Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 3
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 3: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 3. Rigar dake saman rigarta ta kama ta cire ta yar a nan kasa Lulubin dake…
3,334 words
Rigar dake saman rigarta ta kama ta cire ta yar a nan kasa Lulubin dake saman kanta na farin mayafi ta ja ta cire ta yar a kasa hakan ya sa lalausan baki sidik din gashin kanta bayana a kunce ba ko gyale a jiki Gashin ta shiga barbazawa ta kama rigar tata daga baya da sauri ta yaga tana zarro idannuwanta ta ce" Fine, abinda na so yi kennan sai gashi ka taimaka min, ka ga da zan ratso ta nan yaya hudu na hadu da su yan mata a zaune sunna hira, haka kuma na hadu da wasu mazan, babu abinda zai fitar da kai a maganar da zan fada cewar ka zo zakai min fyade ne, Elhaj kana tunanin ko y'ayanka zasu yarda da kai ne bale matanka? Bismillah ,, ga babar shedar da zata nuna cewar na juya dan na gudu ka yagan rigata, na rantse da Allah kaine zaka kwana ciki, ashe baka san kaidin mace ba? Barama ka gani!"
Da sauri ta bude muryarta tana ihun"kai Wayo jama'a ku taimakeni zai ketan hadi, Wayo a taimakeni Elhaji zai fada min, haba Aban husna ka rufan asiri ka barni da mutuncina kar ka manta kaima ka haifa fa, kana da yan matan gasunnan birjik idan akai masu haka yaya zaka ji?"
Ido ya zarro hadi da yin baya yana zarro idannuwansa hadi da dora hannayensa saman bakinsa har yana taune harshe wajen fadin" Ke ashe baki da hankali?, kin ga dan girman Allah ki rufa min asiri, ni ba abinda zan maki, ki wuce ki bar min gidana kar ki tonan asiri a cikin anguwa!"
SHUWAR ta ce" na rufa maka asiri? Ni da ka yankan tikitin zawarci rana tsaka dan an zo an fada maka zance ka so rufan asirin ne? Ka fitar da ni kawai, bilahilazi sai ka bani million goma ko zan bar gidan nan cikin salama idan ba haka ba kuwa ga message dinka na jiya na barazanar da ka min bayan daurin aurenmu cewar maza maza a matse kake idan ba Haka ba kana iya yanka min tikitin zawarci, duda na zo din ka yankan ko? To du na goge rarashin da na maka har magariba ta sanyo kai kafin mu hadu da kai a yanzu Elhaji a shirye nake ko ni ko kai domin idan baka bani kudin nan ba zan maka ka kotu da shedar fada min da y'ayanka da matanka zasu bada da ta wayata inaga dole a leka gidan maza a amshi tarbiya!, ka bani ko na tona maka asiri duniya ta jimu!"
Yadda ka san mai kamun aljannu, yadda ka san mahaukaciya tartibiyarta haka SHUWAR ta zamewa ELHAJ mai shinkafa, tabas idan ya taba yin dana sanin rayuwar bariki to a yau ne, da ta san dalilin da ya sa ya saketa dan ya gane yayarta itace macen da yake mugun son aura ko ta yayane dan su yi zaman aure da junna domin tun ranar da ya ganta a shagonsa ya haukace sai bai kuma ganninta ba, bai kuma san ita ko wacece ba da cewar tana rayuwar bariki ba sai a jiya wanda Hakan ya daga masa hankali ya rikita shi harma ya kaishi ga aikata aiki irin na shirme ya makawa SHUWAR din saki uku wanda dalilin sakin nan sai da ya yi kuka domin ya tashi a ba wan ba kannin duda burinsa daga baya ya samu yayar su yi aure domin ai ba abinda ya shiga tsakaninsu da SHUWWAR din , sai ga kuma wannan wawan dirowar daga sama
A haukace ya ce" Yaya kike tunanin zan ajiye million goma a dakina bayan ga banki ga komai gari cike da barayi?"
Da karfi ta ce" Kar ka raina min hankali, ka manta ka fada min akoy asirin da akai maka na harkar kasuwancinka da aka haneka saurin kai ajiyar kudi banki? Cewar ka'ida ne kudi baka kaisu banki sai ka tara na kwana biyu ko ba kai ka fada min ba? Kudin kasuwarka na jiya yana dakin nan, bari ka ji Elhaji bilahilazi ka fitar min da kudin nan kai Wayo zai tuben rigata......" Ta fada tana daga rigar tata gaba daya ta cire a jikinta wanda hakan ya yi daidai da buga bangarensa inda suka kai dubansu a tare a haukace sannan suka kalli junnansu
Zata kuma kurma wani ihun ya kai gwuiwoyinsa kasa yana hade hannayensa duka biyu jikinsa har yana rawa ya ce" Ki yiwa girman Allah zan dauko zan dauko shuwar kar ki tonan asiri a anguwar nan sunna gannin mutuncina sosai...." Yana fada yana mikewa da yin ciki da gudu gudu haka tuwon duwawu da tumbinsa ke rawa babar babar har ya shige ciki
Da sauri ta wawuri rigarta tana sakawa tana sake waiwayen kofar da ake bugawa daidai ya fito da wata bakkar jaka ta saka hannunta ta warta ta juya da sauri bata ko tsaya ta sake bi ta kansa ba tana fadin" Ban gama da kai ba, yadda ka ciran wahala sai na wahalar da kai !" Kofar ta bude pagam sukai ido hudu da baban dansa da ya zo gaishe shi yake jin yar hatsaniya aman kuma ba zai iya shiga ciki mahaifinsa bai bashi damar hakan ba
Da ido suka raka junna ita da shi kafin ta cire kanta da sauri ta wuce ta nufi get, inda shi kuma ya raka bayanta da kallon mamakin wacece ita a dakin mahaifinsa da irin shigar nan ta riga da wando pakistan damamu kanta ba dan kwali, ga wani wawan kanshi da take bari du idan ta gita?
Kansa ya saka dakin da salama a bakinsa yana kallon mahaifinsa da ya amsa yana juyawa ya nufo tsakiyar falon yana fadin" Zauna zauna Abdul Mutalab ina zuwa"
Maimakun ya zauna din sai ya samu kansa da karasawa wajen da dan kwalinta ke yade ya duka ya dauko yana kallo A hankali ya kai dan kwalin wajen hancinsa yana lumshe idannuwansa ya shinshina , dadadan kanshin da dan kwalin ke fitarwa wanda ta manta tsabar kidima ta tafi ta bari a nan
Dago kan da zai yi ya ga mahaifinsa ya fito sai zarro ido yake da waya a hannunsa ya sauke dubansa a kansa hakan ya sa da sauri ya jimke dan kwalin Yana sake gaisar da mahaifin nasa
Har yana inda inda ya ce" Abdul Mutalab ka ga yarinyar nan da ta fita, ita nake so ka kai kararta domin sata ne ta min, sunnanta SHUWAR, zan fada maka har anguwarsu da komai da komai nata, kudinane a jakar nan million goma sha uku, Abdoul Mutalab ta tafi da su kai dai sheda ne ka ga fitarta da jakata"
Samun kansa ya yi da kure fuskar mahaifin nasa da kallo, SHUWAR?, Sunnan nan kamar shine sunnan da yaron shagon Aban nasa ke fada masa sunnan budurwar da aka daurawa mahaifinsa aure da ita jiya ne? Ama idan haka ne ai ya shiga uku ya lalace...... hasbunnalahu wani'imal wakim ina zai saka kansa ne? Dan kwalin nata ya sake jimkewa yana amsar wayar da mahaifinsa ya bashi mai dauke da numberta yana sake jadada masa cewar ya fa maida hankali tunda likita ne shi yana iya fita idan wani bashi da damar fita ya yi maza ya je ya shigar da karar nan tun yau tun yanzu!
Shi dai samun kansa ya yi da fitowa ya fice a gidan ya shiga motarsa ya zauna yana dora kansa a jikin sitiyarin motar a hankali ya furta " SHUWAR, Allah ya sa ba ke aka daurawa abana ba dan Allah, ke ko barauniya ce ke ba komai zan ajiyeki a gidana na kilaceki ta yadda ba zaki fita bama bale har ki yi satar kin ji?, SHUWAR ke wace yare ne ce?"akinsa da karfi ya ce" cije a kasan zuciyarta tana aya💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 4️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
A daidai lokacin da Abdul Mutalab ke begen SHUWAR da tunanin maimakun ya kai kararta saboda million goma sha ukun mahaifinsa gwara ya nufi kampanin sadarwa a bi layinta a sanar masa ina take wacece ita hankalinsa tashe ya dauki hanyar da ta dauka ba tare da ya san asalin nan din ta nufa ba ita kuma a daidai lokacin Jar danja ce ta tsayar da ita a cikin motar hakan ya sa ta dauki lokaci mai ban mamaki bata saki ba Gannin kamar Danjar ta ki ta saki sai ta saki karinta ta shiga neman ribom a cikin motar ko zata ci sa'a ta samu dan ta daure kanta da shi, a irin lokacin ta taki rashin sa'a domin wayarta dake cikin motar ce ta dauki kuka tana dubawa ta ga bakuwar number, har zata share sai kawai ta daga tana ajiyewa a gefenta tana ci gaba da neme nementa hankali kwonce duda irin yadda yanzu take gannin garin shallllll sai daidaikun mutanen dake tafiyarsu a gefe da gefen kwalta aman a tsakiyar titi duma wanda ya san ciwon kansa ya nemi waje ya ajiye brakarsa dan samun kwonciyar hankalinsa
"SHUWWAR a ina kike ne?" Ta ji muryar namiji na tambayarta da kama sunnanta kai tsaye hakan ya sa ta sake duba wayar dan gannin number daidai da ana kwonkwasa mata gilas din motarta
Dagowar da zata yi ta ci karro da abinda ake fadin kana samun faduwar gaba dake hadasa maka cikinka ya juya daga inda yake ya dawo kasa , a da bata san ana juyawar ciki ba sai yau, Hannun mutumen ta fi kurawa ido wanda hannun ke jujuye irin a mumurden nan irin hannayen da ake nunowa a film din yan indiya wanda yawancin lokaci mukan yi daria mu ce ku ji wata karya wai hannu ne haka, Kafin take sauke dubanta a kan fuskarsa da bakin gilas din dake saman fuskar sannan ta waigo da sauri wajen da aka sake buga mata da gagawa da dan karfi tana sauke numfashi da gagawa tamkar mai cutar athsma, domin har ga Allah sai ta ajiye hakan a matsayin ita kadai ta ga halitar nan
Da sauri ta nemi fitowa dan ta kula hakan yan jagaliyar sojojin ke so ta yi a lokacin da ta sake gannin sojoji ne zagaye da ita tamkar yar ta'ada Lokaci daya magangannun Fauziya suka ringa dawo mata a kwakwaluwarta na irin tsaron da aka saka a kasar da hanni da akai kan fita kwata kwata
Tana budewa tambayar da aka fara yi mata ta sakata shiga inda inda gaba daya ta rasa me zata bada amsa
Babur din ya caka ya ajiye ya sauka yana matsar da sojan xake yi mata tambayoyin dan ya kula kamar ana sako taushi a lamarin, gefe ya maida shi da hannunsa ya karaso daf da ita sosai hakan ya sa ta rintse ido tana dahe rai tana son gane sunna ganninsa suma ?, Kai jama'a yau ta ga halita a gabanta
Tun daga kasa har sama ya kare mata kallo a yan sekwani kama daga shigarta, da gashin kanta dake barbaje kafin ya budi bakinsa a hade ya ce" Kin yi shaye shaye ne?"
Da sauri ta girgiza kanta tana fadin" Aa walahi "
"Ur name?" Ya fada a kausashe
SHUWAR ta ce" SHUWWAR , SHUWWAR ne sunnana Yalabai"
Gilas din idannuwansa ya cire yana fadin" Bamu takardar shedar yar kasa ce ke"
Da sauri ta juya daga wajen nan da take ta saka kanta cikin motar hakkan ya sa ta bado bayanta gabansa ta yadda duwawunta ya gogi kafarsa ta hagu da ta fi kusa da ita a lokacin da bai aune ba
Kansa ya sada dan ganin meye ya taba masa kafa a wajen da hakan ya faru ya dago da sauri daidai ta sake fitowa daga motar da jakarta ta ciro katinta ta miko masa hannayenta har dan rawa suke dan so take ta zauna ta fahimci wannan bawan Allahn mutun ne ko ba mutun ba?
Takardar ya amsa ya dan matsa yana dubawa ya dago yana tsatsareta da kakausan kallo ya ce" A nan an rubuta *IBTISAM*, kin ce sunnanki *SHUWWAR*, "
Hannayenta ta shiga hadawa tana son yin magana a kausashe ya ce" Saurara, ki tabatar abinda zaki fada gaskiyarki kennan domin tsagera na fito kamawa kuma na fara haduwa da ke, kin ga gaba dayanki kama kikai min da wada ta sha giya, sannan kikai min kama da barauniya, da kuma wace bata jin magana, so ki dan saukaka min kama ki mana? Idan kika wahalar da ni zan wahalar da ke ne"
SHUWWAR ta matse fuska sosai tana kikifta ido, a kasan zuciyarta a yau harta da bakon ashar ta hada ta laulayawa wannan gabjejen abin dake gabanta a tsaye, da ya san kudurinta a kan sojoji da bai tsayar da ita ba, wai yar shaye shaye, barauniya, marar jin magana, aka kai ikon kasar nan sata? Aka kaisu yin mankas? Bale wannan aba wai ita magana ai basu san inda aka rawaito jinta ba, shine shi zai tsaya mata a ka ya yi maganar nan? Sai dai ta san a yanzu a nan da take tsakiyar kartin nan idan ta yi wasa sunnanta nama, babu abinda zai raba shi da ita kuma sai Allah Iya gaskiyar lamari a kan maganar sunnanta ta budi baki tana sheda masa ta ce" Walahi sunnan IBTISAM shine asalin sunnan da iyayena suka saka min a garin Riyad, na cenza sunnan nan ne sakamakon sakina da mijina na biyu ya yi a lokacin da na tare a gidana yana sona ina sonsa aka raba auren, Yalabai ba zan manta ranar da Salisu ya mikon takardar nan fara ba mai bakin rubutuuuuuuu......" Sai kawai ta fashe da kuka tana fadin" Yalabai yana kiran IBTINA, ki yafe min, ina maimaita haba habiby kar ka sakeni ka tonan asiri yar bindin uwar babarsa ta saka ya yankan tikitin wahala nake yawo a titi ........Shin Yalabai tsakani da Allah wannan abin adalci ne??????"
A daidai likacin da MUHYIDEEN ke sake kallon wannan yarinyar sannan yana sake yarda da maganar da akai masa cewar garin nan gari ne na tsagera, yana jin sha'awar yarda da zama a garin na shiga zuciyarsa wata motar ta sake kawo kanta wajen wada ba shi ba da ya mutu da mamaki da rashin kunyar wannan mai shige da yan wiwi din ba, harta sauran sojojin da suka saki baki da hanci sunna mamakin wannan yarinya da ta budi baki take magana kanta sake hankalinta kwonce tana yiwa ogansu hira tana bashi labarin abinda ya faru da ita kamar bata san waye MUHYIDEEN ba? Suka juya sunna gannin fitowar Abdul Mutalab dake nuna takardar wuyansa yana gaishe su da girmamawa har ya samu kansa a inda take din da gaskata abinda aka fada masa na wajen da take ya ja da sauri gannin wanda ke tsaye a gaban SHUWWAR din
Wani dunkulelen yawu ya hadiye yana hado jarumta irin tasa ta d'a namiji yana hanna kafafuwansa yin rawa a gaban SIR LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN ya ja daga dan nesa jikinsa bai boye rawar da kafafuwansa ke yi ba ya ce" Allah ya kara maka lafia Sir wannan din matata ce, fushi ta yi na biyota dan na bata hakuri , dan Allah a yi hakuri a bani ita mu tafi gida ita batama san da dokar da aka dora na kar a yi yawo a cikin gari yau da gobe har sai an gama taron nan ba"
SHUWAR da zuciyarta ke dukan casa'in ta raba bayanta da jikin motar da dan sauri ta yi bayan MUHYIDEEN dake son fuskantar bayanan Abdul Mutalab tana zarro ido tana sake leko dan gidan Elhaj mai shinkafa da mugun mamakin irin gileliyar karyar da ya gila wace ko wuka za'a dora mata a wuyanta a yanzu zata iya fadin cewa babansa ne ya turo shi ya kasheta ya amshe kudin da ta karbo, Au ya kai masa ita hakan ya sa daga bayan MUHYIDEEN take danna zuciyarta dake neman balowa ta fito ta bakinta ta kasheta dan tsoro da firgici
Bayan MUHYIDEEN ya karanta sunnan dake saman bage din Abdul Mutalab dake tabatar da shi din cikaken likita ne a asibitin gwamnatin kasar ya dago ya sake kallonsa da mamakin jin wai wannan matarsa ce, Sai a lokacin ya fahimci yarinyar nan a bayansa ta labe hakan ya sa ya dan ja baya yana bata damar bayana a filin Allah ya ce" Meye shedar da zata tabatar min da iyalinka ce wannan?"
Da sauri Abdul Mutalab ya ce" Akoy shedar kudinta dake cikin bak'ar jakarta Million goma sha uku , Code din jakar kuwa shine 098526, ga kuma dan kwalinta dake hannunna da ta bara min ta fito, ka yi hakuri Sir zamu koma gida mu sasanta kanmu"
Da karfi ta ce" Da wa?, Ka koma gida da wa? Ka ga ba inda zan je yanzun, zan biyoka Daga baya ka je kawai ka fara tafiya kawai"
Tsitttt wajen ya dauka yan kwararin mutanen dake wajen masu kakin soja suke kallon kallo hakama Abdul Mutalab ya gama sarewa cewar idan har ta yi yadda aka fahimci tafiyarsu ba daya ba zata ja da farar rigar tasa ta likita MUHYIDEEN ya karkata masa kai, me yasa zata yi haka ne?
Motar MUHYIDEEN ya karasa ya saka hannunsa ya bude ya ciro jakar yana ajiyewa a saman motar ya shiga saka numbobin da ya fada ya bude jakar
Da mamaki ya kale shi yana fadin" Wani abu kuke yi a kasar nan da yake kawo maku kudi irin haka da har matarka zata malaki irin kudin nan ya kasance har tana yawo da su a sake cikin kasa?....." Ya maida dubansa kanta yana fadin" Menene sana'arki?"