Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 17

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 17

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 17: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 17. A hankali SHUWWAR ta girgiza kanta tana fadin" Mun je, mun sake zuwa,…

3,336 words

A hankali SHUWWAR ta girgiza kanta tana fadin" Mun je, mun sake zuwa, mun fadawa mutane sun tayamu nema bamu ga gawarwakinsu ba har aka yi suturar mamata ranar juma'a , a lokacin kuma aka hanna mu shiga dan karancin shekarunmu aka koremu, daga baya mun je kaburbura mun yi ta bin sunnaye aman kun san yawan wajen da girmansa har aka kamo mu aka dawo da mu kasar nan bamu samu muka gama zagayen makwontan ba, sai dangana muka yi kamar yadda makociyarmu ke fada mana cewar mu yi hakuri mu bisu da adu'a, sun rigaya sun rasu babu yadda muka iya hakan muka yi hakuri har aka gama aikin haji aka koma daga nan aka dawo da kame, muka taki rashin sa'a wata fita da mukai zamu je gidan da muke goge goge aka kama mu aka kawo mu kasar nan"

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une..... shine abinda aban Hamza ke maimaitawa kansa a kasa yana girgiza kan nasa Gogon Hamza ta yi gagawar fadin" Dan Allah bayan Buzuwar bata da wani sunnan ne? Yar budurwa kamar na ji kin ambaci wani sunnan bayan wancen?"

Du irin yadda ta cika da tsoron maimaita sunnan da ta taba gani a takardar mahaifiyarta haka ta budi bakinta ta ce" *TINNANA* "

"Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam, dan girman Allah yaya wadinnan yayan Tinanarmu ne, walahi y'ayanta ne Innalilahi wa inna ilaihi raj'une TINANA ta rasu? Ta rasu bamu nemi gafarayar junna ba? Ta rasu bamu nemi afuwar juya mata baya da nuka yi dan ta samu ciki ba? Ta koma ga mahalincinta da mikinmu a zuciyarta? Wayo Allahna"

Hamza da cikinsa ya juya daga zaunen da yake ya yi raf da hannun babansa yana zarro ido ya juya yana kallon baban nasa bakinsa na rawa ya ce" Babana mu je a daura auren mana, daga baya sai a dawo a tatauna inaga kamar sun san su Shuwwana ne ko?"

Da tausayi mahaifinsa ya kalle shi yana jimke hannunsa da kyau ya maida dubansa kan CHIEF OF ARMY da ya yi dan gyaran murya ya kalli NAHIDT, ya kuma kallon Hamza, ya kalli Shuwwa ya maida dubansa kan iyayen nasu, a tausashe ya furta" Subahannalah Astagfrullah, subahannalah "

Gogon Hamza ta girgiza kanta tana fadin" Wani daurin aure Hamza, wadinnan kannenka ne uwarku daya da su Hamza, mamanku daya fa da su, ai ka san ba maganar aure tsakanin jini daya ko Hamza"

Ido ya zarro yana son mikewa tsaye jikinsa na rawa haka Shuwwa itama ta mike tsaye lokaci daya idannuwanta na firfitowa waje ta juya da sauri tana kallon Hamza sannan ta juyo tana kallon NAHIDT da ta yi mutuwar zaune hannayenta bibiyu saman kanta

Maimakun ta ji salati ya fito daga bakinta sai wani ihu da ya fito da karfi ta kurma shi tana dora hannayen nata itama su biyu a saman kanta Idannuwan nan nata masu rukowa waje ta karra rukowa a birkice ta furta" Auntyyyyyyyyy" sai kuma luuuuuuuu ta tafi sakamakon juwar da ta kwasheta ta nemi makata da kasa

A tatare suka nemi tareta ana ta di kira da salamewa daidai wayar Chief of army ta kuma daukan tsuwa hakan ya sa cike da tausayi ya mike yana amsawa

A birkice NAHIDT ta kalli Malan tana fadin" Muhammad, ba za'a daura auren ba kennan?"

