Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 5

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 5

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 5: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 5. Ido ta kikiftaa tana kaiwa wajen madubin dakintaa ta ce" Wani irin toh,…

3,372 words

Ido ta kikiftaa tana kaiwa wajen madubin dakintaa ta ce" Wani irin toh, ba toh ba zaka ce min, ka fada min sone take ta kashe min kai, ka fada min yadda abin ya faru, yaya aka yi ka sani? Me ka yi mata? Wani ne ya aikota? Tun yaushe ta fara zuba maka kwalba a tea? Yaya aka yi ka gane kwalba ce ta zuba maka a tea? Shine suka zo suka nemi da na yi maka magana ita da mamanta? Ka fada min ni kuma sai na yi shara'a da su domin ba zan taba yarda da wannan ba"

Idannuwansa da ya rintse gam dan da karfi maman nasa ke magana ga dukan alamu kai kawo take yi ranta ya yi kololuwar bacin nan tana jero tambayoyin da ya rantse da Allah a yanzu dai da ya wuni bakinsa na haikar magana idan ya ce amsoshinsu zai bata sai an kwontar da shi a gadon asibiti koda baya so ya saku kansa da bude bakinsa da kyar ya ce" Mama kar ki shiga cikin gwagwarmayata da magautana, ni na tabata idan ba *ALKALAMIN KADARRATA* ne ya zo da zanen sai sun cin min ba sai dai su yi su gaji, abinda ba zan iya dauka ba shine a fara hakonki, inda kike din nan hankalina a kwonce yake, so plz ki huta mamanah"

Kasa furta komai ta yi a tsayen da take domin ya kashe kiran ne

Tana kokarin maida masa da wani kiran mesage ya shigo kamar haka" Dan Allah ki yafe min , kukan nan da kika yi kuma ki saka min albarka ki share hawayenki, zan zo gobe tare da Shugaaban kasa.......mamah i love you"

Daga haka ya kashe wayar yana saje mayar da idannuwansa ya rintse ya kwontar da kansa a baya yana jin kansa na sake sarra masa, gaba daya duniya ita daya ke masa irin haka abinta a lokacin da ta ga dama abinta, yanzun babar rigimar da yake tunanin mai kwontar masa da tarzomar hakan sai Allah SHine maganar kaurowarsa garin nan da aiki har na tsayin shekara biyar, yaya zata yarda da wannan kudiri nasa? Anya zata amince masa kuwa?........

I don't know oh LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY😍

Shin yaya wannan salon? Yana shiga cikin zuciyarku kuwa?

Maza garzayo ki samu naki a kan farashi mai sauki yar uwa NAIRA DARI UKU NE KACAL TA ASUSUN BANKINA, KU TUNTUMBENI TA NUMBER WAYANA KAMAR HAKA +22793811618 "na'💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 6️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Taro ne aka gabatar mai sunna taro wanda sai da yama ta yi aka ba al'uma damar fitowa ta kafofin sada labarai

A cikin wa'inda suka dauki wanka suka fito cikin gari harda SHUWWAR da yan uwanta Kowace ta nufi hanyarta da irin kudirin dake cikin zuciyarta a lokacin da mutane suka fara watsewa a wajen taron

A hankali SHUWWAR ta gama yarda da abinda zuciyarta ta saka mata kafin ta juyo ta sauke dubanta a saman kwaltar tana karewa dukan motocin dake wucewa kallo

Cen ta hangi alamu na mota mai motsi na karasowa hanyar da take tsaye hakan ya sakata Sauke ajiyar zuciya a hankali ta saka kafarta ta shiga tsalakawa zuciyarta na dokawa tana tsale cike da tsoron kasadar da zata yi da tunanin Allah ya sa ta yi dace a kudurinta

Ido ta rintse sakamakon horn din da aka dana mata mai kukan gaske sannan aka danno kai kanta da tunanin ai zata kauce tunda shigarta ta farar abaya batai kama da mahaukaciya ce ita ba bale kuma yannayin fuskarta bai nuna makauniya bace ita bale a yi tunanin bata gani ba haka kuma bata ji ba Horn din da ake yi mata

Sai dai direban ya makaro a lokacin da ya kunnace mata wuri ne ya iya take birkin gaba daya hakan ya saka motar bada wani karra kuuuuuuuuuuuuuuuuu sannan ta daki kafafuwanta a da gasken gaske kafin take tsayawa inda Shuwwar ta yi tangal tangal ta saka ihu tana sakin jakarta da sabuwar takardar shedar yar kasa ce ita da ta saje domin wancen din ta nemeta ta rasa kadai a ciki ta fadi kasa sannan ta bita ta zube tana dauke numfashi a mugun tsorace domin bata taba tunanin wannan matukin motar zai iya sakin kansa har ya zo ya bigeta ba, koma waye wannan an yi dan airs walahi

Haya haya haya, kafin ka ce meye wannan, nan da nan wajen neman dinkewa yake yi da al'uma, hakan ya sa sojoji biyun da suka zo da gagawa bada damar yan uwansu su karaso su talafa masu dan a tsagaita cinkushewar hanyar domin Sir bai jima da keta hazo ba, a awa dayan da zai yi kuma a sararin samaniya bata cika bale ace ya sauka garin da zai je, karma ace har ya saukan ba zai iya dawowa da wuri wuri ba balema dawowar tasa ba wani abu ne mai wahala ba idan ya ji ana bukatar ya dawo din zai dawo ne yanzu yanzu ba tare da bata lokaci ba, gashi wanda yake cikin motarma baba ne na polisawa tare da masu bashi tsaro zai nufi gida ne hakan ya faru

Alamu take hange, kuma take ji a kunnayanta masu nuni da kamar wannan motar da ta kadeta ta soja ce

A lokacin da hannu ya kawo dan juyar da ita domin ana yi mata magana ne kan tana farke kuwa? Ta yi shiru, ta yi bakam tana saurare har sai da ta ga alamun hannu zai taba jikinta ta dago da sauri tana dan ja baya hadi da kurawa kakin jikinsa bakake irin na police ido lokaci daya tana fadin" Ka ga kar ka taba ni, ina wanda ya kade ni ne?"

Datijon da ya zubawa kyakyawar halitar ido ya yi dan murmushi yana fadin" Motocina ne suka samu hadari da ke yan mata, ina fatan baki raunata ba? Bismillah kawo hannunki na taimaka maki ki tashi"

Wani shegen takaici mai zafin gaske ne ya taso mata a cen kasan zuciyarta, yanzun du irin wannan wahalar da kasadar da ta yi da rayuwarta dama da mai kaki zasu hade ? Gaba daya sai ta ji hakan da ta yi bashi da anfani, wannan police din kuwa take ji a kasan zuciyarta da idan ta zage shi zata wanye lafia da ta aikata ta ji sanyi a kasan zuciyar tata

Da baya da baya ta sake ja tana girgiza kanta hadi da fadin" Ba sai ka kama ni ba zan iya tashi "

Tana fada ne tana son kama motarsa ta mike da kyar tana sauke mawuyaciyar ajiyar zuciya ta juya tana faman fadin" Ba sai kun rike ni ba ban ji rauni ba, aa ba sai kun rike ni ba ban ji ciwo ba....." A haka har ta samu ta ratsa mutanen ta wuce tana jin takaicin mai kaki a zuciyarta, ta tsani soja, soja bai yi mata ba sam, tana da dalilai na tsanar soja a rayuwa, soja yana da baban kamasho a cikin zanen kadarta!

Da kyar ta samu ta yi wata kwana ta zauna jikin garu tana janyo kafafuwanta jikinta hadi da sauke nanauyar ajiyar zuciya a bayane ta ja tsaki tana bude hannunta zata fara yin magana ta ji wata murya mai laushi an yi mata salama lokaci daya mai muryar kuma ya rage tsayinsa yana kallon kafarta da ta janye abin rigarta sama kadan har zuwa idon sawun kafar tata A hankali ya ce" Bai dace ki zauna a nan yar kyakyawa ba bayan motar soja ce ta kade ki? Na so ki ba sojan cen wahala ki saka shi daukan ki da kai ki asibiti , ki langwabe ki saka shi daukan ki a hannunsa ba a cikin kujerar tuki ba, shima mu saka shi yin gumi kamar yadda yake son gannin ya wahalar da mu a duniya......ko kina son ce min bakya sha'awar ganninsa yana tafe yana share gumi a gaban goshinsa?"

Tunda ya dukan bata dago ta dube shi ba sai yanzu da ya gama karewa soja wulakanci Da murmushin da ya subuce mata ta dube shi tana shirin yin wata maganar ya yi gagawar fadin" Wauh, masha Allah, ur splendid yar budurwa , kin ga I'm Sudais ke fa?, Na san sunnanki ba zai wuce Zahra'u ba domin kin hasken idannuna tunda na kyalo ki a wajen nan a zaune"

Kanta ta dan cire a kansa a kasan zuciyata tana ayana' Ba dai surutu ba shi wannan' A bayane kuma sai ta furta" Am SHUWWAR "

" SHUWWAR, unik, magnifique, SHUWWAR, ko zaki taimaka min na samu na kaiki likita ya duba min kafarkin nan da kika dingiso da ita daga cen har zuwa nan?"

