Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 14
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 14: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 14. Hakan ya karya masa zuciya ainun harma ya samu kansa da dawowa ya…
3,171 words
Hakan ya karya masa zuciya ainun harma ya samu kansa da dawowa ya zauna saman kujerar yana kallonta ya ce" Lafia?" NAHIDT ta rike hannun shuwwar sosai a sanyaye ta ce" Malan, Allah ya saka maka da alkhairi........" Muryarta da ta dauki gargada ta saka shi ya kuma dan dagowa ya dan kalleta kafin ya mike da sauri ya yi gaba ya bar masu gidan gaba daya, ita kuma ta fashe da kuka tana rike kanwarta a jikinta wace gaba daya take cikin wani yannayi A sanyaye Shuwwar ta ce" ki daina kukkan, idab kuma bakya son auren nan ne wannan karron ba zan yi maki gardama ba, domin na fara tsoron kar aje ko dan ina bijire maki bake gannin ba daidai ba, kin ga idan bakya son wannan ko? Bani da ja, sai na je na ci gaba da zamana har Allah ya kawo min wanda hankalinki zai kwonta da shi Nahidt" Nahidt ta girgiza kanta aa sanyaye ta ce" baki da hankali ne?, Ni nake cikin farin cikin wannan lamari, nice nake cikin gagarumin farin cikin gannin mutumen da nake maki marari ne Allah ya kawo mana, shushu kin ga irin son da yake yi maki? Ba dare ba rana sai ya yi kiranmu a gidan nan, du irin yadda Abanki ya gindaya masa sharuda kuwa a haka ya ci gaba da neman kyautata mana ba tare da ya taka daya daga cikin dokokin Malan ba duda kuwa ya san ba malan bane ya haife ki aman ya masa biyaya dan ya ga mun yi masa, kin ga kuwa wannan mutumen abin a girmana ne, abin a mutunta ne, kuma kin ji Malan din ya ce a gidansa zamu je a yi zaman bikin ki, yana so a yi wunin bikinki a cen duda na san matansa ba zasu so hakan ba aman dan dolensu na san zasu yi girki su kuma tarra mutane, Shushuna kin san meye yake saka ni kuka? Farin ciki nake yi kan ashe kina iya yin auren gata, auren da yake ba boyaye ba, auren da yake na an san ke ko wacece kuma aka roku alfarmar ana son ki? Hakan na nufin Ashe akoy sauran musulmai masu koyi da koyarwar adinninmu, Shushu wannan baban farin ciki ne ai"
Shuwwar ta yi murmushi tana share hawayen dake saman fuskar Nahidt cikin zazakar muryarta ta ce"💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 1️⃣5️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
*KARSHEN FREE PAGE*
Cikin zazakar muryarta ta ce" Da Aba ke ce min na ringa dakatawa har ya lazumci lamuran aurena sai na ga wanu lazumi kuma bayan ga haza ana so na, nakan manta dumbin samarin dake nuna min so sai su fito min da wata maganar a tunaninsu shine burina, idan kina fada kan saurayin da na kawo a matsayin wanda nake son na aura sai na ga kamar bakya min adalci, kamar baku damu da abinda ya dameni ba, in na je aka sakoni kuma sai na ga waye ya dace na fara saukewa sama da ke? Tunda dama baki so aka yi auren ba, a mutuwar aurena da SUDAIS sai na fara fahimtar wani abu, tun haduwata da SUDAIS idona ya rufe kamar a kan sauran, SUDAIS na nuna alamun na masa da dan barkwoncin yana son ya aureni a nan take jikina ya kama rawa na ringa taro shi ina nuna masa ai ni kawai maganar nan ta aure daa ya fada itace za'a yi domin itace ke rudani, itace farin cikina, kin ga idan zai zo nice dafa wannan, soya wannan, gyara wancen, na zo na shake masa gabansa da abinci na sala wanka na ringa jiran shigowarsa, da zarar ya ce min gayanan har rawa jikina yake na kamma gindaya maku sharuda kan sshigarku, kan shigi da ficenku, du a kokarina kar ya ga abinda zai sa ya daina aurena dan ina jin kunyar ahalina....., A haka ya nemi a yi aurenmu a rufa rufa, kin san da na fahimci yana jin kunyar abokannansa su san yar gidan da ya aura ne ya saka shi aikata haka? Aman tsabar ban san ciwon kaina ba sai na amince ido rufe na nuna nima din ai bani da daraja, Aunty na san da yana zargina, ina hankalce da irin kalamansa da irin yadda yake kiyaye komai a tsantsamce, sai idan ya ga na dan shiga hali na tunani sai ki ga kuma ya sasauto ya shiga yi min kalamai irin na son ya mantar da ni halin da zuciyata ta shiga a kansa, ni dai du a tunanina auren dai idan na yi na tafi ai shikenan, Aunty a haka aka kaini da sharadin ba zaki bini ba, ba ke ba ba Fauziya ba, na yarda kaina na rawa na bi matar babansa daa wata tsohuwa suka daukeni suka sadani da dakina, Aunty a gidan dama dakin nan shine kadai abinda na isa da shi, Mijin da nake yiwa ya gagari idannuna, Aunty daidai da girki irin na kowace mace ni gagarata ya yi dan kuwa ina ji ina ganni banma isa na taba masu abincin da zasu kai bakinsu ba..........., A hankali na ringa koyon yadda matar gidan ke mu'amalantata tana nuna min ita din mai daraja ce, a sannu sannu na farra gane cewar bayan darajar da take son nuna min tana da ita hakama y'ayanta sunna da ita sai kuma na ga tana kyamata bayan du abinda na ga ya zamto al'adunsu su na ara na yafawa kaina duda dama bamu tashi da banzar shiga irin ta sutura ba, Aunty a hankali na ringa karantar cewa auren nan nawa babu inda zashi shima domin mijin da aka aura min din bai nuna alama ba, amarya da aka ce shine ni na fuskanci haka a tawa rayuwar?, Aman kin san me?" Nahidt ta girgiza kanta tana kallonta Shuwwar ta saki Murmushi tana fadin" a hakan ba dare ba rana fadawa Allah nake yi Allah ya sa ya tuna da ni ya zo ya bani darajata ta mata a gidansa, Allah ya sa ya daukeni mu yi nesa kamar yadda yake alkawarunta min cewar zai aureni zai yi min meye meye ke dai abubuwan da maza kan yi anfani da su dan rudar da zuciyar yan mata irina idannuwanmu ya rufe har mu ringa gannin rannaku sun mana nisa, irin shigo shigo ba zurfi din nan sai mun afka su nuna mana halayansu na samarin Shaho, a ranar da ya shigi ina sakawa falona turaran wutar da kika hada min a ranar ya zo min da raini, da wulakanci, da fitintinnu da zargi karrara, aman kaina a kasa, so nake ya fuskanceni ko ya ganewa kansa ban san abinda yake zargina a kansa ba.......... Aunty sai a zaman nan da na yi na karanci rayuwata na gane ashe da na tafka kuskure? Domin ba wai samuna a cikakiyar budurwa bane zai sa wasu mazan su bani darajata, tun a farko nice na nuna bani da daraja, nice na nuna bani da mutunci, na nuna dangina haka, waye zai mutuntani? Walahi watan uwarta ce karuwar kuma sananen karuwanci aman dan uban wani namijin dole zai bata daraja dan ta siyawa kanta ita!, Nawa suke yawonsu su tashi yin aurwn bayan sun tsaftace kansu su kuma samu daraja? Ni fa fita nake yi neman sa'ar a aureni, to sai aka aurenin kuma aka ci ubana!"
Fauziya da jikinta ya fara sabawa da faduwar gaba a kan lamarin Hamza ce ta yi watsi da komai ta fuskanci mutanen nan biyu, NAHIDT da Shuwwar zata iya cewa sunne ahalinta, a tare aka kwaso su a tare jirgi ya sauke su a garin nan, ba dangin iya ba na ABA tafiyar jirgi ce ta hadda su, aman suka hadu da niyar su taimaki junna ko dan samun abin kaiwa baka, Nahidt dai ta fisu a lokacin kuma ta fisu rashin tsoro a lokacin........a haka suka rungumi junna in wani tudu in wani gangare har suka kawo yau a tare, da dukan karfinta ta kori shedan tana mai ayanawa zuciyarta cewa' zuciya ki bar rudani duniya ki bar rikita ni!' domin ta rigaya ta yiwa kanta alkawarin ko mutuwa zata yi sai dai ta mutu da abin kunyar nan
A sanyaye ta yi murmushi tana fadin" Shushu, me kika rasa na y'a mace? Ki duba ki ga tsarin halitar da Allah ya yi miki, kina da harda a kanki, sannan ba kaifi daidai gwargwado na bokon muna da mu dukanmu, Shushu dan kadararmu ta zo a haka shikenan sai mu yi tunanin bamu da daraja ?, Muna da ita mune muka karra watsar da ita, shushu mace tana da daraja, tana da mutunci, du kuma namijin da zai riki mace dan ya wulakantar da ita tabata bai san darajar mahaifiyarsa ba, da ace ya sani da ya yi duba da irin nauyi da mamansa ke dauka a cikin gidansu ya rike matar aurensa da daraja haka kuma ya dubi na waje da daraja, meye mace ta yi maka? Allah ya halita maka ita ne dan ta kasance abokiyar rayuwarka, wace zaku rayu da farin ciki ko bakin cikinka tare, wace zata haihun maka ta dauki dukan nauyi naka, itace zata zamto abar da za'ana harin rayuwarta har a ringa furucin kar ka sakkar mata fuska zata rainaka ne? Wani raini ne ya yi saura kai da kake kasancewa zigidir a gabanta bayan ka fita shekaru ko yayane? Wani raini kake magana a kansa matar da ta ga ka rikice ka nemi nutsuwa ka kuma samu a tare da ita? Idan a duka bayan wannan bata rainaka ba ai bai dace ka yi tunanin zata rainaka ba a rayuwa, maganar raini ai ta kare da ace kana da hankali, kin ga Hamza yana da mutunci, abinda kike ta jaje kansa kan shaye shayensa kin ce ya halata ka zauna da mashayi bayan ka san mashayi ne? Wannanma gaskiya ne aman yaya kike so mu yi? Mu shine mutun a wajenmu, shansa kuma bai hanna shi ibadarsa ba, ido rufe ya hanna ki sha sannan a bayane ya nuna burinsa ya dauna sha, shaye shaye na saka bawa aikata munanan laifukan da ba zai iya gogewa ba a duniya, a haka zamu amsa mu kuma taimaka masa muma har ya daina, in sha Allah zai daina sha Shushu kuma zaki ji dadin zaman aure da shi" Nahidt na murmushi ta ce" ki kunce min kunshin nan na wanke na yi wanka na je kasuwa, na ga kurkum dinmu da madarar sun yi kasa sosai bara na je na siyo kayan gyara da kuma kayan hada turaran wuta da na ruwa da su humura mu zo mu jika na jikawa mu soya na soyawa mu shiga shiri, Shushuna kin san sai na maki garra a wannan auren..........sai na fitar da bokici bokici na kayan aurenki, yanzu ne zan aurar da y'ata ! Ta karashe da yannayin tsokana dan ta san yanzu shushun zata ce ke ni yayata ce ke mamana ta rasu Sai ta ga Shushu bata ce komai ba tana daria kawai kasa kasa itama ta kama kunshin ta shiga cire mata a nutse
Tabas yanzu ne suka dauki auren nan da mahinmanci Sau uku kawai Malan ya lamuncewa Hamza zuwa wajensu dan shirye shiryen da suke yi, a wannan zuwan nasa uku da ya yi a falonsu ake yin zaman gaba dayansu a ringa hira anna barkwonci Watau Hamza kamar wani jigo mai saka su farin ciki ya zame masu, a ranar kuwa da ya zube kudin gyaran amaryarsa sai da suka kusan haukacewa gaba dayansu domin a bayane suka rikice da tarin kudin nan A lokacin Nahidt ta riki kudin ta ce" kai dai kawai Allah nuna mana Hamzanmu" Shuwwar kuwa kai ta sada tana daria kasa kasa dan ta san fitarsa ake jira su kwaso shoki a gidan nan, domin jiya jiyan nan take maganar kudi ya fara kasa sun shiga uku
Kafin ya tafi yake fada masu maganar kawo lefe ya ce in sha Allah ranar daurin aure karfe bakwai mata zasu kawo lefe, domin a ranar ne danginsa na cen gidansu Tanus zasu zo sun ce sai sun zo zasu kawo lefen da mamana, kin san babana da son ya kankaro min daraja, to dai inaga fen zasu hade su kawo su, mu dai da angwaye zamu zo mu rakashe a kada manaa ganga oh...su Hamza za'a angwance................
Ire iren barkwoncin da ya saka Shuwwar din kanta yi masa waje mai mahinmanci ta ajiye shi a cikin zuciyarta Zata iya cewa sonsa take yi, ta kamu da sonsa ne, yo ai ya isa a so shin, meye aibunsa? Bashi da wani aibu da zai zamo aibu a wajensu gaskiya, ko daya bashi da shi
Daga wannan lokacin bayan gyaran jikin amarya da suke yi sai suka koma gyaran baban falon Watau dafe dafen kaza irin nasu na saudiya da suka koya a wajen mahaifiyarsu babu kalar wanda basu dafa mata ba kuma suka tisa keyarta ta cinye Idan aka zo fannin maganin sanyi, maganin basir , tsumi kuwa cikinta har ya saba du irin yadda take nuna ta gaji cikinta ya cika a haka yayarta zata ajiye mata ta ce da ita ke dai dan karra sha ke dai kin jiya yar kanwata?
Da wannan suka ringa tunkarro lokacin har ya yi saura sati daya daurin auren, a nan ne Shuwwar ta fitar da akwatunnantaa dake jejere a dakin da suma rufe suka baje komai
A nutse suka fitar da kayan dinki masu mugun yawa wa'inda Shuwwar ta murje ido cewar in dai sunna so ta dauka sai sun dauka summa Ai kam suka daukan kayan fitar biki masu yawa suka bari magariba na yi suka shige motarsu suka nufi wajen telensu wanda dama su yake jira
Kaya suka zube masa suka zube masa kudi da kwanakin da suke son kayansu Ya kuma amsa ya amshi kalolin dinkunnan da suke so ya rabawa yarensa suka shiga aiki
Ana sauran kwana biyu daurin auren Shuwwar , hakan ya sa yayunta suka shige cikin hali na busy Ba tarro suke yi nasu na kansu ba, abinda ya shigar da su a busy hade haden garra ne, idasa rurufe tarin uban turarukan da suka hadda mata na wutan ne da na ruwan, ga kuma na saudiya da suka siya a garin mai tarin yawan gaske irin na cikin yan kannanun kwalaben nan mai masifar dadi, Shima sun masa wajensa daban sun daure..............kai gata dai shuwwa ta same shi sai fatan alkhairi da zaman lafia da mijinta
Daga wanka ta fito tana tafia a hankali ta zauna saman kujera gaban sif dinta tana lumshe idannuwanta sanadiyar kanshin da jikinta ke fitarwa mai mugun dadi da irin laushin da jikinta ke karra dauka balema idan ta taba ruwa Manta da ta hada mai karra fitar da darajar fatarta ta janyo a nutse ta shiga shafawa tana sake lumshe idannuwanta dan santsin da yake karrawa jikinta gaba data ga kuma irin nasa kanshin mai sakawa bawa nutsuwa a zuciya
Wayarta mai kirar apple watau iphone wace angwonta ya gwongwajeta da ita ta shiga dan haskawa alamun kira na shigowa
A nutse ta janyo wayar ta daga kiran tana karawa a kunnenta ta yi salama da sansanyar muryarta
A sanyayen shima ya ce" I'm sorry wifey yau du ban yi kira ba, kin san menene? Yadda kika san tashin duniya haka babana ya dauki daurin auren nan, har tunani nake anya anguwar nan ta dauki bakinsa kuwa? Yanzuma daga masaukin da zai sauke uban gidansa nake kin san bayan ya yi ritayama akoy kyakyawar alaka tsakaninsa da Chief of army, so ya tabatar masa shi zai mika sadakina wa Malan shine fa du babana ya rikitamu kan zuwan bawan Allahn nan, ina fata ba'ai min fushi ba?"
Dan murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" Ban yi ba"
Watau jan aji, ko yace girma irin na Shuwwar na bashi mamaki, tamkar wadda ta shafi jinnin sarauta wani sa'in, shi tunda ya santa idan ka ga ta budi baki ta maka doguwar magana ta danganci abubuwan da ta gani na rayuwa ne irin sake saken da maza sukai mata na aure, bayanshi ko da su Nahidt sai dai ya ga kasa kasa ta yi tsokana ta kuma koma ta hade abinta kamar ba ita ta yi ba, sai Nahidt din ce zata ringa bambami ana riketa, wani lokacin har tunani yake shi mai maganar nan sai ya hadasa mata ciwon kai ai, domin shi dai tsakani da Allah, Allah ya yanka masa abin magana yi zai yi ta yi abinsa
Yar dariya ya yi a hankali ya ce" Kina irga awani kuwa?"