own. At first she was scared, then Bilal held her and told her to calm down. Full of respect, she sits on the carpet and greets them, giving them all the status of Uncles. Even Bilal calls him Uncle Villah most of the time. They are also big here, especially Ja'afar and Ma'aruff. After that, they once again restrained themselves and b
49
........Yanda Ammar da Bilal keta sunne kawuna ya saka Dada sake kamewa kamar bai fahimci halin da suke ciki ba. Koda suka gaishe shi maimakon amsawa kai ya jinjina musu yana amsar shayin da Aunty Mimi ta kawo masa. Sai kuma ga su Ma'aruff sun shigo suma. Ganin Dadan a ciki suma suka nutsu daga shaƙiyancin da suka shigo sunayi akan Bilal da Ammar. Mammah suka gaida sannan shima Dada suka gaishe shi. Suma dai kan nasa ya gyaɗa musu kawai yana cigaba da shan shayinsa. Bai kuma bi takansu ba sai da ya kammala sha tas, amma yana lure da gulmar da su Ja'afar keyi da ido. Gyaran murya da yayi ya saka su sake nutsuwa suka fuskance shi. Ya fara da addu'a tun daga kan kakanninsu zuwa iyaye da su kansu. Sannan ya ɗora da nasiha ga Bilal da Ammar wadda hatta su kansu su Ma'aruff ɗin shigar su take. Daga ƙarshe ya rufe da gargaɗi mai tsauri akan sauke hakkokin matansu da tunatar dasu sakamakon da azzalumin maza ke iya samu akan hakkokin iyalansu. Tabbas saƙon Dada ya isa inda ake so, kuma ya tasirantu a jikin ƙannen nasa. Dan daga Bilal har Ammar idanun sun kaɗe kamar masu shirin yin kuka. Barema da Mammah ta amshe da nata itama. Dan ita su dukansu ta haɗe tai mawa yanda har shi Dadan kansa. Daga ƙarshe ta rufe da addu'a ta sallamesu dan dare ya fara yi. Duk miƙewa sukai, sai dai shi kam Dada bai motsa ba anan ɗakin Mammah ɗin suka barshi. Abin sha'awa yanda suka raka su Ja'afar a lokacinsu yau ma tarihi ya maimaita kansa. A tare su huɗun suka fara raka Bilal sashensa. Sun sami Asma'u kwance a falo taci kuka har ta godema UBANGIJI barci ya ɗauketa a doguwar kujera, bayan tasha maganin da Lailah ta kawo mata. Bilal zai tashe ta su Ma'aruff suka hana shi, sai kuma akai rashin sa'a ta farka ma da kanta. Da farko ma sai taji tsoro, sai da Bilal ɗin ya riƙeta tare da sanar mata sune ta sauke ajiyar zuciya. Cike da girmamawa ta zamo ƙasan carpet tana gaishe su, dan duk matsayin Uncles take basu. Hatta Bilal ɗin Uncle Villah take kiransa a mafi yawan lokuta. Anan suma dai manya ne, musamman Ja'afar da Ma'aruff. Dan haka suka sake kame kansu suka fara mata da faɗa sannan aka ɗora da nasiha. Daga ƙarshe suka rufe da addu'a. Sun fito sun baro Asma'u na faman kuka. Suna gama ficewa Bilal ya zamo a kujerar shima inda take. Bai ce mata komai ba ya kamota kawai ya rungume a jikinsa tsam-tsam. Cike da tsantsar kulawa da ƙaunarta dake murmushe masa zuciya ya furta. “Kina son na tayaki kukan ne Asmah?”. Kanta dake kwance a ƙirjinsa ta girgiza masa alamar a'a. Ya shafa kanta yana murmurshin ƙarfin hali. “To dan ALLAH ki bari kinji. Kefa kin baro gida ne kin zo gida kuma. Ƴar gatan amarya kenan Uhyimm”. Ya ƙare maganar yana hura mata iska cikin kunne data sakata ƙanƙameshi tsam illahirin jikinta na yamutsawa. Shima ya cije lips ɗinsa da ƙarfi yana sauke ajiyar zuciya da lumshe idanunsa. Ji yake tamkar ya tsaga jikinsa ya turata a ciki ko zai huta da ƙaunar da yake mata daga ALLAH. Sun jima a haka shiru kafin da ƙyar ya iya buɗe shaƙaƙƙiyar muryarsa ya raɗa mata a cikin kunne. “Asmah ina jin yunwa”. Karo na farko ta ɗan ɗago ta kallesa. Ganin ita yake kallo shima ga idanunsa sunyi wani masifar canjawa daga yanda ta sansu ya sata maida kan nata jikinsa. Sai kuma ta fara ƙoƙarin zame jikin nata muryarta a shaƙe saboda kukan data sha ta ce, “Aunty Shariffa ta kawo abinci”. Bai hanata barin jikin nasa ba, sai dai ya kasa daina kallonta. Ga ƙamshin turarenta da gaba ɗaya ya gama saukar masa da kasala. Ita dai tayi dauriyar dakewa ta koma inda kular abincin suke ta buɗe, sai dai maimakon abinci gasashen nama taci karo da shi na haɗaɗɗun ƴan shilar tantabaru a kula ɗaya. Ɗayar kuma jan nama da akaima wani kalar gashi mai saka maye lashe jariri ko bai shirya ba. Aiko duk da halin da take ciki sai da taji cikinta na ƙugin yunwa. Ta dai daure ta jiyo gareshi tana tambayar wanne za'a zuba masa?. “Duk abinda kika bani zanci Baby”. Ya faɗa cikin wata kalar kasalalliyar murya yana lumshe idanu kamar wanda yasha yayi marisa. Da sauri ta janye idanunta kuwa daga kallonsa tana jinjina masa kai kawai. Sai ma ta ɗauki tray ɗin abincin gaba ɗaya ta dawo gaban nashi da shi......
★::::::::::::::::::::::::::★
Gaba ɗaya Biebah ta gama daburcewa. Dan gaba ɗaya Yaya Haydar ɗin ya juye mata wata kala daban data bambanta shi da Haydar ɗin data sani a baya. Tun tana ƙoƙarin son amshe kanta a hannunsa harta haƙura dan ta tabbatar wargi ma waje yaka samu. Waɗan nan mazan kuma fa ba mazan wasan yara bane. Sai da ya tabbatar ya gama ruɗata da salonsa sannan ya janye lips ɗinsa daga nata. Ƙoƙarin rabata da jikin nashi yake taƙi yarda. Yanda tai masifar shige masa ya sashi yin murmushi, dan ya tabbatar a yanda take ne bata son ya gani, gashi dama fitilar ɗakin a kunne take. A cikin kunne ya raɗa mata, “Haba Autar Mammah, baƙya tausayin Yayanki? Ki bari na ganki Please”. Kafaɗa ta kanne masa tana sake ƙanƙamesa. Yay ƴar dariya mai ƙaramin sauti. “To yanzu ya kike son ayi?”. Da shaƙaƙƙiyar muryarta da taci kuka ta more ta ce, “A kashe hasken ni dai”. “Saboda mi to? Wannan fa Aliyu Haydar ne sak a gaban Matarsa Habibah ba Yaya Haydar a gaban Biebah ba, ko kin manta”. Ta ce, “A'a”. “To miyasa baki son na ganki?”. “Ina jin kunya”. “Kunya kawai?”. Kanta ta jinjina masa. Yay murmushi da sumbatar tsinin hancinta. Cikin ƙara shanye muryarsa ya ce, “Shi ke nan zan baki maganin kunyar nan kawai yau ɗin nan Autar Dada. Are you ready?”. Da sauri ta girgiza kai alamar (No). “Why?”. Ta kasa bashi amsa. Ya sake raɗa mata, “Bazaki faɗa min ba?”. Nan ma tai shiru. Sai dai yanda ƙirjinta ke bugawa har yana iya jin sautinsa. Sai kawai ya kai hannu ya kashe hasken gaba ɗaya yana mai sake matseta da faɗin, “Matsoraciyar amarya”. Ta buɗe baki zatai magana kawai ya rufe shi ruff. Daga haka salon ya canja daga matakin farko zuwa na biyu daya tabbatar mata a yanzu babu sassauci balle samun rangwame a hannun wannan zakin nata da jarumtarsa take a bayyane ga duk mai kallo.....
✨★✨★✨★✨★✨
Kamar yanda Bilal ya samu rakkiya sashensa haka Ammar auta ya samu daga yayunsa biyu da suka saka shi a tsakiya. Sai dai me? ita wannan amaryar a maimakon su sameta kamar kowace amarya tana kuka zaune suka sameta tana charting. Ba kuma da kowa take charting ɗin ba sai ƴar uwar tagwaicinta Nimrah. A kuma nata shirme tana zaman jiran dawowar Aunty Mommy ne da tace mata karta sake ta fito ta jirata zata dawo su koma sashen Mammah baƙi za'ayi shiyyasa aka kawota nan ta zauna itama Nimrah aka kaita can. Daga Nimrah har Ruƙayya bawai basu da hankali bane ko wayo, sarai suna gane komai suna kuma fahimtar komai dan kuwa a cikar ƴammata dai zuwa yanzu shekara sha bakwai sun kai. Sai dai sun sakankance auren da akai musu bazasu tare ba sai sun kammala jami'a kamar Small Mom ne. Yanzu koda akai biki zasu cigaba da zamansu sashen Mammah musamman da sukaga ba'a ɗakko musu kayansu ko ɗaya ba daga can. Dan ɗakinsu na'a yanda yake har zuwa yanzu da aka rabosu da shi. Dan haka babu damuwar komai a tare da su sai ma gulmar Asma'u suke yi ta charting ɗin da su Ja'afar suka shigo suka samu tanayi. Shigowar tasu ya sata turama Nimrah typing ɗin da tai akan tazo taji wata magana. Ba ƙaramar dariya abin ya bama Ja'afar da Ma'aruff ba. Ana samun amarya cikin lulluɓi da kuka ita wannan sai a hankali. Sun san itama ƴar uwar ɗayar hakan take. Da ƙyar suka gimtse, kamar yanda sukai ma Asma'u nasiha da addu'a itama sukai mata, sai a lokacin suka fahimci jikin mata yayi sanyi. Dan da farko ma da suka miƙe zasu tafi catai ita dai su rakata wajen Mammah, tunda ta turama Nimrah saƙo kuma har yanzu bata zo ba. Ma'aruff daya fahimci abin sai da jan ido sai ya harareta. Cikin gargaɗi ya ce, “Bama yanzu ba, ko gobe idan ALLAH ya kaimu naga ƙafarki a waje sai na karyata biyu. Itama Ninah ɗin zamu sameta da safe”. Ƙwal-ƙwal idanun Ruky suka cika da hawaye, ta kalla Uncle Ja'afar dan neman ɗauki, amma sai ta samu tsarabar harara anan ɗin ma. Dole tai ƙasa da kai hawayen suka silalo. Dai-dai lokacin suka fice kuma. Hakan yasa Ammar matsowa inda take tsaye gab. Batare da yayi magana ba kawai ya kamota jikinsa ya rungume. Kamar dama hakan take jira ta sakar masa wani uban kuka..........✍️