Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 22

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 22

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 22: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 22. A wannan rana da SHUWWAR take amarya a cikin gidan MUHYIDEEN ya…

3,326 words

A wannan rana da SHUWWAR take amarya a cikin gidan MUHYIDEEN ya kasance mata rana ce kamar sauran ranakunta da take shigewa dakinta ta yi barcinta a cikin gidansu da ita da yayunta, domin tunda ta koma cikin dakin da aka sauketa cewar nata ne bata kuma fitowa ba, haka kuma babu bakon da ya zo gareta da sunnan ya leko amarya, uwa uba angon da ta gama gane lamarinsa nada bukatar gyara, Aa bangarensama yana dawowa saman table ya je ya dauki tea dinsa da mai aikinsa ke ajiye masa kowani dare da dan pizza ya haye sama da su ya bude dakinsa ya shige ya rufe ya ci gaba da abubuwan da suka zamto masa jiki kafin ya maida hankali ya ci pizzar nan ya sha lipton dinsa sannan ya haye saman bed dinsa da litafinsa na turanci ya bude ya shiga karatu a nutse ba tare da ya tuna cewar an kawo masa wata halita mai zamansa wace take amsa sunnan amarya wace take da bukatar kulawarsa irin na kowace amarya Daga nan barci ne ya yi awon gaba da shi cen dare sosai har sai da kiraye kirayen sallar asubahi suka tashe shi

A gagauce ya shirya ya yi masalaci, ya samu sallarsa ya dawo ya haye sama a lokacin dukan ma'aikatansa sun fito sun kuma bazu sunna ta aiki ka'in da na'in kowa da irin aikin da yake yi kama daga guare gyare da goge goge, da girkin abin kari, da dai sauransu, sannan a cikinsu babu mace ko daya baki dayansu maza ne kuma suma masu kaki ne kananunsu sosai sune suka samu wannan mukami na kula da bangaren LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY

Kamar yadda ya saba shiryawa dan ya fita da wuri bakin aikinsa hakan ce ta faru da shi a yauma

A nutse ya shirya cikin kakinsa masu ruwan haske domin yau bai saka masu duhun nan sosai ba yana yi yana tunanin yadda zai kare da mutanen da sukai masa a gamo a gamo sukai masa auren dole, sai kadai sai ya saki dan murmushi yana juya kansa a hankali sannan ya dantse lebensa wanda ke nuna alamun abinda ke cikin zuciyarsa sam bai tanadar masu abun alkhairi ba, Allah ne kawai zai raba su da junna

Wayarsa ya dauko yana daura agogo a hannunsa na hagu da hularsa yana kallon saman screen din gannin mahaifiyarsa ke kiransa da sasafe haka bayan shi yake fara kiranta da safe wajen karfe tara haka ya gaisheta sai kuma da dare yakan kireta su dan taba hirar kurumci kafin su yi salama kowa ya kwonta

Turaran da yake yiwa jikinsa wanka ya dane kansa bayan ya bale mabalin ya shiga bin sasan jikinsa da shi yana kallon wayar domin ba zai daga ba so yake ta katse sai ya bi kiran

Abin mamaki tana katsewa wani kiran ya sake shigowa hakan ya saka shi dauko macajin da yake gyaran sajen fuskarsa ya juya wajen madubin dakin yana cazar gashin sajen da ya masa lufluf a fuskarsa ya gama ya ajiye sannan ya dauka ya katse kiran da kansa ya maida mata wani

Tana dagawa a dan gagauce ta ce" Barka da safiya MUHAY, yaya ka tashi? Ina amarya? Yaya aka yi baka kireni jiya ka bani ita mun gaisa ba? Sannan me yasa baka yiwa matarka ta nan bayanin ka karra aure ba sannan ka yi mata rarashi irrin wanda ake yiwa kowace mace mai daraja Idan an mata kishiya? Hakama dazun mamanka ke ce min ita rabonta da kai a kadan an yi shekara biyu ko a waya ta kireka bakaa dagawa, wai MUHAY ba zaka iya fitowa a mutun ka fadn me yar uwata da ta fi kusanci da ni fiye da kowata halita a duniya, abokiyar tagwaitaka ta yi maka da raini mai tsanani ya shiga tsakaninku haka? Itama ta yi mamakin aurenka ta kuma ce a ce maka ka kawo mata matar itama ta gaisheta tunda uwa take a wajenka, kana jina kuwa???????" Ta fada tama dan sauke numfashi domin tunda ta farra maganar ko sau daya bata ajiye maganar ba sai da ta kai karshen nan kuma take tambayarsa idan har yana jinta kuwa?

Ajiyar zuciya ya sauke kadan ya ce" Um "

Wayar ta kalla ta sake maidawa a kunnenta tana kallon matarsa dake zaune kanta a kasa ta ci kuka har ta gode Allah fuskarta ta yi mata jajajir idannuwanta du sun jeme kuka ne take na jin wai MUHAY ne ya karra aure bayan ko ita da take matarsa uwar gida bata saj menene auren da shi ba yanzun har a ce ya sake wani auren?

Idannuwanta ta kankance zata yi magana YARINYAR wajen CHIEF OF ARMY ta shiga da gudunta ta zube a gabanta jikinta na rawa hakama idannuwanta na cicikowa da kwallah ta ce" Mama, wai da gaske yayanmu ya yi wani auren a garin da ya tafi aiki? Mama sai ya cike matansa ba tare da ya aureni ba? Mama sonsa nake yi tsakanina da Allah me yasa gani a cikin gida sai dai ya ringa auren wasuna? Da me suka fini ne? Mama ya auri wata mace a garin da kowa ya san sun yi fitt a bin malamai? Ka bari danka ko mijinka ya dauki mace a garin sai dai ka yi hakuri da shi ka barawa duniya shi shine Papa ya yiwa yayanmu aure a cen? Mama ai mu da mu kuma ganninsa sai dai idan Allah ya yi, aman walahi mun shiga uku wayo Allahna"

Matarsa dake kallonta da mamaki ta ce" Ke dama ki ce mijina kike so a nan ? Mijina?"

Idannuwansa ya karra rintsewa a hankali ya ce" Mamanah?, Zan yi kiranki idan na isa office please hayaniyar ta min karfi da yawa"

Mama kanta da ta yi mutuwar zaune tana kallon yan matan da suka mike kowace ke fadawa yar uwarta ba siga tamkar zasu tashi sama sai ta samu kanta da gyada kai ba tare da ta iya amsa shi ba ta katse da sauri tana mikewa tsaye

A hankali ya soke wayar a cikin baban aljihun wandonsa na kusan gwuiwarsa ya rufe ya karasa ya ja abin kusan bed dinsa ya dauko bindigarsa yar karama yana ta hade naman gaban goshinsa domin har ga Allah ihun da sukai masa ya saka masa ciwon goshi, Matsanancin mamakin yaran yake ji a ransa, ya kuma yiwa kansa tanadin shiga garin ko dan ya hada kawunansu ya gwara ta yadda zai hadasa masu kumburin gabam goshi mai tarra ruwan nan da baya warkewa kwana kusa, ta haka zasu dan bambamce shi ba sa'an yinsu bane, itama da ya auran ne take tunanin ta isa wajen da zata saka a kireshi a masa fada kau? Shi kam da ta ga makoncinsa da yaya zai yi da yarinyar nan da raininta? Wai dan ya yi aure ya kireta ya bata hakuri! Hmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmm

Sai da ya gama dubawa ya dura bulet ya dage wajen dannawar ta yadda ba zata harba da kanta ba sannan ya soketa a bayan wandonsa ya ja rigarsa ya rufe

Wani turaran ya karra fesawa ya ajiye ya dauki wayarsa ta cikin dakin dake kafe a jikin bango ya danna kira wajen ma'aikatansa dake kula da gidansa

Ana dagawa bai tsaya ya ji komai ba a takaice ya ce" ka cenza komai na dakin nan, yau 3 days sun isheni!"

Daga haka ya katse ya soke sannan ya juya a nutse ya fice a dakin

Tunda ya farra saukowa yake dan sake baza jinsa dan sake tabatarwa kansa cewa kunnensa hayaniyar muryar mace yake ji ba na namiji ba har kamar taku ake ana kai kawo haka sannan a dawo a ci gaba da magana

Tashin hankali, ko yace abin mamakin da ya gani ne ya saka shi farra tunnanin anya safiyar nan tashi ta yau ba da boom zai farra haduwa ba kuwa? To taratsu na raini da gigin wulanci ke ta kawo masa farmaki ba ji ba gani tamkar ana neman ransa da ihu

A gabansu ta sake tsayawa da doguwar rigarta ta kanti mai lafewa a jiki mai shegen kyau domin baka ce mai ratsin blu wanda ya ciza sosai an yi shar shar da shi har kasa, sannan rigar tun daga sama har kasa ta bi jikinta ta yadda ta matukar bayanar da wace flower mai shegen kyau da kira mai fuzgarwa da Allah ya wadatata da su

Hannayenta ta tafa ta sake nuna su tana fadin" Karti? Dankara dankaran karti goma sha bakwai a cikin gidana? A cikin falona wasu na shara wasu na guga? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une to ku yan daudu ne ko me? Wannan ai wulakanci ne da wulakanta darajar mata!, To bari ku ji daga yau sai yau kar na kuma ganninku a wannan sashen, na maku iyaka dan a gaskiya sanadiyar kunna yawo a bakbalin falona ba zai hannani saukowa da gefto idan halin hakan ta kama ba, ko shi uban gidan naku ba tsoronsa nake ji ba ba kuma na tunanin zan ji tsoronsa a gidan duniya, ina fata kun fahimci bayanina?"

Da yawansu sun dan dago da mamakin furucinta a kan ogansu ne idannuwansu suka sauka a kansa ya jinginar da bayansa ya harde hannayensa duka biyu yana kallon ikon Allah gannin idannuwansa ba a TV ba, ba a kannin labaru ba, gashi dai ra'ayne da ayne hakan ke faruwa, yarinyar nan dan neman fitina bata tunanin a cinye sai su cinyeta rumus su nemi abinci dan bata ishesu ba ne ta tsaya a gaban sojoji take yanka masu kashedi haka?

Su kuma lokaci daya du suka sarra sunna kamewa hadi da sake sada idannuwansu a kanta domin basa so sanadiyar kureta da ido su jazawa kansu balaki

Mamaki ne ya kumeta gannin sai wani sara mata suke dan tsohon munafurci bayan sun gama kiranta da Madame da gaisheta kai a kasa kamar ita din sarakuwarsu ce, a kule ta ce" Kai kai wai ku ba zaku yi hankali ku san ciwon kanku ba? Kun ga ku ajiye hannayenku kamar kunna shirin tayar da kabara ku fice min a falona, na dai gama magana bana son ganninku a cikin gidana kawai, ina dalili da kun san cewa ina fama da allergic du idan na ga kakin jikinku da kun taimakeni kun nisantar da ni da kallon kayan jikinku walahi!"

Idannuwansa ya lumshe yana girgiza kansa a hankali ya idasa saukowa yana yin dan gyaran murya hadi da yi masu alamun sunna iya sauke hannayensu sannan ya zo ya ratsa ya gitata ya nufi hanyar ficewa yana kallon wanda ya haye sama da sauri dan dauko jakarsa ta office

Taku daya biyu ta yi tana kallon yadda du sukka juya da niyar ci gaba da aikin da suke yi tana kunce ribom din da ta kame kanta a tsakiyar kan nata tana kallonsa ta ce" Ehem malan ina magana"

Dan turus ya yi domin ko shi kurma ne ya fahimci da shi take dan ga madubin dake haskata ta bayansa

Juyowa ya yi yana kallonta hakan ya sa idannuwansa sauka a kan lumbukeken Gashin kanta mai duhu da yawa sosai yana walwalin gyaran da ya ringa samu na mamaki

Hannayenta ta harde ta dan zazarro idannuwanta tana kallon gefe hakan ya sa manyan idannuwanta masu dauke da kwali yi masa wal wal sannan jajayen lebunnanta suka hade waje guda suka kuma bude ta ce" ina magana ne a kan gardaye da aka zuba kin a cikin gidana a falona, shine na ce a dakatar da su sannan a zuba min mata masu yawon gaske dan gaskiya ni musulma ce ba zan ci tuwon dan daudu ba"

Gaba daya ji yayi yana ta amsar tayin balakin da take yi masa a tsaye a gabansa

Ya sani ne idan cewa ya yi zai dunkuleta waje daya tsaf zai aikata hakan ba tare da ya wahala ba ya yi wurjin ball da ita ta yadda zata je nesa sosai ta bace batt da gannin masu hangenta Sai dai ya samu kansa da sake kallonta yana tunanin to wannan ai idan ua yi mata haka zai raunanata ta yadda ba zata kuma anfanuwa ba, bayan wannan aiki ne na mahaukaci ke dawainiya da ita, idan ya taba lafiyarta gaskiya ya taka dokarsa da kansa

Kai ya girgiza ya juya ya saka kafarsa daya da niyar ficewa a falon, sai dai wani uban ihu da SHUWWA ta saka a lokacin da ta fahimci a gaban yarensa ne fa yake shirin nunawa cewar ita din ba komai kowa bace sannan bata isa ta saka ko ta hanna ba, uwa uba ya tafi ya barta da su bayan ta gama kiransu da yan daudu su rufe gidan nan su yi dakan sakwara da ita kowama ya huta?

Wani tartsatsin ihun ta sake sakawa lokaci daya ta tatara doguwar rigarta ta haudata saman cinyarta ta wara kafafuwanta ta yadda rigar zata tsaya a nan sannan ta sake barbaza gashin kanta ta kwala wani ihun da ya saka shi sakin kofar ya juyo da dubansa da mugun mamakin hali irin na giya kamar yadda ya gama yin waje ya ajiyeta ya sauke dubansa a kanta a daidai lokacin da ta daka tsale ta rufta ta baya tana ala ala kar ta fada saman abinda zai cutar da ita ta zube a kasa kafin ta aniya gangarawa tamkar an ajiye taya ana garata tana nufar du inda ta ji jikinta zai iya wucewa hakan ya sa da sauri suke matsawa da zarar ta yo wajensu sunna bata fili da sarari dan gannin ikon Allahn da ya fi karfinsu, haka shima idannuwansa sai suka zama tamkar ana yawo da ball a duk inda ta yk uwa uba rigarta kara yin sama take yi daf take da karasawa ta bude cinyoyinta harma ta idasa da wajen pant dinta, wanda Hakan ya matukar dimauta bacin ransa da gannin tsantsar tsagwaron raini na aljannun yarinyar nan da suka rasa wajen faduwa sai a cikin yarensa suke neman yiwa matar da take amsa sunnan tasa zirrr a gaban yarensa? A matsayinsa na musulmin da ya san cewar namijin da baya kishin iyalinsa ba zai taba shiga aljanna bane take neman karya masa karra a ido? Rai bace ya dakatar da sergent da ya nemi da su kamata su kaita sama yana kallonsu ya shiga takowa ciki a zazafe yana fadin"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣3️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Rai bace ya dakatar da shi ta hanyar daka masa tsawa a lokacin da ya yi niyar dukawa dan fara talafawa matar ogansu dake iskokai

Da idannuwansa da suka fara rikidewa ya masu nuni alamun su fice a falon gaba dayansu

Ai kam zo ka ga sauri da gudu gudu wajen fita a falon

Bai yi wata wata ba ya rage tsayinsa ya sungumeta a hannunsa ya shiga haurawa sama da ita ba tare da ya tsaya ya gane alamun ta fa rike shi daf dan kar ta fado haka kuma idannuwanta sai rawa suke tamkar an jijiga bera a cikin kwano tsabar tsoro da ya kamata na daukotan da ya yi kar dai dukanta zai yi ne

Walahi tsananin firgicewa da bacin rai da ya yi kwata kwata sai ya rasa wane nasa dakin bale nata, watau MUHYIDEEN ya kasance baya daukan abin bacin rai da sauki a rayuwarsa ta duniya, hakan ya sa ya murda kofar dakinsa wanda ko AC din bai kashe ba bale ace ya kwakwashe wasu kayan da ya anfana da su ciki harda gajeran wandonsa da ya cire ya karasa ya jefata saman bed dinsa sannan ya dafe gaban goshinsa ya shiga kai kawo a lokaci daya ita kuma ta mike zaune tana jan rigarta kasa tana wiki wikitu da idannuwanta tamkar tana shirin yin gudun ceton rai

Babu irin abinda bai saka a cen cen kasan zuciyarsa ba, ciki harda su tunanin yanzu da Abansa bai masa wannan saka mutun a ukun ba da yau sai ya fasawa wannan abar jiki sannan ya rabu da alkakai ya huta , aman tsabar saka bawa a uku da DAD ya koya shine ya yi abu a cikin dubu bai san yarinyar nan harda iskokai take yi ba du ya kwasa masa, kai lalle dama idan kai ka kasance baka da aiki sai aure aure babu abinda ba zaka gani ba a rayuwa

Juyowa ya yi ya sauke idannuwansa a kan fuskarta ya ga yadda take gumi duda uban ACn dake dakin gashi ta zauna ko yace ta yi irin wannan zaman na kai ba a zaune ba kai ba a tsugune ba tana ta binsa da kallo dukan motsinsa

Takamin dake kafarsa ya sabule kasancewar bai idasa daura takalmin ba ya dora kafarsa daya a bakin bed din sannan ya tokare gwuiwar hannunsa da jikin gwuiwar kafar tasa ta yadda ya dan rankwafa a kausashe yana kallonta ya ce" Bari ki ji, bana so ana saka ni yawon magana, ba'a yi min ihu ba'ai min tartsatsi a cikin gidana bale da sasafe irin haka!"

Ya kauda kansa da takaici ya sake maidowa kanta yana gannin asarar kalamansa ne zata saka shi da safiyar Allah ya dora da fadin" Wa sunnanki?"

Shuwwar ta kale shi da kallo na mamaki da daukaka raininsa a zuciyarta, sai dai a gaskiya bata jin a haka din nan da suka matsewa junna waje in zata nemi kawo masa raini hakan ya sa ciki ciki ta furta " SHUWWAR "

Kansa ya dan girgiza a bayane ya ce" Meye fasarar sunna wai SHUWWAR?"

SHUWWAR da mamaki ta sake kallonsa a kasan zuciyarta ta shiga ayana' ka ga kin Allah karara, kai ba'a yi tambayar fasarar naka sunnan da mutun bama zai iya rikewa ba kaine kake tambayar nawa? To bari ka samu amsa daidai da tambayarka!'

Baki ta dan turo a kasan makoshinta ta ce" Ana nufin yar aljannah"

'Balaki, yanzu yarinyar nan a dakikin karshen zamani ta daukeni da har zata bani fasarar Shuwwa da Aljannah?, Lalle inaga an gamo ni da dangin kunnar bakin wake masu taurin kai, ama ko meye a cikin kan nan naki sai na kwankwale maki shi tassss ta yadda ba zaki kuma fahimtar komai na rayuwarki da sauki ba!'

"Ba'a bin uban gida kuma a bi yaron gida koda uban gidan bai ga wajen kai hancinsa a nan ba bale baya tunanin a gidan duniya zai yi faduwar tasar da zai yi tsalake tsalake ya diro nan , domin ko sarki ne idan fasararsa bariki bashi da cenjin sunna a kudin litafina !, ina fata aljannun kanki sun iya bambance bariki da gidan BARIKI!". MUHAY ya fada a kausashe sannan yana fadan ne kasa kasa sosai cikin furucinsa aman hakan bai hanna mata jin komai radau ba domin ai muryar MUHYIDEEN ba ta yin sirri bace ko kadan

Readers Also Read