Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 4
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 4: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 4. Tsakani da Allah ta yi dana sannin fitowarta a yau din nan, idan sau…
3,304 words
Tsakani da Allah ta yi dana sannin fitowarta a yau din nan, idan sau dari zai budi baki ya yi magana sai ta ji kamar zata saki fitsari , haka kuma gabanta idan ya yanke ya ruguje ya fadi sai ta matse kafafuwanta dan kar ta rubta kasa, watau yadda yake a tsaye haka muryarsa take bawan Allah, ta yiwu bashi da lafiyar makogwaro ne kau?
Da sauri ta ce" Shi ya min kyautarsu jiya, jiya da dare dan na ce sai ya sake ni"
Yanzun sai Abdul Mutalab ya ga kawai yau sai sun ja an masu dukan kawo wuka a yanka ko a rufe su su saka kansu a uku
Yana inda inda ya ce" Eh Sir haka ne, ni kuma na same su ne daga wajen Mahaifina mai sunna Elhaj Mustafa Mai shinkafa"
Har ga Allah daria lamarin ya bashi, sai dai ko a alamu bai nuna ba ya mayar da jakar cikin motar yana rufewa ya ce" Ku koma gida , SERGENT ka basu takardar da zasu ringa nunawa har su koma gida dan kar a rike su"
Ba Sergent din ba, su da kansu sai suka samu zukatansu da dar din barinsu da ya yi haka kai tsaye bayan bai yi kama da sakarai ba bale a ce ai sakarai ne dole ya hadiye magana irin haka tamkar ta tatsuniya Haka yarensa suka cika da mugun mamakinsa wanda karara ya kasa boyuwa a saman fuskokinsu
Amsar takardar suka yi ya mata alamun ta shiga mana, a lokacin da ta saki baki da hanci a kasan zuciyarta tana ayana' Wayo bawan Allah, dama dan adam tara ne ba goma ba, shi wannan gashi da tsayin, da kyan, da mulkin, sai dai ba ilimi, kai tsaye mun masa wayo haka?, To bara na samu na tserewa wannan mahaukacin tun kafin ya rike ni'
Motar ta shige tana ja da sauri ta dauki hanyarta shima ya shige yana bin bayanta da saurin balaki dan kar ta bace masa
Tunda suka fara aikin yanzu ne kadai ya yi wani alamu da ya nuna kamar murmushi ya yi yana raka tseran gudun motocin nasu da kallo yana maida dubansa wajen yarensa a lokacin da LIEUTENANT maman sani cikin ladabi yake fadin" Sir sai na ga kamar karya fa suke yi su dukansu?"
Gaba ya yi kadan hannunsa daya a saman kafadar Lieutenant Maman Sani ya ce" Ka san menene? Ban taba sannin garin nan zai bani sha'awa irin haka ba, ashe haka yake cike da tsagera?"
Lieutenant Maman Sani duda bai fahimci me yasa Sir ya fadi haka ba sai ya yi murmushi yana fadin" Sir a garin nan namu sai mu"
Muhyideen a rarabe ya furta" SAI KUMA NI, Ai wannan ba matarsa bace, sannan kudin nan ba nasu bane su dukansu"
Da mamaki ya ce" Sir aman yaya aka yi ya san code din jakar kuma me yasa muka barsu suka tafi?"
Kafadunsa ya daga yana fadin" Jakar ba tasa bace aman tana da alaka da shi haka kuma ko ta waye mai ita shi ya turo ya amsar masa, idan da ba haka ba da tuni an sanar mana da batan kudi Million goma sha uku ba fa kadan bane in dai ba ba muguwar hanya bane dole mai su zai nemi hukuma, sannan ka takardarta ta bari tsabar a kidime take, ga dukan alamu barauniya ce yarinyar cen! Lieutenant ka gane ko meye a tsakaninsu su duka a tsakaninsu yake kuma a tsakaninsu yake yawo, aman zan gane idan na koma na dawo zaman garin kwata kwata, domin zan shedawa SHIRP OF ARMY cewar na amince zan zo na yi shekara biyar a garin nan kamar yadda ya bukata na kiya a da, Lieutenant ina fatan kunna maraba da bako?"
Sosai gaban Lieutenant ya fadi, harma ya shiga hali na tsoro da jin furucin Lieutenant Ganaral cewar zai sauka a garinsa gaba daya har na shekara biyar? Ai da an yi tashin hankali domin ba ga yayan ba ba ga iyayen ba kan mai uwa da wabi lamarin zai sauka, aman da fara'a a fuskarsa sai ya ce" Da mun kasance masu baban sa'a My GANARAL!" __________________________________
A haukace ta parka motar a kofar gidansu tana waigen bayanta Gannin ya karaso yana shirin tsayar da tashi motar ta sake ruko idannuwanta waje tana furta" Kutumar uban cen har gidan ka biyo ni?"
