Kenza eBookz

Al'farma complete Novel - Chapter 17

Al'farma complete Novel - Chapter 17

Al'farma complete Novel Chapter 17: Al'farma complete Novel Chapter 17. """"""""""Ahankali nace hello maiwayar tana lazumi, saidai zuwa anjima akuma…

3,441 words

""""""""""Ahankali nace hello maiwayar tana lazumi, saidai zuwa anjima akuma kira.cikin hatsala yy magana da fada fada yace akirani nabiyo kiran sanna ace wai maiwayar tana lazumi dan rairin wayo oya mikamata wayar yanzunna.cikin hanzari namikamata wayar inafadin ance nabaki wayar tana karba sainayi saurin mikewa nafice adakin.inashiga bedroom dina nazube saman bed nadafe kaina danaji keyimin azabebben ciwo innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un.kadai nake iya nanatawa jin muryarsa baihaifarmin dakomaiba illa tashin hankali da matsanancin damuwa,toshe kunnuwana nayi dasauri jin muryarsa nayimin zarya acikin kunnuwana, Juyakaina narikayi inafadin kai amma kaicona,nantake najinayiwa kaina mummunar tsana waimeke faruwa daninekam?karya zuciyata takeyimin banasonshi banasonshi zuciya bakiyimin adalciba kinsanko wacce kike damuwa akansa?mutuminda akadauramin aure dashi tun shekaru da dama dasuka wuce amma kosaudaya baitaba taka kafarsa danyaje gareniba baimasan ina duniyarba shine zakinuna damuwarki akansa shine zaki dau sonsa kidaura min alhalin shi basona yakeba inda yana sona ko yadamu dani dayajegareni tuntuni,tonima banasonsa karya zuciyata takeyi banasonka bazankuma sokaba'zuciya bakiyimin adalciba..sosai nadage narika sharbar kuka ahaka baccin wahala yy awon gaba dani.washegari kodana tashi bayan nayi sallah sainakuma kwanciya kasancewar munsamu hutu a schools, karfe 10:00am nafarka nafada bathroom nayi brush sanna nayi wanka nafito nazauna gaban mirro nan nashafa mai da powder sai eye pencil danadan goga.duk motsin dazanyi sainaji zuciyata tamotsa datunamin dashi,niko saikokarin boye damuwata nake inakuma tirsasawa zuciyata akan sam basonsa nakeba,haka harnagama shiryawa nafito parlour "ba'i ne birjib a parlour maza da mata,gataren labulaye hadeda karafunsa birjib asakiyar parlour,Mommy rikeda waya akunnenta tanafadin OK harkun isa to kushigar da su duka cikin parlour din yanzu masu gyaran zasu tawo tana kaiwanan tasauke wayar tadubi mutanenda suke zaune agun tace masu kai kayan harsun isa gidan saikuje dan kufara da wuri toh Hajiya duka suka amsa dashi,sanna suka mike mazajen suka kwashi tarin labulayen da karafunansu suka fita, ahankali na isacikin parlour nagaida Mommy ta amsa sanna tace yauwa yimaza kiyi breakfast kije gun Asma'u yanzunna dama yanzu zanje natadaki kenan..kai najinjina jin zuciyata ta lalace dajin wainaje gun Aunty Asma'u ni wanna shan maganin nadamina,inagama breakfast na nufi part din su Aunty Asma'u " tahada magungunan tabani nayau hardawasu kaloli nadaban,saiwajen azahar nabaro part din..... Yamma lis wadanna mutanen dazun din sukakuma dawowa nan sukesanarwa Mommy cewa sungama aikin komai kuma yy daidai harsuka nunamata video dasukayi nakayakin dasuka tsarashi yanda yakamata,lokacin duk muna parlour Basma tatashi tazo kusa da Mommy tana kallon video din karbar wayar tayi ahannu ta tanafadin kai amma wanna tsarin gidanna yayimugun kyau, kallakigani Aunty RUMAINA sama white & black.. Kasama bedroom & parlour da kitchin white & yellow bakaramin kyau yyba,naleko cikin wayar masha ALLAH nafada dan bakarya ya tsaru iya tsaruwa,nace kai amma wlh yy kyau sosai"duk wanda yakarbi wayar kuwa saiyayaba tsaruwa da kyan gidan.nan Mommy tasallami mutanen datarin alkhairai masu yawa sukayimata sallama hadeda godiya sukatafi.... Ana kiran sallar magrib mukawatse a parlour... Sosai nadage wajen yaki da zuciyata danganin tadaina tunomin shi"nakuma yajircewa wajencewa Sam basonsa nakeba,duksanda tunaninsa yafadomin saina sawa raina cewa shifa baidamu daniba hatsalima baisan ina duniyarba inda yasani da tuni yanimi inda nake tuntuni,dawanna nayi yake wajen yakaceshi sosai acikin raina"saikuma tunanin Ana's yafadomin ALLAH sarki My Nass masoyi nakwarai koyana wani haliyanzu?sainaji hawaye yagangaromin.dakarfi nafurta dan ALLAH My Nass kagafarceni wlh banada ikon yin komai akan komai My Nass kafahimceni dan ALLAH saikuma nafashe da kuka,inacigaba dafadin wlh My Nass bansan yanda akayi naji sonsa alokaci dayaba kuma Kaduba zuciyata zakaga son nasama yafita danshi baicancanci nasoshiba,dan ALLAH My Nass kayafemin kayafemin narokeka..sosai narika kuka kamar raina zaifita haushin kaina da haushin ***I'B sukataru suka tokaremin zuciya lallai naci amanar Ana's dahar na'iyajin son wani bayanshi My nass dina kayihakuri nadaina sonshi wlh nadaina.... Nan take zazzabi maizafi yarufeni ,haka nakwana da matsanancin zazzabi" Washegari ganin harrana tayi banfitoba yasa Mommy lekoni ganin halin danake ciki saitakirawo Dr yazo yadubani tareda bani magunguna dayimin allura,zuwa yamma jikin yadan sakeni harnadan iya cin abinci..dukda rashin lfyr danake baihana Aunty Asma'u narkamin magun gunan nanba........ Yau sati na biyu kenan dakwanciya rashin lfy kuma haryanzu bawai naji sauki sosaibane inanandai haka wata sukuku,inazaune a bedroom dina akayi sallama tareda turo kofar na amsa sallamar nadago ina kallon masu shigowar,Mommy ce dawata mata yarbabba batadai kai Mommy girmaba,sukashigo ciki matar ta aje jakar hannunta gefe tazauna bakin gado ,nagaida matar ta amsa cikin sakin fuska. Mommy tace to hajiya lami' yanzu za afara kenanko?tace insha ALLAHU,Mommy tace OK. tadubeni tace RUMAINA wanna maigyaran jikine yanzukuma zatafara aikinta,nidai kallonsu kawai nayi da ido,hajiya lami tadubeni tace kinci abinci?kainagirgiza mata alamar a'a ,tace wa Mommy to akawomata abinci taci dan idan akafara babu tashi.Mommy tace toh tafita tasa Goggo Larai tahado abinci takawo,nadanci kadan sanna naje nawanje bakina nadawo, hajiya