ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 6
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 6: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 6. *** Wurin karfe tara na safe, ina kwance tun jiya da ya tafi nake jin tashin hankali, ban…
4,450 words
*** Wurin karfe tara na safe, ina kwance tun jiya da ya tafi nake jin tashin hankali, ban kyauta ba sam ina jin haka a raina amma ina tsoron kiranshi kada ya gaya min magana ina tsoron kada ya ce na gama gaya mishi magana zan kira shi na ce mishi me? Wayata ce tayi ƙara na ɗauka a hankali na saka a kunnena. Idanuna a lumshe. "Lubnah baki da labarin abinda ya faru ne?" Jim nayi na san cewa zai bani labarin an kore ni ne don haka na ce mishi." Allah yasa haka shine mafi alkhairi, na gode da haduwa da kai, ka taimaka min sosai shima Ceo ba zan manta alkhairin da ya min ba, yanzu ya ake ciki yaushe samu yi maganar kudin da yake bin family kana tare da shi ne?" Cike da mamaki ya ke kara cewa. "Da alamu baki san abinda ya faru ba kenan? Mr Turaki yayi hatsari har an yi mishi aiki da safe nan!" Wani irin tsoro ne ya kama ni na dafe kirjina kamar zai dirko na ce mishi. "Da yaushe?" Na samu bakina ya furta haka, "Da rana wurin karfe daya zuwa biyu!" Ji nayi kamar zuciyata zata faso fashewa da kuka nayi na ce mishi. "Na shiga uku!" Na fada da karfi ina me kashe wayar domin nasan na ce ni ce sanadin shigar Mr Turaki wannan halin Family dinsa sai sun daure ni, Allah yasa Ya Ado yana gida na fita da gudu zuwa kasa na cigaba da kuka. Allah sarki shi a tunaninsa ma ya zata an gaya min wani abu ne ya faru da Abba, ai kuwa ya riko hannuna da ƙarfi yana faɗin. "Lafiya meye?" "Na kashe shi?!" Na furta tare da rike bakina da karfi, na fashe da wani irin kuka. Na zube a kasa na cigaba da cewa. "Na kashe shi Ya Ado ni ce nayi mishi magana, ni ce na gaya mishi magana, ni ce nayi sanadin hatsatinsa. Wallahi bani da yadda na iya ne, na gaji ne family dinsa ba zasu iya dakatar da shi ba, amma ni sun san dole na nisanta kaina da shi, idan suka san ni ce zasu zo kaina!" Murmushi yayi ya ce min. "Kina sonshi ko?" Cak na ji kukan ya tsaya na kalle shi, "me yasa ka min wannan tambayar?" "Ok shi kenan gara ya mutu kowa ya huta!" Rufe bakina nayi na shiga girgiza mishi kai. "Eh kai meye amfanin saninki da yayi a rayuwarshi tunda bakya sonshi?" Anan yayi ta zazzaga min magana da fada wanda ya sa naji kaina kamar zai fashe na ce mishi da karfi. "Waye ya ce maka bana sonshi?" Sai kuma nayi shiru, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina, na cigaba da kuka. "Kina sonshi?" Gyada mishi kai nayi ina kuka. "Da gaske kina sonshi ba wahala zaki bashi ba ne?" Cikin shashekar kuka na ce mishi." Ina tsoron kada ya min rayuwar Ya Hafiz ne amma wallahi ina sonshi don Allah Ya Ado kada ya mutu!" " Shi kenan daina kuka in sha Allah ba zai mutu ba!"