A guje ta bude motar tana warto jakarta ta arta a dubu ta bankada kofar ta afka ciki tana ihun kiran💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 5️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.
*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
Ta arta a dubu ta bankada kofar gidan ta afka ciki tana ihun kiran " Aunty?, Faufiya na shiga uku ya biyo ni, ya biyo ni har gida zai tonan asiri"
Daidai lokacin da ya shigo balbalin gidan yana fadin" Kin ga SHUWAR, ki tsaya, ki dakata ba abinda kike tunani bane ya kawo ni wajenki tsaya ki ji mana SHUWWAR?"
Idasa shigewa falon ta yi tana sake ihun kiran auntynta dake bayi a irin wannan lokacin tana fadin" ku bani tabarya ko ice, ku daukon gatari ko wani katon katako na sauke masa kai walahi talahi ya biyo ni ni kuma ba zan bada kudin nan ba, wayo na shiga uku tayani danewa Aunty zai bude ya fi karfina"
A rikice auntyn tata ta kama mata tana tayata dannawa tana fadin" Yau na shiga uku da wata jarabar, ke kudin waye kika amso kike rantsuwar ba zaki bayar ba, meye a katuwar jakar nan SHUWWAR?"
SHUWWAR na haki zata yi magana ya daga murya yana fadin" Na rantse da girman Allah ba kudin nan ne ya saka ni biyo ki gidan nan ba, kar ki manta a hatsari na gama saka kaina yanzun nan kin san dai saboda kudin nan ba zan aikata haka a gaban MUHYIDEEN ba ko?, domin kin san a dazun nan da ace ya gane ni ba mijinki bane yana iya daure mu da igiyar dake jikinmu wace sai mun tsufa a gidan yari ba wanda ya isa ya fitar da mu aman na jajirce na ce ke matata ce domin idan na bari ya tafi da ke na shiga ukuna"
Turawar da suke yana turowa ta fara sasautawa tana kallon yayarta da kuma kofar jin furucin bakinsa
Yayarta ta rage murya kasa kasa sosai ta ce" Kudinsa kika sato ne yau kuma SHUWWAR ? Waye shi mahaukaci kika janyo mana cikin gidan bayan kin san jiya na kori baba mai gadi?"
Kai ta girgiza itama ta rage murya sosai tana fadin" Ba mahaukaci bane, kudin kuma ba nasa bane na babansa ne, dan gidan mai shinkafa ne fa, na je gidan ne na masa barazana ya ban jakar kudin nan shine ya turon yaronsa ya kwace bayan inaga million goma sha uku ce a cikin jakar cen aunty"
Ido yayar tata ta zarro tana furta" Million nawa?"
Ta sake maimaita mata adadin kudin, hakan ya saka yayarta gannin a kan kudin nan ko trela ce tana iya tarba, kai a kan kudin nan ko karo ne da jirgi zata iya yi Wata zuciya ta ciyota ta samu kanta da dakatar da Zahra'u dake sake dannewa kar ya shigo ta ja SHUWWAR ta mayar da ita bayanta da jakar suka bashi dama ya bude kofar suka bayana a gabansa sun yi cirko cirko da su
NAHIDT ta sake aro fuska irin ta rashin mutunci ta ce" Kai me kake so a nan ne? Nice nan uwarta idan wani abin ne bismillah ina sauraronka ka fara da ni!"
Wace ta kirayi kanta da maman SHUWWAR ya karewa kallo yana fadin" Mamanta kuma?"
Ta sake hade girar sama da ta kasa tana fadin" Eh da matsala ne a haka?"
Tsaki SHUWAR ta ja tana fadin" Dan Allah ki daina cewa mamana ce ke duba fa ki ga kalar gashin da kike da a saman kanki wa kike so ya yarda ? Ka ga yayata ce fada mata me na maka kake biye da ni !"
Murmushi ya sake yana kallon yadda suke shirin kaurewa da wani fada a tsakaninsu ya budi baki yana fadin" Kun ga, dan Allah ku yi hakuri ba maganar kudi ba ya kawo ni nan, haka kuma ba wani aiken babana da zan yi, abinda nake son sani, abinda ya fi daga min hankali a kan SHUWWAR , dan Allah SHUWWAR a shagon babanmu ake maganar budurwarsa harma aka jadadan an daura masa aure da wata mai sunna irin haka jiya, dan Allah, dan annabi shine nake so ki fadan cewa ba ke bace , domin idan kece na shiga uku na lalace"
Fauziya ce ta iya budar bakinta wajen fadin" Da aka yi me kuma?"
Kallon Fauziya ya yi yana fadin" Baiwar Allah Idan haka ne hakan na nufin wannan matar da kike gani matar ubana ce fa, kuma ni kuma na kamu da sonta bilhaki bilahilazi"
NAHIDT ta kalle shi da sauri sai kuma ta kalli SHUWAR da ta saki baki da hanci tana kallonsa itama
NAHIDT ta ce" Ka ga, ina ga mu shige ciki mana wannan maganar ai ba ta a yita a waje bace ka ji? Bismillah"
SHUWWAR ta ce" wani irin ya shigo daga ciki kuma kamar kina son amsar maganarsa a bayane bayan ni ba bariki nake aikatawa ba kema sheda ce? Ka ga bawan Allah eh nice aka dauran aure da babanka jiyan nan"
Da sauri NAHIDT ta ce" Eh kuma ya sake ki ba tare da ya kwonta auren ba ko dan an ce ni yar bariki ce, ko akoy abinda ya shiga tsakaninki da mai shinkafa ne bani da labari?"
Kai SHUWWAR ta dafe jikinta ya fara mugun yin sanyi ta ce" Aunty, ko dai so kike ki nunan mu je ciki da shi ta yadda zamu tatse shi kudinsa kamar yadda kike gagawar kawowa tunaninki? Kar ki ce min bayan halin rayuwar da muke ciki kin manta cewar D'a baya auren matar ubansa koda kasa ta binni idonsa? Da ace ba'a dauran aure da mai shinkafa bane ake iya duban wani abu makamancin haka, aman aunty so kike mu fara shiga hurumin ubangijinmu kuma?"
"Kin ga SHUWWAR kar ki sakani a uku bayan wanda nake ciki mana, ni bana nufin aure ya shiga tsakaninki da shi dan Allah aman kuma ya shigo cikinma ai ba laifi bane ko?" NAHIDT ta fada tana kallonta da tsatsareta da manyan idannuwanta
SHUWWAR ta girgiza kanta tana juyawa wajen ABDUL Mutalab da ya kai duke a wajen ya kurawa waje daya ido a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri , ban san sunnanka bama, ka ga du iskancina bana son taka dokar ubangijna,, domin na yarda da mutuwa kuma na yarda da tsayuwa a gaban Allah gobe kiyama, shi yasa nake kiyayewa, nake matukar kiyayewa dan da tarin laifukana idan na sake bayana da irin wannan wanda nake tunanin cetonsama zan iya rasawa watau annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam"
Ta sake sauke ajiyar Zuciya tana fadin" ka ga sakina ya yi a cikin motarsa bayan ya gama zazagin yayata da sunnan karuwa, shi yasa na tarda shi gidansa nima, idan dan wannan ne ka barshi ya rama abinsa, aman ni babu wani abu da zai iya shiga tsakanina da d'a namijin da ba muharamina ba da ya wuce aure, AURE nake so na yi, so nake na yi aure mai daraja na raya sunnar ma'aiki, ina so idan na mutu mijina ya salaci gawata, ina so na haihu na samu ahali irin na kowa, ina so na zauna a kasata duk rintsi na kula da y'ayana na basu tarbiya, ina so na rayu da su har karshen rayuwata, kai a ganninka idan na fara biye biyen y'ayan mazan da suka sakeni na nemi Allah ya zuba ruwan sanyi a saman ALKALAMIN KADARRATA kuwa?, Zaman lafia nake nema, bana neman idasa lalacewa"
Daga haka SHUWWAR ta yi shigewarta ciki da jakar kudinta a hannunta ta bar yayarta da binta da kallo baki a sake tamkar tashar anguwa uku sannan ta maido dubanta kansa da sauri jin wata murya garjejiya ya bude yana fashewa da kuka
Ido suka zarro daga ita har Fauziyar sunna kallonsa yana zaune dangalgal yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, leke leken abanmu sai da ya kaishi ya leko wannan yarinyar kuma ya aureta dan wulakanci sannan ya saketa? Gashi Allah zai kama shi a kaina bayan ni kadai Allah ya bashi d'a namiji na kamu da son abinda yake haramun a gareni koda ya bar duniya? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une yanzu yanzu fa na ganta a gidanmu idona ya rufe a kanta ashe haramun dita ce Ita din? Aunty kun tabata Shuwwar ta haramta a gareni kuwa? babu irin sabanin bakin nan da malamai kan yi a kan wasu fatawowin ? Kun tabata harshensu ya zo daya a kan wannan lamarin? Ba abinda ya shiga tsakaninsu fa"
Kallon junna suka sake yi a karro na ba adadi suka kuma kallonsa, gannin tsakaninsa da Allah kukansa yake ya saka aunty cike da tausayawa ta ce" Ka ga, ka daina kukan nan hakanan, ka tashi ka shigo ka zauna har a ga yaya garin idan kana iya fita sai ka tafi gida, kar ka damu Allah zai daidaita zamu tambayi malaman mu ji ka ji?"