Watau ba zaku gane ba, a duniyar SHUWWAR tana matukar kaunar ta ga ana caring dinta, idan ta ga mutun ya bayana a gareta da wannan espri din, gaba daya tafia yake yi da imaninta, 'shin idanma ba maza ba akoy abinda ya kai ku bi maganar Allah ne a kan matayenku? Ku kula da mu, domin mu din halita ne masu rauni mana.....ama da yake kawunanku na daidai da jikinku sai kunna daga mana kai' ta samu kanta da ayanawa sannan ta wani shagwabe fuska irin an samu abinda ake so din nan ta mula kai a hankali ta ce" Ba zan iya tashi ba, kuma gashi bana kama hannun namijin da ba muharamina ba"

Murmushi ya sake yi yana karra kallon yarinyar a kasan zuciyarsa yana ayana' Tabas wannan ta yi, abana da yake faman na fitar da mace gata Allah ya bani sai hankalinsa ya kwonta, ka ji malan bama zata iya bari na tabata ba, a gaban idannuwana kuma ta ki police din cen ya tabata, wannan ita zata kasance uwar y'ayana, ta zamto a kilace a fadata, na juya abina son raina domin da ganni wannan irinsu ne basu da ummm basu da ummm, ni dama burina na zamto sarki a cikin gidana , idan mu ba sarakai bane a duniya ai dole mu mulki mace ko dan yayan bankin da muka malaka zata yi mana biyaya ne'

Mikewa ya yi bayan ya ce da ita yana zuwa, ya shiga dube dube a anguwar Da kyar ya samu dalbejiya ya kama da kyar ya karyo reshenta ya fige ya dawo yana fatan Allah ya sa bata gudu ba duda da gangan ya ajiye wayarsa a gefenta yana tunanin a inocent face dinta ba zata saci wayarsa ba, haka kuma ba zata tashi ta bar wayar a nan ba

Ai kam murmushi ya saki a lokacin da ya ga tana nan zaune ya karaso a hankali yana dukawa ya mika mata icen irin na gentle man din nan ya kashe mata ido daya yana furta" Bismillah madame"

Murmushi ta kuma sakar masa ta amshi icen ta kama a hankali ta mike ta shiga dan dogarawa ta nufi motarsa

Sai da ya gyara mata mayafinta ya ajiye jakarta a gaban motar sannan ya zagaya ya shiga ya tada ya kama hanya

A lokacin da suka nufi wajen likita ya dubata suka fito ya tsaya a pharmacy ya siya mata magungunna sannan suka sake shiga motar yake tambayarta ina ne gidansu a lokacin ta shiga tunanin abinda zata iya fada masa amsa

A sanyaye ta ce" Me zai hanna na shiga adaidaita sahu na karasa gida ne? Malan Sudais sai wahala nake baka bayan ba kai ka bige ni ba?"

Sudais da irin nasa salo ya yi murmushi yana furta" Dama sai kai ka bige matarka zaka tayar da ita ne? Ai ko wa ya bige min matata zan tayar da abina ne"

Jama'a idan ciwo ne ke damun IBTISAM a kan maganar aure ku sake tabatar da cewa ciwon nan ba karami bane bata kuma tunanin idan har ciwon nan zai iya barinta wata rana ta sarara

Samun kanta ta yi da kokowa da tunaninta hadi da dantse lebenta ta rufe kanta a saman cinyarta irin ta ji matsananciyar kunyar nan bayan hanna kanta take da karfi da yaji tanaiwa kanta fada kamar haka' Kar ki zama daga gannin sarkin fawa sai miya ta yi zaki mana SHUWWAR?, Ki yiwa Allah kar ki tambayeshi yaushe zai turo magabatansa, ki yi hakuri ki tabatar idan da gaske yake sai ki masa maganar idan auren yake so a yi, idan kuwa shegantaka ta kawo shi ya karra gaba, SHUWWAR ba haka ake aure ba sha nawa Fauziya ke fada maki tana karra fada maki cewar ba kowani namiji ake rika a matsayin mijin da za'a aura ba, a cikin maza ko wani iri ne ya iya tausasawa a gaban mace idan ya zo neman aurenta, da zarar ya samu kuma yana iya mayar da rayuwarta tamkar ukubarta, sauke numfashi SHUWWAR sauke numfashinki, tauna kalamanki, tausasa muryarki, nuna masa bakya so, zaki iya, zaki iya SHUWWAR nuna masa bakya so wani irin aure daga haduwa? Fatatakeshi ki bude motar ki yi tafiyarki zai biyo ki ne yana magiya, oh yeah ke fa mace ce, kina da sarauta SHUWWAR, ke din sarauniya ce SHUWWAR maza maza yar albarka ja zarenki na mata murda kambunki na mace go, go SHUWWARIN NAHIDT DA ABA'

Dagowa ta yi a lokacin da ya cika da farin cikin irin kunyarta har ya budi baki yana fadin" Kunyar nan ba zata gyara ni ba SHUWWAR, ki sani a maganar neman aure babu irin haka, kar ki sako kunya a gaba ki cuce ni ki kuma cuci kanki, ki bani dama na gabatar da ke a gidanmu a nema min aurenki, idan hakan ya samu kin taimake ni, SHUWWAR ko dai ban maki ba? Ko dogo fari kyakyawa kike son aura ba ni baki ba? Ko dai kin fi son mai kyau kamar su sharukhan ba ni bahaushe mai muni ba?"

Maimakun ta dauki shawarar da ta gama yankewa cewar ta nuna ita mace ce mai aji, sai ta ji bakinta har da yar gagawar nan ya bude yana fadin" Wani irin bakai min ba kuma Sudais, wace mace ce zata ganka ta ce bata sonka?, Ni kam ka min sosaima......." Tsit ta yi tana fifitar da idannuwanta lokaci daya kuma tana rufe bakinta da hannayenta kafin ta sada kanta tana ala wadai da dabi'u irin nata A birkice ta so lalata masa fara'ar da ta kwonta a kan fuskarsa tana fadin" Sai dai ban san ko yayata zata aminta da kai a matsayin mijina ba"

Fara'ar dake saman fuskarsa ce ta fara gushewa lokaci daya kuma yana ayana 'yayarki? To ina iyayenki da furucin yayarki zai fara fitowa a matsayin wace zata iya hanna ki aurena?'

A bayane kuma sai ya ce" Ai da sauki idan dai ba su Aba bane suka ki hakan"

SHUWWAR ta juyo da duke duken kan da take yi tana kallonsa ta ce" Su Aban, ai sun rasu, ita kadai ce ta rage min, ita ce take da wannan damar"

Har ga Allah sai da wani irin tausayinta ya kama Sudais harma ya kasa boyewa a bayane ya yi ta yi masu adu'ar kwonciya hutawa da gafara a wajen Allah sannan ya nemi da ta kwatanta masa gidan nasu su karasa

Wannan karron ba ja ta kwatanta masan suka dauki hanya suka nufi gidansu

A takaice a ranar nan sai da ya jima sosai a kofar gidansu kafin yake tafia inda ta tsaya tana hangen motarsa har sai da ta bacewa ganninta kafin take sauke ajiyar zuciya ta juya da sauri ta zarro ky dinta tana budewa tana fatan Allah ya sa wannan din shine mijinta, wanda zai zauna da ita da zuciya daya

Zuciyarta fessss ta fada saman gadonta tana sauraron jiran kiran sallah daga Abanta, liman din anguwar, wanda shine ya siyar masu da gidan nan ciniki mai kama da kyauta kyauta a lokacin da suka bukaci siyan bayan mutane da yawa suka so yi masu bukulu ta yadda zai ki siyarwa, sai dai Allah ya yi shi din mutun ne dake tsaye a kan kafafuwansa mai aiwatar da dukan dabi'u da mu'amalarsa domin Allah ba dan tsoron wani ba

Sake yin shiru ta yi dan tana jira ta ji liman ya yi kira ta yi sallah sannan ta je ta yi jiransa ya fito ta fada masa ta samu wani mijin , domin shine mai daura mata aure, shine mai yi masu nasiha, shine mai yiwa mutanen anguwa nasiha kan su shafa masu lafia, shine mai jin kansu yana basu daraja irin ta kowasu y'aya masu yanci a duniya, shine ya sake kwadaita mata ladan aure da kaunar yin aure a zuciyarta domin ya kwatanta mata a bayane cewar rayuwar y'a mace ta yita a karkashin ikon mijin aurenta shine darajarta duniya da kiyama

_________________________________

Da mamakin ganninta a irin wannan lokacin bayan a barinsa da ita bayan ya bata sadakinta ne ya mata nasiha yake amsa gaisuwarta yana sake gyara zamansa a saman dardumarsa kafin ya ce" Aa, IBTISAM har kin fara fita ne a gidanki da wuri haka ?"

SHUWWAR ta sake sada kanta a sanyaye ta ce" Aba ya sake ni ne fa Elhajin"

Sai da ya rintse ido da karfi a lokacin da bai shiryawa hakan ba kafin ya bude idannuwan nasa yana kallonta ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, subahannalah wala haula wala kuwata ila bilah, subahannalah subahannalah subahannalah, wani irin saki kuma? Yaushema aka daura auren shi kuma wani irin abu ne ya gita haka ya sau ki?"

Da mugun kaunar Bawan Allahn da shekarunsa shi din kansa ba zasu wuce arba'in da biyar a duniya na a kasan zuciyarta na irin yadda karrara damuwa ta sakinta da akai ta bayana a tare da shi bayan basu hada dangin ina ko na aba ba da shi take kallonsa kafin ta ji zuciyarta na neman tsinkewa.......................................................................mmmm💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 7️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

Readers Also Read