Haka yayi ta rarrashina don nayi shiru ya kira Uncle Auta, ya tambaye shi ya gaya mishi. " Ok zamu zo asibitin ni da Lubnah." Yana gama wayar ya ce min. " Je ki shirya amma ki sani kasa ki sake ki yi wani magana idan muka je." Gyada kai nayi haka na haura sama, na shirya sannan na sauko, muka tafi asibitin hankalina a mugun tashe, a lokacin da muka isa iya mazan familyn ne a bakin kofar sai kakanshi. Wani irin kuka ne ya zo min, haka na isa na gaishe su kafin na isa bakin kofar da kana iya hango shi kwance. Komawa daya daga cikin kujeran wajen nayi na zauna tare da fashewa da kuka, Kakanshi kallona yake yana murmushi ya ga yadda na daura hannu na kaina ina kuka, Ya Ado ya ce min. "Tashi ki koma gida, tunda bakya jin magana!" Hadiye kukan nayi hawaye na zuba, "kina tsoron kada ya mutu ko?" Kallon kakanshi nayi da yayi maganar. "Me yasa kika zo bayan kin ce bakya sonshi?" Wani irin bugawa zuciyata tayi, "sun miki barazanar zasu miki wani abu ne ko?" Hawaye ne ya shiga zuba min. "Lubabatu Bilal yana sonki tun baki zama mutum ba, yana sonki tun da ranar da ya daura idanun akanki, Bilal kowa shakkarsa yake amma ke din kece rauninsa. Yana iya yiwa kowa tawaye har da ni kaina amma ke ya kasa sarrafa kanshi akanki, gani yake idan ya fito ta kowani fuska ya ce yana bukatarki zaku iya zarginsa da cewa ba don Allah yake sonki ba, Lubabatu Bilal ba kashin yadawa bane, yana da kudin da zai aure ki da karfin tsiya amma yana son ya ji da bakinki kina bukatar shi a rayuwarsa. Idan wani ya kara kiranki ya miki barazana akan Bilal ki gaya min kotu ce zata raba mu, amma ke idan kika cutar da Bilal Allah ne kaɗai zai mana hisabi, yana sonki yana kaunarki, yana tausayinki yana jin ciwon halin da kike ciki, yasan idan ya takura dayawa zaki fama ciwonki yasa yake nan a tare da ke, baki yi mamaki yadda kome naki yake tsaye a cikinsa ba, ga Bilal nan a karo na biyu idan ya mutu mun yi asara amma samun namijin da zai tsaya miki a matsayin namiji kuma bango ni dai nasan me na haifa, mahaifinsa kuma yasan me ya bar min, Ubansa a tsaye yake akan kome haka shima yake, shi din zagi ne a waje amma gabanki kamar dan tsako ne, ki yiwa zuciyarki adalci tana buƙatarshi amma tsoronki zai kai ki ya baro. Ki yiwa kanki adalci yana bukatarki, mu kuma muna bukatarshi." Yadda dattijon yake min magana da adalci yasa zuciyata ta bude hankalina ya koma bakiɗaya kanshi. A hankali na mike zuwa kofar dakin, ina kallonshi yadda yake barci a wahale ni ce ma jefa shi cikin wannan yanayin? Ni ce na saka shi a wannan halin? Yanzu nice na saka shi a wannan halin? Ni ce sanadi kenan.Durkusawa nayi kasa ma fashe da kuka, na rasa me yake mun dad'i.." kai ta gida kada itama ta samu wani ciwon?" Haka Ya Ado ya d'aga ni, ya kai ni mota sannan ya koma ban san me ya faru ba, sai dai na ga kyakkyawa farin ciki a tare da shi. Ai kuwa zazzaɓi ya rufe ni.
