Kenza eBookz

Al'farma complete Novel - Chapter 18

Al'farma complete Novel - Chapter 18

Al'farma complete Novel Chapter 18: Al'farma complete Novel Chapter 18. Comments and Share

1,157 words

Comments and Share

MOMMYN TWINS CE

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ALFARMA

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

🅿99👉🏻100😥👋🏻

T.H Hospital mukatafi, muna isa direct labour room akawuce dani,Ya IB narike da hannuna koda akazo shigadani room d'in saida Mommy tayi dagaske kafin Ya IB yasake hannuna dan kafewa yayi yace sam saidai mushiga tare,Mommy tace masa akwai matan aure dayawa aciki suma labour sukeyi baikamata yashiga kansuba, zuwa lokacin fadar kalar azabar danake ciki bazai misaltuba,

Minti 30 da shigata kand'a yasako kai wayyo ALLAH! Ubangiji yakarawa mata juriya da jarumta,yau nad'an-d'ana azabarda duk wata uwa takesha kafin tahaifo d'iyarta, dataimakon nurses dan ya idda fita,suna zaroshi wata sabuwar nakudar tatashi,cikin ikon ALLAH banwani dau lokaciba wani dan yakuma sakokai,nan suka kuma janyoshi,nan take yaran suka gauraye room d'in da kuka,numfashi nashiga saukewa inayiwa ubangiji godiya,saida akakai yaran gun manyan likitoti sukaduba lfyrsu kafin suka dawo dasu suka shiryasu cikin kayan tsanyi,saida suka gama kafin sukafito sukasanarwa su Mommy cewa nahaiwu tahaifi Baby twins,ai dasauri Ya IB yakusa kai zaishiga labour room din nurses d'in sukadakatar dashi,tahanyar cewa bamatarka kadai cikin room d'inba kajira yanzu za'akaita dakin hutu, Mommy kam bakinta yakasa rufuwa sai hamdala takewa sarkin halittu,

Bayan sun kimsani da duk wata kula dayadace subani sai akayidani dakin Hutu,nan Ya IB da Mommy sukasami damar ganina,yakwashe yaran yarungumesu akirjinsa yakasa boye tsantsar farincikinsa agaban Mommy yahad'ani dayaran yarungumemu.yace UMMU RUMAINA kingamin komai arayuwa yara biyu kika haifomin lokaci guda.saiya sakeni yajuya gun Mommy yace Mommy kitayani yawa Baby godiya kiduba kiga kyawawan y'ay'an da tahaifamin,murmushi Mommy tayi takarbi d'aya ahannusa tanafadin masha ALLAH ubangiji yaraya manaku da imani,

Kankace me y'an uwa da abokan arzikin familyn IB NAKOWA suncika Hospital din, ganin haka yasa Dr zuwa yaduddubani ganin babu wata matsala saiya bamu sallama, muka tarkasa mukakoma gida.

Tuni labarin haihuwar ya'iske su Mama,sunyi farinciki mara misaltuwa, washe gari Umma Halima tazo nayi murna sosai daganinta,Hajja Umma da Mommy da Hajiya Maryam kanwar Mommy sai Umma Halima dukansu suke kuladani, Ya IB kuwa kullum muna tare dashi saidai idan yan barka sukazo,bayanda ya'iya haka zaifita,yanafita kuwa zaikirani awaya yacewai nasanyawa yaransa wayar yarikajin numfashinsu..

Gata iya gata nagansa ahaihuwarna sai nan da nan akedani motsi kadan za'atanbayeni kodawata matsalace,

Amarya Ummee sunzo da angonta Anas, Khadija ma tazo,sai dare mazajensu suka maidasu gida.Basma kam kullum muna tare da ita tanalike ajikin yaran, Kwana uku da haiwuwa Ya IB yayiwa yaran huduba,Hassan akasanyama Basheer wato sunan mahsifinsa,yayinda yasanyawa Hussain sunan Babana wato Adam, Za arika kiransu da Juhaim da Junaim,

Tun ana saura kwana uku suna Ya IB yasa akarika kawo kayaki d'aki guda akaware nashirge kayan,har ranar suna ba'afasa shigowa da kayakiba,ganin yanda ake shigo dakaya kamar bada kid'i aketsayaba,nakirawosa awaya nace kayanna sun isa haka meza'ayi dasu haka?yace akwai wasuma dayasa asaya a Switzerland sunacan.nace todai abarsu haka,yace angama madam duk yanda kikace hakan za'ayi.

*********** Ranar suna anyi bidiri da bured'e dankuwa duk girman BAUCHI saida tadauka,bakaramin kudi Ya IB" da Mommy suka narkaba, Su Mama ma ba'abarsu abayaba suma sunyi kokari sun zuba bajintarsu dai-dai iyawarsu, Kyaututtuka kam nasamesu ba'adadi,dan hatta gwomnatin BAUCHI, nasami kyauta daga gareta tasanadiyar Ya IB"

Anyi taro anwatse cikin kamala da mutunci,bayan suna dakwana biyu Ya IB yatafi Switzerland sakamakon kiran dayasameshi na gaggawa, Yan uwanmu da sukazo daga Bokos sukanimi tafiya dani naje nayi wankan gida,Mommy tasanarwa "Ya IB yace sam baiyardaba yara basuyi kwariba suje susha iskar mota harsudebi wata cutar,baitarda atafi masa dayara ko inaba yanzu,

Mommy dai hakuri tabasu Umma Halima tareda alkawari har idan mukayi arba'in zanzo..