Malan gannin sun rikice yana kallonta ido cikin ido ya ce" Na zata farin cikin kun hadu da ahalinku ya fi komai a yanzu NAHIDT ?"

Hamza dake rike sa Shuwwar wace ta dora kanta a damtsen hannunsa idannuwanta rufe ruf ya ce" Haba Aban shuwwa, wani irin farin ciki kake so mu tsinci kanmu a ciki? Tabas ni na ji farin cikin gannin kannenaina, aman hakan na nufin ta haramta a gareni? Aure na uku kennan fa zai lalace min kamar masu bakin uwa ? Ita kuwa na biyar fa kennan idan ban mantaa irgen ba fa?"

Malan zai kuma yin magana Ganaral ya ce" Son, dube ni, ka kwontar da hankalinka mana, na san kana kulace da yan uwan mahaifiyarka aman inaga wannan abin farin ciki ne ga kowa koda hakan na nufin an fasa daurin aurenka ai Allah zai baka wata, itama hakuri zata yi haka Allah ya nufa da rayuwarku ku dukanku"

NAHIDT ta karkata kanta ta ce" Ba zaka gane bane Baba, ba zaka gane ba walahi, wayo Allahna Shuwwa tashi mu tafi kin ji? Tashi"

"Ina zaku je? Kuma kun yi mana fushin ne? Kuma ba zaku sauraremu bane? Daga nan babu inda zaku nufa da ya fi garin Tanus" gogonsu ta fada da dan alamu na iya gaskiyarta ta fada kennan hakan ya saka Shuwwar kureta da ido tana kankance idannuwanta dake ruruwa da ruwan balaki tana niyar yin wata maganar dan ba wannan mata amsa daidai da abinda ta aikata mata CHIEF of army ya sake yin magana a Karro na biyu da alamu na yanke hukunci kamar yadda ya saba yana kallon malan da abokinsa da Aban su Hamza ya furta " My freind Bismillah "

Yana gama fada ya yi gaba kadan hakan na nunin yana son yin magana da su a kebance

Watau amintakar dake tsakanin CHIEF OF ARMY da tsohon GANARAL baban Hamza amintaka ce dadadiya mai karko, sun jima tare hakan ya sa du rike sirri irin na soja sun san sirrikan junna, zan iya cewa da ba dan nisa dake tsakaninsu ba da kulun sunna mane da junna ne, aman koda nisan nan bai hanna masu motsi kadan kwalawa junna kira dan su sanar da damuwar junna wa junnansu ba a ko wani irin lokaci, kai kira ko na tsakaninsu da matayensu ne sukan sanarwa junnansu, zan iya cewa CHIEF OF ARMY tunda ya rasa amininsa sai ya samu yake amintakar da tsohon ganaral, duda bambancin shekarun dake tsakaninsu aman kuma sun san junna sunna mutunta junna

A nutse ya furta" A bayane yake maganar ahali ce ta kama, a yanzu inaga magana ce mai karfin gaske ta kama, Kai ka isa da su dukansu , kai ka isa da Hamza, kai kuma Malan ka isa da yan matan gidanka, so barin wannan lamari a haka inaga zai sake traumatiz kwonciyar hankalin yarinyar cen da kuma shi kansa Hamza, déception na soyaya baban abu ne mai ilar gaske da ba kowa ke iya shanyewa ba, nd furucin yayartan cen ya sakani a cikin halin tunani da ta ce kennan dan iyayensu sun rasu shekenan ba zasu auru ba?, What's t wrld ? Whts t prblm da har zasu rinha fuskantar haka? Ban zauna da su ba aman yannayin shigar yayar da ya saka ta ratso gabanmu haka duda a gigice take na fuskanci akoy lamari na rashin jin magana a cikin zamansu, but ba shine dalilin da zai sa a ringa sake turesu ba, ya dace ne a janyo su, a nuna masu soyaya, summa ai y'aya ne kau? , Idan ba damuwa inaga kar ku fasa daura masu aure a yau"

Dukan furucinsa da yake yi sun matukar nutsu sunna kuma fahimta har zuwa furucinsa na karshe wanda ya saka kowanensu ya masa kallo irin nasa na rashin fahimta, harma amininsa ya dan kamo h💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣7️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Dukkan furucinsa, sun nutsu ne, sunna fahimtarsa, kuma har kasan zuciyarsu sun gane , sun kuma gamsu da bayanansa har kawo wajen da ya furta a daura aurensu, hakan ya sa kowa ya dago da kalar nasa fahimtar da ya fara yi masa yana kallonsa da hakan Amininsa ne ya riko hannunsa yana fadin" Father Lieutenant, ka kuwa fahimci rigimar cen da ta kacame? Ana nufin uwar da ta haifi Hamzana ita ta haifi yan matan cen, ta ina kake so a daura aure kuma? "

Dan murmushi ya yi ya juya wajen da Fauziya ke zaune ta rakube ta hade kanta da gwuiwoyinta tana kuka , takan dago ta sauke dubanta a kansu ta kuma maida ta sake fashewa da wani kukan irin na cikin ran nan mai cin rai din nan ya nuna wajen da take ya ce" Kunna nufin harda wancenma mamansu daya ne?"

Su dukansu ita suka kalla, Malan ne ya furta" Aa, ita din aminiyar NAHIDT ce, tare aka kawo su a kame da ake yi"

CHIEF OF ARMY ya ce" Thats good, ka ga ka aurawa d'anka yarinyar cen, ina kyautata zaton zai samu gata in sha Allah"

Sake kallonta sula yi, haka kuma suka kalli wajen da su Hamza suke sunna ta sake rungumar junna da Hamzan yana ta talabar kumatunsu yana mai yi masu furucin su yi hakuri su daina kuka, in sha Allah damuwarsu zata gushe gaba dayansu, dan an daina aurensu a yau ba damuwa, Allah zai basu abokanan rayuwa masu albarka, gashi ya bayana a garesu zai zamto uwa, ya zamto uba a wajensu, zai zamto gatansu, zai tare masu dukan wata rigima ko raini, zai hanna a zage su , zai daki du wanda ya nemi ya dake su, shi murna yake da ya same su , kuma babansama zai rike su kamar shi ya haife su domin dama so yake yi ya samu wasu y'ayan gashi Allah ya karra masa ai, su kyale wa'incen masu bata farin cikin mutane daga su har yar uwar tasu, su yi shiru su daina kuka haka Allah ya hukunta

A sanyaye Malan ya ce" Tabas haka Allah ya hukunta, na jima ina gannin lamarin launin Kadarrar bayi ciki harda tawa ta jarabawar rayuwa Alhmdulilah, aman ta Shuwwar, ta shuwwar tana bani tausayi ainun, ina mai taya shuwwar adu'ar Allah ya sanyaya mata jarabawar rayuwarta ba dare ba rana "

Sake juyawa Chief of army ya yi yana kallonta, mugun tausayinta ne ke tsirga masa har cen kasan zuciyarsa

Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya fara fita ya bar Baban Hamza zuwa ya sanar masu abinda suka yanke

A lokacin da ya fito ya ga dumbin al'umar da suka saka jikinsa daukan yamyamyam Da mamakin tarin mutanen da suka taru yake karra bin mutanen da kallo wa'inda idannuwansa suka kasa gannin karshensu , a cikinsu kuma ya ga manyan malamai, ya ga datijawa, ya ga matasa, uwa uba sojoji babu kalar hular da babu

A hankali ya kai dubansa wajen da ya kula sun fi zagayawa hakan ya tabatar masa cewar a cen yake Murmushi ya yi mai sanyi yana komawa gefe ya ciro wayarsa ya samu ya fita a cikin mutanen daidai mai rike da 🔊🔊🔊 ya fara sanarwar cewa a shirya kowa ya zauna za'a gabatar da daurin aure

LIEUTENANT GANARAL ya dan tabe bakinsa yana mai sake bin mutanen wajen da kallo da bakin gilashinsa a kasan zuciyarsa yana ayana' In ba malan bahaushe ba, a kasar da ake kawo hari yan bani na iya na shiga da boom sunna watsa al'uma, shine akai wannan tarron mai cinkushewar nan aka cinkushe kowa da babar riga, yanzun ka dauki dan dutse ka furta attakhabir ya jefa kusa da liman din cen da babu abinda zai iya aikatawa da ya wuce diban babar rigarsa ya diba da gudu ko ya sume kafin ta tashi da shi din, shirme dai ba zai karewa malan bahaushe ba, daurin auren a yi shi a cikin masalaci mana a watse?'

Zazaunawa aka yi, du aka samu nutsuwa inda suka shiga gabatar da daurin auren da su rabe raben cingam da komai

A bangare guda kuwa CHIEF OF ARMY idannuwansa ke lumshe yana sauraron maganarta a nutse take furta" Har ka sa na ji kunya, wani irin neman yardata? A kan yaron da kaine babansa?, Dan Allah me na yi maka ne da sasafe haka ELHAJ ?"

Murmushi ya sauke hadi da ajiyar zuciya ya datse kiran bayan ya furta mata kalamai masu daraja ya maida dubansa wajen tarron al'umar nan ya daga kafarsa da dan sauri ya dawo jin ana shafa fatiha wanda hakan ke nufin aure ya dauru kowa na iya tashi

Kamar jira yake ana shafawa shi ya fara mikewa, sai dai gannin Father ya nufo da sauri shima ya sha babar riga fara yana masa alamun ya zauna saman kujerar da yarensa suka bashi ya koma ya zauna sannan ya karasa wajen da yake zaune yana kallon fuskarsa a nutse ya ce" MUHYIDEEN, ni kuwa idan na yanke wani hukunci a kanka yanzun zaka iya yi min biyaya kuwa?"

Kai, watau Father dinsa ya cika son saka shi magana ba lokaci walahi, ya fi sau a irga suke irin haka, kuma fa wani yanke hukuncin saima an yanke ake fada masa sai a biyo ta bayan layi da shi, duda ya tsargu kwarai da gaske da tambayar da akai masa a wannan wajen a irin wannan lokacin, aman sai ya dan kafe shi da ido kafin ya dan gyada masa kai yana sake waiwaige ko zai ga abinda Father ke son saka shi

Murmushi ya yi yana fadin" Ka matso kusa da wajen daurin auren nan yi sauri taso ka matso

Da kallo ya raka bayan Father a lokacin da ya ratsa da sauri yana dukawa wajen datijawan nan da abokinsa da malan dake zaune zagaye da goron da aka karkasa ana ta rarabawa Bakinsa ya karra dan dantsewa yana ayana' Allah , Allah ka sa wani tsagera aka sama min da safiyar nan na ci uwashi na hutama zuciyata!', tunanin haka da ya yi saka shi mikewa da kwarin gwuiwarsa da kakinsa ta sojoji a jikinsa ya matsa da kyau ta yadda zai damki mutun (😌)

A nutse bayan Father ya gama gagaisawa da su ya ce" Ku yi hakuri, na shigo kai tsaye, Malan, Aban su Hamza, Aminina idan har ba damuwa ina nemawa yarona auren SHUWWAR"

Daga Malan din, har sauran al'umar kafeshi sukai da ido, bama kamar Ganaral da ya san waye yaron nasa da mugun mamaki baki bude ya ce" Elhaj, kana nufin SIR?"

Kai ya gyada yana dan waigawa ya ga ashe ya dan matso din kuwa, hakan ya sa ya ringa hamdallah a zuciyarsa

Malan ya kai dubansa wajen da Baban Hamza ya nuna yana fadin ga wanda ake nemawa auren Tsakani da Allah sai da gabansa ya fadi gannin soja a zaune, sojanma LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY? Soja wa Shuwwar? Ji ya yi hankalinsa ya fara tashi bale da ya kula gaba daya dan halaci irin nasu shi suka zubawa ido, kuma shi suke jira ya bada amsa Watau shi a rubuce zai bada labarin wacece Shuwwar , domin idan hankalinta ya tashi ko a gabansa hali take rabawa, uwa uba a kan maganar soja?

Yar zufar daje gaban goshinsa ya saka tissu yana sharewa a hankali ya gyada kansa yana mai fitar da iska ya furta" Na bada in sha Allah, Allah ya sa hakan shi ta fi zama alkhairi"

Murmushi Father ya yi ya mike ya juya wajen da MUHYIDEEN yake ya dan rage muryarsa sosai ya ce" Ya dace ka sauka kasa ka ga sirikanka ne fa a saman tabarma kai kuma yaranka sun kawo kujera kuma sun hanna kowa hawa sama sai kai?, Yanzun dai bani sadaki dukan abinda ya samu kasancewar bamu fito da shirin hakan ba"

Da mamaki baki da hanci ya saki yana kallon Father, muryarsa ya dan gyara ya bude bakinsa ya ce" Sadaki?"

Father ya gyada masa kai A hankali ya sake fadin" Aure zaka yi ne Father?"

Sai da CHIEF OF ARMY ya bude ido da baki yana kallonsa kafin ya girgiza kai ya ce" Aa, ba ni bane, dan da na haifa na kuma isa da shine zan daurawa aure, watau kai"

"Ikon Allah" ya fada kasa kasa sosai yana sake maida dubansa wajen mutanen, 'Watau na zo na kama ne za'a kama ni?' ya sake ayannawa Fuskarsa ya harhada yana dan kallon Father ya ce" I'm sorry Dad ni ai ban fito da ko sile ba"

Father ya kalle shi kallo irin na ni zaka fadawa haka? Ya san da ya san baya fitowa aljihunsa ba nauyi , dan a rayuwa shi din tafe yake yana bada sadaka a wajen da ba'a sanshi ba, jakar kudinsa koda yaishe zai fita a hannun daya daga cikin yarensa take, aman ya ce bai fito da ko sile ba kau?

Dan murmushi ya yi yana fadin" Gashi kuma daurin auren ya kama ne walahi, bara to mu gani"

Ba zato ba tsamani ya ga Father ya mike tsayinsa ya fuskanci wajen sojojin nan dake zazaune da wa'inda ke ta yawo sunna ta aikinsu na bada tsaro Abinka da sojoji Father ya bude muryarsa sosai yana ihun" SOLDIERS!"

Duk wani soja dake wajen nan, da wanda ya yo ritaya, da wanda yake bakin aiki da wanda vai saka kaki ba sai da ya ganshi ya mike tsaye jikinsa na tsuma ya ja ya daka kafa daya a kasa ya dora hannunsa a gefen kansa da alamun sarawa cikin kuwa harda MUHYIDEEN, hakan ya sa dukan wani farar hula zuba ido da mamaki da birgewa yanna kallonsu

Muryarsa ya sake budewa da karfinsa ya ce" Dukan mai naira a aljihunsa Koda naira biyar ce kumu harjada solidarity mu hada sadaki za'a daura auren LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY gashi bai fito da ko sisin kwabo ba!"

Idannuwansa da ya zarro zaka ce yadosu ne zai yi kasa

Da mamaki ya ringa kallon yadda nan da nan wajen ya rikice da hade haden kudade na mamaki daga aljihun kowani soja , domin kowa abinda yake aljihunsa ne yake cirowa yana hadawa kafin kace meye wannan an cinbuzo kudi na mamaki a babar riga a kawo gaban CHIEF OF ARMY , sannan sun layu da fuska ta fara'a da farin ciki shinfide a kan fuskokinsu

Readers Also Read