Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 15
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 15: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 15. A kasan zuciyarta ta ayana' fiye da tunaninka, domin na fika zumudin…
3,357 words
A kasan zuciyarta ta ayana' fiye da tunaninka, domin na fika zumudin son gannin ranar nan, abinda na koya shine rike zumudin hakan a cikin zuciyata domin a aure hudun da na yi na bayana ban ga alkhairin hakan ba' A bayane kuwa sai ta ce" Awani? Na me kuma my Hamza?" Ido ya dan zarro ya ce" To wai me na maki da zaki rama ne my kanwa? Yanzun sai kice bakya duba agogo du wucewar minti kina ayana saura yan awani? Kin ga yama ta yi fa, daga safi ta waye saura kwana daya tak, daga an yi wani wunin sai a fara irga yan awanin da zasu rage Hamza ya zamo mujin Shuwwa" Murmushi ne ya subuce mata hakan ya sa ta kashe kiran da sauri tana sauke murmushinta a bayane Mikewa ta yi tsaye ta shiga dan takawa hakan ya sa duwawunta dake cikin tawul jujuyawa a bayane ta ce" Nd shuwwa ta zamo amaryar Hamza.....wayo Allahna ashe za'ai min auren gata nima kuma har a tarra al'uma irin haka? Wayo farin ciki kasheni?" Tana sambatun farin cikinta wani kiran ya kuma shigo mata wayar Du a tunaninta shi din ne, domin kira a wajensa har ajiye wayar take yi ta ki dauka sai ya kirayi ta Nahidt yana fadin Allahn da ya sa in bakya son jin muryata ai ga Nahidt ga Fauziya sai mu kwana muna labari sai dai haushi malama! Number da ta gani ta sakata dan kura lu'u lu'un idannuwanta tana kallo domin bata san number ba, kuma ta sha dawowa ta tarda misss call da number an yi kiranta bata kusa A hankali ta daga kiran tana karawa a kunnenta ta yi shiru A sanyaye ainun ya ce" Aure bai haramta tsakanina da ke ba Shuwwar, bai haramta ba, na zo yau na samu Malan dan na fada masa cewar na je na yi bincike ina iya aurenki yake fada min ya maki miji?, Shuwwar ni ban san me na yi nake fuskantar jarabawar sonki haka ba, mahaifina ne ya ja min ko?, Shine ya ringa fade fadensa har Allah ya kama shi ta kaina ko?, Shuwwar wani zaki sake aura ya sake ki kina ji kina ganni bayan kin san ni ba zan taba sakinki ba?, Shuwwar tunda na gila karyar ni mijinki ne a gaban mutumen da na san a lokacin da ya yi niya da yanzu sai dai tarihina kina tunanin zan bari wani ya raba mu ne?, Haba my Shu dan Allah ki cewa Malan bakya son wancen ni kike kin ga in ba haka ba zaki karra yin wani auren a sako ki ne" Da dan karfi ta ce" ba Amin ba , kai Abdul tsaya ka ji na fada maka gaskiya, ka ga da kai, da babanka, da sojan nan da kake alakanta kanka da jarumi dan ka yi magana a gabansa na tsane ku!, Ku shafa min lafia ka ji? Mijina da zan aura kuma yana sona, Alhmdulilah ya san wacece ni kuma a haka yake son abinsa, kai barama ka ji ka kuma kirana walahi sai na wahalar da rayuwarka, da ace ban yi rantsuwar ni da soja ko police sai a lahira bane da kai kararka zan yi su rufeka na huta!, But yanzu ina mai gargadinka kan ka shafa min lafiya ka ji bayanina?"
Tana gama fadan ta kashe tana zabga uban tsaki a bayane ta mike ta shiga fitar da nikaf dinta da rigar da take sakawa dan karra dumama dumin jikinta domin a yau zasu fara kunshi da kuma alawa dan cire gashin jikinta da ya kwonkwonta lumbuk, tana yi tana mita da fada a bayane tana fadin jarabar banza da wofi sai ka zo ka sa a sakeni, yo in aurena ya zauna sai na tarda mai shinkafa na ce da shi to azalumi na auru yaya ranka?😂
Babar ranar Kwaramniya ke tashi ta manyan almajiran malan dake sake kimtsa kofar gidan da aka saka manya manyan runfunna har kwaya hudu , irin dankara dankaran nan Mutanen anguwa tuni suka ringa cika gidan malan tunda garin Allah ya waye dan karra ba idannuwansu kalaci da mamakin lamarin Malan din, domin a cikinsu kalilan ne suka dauki hakan da fuskar fahimta harma suke adu'ar Allah ya sa wannan din idan aka yi shine na dindindin
Dankara dankaran sojojin dake zagaye da anguwar kuwa idan ka gani sai hankalinka ya tashi, tamkar zasu je dan jijibin yaki ne domin tuni Tsohon ganaral da amininsa Chief of army, da aban Hamza suka samu karasowa a yanzu da yake karfe takwas sunna baban falon Malan na alfarma sunna karra tataunawa dan idasa shirya lamarin daurin auren, sannan sunna jiran matan da suka zo da sha tara ta arziki na akwatunnan amaryar su shigo su shaoda masu cewar sun bada kuma an amsa
Wayar dake hannun Chief of army ce ya sake bugawa a karro na bakwai, zuwa yanzun an daga sannan da muryar da ya amsa ya saka shi yin dan Murmushi yana fadin" Kai fa ka ce da kai za'a daura auren nan, kuma ka ga mu tuni muna tare ka da san aminina ne Ganaral, me zai hanna na jiyo jiniyar sojojinka kun karaso anguwar ne? Ka zo son zan ji dadi idan ka zo"
Goshinsa ya tatare yana mamakin lamarin Father dinsa, yanzun har sun je wajen daurin auren da aka saka karfe tara za'a daura shi? Eh lalle yaron nan dan gata ne, watau sun je su yi jiran bakinsa ne ko?
Dan nishi ya dan fitar kasa kasa ya ce" Zan zo "
Chief of army ya yi yar dariya yana fadin" Ina duban hanya "
Daga nan ya kashe yana fuskantar baban Hamza ya ce" ka ce min tun zuwan nan da ya yi sau daya da na ce ya je bai kuma komawa ba?"
Daria ya yi yana fadin" Haba aminina kaima ka san zuwanma da ya yi dan maganarka ce ai, ka ga ranar farin cikin da na yi kuwa? Allah dai ya kara girma aman garin nan ana tsoton Lieutenant ganaral walahi, baka ga yadda ake kwasa tsakaninsa da mararsa jin magana ba"
Shima yar dariyar ya yi ya ce" Ai ana cen ana kwasa da mamansama, aure fa aka daura masa sau biyu kadai ya je , kuma a zuwan nasa biyun sau daya tak suka hadu da matar, cewa ya yi mahaukaciya ce sai tana kafeshi da ido kamar mai farfadiya, kai dai ana nan ana fama da rigimarsa "
Ire iren hirar da suke ta yi kennan sunna shan dariya ga zazafan kunnun fulawa da ya sha uban madara da kayan kanshi yana turiri yana ta tashi a gabansu an zuzuba masu a manyan kofofi na kwalabe , ga sanyin AC da falon ya dauka kai abin dai sai hamdallah kawai