Kullum muna makale da Ya IB akwaya munazuba soyayyarmu son ranmu,

**********

Bayan arba'in

Ranar da mukayi arba'in,nashirya kayana nazuwa Bokos, washegari Mommy tasa driver yadaukemu nida Basma tarike Juhaim,maisunan daddynsu,nikuma inarike da Junaim, maisunan Baba, batareda bata lokaciba muka haura hanya.

Koda muka iso Bokos narika baza idanuna ahanya,muna isa unguwarmu kuwa nasha mamakin sauyin da akasamu tundaga farkon layin harzuwa kofargidan da driver yayi horn abakin get d'in gidan, Wani dattijo yataho dagudu yawangale get d'in, a parking lot yadaidaita Parking mukafito nabude baki zan tanbaye driver inda yakawomu, saina hango Hafsat dagudu tafito tanafadin oyoyo Aunty RUMAINA sun'iso.ta'iso takarbi Junaim tace sannunku dazuwa, tayi gaba mukabita abaya,zuciyata cikeda tanbayoyi shin wanna wani gidane,munashiga nagama Mama tsaye atsakar gida tana ganinmu tafad'ad'a fuskarta da murmushi,tace lale sannunku dazuwa, kushiga tanunamana wata kofa,wata lafiyayyiyar parlour muka shiga cikinta muka zazzauna saman lafiyayyun kujerunda suka Kawata parlour, Mama tashigo takawomana abubuwan ci dasha,mukaci mukasha,kankace me yan'uwa da abokan arziki sukarika tururruwan zuwa yimana barka dazuwa dakuma tayamu murnan samun karu, Yamma lis Baba yadawo gida shima yayi farin ciki daganinmu, yadibi yan jikokinsa yayita sanyamu albarka. Da daddare baya kowa yawatse muka kebe da Mama nan take sanarmin tulin alkhairin da "Ya IB yayi mana take kuma sanarmin shiyaturo ma'aikata akarushe gidanna akagina wanna ginin,nasha mamaki dankuwa Ya IB baitaba yimin hirarba,nan naji sonsa nadad'a yimin yawo acikin zuciya.koda nakoma dakin dazamu kwana nakirasa dannayimasa godiya akan alkhairin dayayi mana sai cewa yayi indai bawata magana nakeda itaba to sai anjima..

Kwananmu uku Basma suka koma da driver sukabarni anan, Nazaga gidan yan'uwa sosai.kwanana 20 agidanmu Ya IB yazo babu sanarwa.haka aranar yace bana kuma kwana sai a BAUCHI,nayitayimasa magiya akan yabari mukara koda kwana d'ayane yace baiyardaba, su Mama ko komai basuceba,haka yakwashemu muka tafi.

Kodamuka isa duk yanda yaso mukeb'e firnaki dan ina cikedashi,kwananmu hud'u da komawa yashigo bedroom in Mommy inazaune abakin gado ya isa yazauna kusa dani,batareda yakalleniba yace kishirya gobe idan ALLAH yakaimu zamu koma Switzerland,nakar da kaina gefe nayi kamar banji abinda yafadaba,shiko baikuma cewa komaiba saima mikewa da yayi yaje gaban gadon Juhaim da Junaim,yarika lilasu harsaida sukayi barci yagyaramusu rufuwa yatofesu da addu'a kafin yafita.......

Karfe 4 na asuba jirginmu yatashi zuwa Switzerland,koda muka isa masu taranmu suka debebu zuwa gida,tun isarmu gida dayafita bankuma ganinsaba sai bayan sallar isha, lokacin har Juhaim da Junaim sunyi barci, nima nayi shirin barci inakokarin kwanciya yashigo da sallama,na'amsa tareda hayewa gado nakwanta najuya fuskata tacan, tube kayan jikinsa yy yafada bathroom yy wanka sanna yafito yasanya rigar bacci mai madaurin igiyoyi tagaba,sanna yahaye gadon,yadagoni cak yadaura samansa yasanya hannunsa yazagayeni dashi,asannu yayi magana acikin kunnena,kitaimakeni kidaina fushi dani kiyimin wanna AL'FARMAN narokeki,kaina najuya nahadefuskarmu yanayin yanda yayi maganar saida tsigar jikina yatashi yarrrrr,nace Ya IB nima nakasa jure fushi dakai dan ALLAH kayafemun naroki AL'FARMAN ka,goga fuskarsa yy anawa sanna yake dan ALLAH kicigaba da yimin AL'FARMA irin haka Baby,nace Ya IB indai wanna shine AL'FARMA to zanci gaba dayimakashi har karshen rayuwata,cikin tsananin farin ciki yahade bakinmu daganan zancen tasauya muka lula duniyar maji dad'i.

TAMMAT BIHAMDILLAH👏🏻

TO MASU KARATU AYAUNE NAKAWO KARSHEN WANNA LABARI NAWA, MASOYANA INAYIMUKU FATAN AL'KHAIRI SAIMUN SAKE HADUWA DAKU A LITTAFINA NAGABA,NGD NGD NGD MATUKA DA SOYAYYAR DAKUKA NUNAMIN RABBI YABAR KAUNA💓

MOMMYN TWINS ZANYI KEWARKU👋🏻😥

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull