Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 18
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 18: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 18. Wani irin yamyamyam jikinsa ya kwasa, wani irin abu ya ringa yawo a…
3,344 words
Wani irin yamyamyam jikinsa ya kwasa, wani irin abu ya ringa yawo a sasan jikinsa yanna kallon abokannan aikinsa da wani irin kalloai cike da sakwani kalla daban daban A duniya dama idan kana son gannin hadin kai na ma'aikata to fa ka zo kan soja ka tsaya kennan, ko a titi ka zago soja daya sukan dauki haka a matsayin ka zagi CHIEF OF ARMY ne, idan ka zagi CHIEF OF ARMY kuwa yaya sunnanka?, Sunna da hadin kai, sunna da fahimtar junna, sunna da kaunar junna, uwa uba sunna da daraja manyansu
Kudaden ya saje kallo sai hada kansu ake yi suka kama naira dubu dari bakwai da sitin da biyar
Idannuwansa ya lumshe yana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da mugun karfin tsiya
CHIEF OF ARMY ne ya sake dubansu da karfi ya shiga rera wak'ar sojoji mai saka su taka rawa da karfinsu yana fadin" Agali dogo Agali soja dan Allah agali kai mana gafara!"
Gaba daya anguwar ce ta dauka, da muryoyinsu budadu da basu da wasa idan sunna rera wakarsu, hakan ya sa matayen dake cikin gida fantsamowa da mamaki sunna fitowa dan gannin abinda yake faruwa a lokacin da sojojin suka dire wak'ar LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN YA DAUKA da karfi bayan ya idasa bayana a gaban duban al'uman nan ya daka kafarsa a kasa ya kara ya fukancesu ya bude budadiyar muryar nan tasa ya ce" NA KULE KAYANA, ZANI GIDAN SOJA, GAWA UMA TAI MINI GAFARA, GAYAWA ABA , YAI MINI GAFARA, YAYU DA KANAI KUY MINI GAFARA, IN NA JI DADI CEN NAKA SHEKARA, IN BABU DADI DAWOWA NAKAI DAN NA SAN G I BASU RAGA MINI!" Da wani karfin fiye da na farko harda CHIEF OF ARMY cikin malun malun dinsa aman kasancewar tsumin ya motsa yana gaba gaba shima ya sarawa MUHYIDEEN suka dauki amshi da karfinsu sunna fadin" AGALI DOGO AGALI SOJA GIDAN MAZA BA GIDAN MATA BANE!"
Subahannalah idanma jikinka bai iya daukan bari ba dole tsumar manyanmu, iyayenmu, sojojinmu, masu sadaukar da farin cikinsu, lokacinsu, komai nasu sunna zaune a jeji , sunna kwana a cikin rami, sunna kwana a saman duwatsu, sunne a sahara, sunne a wajen ruwa, sunna yaki da dukan masu son kawowa rayuwarmu hari, a dole ka samu kanka da sara masu harma ka zubar da hawaye ka kwashi rawa Koda baka shirya ba, bale soja da waka sai gani sai bari, kai harta da su Malan dake hakimce sai gasu jikinsu na bari bayan su din ba sojojin bane
Idannuwansa sun kade sun zama tamkar gota ya juya wajen da Lieutenant Maman Sani yake da dan karfi ya furta" Lieutenant zube kudin jakar nan, DAD idan sun yi kadan a bamu lokaci kankani ba tayi mun sayi tsadarta ko wacece!"
Ya salam wata buda tsofafin dake kallo suka cira da ita mai kaifin gaske, waje fa ya sake daukan harama, CHIEF OF ARMY kuwa ya damki kudade ya hada da wadincen ya zube a gaban Malan yana fadin" Alhmdulilah, ga sadakinmu Malan, a bamu muna roko da kokon bararmu"
Dole mutun ya yi hawaye, bama kamar Abansu Hamza, jiki na bari aka shiga gabatar da daurin auren manya Dukan kowa ya nutsu har liman ya shafa fatiha inda aka dauka da taratsi irin nasu sunna sanar da fatiha.....hakan ya sa kowa shafawa
A hankali ya dago hannayensa daga tsayen da yakr ya shafa fatiyar yana jin kansa na sara masa Shi yau ya yarda da maganar malan mahaushe, ya fito kama barawo yau barawo ya kama shi
Gaishe gaishe ake yi, hakan ya saka shi neman hanyar da zai silale dan ya koma wajen aikinsa ko zai samu hayaniyar da DAD ya siya masa ta dan sake shi, gaba daya kwaramniyar wajen ta dame shi
Hannunsa da aka rike a lokacin da yake dan sauri dan ya gifta kofar gidan ya tafi ya saka shi juyowa a nutse yana kallon Abansa
Murmushi CHIEF OF ARMY ya yi ya ja hannunsa ba tare da ya ce da shi komai ba ya nufi cikin gidan da shi a ransa yana ayana' Akoy rigima, akoy kura, Allah ka sa mu fi karfinsa'
Mutanen dake tsaitsaye suke nausawa sunna shigewa, a nan ake nununa shi ana fadin wai Allah shine ya auri SHUWWAR? zuciyar amaryar malan tamkar zata buga, dama wannan rantsatsen sojan na jarida ne zai auri wannan yarinyar? Balaki, bilahilazi in wani tudu in wani gangare sai ta bi ta fada masa shima ya yi hankali ya kwashi HIV!
Hannunsa ya dan ja yana kallon Father wanda ya juyo yana kallonsa
Sai da ya dane dukan bacin ransa kasa kasa yana hararen mutanen dake kallonsa kar wasu mahaukata ya ce" Bayan auren dolen ina kuma zaka kaini ne?"
Father ya yi murmushi bayanane ya sake jan hannunsa yana fadin" Inda su Malan suka shiga zamu je, zo mu tafi mana "
Bakinsa ya dan tabe yana biye da shi har suka shige falon
Kanshin falon na nan, sanyinsama haka, koke koken da ake yi kuma ya dan tsagaita asalima su da suke daka sun dunkule waje daya sunna jira ne a shaida masu an daura auren Fauziya da Hamza dan su tatara su koma gida gaba dayansu da Hamzan wanda ya ki motsawa nan da nan daga kusansu , asalima a jikinsa ne du suka dodora kawunansu, sannan kasancewar kofar fallon mai madubi ne mai nauyin nan ya sa ba'a jij abinda yake faruwa a waje hakama abinda yake faruwa a ciki na cikin ba zai ji ba
Tunda su Malan suka shigo yan matan da Hamza suka dago sunna kallonsu, hakan ya sa shigowar MUHYIDEEN da CHIEF OF ARMYMA a kan idannuwansu ne
Gabanta ne ya tsili, ya tsilira ya rugurguzo ya zubo kasa a lokacin da ta ga fuskar la'ananen da ya yi kiran kuraya fa ita ya kashe mata aure wanda ya kara saka mata tsantsar tsagwaron tsanar sojoji bayan wace take da ita a ranta ta da cen cen cen
Idannuwanta dake warwaje ta sake rukowa a kansa lokaci daya ta kama hijab din nan ta cire dan bilahilazi a yanzu sai ta ji hijabin zai shaketa ya kasheta domin kwata kwata ta nemi numfashi ta rasa , wani tashin hankalin ganninsa kadai ya sakata nuno shi da yatsarta manuniya tana fadin" Kai? Me ya kawoka gidan nan? Hala kaima abokin Wani ne a nan? Baka san na yiwa kaina alkawarin idan na kuma ganninka sai na shakeka ba? Aunty kin ganshi nan, shine Wannan, bari ka gani!"
Tana fada ne tana dira ta tsalake kafar Hamza dake mike yana kallonta da mamaki baki bude, hakama duk wani dake falon kai balema wa'inda suka gama daura masu aure yanzun sun fi kowa kamewa a tsaye sunna kallonta a lokacin da ta nufo LIEUTENANT GANARAL dake tsaye kikam yana kallonta da son tinano a wajen da ya santa ta dira, ta cira ta ........
😂😂😂😂 Comment hlz😭😭😭❤️❤🔥❤🔥 ALKALAMIN KADARRATA❤️❤🔥❤🔥
Na SAJIDA
1️⃣8️⃣
Babu wanda ya kawowa ransa cewa a cikin kasar nan, a kusa kusa akoy halitar da zata nufo MUHYIDEEN da wannan garajen a lokacin da ita SHUWWA, yar mintsiniyar Yarinyar nan ta daka tsale ta nemi kai hannayenta wajen wuyansa dan ta aiwatar da alkawarin da ta yiwa kanta na sai ta shake shi idan har ta hadu da shi ko a ina ne, ta kuwa nemi aikata hakan a haukace tana fadin" Bayan ka jaza min ya maka min sakin a ofishin sojoji tamkar wata yar ta'ada, shine zaka kuma yin gigin zuwa wajen nan? Wollah yau ko ni ko kai a gidan nan!"
Dan kaucewar da ya yi yana sake kallonta da fasarar ko ita wacece na shirin darsuwa a cikin kwakwaluwarsa, lokaci daya ya gane yarenta ya kuma haskota harma ya tuna ko wacece ita da lokutan da ya ringa ganninta kwaya biyu tak
Abinda ya sa gaba daya ta bace masa mugun gyaran nan da ta dauka na mamaki wanda ya karru a kyanta na da
Da mamaki ya dan motsa hannunsa yana tareta dan sake zuwa ta yi da kai kamar rago tana son kawo masa tunguzo tana wani ihun fadin" idan a cen kana takamar da yarenka a wajen ai gashi yau na kamaka babu mai iya tare maka!"
Sallalamin da iyayen ke yi a bayane ne ya saka Malan da ya yi mutuwar tsaye dan zabura kamar an gwaura masa mari da madaukakin mamakin al'amarin Shuwwar da ya kisan sumar da shi wai harda yau ta kama wannan bawan Allahn da idan a hadiye ne zai sakata a bakinsa ya hadiyeta ba tare da ya sha ruwa ba domin ba zata gimshi makoshinsa ba
tafa hannunsa ya yi ba shiri dan shine abinda ya fara zuwar masa kwakwaluwa kusa kusa yana fadin" Subahannalah, Ke Shuwwa, ke Shuwwa meye haka wai? MIMIMIMijinki ne fa, me kike yi haka ne wai?"
SHUWWAR da ta ja wata dungar sai ta samu kanta da yin kiskirim tamkar an zabga mata bulalar rakumi a fuskarta ta dauke hankalinta gaba daya na sekwani kafin ta saketa, dan kuwa sai da ta maimaitawa kanta yaren malan a cikin kwakwaluwarta tamkar karatu kafin ta iya fasa bakin ta gane me ake nufi, hakan ya sa a hankali ta juyo tana kallon Malan da mamakinsa ya kasa boyuwa hakama dukan mutanen dake wajen , ita kuma da wani kallo kamar na tsoron abinda ya fito a bakin Malan din bakinta na rawa rawa ta ce" Innnnnnna ce aure aka daura na Fauziya da yayanmu, ni kuma nawa sai na samu wani mijin kau Abana?"
A yadda ta yi maganar zaka gane baban burinta Aban nata ya bata amsa ne da eh y'ata, sai ta samu déception mai matukar girma a lokacin da yake furta mata kalamai kamar haka" Bayan an daura nasun kema aka daura naki da LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY na kasar nan baki daya wanda daga CHIEF OF ARMY sai shi a iko a kasar nan, shine a tsaye a bayanki gayanan kike aikata aikin nan haka IBTISAM!" Ido, baki sa Hanci su NAHIDT suka zarro gaba dayansu harda Hamza jin wai LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY ne aka aurawa kanwarsu? Wauh , su abin ya basu sha'awa ne, ya birge su ne, ya taba zuciyarsu ne
MUHYIDEEN din kuwa da mamaki ya kalli CHIEF of army yana nuna Shuwwar dake daf da kafafuwansa muryarsa ciki ciki ya ce" Dama wannan ce ka aura min Dad ?" Da hannayensa ya nuna wajen kansa alamun gyadi gyadi ya ce"Mahaukaciya ce fa, nd yarinyar nan du haduwar da na yi da ita sau biyu kadai na gane banda harkar aure auren maza ba abinda ta iya.....ni kuma meye hadina da mace irin wannan da bata da kishin kanta? Kuma ma Barauniya ce har kudin mutane take kwata, Lolz Dad me zan yi da bazawara wacce maza sukai ta dauka? Wannan ai zubar min da mutunci ne za'a yi a cikin kasar nan Father............... ka ga kawai ta je na......."
"Idan bakinka ya bude ka furta kalmar saki wa wannan yarinyar ka sani ka nuna min ni ba kowa bane kuma ba zan taba zama kowa ba a rayuwarka, domin da ace ELHAJ NE Allah ya jikan rai ya daura maka aure ko kafura ce zaka yi hakuri ka daidaitata har ta dawo ra zama musulma!, Idan har ka saki yarinyar nan MUHAY ka wulakantani kuma bana tunanin akoy abinda zai sanyaya min zuciyata dangane da kai har na koma ga ubangijina, idan har ka saketa dan kawai batai maka ba ko dan wani abin ya shiga tsakaninku da ya hadasa maku gaba ka wulakantani Muhay ka nuna min iyakata kuma ba zan taba yafe maka ba, Muhay idan ka saketa dan ta auri wasu kai din ba bazawarin bane? Nawa ka aura ka saka? Kennan sai a zageka da haka? MUHAY yarinyar nan ta zame maka mutu ka raba takalmin kaza!,, Mun gaji hakanan MUHAY, mun gaji, ao kake duniya ta idasa karda zargin da ake yi maka ne? Ko so kake mu shiga uku mu dawo abin nuni da baki? Meye yake yawo a kanka ne? Me kake son nunawa ne?, Kai mai daraja ne mai mutunci ne, jinnin mutunci ne, yaya zaka budi baki wannan karron ka yi saki irin na jahici bayan kana da ilimi?, I'm sorry my freind kana da damar sakinta ko barinta, aman ka sani idan har ka saketan hakan na nufin ni da bake takama da kai da bugun kirjina da kai ashe ni ba kowa bane ba kuma komai bane haukana ne nake yi a duniya ban sani ba?, MUHAY mahaifiyarka kuma zaka karra kuntata mata a kan sake saken da kake yi, Bismillah kana da damar sakintan bismillah" Father ya tari numfashinsa da sauri yana fada
A haukace ta juyo ta daga kanta dan ta matse masa wuri ta yadda dole sai ta yi hakan zata iya duban fuskarsa domin ya fita tsayi
Ido cikin ido suka kalli junna tana motsa bakinta tana masa alamun kamar wace ke furtawa kanta kalmar sakin haka kuma lokaci daya ta hade hannayenta a yau da bakinta ita SHUWWA dake neman aure ido rufe ne take furta "Furta, ka ga, manta maganar babanka ka yiwa girman Allah ka sakeni, ka furta dan darajar mai daraja a duniyarka"
Tsaf ya gama hardace abinda take fada A hankali ya lumshe nauyayun idannuwansa yana sake yarda cewar she is md ya sake budewa ya sauke a kan fuskokin mutanen dake falon baki dayansu har ya dawo kan fuskar SHIEF OF ARMY
Idannuwansa ya lumshe a kansa ya sake budewa a kansa a hankali cen kasan makoshi ya furta masa " Fine it's k "
Daga haka ya juya yana taku irin nasa na sauri mai cike da balaki da tashin hankali da bacin rai ya bar gidan kwata kwata yana tataro jama'arsa yana ayana 'yau zaku gayawa yan garinku tunda sai da na ce ban fito da kudin aure ba kuka hada akai min, daga ku har ita sai kun yi dana sanin sanina a rayuwa!'
Ihu ta kurma tana dukewa a wajen tana bubuga hannunta a kasa tana fadin" Wayo zai tafi bai tsinken tashin hankali ba, ku dawo da shi ya sake ni, wayo na shiga uku na rantse sai ka sake ni, kai waye ya aura min shi? Waye ya aura min soja? Waye ya aura min wannan? Walahi da na tare da shi gwara yara su maida ni biri a kula min igiya ana wasa da ni a titi, da na aureshi gwara na auri Abdul dan mai shinkafa, kai da na aureshi gwara na zauna a haka shine alkhairina, wayo sun kasheni , idan ka yarda na tare a gidanka sai na halaka farin cikinka, sai na wulakanta zaman lafiyarka sai na???????....". Firgitttt ta mike zata kuma saka wani ihun sai kuma lluuuuuuuuuu ta tafi sakamakon sumewar da ta yi numfashinta ya dauke gaba daya ta dimu a kasa kusa da cafet
Sallalamin dake bakin baban Hamza ne ya samu ya fara ambata, hakama CHIEF OF ARMY
NAHIDT ta sauke ajiyar Zuciya tana fadin" Allah ya takaita rigimar, yanzu bara mu samu mu kaita wajen da idan ta farka za'a samu sasauci, MUHAMMAD ina zamu kaita ne?"
Sai da gabansa ya fadi da ta wani ce Muhammad kai tsaye hankalinta kwonce kamar wani d'anta , shi walahi tsabar girmama shi da mutan anguwa suke sunna boye sunnansa da matansa ya sa idan ya ju an ambaci sunnansa kai tsaye har gabansa ke yankewa ya fadi
CHIEF OF ARMY kam Shima sai ya farra tunanin to ko dai bata da lafiyar kwakwaluwar ne?
A sanyaye ya furta" Ya salam, Elhaj anya bamu yi gagawa mukaa yanke hukunci wa yarinyar nan ba tare da mun tuntubeta ba? Ni na dauka farin ciki zata yi da Allah ya bata Son, ka ga hankalinta ya tashi harda sumewa ko dai na maido shi na janye masa magangannun da na masa a kan maganar sakinta ya saketa ko zata samu nutsuwa?"
Da sauri Malan da ya gama kiran likitar dake duba matansa ya ajiye wayar yana fuskantarsu a nutse ya ce" Aa ranka shi dade ba za'a yi haka ba, dan Allah a yi min alfarma a barmata aurenta a kanta, ni na san idan ita wuta ce shi ruwan kashe wuta ne, na tabata zasu zauna da junnansu, kar a kashe auren nan dan ta tada bali, a basu dama idan har basu jitu da junna ba zuwa gaba sai a raba auren, ka san wancen sakin da akai mata dan ya saka an kaisu ofishinsa ne ya sa aka saketa shi yasa ta kulace shi"
Su kam sun ga abu, sun ga mamaki gannin idannuwansu sun kuma kamu da mamakinta har karshen rayuwarsu, ta yadda ta cira din nan nufinta me ta so aikatawa? Kai da wani lusarinema da ta kai masa walahi, anya kuwa zamansu zai yiwu?
Gogonsu ce a sanyaye ta ce" Malan, da Abansu, da Elhaj dan Allah ina so a bani yaren nan mu je gida na basu kulawa koda ta ta sati daya ce , dangi su gansu, a fadawa dangi ga iyalin TINANA , sannan a saki sanarwar nemansu, ni na kasa yarda cewar sun mutu, yaya kuma yaya maganar sunnan nan?"
Wani kakausan kallon da ya watsa mata dake nuni da baya so a taso maganar sunnan mahaifin su Shuwwar ya sakata yin gum da bakinta
Watau gaba daya abin ya rudar masa da kansa Ta so su je kai tsaye gidan sarautar garin nan da yan matan wani tunani ya darsun masa a zuciyarsa wanda ya barawa kansa sai Allah , so yake ya bi komai a ilimance ta yadda zai warware kullin da ya daure masa kai a kan lamarin nan, ya tabata wanda ya yi sanadiyar barin babansu kasar nan koma waye yana bibiye da rayuwarsu ne kuma in sha Allah sai ya gane abinda yake binne!
Zigum zigum dai suke, gogonsu bata samu amsar bukatar da ta gabatar ba domin kowa cikin mazan nan yana da kalar nasa tunanin a kan hargitsin da ya hanga dangane da rikicin zamantakewar MUHYIDEEN da SHUWWA, sunna nan du hankalinsu tashe har likitar ta zo
Ta dubata sosai, ta yi mata dabarun da zasu dawo da ita cikin hayacinta, sai dai tana farkawar da wata rigimar ta farka ido rufe tana fadin" Haba dan Allah, Aba, Aba ka gani kau? Hala shi Aalkalamin kadarar tawa da ake fadi bashi da lafia ne? Ya tashi ya rasa inda zai zana ni yau kuma sai aure da kumurci?, Gwara ya gane rayuwa ya sakeni, domin zama da ni babu alkhairi, ya sakeni na ce!"
Da dan sauri NAHIDT ta karasa kusa da Malan sosai ta yadda sai da ya dago idannuwansa a tausashe yana kallonta ya dan katsa kadan , Ita dai bata damu ba ta yar uwarta take ta rage muryarta sosai ta ce" Ka saka a maka mata wata allurar barci mana kar fa uban mijin nata ya saka a saketa dan bata da hankali, kai ka san hankalinta ne a tashe idan ta farka ka totofeta da adu'a ka mata nasiha zata nutsu ai ka sani ko? Kar ka bari a sakar maka y'a Shuwwa zafa ta rikice ta fara halaya mararsa kyau fa"
Ajiyar zuciya ya sauke kawai ya sake matsawa kusa da likitar a tausashe shima ya yi mata bayana, ai kam ta ce" Ai nima Ustaz abinda nake ta tunani kennan domin jinninta hawa yake yi, gwara a bata nutsuwa ta samu isashen barci, bara nai mata allurar barci Allah ya sa na zo da jakana"
A haka aka samu akai mata Hamza na rike da ita tana dan fuzge fuzge da kyar aka samu ta yi lakwas ta kwonta jikinta ya saki sai barci yaa dauketa
Ajiyar zuciya du suke saukewa sunna kallon kyakyawar fuskarta mai alamu da innocent face, kamar idan ka saka yatsarka a bakin Shuwwa ba zata ciza ba, gashin kanta kuwa ya yi mata lumbuk a gaban goshinta , lebenta yaa sake yin ja sai kyalkyali yake yi na abin dan tawun samman lebenta da take cijewa a ciki alamun rigima na cinta iya ci