Kenza eBookz

Al'amarin maryam Complete - Chapter 2

Al'amarin maryam Complete - Chapter 2

Al'amarin maryam Complete Chapter 2: Al'amarin maryam Complete Chapter 2. Mahaifin Maryam su 2 ne a gurin iyayensu wanda suke fulanin gombe usul awani da…

4,452 words

Mahaifin Maryam su 2 ne a gurin iyayensu wanda suke fulanin gombe usul awani da ake kira kaltungo, Baffa Buhari shine babba sai AL AMIN wanda yake shine mahaifin su maryam din tun suna yara qanana iyayensi suka rasu, sun taso agurin dangi har xuwa girmansu Buhari secondary skul kawai ya gama ya tsunduma kasuwanci da yake anbar musu gadon dukiya sosai, dakadan dakadan kasuwancinsa ya bunqasa har ya kasance maxaunin Kano State saboda itane cibiyar kasuwancin arewancin qasarnan. Yana kasuwancinsa a kasuwar singa na sai da kayan abinci da kayan masarufi, da quruciyarsa sosai yayi aure saboda kudi da yake dashi, ya auri matarsa Hajara (umma) kamar yadda yayanta ke kiranta.

AL amin kuma yafi maida hankali a karatu, duk da yayan nasa yaso kwarai ya tsundumashi harkar kasuwanci ya dunga gocewa har daga baya ya fahimci bayaso ya qyaleshi .

Yayi karatunsa na Law anan ABU zaria ya kammala yaje Law skul dake Lagos ya dawo. AL amin matashin saurayi fari tas kyakykyawan gaske kamar yayan nasa Buhari. Ya dawo xaman gida a inda umma hajara ta dunga yimasa cushen qanwarta husna wadda take gidan a lokacin tana yiwa Umma xaman dabaro a dalilin haihuwar da tayi, tun be ganeba har ya fuskanta hakan yasa ya dena shigowa cikin gidan sosai indai ba kamawa tayi doleba duk abunda xaiyi yana yi ne iyakar shagonsa dake qofar gidan. Saboda sam husna batai masa badan bata da kyau ba sai dan bata cikin jinsin matan dake burgeshi .

Ta bangaren mahaifiya kuma asalin mahaifiyar su MARYAM bafulatanar ce domin iyayenta fulanin garko ne ta jihar Kano, su 9 mahaifiyarsu mai suna MARYAM (hajia) ta haifa da babansu mal SULAIMAN guda 7 maza kuma sune manya sai Adda halima sannan Fadima wato mahaifiyar su MARYAM itace kuma auta mazaunan unguwar tudun maliki.

Fadima ta gamu da iftila'in rayuwa tun tana yar shekara 7 wani Mara imanin wanda ba asan ko wanene ba Yayi Maya fyade (rape) yayi mata kaca kaca wanda hakan ya jawo mata baqin jini a lokacin yan matancinta dan kaf saida akaiwa sa anninta aure amma ita babu labari har ta shekara 14 (kasancewar ba makarantar boko sukeba, dan mal sulaiman yayansa maza kawai ya yadda suyi ilimin boko ) a zamanin budurwa mai shekaru 14 babbar budurwace sosai kuma da kunya a ganka da yarka a wancan lkcin mai wannan shekaru babu aure, duk wanda ya fito neman aurenta sai yan unguwa su tareshi su fada masa abunda ya faru kanta, daga haka har aka dena xuwa gaba daya. Ba tare da shawarar kowa ba Mal Suleiman ya dauki auran fadima ya bawa wani abokinsa direban babbar motar haya (Wanda yake sana arsu daya shima matuqin mota ne) mazaunin qauyen maberaya ta jihar sokoto a wancan lokacin a yanxu kuma zamfara. Saboda xaman fadima haka ya dameshi kwarai, yayiwa Mal Ali bayanin abunda ya faru a kan fadima shi kuma yace yaji ya gani ba komai aishi Me rufa masa asirine.