A cen cikin gida kuwa a falon matan Malan bayan an karbi kayan amaryar matar Malan uwar gida itace a tsaye a gaban lamarin, domin a lokacin da malan ya yi tsaye ya dubi idannuwanta ya nuna mata yin hakan shine farin cikinsa ya saka ita kuma mikewa da dukan kokarinta da zuciya daya ta amshi su Shuwwar harma take hidima da su Ko a yanzun matan da suka zo da akwatunnan sun samu tarba ta mutunci har sun cika da mamakin gannin hakan duba da yadda dan uwansu ya fada masu cewar ko me suka tarar kar su saki su nemi wulakntar da yarinyar, idan har suka ga wani abin batanci a tare da ita kar su manta d'an yar uwarsuma yana da kashi a cikinsa a haka suka amshe shi suka nuna masa so har zasu bashi y'a Su abinda suka tarar kwata kwata basu ga abin tsatsamta ko na wulakanci ba Sai da aka gama zube akwatunnan da suka girgiza matan daje falon Nahidt ta fito da waya a kange a kunnenta tana amsa Hamza dake shaida mata suma sun taso da jama'ar daurin aure sun nufo gidan Malan din , hakan ya sa ta shigo falon tana murmushin da ya sake fitar da kamaninta sak sak sak da mahaifiyarta, domin idan baku manta ba Nahidt ce ke kama da mamansu, Shuwwar kuwa ta dauko kamani da mahaifinta wanda shi har suka rabu da shi ya ki jinnin ya ji an ambaci sunnan kasar nan, mutane da yawa kan cewa ai kurciya akai masa wada ta fitar da shi daga kasar kwata kwata harma ya ki jinnin maganar kasar bale mararin dawowarsa cikinta
Idannuwanta ne suka shiga cikin na matar da ta mike tsaye a tsorace ta kafeta da ido Bakin matar na rawa tana nuna Nahidt ta ce" wannan wannan wannan wacece?"
Amaryar Malan da ta san dama a rina, harma zuciyarta ta gama dumewa da farin cikin gannin haka ya fara bayana, a zuciyarta ta ayana'an zo wajen, dama na san wani sai ya gane da wannan karuwar ce zamu aurawa danmu kanwarta?' hakan ya sa da gagawa ta ce" Wannan? Ai yayar amaryar ce, sunnanta NAHIDT, gidansu a nan baya yake shi Malan din ai taimaka masu ne yayi duba da ba tare da iyayensu suke zaune ba" (Dan adam kennan, domin ba zan ce malan bahaushe kennan ba dan kuwa kaf duniya akoy masu irin halayen nan a kowani yare, hanyar da zata bi ta hanna farin cikin wani take nema dan kawai tana jin tsoron rabarta da farin cikin ke iya yi ya saka ta zama tamkar mahaukaciya)
Dukan mutanen falon da mamaki ita suke kallo da wannan dogon jawabi haka Da sauri matar ta sake kallon NAHIDT da ta yi mutuwar tsaye cikin shagarta ta watsetsiyar farar shada ta sha zubi blue mai haske da fari hakan ya sa shadar kara fitowa sosai take kyalkyali
Matar ta kai dubanta da sauri kan hannun da ya riketa wace ke zaune a kasa muryarta kasa kasa ta ce" Gimbiya ki zauna, nima tunda na ga wucewarta tun dazun sai da na mata irin kallon nan, aman kema kin san ba zai taba yiwuwa ba, ki zauna kin ji?"
Ina hannunta ta janye tana karra kallon NAHIDT da gaba daya duniyar take neman yi mata zafi da mugun tsoro da fargabar kar a kuma fasa auren kanwarta Daidai Fauziya ta fito da Shuwwar tana rike da hannunta ita kuma tana sanye da doguwar farar riga mai laushi sai hijab dinta fari dogo sosai har kasa wanda ta sha wankan ruwan turare da na wuta ya kasance shigowarsu ya sake harmutse kanshin falon sai dadadan kanshinta ya sake dauke dakin gaba daya , a lokacin ne kuma matar ta sake zuba mata ido itama tana kallonta
Kanta ne ta ji ya fara juyawa, harma ta fara tunanin ko ta haukace ne da yan matan nan biyu daya ke kama da yar uwarsu da ta bace masu bat, dayar kuma, wannan din kuma bata yi maki kama da hoton sarkin garin nan marigayi ba? Har farin fatarta? Hoton dake kafe a falon Aba wanda bayan ya rasu aka dora kanninsa da suke uba guda domin d'ansa na cikinsa an wayi gari ba shi ba labarinsa? Hajia duba ki gani ko dai yau na tashi a haukace ne? Ko kuma gajiya ra saka nake hade haden nan?
Hajiyar ta juya wajen da NAHIDT ta ja su Fauziya jikinta na rawa tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une kin ga Shuwwa abinda na so na fahimtar da ku cewar anya zuwan nan namu nan alkhairi ne kuwa zai tabata, kin ga matar cen ta malan ce take son kwatanta kamar zaman kanmu muke yi kin ga matar cen da suka kawo kayan ta kafemu da ido har ana son zaunar da ita ta ki zama mun shiga uku"
Hankalin Shuwwar ne ya yi kololuwar tashi ta juya zata kalli matar daidai matar ta fice da mugun sauri, hakan ya sa ta dora hannayenta bibiyu a saman kanta tana fadin" Idan aka fasa auren nan shikenan, shikenan aunty , idan aka fasa walahi ina iya rasa raina, wayo Allahna na tafi wajen Aban na fada masa ya rufa min asiri ya daura kin ina son Hamza, walahi ina sonsa idan ba'a aura min Hamza ba ina iya mutuwa"
Da mugun sauri ta juya itama har bata gannin gabanta hakan ya sa suka mara mata baya sunna son tsayar da ita aman ta kasa sauraronsu ta nufi falon da ta san a cen Aban yake
Tunda matar nan ta shigo kanta je kasa jikinta na dab rawa ta sake maimaitawaa yayansu wanda yake shine baba a dakinsu gaba daya ta ce" Allah ya karra maka lafia walahi, walahi kamanin sun bace, yarinyar tamkar an zaga karra da *TINANA* , sai dai kuma kamanin yar uwar tata ne suka sakani a rudu, me hadin kamanin marigayi sarkin garin nan da nata? Har farin bayan kar duniya mun san d'a daya ya malaka har ya koma ga ubangijinsa, yarinyarma ta yi kankanta ace y'arsa ce gaskiya idan aka auna mutuwarsa da yanzu"
A guje ta sake warce hannunta ta fado dakin tana neman fuskan Abanta dake zaune shika hankalinsa a tashen yana son jin karshen maganar nan Da sauri ta idasa gabansa ta duka tana hade hannayenta ta fashe da wani kukan da ya saka kowa juyowa kallonsu ciki harda CHIEF of Army da iyayen Hamza , daidai NAHIDT ta karaso ita dinma tana kukan ta tsuguna a gabansa itama ta hade hannayen nata hakama Fauziya ta shigo itama nata hankalin a tashe
A gigice take son yin magana aman ta kasa hakan ya sa Nahidht farin" Sun ce sun fasa auren su dinma ko MUHAMAD ? zasu daina aurenta ne ko? Shikenan haka zamu kare rayuwarmu dan bamu da iyaye?, Menene laifinmu?, Dan Allah ku rufa mana asiri kar a fasa domin ko ni idan aka fasa auren nan da Hamza na shiga uku, dan Allah ku dubi maraicinmu ku bari a yi aurennan, idan har dan maganar amaryar malan ce kar ku dora hakan a kan Shushu, mu mune bama jin magana aman shushu babu abinda ta sani , burinta ta yi aure, burinta ta je ta bautawa aure, burinta ta samu kanta a dakin mijinta, ku yi hakuri a yau a daura auren nan, ko a nan ne a daura kawai ba sai sauran sun zo ba....." Ta idasa da fashewa da kuka daidai Aban Hamza ta mike yana karra kallonsu muryarsa har rawa take wajen furta" *TINANA?*"
DIF Nahidht ta yi da ihun kukanta jin an ambaci sunnan mahaifiyarta wada ba zataa taba manta wani lokaci ta taba gannin takardar mahaifiyarsu da sunnanta na usil banda Buzuwa da ake kiranta da shi
A rikice ta juyo tana kallonsa, shima kuma ita din yake kallo hannunsa still na rawa ya sake fadin" *TINANA?*"
Zabura ta yi ta........
*GARABASA GARABASA, DUKAN WADDA TA BIYA KUDIN ALKALAMIN KADARRATA ZATA SAMU GARABASAR WATA KOKOWAR KYAUTA IN SHA ALLAH, WANNAN GARABASA CE🥰*
Domin samun ci gabansa in sha Allah ki garzayo ki biya kudinki yar uwa, a kan farashi mai sauki ..........domin a gaba ne zamu gane kaifi irin na ALKALAMIN KADARAR bayin Allahn nan Me yake shirin faruwa da su Ina zasu dosa? Yaya maganar gagarumin daurin auren nan da ake shirin daurawa?
Su SHUWWAR da NAHIDHT su wanene su?
Me dangin Hamza suke nufi da maganar ambaton Nahidt da sunnan yar uwarsu?
Meye gaskiyar maganar kamanin SHUWWAR?
Dukan wannan zai zo a bayane a tsare ta yadda mai karatu zai karanta cikin shauki in sha Allah
Daga alkalamin SAJIDA😍🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
+22793811618💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 1️⃣6️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Zabura ta yi ta mike daga tsugunen da take a gaban Malan har sai da daurin dake saman kanta na dan kwalinta ya fadi kasa warwas tana kallon Aba Muryarta ce ita dinma ta dauki rawa rawa ta ce" Ba, Ba , mamanmu ce *TINANA*"
A bayane Aban ya karaso da sauri yana rike hannunta yana fadin" Hasbunnalahu wani'imal wakim, mamanku? Ke da wa? Inna take? Inna TINANA take Hawau itace, kin ga itace wannan din jinninmu ce, yarinya ina TINANA? Ke din ke da waye kika ce mamanku ce TINANA?" Sai kuma ya yi shiru da gagawa ya juya wajen baban Hamza da suma gaba daya hankalinsu ke kan su SHUWWAR din balema Chief of army da yake kallon yarinyar da tausaya
Yana zuwa ya ce" Elhaj, ka ga wannan ai jinnin Hamza ce, yar mamansa ce, ko ba haka kike nufi bane yarinya? Dan Allah ki fahimtar da mu kamanin nan naki da kanwarmu"
Gannin du a rikice suke ya saka Ganaral fadin" Bismillah, Elhaj ka zauna ka ga yarinyar du ta rikice kana gannin kanwarta itama du ta shiga a halin rudu, ku zauna mu yi magana a tsanake dan Allah".......daidai nan kira ya shigo a wayar Ganaral hakan ya saka shi dagawa yana mai amsawa
A nutse ya furta" Masha Allah, ka sa abokinka ya kula da baki ka shigo a nuna maka falon da Malan ya sauki baki muna ciki, ai da dan saura lokacin daurin auren bai cika ba, ba za'a tsayar da mutane ba, ka shigo "
Daga haka ya katse yana fuskantar mutanen dakin shima ya kasa yin magana
Malan da Shuwwar ta yi karkadab da hannunsa ne ya samu a hankali ya janye yana sauke ajiyar zuciya a nutse ya furta" alhmdulilah, in sha Allah dukan abinda Allah ya yi a yau alkhairi ne, domin zabinsa muka nema, shi muka fadawa, koda na tsayin sati takwas ne kadai muka dauka muna fada masa zamu iya cewa Alhamdulilah sannan mu yi hasashen cewar ya ji mu ya kuma amsa rokonmu, NAHIDHT da SHUWWAR, shin zaku iya saka nutsuwa a firgicin dake tare da ku ku bamu labarin abinda ya faru da iyayenku har kuka samu kanku a kasar nan?"