Kai ya ringa gyadawa aman bai shiga ba ya sheda mata yana iya yawo shi dan takardarsa ta likita da kuma wada aka basu yanzun a hannunsa take
Sunna tsaye sai da ya fita sannan suka kalli junna Fauziya na fadin" Yaya zaki ce masa ya dawo bayan kin san wannan abun haramun ne kuma kin san ta san haramun ne ko daureta muka yi muka kaita zata kunto kanta ta dawo ta same mu, balema ta yaya hakan zai iya faruwa?"
NAHIDT ta shiga takawa dan ta he ta sanyo motar gida sannan au rufe tana fadin" Ke baki ga zai sume mana ba a nan? Ni ba dan hakan zai gyaru ba na ce zamu tambayi malamai kuma ma ai ilimi fadi gareshi, ko waye kai ba zaka ce ka san komai ba a kan lamarin, idan fa akoy wata aya da ta halata hakan? Bayan wannan kawai dan dai gani na yi idan ya sume mana ina zamu iya shiga da shi ne a haka"
Ita dai tana biye da ita ta bude mata gidan da kyau ta sanyo motar ta rufe suka rurufe ko'ina suka nufin falon
Sunna shiga Fauziya ta sake ja ta tsaya ta ce" Kin ga, kin sha saka kila wa kala a kan maganarki ki dawo kanta, koda hakan halak ne ki ajiye maganar dan gidan mai shinkafa, kin ga mutun ne mai iyali, y'ayansa yawa ne da su a duniya, koda auren muka je wasu suka daura masu mun siyar mata walahar rayuwa, ba zasu taba karbarta ba koda bayan ran mahaifinsu, maganin kar a yi karma a fara , ki ajiye kwadayin hakan gefe mu fuskanci reality da sauki a garemu baki dayanmu"
NAHIDT ta ce" to uwata, na ce to uwata Fauziya,, na kula du kun daukeni a wata dakikiya ko wata kura, na ce maku na bar maganar ko?"
Fauziya ta tabe baki ta yi gaba a ranta tana ayana' da ace ban san ko ke wacece a kan maganar son farantawa IBTISAM bane da sai ki fadi haka, ke burinki wani wanda zai sota a haukace kamar wannan saurayin, wanda koda ya ji menene sana'armu ba zai gujeta ba ki aura masa ita, bayan idan har muka yi haukan kaita gidansu yaron nan soyayar sai ta dawo ta zama kiyayar da kare ba zai iya sinsinawa ba, baganin kar a yi kar a fara'
__________________________________
Aikin da suka wuni yi, suka kuma raba dare a kai ya saka shi magana yana lumshe ido tamkar wanda ya yi marisa Wayar dake kange a kunnensa ya sake saurarawa yana jin muryar mahaifiyarsa dake magana cikin hawaye wanda hakan ne ya saka shi ajiye komai ya masu alamu ya shiga ciki
A hankali ya kai zaune bakin gadonsa muryarsa a shake dan ya wuni yana ihu da bakinsa ya ce" Kuka kike yi?"
Shiru ta yi tana hadiye kukan dake tukota hakan ya saka shi fadin" Mamah, kin san irin ilar kukanki a kaina fa, saboda Allah dan kawai na saki mace sai ki yi kuka?"
Yanzun kasa rike kukan ta yi tana fadin" Kawai ne? Sakin macen na ce kawai ne? Ana cewa kai ta haka hau ya shigeka auri saki shin gaskiya ne? Yaya kake so rayuwa da mace wace zata zamto ta amsa dukan komai a kan daidai bayan ita din da kanta an hakiceta ne da kashin hakarkarinka dake tankwashe? MUHAY daga kara siga a tea?"
A hankali ya ringa murza hannunsa ya ce" Ba iya shine damuwar ba "
Mamansa ta ce" Mecece damuwar?"
A hankali ya ce" Nikakiyar kwalba ce ta zuba mij a tea ba siga bane ya yi yawa"
Sai da mahaifiyarsa ta mije tsaye a zabure tana fitar da idannuwanta ta ce" Ka ga, kar ka fadi haka dan zama da ita ya fice maka a rai, ka riga ka yi mata saki uku ba dawo da ita zan yi ba, fada ne nake maka dan ka gyara halinka dan bana so gobe ka sake sakin wata kai tsaye daga ta yi dan laifi, domin na gaji da irgen matan da ake yi maka MUHAY"
A hankali ya furta " Toh ba zan sake ba"