Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 13
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 13: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 13. Sasautawa ya yi domin shi da kansa da yake yin maganar sama sama ba…
3,158 words
Sasautawa ya yi domin shi da kansa da yake yin maganar sama sama ba sabawa ya yi ba, wahala hakan ke bashi ainun A sasaucen ya dora da fadin" ba zaku gane cewar babu wanda Allah bai san da zamansa ba tunda shi ya halici abinsa ne?, Shin baku yarda cewar a yanzu yanzu kunna iya mutuwa bane?, Ko kun kai wajen da babu ruwanku kin rayu a kyamace a cikin duniyar kuma ku koma kiyamar ku tarda azabar wanda ya halice ku tunda har kuka ringa rayuwa kamar ba zaku koma gareshi ba?, NAHIDT, SHUWWAR, Fauziya ina da tambayar da nake son yi maku ba yau ba, shin haushin wa kuke ji da har kuke wulakantar da rayuwarku a banza a wofi?, Iyayenku kunne shedar aure suka yi suka haife ku a kasa mai tsarki, yaya haka kuma?!" Ya idasa yana sake kallonsu, ya ci gaba da fadin" ina Tsoron mu kai matakin da zan zame maku abokin gaba, idan na ce abokin gaba ina nufin wanda zai ringa hakon rayuwarku karfi da yaji dan ku gyara rayuwarku, gwara na zamo maku wanda zai tirsasaku tunda na kula kun rigaya kun mayar da kanku wa'inda basu san ciwon kansu ba!, Zan koma masalaci za'a zo a kwashe akwatunnan nan a maida su gidan su Sudais! Bashi da abinda zai ba Shuwwar! Bashi da shi na ce!" Ya karashe da karfin da ya saka SHUWWAR din kanta kallonsa domin da farko du kawunnansu a kasa suke Da sauri kuma ta maida kanta dan walahi har cikin ranta take jin maganarsa, kai wacema ke masa fito na fito din kanta a kasa bale su
A kausashe ya ci gaba da fadin" Hamza, mutun ne kamar kowa, sai dai kuma namiji ne kamar kowani namiji, ba zai kuma shigowa gidan nan kansa tsaye ba har sai na gama tantance hakan, Shuwwar kar ki kuma fita, ki zauna daga yau ki lazumci astagafari, ki ringa azumin litinin da talata, ke koda ba ranakun nan ba ki yawaita yin azumi kinna fadawa Allah sannan kinna barawa Allah zabi a kan rayuwarki, shi ya yi ki, shi ya dora ALKALAMIN KADARRARKI a haka, shi yake da ikon mayar da baki fari, a wajensa ne kawai zamu nemi sauki , ina fatan kun ji abinda na fada maku kuma kun dauka"
Daga haka ya mike ya basu baya ya fice fuskarsa a mugun haden da ya saka suka raka shi da kallo riiiiii kafin Shuwwar ta ce"
Shin labarin na birge ku kuwa?......ku garzayo ku turo shaidar biyanku dan mu taka mu shige cikin labarin Alakamin kadarrata tare da ku........ in sha Allah gobe zamu tsayar da freee page🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥺💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 1️⃣4️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Ikon Allah, du rashin kunya irin ta y'ayan nan ashe idan suka hadu da wanda zai kausasa masu dan kankin kansu zasu kasance masu biyaya ne harma bakinsu ya yi shiru? To dai gasu nan a gaban Malan, sun yi shiru kamar basa nan, ya gama fadan ya kuma tambayi idan har sun fahimci yarensa sun yi alamun dake nuna masa cewar sun fahimce shi
A nutse ya mike yana daukan carbinsa ya juya ya fice a falon gaba daya ransa a cakule sannan ya yi niyar daukan mataki a kan yawon su SHUWWAR, dan ya kula idan ba sakawa abin birki ya yi ba tabas Shuwwar ba zata samu lafiya ba, bama ya bukatar sannin abinda ya fitar da ita daga dakinta wannan karronma, abinda SUDAIS ya fada masa a wayama ya wadatar, sannan zai je ya samu Malan ya tambayeshi shin dama akoy wata yar tsama a tsakaninsu da zai sa ya wulakanta rayuwar yarinya ya sa a saketa a ofishin sojoji kamar wata yar ta'ada a barta ta kamo hanya ita daya tana kararamba a titi ? Yanzun da ba dan Allah ya kawo Hamzan nan ba da ai shikenan ta afka a wata sabuwar rayuwar mai wahalar fita, shin idan a cikin y'ayansa yan matan akaiwa haka yaya zai ji? Walahi, walahi, walahi yadda Shuwwar ke kiransa da Aba ta kuma sada kai idan yana magana sai ya ji ciwon wulakancin da akai mata tamkar an yiwa gudan jinninsa ne, kai yau da shi wani takadarin dan duniya ne da ya auri daya daga cikin y'ayan malan ya maka mata saki a cikin jejin Allah ya barta da kanta ya ji idan akoy dadi!, Shin me yasa mutanenmu suka cika son kansu ne? Menene anfani sako dan mutun a gaba dan aure ya hada ku ne? Abin bacin ran yanzu abun ya zama ba macen ba namijin ba, kowama aikata son ransa yake yi kai tsaye abinsa
Su kam bayan fitarsama a kadan an dauki minti biyar sunna zazaune su dukansu babu wada ra motsa Cen Shuwwar ta sauke ajiyar Zuciya tana kallon Auntynta ta ce" Ashe babama da babansa "
NAHIDT ta juyo da sauri tana kallonta ta ce" Ke SHUWWAR da wa kike?"
SHUWWAR ta girgiza kanta tana hayewa saman doguwar kujera ta ce" Ba da kowa ba "
NAHIDT ta sake juyowa sai karra cika take tana batsewa a bayane ta furta" Sai kace ubanmu? Gaskiya mutumen nan ya iya wulkakanci, yanzu tsakani da Allah meye laifin Hamza?"
Fauziya ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Bashi da laifi, ko daya bashi da laifi, sai dai kuma abinda Aban Shuwwar ya fada gaskiya ne, ya dace wannan karron mu bi komai a hankali, gagawar me muka tsinta a cikinta ne banda wahala?"
Shiru ta yi bata basu amsa ba, sai salamar da aka yi aka ringa shigowa da kayan abincin da ya saka su bin masu shigo da kayan da kallo, sai da suka gama ajiyewa a baki baki yaron ya duka yana fadin" Malan ne ya ce a kawo, ya kuma bada wannan ya ce a bada"
Ambulope din Fauziya ta amsa idannuwanta a waje ta buda ta fitar da abinda yake ciki Gaba dayansu sai da suka zarro ido suka kalli yaron da ya gama yi masu bayani ya mike ya yi tafiyarsa
A bayane Fauziya ta ce" Allah kennan, kin ga yau muma irin haka ce ta same mu? Lalle Aban Shuwwar ba shuwwar kadai ya haifa ba, muma babanmu ne"
NAHIDT kam bakinta gaba daya ya mutu tana bin kayan cimar da kallo, harda madarar peak, da kidin gwongwani, sai ta samu kanta da jin dadin haka a cen kasan zuciyarta aman kuma ta ki yarda ta bayanar da haka a fili saima bara masu wajen da ta yi ta nufi cikin dakinta
___________________________________
Daga wannan ranar suka fara shinfida Rayuwa mai tafe da daraja da mutunci Rayuwa ce da basa fita yawo dan neman na cin abincinsu, rayuwa ce da suke zaune a daki iya tsayin yawonsu falonsu ne sai ko idan zasu rufe gidan Hakan ya sa suka ringa taya SHUWWAR daukan azumin da take yi wanda daga bakin lokacin da ta fara yinsa ta fara fuskantar wata irin nutsuwar zuciyarta Lafiyar jikinta ta karru fiye da da, uwa uba da zarar ta sha ruwa ta yi salolinta sai ta kawo kayan gyaran jikinsu ra hada ta hau Dukhane hankali kwonce ta dauki lokaci mai tsayi a sama tana shan hayaki har sai fatarta ta yi jajajir sannan ta sauka ta dora da damamen kurkum da madarar kauri a jikinta ta murje sosai har sai ya kamata sosai sannan ta sha kadadar madara mai sanyi karara ta haye gadonta ta luluba da bargonta , garin Allah na wayewa kuwa take dora zaman turaran wuta, wannan kuwa sabonsu ne su dukansu ukun kowace da kujerarta da turaran tsugunonsu da na jiki Watau sabon da suka yi tun a saudiya na gyaran jiki da iyayensu ke yiwa larabawa da yan matansu na cen idan aure ne ko biki ne , kai kulun dai cikin gyara ya kasance suma abin baya basu wahala, ba zai yiwu su yi sati basu dora gyara ba, jikinsu har tambayarsu yake yi Sai suka karra samun sirikan gyaran na mamaki wanda ke karra fitar da darajar fatarsu A Yanzu kuma da suke zaman gida ba dare ba rana, abin sai ya zama shine kadai abinda ke debe masu kewa bayan TV Gefe daya kuwa Hamza ba wai kwata kwata bane basu da labarinsa Ta cikin waya ya zame masu karfen kafa Ita da kanta Shuwwar dake mamakin sun yi saurin sabo da shi sai gata ta saba da shi din A waya suke bata lokaci mai tsayin gaske sunna hira, kuma hirar kowa da kowa ne Ta wayar ya nemi sannin su din su wanene? A lokacin da NAHIDT ta shiga bashi labari a lojacin nan Shuwwar ta mike ta nufi ta kwonta A hankali ta lumshe idannuwanta tana jin yadda zuciyarta ke dan bugawa Labarinsu? Labarinsu ai takaitace ne, domin su da kansu basu san menene asalin labarin iyayensu ba, basu san su din yan wata kada bace, su dai sun samu yaren hausa a bakinsu sai larabci sai ko turanci da suke ji An haifi su a Riyad ne su dukansu , daga baya iyayensu suka dawo maka da zama Abinda suka sani da rayuwarsu shine mahaifiyarsu dai farar mace ce kamar zabaya, akan kireta da buzuwa sunna ne na kiranye da abokanan aikinta ke kiranta da shi, sai mahaifinsu shi kam ba fari bane ko kadan, aman mutun ne mai kyan gaske domin a kamani ita SHUWWAR ta dauko kamanin mahaifinta ne, ita kuma NAHIDT ta dauko na mahaifiyarsu, aman gaba dayansu farin mamansu ne suka dauka da gashinta da kirarta Labarinsu bashi da tsayin da zasu ce ga asalinsu har iyayensu suka barsu da sunnan sun tafi arfa a cen aka dawo masu da maganar sun rasu Basu ga gawarwakinsu ba, basu ga kabarinsu ba, a haka suka dangana daa son ganninsu domin sun je sun kuma zuwa basu samu gannin mamatan ba bale su ga gawarwakin iyayensu, gashi a lokacin sunna cike da tsoron kar a kama su a kaisu wata kasar daban A haka suka ci gaba da nema da aikatau dan su ci da bakin su, har ranar da la'ananen nan ya kama auntynta aka kaisu gidan da ake dawo da jama'a kasashe daban daban aka diro su hausa
Ajiyar zuciya ta sauke dan ta san shikenan ko mai yannayin rayuwa irin ta Hamza me zai ci da mai irin rayuwarsu?, Ita kam yanzu a irgenta satinta uku kafarta bata leka waje ba, da zarar ta samu ta idasa sakewa sosai zata fara fita ne dan ta samu aikin yi ko yayane ta ringa yi , zai kore mata kewa
____________________________________
Sati shida kennan da rabuwar auren Shuwwar
A tausashe ya dora da fadin" Ban sani ba, malan ban san ko matsalar halin da ya fada maka kai tsaye bane ya saka ka yi masa iyaka da yarinyar wajenka?, Ka ga wannan da kake ganni yaya yake a wajen mahaifiyarsa , yakan zo lokaci zuwa lokaci, shima a yanzun wani ne a kasar nan, aman Hamza ya ki ya dube shi ya ki ya yafe masa, a yanzu da ya zo na ce bari na janyo shi mu zo mu sameka tare domin zan fi jin kwarin gwuiwa, kuma mai yiwuwa idan muka zo taren koda ka yi niyar hanna mana ne kana iya bamu, Hamza yarona ne, aman ka ga yayan mahaifiyarsa nan, bamu da labarin mahaifiyar tasa dai , an yi neman an hakura an barawa Allah komai"
Malan ya sake kurawa fuskar Datijon dake zaune cikin shiga ta alfarma ido Da sauri ya cire idannuwansa yana mamakin kamanin nan, datijo ne, ga shekaru ga komai, aman cikin ikon Allah kamanin a bayanr suke ba a boye ba
Wata ajiyar zuciyar ya sauke yana fadin" Elhaji, ko daya, ba wannan dalilin ya saka na dakatar da shi ba, ina so ne mu bi komai a hankali, bana so abinda ya ringa faruwa ya sake faruwa da yarinyar nan duda ban isa na hanna kadararta wadda Allah ya kadaro mata ba, aman ina iya yina, so nake ko yayane abin ya zo mana da dalili, ba wai ace a musulman duniya an rasa wanda zai iya yin jihadi ba, wannan shine kawai dalilina, yanzu kuma da ka zo da kanka na yarda cewa da gaske yake, harma zan iya bashi aurenta in sha Allah"
Farin ciko ne karara ya bayana a fuskokinsu, datijon nan ya budi bakinsa da hausarsa mai hade da yare irin na buzun usul ya ce" Allah ya saka da alkhairi Malan, mun gode mun gode sosai, dan Allah a fada masa ya yafe mana, a lokacin da muka kyamaci mahaifiyarsa har muka koreta a gida dan abin ne ya zo mana a birkice, sai muka guji kunyar duniya muka yafawa kanmu ta lahira domin mafanar da nake yi maka mahaifinku shine sarkin garin Tanus, a yanzu haka yayanmu ne ke sarauta a garin, mun tafka kuskure, mu dukanmu muna dana sani, sai dai dama an ce dana sani keya ce, gashi yanzun sai shi kadai muka sani bamu san ina uwar take ba, bamu san tana raye ba ko a mace ba, saudiyar du shigarmu sai mun sake kokarin nemanta a tashihin da yan kasar nan ke rayuwa, aman kulun amsar daya ce basu san *TINANA* ba, Malan idan har ba takura dan Allah a taimaka mana daurin auren nan a yi shi kwana kusa, kar a ja mana malan, shi ba yaro bane karami, itama ba aurenta bane na farko, kar a ce mana ba'a shirya ba domin mu dama bama auren mace ta kuma tare da mana da komai, ko karan tsintsiya bama yarda mace ta zo mana da shi, namiji shi ya dace ya yiwa mace komai ko a adinace, ba adini bane ya zo mana cewar a yiwa mace gado da sauransu, zamu yi komanmu, mu dai macen muke so dan mun san darajarta zamu amsheta da hannu bibiyu in sha Allah"
Wani irin farin ciki ke ziyartar zuciyar Malan, hamdallah yake yi a cen kasan zuciyarsa yana hasaso irin farin cikin da zasu yi su dukansu idan suka ji wannan dadadan labarin Tabas NAHIDT ta yi gaskiya a kaf manema auren Shuwwar babu wa'inda suka zo da niyar taa alkhairi irin wa'innan ba Hakan ya sa shima ya ari bakin yan matan ya ci masu albasa a nutse ya ce" To ai shikenan Elhaj, kamar wani lokaci kuke so? Wata daya ya isa?"
Aban Hamza ya sake Nutsuwa yana murmushi ya ce" Ai shi baban nasa ne yake da tafia malan, bama gagawa aman da mun samu nan da sati biyu, da mun ce Alhmdulilah, ka ga babansa ba yau ba yake shirye shiryen auren dan nan nasa na tabata kofar gidanka sai ta yi kamar zata fashe dan jama'a"
Farin ciki ya sake lulube zuciyar Malan, a sanyaye ya ce" Alhmdulilah, in sha Allah ya yi, zamu fara shiri tun daga yau bi izinillah".............
Da wannan suma rabu da junna, malan kam bai wani yi dogon zama ba ya samu ya je gidansu da karfinsa da kuma rigima daidai da du wanda zai zo masa da tangarda a kan maganar
Sosai ya sake samun Nutsuwa da urin halin da ya same su, kunshi suke yi, wace ke yanyara masu kunshin kuwa Shuwwar ce, Shuwwar ta yi kyau har ta gaji abinta , ga kunshinta dan dasss a kafafuwanta
A nutse ya sanar masu abinda ya yanke da Shuwwar ya dora da fadin" na fi so ku yi taron bikin a gidana, idan har hakan ba takura bane a gareku"
Zuciyarta tsintsinkewa take yi tana kallonsa, a hankali ta ce" Aba"
Kansa ya dago domin du bayanin da yake yi ba wai kallonsu yake yi, dan kwaurin Nahidt a fili kuma ba abinda ya dameta A hankali SHUWWAR ta ce" yadda kake kokari a kanmu, Aba yadda kake nuna mana kauna, yadda bakaa kyamatarmu ABA, Allah ya rufa maka asiri duniya da kiyama......" A hankali ta dora kanta a gefen kafadar Nahidt tana hadiye hawayenta
Fauziya da gaba daya jikinta ya mace mata sosai kanta aa kasa itama adu'a take yi tun karfinta tana korar abinda ke a cikin zuciyarta
A sanyaye ya yi Murmushi yana fadin" In sha Allah, da zarar ranar ta gabato zaku koma ku yi bikin a cen, zan koma masalaci"
Daga haka ya mike ya juya da niyar tafia ya ji muryar NAHIDT a sanyaye ta furta" Malan "
Dakatawa ya yi yana ayana' Na san ai sai mun raba hali ' Yaja juyowa ya ga hawaye ne shar shar shar a kan kumatunta tana kallonsa