Yadda nake kukan ya matukar d'aga mishi hankali, har muka isa nasiha yake min, sai da Aunty Zakiyah ta bani magani na samu kaina, zuwa dare kome ya dawo min. Tsoro da kunyar Kakanshi ya hana ni komawa asibitin har sai da ya cika kwana biyar, a lokacin Ya Ado yayi tafiya, lokacin da na je ni da Yaran Ya Ado suka raka ni. Ubaid na samu sai wata yar uwar Babanshi, shi ya tsayar da ni tare da nuna min shi ana wanke mishi ciwon da yake kafad'arshi, mutumin nan akwai taurin rai. Domin ko gizau kai yadda yake latsa laptop zaka tabbatar da cewa shi fa bai san ana yi ba, a hankali na kai hannuna kan kofar, d'ago kai yayi idanunmu ya hadu da juna. Wani haɗe rai yayi kamar bai taɓa dariya ba, kasa da kaina nayi ina jin wani irin kunya. Har matar ta gama dress din ta duba kanshi sannan ta fito daga dakin. Bude kofar Ubaid ya min muka shiga har da ɗan abin tab'awa nayi. Yaran suka isa gare shi ni ina tsaye rike da basket din na kasa motsi haka ya kula yaran har da ciro musu apple da banana, amma ni ko inda nake bai kalla ba, kasa motsi nayi ina kallon kasa. Wani irin tsoro yana kama ni, Yaran yayi ta tambayarsu. Ina tsaye a wurin aka. turo kofar dakin, Yan matan family ɗinsu ne, sai da suka kalle ni kafin suka nufe shi. "Hamma ya jikinka?" Murmushi yayi ya ce musu. "Da sauki sosai?" Badr da ta koma gefenshi kamar zata shige mishi, tayi ya iyayi har da kukanta, ni dai kaina a sunkuye sai wani abin isgilanci suke suna dariya, ina rike da basket din. "Badr hada min ruwan zafi." Da sauri na kalle shi, bai kalli inda nake na, na sunkuyar da kai, haka ta shiga hada mishi sannan ta fito cikin kulawa take gaya mishi ta haɗa,kwalla da haushi ya cika ni, amma wannan ba matsala ba ce da xan nuna akan idanunsu. "Ku bani wuri na shiga wanka." Kafin su fita na riga su fita, koda Yaran suka fito na mikawa Ubaid basket na ce mishi. "Allah ya bashi lafiya zamu tafi!" "Ki tsaya ya fito mana!" Murmushi nayi na girgiza miishi kai na ce. "Ai mun sallama da shi!" Na kama hannun Yaran ina jin wata cikin yan matan tana jefa min magana amma ban kula da batunsu ba, muka bar asibitin. Gobe ma zan dawo jibi ma xan dawo ga ta ma zan dawo sai ya gaya min har sai ya gaya min baya buƙatar ganina a rayuwarsa zan tafi zan koma inda na fito.
Haka da na saka a raina, har muka isa gida. --- Bayan tafiyarsu ya fito idanunsa yana kan kofa, amma kasancewar ya iya takunsa ko irin a fuska ya nuna yana son ganinta bai yi ba, ya cigaba da abinda yake ta yi. Ganin yadda ya masu a gabanta basu san yayi amfani da su bane don ya cusa mata b'acin rai kuma yayi nasara, shigo da basket din, Ubaid yayi yana faɗin. "Ga abinda aka kawo maka." Kallonshi yayi da harshen larabci ya ce mishi. "Ina take?" "Ba kunyi sallama ba?" Murmushi yayi yana daga cikin abinda yake karawa zuciyarshi kaunarta tasan kanta, "zuba min abincin?!" Haka ya shiga zuba mishi abincin, masa ce da miyar koda. A hankali yake ciki da dumi kuwa. "Ka mata bakin hali ko?" Ubaid ya tambaye shi, banza yayi mishi ya cigaba da cin abincin. Yasan idan Ubaid ya san me tayi mishi da kanshi zai ce ya hakura da ita. Amma ya kalli kwanon yadda yake cikin abincin. "Hamma ka hana bazawarar ce zuwa mana? Babu amfanin zuwanta wurin ka." "Wurinki take zuwa? Idan da ke ce kika samu irin darajar da take da shi ai da kin hauka ce." Inji Ubaid, " kallonsu yayi da kyau ya ce mata. "Na san dukkanku nan babu wacce bata taɓa kwanan a waje ba?" Tsuru-tsuru suka yi suna kallonshi. " Ita kuwa saboda tarbiyyar da aka mata, ko hannunta wani namijin bai rike ba sai wancan Tsinannen yaron da ya aure ta. Ina sonta ne don ita din ta cancanci zama uwar Yarana." Murmushi yayi ya ce musu. " Kuna son aure na ne don abinda nake da shi ita kuma tana gudu na ne saboda abinda nake da shi, kada wata rana na kalle ta nace ta aure ni saboda abin duniya da nake da shi ne........ [12/12/2025, 7:52 PM] Maman Walid: 12 " Ku kanku baku da qualified na matan da nake son aura, baku cancanci na aure ku ba. Ita din rabi da kwatan rayuwata ce, duk abinda xan yi mata ina yi ne don ta san ko babu ita xan rayu kuma zan iya rayuwa da wata mace bayan ita, ina son ta san da cewa akwai mata dayawa da suke bina ina gudunsu ba irinku da basu da aikin yi ba. Sai harin abinda ba nasu, kada na kara jin wani ya zage ta ban hana ku zuwa amma wata tayi mata kallon banza zata gamu da ni." Daga haka ya cigaba da abinda yake yi. Domin yayi imani a ransa zata dawo.
*** Tunda na isa gida na ji a raina kamar kada na kara dawowa amma kuma sai na ji ina son na kara komawa domin na ji yadda yake ji, haka na kwana susuku. Washi gari kuwa bayan Aunty Zakiyah ta tafi aiki kasancewar Yara suna hutu na kara shiryawa muka tafi asibitin da safe. Lokacin da naje na samu har su Uncle Auta, gaishe su nayi suka ce na shiga ana mishi dress juyowa nayi zan fita ya cewa Yaran. " Adil! " Kallonshi yayi a tsorace ganin yadda ake wanke mishi gefen cikinsa yana murmushi. Juyowa nayi na kalle shi, shima ni ya kalla ganin yadda na zare idanu ana wanke ciwon, wani irin kallon banza ya min ya mikawa Adil hannu. Ya zo ya rike shi ban san me suke fada ba, amma yaron ya daura kanshi a kafad'arshi, shi kuma yana shafa bayan Adil kama sauran yaran nayi muka fita wani irin tsoro yana kama ni. Zama nayi kamar zan yi kuka, na ce. "Haka ake mishi wankin ashe jiya ban ga kome ba?" Na fada ina shashekar kuka, dariya Uncle Auta yayi yana faɗin. "Kin ga shi da yake haka yake bai san wani emotional ba, shi yasa kika ga idanunsa babu tsoro ko karaya. Kece rauninsa idan da zaki shiga damuwa sai yafi ki shiga damuwa." Murmushi yayi yana kallon yadda nake rike basket din Abincin, hawaye ya shiga zuba min kamar zan cire ciwon a jikinsa na dawo da shi. A hankali na tashi lokacin yana bawa Adil ayaba yana ci tare da nuna mishi dantsen shi. Ina shiga Adil ya fito daga dakin. Kallonshi nayi a hankali na taka zuwa gabanshi jikina a mace, wayarshi ya dauka yana dannawa. Yadda na zauna na ce mishi. "Am sorry!" Mutumin banza yayi kamar baya dakin, nayi ta bashi hakuri, ina kuka amma bai ce min ci kanki bai ce min ba, tashi yayi ya bar ni a dakin na sha kukana sannan na mike tare da barin dakin, kafin ya fito mun bar asibitin.
Haka nayi ta jera zuwa asibitin amma babu abinda yake hada mu, baya ce min uffan. Ranar da na je na karshe aka ce min an sallame shi, sannan aka bani basket din Abincin da nake kaiwa. A kasar basket faɗin takarda ce da dan girma na bude kudi ne dubu dari. Sai yar shot not. *Kada ki nime ni, ki koma wurin Ex dinki! Na yanke alakata da ke har abada* sai na ji abin kamar a mafarki gashi bai ambaci sunan Hafiz balle na ce kishi ne, tow bai ambata ba, sai nayi ji kamar zuciyata ce ta bar gangan jikina, haka na durkusa a wurin, wani azazzaben tsoro ya shige ni mai cike da tashin hankali, sai naji kamar bani da amfani akan kome. Na ji kome na duniyar ya tsaya min cak, tausayin kaina da rayuwata. Haka na kwashe minti goma har aka fara min magana na tashi da kyar na dauki jakata da basket din da wanda na kawo abincin, na tsare abin hawa ina kuka yau.
A can nesa da inda take durkushe Ubaid ya ce mishi. "Wallahi ta tuba kada ka mata haka, hukuncin yayi zafi ka saurare ta." Sunglasses dinsa ya saka ya ce mishi. "Matsalata ce ba taka ba, muje gida." "Gaskiya you too heartless, haba ka ga yadda take tafiya har." "Uncle Auta matata ce kake fasala tafiyarta wallahi zamu samu matsala da kai!" "Allah ya baka lafiya!" Daga haka suka bar asibitin.