Lokacin da yaxo da maganar aurar da fadima ga Mal Ali hajia ta shiga mugun tashin hankali ita da yan uwan fadiman karma Adda halima taji lbr domin tana mugun San fadima, amma dole sukai haquri saboda sanin halin ubansu mafadacin gaskene.

Haka akai biki aka kai fadima gidan Mal Ali dake maberaya, gidan gandu bayan matansa 2 da yaya 17 harya aurar da wasu ma, ga kuma tagowar yan uwansa dake cikin gidan. Haka dai suka baro fadima uwa ta mutu saboda tunda akai maganar aurenta da Mal Ali ta koma wata iri kamar mai tabin hankali, suka rabu suna kuka ita kuma tana binsu da ido kamar zararriya.

Saida ta kwana 2 bataga angon nata ba, anabata abinci agidan irin cimar mutanen qauye wanda ganin bataci suka dena kai mata dan yanda aka kai haka aka dakkoshi, dan abun motsa baki da kayan fulawa na kayan garar da aka kawota dashine takeci, bata fitowa sai xata bandaki wanda take mugun kyama domin ko wanka takasayi a ciki. Arana ta ukun ne ta fito ta wanke bayin cike da tashin xuciya saboda jikinta ya dameta da ciwo tana buqatar wanka tayi wankan tafito tarar da mutan gidan sun cika tsakar gida da daurin qirji suna ganinta aka hau dariya da habaici ko kallo basu ishetaba ta shige dakinta.

A daren ne kuma mijin ya shigo dakinta tare da kazarsa ta amarci, alkcin yake fada mata wai tafiya yayi kudu dakko kaya shiyasa taji shiru amma gashi ya dawo suci amarci 😂. Duk yadda yakai da sweet mouth (dadin baki) fadima taqi amince masa, ya haqura ya kyaleta har kwanakin girkinta suka qare ya bar dakin, girki ya kuma dawowa kanta ya dawo dakin da sam cimma burinsa saboda ya kwaditu kwarai da fadima kyakykyawar mace jajur da ita ga quruciya, koda taqi yarda dashi yaso kwada mata qarfi ta saka masa ihu dole ya haqura ya kyaleta saboda gidan yawa suke ga yayansa da jikoki cikin gida da kunya aji tanai masa Ihu.

Saida aka shafe wata biyu cur a haka xaman gidan sam ya gundureta kwarai, duk sanda ta fito tsakar gidan da nufin yin wani abu zata tadda cincurundun matan gidan a gidin bishiya suna ganinta xa a ce " ritayar birni sai qauye ga gwallin ga shafe shafen amma anrasa miji a birni sai a qauye " sai a tafa a kwashe da dariyar cike da shaqiyanci irin na shegun qauye (shegu qauyawa 😂😂😂) . Duk da tana dakewa ta nuna bata gane da ita sukeba amma abun yana damunta. A bangaren mijin ma dangantaka tsakaninsu tayi tsami, saboda taqi yarda dashi ya dena bata dan kudin kashewa da yake bata da kuma lallabawar da yake mata shima tsakaninsu sai hantara aganinsa hakan zaisa da yadda dashi. Tayi baqi ta rame ta fita hayyacinta duk ta koma kalar yan can.

Ana cikin hakan girki yaxo kanta kuma a daren ya nuna zulamarsa akanta wanda hakan yasa ta dunga kurma ihu har mutan gidan suka tashi suka firfito tsakar gida, kunya ta hanashi fita baqin ciki yasa ya jawo wayar radio ya dunga tsula mata yana kwallo da ita har sai da yaji ya huce ya kyaleta. Anatada sallar asuba a masallaci ya fita itama ta tashi tasa hijabinta tasa takalma ta fita, lokacin data isa tasha gari ya fara shaaa, tashiga motar Kano bata da ko sisi tayiwa direban motar bayani bata da kudi amma insinje Kano zata bashi ya kaita har gida yayi shiru yana kallonta can yace ke yar Mal manu ce? Naga Kama, tai saurin cewa eh ni yarsa ce fadima yace to lfy naganki haka kuma anan? Tai shiru sannan yace bakomi mun taba aikin mota tare dashi ashe yata ce muje ba komi har gida xan kaiki. Kafin motar ta cika ya sai mata shayi da bread Shayin kawai ta iya sha tana Allah Allah motar ta cika sutafi dan gani take kamr Mal Ali xai biyo bayanta. Da haka motar ta cika suka daga.

