Kenza eBookz

Al'amarin maryam Complete - Chapter 3

Al'amarin maryam Complete - Chapter 3

Al'amarin maryam Complete Chapter 3: Al'amarin maryam Complete Chapter 3. Kyakykyawar budurwace yar kimanin shekaru 25 da haihuwa, skin colour dinta kadai…

4,283 words

Kyakykyawar budurwace yar kimanin shekaru 25 da haihuwa, skin colour dinta kadai ya isa jawo hankalin duk wani lafiyayan namiji fadawa tarkonta bare aje ga dirinta wato structure cikakkiyar fuska gareta me dauke da 👀 darara farare kal, komai na fuskarta matsakaicine wato mastada 'a kamar yadda muka siffanta abaya, bakinta dananne kadan dauke da haqora masu kyau farare kal, wanda daka gani kasan ana ziyartar Dental clinic duk bayan wata 6 domin wankesu, koyaya ta motsa bakinta dimple dinta saiya bayyana. Duk da a ganin mutane MARYAM ba wata kyakykyawa bace compared to yar uwarta faty, ni dai anawa ganin MARYAM kyakykyawar gaskece, saboda ba lokaci daya xaka kalleta ka gano kyan nata ba, nooo sai ka nutsu sosai sannan xaka gano baiwar kyau da Allah ya azurta MARYAM dashi. Bayan haka kuma aiba fuskar mace kadai ake kalla ajikinta asan cewa kyakykyawa ce, da yake mafi yawan mutanenmu sunfi gane cewa farar fata itace kyau, wanda Sam ba haka abin yake ba. Hannayen ta dauke suke da wasu irin xara xaran yatsu wadanda aka tara musu farce (kumba) dai dai misali ma ana ba zaqo zaqo ba, gashi an qawatasu da jan lalle hannu da qafa, qafarta mai ban shawa awa yar dundubus kamar jikinta, yatsun qafarma kamar na hannaye suke zara zara. Gashin kanta wanda cikar budurci tasa ya qara haukata da tsaho da yawa ya kwanta luf saboda amfani da mayukan gyaran gashi irinsu MEGA GROWTH, kwanciyar nada nasaba da retouching da yake samu duk bayan 8 wks saboda shampo baya wuce sati 8 akan Mimi zai fita, fuskarta kawai inka kalla kasan tana gashi saboda gashin dayacika gaban goshin hadi da sajenta. MARYAM AL 'AMIN kenan (Mimi). Wacce yan watanin kadan baya ta kammala degree dinta a fannin sharia (law) a B U K.

AL 'AMARIN MARYAM ya farane tun daga kammala secondry dinta ko ince angane AL amarin ne alokacin da yakamata ace Mimi tana da manema (samari), duk wanda yaji ko yaga Mimi zaiyi mamaki kwarai ace bata da saurayi daya tilo koda na rage dare ne. Duk da cewa Mimi macece mai farin jinin mata a lokacin da take jami a, amma hakan yanada nasaba da kwakwalwa (brain) da Allah ya hore mata, hakan yasa tayi qawaye yayan manyan mutane da kuma dai dai ita yan middle class, wasu sular qawancensu saboda kamun kanta da gayu da kuma kwakwalwar da take dasu wasu kuma sunasan Mimi ne saboda haduwar jini. Sai dai a bangaren samari ba hakan take ba ga Mimi, domin xata iya cewa tunda takai xamanin yan matanci bata taba wata 1 cikakke da saurayi ba, to samarin ma duk gasunanne ma ana yarane qanana masu xaman banxa ko dalibai wanda suke qarqashin kulawar iyayensu balle abasu aure. In saurayi yazo wajen Mimi da wahalar gaske ya dawo inma ya dawo din baya wuce zuwa biyu xai dauke qafa dan kansa, kudan shekaru 6 kenan ana fama da wannan matsala, wadanda suka taso tare a yayan Baffa guda duk anmusu aure hardama yayan dangi na gurin uwa da uba, hakan ya janyo mata gori sosai ita da mama tun anayin abun cikin habaici har takai ana fitowa fili a gotanra musu, musamman inya kasance saurayi yayi musu hidima, (lokacin axumi ko toshin sallah) lamarin dake saka mimin qunci ta shige daki tayi ta kuka ba domin tana musu hassada ba saí dan ta rasa yadda zatasa kanta taji, tunda take bata tabacin ficikar namiji da sunan yana sonta ba to inama samarin suke??? Domin saita shafe shekara ko karen mota be leqo da nufin neman auranta ba. Ta rasa wani irin al amari ne wannan, ko a dangi anasamun masu goranta mata ta haryar shagube da cewa ah! Kedai Mimi kinqi aure kina jiran me kudi ko? To ai kwayi auran tare da yayanmu, abun takaicin da yawa daga masu goranta mata yan uwantane na jini kuma na jiki wanda ya kamata ace sun jajanta mata sai dai aduk lokacin da irin hakan ta kasance yaya Faty intana gurin takan kare mimin da cewa aure ai lokaci ne, ita Mimi nata lokacin baiyiba.

A bangaren mama AL AMARIN Mimi na mutuqar daure mata kai, domin Mimi macece Abida (mai yawan ibada) domin da ace ibada tana bada miji da Mimi bata rufe shekaru ashirin ba tare da aure ba, amma da yake aure AL 'AMARI ne na Allah sai gashi shiru, ta bangaren kyau, tsafta,gayu,nutsuwa da gwarjini badan ita ta haifi Mimi ba xata iya cewa ta dade bataga mace irin haka ba. Ta rasa a inda matsalar take amma ta tattara ta barwa ubangiji lamarinsa itadai kullum goshinta a qasa tana roqawa Mimi da ma masu irin matsalarta Allah ya kawo musu mafita. Duk da xuciyar mama tasha shawartar maman akan taje ta samu daya daga cikin yan uwanta maxa su hada mimin aure da yayansu kodan saboda matsin lambar da mimin ke fuskanta a gurin Baffa, amma abu daya ke taka mata burki wannan Abu kuwa shine : kada auren ya tabbata daga baya mijin ya wulaqanta Mimi saboda bashi ya nema ba, bashi ita akai, kuma dama ance matar shige bata daraja. Kuma inta xurfafa tunani sai taga da daya daga cikin yayan yan uwan nata sunso ai da sun furta San auran Mimi tunda duk Sá anin ta na bangaren jikokin mal SULAIMAN anmusu aure. Tana mutuqar tausayin Mimi, yarinyar bata da qoshin lfy amma tana da qarfin xuciya, indai Mimi na gida to mama aikinta xamane kawai ko kuma tayi dinkinta abunta sai taso xata taya Mimi da aikin girki kona shara amma duk aikin da mace ya kamata tayi a gidan miji Mimi ta daukewa mama hakan ya qara xafafa qiyayyar mimin a gurin Umma da Anty wato kishiyoyin mama matan Baffa, badan basu da yayan da xasuyi musu ba sai dai dan basu yiwa yayan tarbiyar temaka musu ba.

A bangaren Baffa kuwa shi babu ruwanshi domin aganinshi iya shegene ya hana Mimi fitar da mijin aure, saboda shi Allah bai taba jarrabashi da dadewar yaya agabansa ba babu aure da sun fara jami a kamar jira suke Allah yake kawo musu miji. Hakan yasa ya dau lamarin Mimi iya shege. " in har baki fitar da miji ba har kika kammala makaranta to tabbas xan cire hannuna daga kanki domin naga abun naki ya koma iskanci, neman xubarmun da mutunci kikeyi a unguwa gandamemiyar budurwa dake kina yawo a gari ko kunya bakiji tun kina xuwa auran sa anni kin koma xuwa na qanne." wannan shine fadan Baffa Kullum akan Mimi, wanda yau da gobe tasa mimin haddacewa kaf, kuma hakance ta faru domin bayan graduation din Mimi anyi sallah qarama ba dadewa kuma a wannan sallah Baffa ko sisi baibawa Mimi da sunan kudin kayan sallah ba lamarin da yayiwa matan gidan da yayansu dadi kwarai, kuma wannan alamarce ta nuna tabbas Baffa ya cire hannu akan Mimi kamar yadda ya alqawaranta, ko gaisheshi tai a ciki yake ammasawa shi a lallai yana fushi da ita kan abunda ba ita ta dorawa kanta ba (Allah sarki).

A yanxu haka da take shirin tafiya law school, a gidanma shirin aurar da mutum 3 biyu mata wadanda mimin ta girmesu da shekaru 3 sai namiji 1 yaya Ali, wanda ya kasance da na biyu a jerin yaya mazan gidan, domin dan Baffa namiji na farko (yaya jafar) wanda kuma ya kasance dan Umma yana kaduna yana aiki , kuma da shine yake nuna kamar yanason Mimi duk da bai furtaba amma daga baya maganar tabi ruwa tun bayan samun canjin gurin aiki daga kano xuwa kaduna. A duk lokacin da Baffa zai aurar da yaya mama ce keyi musu labulaye da xannuwan gado na alfarma a matsayin gudummmawa, wanda hakan ya zamewa Baffa jiki a tun bayan Koyan labulaye da xanin gado da mama tayi yayi bankwana da siyansu a harkar bikin yayansa, kawai in aure ya tashi xa a bata kalar kayan falon da xa ai wa amarya ita kuma zata zauna ta qure basirarta Ta tsantsara labulaye da bed sheets set uku uku ta bayar da sunan gudummawa kuma a karba bako godia kamar kudin suka bata kuma hakan bazaisa ana jimawa kadan aiwa yarta gorin aureba. Domin matan Baffa hamshaqan jahilai ne, jahilci irin wanda aka denashi saboda sauraran radio koda bakaje makaranta ba to yana existing a gidan tunbama suna fada akan yaya ba sai kaji kamar ka binne kanka, wannan yasa yayansu basu da tarbiyya ko kadan.

Gidansu Mimi gidane na kwalliya koma ince competition dinta ake da yake duk wacce ta gama karatu Baffa na samar mata aiki, hakan yasasu qarya daga yan matan gidan har wadanda ke gidan miji, yawancinsu suna da mota koma ince dukkansu wasu su suka siya wasu kuma mazajensu suka saya musu, acikinsu kuwa harda yaya Faty wacce ya Ahmad ya siya mata tun kafin ya siyawa kansa. Hakan yasa gidan ake gasar saka suttura da kwalliya da kuma shiga mota. Ta bangaren sutura Mimi kan sai hamdala tufa dai akwaita mama tayi mata, yaya Faty tayi mata, hajia kakarta ta wajen uwa wacce taci sunanta itama Kullum a hanyar yiwa takwararta sutura take , sannan mummy (Adda halima) yayar mama tayi mata sutura kam sai dai ta jira Mimi, ba Mimi ta jira ba. Hakan yasa koda Baffa bai mataba bata damuba.

Ana saura sati biyu bikin gidan ta tafi law school wanda yan gidan suka danganta haka da baqin ciki suka dunga sakin maganganu marasa dadi, domin Anty cewa tai ai dole aqirqiri tafiya law school domin da kunya a xauna to! za ayiwa yara aure ga gyatuma xaube ajabe agida.

Mrs Muhammad 😊 [9/30, 1:04 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼 AL' AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼

📝FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}

Editing by mmn khairat 😍

Page 1⃣2⃣ Yammacin ranar juma a ne rana gaf take da faduwa, a zaune akan tabar rila ta gidansu Mimi matasa ne guda biyu zaune akan tabarma suna jiran Baffa dake daga cikin sitroom din yana sallamar wasu baqi. Badaru sunan babban mai shekaru 33 sai Badamasi qaramin kenan me kimanin shekaru 30 a duniya, yayan abokin Baffa ne ya turosu gaida Baffa kamar yadda yake a al adar mahaifinsu (alh Inuwa) yakan turosu gaida abokin nasa aduk sanda ya kasance Badamasi na gari, saboda ba a garin kano yake aiki ba. Fararene tas kana ganinsu kaga fulani amma babban wato Badaru yafi Badamasi haske sai dai Badamasin yafishi jiki da kuma cikar zati irin ta maxa, sannan kuma yafishi alamar wayewa da kuma kwarjini, kodan hakan yanada nasaba da ilimin boko da Badamasin yafi Badaru oho.

Tafe take cike da gajiya saboda tafiyar da tayi daga Law skul (makarantar koyar da aikin lauya) xuwa gida sakamon samun hutu 1 wk da sukayi tazo gida domin yin hutun, sanye dake cikin suit baqaqe riga da skirt kamar yanda yake ga dokar makarantarsu, sai dan Baby hijab dake maqale a wuyanta kayan sun mata cif sun fito da surarta, qafarta sanye cikin rufaffen takalmi (cover shoe) baqi sai jakar goyo irinta dalibai itama baqa, ataqaice dai hijab dintane kawai fari a jikinta, jakar na goye a bayanta wacce ke dauke da yan kayan da xata iya buqata kamarsu brush, charger da kuma system din ta ( wato laptop) sai wayar dake riqe a hannunta. Duk da gajiyar da tayi hakan bai hana kyanta fitowa ba, babu kwalliya ko digo a fuskarta sai gashin gaban goshinta wanda baya iya rufuwa koda ta kwatanta rufeshi fatarta tayi tas ta kuma yin kyau saboda zama guri daya data samu. Mimin mama da Yaya Faty kenan .

Harta qaraso cikin rilar wacce xata sadata da sorayen gidansu bata kula da wanxuwar su Badaru a cikin gurin ba, wanda su kuma tunda ta tunkaro gidan suke kallonta harta shigo cikin rilar shigowarta yasa suka sauke ajiyar xuciya atare suka kuma shagala da kallonta ganin tana shirin shigewa cikin gidan yasa Badamasi tashi da hanxari ya qarasa inda take tare da cewa "Assalamu alaikum" . Yayin da Badaru ya kashingida ya cigaba da kallonta bako qiftawa. Bayan sun dan gaisa da Badamasi sama sama saboda ta qagu ta qarasa gida, ya kalleta a karo na barkatai sannan yace kamar daga makaranta kike ko? Taqanyi yaqe tace eh, ok wace skul kike? Ina Law skul ne dake nan jihar kano, ta bashi amsa a gajarce. Kai 😳 kice da Barrister nake tare, yasunan malamar? Maryam ta bashi amsa tana murmushi 😊. Barrister maryam gaskiya kin burgeni inason inga mace tayi karatu me xurfi haka. Well naga a gajiye kike ni sunana Badamasi wancan na kwance yayanane sunansa Badaru munxo gurin Babanki ne, kuma ina fata daga yanxu xumunci ya shiga tsakaninmu. Tace to nagode bari na qarasa, Ok to Mimi sai nazo karki manta sunan Badamasi da haka suka rabu ta shige gida.

Bayan ta kwana biyu da xuwa ne kuma ta shirya xuwa gidan Rashida da Rahana (wato amaren gidan da akai biki bayan batanan) ta Ware 10k da nufin ta bawa ko wacce 5k a cikinsu. Mama sam batazo xuwan Mimi gidan Rashida ba saboda Rashida (yar Anty jamila) tafi tsananta qiyayyar Mimi akan kowane mahaluqi dake gidan Baffa, qiyayyar Rashida ga Mimi a bayyane take kowa yasan Rashida ta tsani Mimi tsana ta qarshe, domin anshayin taro acikin gidan ko a wajen gidan Rashida tayiwa Mimi gorin aure (tun kafin ita Rashida tayi auren kenan) ko kuma ta duxgata agaban mutane ko qawatenta. Dan akwai lokacin da yaya Zainab yar ita Rashidan wato yar dakin Anty ta haihu ranar suna duk antaru anata aikin dambun shinkafa a gate din gidan Anty Zainab din anata hira kowa na tofa albarkacin bakinsa, hirar dai akan karatune da kuma wahalar samun aiki, Mimi tasa baki acikin hirar da cewa " ai aiki kam na wahala akasar nan indai baka da wanda kasani saika gama karatunma ka xama jobless Allah dai ya kyara qasarnan, sai kuwa tsulum Rashida tasa baki tare da cewa "ai koba aiki inkanada mashinshini sai kai auranka ka huta, damuwa akan aiki ai Sai irinki wadanda kukai kwantai kuka kai matakin bandaro (🤣🤣🤣🤣) ,ta fada tare da kwashewa da dariya. Kowa agurin yayi qim maganar ta bashi mamaki domin bata taba fitowa fili ta fadawa mimin magana ga da ga hakaba, maganar ta daki Mimi kuma tai mata ciwo saboda ganin yadda gurin yake acike da mutane daga na gida har qawayen Anty Zainab da dangin mijinta, ta rasa abunda ta tsarewa Rashida take mata wannan muguwar qiyayyar, duk da tasan cewa a yayan Baffa wadanda suke santa basu wuce 4 ba xuwa 5 amma ba wanda yake mata qiyayya kwatan kwacin wadda Rashida ke mata tasha goranta mata abunda ba ita ta dorawa kanta ba (jinkirin aure) hawaye ya wanke mata fuska ta kasa dago kanta ta kalli kowa a gurin saboda jitayi duk ta muzanta, qarar marin ta tajine ya dawo da ita daga tunanin da take, tai saurin dagowa taga wanda aka mara tai toxali da Rashida riqe da kunci gefe kuma ga yaya Faty tana huci da alama itace ta mari Rashida. Dai dai lokacin kuma Rashida ta yunquro cike da fitsara ta fara nuna Faty tana cewa akan wannan 👈🏼 ta nuna Mimi kika mareni? Dan ance tayi kwantai? Qarya nai batai kwantan bane? Shekararta nawa batai aure ba? Age mate dinta hardame yaya 4 amma ita ta gaza samun even tsayayyen saurayi saboda rashin kamun kai, duk wanda yaxo sai tabashi ya dana, ya za ai kuwa ya aureta? Kema Faty (yau ko yaya fatyn babu 😄) duk randa kika kuma taba fuskata da sunan duka wlh sai.. Adaidai lokacin Anty Adawiyya wacce akaje cikin gida aka fada mata abunda ke faruwa ta sharawa Rashida mari ta kuma kifa mata wani, sannan ta dora da xagin Rashida da yimata gargadi cikin kakkausan lafaxi kasancewarta Principal din makaranta kusan tasan takan iya shege (kusan principals ba wasa 😜 akwai displine) . Ko takansu Faty bata kuma bi ba taja hannun Mimi ta bude motarta dake cikin gate din tasaka mimin aciki sannan ta koma cikin gidan ta debo duk wani abu nata da taxo dashi da na mimin ta xuba a Mota Anty Adawiyya na kiranta ko juyawa bataiba bare ta nuna taji, duk kuwa da tsanin girmamawar da sukewa Anty Adawiyya sabida itace babbar yar Baffa (mai haquri bai iya fushi ba) amota suna tafe Faty kuka take kamar Mimi koma fiye da ita, fuskar tayi jajur kan Hancinta har Pink yake saboda kuka. Wannan shine dalilin da Mimi ta daina xuwa taro domin intaje sai anmata abunda akasan ranta zai baci koda cikin hirane, kuma shine dalinlin da yasa bata xauna bikin su Rashida ba kar atara mutane aci mata mutunci. Duk da Anty tasan da duk abunda Rashida kewa Mimi amma ko afuska bata tava nunawa Rashida tayi lefi ba.

Mimi nikam da xaki haqura da xuwa gidan Rashida duk abunda ki kai niyyar bata ki aika mata dashi sabida gudun fitina. Mimi tayi murmushi tare da dafa cinyar mama tace mama duk lalacewar Rashida duk qiyayyarta gareni yar uwata ce jininmu daya kuma innaje gidan Rahana banje gidan Rashida ba bakya ganin hakan xai xama abun magana? Mama tadan nisa kana tace eh hakane kam kuma ai duk tsiyarta tunda gidanta kikaje ai batayi miki ba, yawwa mama kingane kenan. Mimi ta fada. Mama ta kalli yar tata, sanye take da riga da skirt na atamafar nouvo dark blue me adon Yellow ta saka veil (mayafi) Yellow tasha daurinta me steps ta bude tsakiyar daurin inda gashinta da tai dunnot dashi ya fito, Mimi ta taba mama tace mama kodai infasa xuwa naga hankalinki bai kwantaba, Maman tai saurin cewa a a wlh uwata kyau kikayi shiyasa nake ta kallonki, Allah ya kiyaye hanya Allah ya sa asamon suruki. Mimin tayi murmushi ta sunkui da kai cike da kunya sannan ta fita.

Duk da ba wani good time suke da Rahana ba, amma ta karbeta da girmamawa ba kamar a gida ba da suka rainata dan batai aureba, hakan kuwa yayiwa mimin dadi sosai Rahana ta zagaya da ita taga gidan ya tsaru komai tsaf mijin nata nada yan canji (kudi) 😄 har ta kirashi ya sunkuya har qasa ya gaida ta, itama kuma taja girmanta ko 30mnt bataiba a gidan ta bata 5k taita godia.

A gidan Rashida kam to abun babu dadi domin Mimi na shigowa falon tahauyin wayar qarya tana cewa "kedai bari ai duk macen da batai aure da wuriba ta cuci kanta domin kinsan in mace ta wuce 25 yrs ance ita damai haihuwa goma duk daya namiji yake jinsu, nikam na dace inkinga yanda my Adams ya dunga tarairayata ba har pant wankemun yake yanxu hakama yaban kyautar Mota, abun Allah tana cikin wannan maganar ne wayarta tai qara alamar kira ya shigo, wanda hakan shiya fallasa wayar qaryar da take dan taciwa baiwar Allah mutunci, nan danan kuwa ta dibibice ta wayance da cewa wata wayar ta shigo. Suka gaisa tana wani daga kai ita adole madam saboda ta auri me kudi da gidan alfarma, batacewa mimin tashiga taga gidaba itama batai gigin leqa ko ina a gidan ba, tadai kira kukunsu tace ya kawo mimin pure wata (ruwan leda) ita kuma tace ya dakko mata gorar ruwan Faro, yaje ya kawo kamar yadda tace Mimi ta dauki ruwan tasha ita abunma dariya ya bata dan ita ba baquwar ruwan roba bace, ta bata kudin da ta kawo mata tare da cewa ta gaida me gidan inya dawo ta karbi kudin a yatsine ta watsasu kan centre table din dake dakin cike da ixxa tare da cewa xan fada masa kina gaidashi inban manta ba 😏 ko tashi bataiba balle ta raka mimin tana daganan tace ki gaida gida.

Ta tafi tana qissima kyan gidan Rashida a ranta, Allah me yadda yaso dama Rashida macece mesan qawa da fantamawa da kuma rayuwar kece raini gashi kuma Allah ya bata. Koda taje gida babu wanda ta fadawa abunda Rashidan tai mata sabida fadar bata da amfani, da haka ta qarasa kwanakin da xatai a gidan dagan tai gidan yaya Faty ta qarasa kwanakinta sukasha hirarsu ta xumunci, daga can ta koma skul cike da kewar yan uwanta danma ta kusa gamawa.

Mrs Muhammad 😊 [9/30, 1:04 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼 AL AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼🙆🏼

📝FANTASTIC STARS WRITE {F S W }

WRITING & STORY BY rahma Muhammad {hajia}

Editing by Maman khairat 😍

Page 1⃣3⃣

Alh Inuwa da Haj Kaltume wato mahaifan su Badaru yan asalin misaune da jahar bauchi harkar kasuwanci ta kawoshi garin kano, kuma harkar kasuwancin ce ta hadashi da Baffa (alh Buhari) yayan biyar biyu maxa Badaru sannan Badamasi sai mata guda 3 kuma sune qanana yanxu haka kowacce tai aure tana gidanta kasancewar ba ba karatu suke me xurfi ba iya secondry suke tsaya saboda alh inuwa bashi da wayewa irinta Baffa, haka ma kuma a fagen kasuwanci Baffa yayi masa fintunkau, duk da cewa shima dai baza a kirashi talaka ba yana sahun masu rufin asiri. Badaru sam baiyi wani karatun boko mai zurfiba domin yana gama secondry skul yayi nufin ajiye karatu sai dai kuma abbansu yanason yayansa maxa suyi karatu me xurfi, ala dole Badaru yayi applying a AMINU kano college of islamic (legal) tunda result dinsa baiyi kyan da xai shiga jamia ba kuma dama yafi qarfi a bangaren arabic saboda ko secondry dinsa ma arabic skul yayi. Ko da ya shiga legal din ba wani maida hankali yayi ba domin hankalinsa yafi karkata kan kasuwancin mahaifinsa da yake a kasuwar singa yana saida kayan masarufi. Da kyar da sudin goshi ya kammala diploma a legal saboda shi dama can karatun boko be dameshi ba ko kadan kuma yana daukan duk wanda ya zaqe da neman ilimin boko a matsayin Bayahude be bautawa turawa, awani bangaren ma yana yimasa kallo kafiri kafiri (waiyazubillah). A bangaren halitta farine tsamurmuri bashi da tsaho ko kadan sai yar qiba daya fara bayan kammala karatunsa, hakan yasa yayi tumbi kamar dan yaye 😄, ga dukkan alamu inyasamu Jin dadi anan kusa zaiyi qiba wacce xata qarawa xubin halittarsa muni sosai. Irin mutanenne masu zafin aqida da taurin kai da kuma kafewa akan abunda suke ganin dai dai ne koda kuwa sauran jamaa suna kallon abun a matsayin kuskure, a fuska bashi da muni duk da kuwa karan hancinsa da yaso ya shafe wanxuwar idanunsa 👀 a fuskar ma 'ana idanunsa qananane sosai ya tara qasumba har xuwa dan madaidaicin gemunsa. Saboda burkitaccen ra'ayin Badaru yasa bai cika abokai ba, saboda kallon kowa yake a matsayin bayahude daya shagala da bautar masu jajayen kunnuwa (turawa), sai dayake bahaushe yace ba a rasa nono a ruga hakan yasa Badaru bai rasa dai daikun abokai ba masu irin ra'ayinsa. A fagen soyayya kuwa ya dade da fadawa tarkon wata yarinya Nafeesa yarinyace batafi 16-17 years ba, dominshi a ra'ayinsa babu auran babba aciki yafison yara wacce zaiyi tarbiyyarta ya juyata san ransa, amma fa a ganinsa (ni kuwa nace banda irin yaran yanxu, domin sunfi manyan iya shege) 😊 yanason Nafee wajen shekararsu 2 tare da ita. Nafeesa kyakykyawar gaskece fara wanda hanken fatar tata yasamu tagomashi da bleaching (dama ance yanxu farare ne ke bleaching) yar siririya sosai ko ince shapeless, duk da cewa Badaru yafison yaga mace dirarriya wato 8 figure, amma a kan Nafeesa wannan raayi nasa ya kasa tasiri saboda san dayake mata. Itama a bangarenta babu kamar Badaru duk duniya 😳 ( wai ina ruwan kucaka 😂) saboda hidimar da yake mata, biyayya take masa sau da qafa kamar mijin auranta ko ince kamar ubanta wanda hakan ya qara janyo mata soyayyar gurinsa. Qiriri Nafee ta tsaida karatu tun tana JS 3 saboda Badaru bayaso tai ilimin boko dan kartafi qarfinsa , iyayenta kuma suka xuba mata ido saboda kar suce lallai sai tayi Badaru ya daina yimata hidima ta koma xaman kashe pant ( xaman banxa da yawon bin gidajen maqota) kasancewar iyayen nata masu qaramin qarfi kwarai, tun shekarar data gabata Badaru ya kai kudin aure kuma akai musu engage ana jira ya gama ginin gidansa asaka rana kuma gaf yake da gama ginin.

A bangaren halayen Badamasi qanin Badaru kuwa xan iya kiran lamarin da bil akasi, domin duk da kasancewarsu uwa daya uba daya halayensu kishiyoyin junane, Badamasi yayi karatunsa har xuwa jamia inda ya jika burin mahaifinsu na xama cikakken likitan qashi kuma yasamu aiki a babban asibitin Dutse ta jahar jigawa, duk da suna kama da Badaru a fuska hakan be hana Badamasi cikar kamala da cikar halitta fiye da Badaruba shikam yana da tsaho fiye dana dan uwansa ga saje da ya tsayar kuma yake gyarashi, dan bokone sosai kallo daya inkai masa xaka iya gano hakan daga yanayin shigarsa, atsarinsa ya fison mace matashiya ba yarinya ba ba kuma over age ba (tsaka tsaki) kuma mai ilimin addini dana boko sannan wayayyiya wacce xata iya kula dashi, baiyi katarin samun macen data hada wannan abubuwa ba sai kuma yanxu daya ga Mimi, tundaga lokacin da suka hadu xuwa yau kimanin 5 wks kenan Kullum tana maqale a ransa da wata irin faduwar gaba da yake a duk lokacin daya tunata, ya rasa dalilin dayasa har yanxu ya kasa komawa gidan ko no wayarta ya karba dik da cewa kuwa takanas yake baro dutse duk sati da nufin xuwa gidansu amma yana zuwa saí xancen ya shiririce ko wani abun ya sha gabansa. Da yayi tunanin fara yiwa abba maganarta dan anemar masa auranta in da hali ma so yake a hada bikin dana Badaru, amma sai yaga gara ya fara neman soyayyarta yanda xasu gina gidansu cikin soyayya da fahimtar juna.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull