Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 23

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 23

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 23: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 23. Ita dai dukan amsoshin da take da dan bashi bata budi bakinta ta…

3,375 words

Ita dai dukan amsoshin da take da dan bashi bata budi bakinta ta furta koda A ba, dan ta kula shi allurar da akai masa ta sojoji irin ta mahaukatan sojoji ce, kar ta je ta jazawa kanta fitinar da ba zata iya fitar da kanta ba, a banza a wofi ya ilata mata rayuwa ya barta da ha'ula'i ta jewa nex mijinta a gurgunce ko fuska a cacabe da tabon auren soja auren shan duka

Kafarsa ya sauke ya saka takalminsa ya juya Har ya kusan ficewa kwata kwata sai ya dakata ya juyo yana kallonta sannan ya bi dakin da kallo ya ce" Kin siyawa kanki, kin dakatar min da wa'inda ke min aiki yanzun ke zaki dauke shi a hannayenki, kar ki saki wata mace ta shigo min dakina ke zaki gyara shi ki cenzan komai, nd idanma su suka yi girkina du ke ta gano abinda bana so a kuskure shine dahuwar lipton dina, akoy yadda ake yi a kafe a kicin din kasa.........idan aka min ganganci komai na iya faruwa!"

Daga haka ya fice ransa na kunna sai cije lebe yake yi yana tunanin yanzun wannan ifirituwar yarinyar a kwananta daya tak a cikin gidansa ne zata cenza masa tsarin ma'aikatansa da sai da ya dauki lokaci yana tantance su kafin ya iya tsayar da masu yi masa aikin dahuwar abincinsa duba da irin abubuwan da ake tsatsakura masa a abincinsa ko na shansa shine ita zata jaza masa soson tsiyar dakatar da su rana tsaka? Yana karra masa wani aiki a kan wanda yake da na bincikar abincinsa du idan zai ci? Nonsenss! Nonsense kawai

Yana fitowa ya tarda su a cen filinsu na sojoji da ake haduwar safe a dora tutar kasar

Bai basu explication din komai ba ya saka a kawo masa matan sojojin da zasu maye gurbin mazan

Zo ka ga yadda wajen ya kaure da ihun yan matan da suka jima sunna jiran irin occasion din nan, ai da farko matan aka kai masa, sai ya ringa gannin abubuwa gannin idannuwansa na irin tsarin shigar da suke yi da sunnan sun zo yi masa aiki, du a tunaninsu yana daya daga cikin manyansu da basa barin ramin cikin sket ya wuce ta gabansu ba tare da sun amsa tayinsa ba ko na wace irin kucakar mace ce kuwa Gannin iya shegensu na neman taba girmansa nasa na shi kansa sai ya dakatar da su a kwana kusa da fara yi masa aiki ya saka aka kawo maza, wannan abin ya masu ciwo sosai domin mazan nan haka suka ringa binsu da neman magana da dariya , kai takamama da suke yi masu abin ba'a cewa komai, haka sunna ji sunna gani sai maza ne ke aikin cikin gidan LIEUTENANT GANARAL, sai gashi yau ta fadi gasasa, hakan ya sa dukan wata wace ta kware a fannin girki ne, hada kayan marmari namu na hausa da na waje ne, iya kwarewa a tsafta da rashin gajiya da aiki, ta garzayo da takardar shedar haka da ta samu ta kaiwa baban dake zaba hakan, shima a gagauce ya amsa ya karra nazari a kan sannin da ya yi kafin ya zazabi wa'inda ya dace ya saka su garzaya Wajen amsar kayan girki na cikin barikin sojojin maza su dawo su shige ya kaisu da kansa ya nunawa madam su sannan ya rabawa kowa aikinsa

Tabas Madame din oga da ta kwana jiya ta waye a cikin BARIKIN su ta kafa masu baban tarihi da shayinta a cikin zukkatansu, sun kamu da mamakin ashe akoy wanda zai iya cenza ra'ayin ogansu kai tsaye haka? Sun dauki hannu sun kuma gane cewar ta yiwu wannan din ba auren hadi bane kamar yadda gaba daya aka dauka ake fadi cewar CHIEF OF ARMY ya yiwa oga auren dole, ta yiwu surprise dinsu akai aman ba auren hadi bane auren soyaya ne!

Dakin take bi da kallo a hankali bayan fitarsa na tsayin lokaci Zata iya cewa rabonta da ta ji nutsuwa a cikin waje irin wadda take ji a Yanzu a cikin dakin nan tun a lokacin da mahaifiyarta ke kwonciya a gefenta ta sakata a cikin jikinta a cikin dakinsu na saudiya

A hankali ta ringa sauke ajiyar zuciya tana sake shakar kanshin turaran ruwan da dakin ya dauka mai nutsatsen kanshi sannan ta ci gaba da sake bin dakin da kallo tana ta aikin lumshe idannuwanta da daukan yannayin wajen wa fatar dake jikinta har ta sadu da gaban madubin dakin ta ja ta tsaya tana kallon kanta tun daga sama har kasa ba tare da ta san me take son ganni a jikin nata ba

A hankali ta sauke dubanta a saman kugunta sannan ta sauke a saman fuskarta

Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi tana kallon kanta a hankali ta furta" Me yasa kowa ke yanke mana hukunci daga ya ganmu ne? Shin kamanin halitarmu keda bamban da ta sauran al'uma ko kuma dabi'unmu ne ba irin nasu ba?"

Dan jan numfashi ta yi jin abin na neman sakata a wani haki na mutuwar zuciya, hakan ya sa ta tatara gashin kanta ta hade a cen tsakiya da dan siririn ribom din da ta cire na sama ta maida shi a tsakiyar ta kame kan nata tana juyowa ta fuskanci dakin

Bakinta ta yatsina ta mayar da muryarta kamar ta karti a tunaninta ta wani kausasa fuska ta ce" Kuma ki gyaran dakin nan ki cenzan komai dake cikinsa!, To malan ina koman da zan cenza din ne? Ni dai ai bakuwa ce kuma ban ga waajen da aka rubuta abubuwan cenza maka ba a nan, sannan me bedsheet din nan suka yi in ba almubaranci irin na mai kudi ba? Ina kayan share share da gugar dakin? Ni banma ga datin da dakin nan ya yi ba sai iya yi kamar na matsiyacin miji!, In dan a tunaninka aiki zai dakatar da ni SHUWWA girman saudiya ka fado babu nauyi domin babu abinda zai dakatar da ni wa aikata aikin nan a dan kankannin lokaci sannan na sauka na karanta wajen dora girkin na gani idan wasu sababin launin girki da hada tea ne za'a koyawa wace ta yiwa larabawa aikatau fine ai shi ilimi fadi gare shi mu kuma muna so!"

Zannin gadon ta fara yayewa bayan ta dauke gajeran wandon dake ajiye a saman gadon tana zarro ido ta yi sauri nufar bayi ta ajiyr ta fito tana tunanin yaya zata yi da gajerun wandunnan da ta gani uku cif a ajiye a wajen snk ne?

Tana zuwa ta idasa yayewa ta nufi bayi dan ta ga ko akoy injin wanki? Ai kam akoy shi, kuma tsaf ta iya anfani da shi, hakan ya sa ta bude ta saka zannuwan gadon ta zuba omo ta daidaita komai ta rufe ta koma tana tunanin wajen kayan aikin aka yi kiran wayar dake makale a dakin nasa

Da neman fitina ta karasa ta daga dan ta amsawa koma waye, sai ta ji cewar an kawo mata masu aiki ne ta fito ta gansu, hakan ya sa ta yi dan murmushi ta ajiye sannan ta je wajen kayansa ta bude ta tsaya tana bin kayan da kallo

A nutse ta janyo rigarsa irin na gudu masu babar riga da dogon wandon nan ta saka a saman rigar dake jikinta hakan ya sa rigar ta kusan zuwan mata gwuiwarta, sannan ta dauki hularsa ta kakin sojoji hankali kwonce ta dora a saman gashin kanta ta rufe tana fadin" yanzun wadinnan iya kayan gudu ne da na kakin soja? Gaba daya mutane ba tsoron Allah a lamuransu kwata kwata!"

Tunda take saukowa kowace mace da aka zo da ita ta dago daga tsaotsayen da suke ta zuba mata ido, Wace dai ta shigo a matsayin matar jarumin nan ce a gabansu

Watau kyanta da kyan fatarta a bayane ba a boye ba abin mangari ne a garesu, sai dai sun yi mamakin kankantar jijinta domin rigar nan boye du wani abu mai motsi na jikinta ta yi sosai da sosai

Bata tashi basu mamaki ba, a lokacin da suke jira yar innocent murya ta gaishe su, ta yadda zasu fara dora mata nasu kalar ikon ta yadda zasu yi kata wayau da takamar mijinta ne su nuna mata sun fita iya karbar miji, sai suka ji dakakiyar murya tana kallon Chief dinsu a nutse cikin fitar da wararun harufa da yaren turanci bugage na Habuja😌 ta ce" To aman wadinnan wasu zan dauka a cikinsu a cenzo min wasu ko?, Kama yi hakuri ni gani nake mace daidaidai har goma sha uku sun yi yawa a aikin gidan nan gaskiya Sir, ka ga ka ware min mace takwas, suma su raba aikin ta yadda zasu anfana da lokutansu, idan hudu sukai duty yau, gobe sai hudu su yi, sannan duka a nan uku kadai suka kwonta min ka ga ba saman dakunan gidana zasu ringa hawa ba, iyakarsu gyaran falon nan shima ya min girma sosai ne, sai gugar diner, mutun uku sun isa su raba aikin nan su wuni sunna yi, daya kuma sai tana rakani kicin dan ta ringa mimiko min abubuwan bukata irin su turmi, tabarya, dan jajagen tarugu da barar tafarnuwa, da yankan albasa .....wannan shine kawai bukatata, gashi sauran nan basu da dabi'a ta suturta jikinsu, ka ga wancen wandonta kamar ya tsage a jikinta, wannan kuma rigarta daga sama botira a bale, ka ga wancen ita kanta ko hula babu tsakani da Allah mu da muka zo aiki ai za'ana sakani yawan magana ne, ka fa san yan mata da gwali kar a je a zo a ringa shara ana tsoron kurar falona ta taba kafar yan gayu!"

Lahaula wala kuwata ila bilahi aliyul azim, watau da ake cewa kar ka yankewa mutun hukunci daga yannayin halitarsa haka ne Wannan yarinya a yan sekwani tana neman kafa tarihin da sauran matan cikin barikin basu kafa ba Domin a bayane , karara take kiran gidan ogansu da gidanta kanta tsaye, kuma a furucinta dukan wata mai rawa da kai sai ta sha jinnin jikinta harma ta yi data sannin zuwa ba da hijab ba dan kuwa basu san cewa matar ogansu koda yarinya ce to fa ta san ciwon kanta ga dukan alamu, idan kuma takamarsu bariki alamu sun nuna a bayane cewar kamar ta ce kau ku bani waje ne!

Shi da kansa sai ya ringa jin kwarin gwuiwa da jin shayinta sosai , duda dama shi din ba mai katsala bane, ya kasance mai kiyaye dokokin iyayen gidansa ko ta halin kaka, shi fa Tunda ta sauko da hular oga a kanta ya ji yana tsoron dagowa idan tana magana, watau matan BARIKIN sojoji sunna cewa a sama masu Mama ko? Sun samu, ga yarinya Uwar manya ta bayana sai fatan mai tafia da ita ya shirya

Dukkan masu gwalin nan masu cike da burin nan aka tarkata aka koma da su aka bara mata ukun da suka rage wa'inda suka kasance shiru shiru da daukan aikinsu da mahinmanci, ya koma da zulumin samo masu dama dama domin a gaskiya da wahala ace ana son masu nutsuwa da yawa a cikinsu, sai hamdallah kawai Ita kuma ukun nan da suka rage su suka fada mata wajen ajiyar kayan aiki, da komai da komai, hakan ya sa ta raba masu aikin gyaran kasan ta haye sama ta zagine ta shiga aiki ba ji ba gani cikin sabo da kuma kaunar aikatuwa ba da gajiya ba. (anfanin ka horar da yaronka da yin aikace aikace a cikin gidajenku kennan, ki barshi ya ringa yin wankinsa da kansa, ki koya mata ko mashi juriya a wajen yin aiki, koda le na kayan aiki irin na zamani su injin daka tafarnuwa, injin yanka albasa, injin meye da meye, wannan taki kalar rayuwar kennan, ki yi hakuri ki jure ki koyawa yarinyarki aiki da su a gargajiyance, domin baki san ina zaki mikata ba, wani gidan mai kudin ginnin ne hajiyata, ba lale bane ta samu sukunin da kika samu na rayuwa ba, idan ba'a iya ba sai ki ga ana samun gagarumar matsala ya ke yar uwata.....)

A gidan CHIEF of army

su dukansu a zaune suke a falonsa kama daga manyan iyayen yaren har zuwa maman MUHYIDEEN da matarsa, kowace ta cika ta batse sunna jira ya ajiye jaridar da ya dauka bayan ya tara su a gabansa ya zartar da hukuncin da ya dace wa laifinsu baki dayansu

Wata ajiyar zuciyar Hajia Hasana ta sake saukewa cike da bacin rai, da tashin hankalin abinda ya faru da yan matan a yau sanadiyar soyayar da suke ikirarin sunaiwa yaronta...............

☹️☹️☹️☹️☹️to cmmnt din f💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣4️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Wata ajiyar zuciyar Hajia Hasana ta sake saukewa cike da bacin rai, da tashin hankalin abinda ya faru da yan matan nan a yau sanadiyar soyayar da suke ikirarin sunaiwa yaronta

Wace irin soyaya ce wannan da babu tarbiya a cikinta? Ita Uma yar gidan uwar gidan CHIEF of army a bayane suke nuna dan tana auren baban yarinyar dole ne ta saka yaronta ya auri yarinyar, harma suke nuna ai ya zama wajibi tunda ubanta ake aure a faranta mata rai , ba maganar tausasawa a tsakaninta da uwar y'ar bale Y'ar da ta samu tarbiyar uwarta sai ya zamto itama tunaninta ya sauka ne a kan cewa dole ne a yi mata ko dan isarta , sun manta uwaa take a wajen Uma koda babu aure tsakaninta da ubanta, uwa uba ita wani irin abu ne zai debeta tana ji tana ganni ta hada zuria da maman Uma? Uwar kanta bata da wadataciyar tarbiyar da za'ai mangarin samu bake gar y'ar ta koyar ta bayar da exemple Sai kanwarta da take Cikin gorin yayar tata ba dare ba rana na ai ita mahaifiyarta ba yar kowa bace ba kuma ta da komai, tausaya mata babansu ya yi ya aurota shine har zata samu wajen da zata nemi yin soyaya da abinda ita take so?, Lalle ta taro mach, kuma sai ta bambance mata aya da tsakuwa, ita kakin kanta mahaifiyar MUHYIDEEN kofa zata iya amincewa da auren hadi na familly to fa sai dai a hada da yarinyar nan ita karamar, domin ita din akoy ladabi da biyaya, tana da mutunci sosai, batama san a kan me zata nace da son MUHYIDEEN ba bayan ta san wahala ce zata sha, ga masoyinta Aliyu dake da nasa mukamin da nasa kyan da nasa koman, aman sai tana ture shi karara tana nuna ita ga wanda take so?, Matsalar daya ce ita dai ta fada ta kuma rantse cewar babu ita babu auren hadi gaskiya! Bata ciki, bale da hakaya irin na yaronta? Idan ta yarda aka hada maimakun a samu farin cikin hakan ta tabata sai dai a hadu da vacin rai mai tsananin gaske

Sai da ya dasa aya a karatun jaridar da yake yi na labarin fitar MUHYIDEEN ne da sojojin mabambanta gari sukai wani meeting a kan karra wanzar da zaman lafiya a cikin kasar inda suka bayar da bayani a dunkule, jaridar ta masa dadi dan a cikin maganar da aka rubuta MUHYIDEEN ya yi bayan takaitacen labarinsa ya gane sakon dake boye a cikin nanadadaden harshen da ya yi anfani da shi dan usar da sako ga dukan wani mai hankali da lura cewar a tare da dan kasa akan yaki kasa, watau ba zai yiwu ace bakon da bai san kan gari ba ya iya shiga ya yaki gari, mutanen da ake cudanya da su a cikin gari ake kwana ake tashi da su sune ke siyar da rayukan yan uwansu a kan yan kudade da alkawarin ba za'a taba nasu rayuwar ba, su bayar da information din da za'a kare da yan uwansu yan garinsu, a nasu rashin wayon su sun tsira ne?, A nasu tunanin su sun ketare ne? Basa aunawa su ga shi makashin waye a gefensa nasa rayaye? Ai yaki kan ci gida ne wannan shaka babu

Dan Murmushi ya yi a bayane kasa kasa ya furta" Ni na san cewa kai din magajina na, sannan farkuwar kasata ne in sha Allah"

Dubansa ya dago kan matansa da y'ayansa dake jiran hukuncinsa

Walahi, marin da Uma ta wankawa matar MUHYIDEEN Ya bashi mamakin da madaukakin Tsoron rashin kunyar yayan nasa

A dan dake ya ce" Uma zo nan "

Uma ta mike daga kusa da mahaifiyarta dake ta rarashinta kan kukan da take shekawa ta nufi mahaifinta da dan kwarin gwuiwarta duba da kanwarta ta mata rashin kunya ta shiga bayan matar yayansu dan wani shishigi da nemn raini

Tana zuwa ta duka a gabansa ta budi baki ta ce" Ab......." Zata karasa da fadin abanmu gani ta samu hakoranta da dantse harshenta hakan ya sa ta zunduma wani gigitacen ihu tana komawa ta ririke kumatunta domin a yadda mahaifinta ya zaburo ya mata nuni da wani marin ne zai wanka mata hakan ya sa a haukace ta duke tana rike da kumatunta wanda ya saka mahaifiyarta mikewa gar kamar zata kifa ga jikin manyanta ga sakawa rai fitina ita an daki y'arta a dole zata fuskanci ubaan y'ar wanda hakan ya saka babar yarsu gaba daya da mamaki ta bi maman tasu da kallo ta maida kanta tana sokewa tana tunanin lalle ammansu na sin balowa kanta dan jijibin yaki da mahaifinsu a irin wannan lokacin

A kausashe ya nunata da yatsa yana fadin" Idan kika karaso wajen nan, ko kika yi gigin furta min kalma daya a zaman da zamu yi ta rashin da'a a wajen nan har muka tashi a bakin igiyoyin aurenki dake kaina gaba daya, daga ke har sauran dake tunanin sun haihu ne sun isa da y'ayan da suka haifa harma suke gannin kanmu ya zo daya da ni da su da yayansu a cikin gidana, ke na karre maki harma kike tunanin dadewa da aurena da ke ne zai baki damar wulakantani da wulakantar min da tarbiyar yayana to bismillah ki kwatanta ki ga ikon Allah Mariya!"

A tsorace duka matan suka zuba masa ido hakama babar yarsa a tsorace ta saje dagowa da carbinta da take ja ta sauke dubanta a kan mahaifiyarta da mahaifinta sannan ta sauke kakausan kallo a kan kannen nata ta sake maida kanta ta soke kasaa domin bakinta ba zai furta komai lokacin da mahaifinta yake fada ba

Rai bace ya ce" Fuskar matarsa ?, A me kika dauki kanki? Wacece ke? Ke din banza ke din wofim da ba dan kunya da kawaici kina tunanin zaki ringa zuba rashin kunya yana daga maki kafa ne a banza a wofi? Ke kin san wanene shi? Dan kina ganninsa yana dukawa yana gaishe ni shine aka ce maki shi din zai zamto abin raininki? Uma salwah bari ki ji ki fitar da miji a cikin watan nan na daura maki aure da ke da yar uwarki idan ba haka ba ni zan sama maku mazajen auren na daura maku su!, Idan da wanda yake da ja kuma bismillah!"

Readers Also Read