Mrs Muhammad 😊

🙆🏼🙆🏼🙆🏼AL 'AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼 8⃣ Azahar a cikin gidansu tai mata direban motar daya kawota ne yayiwa Mal sulaiman halin da ya ganta aciki, yayi masa godiya ya shiga da fadiman cikin gida. Ransa ya baci kwarai da yaga kwanciyar bulala ajikin ta kota ina, haka aka dunga biqinta har ta warke yayyunta maza sukace aure anyi angama. Sai dai har fadima ta share 3wks a gidan Mal Ali bai nemeta ba, hakan yasa Mal sulaiman ya nemshi cikin xafin rai yanuna masa bacin ransa kan abunda yayiwa fadima, shima Mal Ali cikin nasa xafin ran ya balbale Mal sulaiman da nasa fadan tare da cewa yar tasa ragowar wani da bata da mutunci yaje ya saketa. Jikin Mal sulaiman yayi sanyi kwarai ya tara yan uwan fadima ya fada musu kuma ya nemi yafiyarta. Dama duniya makarantace Wannan avun shiya koyawa Mal sulaimn hankali ya lura cewa bada fadima sadaka bashine mafitaba gara yayi haquri har Allah ya kawo mata wanda xai sota a yanda take. Saboda haka ya bawa yan uwanta damar da suka dade suna nema a kanta, suka sakata a makatanta library ta fara xuwa inta tashi ta shiga ajin koyar sana a dinki da saqa.

Bayan shekaru 2 fadima ta goge sosai kasancewar ansakar mata mara tana fitsari babu takura, ta goge ta cika ta xama cikakkiyar mace tuni ta kware akan dinki takan dan taba saqa amma tafi maida hankali akan dinki, ta bangaren karatu kuma ta kusa kammala primary.

A na cikin hakan suka hadu da AL amin a lokacin yana service (bautar qasa) ta dawo daga skul suka hadu ahanya ya bita har gida, Sun fara soyayya ya mace akan kyakykyawa fadimatu itama tana qaunar Guy din amma tana dari dari saboda kar yaji abunda ke tare da ita, saboda haka ta kwashe komai ta fada masa kafin asamu wani daga waje ya fada masa. Ga mamakinta saiya tausaya mata tare da bata tabbacin wannan bazai rabasu ba,

Bayan dogon dauki ba dadi da kai ruwa rana da aka samu ta bangaren AL amin. Saboda a cewar Baffa Buhari bazai auri bazawara ba sai dai ya samo wata tunda yace bayason husna qanwar hajara, shi kuma AL amin din ya kafe yace ita yakeso, duk da Baffa ba ra ayinsa bane, zugar hajara ce kawai ke aiki dashi kasancewarsa namiji mai daukar xuga, shidai kawai ya tsani fadima tun kafin ya ganta saboda yanda yaga Dan uwansa na qaunarta , wannan ra ayi nasa ya hadu da xugar hajara ya jawowa fadima tsana sosai a gurinsa, a bangaren hajara kuma ji take kamar ta kashe fadima tun kafin ta ganta, gashi alokacin anmata kishiya wato Anty jamila abun ya hadu yayi mata yawa. A karshe dai Allah yayi ikonsa domin AL amin da Fadima sun kasance ma aurata.

Ta haifi yarta fari Mace ya maida sunan matarsa, wanda hakan ya kuma janyowa fadima qiyayya a gurin Baffa da matansa, saboda hajara tayi masa famfo cewa kamata yayi AL amin din yasa sunan mahaifiyarsu amma yasa sunan shegiyar matarsa. Xuwa wannan tym din gidan Baffa ya fara cika da yaya kuma arxiqinsa ya bunqasa kwarai da gaske ya gina qaton gida me part 4( gidan da suke ciki yanxu) gida me kyan gaske ginin irin wancan xamanin da daku 2 asoro na mazan gidan da seat room daga waje da rila xagaye da gidan. Tun lokacin da aka auro fadima ta tadda yara 7 a gidan 5 na hajara 2 na jamila, daga baya suka fara competition din haihuwa, a inda nan da nan suka cika gidan da yaya maza da mata amma matan sunfi yawa.

AL amin yasamu aiki a tun farkon aurensu a inda yasamu aiki a jamiar da yayi karatu wato ABU kuma yana ci gaba da karatunsa, agefe kuma yana taba aiki a wata chamber kasancewarsa lawyer, suna zaune a unguwar sharada fadima ma tana cigaba da karatunta AL amin ya tsaya mata da kansa inyana gari yakan koyar da ita, ga kuma sana arta ta dinki tanayi.

Bayan shekaru 5 da haihuwar Faty ta haifi MARYAM taci sunan mahaifiyar fadima kenan suke kiranta (Mimi). AL amin ya kasance mutum mai mutuqar San iyalinsa yanasan yayansa kwarai, yakance in Allah ya yarda Faty ma aikaciyar jinya (nurse) Mimi kuma yakance shixata gada wato lawyer, in ya fadi haka fadima kance Allah ya rayaka Barrister ya kuma yara maka sister Faty da Barrister Mimi . Yakance amin amin fadimatu.

Mimi nada 4yrs ya jefata a skul sai dai ita sabanin yar uwarta miskilace kuma mai yawan lalura da fari Sun sikila ce sai da suka je asibiti sukaji sabanin haka domin bincike ya tabbar da A S ce, kawai dai Allah ya halicceta me lalura. Alokacin kuma fadima takuma samun wani cikin, cikinta na wata 6, Allah ya dauki ran AL amin a dalilin hatsari da yayi a hanyarsa ta koma Zaria gurin da yake aiki, mutuwar ta girgiza fadima da Baffa Buhari kwarai da gaske a dalilin mutuwar fadima tai haihu lokacin haihuwar beyiba ta haifi jariri dan wata 6 babu rai. Bayan 40 Baffa ya buqaci a bashi yayan AL amin, da farko fadima da danginta sunqi amma daya kafe cewa dole ta bashi domin baza a tafi da yayan dan uwansa wani gidan ba da sunan aure.babu kunya da lokacin da yan uwan fadima maza suka nemi xama sulhu yace in fadima ta matsa tanasan rayuwa da yayanta ta aureshi taje ta riqe yayanta, lamarin da taqi yarda sam saboda tasan halin matansa da yadda suka tsaneta a matsayin faccala bare kuma ta xama kishiyarsu, sannan kuma ita bazata iya cin amanar AL amin ba ta auri wansa. Shi kuma yayi amfani da wannan damar ya kwace yayanta yakai gidansa ya watsar. Kunji yadda lamarin ya kasance.

Mrs Muhammad 😊 [9/30, 1:04 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼AL 'AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼

Writing&story by Rahma Muhammad {hajia}

Editing by mmn khairat 😍

📝FANTASTIC STARS WRITERS {F S W } Pege9⃣

Maryam (Mimi) da Faty, Sun taso kai daya kasancewar Mimi mai garun jiki saita xama kamar saar Faty, baxaka taba kallonsu kace Faty tabawa Mimi tazarar shekaru biyar ba. Faty ta kasance fara sol kyakykyawar mace sosai doguwa mara jiki, kamarsu daya da uwarta sak mai yalwar sumar Kai. Yayin da Mimi ta kasance doguwa me murjajjen jiki me cikar halitta, bata da qiba Sam amma duk inda ya kamata ya xamo me cika ajikin mace kamarsu qirjinta da kuma hips to ajikin Mimi dai sai Masha Allah, dangane da skin colour kuwa Mimi wata irin colour ce ba fara bace kuma ba baqa bace ko kadan, itadai gatanan kamar ruwan xuma ( honey colour) fatarta me daukar hankalice irin colour din dake matuqar tsada a duniya, a taqaice dai xamu iya kiranta Kalar bargon kaza. Bata da wani shaharren kyau a fuska irin na yar uwarta komai nata a fuska tsaka tsaki ne inka cire manyan iduwanta farare tas, sai kuma haqoranta farare tas dogaye ,itama tana da gashi sosai koma ince duk jikinta gashi a kwance ( irin matannan masu gargasa) har fuskarta gashi ne a kwance tun daga gaban goshinta xuwa sajenta har xuwa qeyarta. Amma gashin mai qarfin gaske kamar izgar doki ga cika ga tsaho wanda yasa dole mama take mata retouching tun tana qaramarta inba hakaba baya kitsuwa yanka hannu yake. Itakam tafi kama da AL amin (mahaifinta) inka kalleta tsaf komai nata sai kaga tana kama sosai da SASHA OBAMA ( yar Barrack Obama) kai kace sun hada dangantaka, babu a bunda ya hadata da yar uwarta Faty ta bangaren kama sai muryarsu da take iri daya sai kuma dimple (beautiful point) din da suka gada ta bangaren uwarsu, domin yawanci yaya da jikokin gidan sunada shi. Wannan kenan.

Sun taso da mutuqar soyayyar junansu, hakan baya raba nasaba da adduar mama domin duk sanda tasa goshinta a qasa tana adduar Allah ya hada matá kan yayan nata kamar yadda ya hada nata da Adda halima, domin su kadai Allah ya bata (bata haihuba a gidan Baffa). Dayake Allah maji roqone ya amsa mata, ita kanta tana alfahari da yayanta inta kallesu tana tasbihi ga Allah, Faty kyakykywa tá qarshe San kowa kin wanda be samu ba, da kuma Mimi wacce da wuya ka dora ido akanta kadauke batare da tasbihi game dukaba musamman inbaka da cutar hassada. Duk da yawan gorin da ake mata a gidan na cewa "duk macen da bata haifi namiji ba bata haihu ba " wannan maganace da Kullum saí Anty ( jamila) ta fada mata ita. Da yake anty kamar yadda yaran gidan ke kiranta, ta kasance mahaukaciyar mace me mutuqar kishin mama ta tsaneta da yayanta, kuma bata iya boye abunda ke xuciyarta baro baro take nuna kiyayyarta ga maman tana taqama da yayanta kwarai kuma da fifitasu akan komai da take dashi. Yayin da Umma (hajara) ta kasance makirar mace kuma karuwar cikin gida, (fir'auna a xuci Musa a kan sharshe) wacce da wuya ka gane ainihin abunda ke xuciyarta inba mugun Sani kai mata ba, bazaka taba cewa ta damu da wanxuwar mama da yayanta a cikin gidanba. Amma a gaskiyar lamari tafi Anty tsanar su, domin lokacin da aka auro fadima itace ta nemi hadin kan Anty duk da tsananin kishi da fada da suke gwabzawa a lokacin, ta shawarceta da su ajiye kishi guri guda su yaqi fadiman. Kuma ta jagoranci Anty suka bi duk wasu hanyoyi suka hana fadima haihauwa domin a cewarsu be kamata taci gadon qani sannan tazo taci gadon yayansa ba. Shiganan fita can haka sukai ta xagaye guraren na tsugune (bokaye) har sukai nasarar rufe mahaifar fadima . (nikuwa nace Allah dai be qaddara rabo tsakanin fadima da Buhari ba domin daya qaddara bokaye basu isa hana Allah ikonsa ba). A duk sanda Anty taiwa mama gorin rashin haihuwar yaya maza takance ita haihuwa ai mai albarka kawai ake nema bawai jinsi ba Allah ya yiwa wanda yabani albarka .

Arziqin Baffa ya bunqasa kwarai domin yanxu har gina gidaje yake yana siyarwa ko ya saka haya ga gidan gonaki da yake dasu wanda yake kiwon kaji, kifi , raguna da kuma shanu. Mutanen da sukecin abinci a qarqashinsa suna da yawa, xuwa wannan lokaci ya aurar da yayansa mata da dama, kuma baya aurar dasu sai ya kaisu sun sauke farali (hajji) kusan ma yarinya tana gama secondry a gidan yake kaita maka, dayake yawanci bibbiyu suke tashi yaran gidan saboda tare Umma da Anty ke haihuwa sai dai tsiran watanni. Duk da cewa baiyi karatun boko mai xurfiba ya bawa yayansa ilimi domin dukkansu sai sun haura secondry yake aurar dasu kina fara jami a level 100 xuwa 200 saiya aurarki kya qarasa agidan mijinki. Kuma bai yarda da bawa karabuti auran yayansa ba, domin yace bazai sayar da akuya ta dawo tana cimasa danga ba, sai wanda ya tara (mai kudi) komai rufin asiri sosai yake bawa auran yayansa. Kuma Allah ya dafa masa akan hakan domin wadanda yake muradin yayansa su aura shi Allah yake kawo musu (masu kudi) kasancewar yayan nasa kyawawa gasu da kwalliya da kuma ilimi domin yawanci Baffa suke yowa kuma Baffa kyakykyawan bafullacene.

Sai dai ta bangaren yayan mama ba haka lamarinsu ya kasance ba a gidan domin Faty tuni ta gama secondry har ta shiga school of Nursing (makarantar koyan aikin jinya) amma ko airport Baffa bai kaitaba bare saudia dan sauke farali. Da mama taji zafin abun amma daga baya saita barshi abisa ajizanci irin na Dan Adam, musamman data duba alkhairinsa na kaita saudia shekaru 3 abaya, sai ta goge laifin rashin kai Faty, dabeba. Baffa yana muqar San mama domin kuwa bambamci tsakanin mama da sauran matansa a bayyane yake, mama macece mai tsari kwalli tsafta iya girki Kullum cikin kwalliya take yatsunta basa rabuwa da kunshi hakan ya qarawa kyanta armashi da soyayyar miji Baffa a Kullum godewa Allah yake daya qaddara masa auran fadima ,domin shi mutum ne besan gayu da tsafta matansa kuma basu da lokacin wannan saina gasar haihuwa saboda gado.

Mama ta dade da samun shaidar karantun NCE a kwalejin horar da malamai ta tarayya (FCE), domin bayan kammala secondry school dinta a gidan galadima taci gaba da karatu bisa shawarar Adda halima wacce a lokacin take B ED (Bachelor in Education) a FCE din domin mijin Adda (Alh Abdul Aziz) dan bokone na qarshe saboda haka a hannunsa ta fara karatu tundaga yaqi da jahilci har takai matakin samun degree. Da farko Baffa yaso hana mama karatu, amma ta burkese masa dole ya yarda saboda son da yake mata da kuma tausayinta da yakeji na rashin qara samun haihuwa saboda yana sane Kullum cikin gorin haihuwa take a gidan, koda komawarta makaranta matan gidan basu wani damuba tunda ba sanin darajar ilimin sukayi ba, sai data kammala mijin Adda halima ya samo mata aiki a wata junior secondry school sannan suka nemi yiwa Baffa bore saboda baqin ciki da hassada, shi kuma yace duk wadda xatai karatu acikinsu kofa abude take kuma intagama da kansa zai sama mata aiki. Dole sukai shiru domin sunsan basu da tym din karatu.

Soyyar dake tsakanin Faty da Mimi baki bai iya fadarta, Faty yarinyace mai dattako da sanyin hali. Ta bangarenta bata hada San Mimi da komai ba, za a iya cewa tafisan Mimi da ita kanta, sai kaiwa Faty laifi ta haqura amma in kaiwa Mimi ta yini tana fushi dakai. Mafi yawan qawayenta sunan MARYAM garesu kuma tana qawance dasu ne ta dalilin alaqar sunansu da Mimi. Bata cika xama a gidan Baffa ba mafi yawan rayuwarta tana yinta ne a gidan mummy (Adda halima) dake rijiyar zaki. Mummy nada yaya 7 maza 3 mata 4. A cikin yayan mummy akwai saar Faty da kuma saar Mimi. Duk da gidan mummy gidane na yan gayu da daula hakan besa Mimi cika san xaman gidan ba duk kuwa da qaunar da mummy kewa Faty da Mimi, tasamu Faty dai amma Mimi Kullum tana jikin mama. Lokacin da mama ta tafi aikin haji 3yrs back dole tasaka Mimi xaman gidan mummy. Datai duba na tsanaki sai ta gano abunda yasaka Faty San xaman gidan, wato daddy. Mijin mummy mutum ne baisan iyalansa kuma ya sakar musu abunda sukaga dama shi sukeyi, (ba irin sakarwar da xata xama ba tarbiyya ba) Kullum yana cikinsu in dare yayi a hadu ayi karatu ya koya musu sannan a dasa hira har 10 pm sannan kowa ya nemi makwanci, hakan yajawo Faty San xaman cikinsu saboda inda ta taso tsangwama kawai suka Sani daga gurin yan uwansu wato yayan Baffa.

Abunda ke daurewa mama kai shine batasan dalilin da yasa anty da Umma suka tsani Mimi fiye da Faty ba, ita a ganinta in qiyayyace Faty ya kamata afi zafafawa ita fiye da Mimi, domin kuwa in kyau ne kaf iyalan gidan Baffa sai dai su xamo a bayan Faty domin babu wanda ya isa ya hada kafadarsa da Faty ta fannin kyau, amma memakon suyiwa Faty hassada kodan kyanta sai ya zamo Mimi akewa. Amma mamakin mama ya qarene a lokacin data fuskanci tsanar Mimi ta samo asaline fisa tsananin soyayyar da Maman da Faty kewa mimin, sai ya zamo anaiwa Mimi abune kodan mama taji haushi kota tanka musu. Hakan yasa ta gayyato dauriya ta qara akan wacce take da ita akan Mimi in anmata abu ta kau da kai, duk da ciwon da abun ke mata.

Mrs Muhammad 😊 [9/30, 1:04 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼 AL 'AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼

Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}

Editing by Mmn khairat 😍

📝FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 1⃣0⃣

Faty tai sallama dakin mama daga makaranta take, sanye da fararen kaya Sol (uniform) da dan hijab iyakacin gwiwar hannunta. Mama tana zaune kan sofa tana kallo Mimi na kwance itama kan sofa din ta tada kai da cinyar mama hannun mama cikin gashin mimin tana shafawa ahankali. Ta qaraso ta dafa Mimi sannan ta kalli mama, mama Mimi ba lfy? Ta tambaya arikice. Eh ciwon mara take tun safe tasha magani, amma har yanxu be saketa ba. Wayyo inji Faty ta janyo Mimi jikinta ta rungume tana mata sannu mimin ta gyada mata kai cike da galabaita. Ta maida mimin jikin mama ta dau kudi a jakarta tare da cewa ina xuwa ta fita. Can sai gata ta dawo da allura ta bude ta hada, ta kama mimin suka shiga dakinsu dake parlourn ta kwantar da ita a kan gadonsu sannan tai mata allurar. Ko minti biyar bataiba bacci ya dauketa. Taiyi sallah ta canja kaya tazo ta kwanta a bayan mimin bacci ya dauketa itama. Mama taji shirun yayi yawa ta shigo domin kawowa Faty abinci ta tarar dasu kwance kamar yadda suka saba Faty abaya Mimi agaba akan filo daya hannun Faty akan cikin Mimi yayin da mimin ta sa hannunta ta riqe hannun Faty. Wannan shine salon kwanciyar yayanta tun suna qanana wani sa in kuma su rungume juna suna baccin. Tai murmushi ta qarasa ta sumbacesu ta kashe musu fitila taja musu qofa.

Tun Faty na secondry skul masoya sukai mata ca kuma manyan masu kudi da yayan manyan mutane harda jinin sarauta, saí dai Baffa yace saita fara makaranta domin haka dokar gidan take, a bangaren Faty kuwa duk basa gabanta domin akwai tsumammiyar soyayyar quruciya aranta, duk kashe kudin da samari keyi akanta baya gabanta hasalima bata kulasu. Tanason Ahmad (yaron maqotansu wanda ke shiga gidansu gurin mama). Tun lokacin da Ahmad ya farga da manyan masu kudin dake kawowa Faty hari ya shiga tashin hankali ba kadan ba, domin ya mace akan Faty tun tana qanqanuwarta kuma da ita kadai yake tsara rayuwarsa, hakan yasa yaje ya sakawa mama kuka da roqarta ta bashi Faty indai baso ake ya kashe kansa ba. Maman ta bashi tabbaci in shaa Allah Faty bata da miji sai shi domin ta fahimci Faty ma tana qaunar Ahmad shi yasa bata kula kowa cikin manemanta.

Duk da Baffa yaso turjewa lokacin da aka gabatar masa da Ahmad a matsayin manemun Faty, domin be tabawa kamar Ahmad (talaka) auran yarsa ba, amma kafewar Faty da mama akan auran yasa dole ya sakko musamman da yaga irin dukiyar da mahaifin Ahmad din ya kawo a matsayin kudin neman aure. Domin a lokacin giyar asiri da matarsa ta dena tasiri akansa, ya kuma bawa Ahmad din gida makeke a NNDC sannan ya samar masa aiki saboda a lokacin ya gama karatunsa har yayi service. Hakan yasa Baffa yadan sakko. Saí dai sabanin yadda Baffa ya saba aurar da yayansa iyayensu matá ko cokali basa siya shiyake komai kuma na bajinta. Amma akan Faty Set din gado kawai ya siya da Set din kujeru daya yaja bakin aljihunsa ya tsuke, abun ya bata mamaki kwarai ganin yadda yake banbanta yayansa da nata kamar ba yayan dan uwansa ba, amma sai ta danganta hakan da rashin San auran Ahmad din da yakeyi hakan yasa ta fitar da kudi maqudai da hadin gwiwar yan uwanta maza da Adda halima sukayi komai na bajinta suka yiwa Faty kayan daki domin na Baffa ma a dakin baqi aka xubasu, (dama dadin nema kenan) . Akayi aure amarya ta tare dakinta, da ike ance dan halak bai manta alkhairi Ahmad ya riqe Faty hannu bibbiyu ya zamo kamar bawa a gareta tana kammala karatu dayake maaikatan lfy basa rasa aiki, Baffa ya samo mata aiki kamar yadda yakeyiwa duk wacce ta gama karatu acikin yayansa, tana aiki a bangaren karbar haihuwa a AKTH wato aikin unguwar xoma (midwifery).

Mrs Muhammad 😊 [9/30, 1:04 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼 AL 'AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼

Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}

Editing by . Mmn khairat 😍

📝FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

PAGE 1⃣1⃣

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull