Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 24

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 24

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 24: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 24. Shiru dakin ya sake dauka ba mai kwakwaran motsi ciki harda Hajia…

3,371 words

Shiru dakin ya sake dauka ba mai kwakwaran motsi ciki harda Hajia Hasana, kanta a kasa yake itama zuciyarta na dokawa da karfin gaske

Wani tsakin ya ja yana mikewa da fadin" Ina da meeting, zan waiwayeku gaba dayanku!"

Daga haka ya juya ya fice hakan ya sa matan nasa raka shi da kallo

Kallon kallo aka shiga yi a fallon kafin Hajia Mariya ta fara ficewa da saurin da har bata iya gannin gabanta da kyau

Matsarsa mai dakin tsakiya ce ta sauke ajiyar zuciya tana fadin" Masha Allah, alhmd, hakan yaa yi daidai, na jima ina jira Abanku ya yanke maku hukunci daidai da tsagerancinki, yau rana ta zo sai ku yi aniya, Matar son taso mu je na baki magani ki sha, aunty Allah ya huci zuciyarki dan Allah a karra hakuri,"

Ta dubi y'arta da harare ta ce" Ban san a ina kika dauko wannan halayar ba sam, ni dai ba hak nake ba, na san cewa a duniya Allah shike da komai, hakan ya sa ban cika zafafa abu ba, nakan fuskanci komai a sukake dokin na san babu wanda ya isa ya bani ko hanna min abinda Allah bai bani ba, rayuwa kuwa idan ka sakawa kanka fitina kana cikin tashin hankali, domin zia zamto lafiyar jikinkama ta maka karanci bale ta kwakwaluwa, Allah ya sa kema idan ya dawo ya baki naki marin da sai kin yi fitsari shashasha!"

Daga haka ta bi bayan matar MUHYIDEEN da ta fice da sauri tunda ta ce ta taso su tafi

Ajiyar zuciya Hajia Hasana ta sauke tana kallon yayarsu da ta dago a kausashe tana kallon yan matan falon gaba dayansu Tana kokarin fara yin magana yayarsu ta fara da fadan da bata taba sanninta da ita ba, domin a kaf cikin y'ayan hajia mariya wannan itace mai sanyi fa kuma hakuri da hangen nesa

Rai bace ta ce" Yaya MUHYIDEEN din ne ya zama abokin wasanku? Ashe baku da mutunci? Sa'ankune shi ko meye ya yi na raini da har haka ke faruwa da shi a cikin gidan nan? Ko a tunaninku gidan ubanku ne shi makusanci ne ga ubanku? To albishirunku, ku tsaya ku ji abinda na tabata iyayenku matama basu sani ba domin nima da kyar aka sanar da ni a gidan nan!, Kasuwancin da uban naku ke juyawa kudin MUHAY ne!, Kampanin kayan ginin dake dauke da sunna MUMU ba komai bane sai fasarar MUHYIDEEN MUHAY !, kai bari na kankare maku matsayin da ubanku ke kai"

"Ke Bilkisu" hajia Hasana ta fada a sanyaye dan ta katseta da fadin abinda take fada din nan domin bata ga meye anfanin hakan ba, sai dai a sanyaye Bilkisu ta ce" Mama, dan Allah ki yi hakuri ki barni da mararsa kunyar nan da suke so su wulakantar da darajar mai daraja a idannuwan iyayensuma bale su!, Ke Uma dan ubanki a haka me kike son nunawa? Haba Uma ai dama daya ce kuma kin yi wasa da ita, inace a gidana na baki shawarar ki ajiye wannan magana domin ba wajen warginki bane?, Ke kuma kema da kike da hankalin da nutsuwar, da ladabin da biyayar, shine kika yarda adu'ar da na baki wace na ce da ke koda Allah bai baki yayanmu a matsayin miji ba Allah zai baki wanda zaki anfana rayuwar duniya da ta kiyama domin wata soyayar guba ce a rayuwarka kai baka sani ba, shine kika biye mata har aka san kema sonsa kike yi?, To ku tatara mu je gidana, na kula harda sakaci na iyayenmu ke son haukata ku, ku tatara mu karra gaba kafin Aba ya daura maku auren na gane idan har kun tsaya kun iya girki da tsafta da ladabi da biyaya, ko kuma haukan kadai kukai harda ne ba'a sani ba? Kumu jr kowace ta shiga dakin babarta ta dauko suturarta mu je ina mota domin babu wace zan bi har a nemi dakatar da ni, Walahi da ni kuke zancen shirmamu da baku san ruwan wankanku ba!"

Hajia Hasana kam tana so ta dakatar da ita wayarta ta dauki tsuwa

Daga ringin din ta gane mai kiran hakan ya sa ta mike ta fice tana dagawa ta karra a kunnenta ta yi salama sannan ta saurara yana gaisheta a nutse

A hankali ta amsa shi tana fadin" kana ofice din ne MUHAY ?Yaya ka baro iyalinka?"

Agogon dake hannunsa yake dan kallo a hankali ya ce" Ni dai marabina da ita ta tada aljannu wai dan kawai maza ne ke mana aiki ta ce a cenza su na kyaleta sai kawai aljanunta suka tashi, yanzun dai inaga sun barta"

Ido Mama ta zarro ta budi baki ta ce" Iskokai kuma? Subahannalah dama tana fama da aljannu ne Son? To rai aka bata mata ne da har suka tashi ko?"

Bakinta ya tabe a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" I don't know, Mama to ita kanta kama take da aljannun fa , bama wannan ba ni dai tana ce min ji mana na kyaleta shikena ta shiga ihu, baki ga burgimar da take yi a kasa ba sunna Neman daukanta , da yake bata da hankali bata wani damu ba, Mam dama kun saka min wasu a nan sun min ihu ta karra min da wani ihun, kin ganni a zaune a office kaina na ciwo sosai"

Mama da murmushi ke neman subuce mata, cike da dokin son jin wai yaya iskokan suka kare da shi da ita da tsoron kar dai a je dukanta ya yi,, da wata kaunar yarinyar a raanta wace haka kawai ta ji abinda ta yi na 💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣5️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta idala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A sanyaye ya ce" NAHIDT wani abu na damunki ne?"

NAHIDT ta dan buda idannuwanta tana kallon wajen kofa Itama muryarta a sanyaye ainun ta ce" Tuban ne ba sauki Aban Shuwwa sai na Allah "

Gaba daya sai da tsigar jikinsa ta tashi ta yadda ya samu kansa da lumshe idannuwansa ya kuma budewa yana dan jimke hannunsa a hankali a hankali yana sake yin hakan ko zai mayar da abinda ke masa yawo a sasan jiki

Kuryarsa a matukar tausashe ya ce" Dama na Allahn muke fata ba dare ba rana Nahidt"

Ajiyar zuciya ta sauke tana mirginawa ta ce" Ka ga ina missing din Shuwwa, ga fauzy a gefena da yayanmu aman sai nake ji kamar na koma gidan Shuwwar da zama, ban taba aurar da ita na ji kewarta irin wannan karron ba, sai nake ji kamar ta tafi dindindin ba zan kuma gannin kanwata ba"

Dan murmushi ya yi yana shafa sajensa ya ce" Idan aka ce ki koma gidan kanwarki ke sai ki koma ne?"

"To meye a ciki? Ai kamawa ta yi kau Muhammad" ta fada a sanyaye

Idannuwansa ya dan zarro ya ce" ke, wai ni ba yayanki bane da zakina kama sunnana gatsal?, Ke gabanki baya faduwa idan kika ciro sunnana sama kai tsaye?"

Nahidt ta yi murmushi ta ce" to idan ya fi min dadi fiye da na ce da kai Malan fa shikenan sai na tauye jin dadin harshena?"

Ya salam, watau idan matar malan ta taba gannin wulakanci da rainin hankali a tsayin rayuwarta to bai taba kamo irin na wannan lokacin, kuma wannan ranar ba Babu yadda bata yi ba dan ta samu wanda zata kaiwa sukar dayar boyayiyar karuwar abun ya gagara, ita bayananiyar kuma itace ke kiran mata miji da tsakiyar dare? Salon ta yi magana ya nuna mata taimako yake yi shi ba wani abu dake tsakaninsu? Idan Malan ya yi wasa Nahidt zata kaishi wuta!

Karasowa ta yi ta zauna ta shige jikinsa a hankali ta kai hannunta sasan da ta san sai sun motsa abin yake tashi, sai dai abinda ta ji a wajen a yanzu da ta tabata ba taba shi ta yi ba ba komai ba ya sakata dagowa da sauri tana kai hannunta ta janye wayar dake kunnensa ranta bace ta ce" Ke Nahidt kike ko wa? Barikin zaki ringa baza min a cikin gidana a tsakiyar dare a lokacin da mijina sai sadu da ni? Walahi bari komai ji........"

Warce wayar da ya yi yana kallonta da mamaki ya kai dubansa da sauri kan wayar ya ga an kashe ya saka shi sake kallonta da mamaki ya ce" Subahannalah, me haka yake nuni kennan furera?, Ya salam wannan furuci naki zaki yi gatsal a kunnen yarinyar dake mutuntani take min kallon yaya a gareta?, Me hakan yake nufi da furucinki?"

Hawayen da take rikewa ne suka shiga zubo mata tana kallonsa ta ce" Mun kasa fada maka dan muna shayinka, ko nace dan muna Tsoron bata maka rai kuma abu sai hauhawa yake yi?, Wani girmamawa ga macen dake kama sunnanka kai tsaye? Fitsarariya ce, watsatsiya ce Malan, me kake ji a hira da ita? Me zuciyarka ke son kaika ta baro da girmanka da darajarka, da karatunka, duniya na mutuntaka kana waya a tsakiyar dare da wannan matar? Ka manta kanwarta ce ke kiranka da Aba aman ita tana kama sunnanka ne gatsau Akaramalahu ? Yanzu da nake cikin bukatarka na fito na sameka a waya da ita tana kashe maka murya duba ka ga ka amsa gayatarta ta waya ya Ustaz baka gannin tunkudaka take yi bakin rami ne A'UZUBILAH?, Yaya zaka yi da hakina ko kuma kyautata mana da kake na tsayin lokaci ne zaka zubar a tashi daya ka riki sharin yar bariki?"

Hannunsa ya jimke yana kallonta yana girgiza kansa a tausashe yace" Subahannalah, yanzu da tsarkakeken harshenki kike munana zato wa yar uwarki musulma dan ta kasance a cikin kadarar rayuwa sannan ki dora a kaina dan kin ji jikina a amshe da yannayi sanyi sanyin dake hurawa ko kin manta irin lokacin nan koda baki tabani ba a tabe nake ne ya subahannalah shine zaki yi kalaman nan dan zuciyarta a tabe take ta nemi da jin daga gareni a kan kaurarta gidan kanwarta sai hakan ya zama laifi har ki ce yaya hakinki da nake ci?, Ki yi hakuri idan har ina take hakinki kin ji? Ki tashi mu je daga daka dan mu waye damuwar in sha Allah" (😌 kai jama'a😌)

Nahidt kam wani abu ya ringa tukar zuciyarta ta kafe wayar da ido Gaba daya kanta ne ya kama ciwo da wani madaukakin bacin rai dake shigarta na musaman A duk fadin duniya idanma ana tunnanin basu da kara da kawaici kowa ya zo ya ji sunna da shi domin sun yiwa malan a kan matarsa Dukan abinda matarsa ke yi sun san ita ke yi sun kuma san rura wutar kiyayarsu da yan unguwa ke sake yi harda huduba ta matar malan da suke samu ba ji ba gani idan ta dauki magana da nufin zatai wa'azi sai ta ringa kamanta shedancin kansa da sunnansu tana kwatanta ko makotaka ta hadaka da su to fa ka yi kokarin kiyaye imaninka, watau ita tana rayuwarta ne da neman fitina da hayewa musuluncin kansa bayan ba haka musulunci ya zo mana da shi ba

Tamkar mai fama da cutar hawan jinni haka kanta ya kwashi ciwo sannan jikinta ya ringa daukan mijirya yana sakawa , barci kuwa ya ce mun yi da ke yau zan ziyarceki ne? Kama kanki malama, hakan ya sa ta ringa hawaye tana sharewa a hankali ta fashe da kuka tana fadin" Bariki kennan, mai barin bashi kala daban daban, ita bariki ko baka shige ba ka kwatanta bale ka shige har ka mutu sai ka samu wanda zai bika da bita da kulli, Bariki mai zubar da mutunci warwasss a kasa, da ba dan Bariki ba anya kuwa da matar malan zata iya wulakantani? SHUWWA, Shuwwa kin gani ko?, walahi gidanki zan kaura ni dai, gidanki zan kaura, kin ga da kina nan na fada maki abanki ya mikawa matarsa waya ta zageni da kin ci min uwata har cikin gidanta, ni kuma da na samu Abanki na fada masa me yake tunani? Hala abinda ta fada haka shima yake tunani?, wai Shuwwa dan kawai na kireshi zan gaishe shi shine ya kashen waya? Allah kaimu safiya tun karfe shida zan tafiyata gidanki ba wanda zai sani dan na kula nema suke su rabani da kanwata bayan ita kadai ta rage min !" (🤔, Nahidt kin fara zuwa da bidi'a gidan Shuwwa kuma?☹️ Soja mata saman kanka☹️)

A cikinsu kowace ta kwana ne da abu bako a cikin zuciyarta SHUWWA haka kawai take jin wannan abin da ya yi a bayane ba banza ba, koma meye ba karami bane ba zai saka shi zuba mata tea ta sha kafin ya tafi da shi, shin haka yake yi da kowama ko tsabar bai yarda da ita bane ya saka shi aikata haka? Nahidt kuwa ta kwana da kudirin zakara ya bata sa'a ta sauka a kusa da kanwarta, sosai zuciyarta ke ciwo da abinda take kira wulakancin Malan, ta gama yarda cewa a kusa da Shuwwa ne kadai zata yi rayuwa cikin farin ciki, a gidan yayanta babu abinda ta rasa na rayuwa, Fauziya na gefenta koda yaushe, sai dai bata san me yasa ba yanzu Fauziya ta cika sada kai idan sunna hira, bata sakewa irin na da a yi ta ihu da kakaba daria, takan zauna du a takure ne bata san dalili ba sam, duda takan yi tunanin ko matsalar barikin da suka taba tare ne yake saka Fauziyar rashin sakewa a kusa da ita? Ko a tunaninta zata riketa ne ko meye? Koma dai menene ta kawo ido ta zuba zata koma kusa da wada ba zata taba wulakantata ba duk rintsi, wace idan ta budi baki ta ambaci sunnan bariki dan ta yi kuka ta wawureta ne ta kuma tambayeta yaushe zata daina, ba dai dan tai mata gori ba

__________________________________

Shi mutun idan ya san ciwon kansa ya kasance mai yin sauko dan aiwatar da aiyukakan dake gabansa, bama mace wace ya dace ace ta yi safiyar mamaki ta gyara gidanta dan gudun mutanen daka iya yi mata safiya ko mijinta kansa dan kar kazantarta ta zauna a idannuwansa, babu abinda ke kawo wulakanci irin kazanta, kazanta batai ba a rayuwa, Wadinnan dalili da Shuwwa ta rike ya sakata karfe biyar na yi ta diro daga saman bed ta nufi kasa ta kunna fitilu ta shiga kunna kayan wuta ta zuba turaran wuta sannan ta dauko kayan share share tana dan yatsina fuska ta gyara zaman audugar matarta da ta saka domin yau ta farka da jinni

Saman ta haura tana dan nishi dan ta jido kaya ta ajiye a kofar dakin nasa ta kwonce zanin da ta daura a saman yar yololuwar rigar barcinta wace da kadan ta dara cibiyarta ta dan zazage zannin da kyau ta dan wara kafarta dan ta gyara daurin zannin kanta a kasa , kan nata sanye da hular barci mai laushi mai kyalkyali fara kal ruwan rugar dake jikinta itama mai santsi mai lafewa a jikin mutun sannan mai siririn hannu

Kofar dakin ya bude yana dan yin hamma idannuwansa suka sauka a kanta da zannin a hannunta tana sake kabewa zata daura

A zabure ta dago sukai ido hudu, ta maida dubanta kan cinyoyinta dake waje har zuwa kan jan pant dinta mai raga raga A haukace ta juya da zannin ta gyara tana daurawa hakan ya sa ta bashi bayan kafin take rufa zannin a cumurmure ta daura shi sama sama sosai tamkar bagwariya hakan ya sa gaba daya idannuwansa a kan duwawun nata har ta juyo du ta rikice kirjinta na hawa sama da kasa kar zai bale ya fito daga ciki ta raba gefensa bakinta na rawa ta ce" Zan , Zan shige ciki"

Daga haka ta yi kasan hannunsa dake dafe da jikin garun ta shige dakinsa wanda ya yi mutuwar tsaye a wajen da yake ba tare da ya gane halin da yake ciki ba

Da balaki ya juya ya bi bayanta a lokacin itama ta rasa ina zata nufa, gaba daya ta rikice ganninta da kato ya yi a haka, waima uban me ya fitar da ita da asubar nan ne? Ta bari idan ya yi tafiyarsa sai ta yi aikinta mana, yanzun a banza katon wofi ya kaleta?

"Ke ke zo nan!" Ya fada a kausashe yana nuna mata gabansa

Gaban nasa ta kalla ta karra karewa tsayuwarsa kallo, adu'a ta shiga yi a cen kasan zuciyarta na neman tsari da shi, sannan ta shiga takowa jikinta ba karfi sosai ta nufo inda ya nuna matan

Hannunsa ya saka yana fadin" Ki gyara wannan abin dake jikinki kafin ki karaso min nan!, Kin ga tsayama a cen na fada maki ki fita a harkata a cikin gidana kin ji abinda na fada maki!"

Dukan jarumta, da tsaurin ido irin nata da rashin Tsoro ta yafo tana kallon hannayensa da bemab maboya a dakin nasa kasa kasa ta ce" wai gidansa, gidana dai"

Dif dakin ya dauka domin tsittt ya yi da fadan dan ya ji abinda ta ce Kai, wayo, anya ba gamo ya yi ba? Anya ba aljanna bace ta shiga lamuransa aka daura masu aure? To aman idan aljanar ce shi me ya mata? Yanzu ace yyarinyar nan ta rasa wanda zata raina sai shi? Cewa fa ta yi gidanta ne fa?

A kausashe ya ce" kika kuma cewa gidana naki ne sai na baki mamaki a cikin gidan nan, kin ga ni fa ba shashasha bane da kike son mayar da ni abin wasanki, sannan da kika fito kike sakin zani a gabana a tunaninki da irinku na kai min da tuni ban zama bunsuru a kasar nan ba? Ki kiyaye haye min har na samu mafitar rabuwa lafiya da ke domin idan kikai wasa sai dai ki sake jewa wani katon a kakarye!, Shirmen banza da wofi, ke mema kika zo yi dakina ne?!"

SHUWWA ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" To aman ai gyaran dakin zan yi ko?, kumama ka ga soja nifa ba abinda kake tunani na zo yi ba walahi ko daya, gani na yi a dan zaman da zamu yi da kai wanda nake fatan ko yau ne ya katse nima a yabeni ya fi da ai min Allah wadai kau?, kuma da nake cema gidanka gidana ne ba fa dan ina nufin hakan har cikin raina bane dan dai na dan farkar da yarenka ne kar sunna neman kawo min raini, bayan wannan gidanma ai na gwamnati ne gaba daya......". Ba da tsayaya bane take bashi amsa, irin amsar nan ce kana magana kana marairaicewa kana karya kai da nuni da hannayenka wanda ke nuni ala dole kai a tsoracema kake da mutun sannan a ladafce kake bashi amsa fa ba wai a hargitse ba, idan dai mutun mai rauni ne dole zai birkice a kallonta, idan ba mai rauni bane kuwa bakinsa zai iya yi maka gum ko ka ga mutun ya rikice yana zaginka da magulmaci ka bar masa waje, ba wani gulma ya rikice ne bawan Allah

Readers Also Read