Akwai karamin hauka da wanda ya dara soyayya yake, wnada na fahimci cewa ina cikin waɗanda suka haukace ko suka zauce a kan sha'anin zuciya. Bakiɗaya na ji kome ya tsaya min cak. Tunda na dawo gida na gane bani da hankali, sai na ga ashe da ban yi kome ba, domin a daddafe na yi kwana biyu me kyau na uku kuwa sako nayi ta tura mishi both what'sp da Text message, amma babu reply sannan uwa Uba ko zan kare ranar ina kiranshi wayarshi baya shiga, kaina ya kunce bana son fita koda waje, ina nan zaune na rasa meke min dad'i. Haka na kira Mama ina kuka na kasa magana. " Ba kin ce gidan Hafiz zaki koma ba? Tow wata sati na ce Yayanki ya dawo dake gida sai ki ji dadinki. Tunda gidansa kika zab'a amma ki sani ko namarki Hafiz yake yanka yana gasawa wallahi ba abinda ya dame wawuyar banza shi kuma Turaki Allah ya bashi budurwa ba ma ke da wani ya gama da ke ba, ba wani baki da lafiya. Lafiyarki lau iskancin ne kawai da renin hankali mara kunya wacce bata da godiyar Allah." Tayi ya fada kafin ta ce min. "Ki sani tunda Hafiz kika zab'a bani ba ke, ki je kada ki sake ki shiga inda nake na gaya miki."
Zan iya cewa ko abinda nayi Mama da Yayuna basu dauki zafi kamar yadda suka dauka don sai na ji ina tsoron kiran kowa bayan Ya Ado. Shi ɗaya yake saurare na. Bayan ya dawo ya sake min fada da nasiha. "Ya Ado ka ba Mama hakuri tayi hakuri, wallahi ba zan kara ba." "Ya isa haka in sha Allah babu abinda zai faru." Fushi Yayuna mata suka dauka, kusan na rasa inda xan saka raina. Karshe Taj na kira na tambaye shi ko Oga yana gani ya ce min eh yana nan." Don Allah ka zo ka kai ni na gaishe shi." Shiru yayi kafin ya ce min. " Ok zan zo yanzu!" Wata Turkish gown ma saka, sai mayafi da na lallube jikina da nayi da shi, na fita tare da yiwa Yaran sallama na fita bayan na turawa Ya Ado sakon zan fita. Taj ya zo ya dauke ni na ce mishi. " Na gode amma ka taimaka min mu saya mishi fruit! " Tunda na shiga ya ce min." Amma wani ya taba gaya miki kina da kyau? Gaskiya kin haɗu. " Haɗe rai nayi ban kuma magana ba, har muka isa inda na saya mishi fruit, muka nufi gidanshi. Sai magana yake min amma naki amsa mishi. Har muka isa gidan, yana tsayar da motar na saka kai xan fita rike hannuna. " Meye haka ina miki magana kin share ni?" Juyawa nayi na kalle shi, kafin na kalli hannuna. Yadda na mishi wta irin kallo sai da ya ji tsoron sake ni yana cewa." Sorry na jima ina son na gaya miki gaskiya ina sonki!" Murmushi nayi mishi sannan na ce mishi. "You too late, domin ni da CEO muna son juna!" Da wani irin sauri ya cire hannunsa a kan nawa yana faɗin. "Don Allah kada ki bari ya san da wannan zancen wallahi zai iya korana." "Ni ba haka nake ba, amma ka kula sosai kowacce kwarya da abokin burminta." Daga haka na fita a motar, haka na fito dauke da abinda na sayo mishi na nufi cikin gidan. Da sallama yana tsaye jikin window, yana juyowa muka yi ido hudu da shi. Sunkuyar da kai nayi ina wasa da jakan hannuna. Takowa yayi ya wuce ni zuwa upstairs, wani irin abu na ji, ina tsaye sa ga Airah tana saukowa a hankali. Wani irin rufewa idanuna yayi na sunkuyar da kai ina ambaton Allah. Bayan ta fito ta wuce kitchen. Bai sau ko ba ita kuma bata ce min na zauna ba. Haka na cigaba da tsayuwa har zuwa wani lokaci. Ya sauko daga sama sanye da wasu kananan kaya a jikinsa. Idanuna yana kanshi. Na ce mishi. "Ya jikinka?" Kamar bai ji ni ba, ya wuce na ajiye mishi kayan a sama inda yake na ce mishi.." nazo na kara baka hakuri ne!" Sosa kunnensa yayi yana latsa wayarshi, da na cigaba da magana tashi yayi ya riko hannuna ya janyo ni ya kai ni bakin kofar ya ce min.. "kada ki kara zuwa inda nake!" Ya bude min kofar, zuba mishi idanun nayi na ce mishi. "Ba zaka kyale ni haka, ka gaya min ba bukata na ne a rayuwarka ne? Idan ka fada min haka wallahi zan tafi na rantse da Allah zan tafi, ba zan kara zuwa gare ka ba amma idan ka ci-gaba da tureni zan cigaba da zuwa har sai ka gaya min abinda yake ranka." "Zan rufe gidana kin ga yarinyar da zan aura tayi shiru kada ta ji babu dad'i." Haka ya saka na fito, na tsaya a kofar shiga gidan, ina tsaye har danginsa suka zo, babu wnada ya ce min ke uwaki. Ko sun yi maganar ne sai ga Uncle Auta, ya shigo bai shiga ba ya ce min. "Zo muje!" Girgiza kai nayi na ce mishi. "A'a ba zan tafi ba sai ya gaya min me yasa yake ture ni."yayi juyin duniyar nan amma naki binsa Sai da ya shiga sai gashi ya fito. Amsar key yayi ya wuce ni, na tashi na bi bayanshi. Tunda na shiga motar yake waya da harshen Russian, bai fada wayar ba har muka isa gidan, dab zamu shiga kwanar ya mai da wayar video call. Wata har dattijuwar baturiya ce ta ce min. " Labobu;" kallonshi nayi fuskarshi a haɗe, gaishe ta nayi da harshen turanci ta amsa mun jima muna magana tana min tambayoyi ina amsa mata, kafin ta juya cikin taushin murya take rarrashinsa, ban san me take ce mishi ba, naga ya sake mata murmushi. Nima sai na tsinci kaina da murmushi.
Bayan sun gama ya karasa da ni gida. Sai da na zo fita ya ce min. "Ki daina zubar min da mutunci, idan zaki yi haukarki ya tsaya ina nan, kada ki kara zuwa kada ki kara kusantar inda nake idan ba haka ba, zan miki wulakancin da kare ba zai ci ba, wai ke an taɓa yin wa mutum dole ne? Bakida zuciya ne? Kada na kara ganinki a gidana. Idan na kara ganinki nasan me kike nufi da haka!" Ya fara min wani irin kallo irin na yan iska, da sauri na kare kirjina tare da yin baya, ban san lokacin da hawaye ya zubo min. Na ce mishi. "Hakuri nake baka, ni ba yar iska ba ce amma tunda kallon da kake min in sha Allah ba zan kara zuwa ba, idan na kara zuwa ko na kulaka suna na ba Lubabatu ba ce!" Na fita daga motar na barshi a wurin ina kuka domin na fahimci wani irin kallo yake min.
Jan motarshi yana faɗin "Good gurl kada ki kara zuwa ni kika sayawa mutunci. Da gudun tsiya ya bar unguwar ko tunawa da ya yi hatsari baya yi. Lokacin da ya isa gidan damuwarsa biyu ya tirke Taj domin ya ga abinda yayi mata daga window yana daga cikin dalilan da yasa ya mata haka, na biyu abinda ta kawo mishi. Lokacin da ya isa kai tsaye inda ta ajiye mishi leda bag din ya nufa, yadda ya je ya ga babu shi babu dalilinsa ya kwalawa Airah kira tare da tambayarta. Da sauri ta ce mishi.." yanzu Badr ta wurga a wancan gwandon sharan. " Wani irin zare idanu yayi kafin ya ce mata. " Ko Ubanta da Uwarta basu isa na ajiye abu su sauya min wuri ba, ke ubanki ne ya ce ki sauya mishi zama daga inda yake? " Da sauri ta nufi inda ta jefa ta ciro tana faɗin." Kayi hakuri hamma." Kamar zata yi kuka ya ce mata. "Oya je ki wanke ki kawo min, abin Lubnah ko a kashi aka saka zan wanke na ci!" Mahaifiyar Badr ta ce masa. "Allah yasa na asiri ake baka ba." "Ni nake bata kudin da zata kaiwa bokonta domin wallahi ya iya aiki. Domin ta mallake ni." "Allah yasa ba wani abu take wankewa take baka ba ." "Ai yanzu nake son gaya miki ko shi ta bani nake sha, ba matsalar babban matsalata shine yadda ba ayi mana aure nayi da kaina naji abinda masu mata suke ji, idan suna..... (Dan iska 😂🤸🏼♀️🤣) [12/13/2025, 7:26 PM] Maman Walid: 13 Watsa mishi ruwa Ubaid yayi domin kaf a duniya babu kunya cikin lamarinsa, ya kauce ruwan ya watsu a gefenshi. "Kai wani irin mutum ne da bai san ido ba?" Ubaid ya tambaye shi, "ido? Sun aka ace maka sun san idon ne? Matar da nake so zasu gayawa Magana sai nayi shiru saboda ina son su so ta? Kai ji idan suka ce basu sonta ni ina sonta. Zan iya rayuwa da iya ita ba tare da nayi nadama ba, zan kuma iya datse alaka da kowa domin ita, gaya min wani abu nake bukata? Yau suna tare da ni ne domin abinda nake da shi ita kuma tana guduna ne saboda su. Idan da yau babu su babu abinda nake da shi tabbas rayuwata sai tafi haka citta." "Me yasa kake karawa matsalar nan fetur ne?" "Saboda na gaya maka su din basu gaba, idan babu su iya Mujitafa gare ni su basu da abinda zasu ba ni, idan aka ce iya kai ne babu abinda zai saka na kalle su. Su gode ma da nake kula su oya su bar min gida!" "Amma kasan dole matarka ta shiga cikinsu?" Ya fada yana kallon shi ya kara da cewa. " Dole Matarka tasan su din naka ne? " "I fuck su nawa ne, kai dalla su fita min ina da kake magana anan basu ne suka turawa Matarka hotonka da Lunah ba? Ko an gaya maka basu ne suka tura min hotonka da Lunah ba, kai ma kana manta da bala'in mutanen nan su fita kafin na kira Dattijo ya min waje da su." Jin haka yasa bakiɗaya suka mike tare da barin parlourn musamman yadda ya kara da cewa." Damuwarku na auri Yaranku idan suka samu ciki da ni na zama next victim to ba da ni ba! Da naci guba a hannunku gara na mutu a tsaye. Sai kace an taɓa soyayya ko auren dole kun bi kun dame ni. " Suna fita Ubaid ya mishi magana ya d'aga mishi hannu yayi ya ce mishi." Tsaf kafi kowa sanin waye ni Please je ka wurin matarka kada ka dame ni! " Shima ya samu nashi kason, ba musu ya bar gidan, ya kara wanke fruit din da kanshi sannan ya zauna ya fara ci kusan abinda ya ci kenan, fitowar Airah da take jin kome ya watsa mata harara ya ce mata." Ki tattara abinda kika dafa ki je na gode." A rud'e ta ce mishi." Sir me na aikata? " Wani haɗe rai yayi sosai ya ce mata. " Taya xan yi bakuwa tazo gidan nan amma ki ganta ki basar da ita kin san how she meant to me? Da zaki ganta ki share ta don ni na share ta? Daga yau kada ki kara zuwa gidan nan, wannan shine zuwanki na karshe sannan ji gayawa mutanen da suka turo ki ita din rayuwata ce. " Yadda ya mata tas ya kore ta, abin ya bata mamaki domin kuwa yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake bala'in ashe basu shiri Yes tasan basu shiri amma kuma meye na jin haushin kowa?