lami ta isa jikin kopa takulle nidai kallon ikon ALLAH nake tadawo tace natube kayana fir naki datagadai banada niyyar cire Mayan saitakirawo Mommy awaya Mommy nadagawa tace toh Hajiya tafaki cire kayanta saikiyimata magana kozataji,Mommy tace tabani wayar kodana karbi wayar saitarika lallabina tanafadin kamshifa zakiyi kumanasanki da son kamshi Dan haka kitube kada kidamu kinji toh nace da ita sanna namikawa Hajiya Lami wayarta nashiga tube kayana safnacire amma banda pant da bra na tashiga mulkeni dawasu fitanannu kayakin kamshi tundaga sama harkasa tamulkane tsafdasu,sanna tamikamin robar datayihadin aciki tace togashi kishafa lungu dasako na inda bakyaso naganinna takarashe da murmushi nakarbi robar inajuyashi ahannuna "saita juya bayanta tanafadin kishafa yanda yakamata.inbahakaba nakarba nashafa miki dakaina ,ganin tajuya baya cikin sauri nayi kasa da bra na nashiga murzawa kamar yanda takeyimin ajikin sanna namaida bra din nakumayi kasa da pant din shima nashafa lungu dasako kamar yanda tacemin, inagamawa nace mata nagama.tace toh nan takuma hadawasu sinadaran cikin cup tamikamin tace nashanye duka ,nakarba inakwabe fuska nashanye dakyar...... Yau wunin daki mukayi koda lokacin sallar azahar yy saitashiga bathroom tahadamin ruwan wanka acikin bath tafito tace najenayi wanka kuma idan kinje kishiga cikin bath din kizauna saikinkai kamar 30min saikifita saikiyi alaula. Kodanashiga cikin bathroom din wani azabebben kamshine ya bigi hancina shikansa ruwan wankan wani kalane nadaban yanda tafadamin haka nayi saida nayi 30min cikin ruwan kafin nawanke jikina da sabulun data aje age kafin nafita nayi alaula nafito,bayan nagabatar da sallah takuma mulkeni kamar nadazu" haka mukatayi duk lokacin sallah idan yy saitaje tahadamin wanna zuwan turare hade dana maganin..... haka Kullum muna daki banafita konan dacan Aunty Asma'u ma tana zuwa kullum takawomin kalarnata maganin.... Ahaka mukashafi sati biyu,nikaina idan nakalli kaina sainarikagani kamar banibace,... Ana gobe zamucika sati biyu akulle adaki ranar hayaniya narikaji sosai acikin gidan washegari kuwa sai hayaniya da zirga zirgar mutani yazarce najiya,yau tunda safe naga Hajiya lami tahada yan kayakinta zuwa ala'asar tacedani naje nayi wanka tahadamin ruwan wanka.bayan nafito nagabatar da sallah nazauna inazaman jiran tazo tafara aikinta sainaga tadau mayafinta tayafa tareda daukar jakarta tarataya sanna tadubeni tace acikin wardrobe dinki nadakin sama idan kk je wanna shine makullinsa tamikamin wani key nakarba inajuya key din ,tace wanna shine makullin daya dagacikin marfin wardrobe dinki,akwai kayan gyaran jiki dana ni 'ima kamar yanda nakeyimiki amfani dasu haka zakicigaba da amfani dashi.kallonta nayi cikin rashin fahimta..tace toh ALLAH yabaku zaman lfy niyau aikina yakare zankoma gida,tanakaiwanan tayimin sallama tafita... toh waimetake nufi kenan?..................

Comments and Share

MAMYN TWINS CE [10:03am, 11/03/2020] Rashida: 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ALFARMA

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

🅿85👉🏻86

""""""""""Duka suka maida kallonsu kaina Mommy tace jin ciwo kuma garin yaya?harara yadallawa Basma ai bashiri tabar gurin.kunya yagama rufeni kamar katsa tatsage nashige ciki haka naji,ahankali na isa cikin parlour Mommy datunda nafara tafiyar takuramin ido harsaida nazauna kafin tajuya dakallonta ga ya***I'B ,shiko fuska yamurtuke saiwani muzurai yake,Mommy tadubeni tace meyasameki akafa?sunkuyar dakainayi inawasa da yan yasuna..Hajja Umma tace yoh tayuwu wanna mijin nata maikamada kububuwa shi yahangizota daga saman bene tafado tabuga kafar yoh inbahakaba atanbayeki kiyishiru,Goggo Larai tace kaihaba Hajja Umma ai idan aka turo mutum daga saman bene saidai karyewa ba buguwaba watakiladai kotayi tuntubene, mikewa Mommy tayi tariko hannuna tanafadin zomuje nashafamiki magani akafar zata warwareki,namike tsaye muka nufi bedroom dinta.kodamukashiga saita nunamin bakin gado tace zauna inazuwa,toh nace da ita, saitashige bathroom jim kadan tafito tadubeni tace rage kayan jikinki kishiga bayi nahadamiki ruwa saiki shigaciki kinji inazuwa tafada tana fita daga dakin,tunda tafara maganar kaina kesunkuye saijinayi kamar nasanya hannu akai nayita zandara ihu,shikenan Mommy tasan abunda yafarukenan sainaji hawaye yacikamin ido,ahankali namike narage kayan jikina nashige bayin ruwa nagani cikin bath din saina cire ragowar kayanda kejikina nashige cikin ruwan,maidauke dasinadaren kishiri aciki,sosai ruwan yarika ratsani dukda zafin danakeji hakanadaure najima sosai aciki harsaida naji ruwan yawuce kafin nafita,abin mamaki sainaji zafin yaragu sosai bakamar dazuba,nadaura zanina nafito namaida kayana inazaune Mommy tashigo daukeda tray tadire bisakan table dindake gefen bed in.tazauna tareda turomin plt maidake da parpesun kayan ciki mairuwa ruwa wanda yaji yaji da kayan kamshi saitashi dakamshin kayan yaji yake gefekuma cup ne maidaukeda kunun gyada shimadin sai tururi dakamshin kayan yaji yake,nidai kaina nasunkuye dan gabadaya kunyanta nakeji,tace cimaza saikisha wanna kunun tadada matsomin da plt din gabana"asannu nafarashan perpesun aiko kankace me zufa yashiga sassafamin bashiri na aje cokalin,ina waige kozanga ruwa nasha ganin babu ruwa kusadani saina dauki cup din kunun nakafa abakina shanruwa nashiga yimasa aishi ma a70 na'aje ina jan yaji"tace yimaza kicinye aizafi shike cire zafi..haka bayanda na iya nacigaba daci harsaida nacinye duka tadau cup din tamikamin shima tace nashanye duka haka nasha kamar kaina zaibude, sai nishi nake dankuwa cikina yacika sosai,takwashe yakin tafita..ahanka nakwanta gefen bed din nalumshe idona.... Mommy nafita Rukayya tayi saurin karbar tray din hannuta takaisa kitchen kodatadawo dakinta tawuce,Goggo laraima tatafi nata dakin,Hajja Umma kam tundazu tawuce daki acewarta waibatason ganin sa dayakeyimata muzurai kada yacinyeta danye .... Mommy ta isa tazauna bisa kujerarda tatashi,tadubi ***I'B daketa latsar wayarsa tace tun dazu akakawo maka abinci amma bakaciba,ya'aje wayar gefensa sanna yace Mommy ina UMMU RUMAINA take ita bazataci abincin bane?harararsa tayi tace itataci nata kaidai kaci naka kawai,yace au Mommy abunma wariyace shine zaki kaita daki kibata maidadi toni meyasa bakibani irin natanba"masacan kabani guri dakagamayimata mugunta shine zakace wani nabaku abinci iridaya, ai wlh kakuma yimata mugunta irin haka zan dauki diyata kajecan kakarata badunma yarinyar maidauriyabace aidako tabuka komai bazata iyaba.. Kai yasunkuyar tareda sosa keyarsa saiyanzu yafahimci inda zancen Mommy yadosa aransa yace wai maidauriya inajaruman anan yardatayi tamin ihu kamar wanda yankata nake,saikuma yadago yanacewa ayi hakuri barinaci wanna din haka,tace dadai yafi akasan rantakuma farincikine falciki tanabin yaran da addu'ar dauwamar farinciki arayuwar aurensu,saidai taji tausayi RUMAINA kasancewarta yarinya dan tasan tasha wuya sosai..nan yafaracin abimcin sunadan taba hira nan yake sanarmata gobe zaitafi Switzerland,tayimasa fatan alkhairi.kodayadagama cin abincin yayita zuba ido kozaiga fitowarta amma shiru saiyamike yacewa Mommy bariyaje wani guri yadawo.tace toh adawo lfy... 2:00pm nafarka daga barcinda yadaukeni,alaula najenayi sanna nagabatar da salla,inabisa sallaya Ummee da Basma suka shigo sosai nayi murnan ganin Ummee amma saina bata rai namike naninke sallayar na aje sanna nazauna saman doguwar kijeranda ke gaban gado nabasu baya ,murmushi Ummee tayi tazauna kusadani tareda dafa kafadata tace Bad'd'o banza nayimata, tace haba tawan dadai kintsaya kinji uzurina tukun saikiji dadin yin fushin,nace bubu wani uzurinda zaki kawominshi dan kare kanki nayarda ai daman nasan abunda zakice kenan nidan ALLAH rabudani,kai Bad'd'o kedai kisayakiji ranna nashirya zanje gidanki nazo Basma tarakani shine tace wai ita bazataba kada taje ya***I'B yakuma koranta koma yabigeta shine nima naji tsoro kada naje yakoreni,nace dake kunmaidashi mahaukaciba dole kuce haka, haka kawai bakuyiwa mutum komaiba saiyakama dukanku,hada ido sukayi sanna suka fashe da dariya harda tafawa, Ummee tace hmm kaji masu miji. Basma tace aikam harwani kareshi take saikace batasan halinsaba, nace kudai kukasani duk wani abunda zakufadamin bazanyarda dashiba.toshikenan tunda bakiyardaba mudai gaskiya mukafada miki cewar Ummee"tasunkuyo tanafadin garin yy kikaji ciwo akafarki Basma ce kefadamin.kallon kafar nayi saikuma nace jiyane nazame bathroom buguwace kawai,tace to ALLAH yasawaka.ameen nace, nan muka bude shafin hira koda la'asar tayi adakin mukayi salla muka kuma cigaba dahirar...har lokacin sallar magrib yy Mommy tashigo tace kutashi kujekuyi sallah toh mukace... bayan mun idar.Ummee tace baritaje part insu tadawo kafin lokacin tafiyarmu gida yy,Basma itama tace baritaje tayi wanka,duk sukafita,Mommy dayanzu fitowarta daga bathroom tace dani jekikuma gaza jikinki dan kidadajin karfin jikinki sosai"na'amsa cikedajin kunya ,kodanashiga bayin sosai nagasa jikina.nakumaji dadi fiyedana dazu nayi wanka sanna nafito..zaune nataddashi shida Mommy ahankali namaida kofar narufe yadago aiko karaf mukahada ido sainayi saurin sunkuyar dakaina kasa,ahanki natako na isa bakin gado nadau hijjab dinda dazu nayi salla dashi nasaka,yisauri kishirya mutafi dare yy yayimaganar idonsa akaina,Mommy tace a'a ita ai anan zatakwana harsaitaji sauki kafin"ido yawaro Mommy saitaji sauki kuma ay lfyrta kalau, kuma ay Mommy saikuma yy shiru ,Eh dole kace lfyarta lau to barikaji anan zatakwana kaidai katafi abinka"bakaramin dadi najiba dajin abunda Mommy tafada,saina zauna bakin gadon nakishin gide harda yar murmushi na.shiko cewa yake gobefa zamuwuce to idan yanzu bamuje munyishiriba gaben yaushe zamu samudamar yin shirin cikin nutsuwa?,tace nidai nafada maka katafi kawai abunka saita mike tsaye tanafadin tonidai barinaje nayi alauna tafada tareda shigewa bathroom, binbayan Mommy yy dakallo hartashige saiya mike dasauri yazo indanake,cikin hanzari namike zaune ganinyanda ya iso kamarzai fadomin akai.fincikoni yy yamikardani tsaye yahadani dajikinsa yayinda yasanya idanunsa cikin nawa,cikin kasadamurya yace harkina murna dan tace anan zakikwana,saiyadaura yasar hannusa akan Lip dina yana zagayishi asannu yatura yasar cikin bakina saiya lumshe ido tareda sake waresu akaina,yace har barcin yau zaiyimiki dadi bayan bakitareda mijinki?yayi tanbayar yanamaicigaba da juya yatsar cikin bakina,yadaura dafadin zanbarki yau kadai kozuwa gobe zakizamo jaruma kikwana dashirinki dan gobe hmm,saiya zare yatsar cikeda wani irin salo,yayi kasa da hannunsa yadaga hijjab din jikina sama saiya kunce daurin kirjin danayi yy kasada zanin yasunkuyo dakansa yamanna bakinsa kan nonona saiya zuko saiyakuma sakewa yakama dayan shima yazukoshi,sanna yabi kowanne da kyakyawar kiss,saiyadago asannu yadaura bakinsa kan Lip dina yacafke yarika tsotsa,kokarin kwatar kaina nashigayi jin motsin ruwanda Mommy ke alaula dashi yatsaya.dakyar nakwace kaina nayi saurin jadaba,aiko lokacin Mommy tabude kupar numfashi nasauke taredayin hamdala araina,takaraso ciki tanafadin bakatafiba haryanzu,yanzu zantafi yafada tareda shafa sajen faskarsa,yayimata saida safe saiya kalli gefendanake sainayi saurin kawar dakaina gefe,saiyafita numfashi nasauke tareda komawa nakwanta............

Comments and Share

MOMMYN TWINS CE [10:03am, 11/03/2020] Rashida: 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ALFARMA

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

🅿87👉🏻88

""""""""""Washegari bayan nayi salla nakuma komawa nakwanta,karfe 9 Mommy tatadani ta umurceni danaje nakuma gasa jikina kodanaje bathroom din bayan nagasa jikina sainazarce dayin wanka kafin nafito" zuwa yanzukam sosai nadaina jin zafin harnakan mance dawani abu yafaru,simple makeup nayi harnadau kayana danazodashi jiya ajikina zankuma maidashi sai Mommy tace ay ga kayan dazakisanan abayanki,nawaigo danganin kayanda take nunamin din,watah garnanniyar atamface dinkin riga da sket kallo daya zakayiwa atamfar kasan bakarama bace,nadauka nasaka sanna naje gaban mirro nafesa turaren Mommy nadaura dankwali saina koma nazauna.jim kadan Mommy tashigo daukeda kayan breakfast tadireshi saman table,tace gyara maza kici yanzu nace toh saitafita.nagyara zamata nafaracin lafiyayyiyar break dinda Mommy tashirya da hannunta,dasallamarsa yaturo kopa,na amsa sallamar batareda nadagoba kamshinsa yaharwaye dakin asannu nalumshe idanuna tareda shakar daddadan kamshinsa,bansan isowarsaba sai jin sa nayi yazauna dafdani asannu nabude idanuna cikin kasa da murya nace inakwana,yasakala hannunsa tabayana yadada masodani jikinsa sosai,An'tashi lfy?yakwanan kadaici da sanyi?shiru nayi bance dashi komaiba,yasunkuyo da fuskarsa yaleko fuskata saiyadan shafi gefen fuskata da alama kinsha sanyi yau dakinbi mijinki jiya dayabaki dumi maigamsarwa,naturo baki gaba araina nace saikace kullum dashi mukekwana indai wanna duminne banaso.saiyagyara zamansa yasanya hannu mukacigaba dayin break din tare,koda muka gama saina kwashi kayakin nakaisu kitchen kodana dawo dakin saina taddashi tsaye rikeda mayafina ahannu yanaganina saiyayi saurin masowa inda nake yasanyamin gyalen akaina saiyariko hannuna yanafadin taho mutafi lokaci zaikuri"binsa dakallon tanbaya nayi kannace wani abu Mommy dayanzu shigowarta tarigani fadin ina kuma zaka kaita bayan kasan balafiya garetaba,yace Mommy wani rashin lfy kuma kokinmance 11:30pm zamubar kasan,kiduba kiga yanzu 11:19pm,zatakuma magana saiyayi saurin sakin hannuna yakariko na nata yace Mommy da itazamutafi dole saboda wanna time din bazan samu damar kuma zuwa Nigeria dawuriba Mommy to taya zanyi natafi nabarta,dan ALLAH Mommy kada kihana intafi da ita pls,bakaramin dadi Mommy tajiba aranta dankuwa tasan RUMAINA tasamu babban muhalli acikin zuciyar dan nata bazatamance lokacinda Nazeerat take kuka akan zatabishi shikuma yaki harsaida itada kanta tatirsasashi kafin yatafi da ita saigashi yau shiyakeson tafiya da RUMAINA har yana magiya,saitayi hamdala ga Ubangiji daganin dannata yasami farinciki ga matar nasa,saitadan batarai sanna tace,kada katafimin da diyata kaje karika wahalarmin da ita kokuma karikayimata mugunta har idan nasami labari tofa dakaina zanji nadauki yata,dasauri yace ALLAH Mommy nayarda saiya sanya hannunsa a aljuhu yazaro waya ,yace wanna wayar natane dazunna nasaimata shi kinga tawanna hanyar zaki rikajin komai daga gareta,cikin jin dadin kalamansa saita jawo ni tahadamu gabadaya tarungume tanafadin ALLAH yayimuku albarka yadauwamar da farinciki arayuwarku, ameen muka amsa dashi,nan tariko hannumu mukafito waje har parking lot takaimu ,kaman anyi usur wa yangidan sukarika fitowa sunaimana fatan alkhairi nida Ummee da Basma rungume junarmu mukayi saikuma mukafashe dakuka dakyar Mommy tajanyeni tashigardani cikin motar sanna ta umurci driver yaja mutafi"nan motocin sojoji sukarufamana baya da jiniyarsu,muna fita daga gidan saiyajanyoni jikinsa yarungume yana bubbuga bayana,lamo nayi ajikinsa sai sauke ajiyar zuciya nake,batareda bata lokaciba muka isa airport munasauka anakiran sunanmu,driver yadau akwatinmu ya isaga ma ay katan jirgin,jama'a saitururruwar zuwa suke sunata gaisuwar da kirarin bangirma,sunafadin ALLAH yakare NAKOWA yatsaremaka hanyarka,shiko sai daga musu hannu yake yanabinsu da murmushi,yana rikeda hannuna muka haura matattakalar jirgin.saiware ido nake waiyau nice acikin jirgi mamakina bai karuba harsaida mukashiga cikin jirgin,nan nashigayiwa Ubangijin hatittu tasbihi lallai ALLAH maigirmane kuma mai daukaka maiyin abundayaso gabawansa,lallai wanna rahamar daga ubangijinane,sit dindayake tacan baya mukazauna ni inata gefen window shikuma yanagefena, koda ma ay'katan suka fara sanarwa akan adaura belt's jirgi zaitashi nidai ido nakurawa sarautar ALLAH dan bansan ta inada zanfaraba,saibin mutanecikim jirgin nakeda ido ganin kowa natakorin daura belt's insa araina nace yau akeyinta,ban inda tunaniba sainaji hannuna ajikina yana sakalamin belt' in,nasauke numfashi ahankali,yana gama dauramin shima yadaura nashi,batareda batalokaciba jirginmu yadaga....... 4:00pm na Nigeria wanda yayi daidai da 2:00pm abirnin Switzerland ,jirgin yasauka ababban filin saukar jirgi dakecikin birnin Switzerland. Bayan minti 15 dasaukar jirgin asannu jama'arciki sukafara sauka,muma mukarufamusu baya"ya'ilahi yalillahi fatubarakallah masha ALLAH"abunda nafurta kenan lokacinda nasinci kaina acikin birnin Switzerland, fadar tsaruwansama batalokacine, dagacan wasu mutane masu sanye dakakin sojoji nakasar Nigeria dakuma na nan kasar Switzerland din sukafito daga cikin wasu motoci wanda akalla yawan mutanen sunkai 30 cikin sauri sauri gudu gudu sukanufomu gamanyan bindigogi ahannunsu sunkuma daddaga bakin bindigar kamar masushiga filin daga.cikin firgici da kidima narike hannunsa da karfi jikina narawa nakifa fuskata jikin damtsen hannunsa,cikin hanzari yadagoni tareda juyodani gabansa yace menene meyasameki??zillewa nayi nashige cikin kirjinsa sainasaki kuka cikin muryar kuka nace banason ganinsu tsoro sukebani,dada rungumeni yy yanafadin sojan susuke baki tsoro?" cikin sauri narika nagyada masa kai"murmushi yy maisauti saiyace kedayau zakisa kayan soja kokinmance kematar soja ce to amma kike tsoron soja,saiyashiga bubbuga bayana alamun lallashi,nidai dada cusa fuskata nayi cikin kirjinsa... Suna isa dafdamu sukatsaramasa tareda kamewa guri guda,wani dagajikin sojan narikedawata riga Wanda tun durowarsu daga saman motocin rigar dakuma hula rigar irin nasune,cikin girmamawa irin nasoja yakima tsaramasa sanna yamikamasa rigar"shikuma yamika hannu yakarba nan sojan yakuma kamewa,asannu yacironi daga cikin kirjinsa yanayimin magana cikin kasa damuya yace idan kikabari sukagane tsoronsu kikeji tofa harbeki zasuyi dan haka yanzu kiboye tsoron nasu kinuna kamar bakijin tsoronsu zakiga su yanzu sundawa jin tsoronki kinji?cikin dardar nagyada masakai yace good girl, rigarda kerike ahannusa yasanyamin gabanrigar abudeyake ana iya hango kayana wanda dama yake jikina sanna yakuma daura hular akaina saman gyalena" saiya juyar dani kamar yanda yake tsaye muna fuskantarsu,jinayi kamar nakwalla ihu dana kalli jikina nakuma kalli gungun sojojin dasuke tsaye agabana,danatuna cewa idanfa naji tsoronsu tofa harbeni zasuyi saina tattaro duk wata jarumtata nahadeta guri guda nakankame hannunsa dakecikin hannuna,yana juyo dani gabadayansu suka kuma tsarawa hadeda kamewa"hannusa yasaka daidai saitin kunnensa alamun tsarawa saiyacemin kema kiyi yanda nayi dakyar na iya daga hannuna nayi kamar yanda naga yayin"saisuka daga bakin bindigoginsu sama suka saki harbi tas..tas.."cikin rudu da dimaucewa nacakumeshi tareda kwalla kara,dasauri yarirrikeni taredayima sojojin nuni dahanu sutafi,nanma saida sukadada tsaramasa kafin sukajuya sukaje jikin motocinsu, Mannani yadadayi akirjinsa nace wayyo ALLAH zasu harbeni nidai kamaidani gida bazan zauna ananba,yarankwafo dakansa yakawo bakinsa saitin kunnena yace gaisuwafa sukeyimiki ba harbinki zasuyiba,nidai kin sauraransa nayi Dan gabadaya nagama firgicewa, saiyajanyo hannuna muka isa jikin wata mota kan mukaraso aka bude marfin kulle idanuna nayi harmukashiga motar wani soja dakecikin motar yaja muka haura titi...........

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull