Kenza eBookz

Al'amarin maryam Complete - Chapter 43

Al'amarin maryam Complete - Chapter 43

Al'amarin maryam Complete Chapter 43: Al'amarin maryam Complete Chapter 43. Sunanan xaune suna hirarsu Bature ya dawo aiki, kamar yadda ya saba ya shigo…

4,459 words

Sunanan xaune suna hirarsu Bature ya dawo aiki, kamar yadda ya saba ya shigo yana waqa, Sam bai lura da mutanen dake gurinba idonsa Mimi kawai ya hango masa. Ya taho gurinta yana waqa, yayin da su jafar suke daga bayansa, wato Mimi saitin qofa ta kallah shiyasa yana xuwa ita ya fara gani ya bude hannusa yana cewa "hlo my african queen" ya tsuguna gabanta tana kan kujera ya dafa gwiwarta, ta danji kunya tace "bakai sallama ba" ya lakace mata hanci yace "nayi kene bakiji ba, bakixo kin taroni ba kin rungumeni" ta dunga qifta ido tanason nuna masa da baqi fa a dakin amma ina bai ganeba saima cewa yayi "ki dainamun wannan farin nan, kixo muje ciki kimun in biyaki. Ya sumbaci goshinta,lips, dinta sannan ya sumbaci cikinta daga baya ya rungumeta. Su jafar na zaune a daskare suna kallon luv.

Tana tureshi daga jikinta ta rada masa "akwai fa mutane a falon" ya dago yakai dubansa bayansa, suka hada ido dasu jafar. Kunya ta kamashi ya dan sosa kai yace "jafar kune a garin namu yau?" jafar ya danyi yaqe yace "wlh kuwa aiki ne yadan kawomu Abuja na kwana uku shine na biyo duba maryam, yanxu xamu wuce masauki" yace "kai amma kun kyauta" yaje sukayi musabiha aka kuma gaisawa sosai da tuntubar juna. Bature yace "ai nanne masaukinku, ina xakuje bayan ga nan din. Duk girman gidannan ace kun fita hotel" jafar yace "a a wlh ai kuwa dai baxan sauka gidan qanwata ba da girmana" Bature ya dubeshi yace "au maryam kake kallo a matsayin yar uwarka? Ni bareni a cikinku? Hakan yayi, nagode sosai" jikin jafar yayi sanyi, yace "kayi haquri sulaiman ba nufina kenan ba." haka ya dunga bashi haquri Mimi tasa baki. Yace "is Ok, taso muje mu dakko kayanku" dole jafar ya tashi sukaje mota ya bude aka fito da kwatinsu. Bature da kansa ya dakko ya shigo da ita. Maryam din jafar kuwa kwanciya tayi bisa kujera, hakan yayi mata dadi xataso kwana a wannan aljannar duniyar dan tasan mijinta bashi da kudin da xai kama hotel din da xai kama koda kafar wannan gidan.

Suka sake xaman hira anan falon, ya tashi yaje kitchen yayi blending fruit ya xubo a cup. Sai da yasha ya rage ya miqawa Mimi ragowar ta shanye. Kiran sallah ya data su, maxan sukai masallaci Mimi ta ja maryam dakinta sukai sallah. Ta dunga kallon makeken bed room din, yayi girman wani gidan wai duk bed room ne, tab Mimi ta samu duniya. Bayan idarwa Mimi da kanta taje ta gyara musu daya dakin tasa sabon bed sheet ta fesa maganin saura ta kai musu duk abun buqata irinsu masubulun wanka, maclean da sauransu. Ta ja maryam suka koma bedroom din ta sake wanka, maryam kallonta take, yanxu bayan wannan wankan har wani aka sake? Tab ita wanka daya take. Taga Mimi ta kuma chada kwalliya cikin bubu din atamfa. Bayan dawowarsu masallaci kowanne ya shige dakin matarsa. Jafar yayi wanka ganin haka itama maryam tayi dan kar ace mata qazama.

Har daki Mimi taje ta kirasu xasuyi dinner. Suka hadu jafar idonsa akan Bature da Mimi yana ganin wata irin salon soyayya me ban mamaki da shaawa. Ya raya cewa da tuni shi Mimi kewa wannan kulawar. Bature ya tashi ya xuba musu abinci da kowa a plate dinsa kana ya xauna, ya dauki plate din Mimi yaci cokali daya sannan ya tura mata gabanta yace "Bisimillah Mimi luv" tace "to ya Bature" suna cin abinci cikin nishadi ana hira jefi jefi. Mimi ta janyo kwanan da aka gasa nama ta bude, yayi saurin karbarta ya tashi ya sakawa kowa a gabansa. Maryam din ya jafar a ranta tace "tabdi bata girki kuma xubawar ma sai anyi mata? Inama nice" cikin san nuna ita watace ta kalli naman da Bature ya ajiye mata gabanta, azatonta kaza ce ta yatsuna fiska tace "ni banacin naman kaxa" jafar kunya ta kamashi dan yasan qarya take. Mimi kuma ta yarda da abunda tace, dan tasan mutum iri iri ne kowa da yadda Allah ya halicceshi, tace "ayya sry Anty maryam ko in gasa miki red meat? Wannan ma ba kaxa bace, ba a cin naman kaxa a gidannan. Talo -talo ne." Bature yace "a a Mimi luv, cewa xakiyi tunda kikai ciki kika daina cin kaxa sai talo talo." dajin ance talo talo ne tahau yaga tanaci dan tasha ji ana cewa wanda ya saba cin naman talo talo baya iya cin kaxa sabida dadinsa.

A daren Mimi ta kwaba funkaso dan tasan shine favourite din jafar, ta hada miyar taushe ta dafa fari Sol din naman kan Sá ta rufe.

Da sassafe yana kan gym ita kuma tana kitchen tana suyar funkaso, harya gama motsa jikin yaxo ya tayata aikin. Sai wajen tara suka gama komai ta bar Aisha ta shirya table ita kuma taje tai wanka. Goma sun gama komai har maxan sun fita aiki, ita da Anty maryam kuma kamar yadda take kiranta sunata hira tana janta duk gurin da xata a gidan tana nuna mata. Itama maryam ta saki jiki da Mimi suna hira duk da rabin hirar tata qaryace dan a tunaninta gara ta hada da qarya kar Mimi ta rainata, batasan ita ba haka take ba.

Yauma kamar jiya, sun hadu falo da yamma bayan dawowarsu office. Jafar yana ganin wata extra ordinary caring da Bature kewa Mimi, inxata xauna saiya miqe ta zauna sannan shima ya zauna kamar wani yaranta, in abinci xataci saiya faraci kamar mai tsoron kartaci guba kuma in ruwa xatasha saiya tsiyayo mata, duk maganarsa daya sai yace "Mimi luv"

Yauma suna zaune kan dinning Mimi da kanta tayi jellof rice wacce tasha baqin kifi busashshe tayi shar sun cinye abinci tas dan yayi dadi sosai.

Wajen 8:23 pm Farida ta shigo gidan tasha kwalliya sosai, da ritsetsen cikinta. Ta dubi Mimi tada taso ta dosota kana takai kallonta kan maryam matar jafar. Taci kwalliya da tufa me tsadar gaske ta xuba golds hannu da wuya a wannan daren kamar mai zuwa competition. Amma kash! Kwalliyar daban ita daban dan Sam bata iya kwalkiyar ba dagani bata da wayewa. Farida tai qasa da murya tace "money miss road" Mimi ta tsunkuleta ta nuna mata jafar da ido tace "matarsa ce" sai a lokacin taga jafar suka gaisa. Ta kalli Mimi tace "besty ya baki shirya ba? Cinema fa xamuje kallon wannan film din" Mimi ta dafa goshi tace "kash namanta bari in sake kaya" ta wuce daki Farida ta xauna kan kujera tana kallon maryam din jafar a sace tana dariya. Anata bangaren maryam tayi wannan kwalliyar ne dan nunawa Mimi itama fa tana da kayan qarya dan bata taba xuwa Abuja ba, daji ance xa a je ta kwaso kayan qasan akwati da nufin axo Abuja ai fafa dasu, sai akai sa a kayanta ya tsinke bakin kaba taxo gidan yan gayu dan haka ta fito da tanadi ta fara bawa Mimi mamaki a ganinta🤣

Ishaq ya shigo yace da Farida "dabaki tsayani ba gashi duk saurinki na taddaki" tace "wlh kuwa ya ishaq Mimi wai ta manta" Bature ya kalli jafar yace "koxo muje cinema kallon wani nollywood film kuma da jaruman film din shiyasa su Farida ke rawar kan zuwa sunason ganin jaruma jackie appiea" jafar yace a ransa lallai Bature ka cika shedani anbaka yarinya me tarbiyya amma har Cinema ka koya mata xuwa" a fili kuma yace "ba damuwa maryam tashi muje" Farida kamar tace da wannan shigar xaki cinema din, sai kuma tai shiru.

Mimi ta fito cikin shiga english gown me taushi amrless ta dora boy friend jacket akai ta samu qaramin gyale tayi vieling fuskarta babu kwalliya sai powder da man lebe tayi kyau sosai. Suka kama hanya.

Daga wajen cinema suka tsaya suka sayi pop corn, Mimi taje gurin kayan sanyi ta dauki qaton roban ice cream tace da Farida kawo kudi ban fito da jaka ba, farida tace nima haka, amma ina zuwa. Taje gurin su ishaq dake tsaye ta xare masa willet dinsa be sani ba, sukaje suka biya kudin, sai gasu kowacce na tura ciki da robar ice cream. Farida ta miqawa ishaq willet dinsa. Yace "yaushe kika dauka bansani ba?" Bature ya dubi Mimi ta robar ice cream din yawunta har ya soma tsinkewa so take su shiga kawai tasha yace "wa ya sai muku? Ban hanaku shan sanyi ba?" ishaq yace "kyalesu shammatata sukai suka xaremun willet.

Sun nutsu a kallon film din kuma yayi kyau sosai, Mimi dai tunda ta cika cikinta da ice cream tai bacci a kafadarsa, koda aka tashi sai dakkota yayi yasata a mota da sukaje gidama haka ya dau barsa har dakinsu. Jafar kallonsu yake cike da burgewa.

A yan kwanakin da sukayi da su ya fuskanci qaryane ace Bature baisan Mimi, domin wannan kulawar da sukewa juna ta wuce misali. Farko ya dauka ganinsune yasa Bature yiwa Mimi irin haka amma daga baya saiya lura haka suka gina rayuwar aurensu, sonta yake tattalinta yake kamar ya maidata ciki ga kuma girmamata da yakeyi. Wani dare sun zauna zasuci abinci Mimi ta miqe tsam ta koma bisa carpet ta fara kukan shagwaba, ya miqe yace dasu, kuci abincinku ni yau Mimi rigimar ta motsa, ai kuwa abinciin da baiciba kenan ta dunga kuka tana burgima tsakanin qafarsa wai cikin yana mata motsi ya danne mata. Ya dunga lallabata har tai bacci ya kaita daki.

Har kwanakin aikinsu ya qare amma suka hanasu tafiya, wai sai week end ya koyi abubuwa da yawa a xamansu, wanda inka riqesu xaka xauna da matarka lfy duk tsaurinta. Kuma yayi aniyar gyara rayuwar aurensa in shaa Allah. Anata bangaren Mimi taja maryam ajiki ta dan koya mata tsaftar jiki wacce ta fuskanci tana da rauninta. Randa zasu tafi Mimi ta bata lace da mayafi sai fashion din yari da sarqa, shi kuma ya jafar ta dakko masa wani filtek a cikin kayan Bature wanda bai dinka ba, koda taje dauka tace in dauki wannan ya Bature? Yace dauki maryam dan nasan kyautarwa xaki Allah ya hadamu a ladan. Tace nagode yace "nima nagode da koyar dani da kikayi cewa mutum koda mawadacine in ammasa ihsani yana jin dadi" sun rabu cikin kewar juna. Jafar ya yadda soyayya ce me qarfi tsakaninsu babu xancen yaudara.

Passing out dinsu na gama service lokaci yayi ana gobe xa ai suka tafi kano a motocin data saiwa su mama, ita da Bature a guda daya driver ya Biyosu da dayar suka tafi tare.

Washegari da safe sukaje state sect P O P din, yana xaune yana jiranta suka gama ta amshi cert dinta na NYSC sukayi pics din tarihi da qawayenta aka rabu. Tana shigowa motar yace "BARRISTER MARYAM AL AMIN congrat" ta farareshi tace "kawai dai kace kanason fadar sunan Babana amma inba haka ba kace congrat din mana kawai" ya sheqe da dariya yana mamakin daru irin nata yace "sry ranki ya dade, na gyara congrat Maryam"

Basuje ko inaba tunda jiya sukaxo, da yamma suka shirya suka dau motacin iri daya sak ita daya shi daya. Gidan Faty suka fara xuwa, bayan murna da kewar juna da mamakin girman cikin Mimi da Faty tayi suka rabu ta rako su gate. Mimi ta shiga Mota ta debo takaddun motar ta ciro key din ta bawa Faty tace "gashi takice na saya miki" Faty ta daskare ta kasa magana sai bin Mimi take da ido har suka tafi batace komai ba.

A gidan mama ma bayan murna aka gaisa, mama tace "sakko daga tudunnan in matsa miki qafar ta fara kumbura. Mimi tace "kafin nan xo muje kiga" sukaje qofar gida ta dakko takaddu da key ta bawa mama tace gashi mama asa albarka mota na sai miki. Mama sai hawayen farin ciki, suna tsaye saiga Faty a tata motar taxo nunawa mama dan abun baxai fadu a waya ba. Ta tarar da wata mamakin. Suka hadu suka dunga kuka sunawa Mimi adduar alheri, sulaiman na gefe na dubansu yana mamakinsu kamar su cinye juna. Baffa ya fito yaga motocin yace "tofa aiki game qareka, fadima haihuwa ta miki rana Allah ya sa albarka yasa a kashe lfy" matan gidan kuwa kamar wadanda suka gamo haka suka burkice basu wani boye baqin cikinsu ba. Mimi ta nuna musu cert dinta na NYSC tace "mama i m now a Barrister maryam, na cika burinki ko?" mama ta rungumesu duk tace "kun cika burin mahaifinku da ace yana raye da bansan irin farin cikin da xaiyi ba" Bature sun burgeshi har vedio yayi musu.

Washegari suka koma Abuja sabida aikinsa

Farida ta haihu, yayin da Mimi cikinta ke 7 months daga asibitin aka wuce da ita gidansu dake Abuja, wanda Umman ta taxo ta xauna da ita.

Mimi ta sameta gidansu ita da Bature, bayan gaisawa da yiwa juna barka Umma ta basu guri, Mimi kallon Farida take a tsorace ganin yadda ta rame a lokaci daya duk idonta ya xurma. Ta karbi Baby girl ce ta miqawa Bature ta koma ta xauna tace da Farida "Farida haihuwa da wahala ko? Naga duk kin rame" Farida tace "Tab, ai wahalar ma baxata fadu ba, nifa inaga mutuwa nayi na dawo. Wai a hakanma dan ya ishaq ya temaka mun dan yana tsaye kaina harna haihu. Kuma wlh ina dawowa hayyacina ke na tuna" Mimi ta dafe qirji tace "na shiga uku" ishaq ya harari Farida yace "ke ya isa haka, Mimi wasa take miki kowa da irin tasa haihuwar wani baya wahala"

Tundaga ranar Mimi can take yini, Kullum inxai tafi office yake kaita in ya dawo ya biya su taho tare. Ishaq ma can ya tare kwanciyar bacci ke dawo dashi nasa gidan. Ranar suna yarinya taci sunan Umman ishaq Hawwa amma suna ce mata Jidda.

Mrs Hajia 😊 [9/30, 1:05 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼AL 'AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼

Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)

📝FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 6⃣5⃣

Dedicated to ANTY SIS, MARYAM BAITA & NAJA'ATU NAFI'U (yar malam

LAST PAGE

Farida nayin 40 dayz Umma ta tarkatota ta dawo da ita dan tace tagaji da xaryar ishaq, itama ta tafi kano nata gidan.

Mimi ancigaba da rainon ciki, tafi duhu sosai irin na masu ciki wuyanta yayi baqiqirin ta kumbura kamar xata fashe. Mijin Kullum cikin lallaminta yake dan ta tsorata da haihuwa tunda farida ta bata lbri.

Ta fito daga wanka ta xauna gefen gado, yana kwance akan gadon, ta dan bigi qafarsa tace "ya Bature aramun t shirt dinka insaka da zani banasan saka gown xafi nakeji." ya tashi ya bude drawer ya dakko mata wata qatuwar t shirt dinsa yana cewa "sannu Mimi luv kin kusa in shaa Allah" ta saka rigar taxo mata har gwiwa. Tace "shikenan ma na huta daura xani" ta bashi dariya, amma baiyi a fili ba sai a ciki, baisan ta jishi ta hade rai tace "ai dole kaimun dariya tunda na gama yimaka amfani ka maidani haka" yayi rau rau, baiji dadin maganar ba, ya rasa abunda yasa Mimi ta xama haka abun kadan sai fada, yace "haba maryam, nasan ba haka na aureki ba nine silar komawarki haka kuma in shaa Allah kin kusa haihuwa kiyi haquri my luv" ta dan samu sauqi jin kalamansa. Ganin tana gumi ya qure AC amma duk da haka zuffa take. Yaje ya kira yadukko taxo taga yadda Mimi ke nishi da gumi. Tana xuwa tace "sulaiman wannan yarinyar naquda take ku tafi asibiti." tace "maryam kina jin ciwo?" tace "eh tun jiya amma ba sosai ba. Mamace tace in dunga daurewa" yaje ya dakko akwatin da suka dade da hadawa ya tattagi Mimi suka tafi. Sun sami ishaq yasa aka dubata nurse din tace tabbas labour take amma yanxu tana 1 stage da ragowa sosai. Haka aka kwana tun ciwo na qarami har ta fara jigata sosai.

Da sha biyun rana tayi washegari wanda Mimi tayi 24 kenan tana abu daya ya Taheer ya buga ya sanar da mumy dan tun akan rashin lfyar Mimi yayiwa kansa alqawari baxai qara dakata Bature ba a boye AL 'AMARIN MARYAM.

Bature kam baya cikin hayyacinsa kai kace shi yake labour din, sai shige da fice yake a dakin xuwa office din ishaq.

Dab da magrib saiga su mumy ita da mama da ya Faty, sukaxo da rubutu tsibi tsibi wanda aka karbowa Mimi a gurin malamai daban daban na naquda. Lokacin Mimi ta gama fita hayyacinta, aka dunga durawa Mimi rubutun. Bature kawai aka bari ya shiga dakin, su kuma suna tsaye a qofar cirko cirko daga ciki suna jiyo nishin Mimi. Ya fito yanawa su mumy bayanin har yanxu da ragowa amma xuwa 8 din dare inbata haihu ba xa ai mata CS. Nurse ta leqo tace yaxo, ya tafi Faty tabi bayansa amma ta hanata shiga, ta ciro ID card dinta na aiki ta nuna mata, ta barta ta wuce. Tasa safar hannu ta fara duba Mimi, tabbas da ragowa dan naqudar inta taho gadan gadan saita koma. Ta kalli Mimi cikin tausayawa duk tayi laushi ta hada xuffa kamar ruwa ya daketa tace "Mimi ki daure kiyi nishi Kinji" bata amsa ba. Bature yaje saitin fuskarta yace "maryam kiyi nishi ko kadan ne, daure kiyi danmu xaki kawo mana duniya" ta bude jajayen idanunta tace "baxan iyaba, numfashina iya qirji yake tsayamun baya kaiwa ciki kasan ina sonka da xan iya ya Bature da nayi" ya share kwallah aransa yace dama haka mata ke wahala wajen haihuwa.? amma wasu matan suyi ta haihuwa kamar mahaukata ko ciwon jikinsu basaji? A fili kuma yace "nasan kina sona Mimi, tunda kina wannan halin ma baki manta soyayya ta ba kuma kina wannan wahala ne don ki haifar mana sanyin idaniyarmu." ya miqe ya fita ya koma office din ishaq.

Ya daure fuska yace "ishaq na rasa dalilin da yasa kake haka, na rasa me Maryam tai maka kake mata wannan hukuncin. Kai lokacin da aka kawo matarka ai tsayawa kai ta haihu cikin sauqi, saini xaka azabtar da tawa, tun jiya take abu daya gashi tana neman kuma kwana duk qarfinta ya qare" ishaq ya dan diririce dan tunda aka kawo Mimi yaqi shiga dakin da take sai nurse da likitoci mata yake turawa su dubata. Shi anasa ganin xuwa kan Mimi a halin labour kamar keta alfarmar aminin nasa ne. Tun safe Bature ke fama dashi yaje yaga meya hana Mimi haihuwa a matsayinsa na babban likitan mata, amma sai sun tafi rimi rimi sun kusa xuwa dakin sai ya xame yace ya manta be dakko wani abun ba.

Ya kalli Bature yace "kayi haquri, na tura Dr Salma yanxu ta dubata inda matsala xata fada ko banjeba" Bature ya fusata ya buga table din gabansa yace "ishaq wlh in Mimi ta rasa ranta bisa wani dalili naka marar ma'ana Allah baxan duba tsakaninmu da kai ba makaka xanyi a kotu" ishaq yace "to Allah ya baka haquri muje in ganta" ya miqe ya fara duba lokar jikin table din kaman yana neman wani Abu. A zuciyarsa kuwa addua yake Allah ya kawo masa mafita dan bayaso ya keta alfarmar Bature ya duba masa mata. Dr Salma ta turo kofa tashigo, yayi hamdala a xuciyarsa tace "Dr. Na dubata, da naxaci fitsari ya hanata haihuwa amma na xuqe mata har yanxu shiru qarfinta ya ida qarewa inaga CS ya kamata atafi da gaggawa kan wani abu ya faru." Bature ya runtse ido, ishaq ya miqe ya dakko takadda ya tura masa yace kasa hannu xamu shiga CS da ita. Dr Salma ta fita bayan ishaq yace taje ta shirya Mimi xuwa dakin operation. Shima ya miqe ya fara saka kayan aiki, Salma ta dawo da sauri tace "Dr yanxu muka hadu da sister zubaida a hanya, maryam din ta haihu yanxu." ai kafin ta gama fada Bature tuni yayi waje yana hamdala. Yaje shiga dakin ya ganta a kulle an rufe ta ciki, ya juya ya kalli su mama suma fuskarsu na nuna alamun murna yace "suna ciki ne?" tace "eh su ukune ciki har Faty ta hudu" sunata xaman jira har ya gaji yaje yayo sallar da ake binsa beyi ba ya dawo amma basu bude ba.

Sai da suka kusa 2 hours ciki suka bude lokacin harya fidda tsammanin lfy kuwa? Suna budewa suka duru dakin, angyara komai qal dakin sai qamshin dettol yake. Anwa Baby wanka, Mimi ma anmata tana sanye da kayan asibitin dark blue kamar yadda dokar take me jinya bayasa kowane kaya se nasu. Tana kwance sunata daukar Baby ita kuma tana kallonsu tana murmushi, ta kafe mama da ido wani masifar san mama take a yanxu data xama uwa, ashe haka iyaye mata kansha baqar wuya kafin suga dansu? Gaskiyar farida da tace mutuwa tayi ta dawo. Duk Dan dabebi uwarsa ba ya shiga uku.

Mumy ta dubeta tace "sannu maryam, kin samu diya mace" batace komai ba sai lumshe ido da tayi, tayi baccinta sabida allurar da akai mata. Sama sama taji shigowar ishaq ana xuxuta kyan Baby.

Tayi bacci me yawa ta tashi batasan ko qarfe nawa ba lokacin, Faty ta rakata bandaki tayi brush ta canja pad kana ta dawo ta fada mata tea a qaton cup ta shanyeshi tas. Mama xaune da jaririya a hannunta tace a xuciyarta "wai yau nice riqe da dan Mimi? I kon Allah kenan, mimin da akasha fama akan neman mijin aure yau gashi abu ya wuce lallai komai yayi farko xaiyi qarshe, kuma komai lokaci ne"

Aka miqa mata yar, ta karba a kunyace tana kallonta, babu inda tabar mumy, kamarsu daya sak, sumar kantace kawai irinta Mimi dan gatanan a cike. Mumy tace "bata nono tasha tun daxu take tande baki da Bature ya bata dabino" Mimi tace "mumy ai babu ruwa" tace "bata haka ta kama xata xuqo" Mimi ta fara yarfe hannu tace "mumy wlh da xafi abata madara kawai" abu dai ya xama babba tun suna ganin abun wasa har ya xama gaske dan Mimi ta hana Baby nono. Suka fita xuwa office din likita dan tambayo wace madara ya dace a bawa new born Baby.

Bature ya taso bayan fitarsu ya kwanta kan gadon suka saka yar a tsakiyarsu, yace "dan bata nono Mimi luv, kinga inkika bata yanxu shine first anaso Baby ta fara shan nonon uwa dan ya wasar mata da kwalkwalwa, inkika bata shikenan sai acigaba da bata madara" tace "to" ya miqo mata yar ta xauna ta fara bata, tana cije baki dan da xafi, yana bata baki harta haqura ta saki jiki. Ya matso yana mannata a jikinsa ko anan aka tsaya burinsa ya cika, Mimi ta haihu dashi tana kuma shayar da diyarsu nono. Yace "Mimi kiyi haquri, naso ace yadda kika wahala sunanki na sakawa Baby, amma sai dai na riga nayi alqawarin saka sunan mumy tun sanda scanning ya nuna mace xaki haifa" tace "babu komai ya Bature nima nafison taci sunan mumy dan da mumy take kama kamar ita ta haifeta." yace "to nagode Mimi amma naji mumy tana cewa wai kamarmu daya ina jariri"

Faty ta shigo ta gansu ta koma da baya ta tarar dasu mumy riqe da takaddar madarar da likita ya rubuta tace "mumy ina xaku?" mama tace "sunan madarar xamu kaiwa Bature yaje ya siyo abata" Faty tace "to ku koma, Mimi dai da mukasha fama da ita ta bawa Baby nono taqi, gatacan mijinta ya lallabata tana shayar da diyarsu." mama da mumy suka kalli juna.

Sun shiga daki sun taddasu kamar yadda Faty ta fada musu, yana ganinsu ya sanfe yace "mumy takwararki aka samu HALIMATU" suka hada baki da mama sukace "mashallah Allah ya rayata" murnar sunan mumy da aka ya mantar dasu abunda ya faru.

Washegari aka sallameta suka wuce kano akabar Bature da kewar family dinsa.

A can kano gidan Baffa kuwa tun bayan sewa mama mota kowacce a cikinsu ta tasa yayanta gaba da takurar lallai suma sai sun saya musu motoci dan ba daya suke buqata, in sukai daya ai sunyi kunnen doki da mama. Yayan gaba daya sunyi karatun ta nutsu suka hada kai sukace basu da kudin siyan musu mota su bari komai lokaci ne, kuma ai akwai motar gida wacce Baffa ya siya ake kaisu duk inda zasu, bayan haka kuma sunsan mama a nata bangaren baxata daga musu kaiba sabida tana da Mota basu da ita.

Rashida kuma mijinta ya dawo tun bayan dashi da amarya kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta, ita kuma ta qeqashe qasa tace ai sun rabu kenan. Bai haqura ba yanata naci ita kuma tana yangwanashi.

Mimi jego ta samu irin na mutanen da, mama macece me kula da Dá ko ruwan sha sai ta tafasa take bawa Mimi tasha. Tsakaninta da Baby kuwa sai dai in bata nono xatai, Kullum tana bayan mama. Mutane kota ina barkowa suke, fauxa taxo daga Lagos kuma ta kawowa Mimi wani yoruba lace irin wanda suke sawa a event dinsu 15 yards, kana ganin lace din kasan tsayi masifar tsada kuma duk wanda ya badashi a matsayin kyauta tabbas hannunsa ya cudi baya. Daga ninta kasan ta fara kama qasa harda motarta taxo wacce sunusi ya siya mata. Mimi ta dunga murna, mama ta karbi lace din takai shagonta na dinki wanda ta bude ta xuba yara maxa. Suka dinkawa Mimi buba da xani Bature kuma sukai mai irin dinkin yarbawa. Alheri kota ina barkowa yake. Bature ko tsinke bai saiwa Baby ba, Anty mami ce tayi komai har kwanan da Baby xata fara cin abinci in aka yayeta sai data aiko dashi. Ranar suna Audu ya kawo Sá da rago aka yankawa HALIMATU wacce little ta fara kiranta da MIMA. Ranar suna da yamma ya iso, Mimi ta bashi lace din fauxa ta fada masa fauxace ta kawo musu ya karba ya saka sanin matsayin fauxa gurin Mimi, itama ta saka aka dunga hotuna yana riqe da Mima. Fauxa taji dadin saka kayanta da sukayi.

Ta cigaba da rainon mima ita da mama, kuma a xamanta da Rashida ta dunga bata shawarar ta yadda ta koma ta haqura kodan Dan dake tsakaninsu. Taji shawarar Mimi, ta tatseshi kudi sosai kafin ta yadda a qara daura aure ta tare. Amaryarta dole ta kwantar da kai aka xauna lfy domin yanxu ita yakewa wulaqanci akan Rashida. Dama hausawa sunce bulalar da aka daki uwar gida da ita tananan tana jiran amarya dan haka ki dena murna dan mijinki na wulaqanta kishiyarki akanki dan wata rana ke xai wulaqanta.

Mimi tayi tas tayi kyau dake ansamu jego original, tayi shar kamar bata haihuba, tana yin arbain yaxo ya kwana suka koma tare. Mama ta dunga cewa su kular mata da mima, dan kowa yasan yadda mama ta dorawa mima son duniya fiye da komai a yanxu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull